Showing 15001 words to 18000 words out of 69951 words

Chapter 6 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8181

ta.
Uban gudu yake tsalawa a cikin motar wanda gudun har ma ya kusa tsorata meerah amma dake zuciyarta a dake dake sai taƙi barin tsoron nata baiyanuwa. Sunzo daidai round about wata kafurar Mota ƙirar Mercedez Benz tazo tasha gabansa, sai kuma yaji tsaiwar wata ma da bayansa hakan ya sanya zuciyarsa tsinkewa, amma sauya dake yana kawar da hasashen da zuciyarsa keson bijiro masa. be gama tunanin me ke faruwa ba ya ji ana ƙwankwasa window'n Motarshi da Bindiga daidai saitin kanshi kululu cikinsa ya kaɗa hanjinsa ya ɗuri ruwa nuni suka mishi da ya fito. hannu na rawa ya fito ganin wasu uban samudawan da yasan kuskure kaɗan zai musu su aika shi inda in aka tafi ba'a dawowa, yayi ɓeshi dukkaninsu suka yi suna sanye da facial Mask.
Umurnin da suka sake bashi ne a karo na biyu ne ya sa shi tunanin wannan wasu irin ƴan fashi ne? Inda ɗaya daga cikin wannan samudawan ke ce mai "Take off your clothes" da sauri yace "What?" sauƙar wani abu me ƙarfi yaji a gefen fuskarshi, da sauri yayi ƙara tare da dafe gefen kanshi yaji danshi danshi Alamun jini, cikin ɗaga murya yace "take off your clothes,i wont ask again" da sauri dan farin dattijon yayi yanda sukace, ya rage daga shi sai gajeren wando da guntun singileti, hatta takalmanshi zobe da Agogo, sai da ya cire, bai dawo daga duniyar daya tafi ba na wuccin gadi yaji sauƙar
Bindiga a kanshi.
Ɗaya daga cikin samudawan ne yama na kusa dashi alamu da ido.
Gaban motar ya nufa kai tsaye Sleeping powder'n dake hannun sa ya shaƙama Meerah, Kafin ta samu damar cewa komai ne taji abu a fuskanta. Yuuuu taji kanta ya fara mata, Cikin zabura tai yunƙurin dira daga cikin motar ɗin, sai dai ta kasa hakan dan cikin ƙanƙanin loƙaci jikinta yay wani irin masifar nauyi nan ta silale jikin kujera idanunta na lumshewa. Daga haka bata sake sanin mike faruwa ba kuma.

Baifi 10 minute da fitar motar ba baffan meerah ya shigo station ɗin, sosae hankalin sa yayi wani kalan masifar tashi, jin wai mahaifin meerah ɗin yazo yayi belin meerah ɗin. To waye mahaifin meerah kuma wanda ya wuce shi?, Kodai hankali ne kawai suke neman rena masa. Amma saiya danni zuciyarsa cikin tsanako da dattako irin nasa yabar station ɗin ya barma zuwa an jima kaɗan, wai a ganin sa kawai yau ɗin ma basa da ra'ayin barin sa ya ganta ne kawai shi yasa suka ɓullo masa da wannan zancen.
★★★
Wani kalar furzar da iska yayi yana maida kansa jikin saman sopa ya kwanta tare da lumshe idanunsa a hankali. Shi kaɗai yasan abinda yake ji game da taurin kan yarinyar data zaba buga game dashi. Ya fahimci lallai bata fahimci a ramin da take neman jefa ƙafarta bane. Amma zai bata loƙaci ta gama nata kalar ɗan ƙaramin wasan kafin ya fara buga babban game da sai tayi dana sanin sanin AK a rayuwarta da tayi. Idan ita ƙaramar ƴar iskar layi ce, zai tabbatar mata shi na duniya ne baki ɗaya, dan ba zubar da jini kawai ya iya ba harda cin uban duk wanda ya shiga sabgarsa. Lallai ta ɗaukarma kanta Dala ba gammo tunda tayi kuskuren zana fuskar sa, ya fahimci ita ɗin ƴar zafin kaice tun daga yanayin yadda ta mu'amulance shi a gidan jaridar su, amma ba komi tayi nata zafin kan ta gama duk zai sauƙe mata su kuwa nan bada jimawa ba.
      Ya jima a wajen zaune har su Axton suka dawo ɗauke da abincin da Vincent ya sasu suka yo order. Amma shi boss ɗin sai yace bazai ci ba. Ya haɗa coffee kawai da biscuits mai daɗi. yana shan coffee ɗinsa da biscuit tare da nazartar yarinyar. Koda ya kammala shan coffee ɗin bedroom ya wuce kai tsaye Maimakon kwanciya bathroom ya faɗa, ya haɗa ruwa mai ɗumi cikin bathtub tare da haɗa kayan ƙamshi kala-kala a ruwan sannan ya shiga ciki. Sai da ya kashi mituna a cikin ruwan na ratsashi da miƙar masa da kowace gaɓa sannan ya fito ya shiga wajen wanka ya ɗauraye jikinsa. Bayan ya fito salla ya fara gabatarwa tare da shafa'i da wutiri sannan ya shiga shiri. Yayi ƙyau sosai cikin shigar tasa tamkar ka sacesa ka gudu. Ga wani uban ƙamshi na tashi tamkar duka Company'n haɗa turaren ne a jikin sa. Sumar nan tasha gyara daka gansa kasan ya haɗa jini da masu jajayen kunnuwa. Hakama kwantaccen gashin sajensa sai walƙiya yake gashi kwance luf-luf ya sake fidda taswurar doguwar fuskarsa. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata sannan ya fito cikin nutsuwarsa da takunsa na tsayayyen namiji.


National Hospital atarubus
3:45pm

Accidents and Emergency aka shiga da wannan farin dattijon dake sananne ne shi babu wanda bai san waye Isa Manu ba, A kaff cikin Lagos harma da zagaye ta cikin ƙanƙanin loƙaci aka shiga bashi taimakon gaggawa.

Ba ƙaramin tashin hankali su anne suka shiga ba ganin har bayan sallar isha'i babu baffa babu dalilin sa Raiha sai kuka take, baffa kuwa da kansa ya gama kullewa ne yasa jininsa naiman hawa nan take, bai sake tsorata da lamarin ba sai loƙacin ƴan sanda suka zo da batun mutumin da ya yi belin meerah ƴan fashi sun sun tare sa a hanyar sa ta mika Meerah ga iyayen ta a round about ɗin sa na shan kwanar anguwar su malam Abdullahi gwani.
Cikin abinda bai wuce kiftar ido ba labaran suke zake hargitsa media, ƙura takai ƙura kam a wannan loƙacin, a kuma daidai loƙacin ne aka shiga musu da malam Abdullahi gida a yanayi mafi munin gani. Nan da nan matan baffa biyu suka shiga yaɓama Anne maganganu baƙaƙe. Wai akan yarinyar data gama gantalewarta a titi suke neman rasa malam, wllh baza su yarda ba. Anne kammm zuwa lokacin ma ita kam babu abinda take iya fuskanta daga cikin maganganun nasu, a fisge taji kalmar ƙarshe daga cikin ɗaya daga cikin matan.
"Dama ai barewa ba zata yi gudu kuma ɗan ta ya rarrafa ba, wllh malam ka auro mana masifa da bala'i, gashi kuma masifar daka ɗaya ƴanta sune suke ƙoƙarin ajalinka, kaje garin kwashe kwashenka ka auro mace mara asali wanda ba'a san inda asalin ta take ba, wanda ya wuce ƴar gaba da fatiha me bakin duniya"
Dipppp ji da ganinta suka ɗauke daga nan bata sake sanin ainihin abinda ke faruwa ba.
★★★
Sannu a hankali na shiga motsa idanuna da suka min matuƙar nauyi da ɗaurewa. Sai kuma na shiga buɗesu sannu-sannu harna gama buɗesu. hasken daya cika idanunane ya sanya na ɗan tashi a zabure da sauri. komi daya faru ya ringa dawo min daki daki har zuwa sleeping pawdern da suka shaƙa min. Ƙirjina ne yay wata irin masifar bugawa da sauri na ambaci sunan Allah.
Cikin sauri na mike na nufi ƙofar bathroom ɗin da nayi amfani dashi wajen uzurina. Alwala na ɗauro sauri² gudu² na fito praymad ɗin da nayi sallah akai jiya yauma na nufa, a nutse na fara sallar cike da nutsuwa.bayan na idar na sulale a wajen ina saki wani irin kuka mai tsuma rai da da zuciya. Na jima kwance a wajen ina kuka kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Nama rasa ina zan kai tunanin na. Handle ɗin dakin naji an taɓa tare da shigowa mutumin jiya da dare ne duk da cewar fuskarsa a rufe take amma tsab na gama gane shi, kasancewata mutum bai kaifin basira, plate ɗin dake ɗauke da soyayyar wainar kwai ya ajje min tare da ledar bread recipe ya juya abinsa da niyar tafiya.
"Lallai hakan da kuka yi shi ne ya sake tabbatar min da cewar ku dukkanin ku lusaraine, kolaye ne tunda har kuka rasa abinda za kuyi sai kidnapping mace" nayi maganar tare da jan wani mugun tsaki.
Duk da ya tsaya cak tun fara maganata bai juyo ba. Harna kammala maganar kuma bai tanka min ba ya buɗe ƙofar ya fice tare da sauri tare da kulleni ta baya. Ido kawai na zubama ƙofar wasu kalar hawayen bakin ciki na sake gangaro min da gudun tsiya.
A yanzu ba wai kaina kawai nake tausayi ba su  Annena baffana Raiha ɗina nake tausayi da halin da zasu shiga sune suke matuƙar tada min da hankali fiye da komai.
Bai cika 20 minute da fita ba sai gashi ya sake dawowa farin handkerchief ɗin dake hannun sa ya jefa saman fuskana hakan yasa na fara ganin bibbiyu kafin kuma na tafi luuuuuu.
Ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai bayan sallar zuhr, a wani bedroom ɗin na daban na sake tsintar kaina ba wanda aka fara kaini ba. Da kyar cikin mutuwar jiki na miƙa na nufi hanyar da tsammanina ya gama bani bathroom ne, ilai kuwa bathroom ɗin ne toothpaste da brush na farke su a ledartarsu, saida na fara wanke bakina kafin alwala sallar zuhr tayi tare da fara duk wasu addaoin da suka zo bakina. Ledar takawey ɗin dake gaban gadon naja bisa dole zuwa gabana. Domin kuwa in banda kukan yunwa babu abinda cikina yake. Kaɗan na ɗan chakala na ture gefe domin ma samm sai naji bana jin cin abincin ma.
Mahaukacin ƙamshim da hancina ya shaƙar min ne ya sanya ni saurin ɗago kaina zuwa Said ɗin da naji ƙamshim na fitowa. Da wannan idanuwan dana zana na fara cin karo, wanda har ƙarshen numfashina baran taɓa mancewa dasu ba.
Sanye yake cikin wasu tsadaddun luzary Ride vizzon sky blue colour daga ƙasar rigar kuma fari kaɗan irin hadarin Dubai ɗin nan ce dai.sai lallausan farin wando trouser kansa sanye cikin hular luxary supereme irin ta sanyin nan sai facemask irin Turkish ɗin nan shima, yau kam babu glasess ɗin da yake toshe idonsa dashi. Fuskarnan a matukar haɗe. Chair lind ɗin dake gefe da gadon ya janyo zuwa gabansa, zaune yakai zama irin na wanda suka isa zama ne irin na zaratan sarakunan da suka kai sarakai ba muna sarki ba. Wanda hakan da yayi ne ya shagaltar da Meerah a kallonsa.
"What wrong with you flower pie?" Ya faɗa cikin daƙilallalliyar muryansa, a rikice ta dawo nutsuwarta tana dedeta kanta, tare da hararar inda yake zaune. A fusace ta furta
"miye Amfanin kidnapping na da kuka yi?"
Wani malalacin kill smile ne ya subce mishi a bazata. Domin samm baiyi zaton bakinta zai iya murta wata magana ba, amma kuma idan yayi duba da tsaurin idonta da tsaya samm hakan ba abin mamaki bane.
"Wannan bakin naki zai kaiki ya baro ki silly girl! Idan kika ce zaki buga game da Ak to kuwa tabbas zubar hawaye bata shirya barin idaniyarki ba ke nan"
Cike da tsiwa da son hana ganin lagona na sake maida fuskana gare shi tare da furta "Never for ever ka rubuta ka ajje Ni Meerah Abdullahi gwani saina sanya ka gudun ceton rai a tsakiyar karnuka"
A bazata yaji sauƙar kalaman nata don haka ya zuba mata cat eye's nashi tare da folding hannun wansa saman ƙirjinsa. Don shi maganar nata dariya ne yaso bashi amma dake tantirin kansa ne hakan ko ajikin shi. Saima gira ɗaya daya ɗage mata tare da furta "weldone pie" tare da juyowa da kallonsa a kanta ya sakar mata wani lalataccen murmushi.
"Tabbas kuwa karen zai mutu da haushin kurar"
ya faɗa idonsa cikin tsakiyar nata idanun still murmushin gefen bakin nan bai bar fuskarsa ba.
"Bad boy da dukkan alamu kana wasa da wannan Meerah ɗin amma dai muje zuwa musu iya magana sukance ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare"
Cikin majestical takunsa ya nufo inda nake tare da matsowa daf dani. "Did I look like a comedian to you?"
Yana faɗar maganar ya nufi hanyar barin bedroom ɗin baki ɗaya cikin nutsatstsen takunsa mai cike da ƙasaita. Bayan ya mata wata halamar data gaza fashimtar kota miye.
______
       Shigar Isa Manu a zancen ya saka ƴan sanda sake ɗaukar zafi, Dan a yanzu D.c.o ɗin ne ma da kansa yake gudanar da binciken kidnapping ɗin Meerah ɗin tare da Inspector atya murail.
Al'amari kamar wasa akan ɓatan Meerah ƙaramar magana na neman zama babba. Dan ƴan sanda sun matuƙar zafafan bincike akan maganar duk inda ka wulla magana ɗaya ce, duk da kuwa shi kansa Isa Manun kidnapping yarinyar yaso yi.





*🦅 MIKIYA 🦅*
{Mai hangen nesa 👀}

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH
*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 13&14
#ROMANCE##
#BLACKMONEY
#KIDNAPPING
*DRUG TRAFFICKING
#AGGRAVATED ROBBERY##
#AMAZING W*w(☞ ಠ_ಠ)☞

https://www.aihausanovels.com.ng********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
******* FOLLOW US ******
WhatsApp Number: 08104493215
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ *************************
_______________________________
***Sosae police report ɗin da suke kan aikin nemo wanda sukai kidnapping yarinyar tare da case na Isa Manu suka sake ɗaukar zafi na gasken gaske.duk da shi kansa bai san inda kansa yake ba tunda yana very critical condition ne, wanda hakan keda matuƙar haɗari sosae.
Duk wasu wuraren da suka san zasu sami news ko yaya ne samm basa wasa da damar su, gashi babban yaron Isa Manu'n wanda baya a Nigeria'n ma yana daga ƙasar Poland ne yayi stating ƙarar . sannan yasa a tsananta binciken case ɗin duk faɗin Lagos dama kewayenta ya kuma yi musu albishir ɗin kyauta mai tsoka, muddin suka samo masu hannu acikin case ɗin. Abinka da manya nan da nan suka bazama don sosai ya mugun sakar musu kudi masu gwaɓi, tako ta ina jami'an tsaro sun ɗau zafi sosae kawunansu ya ɗauki ɗumi. Kan kace me maganar tayi spreading kamar gobara a bushashshen ciyayi.
Gidan su Meerah sosae hankalu suka sake tashi ganin malam Abdullahi yana a mugun yanayi,ga Amma dake hospital har yau bata san inda kanta yake ba. Sai wasu siraran hayawe da suke ɗan zubo mata time to time sosae likitoci suke iyaka bakin ƙoƙarin su akanta.
Sai dab da Asr Amma ta farfaɗo abu na farko data fara nema itane Meerah.
"WHO WHY su waye ? Su waye masu son rabani da hasken rayuwata! Su waye ku?¿"
Dr nimra dake tsaye tun farkon farkawar Ammance ta shiga bama Ammn baki akan ta kwantar da hankalinta. Sadda kanta kawai ƙasa not saying anything saidai ita kaɗai tasan irin halin da zuciyarta take a ciki da irin ɗacin dake danƙare acen cikin tsakiyar ƙirjinta. A hankali ta maida idanunta ta lumshe tana haɗiye yawun daya tokare makoshinta, zafi mea mugun raɗaɗi take ji a zuciyarta ji take kamar ana gasa mata zuciyar a oven ne kuma a tarfa mata narkakkan Salman. Meerah ita kaɗai ce jininta daga ita Raiha sune suka maye mata gurbin ƴar uwa, ɗan uwa, UWA,UBA dangi baki ɗaya.
Su kaɗai ne hasken rayuwarta kuma sannan rana tsaka ace irin waɗannan muggan musifun sun faru da rayuwarta?. Ita da Meerah ɗin ta kuma har ake tunanin ma zata kwantar da hankalinta abin ma da bazai taɓa yi yuwa ba kenan. Ahankali ta maida idanunta ta lumshe tana jin yadda ƙirjinta yake mata wani mugun bugu tarkar ƙirjinta zai fashe zuciyarta ta fito fittt haka take ji.
Faɗowar mutum ajikin da kuka kukan da aka fashe mata dashi ne yasa ta san Raiha Raihan tace a jikin ta. Wani irin ƙanƙameta jikinta tayi domin gani take itama amana iya kidnapping nata kamar meerah'ɗinta. Ahankali ta shiga ɗan bugun gadon bayanta comfortably tana streaming abubuwan dasu faru da ita koma tace suke kan faruwar.
Malam Abdullahi da ya zuba mata idanunsa tun farkon shigowar su da Raiha ne ya ɗan shiga takawa zuwa gareta jiki a matuƙar sanyaya.
"Ita ƙaddara wajibatunce akan ko wane bawa kuma mumini mai iman domin Allah baya taba dorama bawansa kaddarar da bazai iya dauka ba. Kana ita kaddara da kike gani rubutacciya ce tun daga rabbis samawati! Me yasa kike ma taki ƙaddarar kuka?. Idan muka sanya ma zuciyarsa mu nasibi da miƙa al'amurra ga Sarkin da shi kaɗai ne buwayi gagara misali sai kiga ya sauƙaƙa mana tarin ƙalubalen dake cikin makauniyar ƙaddarar mu. Ya kuma kawo mana mafita akan hakan cikin sauƙi!, Duk da zuwa yanxun nasan shuɗaɗɗan al'muran da suka faru ne shuke zeroying main naki. Ki daure ki daure ki daure kiyi haƙur AYSHATUL
MUBINA"
Ƙara ƙanƙame Raiha tayi a cikin jikinta tana jin inama inama inama ace, saidai tasan wannan inama ɗin ta barta har gaban gaban abada abadan. Ahankali ta shiga noding kanta tanayi tana ƙara ƙanƙame Raiha dake matse a cikin jikinta.
"Bawai ƙaddarata nake ma kuka ba Abbu maira tarin ƙalubalen dake tattare da ita nake ma kuka. Bawai kukan faruwar wani abu ba kukan ƙinnn.....
Sai kuma wani irin kuka yaci ƙarfinta irin mai sarke numfashin nan.
Hawaye taci gaba dayi tana sobbing ahankali tana jin raunin zuciyarta daya fara kamewa komai daya faru na dawo mata kamar yanxune komai ke faruwa.
" Hasbunallahi wani'imal waqeel! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ya Allah help me, don't take her away from me now.Not now please I can't take it....
Malam Abdullahi ya shiga fada cikin tsananin tashin hankali ganin numfashinta chakkk ya tsaya da bugu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login