Showing 9001 words to 12000 words out of 69951 words
lumsasaun Idanunsa tamkar mahaifiyar tasa ce agaban sa,Ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi,yana ƙara lumshe birkitattun idanunsa.
yana jin yadda namomin jikinsa suka ɗauka rawa, daga cenñnn ƙasar zuciyarsa kuwa wani irin mugun zugun masifa yake ji. Kife kansa yayi da tafin hannunsa yana cusa kansa tsaƙiyar cibiyoyin sa.
Daga nan bai kuma koda ɗagowa bane har Saida yaji an buɗe masa ƙofar motar, alamun sun iso keñan.
Kai tsaye yana fita wajen sink ya nufa alwula ya ɗaura domin anata ƙiraye ƙirayen sallar magrib ne, hakan yasa suma sauran yaran nufar gaban tarin sink ɗin dake jere reras suka shiga ɗaura alwular suna take masa baya wurin bautama mahaliccinsu.
Sune ne basu dawo gidan ba sai wajajen ƙarfe taran dare, a parlourn suka dakata suka fara shirya dining ɗin domin suna buƙatar suyi ɗinner.
A nutsen sa ya shiga saƙƙowa zuwa loƙacin 9:35 ne, ahankali ya doshi kan dinning ɗin nasu yana baza wannan mayataccen ƙamshin nasa cikin shigar short trouser fari da kuma vest blue wadda takara haska farar fatarsa,yau kammm ko ƴar p-carp ɗin babu saman kan nasa, hakan shi ya bama lallausar baƙar sumarsa bayyanu wacce aka yima wani irin kwalliyar dada, gefe da gefen kuma an kitse shi sai tayi shilim a tsakiyar kan sa tare da sakkowa har ƙeyarsa, wani irin shining take yi na tsabar kyau da makudan kuɗaɗen da ake narka mata.
zama yayi yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tare da buɗe wani kyakkyawan food plask lafiyayyan tuwon semo ne da jar miyan dage dage domin shine abu mafi sauƙi daga cikin jerin abinciccikan boss ln nasu, kuma dama best favorite food nasa kenàn, idan kana son ka birgisa to ka masa tuwon semo.
Duk da baya a yanayi me daɗi hakan bai hana fuskarsa nuna jin daɗin saba.
Barka da dare suka masa kafin axton ya matso ya fara saving nashi, tuwon semon ya zuba mishi , ya ɗora masa A gabansa tare da sanya masa spoon a ciki,
karamin cup na glass yaja yana tsiyan ya masa win with alcoholic a ciki, A hankali ya fara feeding kansa, ya danci da dama kafin ya ture plate ɗin, wannan glass cup ɗin ya ɗauka tare da fara sipping nashi tamkar wani King. Tsammm ya miƙe yana komawa saman sopa tare da jan shisha ya shiga zuƙar ta yana fesar da hayaki.
Suma Abincinsu suke ci hankali kwance, suna kammala cin farar shinkafa da jar miyar suka miƙe tare da zagaye boss ln nasu. tamkar wanda zasu hana zarar ransa idan loƙacinsa yayi.
Wayar sa ya ɗauka kawai yawuce warsa bedroom, cikin tafiyar ƙasaita wadda sarauta tagama ratsa jinin jikinsa. Yau kam babu aikin babu aikin daya tsaya yi kai tsaye kwanciyar sa yayi bayan yayi adda'oin barcinsa kamar kullum.
♥️🤍🤎
*MEERAH*
Kamar kullum gidan na nan kamar kasuwa, duk uban sallamar data rinka yi amma babu wanda yayi ƙoƙarin amsata, itafa har mamakin gidan su take yadda abubuwa suke tafiyar musu tamkar irin gidan jahilan nan, kanta kawai ta sanye xuwa barandar da mahaifiyarta take zaune tana aikin zuzzuba humra cikin kwalabe.
Zaune takai dab da mahaifiyar nata tana faɗin "AMMANMU sannu da aiki!, ina raiha tayi ne naga ban ganta ba?"
Dago kanta wacce ya kira da amman tayi tana cewa "yawwa meerah raiha na ɗan aike ta ne bayan layi, gidan jajiya kareemah zata kai mata humra"
Nooding kanta kawai tare da cewa "Ina Affan naga ban ganshi ba..... Kafin ma ta rufe bakin saiga wani ɗan bakin yaro nan a guje irin ɗan shekara shida ɗin nan zuwa bakwai, a guje ya faɗa jikinta tare da faɗin "oyoyo aunty meerah na!"
Rungume shi tayi tana sakin dariyar farin cikin nan ta buɗe bakinta kenan da niyar yin magana, gaji an wani janye shi a jikin ta.
Cikin haki da masifar dake cin gabjejiyar matar dake tsaye ta rike hannun yaronta ƙammm, "meerah ki fita a harkan Affan fa, ko sai kin iskan tamin da?, duk yaran gidan nan da suke nan ga sunan kamar jamfa a Jos, amma duk babu wanda kika liƙema sai ɗana dalilin ki iskanta min ɗa ko?, to wllh bari malam ɗin ya dawo bazai yiwu ba dole ne yau na datse alaƙar dake tsakanin ki da Affan"
Kanta dake mata ciwo ta riƙe domin dama komai take yi dauriya ne kawai sharrrrr wasu hawayen takaicin familynta ya saukar mata,
_Wai sai yaushe kan family's nasu zai haɗu wuri guda?, sai yaushe zasu gane Allah da girma yake?, yaushe ne zasu san daɗin zumunci da ƴan uwan taka, gidan mu ya kasance wani irin gida ne me cike da son kai da son zuciya, kowannensu yana tafiya ne ya kife kansa kaɗai ya sani da rayuwar yaran sa.
Gidan mu yafi karfin a ƙira shi da ko wanne irin suna, domin kafff iyaka bincike na na gaza samun sunan da yayi daidai da rayuwar gidan mu, kawai zan baku abin a dunƙule ne kowa yaje ya nemi fassara!.
Mahaifin mu malam Abdullahi gwani yana da mata huɗu, duk wani haƙki na uba ɗa yana bamu saidai sammmm iyayenmu basa taɓa fashimtar hakan, kullum babban burinsu shine meda gidanmu filin yaƙin sunƙuru dana fili.
Ga yawan tarin iyalan da Allah ya bashi, gamu da masifar dangin kamar tsaƙi amma sai ka kasance jajirtacce ɗan zamani zaka zauna da kowa lafiya a sannu a sannu muna tafiya, zaku fashimci halin kowa da kuma manufa na_
Wannan keñan
Amma dake zaune tana ci gaba da zuzzuba humrarta cikin kwalabe idan ƙasa tana magana to kuwa tayi ita ma, haka Maman Saude ta karaci bala'inta tayi gaba ita da Affan dake ta kuka, yana miƙo min hannu, sai tallar ƙeyarsa take.
Na yunƙura zan tashi keñan ƴar ƙaramar wayata irin tecno common ɗin nan tahau ruri cikin waƙar hamisu breaker me taken _Kada ki bari zuciya ta zuga ki_ saurin kallona Amma tayi tare da tsare Ni da manyan Idonta wanda duka muka gada daga gare ta, Cikin in ina nashi ga faɗin.
"M.... MD ne, Ammah wai yana son za'a fira dani, kuma kinji wai dole sai dani za'a yi firarn, bayan duk ga su mardiyya nan su hayatu amman dole sai dani za'a yi wai"
Kanta ta mayar taci ga
*🦅 MIKIYA 🦅*
{Mai hangen nesa 👀}
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH
____________________
*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 7&8
🤍🔥✅
Aikin ta ba tare da tace komai ba, haka yaci gaba da ƙiran Ni ban ɗaga ba kuma ban tafi ba.
"Ki amsa shi, Idan kuma baki so ki bashi amsa ki dena ja masa rai har haka!"
Ganin abinda nake son ta fashimta ɗin bata fashimta bane, ya sani faɗin.
"Fuskata za'a haska a yayin firan Ammah!"
Saurin ɗagowa tayi tare da dubana sai kuma tamin nuni dana shige ɗakin kawai, alamun bata son maganar. Handbag ɗina na ajje a kan doguwar kujerar dake parlourn mu, dake ciki da parlourn ne dakin namu, kayan jikina na rage ina faɗawa kan kujerar tare da kwanciya bayan nasha maganin ciwon kan.
A take nannuyan barci yayi awon gaba dani, ban farka ba sai bayan sallar magrib, daƙyar nake Iya buɗe ido na sabo da nauyin da suka min, Adda'ar tashi daga barci nayi tare da tashi ina fita alwula na ɗauro na data salla ina zaune na haɗe kaina da gwuiwa na abin duniya duk sun gama sanyoni gaba raiha ta shiga ɗakin, zama tayi kusa dani tare da daura kanta saman ƙafafuna tace, "Yaaya kije Inji baffa yana ɗakin zaure"
Dammmm gabana ya bada sautin bugu baffa kuma yake ƙirana a irin wannan loƙacin kuma. Jiki babu ƙarfi na miƙe ina fita tare da nufar ɗakin zauren.
Da sallama na shiga ya amsani tare da nuna min wurin zama, zaman nayi tare da gaisa shi ya amsani a nutse, "ko miye dalilin daya sanya Maryam ƙin amincewa Md firar da ake son yi da ita?"
Kaina sunkuyar ina wasa da yatsun hannuwana cike da ladabi na furta, "Videon kai tsaye ne za'a haskaka ma duniya!, shi yasa sammm naƙi aminta da hakan, domin acikin sharruɗanka babu ɗaukar video!"
Wani gwauron Numfashi ya kawo ya sauƙe tare da dubana, "A gaskiya banyi tunanin haka abin yake ba amma kije babu komai kije ayi firar kariyar Ubangijii yaci gaba da tabbata a gareki, Allah Miki albarka tashi kije"
Da saurin umman mariya ta ɓoye bayan bishiyar dake kofar fita a dakin, domin dama badai iya laɓe ba, Ni kuwa banma san tanayi ba tunda cikin yanayin dana kasa gane masa na baro dakin.
*AK*
Ahankali cikin nutsuwar sa yake saƙkowa daga upstairs nashi zuwa wangamemen parlourn gidan, loƙacin sha ɗaya da minti sha biyu, kunga kenan minti uku ya rage masa.
Zamani tv
Duk da kasancewar yau kwata kwata bata niyar zuwa wurin aiki, amma haka ta danni zuciyarta ta fito tun sha daya saura, gudun kada tayi lettt, sai gashi kuma har yanxun wajen sha ɗaya da minti goma shiru shiru babu labarin zuwan nashi.
Ɗan madaidaicin Agogon Rolex ɗin dake hannunta ta shiga dubawa ganin har sha ɗaya da mintinan ashirin da biyar tayi bai iso ba, hakan yasa ta jan ɗan ƙaramin tsoƙi, domin jira na ɗaya daga cikin abinda tafi tsana a cikin rayuwarta. Na miƙe kenan ina fita daga cikin department namu wasu irin fitattun narkakkun motoci guda uku suka sanyo kansu cikin coumpaund na gidan jaridar namu, hakan ya sanya ni ja baya ina komawa cikin dakinmu inda mardiyya ta shiga tsokana wai kwana biyun nan kamar wacce akama turen rashin son magana, nidai ci kanki ban ce mata har zuwa loƙacin da Md ya ƙara so cikin department namu, cikin wani irin rawar jiki sai faman zazzare idanuwa yake ya tsohon maye.
A kaina ya fara sauƙe Idanu, cikin rawar murya ya furta, "MEERAH da dukkan alamu wannan baƙon namu wani ƙusar ne ke kinga wasu irin rantsantstsun motocin da yazo dasu?, tare da wasu samudawan escort, baki ɗayan sa tun daga ƙafarsa kamo fuskarsa a rufe suke cikin wasu haɗaɗɗun suit baƙaƙe ke hatta takalmin ƙafarsa abin kallo ne, maza yi sauri ki fito, kana ki tabbatar kin cire wannan liƙabin da kika kwama a fuska"
Ko amsata bai ji ya fice harda haɗawa da ɗan gudu gudunsa, yake zai shiga kenan ya kusa cin karo da hancin bindigar dake hannun miles, wani irin zaro Idanu Md yayi, domin shifa sai yanxun ma ya kula da uban manyan bindugun dake hannuwansu, kuuuuuuu cikin sa ya bada sauti, gumi na keto masa, miles dake zuƙar cigarettes Samm bai kula da yanda ya tare hanyar da bakin bindigar saba, hakan ya sanya shi saurin janye wa yana tsare Md da firgitattun idanunsa da suka kada sukayi zajurr. A gujeeeeeeee MD ya zura har yana neman hantsilawa "innalillahi wa'inna ilair raji'un, me yake shirin faruwa damu kodai kidnapped namu aka zo yi "
Ya faɗa a bayyane amma sai ya daure yana ƙaraso cikin Office ɗin nasa.
A ƙalla Saida na ƙara wajen 10 mint da fitar Md ɗin, kafin na fito, Nima dai ganin wannan samudawan hannuwansu riƙe da manyan bindugun Saida ya razanani, amma na dake don nasan matsoraci baya taɓa zama gwani.
Haka na ratsa tsaƙiyarsu na fice cikin takun daya fi kama da a ƙira shi dana yanga, saidai sammm ba haka bane haka Allah ya halicceni, zuwa wannan loqacin tuni wanda yake zaune harya fara fusata da zaman jiran yarinyar da murya ta kaɗai yaji, don ko photon ta bata yarda ta taɓa ɗaurawa a media.
Wani irin mahaukacin ƙamshim turare ne ya fara welcome nawa, tun daga bakin ƙofar, a nutse na sanya zara zaran yatsuna ina tura ƙofar Office ɗin, ya ɗago kansa da Nijar yama Md magana yaci karo da zanen jan lallein yatsun hannunta, kafin na bayyana kaina cikin qaton hijjabina da kuma niƙab ɗina.
Cikin ƴar siririyar muryata nayi sallama wanda Md ne kaɗai ya amsa ni banda mutumin dake haƙimce saman kyakkyawar kujerarn da nayi tunanin daga ina Md ya samo ta, don dai nasan Bama da irinta cikin kaffff gidan jaridar namu.
Banko damu da yadda duk mutanen dake cikin Office zubo min Ido ba, domin duk da ko ina na jikinsa a ɓoye yake amma sai suka gaza samun sukuni. kujerar dake pacing dashi naja na zauna,kasancer nasan shine nawa mazaunin. sai table ɗin dake gabanmu wanda ya raba tsakanin mu, an ɗaura glass cup guda biyu masu ɗauke da ruwa, sai dai an rufe su da ɗan ƙananun fai-fai.
Ta ƙasan ido na ɗan saci kallon sa dan koda na zauna ban tanka musu ba, ban kuma zare niƙa ɗin fuska na ba. Haka naci gaba da ƙare masa kallo duk kuwa da cewar bana iya ganin komi nashi, har yatsun hannuwansa kuwa abinda zan iya faɗi kawai shine da ganinsa ba karamin mutum bane, ko daga yanayin zaman da yayi irin na shahararrun sarakunan nan ba muna sarki ba, sai hujin dake kunnensa ta ɓangaren hagu ya sanya wani diamon ring barima color'n gold.
Ɗan taɓe baki na nayi tare da janye idanuna dake kansa, Cike da ladabi Md ya ƙaraso tare da maƙala masa abin magana a jikin jacket suit ɗinsa. Nima ya miƙomin na maƙala a jikin hijjab ɗina, Sai da aka tabbatar mun gama kimtsawa sannan aka ɗora camara a kanmu. A nutse na sanya fararen hannuwana ina janye niƙab nawa zuwa saman fuskana, cikin aro jarumta da bada attention Kamar bani ba, sai da na kalla cemara naima masu kallo sallama tare da gaisuwar barka da wannan loƙaci tare da fatarn sake kasancewa damu a shirin mu na kai tsaye, dangane da wannan bawan Allah dake son bamu ƙarin haske game da AK. (Wama ya sani ko AK ɗin ne) Na faɗa aceñnn ƙasar zuciyar, sai kuma nayi saurin faɗin (kai hakan ba bazai taɓa iyuwa ba, bayan ance shi kamar aljani yake kuma tunda yake babu wata cemara data taɓa haska shi aduk tsawon rayuwarsa, saidai kawai sunan daya karaɗe ko ina sabo da mumman aikinsa)
Saurin dawowa cikin hayyacina nayi dan gyaran muryan da aka min a take na dawo da ainihin nutsuwa na zuga ga dubban jama'ar da ke son kallon mu. Cikin tsare sa da Idanuwana duk da cewar bana iya ganin ƙwayar idon sane, na furta.
“Assalamu alaika ranka ya daɗe”.
A hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa min da “Wa'alaikissalam”
cikin muryar dake tamkar wanda akama dole. Kai tsaye zaka taɓa fahimtar kallona yake ko akasin haka ba saboda akwai eyeglasses mai duhu a idonsa. Bayan irin hular nan ta sojojin da suke sanya wa.
Yinai kamar ban damu da abinda yay ɗin ba nima, na cigaba da faɗin, “Wannan shiri na maka barka da zuwa, tare da nuna farin ciki matuƙa wajen zaɓarsu da kayi duk da bamu san dalilin ka nayin hakan ba, duk da bamu san waye shi ba"
“Barkanmu tare fatan Alkhairi ma duka jama'ar dake sauraraen wannan shirin!"
"To masu kallo zan iya cewa duk sai ku sake matsowa gaban akwatinan talabijin naku, masu rediyo su ƙara sauti domin ji daga bakin babban baƙon namu da musan waye shi ba!”
Sai kuma na sake juyowa garesa tare da faɗin, “Ko zamu iya sanin cikakken sunan ɓoyayyen baƙon namu?”
Wani irin kafirin murmushi ya saki irin na gefen bakin nan, Cike da wani salo ya sake harɗe ƙafafunsa da yay crossing cikin motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta. “ABDOUL-MALEEK KUWAIT"
“to Saidai kanmu ya daure da sunan baƙon namu, gashi kuma bama iya kallonka kai tsaye, duba da cewar kazo mana da batu ne akan wannan babban CRIMINAL ɗin Wato EAGLE, wanda ya kasance cikin aikata tarin ɓarnuka marasa ƙyau, wannan shi yaja hankulan masu bibiyar wannan tasha ta zamani tv jin batu ne akan CRIMINAL ɗin da ake nema ruwa a jallo!"
Wata zazzafar iska ya fesar daga cikin bakinsa na wasu sakanni sannan yay wani ɗan murmushin gefen baki, a taƙaice ya furta, "Kai tsaye ki ɗauka kina tare ne dashi wannan babban CRIMINAL ɗin da kowa ke nema ruwa a jallo"
Manyan Idanunta da suke kama da na mashayiya, uwa uba tsarin halitarsu da girman da suke ta ware baki ɗaya, tare da wani irin zaro su Wanda har saman fattar idon Saida ta ɗan kara faɗi kadan. Tana tsare shi dasu tamkar irin me tuhumar nan nasa, A nutse ya zare baƙin sun glasses in daya manne fuskar sa dashi, tare da kafe ta da nashi manyan Idon wanda kana kallon su zaka so fara kawar da dubanka, dan ba irin idannuwan da ake tsatsarewa da kallo bane, ga wani ruwa ruwa mai nuni da cewar Saida aka shawu kafin a fito,wanda ba dan ta kasance mai tsaurin ido ko mai taurin kai bane da taurin zuciya babu abinda zai hana ta kutsawa a gujeeeeeeee.
hasalima ana ƙiran da farar kurane amma Halittarta mai bayar da tsoron ce ita ma
Farar fuskarta dake ɗauke da kwantaccen gashi a gaban goshinta, wanda lafcecen hijabinta bai