Showing 60001 words to 63000 words out of 69951 words

Chapter 21 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8191

gashin nan daure daga kasan keyarsa ya dauresa har yana dan sauka jikinsa. Kai tsaye saiya fiti a hasalin balarabensa. Babu mai ganin idanunsa kasancewar toshe yake da shade mai duhu sosai. Wanda hakan shine ya sake bayyanar da taswurar halittar kyawun hancinsa daya zauna daram kan fuskarsa. Kafin kace mi tuni kamshinsa ya baje wajen, Gaba daya securityn ne suka sake kamewa kansu sukai cikin nuna tsantsar girmamawa a garesa. Wani irin dakune fuskansa yayi daidaj lokacin da fadawan ke zunewa akan gwawowinsu.
Sassanyan iskan dake kadawa da kamshin furanni ya sake shaka. Kafin ya fara takawa a hankali cikin yanayin izza da zallar sarautar dake ratsa shi gaba da baya. Kai tsaye part dinsa dake tsakiyar masarautar ya nufa dake dama zaid da kanshi ya gyara may tare da jesra sukai aikin.
Wohoho anan fa akeyinta mutanena Ni naga ikon Allah a wurin nan.
Tashin kai tashin gari kenan, na tabbata idan mutum karamar kwakwalwa gareahi babu abinda zai hanata juyewa a wannan lokacin, zanso ace kunga yadda Nera da nera ke kuka a cikin bangaren Ak. Luxury da luxury life ake magana malam, komai dake Cikin bangaren luxury da luxury ne ka iya siyansa sa, wani irin mahaukacin passage ne me kayatarwa, a nutsetstsen lafiyayyen parlounshi na farko oummey'nshi sai jesra ne a zaune domin gani suke tamkar kafin goben abinda suke son gani ga gudan jinin nasu ya disashe.
Wani irin murmushin bazatane ya bayyana a saman kyakykyawan farar fuskan shi da gudu jesra ta fada jikinsa tana saki kuka mara dalili. "Trouble meker har yanxun baki girma yhuyhu gurl"
Sai kuma yadan yi jimmmm tuno waccen yarinyan da yayi. Oummey ce ta karaso itama tare da hugging yaronta tana sama lallausan gashin kansa. Gashin kansa tadan ja tare da balla masa harara irinta uwa da dan nan.
"Ouchhhhh Ommu!"
Ya fadi yana kaiwa durkushe gabanta.....

*BY AMMEY LAYLERH*




*🦅 MIKIYA 🦅*


*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 45&46

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# Hope
# courage
# Survival
# Humanity
# Inspiration

🤍🔥✅✅✔
Wani colourn kyakykyawan murmushi ta saki tana sake janyo kansa tana dorawa akan kafafunta.
Kafin wasu hawaye masu zafi suka shiga zubo mata. "Garga me martaba! Lokacin bayyanuwar boyayyiyar gaskiya ne yayi, Alkawarin kare masarautar EMAAR's nake son kamin....
Ta fadi hawaye sosae na balle mata wani irin dauke kansa yayi yana kallon bayansa. Sai kuma ya juwo tamkar wani zaki ya goge mata hawaye ya ce, " You don't have to cry since you have me, i promise Insha ALLAH to be there for you no matter the weather, I promise to you and I promise to be your one and only till the end of time! Na dauki Alkawarin kawar da gurbatattun cikin masarautar nan Insha Allah Oummeyyy!!!"
Ya fadi yana me dafa saman kanshi da hannunta yake hade da nashi hannun. Wata nannauyiyar ijiyar zuciya ta sauke tana mikewa tsaye.
Ganin dare ne ya sanya oum yi masa sallama ita da jesra suka tafi, har bakin part dinsu ya mikasu da kansa cikin daya daga cikin motocin da suka daukosa.
Shima zaid nashi bangaren ya wuce dake jikin ma ak din daga barin damarsa, kayan jikinsa ya zame tare fadawa bathroom wanka yayo duk da kuwa cewar dare ne, Silk kayan barci mara nauyi ya zira bayan ya feshe jikinsa da mayun turarukan.
kai tsaye lafiyayyan hadadden gadonsa me kama da alkaki ya nufa. Dakatawa yay daga shirin kwanciyar da yake ya sake dora idanunaa akan yar karamar cctv footage din dake sakale tsakanin wasu manyan flowers guda biyu, murya kasa kasa ya furta.
“camera?”
Wani irin bacin raine ya ziyarceshi lokaci daya tare da furzar da huci mai zafi daga bakinsa, sai kuma ya cije lips inshi yana ayyana shikenan da aure ne ma dashi. Camarar ta riga ta gan may mata masu ita su gane masa sirrinsa, Sa'ar shi daya shi mutum ne da bai iya tsiraichi ba kowa shi kadan sane kuwa. Wani irin naushi ya kaima manyan flowers din a take suka tarwatse.

Duk wani lango da sako na bedroom din sai daya bincike ko ina. Babu wata kamara bayan wannan din dai, fasa kwanciyan yayi ya dau systerm nashi ya fara aiki cikinta, da dukkan alamu ransa a bace yake daga yanayin yadda yake sarrafa laptop din kadai zaka gane haka.
Kiran sallar farko ya mike tare fadawa bathroom alwala ya dauro yana ficewa a part din kai tsaye. Babu wanda ya ganshi in banda ladanin daya kira sallar, Kai tsaye bangaren ladani ya nufa yana zama haka har mutane suka cika masallacin Aka tada sallah!.
Babu wanda ya san da zuwansa haka babh wanda yayi tsammanin ganin a time din, Wannan nutsatstsiyan muryan nashi shine ya ankarar da mutanen dake cikin masallacin tare da zaburar da wasu da sanyasu faduwar gaba. Haka sautin kamilalliyar muryansa yacu gaba da tashi cikin kyakykyawar kira'arsa a cikin suratul Ma'ida. A kuma daidai lokacin me martaba ⭐ sarki Hassan Al-hassan gabban jikinsa suka fara motsawa ata sanadiyar jiwo wani babban gurbin dake cikin tsakiyar kokon Ranshi. Sanadiyar karatunsa daya karade baki daya katafanin cikin masarautar.
Haka muryansa ya ringa karade ko ina da ina na cikin fadar tare da ratsa zukata, inda wannan muryan dai ke firgitar da wasu! Wasu kuwa ta saukar musu da nutsuwa tare sa sanyaya gabban jikkunansu.
MOH JIDDOH kuwa wata kalan katantanwa tayi jin sautin fitar muryan da ko baka gaban me ita take da tsananin rusuna zuciyar mutum da ladabtar dashi.
AL-HUSSIEN kuwa dake daya daga cikin na gaba gaban jam'i baima san sanda kafafunsa suka soma rawa ba yana neman kaiwa zaune. Amma ya dake yaki bama ko wacce alama nuna kanta a tattare dashi, Yana sanye ne cikin cikakkiyar shigarsu ta larabawa cikin wata farar kuwait jallabiya sai shiramin daya nade kansa dashi, sai wani farin glass din daya sanya.
Bayan idar da sallarn nashi sosae yayi karatu tare da gabatar da adhkar, Har zuwa sanda gari ya fara haske. Xuwa lokacin manyan dogaran fada sun kewaye gaban babban masallacin musamman ma hanyar da zai fito ta wurin, Wambai, Waziri, maga tajarda, Riga daki, suna can sashen me martaba zaman isowar Garga din, Cikin wannan izzar da dan banzan takun nan nashi ya fito nan fa dogawarawan nan suka masa wani irin dafifi. Kowa nason bashi garkuwa wasu suna gaba wasu suna baya.
Kai tsaye apartment din me martaba suka nufa yana a tsakiyarsu, sun sanya wasu kyawawan sandunan zinare gefe da gefen Ak din. Hasken streetlight din dake kewaye da ilahirin masarautar na sake
Duk inda tawagar Ak suka gitta hadimai zubewa suke akan gwuwowunsu suna mika gaisuwa. Ko sau daya bai daga ido ya kalla kowa ba, sai hadimansa ne ke amsama duk wanda yay gaisuwarn. Tun a harabar shiga babban sashen me martaba sarki Hassan Al-hassan din ak ya dakatar da dukkanin hadiman. Sashen Sarkin⭐ shine shahi mafi kyawu da kawatuwa da duk wasu kayan kyale-ƙkyale a masarautar EMAAR's din. Gini ne da aka ginashi da zallar gilashi. Yana da hawa biyar dan haka sai da lifter kana kake isa apartment na sarki hassan din, Asalin apartment nashi kenan zama lissafa muku irin uban dukiyar da aka narka a ciki ainahin fadar me marta ban batama kai lokacine kawai.
Su kansu dogayen benayen dake gine a fadar abin azo a kallo ne. Idan kahau hawan karshe kuwa na cikin ainihin fadae duk abinda ke faruwa a cikin masarauta EMAAR's din kana iya kalla daga saman fadar.
Kai hatta da wajen masarautar ma kana iya hangowa. Hadiman dake tsaron sashen matsayin sojoji suka maye gurbinsu wajen take ma Ak din baya har xuwa parlourn farko. Anan din ma hadiman zubewa suka dingayi kasa kawunansu a risine domin girmamawa a gareshi har zuwa falon na biyu. Haka anan dinma wanda suke tare dashi zuwa parlou na biyu suka dakata, na falon na biyun na take masa baya har zuwa parlour na uku suma iyakarsu nan,Anan kuwa wani basamuden soja daya ne ya masa rakiyar wanda shine amintacce da yake iya haurawa har zuwa falo na hudun. Wani badakare ne kwalli daya tal a hawan karshen wanda saida amincewarsa ne kake iya ganin Sarki hassan Al-hassan kai tsaye din,Anan riga daka ha kwashi gaisuwa wurin Ak tare da bashi izinin ganin me martaba kai tsaye.

Saida na'ura tayi kururuwar isowarshi tare da tantance shi kana ya sanya kansa zuwa hasalin FADAR EMAAR's din. Wani irin numfashi ya sauke me dumi yana jin yanda namomin jikinsa ke wata iriyar tsuma, Ahankali ya lumshe kaifaffan idonsa yana ambatar sunan Allah. Kafin ya sake bude idon ahankali kai tsaye akan MOH JIDDOH dake harde bisa kilisa tana cin inibi cike da ƙkasaita irin ta masu isa ya fara sauke idonsa.
Itama daga idanun kadan tayi ta dube shi a sheke tare da zubarwa
tare da kara hura hancinta sama,

Wata Kujerar narkakken zinaren dake dunkule lik rug maga daka ya janwo zuwa gaban Ak. Wani irin zaune yakai zaman nan nasa mai cike da isa da tsantsar izza. Wanda hakan ke haukata wasun su domin zamane da yake fidda tsananin kwarjini da haibar da Subhanahu wata'ala ya masa.
Crossing kafarsa yayi daya kan daya yana jan trow trey'n dake gaban MOH JIDDOH wanda yake shake da yayan itatuwa.
Inebin dake narke cikin zuma ya dauka tare da kaiwa bakinsa yana dan cirar kadan. Wani irin motsa bakinsa yayi tare da lumshe idonsa saboda yadda tsananin zakin inibi da zumar suka tsinka yawun bakinsa. Tare da ratsa har tsakar kansa kai tsaye.
Wani irin marin bazata takai ma fuskan Ak din da idonsa ke lumshe MOH JIDDOH tayi. A bazatan taji shima ya rike hannunta karafff tare da bude tsayayyun idonsa yana dan girgiza mata kansa. Irin I DON'T CARE MANNER's din nan.

Kyawawan idanunta ta juya a fuskar Al-hussien sai kuma ta janyesu zuwa ga Mahboob da mandood. Dama duka sauran mutanen dake cike da dakin.
Shi kuwa Ak dake rike da hannun Moh jiddoh yi yayi tamkar besan abinda ya aikata ba, saima maida idonsa da yayi yana sake kullewa. Yanda yai tamkar besan mike faruwa a wajen ba shine ya sake hasala Moh jiddoh..
Cikin muryan daya fara manyanta amma kuma yana fita da tsananin kaushi ta furta
"Me kuke bukata da bazaku wanke min fuskan wannan tantirin yaron da mari ba! Kana kumin dumu dumu da jikinsa da duka? Ko saina baku umarni ehhhhh!!?"
Ta fadi tana watsama su Alhussuen din wani mugun kallo.
Cike da girmamawa Al-hussien ya dan rankwafa. Tare da fadin. "An gama Ya ummienah Umarninki shine abin jiranmu kana kuma wajibane a garemu"

Kamar yanda be motsaba ba haka be bude idanuwansa. Saima karkada kafafuwansa da yake yi cikin isar da yake jin yakai koma ya zartata.
Yunkurowa Al-hussien yayi da niyar kashe fuskan AK da mari. Wani irin bude idaniyarsa yayi tamkar zaki wurgi da hannun Moh yayi tare da damkar na Al-hussien din yana sauke firgitattun idonsa akan shi.
Kafin ake yayi wani abu Moh ta dauke kyakykywar fuskarsa da wani lafiyayyan mari.

"Ka sani HAU'WA KULU bata yafiya haka bata daukar kuskure koda kadan ne bare kuma me girma irin naka, ka sakar min da hannun yaro daka rike shi da kazamin hannunka da bashu da tsarki!. Ka sani taba hannun mutum irinsu Al-hussien sai hannun daya cika duka sharrudan musulinci, ba kazami irin naka ba daya gama cakuduwa da dattin zina"
Atare Oum, Adeenerh, jesra, al-mustapha suka wani irin kulle idonsu da karfin masifa.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"
Oum ta furta tare da RAZEENERH da suke kira da MAH. Mahaifiya Almustapha sai kuma yarta ta fari wacce tayi batan dabi sama kasa aka nemeta aka rasa.
Shi kuwa boss din wani irin tsuma jinin jikinsa ya dauka.
A fusace zaid da bazai iya jurema cin mutumcin da ake ba biyuninsa bane ya mike.yana toshe kunnuwansa tare da furta
"STOP"
Mandood ne ya mike tsayen shima ta hanyar tarar zaid din yana jefa masa wani shegen kallo tare da fadin.
"Me yasa kake da taurin kaine?, Idan ba'a kasa dakai ba baka gaggawar dauka domin gudun abin fada ko martanin da za'a iya maida maka"
Wani shegen kallo ya wurgama mandood din tare da cewa.
"Niba rago bane da zan zauna a gaban idona naga ana aibanta jinina na kyale haka! Taurin kaine dani! Ni mutum ne da ako da yaushe yake cin nama da nama karya kasuwan nake nabi ta kansu na mitsitstsikesu domin na gama amfana da tsokar jikinsa"
Luuuuuu Ak yaja idonsa dayabi zaid dashi kamad zai kulle su gaba daya sai kuma ya budesu war akan twins dinsa gudan jininsa zaid.
Wani irin fashewa da kuka Moh tayi tana mikewa tsaye tare da fadin.
"Tabbas jinin Maryam masifa ce a garemu, ni dama tun farko banso hassan ya aurita ba wllh! Har iyaka na ketara masa akan auren wannan me bakin jinin, na rantse ba zata shigo cikin gidan a matsayin matar aure amma saida ta shigo tazo ta haifa mana jaraba da masifa a masarauta"

"Ashe kinga kenan baki da matsayi da iko akan dan da kike ikirarin naki ne, duk da kin yankamar iyaka amma saida ta ketara, kince ba zata shigo ta shigo! Ko wanne mutum yana da gari kana yana da iki a inda yake. Ba tare da kin tare ta daga shigowarma kuma ta shigo harta haifa miki magadan masarautar EMAAR's kina ji kina gani wannan masarautar ta zama tata. Wannan garin ya zama nata bayan wannan mene bakyason ta sake tsallaka miki, wannan masarautar tamu ce garin ma namu ne a gaban idonki zamu mulki masarautar dama kasar da kike ikirarin Oum bazara shigo ba. Saidai masu hadiyar zuciya su hadiya in yaso ta buga su mutu"
Ak ya yaboma Moh maganfanun da tunda uwarta ta haifeta ba'a yaba mata koda kwatancinsu ba.
"ABDOUL-MALEEK"
Muryan Oum ya katse shi daga wata maganar da yake shirin sake yanko mata.
Hatsaniyace sosai ta kaure a cikin dakin kowa yaki ya rusuna kowa ji yake da nasa zafin kan. Abinda ya rusunar da rigimar nasu faduwar da Oum tayi. Wannan shine dalilin lafawar komi haka Ak yama Oum dinsa daukar jarirai ya fice da abarsa zuwa clinic din masarautar, Shine da kansa ya duba Oum nashi kasancewarsa dactor, kana pilot ne idan yaso babu inda baya ketawa a kasashen duniya. Kana gashi Babban soldiers wanda matakin farko ma da Marshal ya soma.....

⭐Washe gari ⭐
A nutse yake Sakkowa daga matakalar benen zuwa entrance din da zai sada shi da bangaren oum dinsa. yana sanye cikin wasu fitinannun lallausan farin yadi. yayin da kuma ƙkafarsa ke sanye cikin wani black combat toms mai kyau irin na yayan sarakunan nan, Sai wata mini jacket din daya dora saman kayan yar filic da ita.
babu abinda ke tashi ajikinsa sai wannan fitinannen kamshin turaren nan nasa me azabar tsada da bama wanda yake shakarsa cikakkiyar nutsuwa ta musamman.
Tamkar wanda akema wanka da madara haka farar fatar jikinsa ke daukar idon me kallonsa. Cikin cikakkiyar takun da kallo daya zakayi masa ka gane cewar kakkarfa ne sabo da motsa jikin da yake aduk kwanan duniya ta hanyar machine gams.
Blue eyes din nan rufe cikin wani luxury sun glasses wanda ya sake bayyana taswirar karan hancinsa da yake mike ziyat tamkar da biro aka zama masa shi daram. pink lips din nan nashi sai wani kalan glowing yake tsananin taushin na bayyanuwa wa me kallonsa, kallo daya zakama Ak ka gane shi din me kyau ne kana na musamman masha Allah,domin allah ya wadatashi da komi najin dadin rayuwa. cike da kwanciyar hankali da nutsuwa yake takawa irin takun dake nuna shidin kakkarfan namiji ne kana tsayayye. Marar daukan wargi da in Manners din nan.
Kai tsaye babban katafaren parlourn Oum dinsa yama tsinke wanda girmansa yake dauke da wasu tsadaddun furnitures, parlour ne mara tarkace amma yana da kyau na fita daga hayyaci. Kayatattun royal cushion din dake zagaye da parlourn sunyi may kawanya, daga tsakiya kuma akwai wani shimfiɗaɗdiyar red carpet da throw pillows akai, sai wani ƙkaramin round table daga gaban wani kebantaccen rug, sai babban plat screen plasma din da ya kusa cinye bango guda na parloirn don girman shi. iskan A/cn dake kasawa kai tsaye yake fidda wani irin daddan yanayi a cikin parlourn, dubansa ya kai ga ƙkaton

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login