Showing 30001 words to 33000 words out of 69951 words
yake cikin ash wandon fendi da farar rigar rugby shirt sai blue Lorenzo snickers a sawayensa. Fuskar nan saye cikin Sun glasses sai nose mark daya sanya.
Da sauri daya daga cikin samudawansa ya bude masa wata shegiyar blue car 2024 Bugatti, Cikin tsantsan jin kai ya shige cikin motar rufewa yayi driver ya bata wuta, Sauran motacin na Mara musu baya.......
*ISA MANU empire*
Hannuwansa goye a bayansa baki daya kansa ya kulle yama rasa wanne tunani zaiyi, ”Dom ITT"
Ya fada cikin daga sauti. Wanda kuma yayi daidai da shigowar Salman a rike ce. Ganin yanayin daya tadda dad nashi ya sanya hankalinsa sake tashi over,Saida ya dan fesar da wani zazzafan numfashi kana ya furta.
"An dauke Assembly leader wayewar garin yau na Serevellar”
“What!?”
Isa manu ya fada da karfin masifa tare da kaiwa kasa yana fidda numfashin da yaso sarkeshi sama².
Komai bai Iya furtawa a lokacin saida ya debi wasu minutes kafin ya furta.
“Lallai yau duk yanda za'ai ina bukatar ayi zanga zangar nan, Kaiiiiiiii abin yayi yawa haka nan, nasan next target nine kuma ko kai”
Yayi maganar zuciyarsa na wani irin beating very fast........
Cikin abinda bai gaza 50 minutes ba gangar samari yan ko ta kwana suka gama hallara kansa a babban gidan gonar Isa manu.
*By AMMEY LAYLERH📝💐*
*🦅 MIKIYA 🦅*
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________
*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*
Page 25&26
# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# BEST LOVE
🤍🔥✅
★★★★
*5:55am*
Cincirindon matasan suka zagaye babbar police ɗin dake birnin Lagos da kuma headquarters na sojoji, Suna faɗin *ADALCI* suke so. Su a fito musu da gwamnansu tare da ministan su da assembly leader nasu.
Wannan zanga-zangar ta matasan ce ta kuma janyo hankulan jama'a kansu, dan danan cikin mitsitsin loƙaci jama'ar gari suma suka firfito ana zanga-zangar dasu, kafin kace meye Social media ma ta ɗauka.
Suna son soldier's da police's su jajirce wajen dawo musu da governor da minister'nsu tare da Assembly leader, Tuni wannan zanga-zangar ta yau lanar Laraba ta zama latest a kafafen yaɗà labarai. Irinsu magazine, Television, Radio.
Su Isa Manu da suke cikin gidajensu suna kallon duk abinda ke faruwa tuni suka cika da maɗaukakin farin ciki, lallai haƙarsu ta cimma ruwa dama abinda suke da buƙatar kenan. A tada hazo a cikin garin na Lagos dama kewayenta.
Acen kuwa cikin babbar police da kuma headquarters ɗin kuwa duk da barkonon tsohuwar da aka baɗesu dashi sunƙi ko gezau balle su gudu. Ga na cikin gari ma hakan take dole ƴan sanda dama sojoji suka bazu ko ina don bada tsaro wa al'umma.
*******
*MEERAH*
A Yau Lahadi akayi adda'ar sadakar ukun Affan wanda har zuwa wannan loƙacin meerah na'a cikin alhinin mutuwar.
Daren daya kasance dare mafi matuƙar muni a cikin tarihin rayuwar meerah, domin Sai yanxun mutuwar Affan ya dawo mata sabuwa filll. Domin sai yanxu ta sake tabbatar da cewar ehhhhhh lallai ta yarda ta rasa Affan ɗin ta har gaban abada abadan abada kenan, A wannan dare na sadakar ukun ta kasa rumtsa kwayar idonta shi yasa ta ƙira daren da baƙin dare.
Dare ne mai ɗauke da tsananin duhu tare da cushewar yanayi kasancewar babu yalwar iska ko kaɗan dake kai komo acikin gari, yayinda sama tayi duhu dulum kasancewar babu hasken farin wata ko ɗigo, haka ma hasken taurari duk sun disashe wannan yana ɗaya daga cikin abunda yasa duniyar tayi mata tsananin duhu, yayinda ko ina ya zama shiru babu motsin kowa a cikin gidan sai ita kaɗai da take kowawa da numfashinta. kasancewar adaidai irin wannan loƙacin kaso 90 acikin 100 na mutanen duniya bacci sukeyi, saboda kowa yasan akance *DARE* mahutar bawa.
Saidai awani ɓangare tsawon awanni ashirin da bakwai kenan da MEERAH ke kokawa da numfashin dake shirin barin gangar jikinta.Luuuuuuu idanunta suka rufe kirib, yayinda bugun zuciyarta ya yi ƙasa sosai kasancewar ta jima da fita acikin hayyacinta, wannan yasa ta shafe tsawon awanni 30 batare da tasan
duniyar da take ba, ta manta wacece ita da kuma duk wani abu daya shafe ta, ta manta da Cewar an taɓa halittan wata jinsi irinta, komai ya tsaya mata ne cak kamar ba’a taɓa wanzar da ita adoron duniyar ba.
Ammma sai' gashi cikin hukunci na Ubangiji maji ƙan bayinsa cikin ƙarin wasu awanni, numfashi ya fara ziyartar wannan kirjin daya jima ba tare da ya shaƙi numfashin duniya ba, wanda hakan yasa ahankali ta soma motsa babbar ƴar yatsar ƙafarta wacce ta ƙame waje guda, A loƙacin da numfashinta ya gama daidai ta a kuma wannan loƙacin ne wani irin ɗaci da ciwo me gigita zuciya ya ya sake sarƙafe tsaƙiyar ƙirjinta.
“MEERAH?...”
Amma ta ƙira sunanta cikin sautin fitar amon daya sake gigita duniyar Meerah, wanda tarin ƙalubalen da take kan fuskanta ke haifar mata, wani irin rumtse idanunta tayi tare da matse hannuwanta dake rawa sosae. Wani irin mashahurin sanyi na ratsa cikin jikinta.
Da sauri Anne ta ƙarasa shigowa ganin kamar Didinta bata a mood me daɗi, domin yau ita ce da malam Abdullahi haka kawai jikinta ya bata Didinta ba lafiya ba. Zaune takai gefen gadon da take kwance. Wata guntuwar kwalla data tarummata ta share zuciyarta na mata suya.....
_Shin sai xuwa yaushe zata dena zubar da hawaye akan ƙaddara?_
_Shin yaushe ne babin rayuwar su zai juye zuwa wani mataki na daban?_
_Shi sai xuwa yaushe rayuwarta ita da ƴaƴan ta zatayi haske? Yaushe zasuji daɗin rayuwa ita da ƴaƴanta kamar ko Rai me numfashi?, Yaushe haske zai ratsa cikin rayuwar kowannensu?_
_Shi dama laifi ne dan ƙaddararsu tazo musu a yadda ba suyi zato ko tsammani ba?, Ashe haka duk wata ɗiya ta kwarai take ji idan aka shegentaka? Wani irin ɗaci da raɗaɗi me zafin gaske take ji a duk loƙacin da kishiyoyinta suka jefeta da kalmar shegiya_
_Bafa ita ta zaɓama kanta tasowa a inda babu kowa nata ba! Bafa zaɓen ƙaddararta tayi, ba itace ta zaɓi da rayuwa tayi ta watan gaririwa da itaba, ba kuma itace ta tsara ma kanta yanayin rayuwar da suke ba. Ta buɗe idontane kawai ta ganta inda bata san kowa nata ba, ba UWA ba Uba, ba ƴar uwa ba ɗan uwa.
Babu kowa nata data sani itama tsintar kanta kawai tayi a cikin rayuwar da take a yanzu tsumu-tsumu, Tana ƙara roƙon Allah har kwanan gobe Ubangiji karya ɗauki rayuwarta saiya bayyana mata wani nata a duniya........._
_Tana son ta tambayi wanne irin laifi ta musu da suka zaɓi su jefar da ita? Tana son ta tambayi wanne irin mutane ne su masu son zuciya?_
_Ita kaɗai tasan abubuwan da suke cunshe a cikin Rai da ruhinta, wanda suka kusa tarwatsa zuciyarta ta buga ta dena aiki, domin tasan tana dab da bugawar. Badon Allah yayi ta mace me tsananin haƙuri da danne abu komi girman sa a cikin zuciyarta da tuni numfashinta ya jima da barin gangar jikinta.....
A bayyane ta sauƙe wata nannauyar ijiyar zuciya cikin muryan da yayi low sosae ya furta.
"Me yake damun DIDINA haka?"
Kanta ta ɗago tare da kallon mahaifiyar nata cikin raunatacciyar murya ta shiga faɗin.
”Nima bansan abinda ke damuna ba Anne! Kawai dai inajin yanayin cinkushewar zuciya ne, da rashin jin dadin yanayin rayuwar ma baki ɗaya”
”Ce ALHAMDULILLAH domin Allah shine abin godiya a koda yaushe!”
ALHAMDULILLAH ɗin kuwa ta furta tare da duk sauran adda'oin da suka zo mata.
Ƙiran sallar asuba da aka ƙirane ya fitar da Anne a ɗakin bayan taci kukanta harta gode Allah.
Ko Washegarin ranar Meerah kasa fita ko ina tayi, kayan karin tama har ɗaki Raiha ta kawo mata..........ita kuma ta wuce makaranta.
Tana zaune a ɗaki Sai wajajen sha biyun rana kana ta fito verander inda ƴan uwanta aurarru suke zaune. Gaisar dasu tayi wasu sama sama suka amsa wasu kuwa arziƙin kallo bata samu daga gare su ba.
Kwanciya tayi ba tare data nuna damuwarta akan rashin amsanta ba basu yi ba.
Babbar yayarsu da suke ƙira aunty Zaheedah ce tace.
”guys na manta ban baku wani latest story ba"
Shewa suka sanya a tare kusan su biyar kana aunty Sumayya ta furta.
”Bamu musha ƴer uwa”
Saida tayi ƴar dariya kaɗan irin ta rashin mutuncin nan kan furta.
“Kai Wllh na daɗe banga mara zuciyar mace irin zulaiha ba, Ata zaluntar mutum amma saiya nuna baimasan ana yimay ba. Kunsan a wayewar garinda Affan ya rasu sai dana sake banka musu ɗaki ita da Belle"
”Kai Wllh na daɗe ko'a littafin Hausa Novels banji me hali irin na matar nan, ayi yarinya sai kace me zuciyar takarda ko ma wacce bata da zuciyar a tsakiyar ƙirjinta”
Aunty labiba ta faɗi tana gyara zama
"Nake baku labari shegen kamar kullum ranar ma kasa tanka min yay saima rawar jikin daya fara min...... Ita kuwa shegiyar Wllh ko kallo na kasa yi tayi kamar dai ko yaushe”
Aunty Maryam da tunda suka fara maganganunsu ce dama kuma bata ce musu komi ta furta.
”Innalillahi! Yanxu dama har yanzu Zaheedah baki dena wannan banzan halin naki ba?, Na cutar yarinyar mutane ta shigar mata ɗaki kina gane mata sirrin aurenta......Wllh kiji tsoron Allah domin ɗaurin talala ya miki duk randa Ubangiji ya tashi nuna miki ikonsa a kanta Wllh daga ranar zaki gane Allah ɗaya yake”
"Huyummmmmmm me zuciya irinta marasa kan gado, ke dai kici gaba da zama a cikin duhun kai da bar abada bazaki waye ba"
Cewar aunty labiba, shewa suka sanya mata nan fa suka koma kanta suna mata cin mutuncin da suka ga dama.
Ni kuwa dake kwance a wurin tsammmm na miƙe domin kunnuwa ba rasuji gaba da jin zunufi ba. A cikin zuciyata kuma ina musu fatan shiriya duniya da lahira.
★★★
*ABUJA*
Zaune take akan caution ɗin da yama ƙatataccen parloun ƙawanya, tayi zurfi sosae a duniyar tunanin halin da rayuwarta take ciki.
Tana zaune cikin ƙunci na rayuwa da azabtar War kishiya.
”Zulaiha! Zulaiha!!"
Shiru alamun tayi nisan kiwo a cikin kogin tunanin data faɗa.
”Zulaiha kodai kin sanya wata damuwar ne a cikin ranki?”
Matashin mutumin dake kanta tsaye ya tambaya wanda a shekaru zai iya kaiwa irin Talatin da bakwai ɗin nan ko da shida.
zamanta ta gyara tare da fuskantar sa sai kuma idonta suka ciko da kwalla.
”Yanxu Bello tambayana ma kake ko damuwar woni abu nasa a raina? Duk irin ƙalubalen da nake fuskanta a cikin gidan nan?
Haƙuri na yana dab da ƙarewa Wllh na gaji- na gaji *NA GAJI BELLO!* Duk irin abubuwan da ake min woni a gaban idonka woni a bayan idonka amma kanzil ba zaka iya furtawa akan anyi min ba daidai ba”
Ta furta cikin muryan kuka sosai da sosae.
Kafaɗunta ya dafa cikin kwantar da murya ya shiga furta.
”Har abada ba zan gaji da cewa kiyi haƙuri ba zulaiha, ita rayuwar duniya ƴar haƙuri ce kuma duk wanda yayi haƙuri baya taɓa faɗuwa ƙasa....Ƙarshen ko wanne haƙuri nasarace, ƙarshen tsanani darajace, ƙarshen wahala ɗaukakace, ƙarshen jarabawa kuma Alkhari ne ciki gaba da zaman haƙuri dakai kukanki wurin Allah domin shi maji ƙan bayinsa ne"
Daga haka ya saki kafaɗunta yay taku ɗaya ana biyu ta riƙo hannuwansa, Sai kuma kawai ta faɗa jikinsa tare da cusa kanta cikin ƙirjinsa rana fashewa da wani irin kuka me cin Rai.
Tsammmm ya rungumata ya fara lallashinta,Saman sa ya nufa da ita tana cikin jikinsa.
★★★
Ayau wayar garin litinin zazzafan martani ya fito daga bangaren *AK* Wanda indai mutum masoyin media me to da wannan zazzafan latest news din ya karya.
Ga abinda martanin ya kunsha na farko a cikin tiktok.
Yana zaune a wani kayataccen palo ne wanda Wanda ya wadatu da komi na mo re rayuwa, sanye yake cikin shigar bakaken Riga da wando yayi covering duka jikinsa ko kwayar idonsa babu me Iya gani.
Shi kanshi video'n don ka tabbatar dana musamman ne idan ka shiga kafin ka fara ganin komai said kamar 5 minute haka xuwa 7. Kafafun nan a harde kamar kullum cikin nutsatstsen sautin da yake fita cikin wani irin low voice nd sweet ya shi fara mayar da martaninsa kai tsaye.
_Fusata ya kamata ace kunyi bawai nuna fushinku a kaina ba!. Kasancewar kun gane wannan shugaban da kuka zaba ha'intarku yake yi, akanshi ya kamata ace kun nuna fushinku sakamakon zabarshi da kayi_
_A yayinda fitilun titi suka dauke hanya ta cika shara da kuma tarkace,
A yayinda ake wulakanta talakawa tamkar dabbobi a asibitin gwammanati!, cin hanci ya wanzu a kowanne ofishin ma'aikacin gwammanati anan zaku nuna fushinku.
Me yasa ba baku nuna fushinku fusatarku a ire-iren wadan nan abubuwan?, amma a yayin da gurbataccen shugaba ya shigo hannu shine kuka harda fitowa wata zanga zanga?
Kukayi kone-kone kuka har gitsa komai da komai a cikin ko wanne lunguna na wannan gari dama wajen garin?.
Idan har wani iftilati ya faru daku ya kasance kuma kuna bukatar taimakonsu to amfani Duke wannan hatta shi wannan taimakon Right?.
A wannan kasar shima talakan ba wani salihin bawa bane, shine ma hanya mafi gurbata a wannan fannin.
Rashawar dake tattare da kuri'a itace ke bama shugabanni wannan ikon.
A yayinda da suka zo suka raba muku wasu yan tsirarun abubuwan amfanin yauda kullum da bazasu wuce wuni daya ba.
Shine kawai kuke zabarsu ba tare da tunanin menene abinda gobenku zata haifar muku ba.
Sabo da rashin sanin yanci zarmammun cikinku suke dauraku akan ra'ayin da ba naku ba, domin kasa ta sanja dole sai talakan gari ya fara sanjawa domain kawar da rashawa da kuma son zuciya.
*DON HAKA MU FARA SANJAWA.....*_
Kafin kace mene tuni media ta dauki hayakin bala'i domin wannan zazzafan martani na ABDOUL-MALEEK AK tuni ya baza ko INA.
Har wasu na mai dashi rubutu ta hanyar copy suna dorawa irinsu Facebook, Twitter, Instagram, telegram dadai saurinsu haka gidajen radio suma suka ringa maimaichin abun kamar ba gobe. Sai yanxu hankalin mutane ya fara dawowa jikinsu.
Tuni hankalin jami'ai kuma ya tashi da wannan ballo ruwa da AK yayi Wanda suka rasa ta inda zasu toshe hakan. Hankalin duk wani Dan siyasar dake Nigeria a tashe yake da ganin wannan video, tuni jamaar dake kiran AK da criminal suka dawo girmama koda jin sunan shine. Saidai amsa daya da ko wanne mutum ke dokon jira a jirace shine bayyanar ak a zahirance. Da kuma asalin kasar shi da inda yake zaune domin kuwa kallo daya mutum zai yi masa yasan cewar shiba mutumin NJ bane, ko daga yanayin zancenshi da baya idasa fita duka.
Wannan Abu shine yayi sanadiyar takawar shugaban kasa har xuwa Lagos. Inda suka tattauna da manyan Jami'ai da kuma wasu kuso shin gwommanatin dake mulkarmu ta karkashin kasa......
Meeting din gaggawa suka shirya tsakanin masu ruwa da tsaki a cikin tafiyar.
After like 50 minutes haka suka shirya meeting ɗin gaggawa cikin wani haɗaɗɗan building mai haɗe da wani ƙaton hall acikinsa, coutions ne acikin sa na alfarma wanda hall ɗin yaji kayan mo re rayuwa, ko ina stainding A/C ne manner a wurin sai sanyayyar ƙamshi da kuma fitar numfarfashin jama'ar da wurin ya tara ne ke tashi.
meeting sukayi me sunan meeting Dan sai dab da magrib suka tashi suna ta faman kulli da warwara, ahaka har suka sami mafita kana kowa ya kama gabansa bayan zaida mafitar da suke ga itane kadai mafitarsu.
Kwanan Armstrong hudu AK yayi dirar miki a boyayyen wurin da suka boye shi ta hanyar footage din dake cikin karkashin harshensa.
Tsaro sosae akama wurin duk don kaicema samin kuskure,amma hakan bai hana ak bayyana a gabansu ba. A lokacin su Mr President, Ajmaal, Isa manu, dadai sauran manyan kawunan suna a cikin setrest din ne don sun fitar dashi a station din ma baki daya.
Suna kan azabtar da Armstrong Woyar dco ne yayi kara hakan ya sanya shi dakatawa da bugun Arms din.
”What AK kuma?”
Ya fada a zabure har yana kokarin hantsilawa saida Ajmaal yayi saurin taro shi tu kuna ya daidaita tsaiwarsa.