Showing 18001 words to 21000 words out of 69951 words
A guje Norse suka yo dakin don suka komi dake faruwa ta cikin camera'r dakin, Nan suka shiga kokarin ceto numfashinta.
*AK*
Tsaye yake jingine da jikin Railer fuskarnan a matse wandan jeans ne a jikinsa army green da farar singlet yayi stocking nata ta cikin wandon ya daure da beld. Sai light green din top wadda ya balle duk maballanta ya barta a bude iskar da ake kadawa a gurin na diban rigar nashi kamar zata cire.
Gaba daya rigar tabar jikinsa sai singlet din kawai, zaune akan chair lind din dake cikin balcony'n tare da crossing kafarsa daya kan daya. Sosae iskar dake kadawa a wurin tare da kamshin flowering dake wurin suke bashi cikakkiyar nutsuwa, Shi yasa most especially yake zaman wurin. Lumshe idanunsa yayi tare da fadawa duniyar tunani tamkar komai daya faru ne a wancen lokacin haka komai ya Shiva zeroying maind nashi.
_"Waya baka umarnin kai harbi? Ka gaya min waya baka umarnin kai Harbin?"
Ya fada a matukar tsawace
_"Ba kowa Sir"_
Wani dan iskan kallo sir din ya cillo mass cikin yanayin fusatar zuciya ya doka table din dake gabansa.
_"Me yasa kayi?....
Folding hannuwansa yayi akan kirjinsa tare da furta.
_"Bacin Raine sabo da manyan shugabaninmu suna Neman ruguza kasar da muke_" ya furta cikin rashin shakkun a gaban Wanda yake.
_"Sanin kan Kane wannan mutumin da muka kama shine babbar hujjarmu......_
_"wacce hujja kuma sir kullum maganar kenan, munje mun shayo bakar wuya tukuru wajen kame masu laifi amma daga karshe manyan kasar sai su fitar dash_"
******
_" Shi yasa kai kuma ka harbe shi?, Hukumar soja tana da dokoki bada k'awa zuci take aikiba. Sojoji sama da dubu dariya ne a wannan sansanin maciya kyakytattukan yabo macimma nasarori masu lambobin yabo. Saidai a cikin su akwai wani bakin digo daya Kaine. A duk lokacin da Muke kan aiki irin haka Kaine mutum na farko da take fara bamu marsala, A matsayinka na soja ko kadan baka iya sarrafa kanka. Ko kadan baka iyawa koda yaushe cikin fada kaiba kowa bane face Dan matsala ba bama sojoji da kasar sa matsala ABDULMALEEK KUUWAIT_"
Wani irin doka coffee table din dake gabansa yayi, cikin tsananin bacin rai ABDULMALEEK KUWAIT da gajiyawa da rainin yawon da sir din nake yake kawo masa ya damki wuyar rigar sir din.
_"Sabo dani jirgin kasa ne duk Wanda ya shiga hanyata markadeshi nake, sannan zaku iya dakatar da ruwa idan kuka tare shi saidai idan ya tashi ballewa tamkar teku yake hadawa yake ya tafi da duk wani gurbatacce wadan da suka kasance marassa amfani_"
Wani wurgi yayi da Mr.president tare da sutale rigar kakin sa ya cilla masa a saman fuska hadi da hular pcarp nasu na soldiers.
"DUDEeeee....
Jaheed ya fada da karfin bala'i amma ina duk yadda jaheed yake kiransa da son dakatar da shi haka ya fice abinsa. Wannan shine mafari silar komai da komai......
************
"Are you okey Boss?"
Muryar Vincent ta katse shi daga zurfafa dayay a duniyar tunani.
Shisha pot dinshi ya janyo zuwa gabansa ya kunna tare da janyi pipe din ya fara zuka yana fesar da hayakin ta baki ta hanci. Comfortably yake shan shishan yana streaming shudadden lokacin.
Runannun idonsa ya dago tare da duban Vincent dake tsaye akansa har lokacin tamkar wani me gadin hana dan Aiken mutuwa daukar ransa.
"Ina bukatar a safiyar gobe media tayi kalace da wancen luxuries story in!"
Dan risinar da kansa yayi tare da furta
"An gama Boss"
★★★★
Duk yadda naso sha re dinner lunch da ake ajje min as dinner night kasawa nayi, domin kamm kowa yasan bana da juriyar yunwa don ko ina cikin ciwo ne tofa bana iya fushi da abinci bana wasa da cikina samm. Warner's din na janwo gaba na takeaway ne kusan 3color's akwai pizza, sai potato's abalon, sai jollop rice wacce taji namomi masu dan banzan yawa.
*🦅 MIKIYA 🦅*
{Mai hangen nesa 👀}
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH
*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 15&16
#ROMANCE##
#BLACKMONEY
#KIDNAPPING
*DRUG TRAFFICKING
#AGGRAVATED ROBBERY##
#AMAZING W*w☞ ☞
______________
#DON
_Wannan itace duniyar da muke rayuwa a cikin ta wacce take kunshe dajin dadi da kuma tsatsanin azaba. Kalilan daga cikin ta sine suke jin dadinta mafi yawan cikin ta kuma sune suke shan hawalarta. KIYAYYA, HASSADA da MUGUNTA sune ababen da suke kara ta'azzara komai a cikin wannan duniyar.
Karni bayan karni shekaru naci gaba da shudewa amma babu wani Abu da yake sanjawa, saima kara ta'azzara yake abun tambayar anan shine.
Shin wannan duniyar zata taba sanjawa kuwa?....
Sabo da masu karfin ikon cikin sune koda yaushe suke azabtar da talakawan cikinta, burinmu NIGERIAN'MU ta gyara dama duniyar baki daya. To amma ta yaya hakan zata faru???...... Let's go a comments section
DON√_
Wannan kayataccen rubutun shine baki daya yayi trending a safiyar yau ta raba.
Inda baki daya ya message din ya dauki hankalun mutane fiye da tunanin mai karatu, domin magana ake ta gyara da gyara kai.duk wata kafa sune dai labaran da suka zama latest irinsu.....
Facebook
Tiktok
Instagram
Telegrams
Twitter
Jikin sanyin safiyar yake dan running kadan kadan a cikin kewayen anguwar ta victoria Islan gefensa lioness, said gefen damar sa Vincent ne gefen haggunsa kuma axton ne, daga baya kuma miles ne sai lioness dake a gaba.
Kare ne na musamman ba irin sauran karnuka bane ROSER ce ta Haifa mishi.
Tana haihuwasa tabar duniya shi kuma Ak ya dauke shi ya kaishi wajen ZAKI aka chakudashi da yayanta ita ta shayar da shi duk ayyukansa irin na zaki yake yi komai tare da lioness yake yi. Suna kaiwa gida ya bude dakinsa ya maida shi bayan ya dan shafa saman kansa tare da zuba masa ruwa a tsakiyar kansa. Tamkar wani mutum ya wani irin girgiza tare da fesar da ruwan dake jikinsa, Ahankali yabar wurin yana nufar compound din gidan.
Duk inda ya wulga sai kaga wadan nan samudawan dai suna risina masa tare da gai da shi.
★★★
"Will you shut that your dirty mouth up!, are you stupid Ina magana kana yimin zancen banza da wofi, kodai ka samu tabin hankaline ban sani ko ban sami labari Impossible wannan bamai yiyuwa bane"..
Yadda ya hayayyako yana masifar kadai zai sheada maka koma miye aka fada masa a cikin wayar bame dadi bane.
" Me gida ka yarda dani na rantse da uban daya haifi ubana Salman baya cikin airport din nan, kasan bazan maka yawa ba fa me gida"
Sosae jikin Isa Manu ya dauki wani irin Mazarin bala'i Wanda safiyar yau ne aka sallameshi daga hospital, ta karfin tsiya bawai don ya gama samun sauki ba.
"Kai lele karka sa jinina ya tafasa fa, in banda zancen banza taya za'ace an rasa dan mutum sukutum tum a airport. Hauka ma kenan yanfa kaga last call nawa da salman din du du du bai wuce 40 minutes ba"
"Na rantse da assamadu me gida bincike iya bincike nayi amma fa maganar gaskiya salman sammm baya cikin airport din nan.....
"Stop your dirty mouth Lel...
Chak ya tsaya ba tare daya kai ƙarshen Eee ɗin ba sakamon rumgumeshin da yaji anyi ta baya, kafin ya tsinci murya ɗa mafi ƙololuwar soyuwa a gareshi yana furta.
" Nayi Surprise Daddy"
Wani irin guntun numfashi Isa Manu ya fesar tare da juyo da Salman zuwa gabansa, sai kuma yaɗan shiga bubbuga gadon bayansa tare da furta.
"Daddy's boy kafa tsoratar dani sosai irin sosae ɗin nan fa nake nufi"
"So sorry daddy" Salman ya furta tare irin kama gefin kunnen sa guda. Wani ƙayataccen murmushi Isa Manu ya saki tare da nufar stairs da yaron nashi Yana faɗin "kai dai muje sama akwai abubuwan yi da yawa a gabanmu" nan suka nufi saman abinda.
Har ɓangaren sa ya kaishi saida ya tabbatar Salman ɗin ya shige bethroom kana yabar ɗakin yana furta.
"Karka ɗauki dogon laƙaci daddy's boy ka sameni cikin office ɗin cikin gida just 40 minutes kawai na baka"
Ficewa yayi a sashen ta wata ɓarauniyar hanya.
45 minutes ago
Sai gashi ya fito sanye cikin ƙananun kaya na shan iska, office ɗin daddy'nsa dake cikin gidan ya nufa direct. Yana tafe yana latsa faskekiyar wayar dake rike a hannunsa.
Kai tsaye ya tura office ɗin mahaifin nashi ba tare dako neman izini ba, da sauri Isa Manu daya lula wata duniyar ta daban ya ɗago kansa tare da duban her yaron nashi abin alfaharinsa, ganin yadda daddy'n ke kallon sane ya sanya shi ƙarasowa cikin office ɗin yana zama kan kujerar dake facing da mahaifin nashi. Wasu files ya janyo tare da turasu zuwa gaban Salman.
Files ɗin ya shiga dubuwa sosae kafin ya ɗago kansa yana dubar mahaifin nasa tare da ɗan fada fuska yana wani irin yamutsata.
"Daddy?"
Ya faɗa cikin wata kasalalliyar muryan dake nuni da taɓarar nan irin ta ƴaƴan hutu.
"Yes daddy's boy duka abin da kagani a jikin files ɗin haka nake son komi ya tafi a yadda na tsara"
"Amma daddy meye amfanin haɗa alaƙana da ita yarinyar da ka sako batun neman neman aurenta?"
Wani dogon numfashi Isa Manu yaja tare da tattaro hankalin sa baki ɗaya zuwa ga Salman ɗin.
"Ita kuwa take da amfani daddy's boy, idan har hasashena ya bani daidai yarinyar tana da wani ɓoyayyan abu kodai tana akwai abinda ta riga ta sani kame da wani abu!"
Ya sauƙe numfashi kafin yaci gaba da faɗin.
"Tunda har akayi kidnapping nata Ni meyasa basu haɗa dani ba, neman aurenta da zaka shiga shine zai janyo hankalin koma waye zuwa gare mu. Kuma yarinyar zata kasance a ƙarƙashin ikon mune hakan shine first kafin mu tafi plan B"
"Amma daddy....
"Amma me? Daddy's boy"
Isa manu'n yay saurin tarar numfashin Salman ɗin. Hakan ya sanya shi yin shiru ba tare daya sake yunkurin furta ko wacce kalma ba.
"Hakan shine best solutions namu boy kana a tada hankulan jama'a. Ka sanya su Bom fire su tada zanga-zanga game da kwamushen su governor da kuma minister da Akayi ta haka ne kaɗai zamu cimma burin mu. Ya zaman mun jefi tsuntsu ɗaya da dutse biyu kenan Ni dasu Boshosho zamuji da sauran".
"Wow Wow hoooooo wuuuu woohoo hooo good idea daddy ina alfahari dakai....
Salman ya fadi yana ihu tamkar wani ɗan daba.
Mu haɗe a next fage my gold fan's......
~ BY AMMEY LAYLERH ✍️~
*🦅 MIKIYA 🦅*
_Mai hangen nesa 👀_
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________
*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 17&18
🤍🔥✅
★★★
#ANNEH POV
Kwananta biyu aka sallamota bawai don ta gama warware wa ba saidan sallamar data naima da kanta. Tunda ta dawo cikin matan gidan babu wanda ya ko leƙo inda take, duk da kuwa cewar suna sane Amma baƙin hali da sama Rai wahala ya sanya babu wanda ya kalli inda take.
Ita kuwa samm ba su bane a gabanta ɓatan ƴar tane kawai damuwanta, duk irin uban fari da jikin da take da a cikin kwanaki uku babu shi ga duhun da farar fatarta da sirka. Kasancewar jikinta da suffarsu irin na cikakkun larabawan nan ne wani irin kyau da haiba Anne ke dashi. Wannan shine kyau nata da yanayin kyawun jikinta shi yafi komai ƙona zuciyarsu abokan zaman nata.
Tana zaune saman darduma tayi irin kifa kan nan na rashin samun nutsuwar zuciya. Yanzu a wanne hali *DIDI* take dama haka rashin ɗa a kusa dakai yake?, Dama haka ko wacce uwa take ji idan tana a irin halin da take?.
Toma wai miya haɗa *DIDI'ƊINTA* ta wannan AK ɗin? Ak is a known criminal in Lagos, ta gagari kowa he is a kidnapper as well as an arm robber.
"Ya ALLAH ya ARRAHAMANU ka kare min *DIDI* aduk inda take ka bayyana min ita cikin amincinka ya zul'Arshim majeed"
Wani irin suya zuciyarta take mata yau inama ace tana da Asali? Inama ace tana wata ko wani ɗan uwan, yau inama ace tana da mahaifiyar da babu abinda zai hana ta rungume ta tayi kuka, tayi kuka iyaka kuka tayi kuka me sunan kuka ko zuciyarta ta samu salama da nutsuwa. Cikin zubda hawaye ta furta _"SHIN WACECENI?"_
Kamar daga sama taji Muryar maman haidar tana furta.
*"KEBA KOWA BACE face tsintacciya mara asali mara galihu ƴar tsintuwa wacce uwarta tayi cikin shegenta ta hullar a bola"*
Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfin bala'i tana jin yadda ƙirjinta ke sama da ƙasa.
"YA RABB!"
Ta faɗa tana wani irin fesar da iska ta cikin bakinta me zafi.
Kamar daga sama taji ƙarar shigowar sako a wayar *DIDI'ƊINTA*
Sake kulle idanuwan tayi kafin jikinta na rawa da janyo wayar data zame mata tamkar itane meerah'ɗinta. Hannunta har karkarwa yake wajen buɗe saƙon domin gani take a kowanne loƙaci kan iya turo saƙon bayyanar meerah'ɗinta ne ta cikin wayar.
Sai dai kash!.....
Saƙon ma bai hada hanya da kidnapper's ɗin ba, saƙo ne da akan turo mata duk shekarar duniya na zagayowar ranar haihuwarta ta wata ɓoyayyar Number.
Ga abinda sakon ya ƙunsa.
*_ OHhhhh On your birthday, I want to remind you that you are special, not only to me but to all those who are privileged enough to know you for the amazing person you are. People like you are hard to come by, but getting to have a woman like you is indeed a gift, People tell me that the best years are still to come. I have to agree with that because my upcoming years will be spent with the world’s most amazing woman.
Happy birthday to someone who improves every life she enters. You always know how to make an impact, but none so strong as the one you made on my heart. I will turn your black and white world into full-blown technicolor. Happy birthday to the leading actress of my JAAN my SUNSHINE,
If anyone is deserving of all the happiness in the world, it’s you, you are a wonderful mom, a loving woman, and a fantastic human being.
Happy birthday 4ever❤️ Barka da zagayowar ranar haihuwa my JAAN May your birthday be filled with joyful moment❤️_*
Tun bata kai ƙarshe ba taji wasu zafafan hawaye suna bin gefen kumatunta
*"ALHAMDULILLAH"*
Ta faɗa cikin wani irin amon murya Incheerfully.
"ABTINI MEERAH, I Missed her with All my heart ANNE ki kaini wurin beloved Nima"
Raiha ta cikin muryan da yaci kuka sosai.
"DIDI adda'armu take da bukata yanzu Raiha kici gaba dama addanki adda'a Allah ya bayyana mana ita cikin amincinsa.....
Da sauri Hajiya Hajiya umma dake tsaye tun ɗazun ta sanya bayan hannunta tana sharce ruwan hawayen tausayin Anne'n, Wacce ta kasance itane tamkar uwaa ga Anne'n. Domin wani irin girma take bata irin na ƳA da UWA. Labulen ta tura tare da shiga ɗakin da sallama kasa amsata duk suka yi domin rumgume junansu sukayi suna wani irin kuka me tsuma zuciya.
Zaune takai kan ɗaya daga cikin kujerun parloun.
"Shin dama ashe idan Allah ya jarrabi bawansa da wata ƙaddarar kuka ake AYSHATUL HUMAIRA?, Allah ake miƙama dukkan al'amurran ata kai kuka a gareshi domin shine buwayi gagara misali mai kowa mai komai! Ce ALHAMDULILLAH"
"ALHAMDULILLAH"
Ta sake maimaita wa cikin ɗacin murya, kafin ta kife kanta saman ƙafafun Hajiya umma cikin wani irin raunin murya ta shiga faɗin.
“Ni ma ina da buri ina da mafarkai irin na kowacce ƴa mace ina da burin na rayu tare da ƴaƴana ba kamar yadda nawa IYAYEN suka zabi wulaƙantar dani ba. sai dai kash ƙaddara ta shata min liyi da hakan ta sanja min nata salon yadda alƙalamin ya zana dole haka zanbi babu yacce na iya. Ni musulma mace me ƙarɓar ko wacce iriyar aduk yadda tazo min.
Daga loƙacin da Akayi kidnapping DIDI sai tsoro da fargabar me zai faru ya tasoni gaba! Amma dana tuna Allahu buwayi gagara misali sai tsoron hakan ya fita a raina.
Zuwa yanxun yaci ace na daina ma ko wacce iriyar ƙaddara kuka UMMA idan nai duba da yadda zanen tawa ƙaddarar ta kasance min. Kenan ƙaddarar ɓatan DIDI Share fagen wata tafiya ce mai sarkakiya da ɗaure kai.