Showing 24001 words to 27000 words out of 69951 words

Chapter 9 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8183

cike tsantsar izzar sarautar dake gudana a cikin kowacce magudanar jini ta jikinsa. Shade ɗin dake saman kyakkyawar Innocent face nashi ya zare tare da jona manyan na'urori room ɗin. Sosae ya ɗauki lokaci me tsawo a cikin Restroom ɗin don wajajen 2:30am na dare ya fito.

Bathroom ya faɗa wanka yayo me rai da lafiya ya fito sanye da blue bathrobe a jikinsa, farar fatar nan sai walƙiyar kyau da tsantsar jin daɗi take. Tsaye yakai gaban ƙaton mirror'n hannun sa ɗaya riƙe da ƙugunsa, ɗayan kuma yana sharce ruwan dake yarara saman jikinsa.




*🦅 MIKIYA 🦅*


*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 21&22

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# Treason
# Strong love
# Right
# Women's travel
# The Secret Society
# Oppression

# KIDNAPPER'S
# Informants
# DEEP
# BEST LOVE

🤍🔥✅

★★★★
_5:6Am_

Ahankali ya shiga ware lumsassun idanunsa da suka yimay nauyi sosae kasancewar daren jiya ba wani baccin kirki ya samu ba, Zara-zaran fararen sawayensa ya fara zirowa ƙasa tare da miƙewa tsaye daga shi sai tattausan farin dogon na bacci a jikinsa. Jikinsa babu riga hakan shiya bayyana ƙaƙƙarfan surur jikinsa ɗan ƙaramin hasken daya haska ɗakin ya bayyana shati shatin muscles nashi.
Bothroom shige tare da sakarma kansa shower ya gurguje yayi wankan haɗi da ɗauro Alwala, ɗaure da towel ya fita ɗayan hannunsa kuma riƙe da wani mini towel na daban yana tsane tulun sumar sa. Saida ya busar da lallausan sumar shi da Hair dryer tare da parking nata da robber beld. Har zuwa wannan loƙacin kuwa kyakkyawar Innocent face nashi babu sassauci ko kaɗan. Sanye ya fito cikin wata tsadaddar Morocco jallaba ta maza A nutse ya sanwo kansa cikin haɗaɗɗen parloun.
Dasu Axton dake tsaitsaye a parloun ya fara cin karo. Ko inda suke bai sake kallo ba duk kuwa irin yadda suke miƙo gaisuwa. Masu sallah ne daga cikinsu suka rufa may baya dama jiran fitowar Boss in suke.


6:20am. Suka shigo gidan baki ɗayan su a parlou suka dakata shi kuma ya nufi ɗakin da Meerah take cikin majestical takunsa.
A nutse ya sanya zara zaran fararen hannunsa ya tura room ɗin, Wani irin tsayawa chark yaji zuciyarsa tayi sakamakon daddaɗan sautin karatun Alqur'anin da kunnuwansa suka jiwo mashi. A hankali ya ware lumsassun idanunsa tare dabin wurin da sautin karatun yake fita da idonsa.
Jingine take da jikin gado idanunta a lumshe hannuwanta duka biyun suna a saman gadon ne. Karatun take rairawa cikin sassayan sauti irin mai raunata zuciyar nan tamkar *AFIf MUHAMMAD TAJ* wannan shashararren mahaddacin Alqur'anin mai girma wanda yayi shura a duniyar yanar gizo dama duniyar baki ɗaya. Har yadda yake motsa lower lips in nan nashi haka meerah ke karatun cikin sanyi da sanyaya zuciya cikin suratul YUSUF.

Kafeta yayi da catly eye's nashi yadda karatunta ke ratsa zuciyarsa, da kuma yadda hawayenta ke sobbing ahankali a saman kyakkyawar fuskarta. Samun kansa yayi da motsa nashi lower lips in ta hanyar binta. Jingina yayi da jikin ƙofar tare da jan idanunsa ya lumshe duk wani tarin ƙunci da zafin zuciyar da kansa ke ciki ya nema ya rasa loƙaci ɗaya.
Ahankali ya shiga buɗe idonsa dake a lumshe sakamakon yadda yaji a jikinsa kallonsa ake, 4 eye's suka yi shida Meerah domin samm itama bata san zai buɗe idon har ya kamata tana kallonsa ba.
Luuuuuu yay kamar lumshe su amma kuma bai lumshen ba hakan yasa tayi saurin kawar da kanta daga kallon kurillar da take may. Folding hannun sa yayi a saman ƙirjinsa tare da harɗe ƙafafunsa wuri guda.
Saurin ficewa yayi a ɗakin Kamar wanda ya tuna da wani abu.

Zaune yakai saman turkish Royal bed insa tare da cusa hannuwansa cikin kwantaccen gashin kansa. Ƙarar da woyansa ya ɗauka ne ya dawo dashi hayyacinsa, Dubawa yayi ganin sunan
*Armstrong* ya bayyana shine ya sanya shi peak calling ɗin tare da manna woyar a kunnensa.
"BOSS I'M BACK"
Aka faɗa daga cikin woyarsan. Wani lalataccen murmushi Ak ya saki tare da furta.
"Ur well come 2 u Lion🦁 🫂"

Daga tacen ma murmushin shima ya saki yana faɗin

"thanks U Sir"

tare da sara masa don har ƙarar ƙafar daya buga Saida Ak ɗin yaji, kasancewar sa mutum mai kaifin ji.


★★★

Tun ya fito tarin guard ke famar sara mishi har ya nufi kitchen fridge ya buɗe. Anan ɗin madai tarin maid ɗin dake ta faman ayyukansu ne suka shiga kaida shi cikin girmama, domin kowa dake gidan yasan matsayin Armstrong ɗin. Kai tsaye Grilled chicken, Chicken cutlet, Shredded sauce ɗin da suka gama shiryawa tamkar a restaurant ya bubbuɗe Saida ya gama research na komi dake kitchen ɗin, kana ya ɗauka
tare da ɗauko ruwa me sanyi sosai guda ɗaya ya ɗauko ɗaya marar sanyi tareda glass cup ya jerasu a trey, kana ya fita kai tsaye ɓangaren Ak ya nufa.
Tun daga farkon shigarsa parloun har zuwa ƙarshensa gaisuwar ban girma Armstrong ke karɓa daga zaratan samudawan Ak ɗin.

Knocking yayi ahankali Shiru babu alaman Ak ɗin ma yaji baiyi saurin sake knocking ɗin ba ya ɗan Jira na kamar 3 mints kafin ya sake ɗan buga ƙofan a hankali.
Ahankali ya buɗe idanuwansa a ɗan galabaice domin baccin daya fara bawai ya gama ɗaukar sa bane duka, ɗan kallon ƙofar yayi cikin qaramin sautin da baiyi tinanin ma za'a ji ko ba za'a jiba furta.
"Come in!"
A nutse ya murɗa handle ɗin bedroom ɗin tare da shigowa, ni'imantaccen sanyin da kuma qamshin da ɗakin Ak ɗin keyi Armstrong ya shaƙa. Da kyakkyawan murmushin da shine kaɗai ke iya samu daga Ak ɗin ya tarɓi Armstrong ɗin.
A nutse Armstrong ya ajje trey in tare da ɗan hugging Ak ɗin, wani ƙayataccen murmushi Ak ɗin ya sake saki a karo na biyu tare da ɗan tapping gadon bayan Armstrong ɗin tamkar wani yaro. A tare sukayi breakfast ɗin bayan sun kammala suka nufi study room ta cikin ɓoyayyar hanyar da daga Ak ɗin sai Armstrong ne suka san da ita. Wasu abubuwa masu matuƙar mahimmanci saisae Armstrong yama AK bayaninsu bayan ya gama zana masa su a bayyane.
Daga nan computer room suka kuma nufa anan kammm sun ɗauki loƙaci baɗan kaɗan ba. "Yes Boss na fahimta Insha Allah ba za'a samu matsala ba"
Saida Ak ya rumtse idonsa da ƙarfi tare da matse hannuwansa, shifa a cikin rayuwarsa ya tsani jin wannan kalma ta matsala. Noding kansa yayi tare daci gaba da numa Armstrong duk yadda yake son komi ya tafi masa a yadda ya tsara.



*ISA MANU EMFIRE*

*Salman POV*

Ahankali yake saƙƙowa daga stairs zuwa katafaren falon dako gidan shugaban ƙasa sai haka, ahankali yake saƙkowa yana yi yana duba tsadaddar agogon deke ɗaure da tsintsiyar hannunsa.
Daidai loƙacin wata babban mace da a ƙalla zatai 57 tana sanye da shiga na alfarma, tabuɗe ƙofar wani ɗaki wanda ga dukkan alamu kitchen ne sabida ƙamshin girke girken daya cika ko'ina tafito bayanta kuma wata maid ce dake sanye da uniform ɗin masu aiki tana riƙe da babban warmer da alamu abinci ne aciki.
Tsayawa tayi bayan matan itama ganin uwar ɗakin nata ta tsaya itama, wani ƙasaitaccen murmushi ta sakinma yaron nata kafin ta ware masa hannu, Cikin ƴar tafiyar sassarfa Salman yazo ya ɗan yi hugging Mom nashi. "Good morning My love"
Ta faɗa ba tare kuma tajin amsar shiba ta tubi wannan maid ɗin tare da furta.

"Zeeynab kai kulan dining"
sanan tacigaba da tafiya wuceshi tayi tai dinning taja kujera tazauna taɗau mug tareda buɗe flask ta tsiyayan ruwan zafi sanan ta waigo ganin har lokacin yana tsaye inda ta barshi yasa ta furta "anan zaka tsayane ne ba break zakayi ba"
Saurin janye idonsa yayi daga mayen kallon da yake bin zeey dashi. Rashin ƙin masa magana da tayi ba ƙaramin ƙona ransa yayi ba ko a daren jiya ƙira nawa ya mata taƙi ta amsa. In banda ma samun wuri har tana ƴar aiki shi Salman Isa Manu ya ɗau waya ya ƙirata taƙi ta amsa. "Hmmmmmm!" Yaja ajiyar zuciya tare da nufar dinning ɗin.

"We're in my daddy?"

Ya faɗa yana kallon Mom nashi, "na mishi magana kasan shi da shegen baccin tsiya mebi komawa yayi" ta faɗa tana wani yatsine fuska. "Keeee zeey yi maza je bedroom ɗin Alhaji ki sake may magana"
"To!"
Ta amsa tana yin sama da wani irin munafin kallo Salman ya bita, A hankali ba tare da knocking ko neman a bata izini ba ta murɗa handle door ɗin ta shiga bedroom kanta tsaye, fitowar sa daga bathroom kenan yana sanye da rigan wanka jikinsa sai ɗigar ruwa yake. Wani shegen kallo zeey ta shiga bin jiki Isa Manu dashi. Shima kallon ya shiga binta dashi da hannu ya mata nunin tazo. Har da ƴar sassarfarta ta haɗa wajen zuwa gare shi saman jikinsa ta faɗa.
Wata shegiyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da naɗe ta da hannayensa a cikin jikinsa, hannunta ta cusa cikin tsakiyar ƙirjin sa tare da kwantar da kanta a jikinsa tana furta "I miss U Alhajina"
Wani jahilin murmushi ya saki irin wanda saidai kaji sautin fitar san nan. Kafin ya fara ƙoƙarin tura hannunsa cikin jikin ta, da sauri ta zame daga jikinsa tana faɗin.
"Sorry Hajiya ce tace ka fito breakfast"
Taga haka tayi saurin barin ɗakin gudun kar tayi lett. "Hajiya yace yana zuwa" wuff ta faɗa kitchen daga haka, tsamm Salman ya miƙe shima yana nufar hanyar kitchen ɗin, "Ina kuma zaka je?"
Mom ta tambaya.
"Coffee zansa yarinyar cennnnn ta haɗa min naga babu......
Ta baya kawai taji an rungumata shiru tayi domin gudun kar tayi kuskure, domin tasan tana tsaƙiyar damisai ne masu farauta.
"Me yasa jiya nata ƙiranki kizo ki tayani kwana amma kika ƙi amsa woyana?"
Salman ya faɗa yana ɗaura haɓarsa kan wuyanta, "Ina bacci ne ban san ka ƙira ba" ta bashi amsa itama. "uyummmmm to yanxu da kika shareni fa? Ko shima baki gannin bane?" Ya sake jeho mata wata tambayar " kana son Hajiya tasan alaƙar dake tsakanin mu kenan?" Itama ta jefa masa Tata tambayar shiru yayi domin yasan baya da amsar da zai bata.


"Daddy's boy wai me kake a kitchen ne bayan kuma kasan kai muke jira! Kana karka manta yau muna da fita ma"
Saurin zareta a jikinsa yayi tare da fitowa yana faɗin "Naga tana wani aikin ne shi ne nayi tunanin ɗorawa amma nama fasa kawai right"
Zama yayi tare da furta "good morning daddy.....
"Morning how are you doing today daddy's boy.......
"Fine with you?"
"ALHAMDULILLAH" daga haka kowa yaja abinda ransa yake so suka fara breakfast nasu, good 30 minutes suka kammala suna gamawa bayan sun wanke hannayensu Salman da Isa Manu suka fice zuwa gidan iyayen MEERAH wanda a yau suke son cika ƙudirinsu.

★★★
*AK*

Gudu sosai bugaggun motocin suke akan kwaltar da zata sadaka da wannan rantsatstsen Company'n na *LIVESTOCK AND FEEDING INTERPRICESS* duk inda suka gilma mutane basu hanyar wucewa suke, dubada da irin uban gudun da motocinsu keyi na tashin hankali. dukkan hanyar da suka biyo kowani mai abun ha wa  ƙoƙari yake ya basu hanya kar a halakashi. Wasu na Allah wadai da su wasu kuma na musu fatan shiriya ne kawai.


Ahankali yabuɗe idanunshi jin motocin sun tsaya buɗemai motar Armstrong yayi da sauri, fitowa yayi yana bin parking space ɗin wajen da kallo dayaji flowers da kallo komi looking neat a perfect kaman a dubai,
wani guy ne fari dogo ya ƙara so wurin yana sanye da baƙin suit da necktie a wuyansa hannunsa riƙe da Ipad ƙirar apple. Cikin girmamawa ya sarama Ak ɗin da yake jingine da jikin motar yayi folding hannun sa a kan ƙirjinsa.
Duk da yasan bai zama lallai ya amsa shi ba, Drectly cikin tamfatsetsen Company'n suka shiga, Armstrong, Axton, miles, ne kaɗai suka mara musu baya, duk inda suka gilma sai kaga idanu caaaaaa akan Ak kasancewar ba sananneba duk kuwa da cewar shine mai Company'n, Kasancewar Ak wani irin mutum ne mai murɗaɗɗan hali na rashin bayyana kai ko sirrinshi.
Mutum ne da idan ba sanin shi kayi ba baka taba sanin shine mai amsa sunan Companonin dake zagaye da Nigeria.
Don be yarda da baza sirrinshi ba irin yadda sanannun keyi shi yasa wani loƙacin harya shiga wuri ya fita ba'a taɓà sanin shine wannan me campanins ɗin, baka taɓa sanin shine wannan babban criminals ɗin, baka taɓa sanin shine *AK*. Kuma *ABDOUL-MALEEK EMAAR KUWAIT* He's not a social media fan.

Restroom ɗin dake babban Company'n suka shige su biyar cifff, suna zama Kabeer ya matso tare da ɗan ranƙwafowa kan Ak ɗin, ɗan danna screen din ipad ɗin dayake riƙe da shi ya shiga masa bayani ta cikin ƙaton magazine ɗin dake room ɗin, A kan wani business daya taso musu da manyan tycon na ƙasashen woje. Bayan sun kammala tattaunawar ne Kabeer yace "Sai 5 marcopolo buses dazamuyi amfani dashi for excursion's"

"All right okay"

AK ya faɗa daga haka suka miƙe daga zaman tattaunawar, bayan sun biya ta breakroom sunyi ɗinner, daga nan *A MALEEK MEMORIAL ORPHANAGE HOUSE* ɗinsa suka nufa. Bayan ya gansu ya buƙaci a bashi list na abubuwan da suke buƙata,nan suka bashi ba tare da sunga fuskar saba kamar ko yaushe. Wasu mahaukatan kuɗi ya tura ta account ɗin Managern gidan.
Daga nan *TEXTILE FEED INDUSTRY* suka nufa nan ma yaga yadda komi ke tafiya haka dai suka ta zagaya wurare daban-daban ta har dare, daga ƙarshe a wani haɗaɗɗen Restaurant suka yada zango nan sukayi ɗinner amma banda boss ɗin da yaki cin koma, Dole Armstrong ya mashi takawey .


_WASHE GARI_

Yana kwance akan ƙayataccen Royal Italian bed nashi woyar shi da yay ƙara ya farkar dashi, kunne yakai woyar bayan yayi peak calling woyar. "Boss anyi arresting ɗin Armstrong a hanyarsa ta maida Meerah ga iyayenta."
Wani ɗan banzan murmushi ne ya kuɓce mishi a bazata.
(Aikin ka nakyau Lion)
Ya faɗa acikin zuciyarsa a bayyane kuwa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da datse ƙiran.


A cennn station kuwa tunda suka samu damar arresting na Armstrong suka kulleshi a wani matsiyacin ɗakin kulle masu aika mugwayen lefuka.
Kai tsaye hospital aka nufa da meerah bisa jagorancin Isa Manu daya samu damar ganawa da mahaifin meerah A safiyar jiya dan gane da neman aurenta ga babban ɗansa Salman. Kai tsaye dake Isa Manu sananne ne kasancewar shi Father's na manyan ƴan siyasa yasa malam Abdullahi amincewa da batun da yazo may.
Daɗi da ƙari kuma duba da yadda yayi ruwa yayi tsaƙi akan ɓacewar Meerah.
Saida lilitoci sukayi checking up nata suka tabbatar da babu wata matsalar bayan ta sleeping pawdern da suka shaƙa mata.
Amma ce ta kwana wurinta wacce take tama Allah godiyar bayyana mata DIDI'ƊINTA da yayi cikin amincinsa.

Tana zaune gaban gadon da MEERAH take kwance wacce tayi ƴar rama kaɗan wasu abubuwa ne suke mata kai da komo a tsakar kanta, Har bata ga sanda meerah ɗin ta farka ba sai ji tayi ta riƙo hannunta.... A hankali cikin muryan da yayi low sosae ta furta.
"Anne na yauma mafarkin nake yi ko kamar yadda na saba?".
Cikin maɗaukakin farin ciki Anne'n ta rumgume ƴarta cikin muryan kuka ta shiga faɗin. "Wannan ma mafarki bane DIDINA, wannan zahiri ne a zahirance Allah ya tseratar mana dake cikin amincinsa"
Kanta ta ɗora a kan ƙafafun Anne'n tanaji inama itace ta samu damar da hawayenta yake zuba kamar yadda na Anne'nta ke zuba, ƙara cusa kanta tayi a wuyan Anne dake sheshsheƙar kuka ta lumshe. ido tana sauraren kukan Anne'n.
Tana jin dama ita Allah zaiba damar yin irin wannan kukan, koba komai hawayenta zai wanko kaɗan daga cikin raunin dake danƙare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login