Showing 21001 words to 24000 words out of 69951 words
Wata kalar ƙaddara ce mai rikitarwa shimfiɗa ce wacce take tafe da nata salon. Yaushe wannan rufaffen sirrin dake shimfiɗe a cikin zuciyata! Zai fito fili?, A cikin ko wacce rayuwa akwai mutuwa haka ma a cikin mutuwa akwai rayuwa toni a wanne mizanin nake?
Mabuɗin kowacce ƙofa makulli ne sai dai Ni tawa ƙofar wani irin wawakeken rami ne wanda aduk loƙacin da wani yayi yunƙurin bi ta cikinsa yake ruftawa dashi. Shin Me nama nawa IYAYEN da suka zabi wulaƙantar dani? Ki bani Amsata UMMA!!!..........
Ta faɗa da wani irin gursheshen kuka irin wadan yake fitowa daga cikin tsakiyar ƙirjin nan "ALHAMDULILLAH Allah abin godiya Allah mun gode maka"
Sune kalaman da Hajiya umma tayi ta maimaita wa kafin ta shiga nanata kalmar
_INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN²_
Hakan ya sanya Anne kamawa itama suka hau maimaitawa a tare harda ma Raiha.....
By AMMEY LAYLERH ✍️~
*🦅 MIKIYA 🦅*
_Mai hangen nesa 👀_
*~We want an end to oppression💪~*
https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________
*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 19&20
🤍🔥✅
★★★★
*_KUWAIT_*
_Kuwait officially the state of Kuwait. Is a country in west ASLA.. it is situated in the northern edge of Eastern Arabic at the tip of the Persian gulf. Bordering Iraq to the north and Saudi Arabic to the south. With a coastline of approximately _
*_KUWAIT_*
*_7:16pm_*
_ARABELLA BEACH HOTEL_
*_Bad decisions mayco lates is let's party alcohol our later. The palms beach_*
★★★★★
Wani irin deep romantic sound ne ke tashi ƙasa sosae cikin wata iriyar romance voice ne ke tashi cikin muryan larabawa. Sanye yake cikin wasu fitinannun fararen qanannun kaya da farar singlet yayi stocking farar singlet in ta cikin wandon ya ɗaure da belt. Sai farar rigar daya ɓalle duka maɓallanta ya barta a bude. wuyanshi rataye da guitar yana kaɗawa ahankali....
Abinda zaifi ɗaukar hankalinka a wajen shine tarin jama'ar dake cike da wurin, yadda kasan tururuwa sai ihu suke da whistling yayinda shikuma ke rero waqarshi cikin cool voice nashi cikeda nutsuwa da kuma burgewa.
kamillaliyar fuskarnan tashi ma'abociyar fara'a dakuma yadda dimple dinshi ke loɓawa shine abu mafi ɗaukar hankali a gareshi.
Idanunshi a lumshe suke wanda hakan yaba zarazaran lashes ɗin shi damar haɗewa, ga uwa uba pointed nose ɗin shi daya dace da fuskarshi.
Dama duk wani ɗan zafin Kai duk inda 8pm to a Arabella hotel take mashi kowa hankalinshi da imaninshi ya tattare ne akan wannan tsayayyen matashin dake tsaye gabansu.
kanshi sanye da headphones samm babu ko pcarp a kansa, sai kwantaccen gashin dake nan kwance saman qeyarsa irin na cikakkun larabawan nan in banda walwali da ɗaukar idanu babu abinda sumar take aikin yi, ga wani irin qamshin haɗa haɗen mayuka masu azabar ƙamshi da tsada keta faman tashi.
Har wani irin luuuuuu ya keyi da idonsa alamar waqar na hawan kansa sosea
Tsaiwarsa ya ɗan gyara hannuwansa zube cikin aljihun wandon sa idonsa lumshe, Cikin wani irin Sound wizard In dake tashi a cikin iyaka zagayen room ɗin da yake. Ga color's blue red popple dake haske irin ta cikin dum Night ɗin room ɗin. Mutane sai ihu da whistling suke suna ƙiran *_ZAID EMAAR's_*
*_ZAID KUWAIT_*
Shi kuwa ya riga yayi nisa Afif tajuddeen ne ya hauro kan step ɗin da ZAID ɗin ke tsaye ɗan raɗa ya masa a kunnen sa kafin ya lalubo tafin hannun ZAID ɗin ya saka mishi BURGER yana barin wurin.
_9:30pm_ ya tashi duk da kuwa maganar da Afif tajuddeen ya raɗa mashi amma saida ya gama harkan gabansa.Duk da haka Bai samu kansa daga barin hotel ɗin ba sai 10:10pm.
Yana fitowa coumpaun ɗin hotel mahaukatan security'n dake girke da wurin suka yi saurin buɗe may ƙaruwar 2024 Toyota grand Highlander.
Yana faɗawa ciki suka ma manyan motocin key tare da cilla hancinan motocin nasu kan shimfiɗeɗen kwaltan babban birnin kasar Kuwait ɗin.
A gaban wani irin Mahaukacin katon gine nema zance ne ko mention OHO min, amma dai zanen ginin kai da gani ma ba sai an tsaya baka amsa ba zaka gane cewar a masarauta ce.
*_EMAAR's EMARANCE MENTION_*
Shine sunan dake walƙiya ta saman ginin DPY WELPAPER ɗin dake haskaka ginin da difference color's.
A ƙa'idar wannan masarautar ba'a hong ko kaɗan. Wani ɗan ficik ɗin yellow'n card ɗaya daga cikin security'n dake cikin motar ya zira. Abin mamaki sai kawai Ross gold get suka raba tsaƙiya nan motocin suka sake danna hancinan motocin su da mugun gudun tsiya.
Ya Ilahi wani irin Mahaukacin katon mention ne ya bayyana masu passage daban da daban.
A bakin Ross gold get ɗin farkon wasu irin mahaukatan TIGHT SECURITY ne jibga jibga. Hannuwansu rike da manyan bindugu na tashin hankali.
harabar gidan kanta tamkar gari guda ne domin girmanta abin azo a kallane. gashi qasan shimfide yake da kwalta ga flowers of different types shufke a gefe gefen titin.
Haka suke wuce get na farko cikin uban sharara gudun nan tafiya mai nisa koko ince gudu mai nisa suka kafin su isa maid entrance ɗin gidan. Nan ma saidai Saida suka sanya wani card ɗin different da wance domin samm ma basu haɗa koda kama bane kana get na biyu ya buɗe. Ya Ilahi kai jama'a shi kanshi wannan gida ko ince masarauta yafi qarfin a ƙirata da SOLDIER'S HOUSE sai dai a ƙirata da HOUSE DIE. Eeeeeeehhhhhh mana tabbas kuwa house die tunda abinda idanuwana suka gano min kenan. A haka har Saida suka kai get na ƙarshe wanda a nan babban tashin hankalin yake.
#tight security
#Movel : mobile
#Police interpol
Kai jami'an tsaron da babu wandan da babu a cikin wannan shahararriyar masarauta, banda tarin kuyangain da suma sukama masarautar ƙawanya suka mata GARKUWA.
A hankali wannan 2024 Toyota Highlander grand tai parking a dab da wani irin azababben flat Wanda yake zagaye da tarin barori na tashin hankali, fararen sawayensa ya fara zirowa wacce take sanye cikin lallausan takalmin fata irin na sarakai,kafin gangar jikinsa ta biyo baya. Ga hasken street lights ɗin da haske harabar wurin tamkar rana, hakan shine ya sake bayyanar da tsantsar kyawun da subhanahu wata'ala yamay kana ganin mutumin kasan ƙarshe ne wajan tsari da kuma iya ado. Tuni wannan tarin kuyangain suka shiga masa kirari cikin harshen larabci. Wani irin mugun kallo Zaid ya watsa musu Azafafe cikin tafiyarsa ta sanyi² zafi² ya juya kai tsaye ya nufi plat na mai martaba *ONOYIN* (sarki).....
_"OUMMIEYHHH?.....
Ya faɗa da ƙarfi cikin ɗaga murya yana shiga makeken falon daya qawatu da kayan alatu ga tattausan carpet da duk takawa ɗaya zakaji kamar zaka nutse aciki don taushi da laushi ne.
"OUMMIEY! ONOYIN أين هو بابا ن ياكي؟ "
Ya faɗa da sautu me amsa amo.
Sama ya nufa ya fara hawa stairs ɗin da shima kanshi abin kallo ne Kasancewar stairs ɗin irin mai lanqwasar maciji nan ne. Saida ya ɗauki loƙaci kafin ya isa.
Wani qaton falon ya sake kutsa kansa ciki shima mai mugun kyau ya sake wuceshi sannan ya shiga passage din dazai sada shi da ɗakin oummiey.
Koda ya qarasa ƙofar ɗakin oummie banda haki babu abinda yake yi don yasha ha gudu sosai gani yake tamkar elevator bazai kai shiba.
Wata kyakkyawar dattijuwa na hanga zaune bisa tattausan carpet gefe kuma irin pillow dinnan ne masu kyau zagayayyu irin wanda akafi gani mostly dama na gidajen sarauta ne ta kishingiɗa akai, plate ne a gabanta cike da yankakkun fruits wanda take ɗauka da ɗaɗɗaya tana ci. Ɗayan gefen kuma shako mako ne, sai tea party, tare da mia piatte ga kuma milagro
Saurin dagowa matar tayi ta kalli saitin data jiyo muryan hubby Inta hasken dake haskaka duniyar ta wato ZAID.
(_Tsarki ya tabbata ga ubangiji mai talikai daya halicci wannan halitta mafi kyawu mai cike da haiba_)
Na faɗa daga cikin zuciyata
"Where is my papa? Oummiety!"
Ya sake tambayar mahaifiyar nashi cikin cukurkuɗaɗɗen English nashi. Idanunta ta ɗan lumshe kafin ta miƙa mashi kyakkyawan farin hannunta, noƙe nashi hannun yayi a bayansa tare da furta.
"Ohh ohh Papa na" ya faɗa cikin sakalci tare da noƙe kafaɗa.
Da hannun tamai nuni da wani tsararren room wanda yafi kama da ɗakin tan garan Domin an kawata room ɗin ne da wasu shiles row glasses tamkar irin gidan lantarkin nan.
A zafafe ZAID ke taka ƙafafunsa yana tafe yana fesar da numfashi ta cikin bakinsa kansa ƙasa yana tafe cikin sassarfa. koda wasa bai yadda ya ɗaga kansa ba bare ya kalli irin yadda uban kuyangain ke zubewa ƙasa bisu gwuiwowinsu. Shifa sammm koda wasa bai ƙyaunar duk wani abu daya dangaci sarauta ya tsani gaba ɗaya calture nasu komai a takure yake yinsa. So shi yasa sammm Allah bai haɗa jininsa da wannan sarautar ba shi mutum ne da yake son yayi rayuwarsa yadda yake so.
Da wani irin sauri yakai gwuiwowinsa ƙasa tare da kafe mahaifinsa da lulu eye's nashi da suka sosae ganin yadda jikin PAPA'N ya koma loƙaci guda.
"PAPA?" Ya ambaci sunan mahaifin nashi cikin wata iriyar raunatacciyar murya. Tare da ƙoƙarin kai hannunsa jikin PAPA'N shi.
Da wani irin Mahaukacin mari yaji ya ɗauke kyakkyawar Innocent face nash, amma tsabar jinin sarautar dake yawo a gaba ɗaya ko wacce magudanar jini ta jikinsa ya sanya ko gezau be yi ba.
"Kada ka kuskura ƙazamin hannunka ya taɓamin tsarkakken jikin ɗan UWA na" muryar 2wins ɗin mahaifinsa ya katse shi a kausashe a karo na biyu da yake kokarin sake kai hannunsa jikin PAPA'N shi bayan uban marin da MOH Ta bashi.
Da wani irin mugun gudu *JESRA* ta kulle idanunta cikin kunar zuciya.
A nutse Zaid ya ɗago da kansa zuwa ga baki ɗaya jama'ar parloun.
EL-HUSSAIN wanda ya kasance biyunini PAPA'N shi, sai MOH JIDDO wadda ta kasance mahaifiyar su PAPA'N shi.
MAHBOOB,DAWOOD, MUZAFFAR, MUSADDIQ, AL-MUSTAPHA, MANDOOD, EYESHA, MANSOOR ,REYNA.
Sune a room ɗin baki ɗaya wanda mafi yawancin cikin su ke binsa da wani irin mugun kallo, kallo ne irin na tsantsar tsana suke binsa dashi.
A...MALEEK.....
Idan baiyi ƙarya ba kamar haka Papa ya ambata saman laɓɓansa ko takan jama'ar da suka ma room ɗin ƙawanya bai biba ya haɗe fuskarsa dana mahaifinsa sa. Ta ƙarfin bala'i ZAID ya furta "ABDOUL-MALEEK?"
Wani irin razanannen kallo mafi yawancin ɗakin suka shiga bin ZAID dashi. _ABDOUL-MALEEK_ kowa ya shiga maimaita wa cikin zuciyarsa har jikkunan wasun na ɗaukar mazari, sunan da Ambatarsa kawai tashin hankali yake haifar wa, sunan da jinsa yake tada hankula bama hankali, sunan da suke ɗaukar sa wani shuɗaɗɗan al'amari a cikin tarihin rayuwar su.
_Tasssss_
Wannan karon EL-HUSSAIN ne ya ɗauke fuskar ZAID da wani irin bahagon marin da dole ya sanya shi dafe kuncinsa. Kiiiiiiiiiiiiiii MANDOOD da yafi kowa na wurin zuciya haka yaja hannun Zaid ya kaishi har bakin door yana cilla shi woje. Cikin tafasar zuciya MANDOOD ya dubi Zaid rinannun eye's nashi ya furta.
"Wannan wani shuɗaɗɗan al'amari ne, wata kirkirarriyar tatsuniya ce, sunan ABDOUL-MALEEK shafaffene a cikin tarihin wannan masarauta ka kula"
Fuuuuuuuu ya kaɗa da niyar juyawa chark ya dakata jin wata mahaukaciyar dariyar da Zaid ya sheƙe da ita. Hakan ya sanya A tsananin fusace mandood ya ɗaga hannu zai wanke fuskar Zaid ɗin da wani wawan mari. Cak Zaid ɗin ya rike hannun nasa tare da cewa "Kada kayi wannan ganganci"
Zaid ya faɗa tare da wurgar da hannun mandood ɗin gefe tare da sakin wani ɗan iskan kill smile Yana furta.
"Waya faɗa ma cewar haihuwar Sarki a Dawa kamar ABDOUL-MALEEK yana zama shuɗaɗɗen al'amari, An haifesa ne a Dawa tsaƙiyar karnuka domin farauta. Ubangiji ya bashi ƙarfin zuciyar da zai iya fuskantar ko wanne irin ƙalubale, Iyaka ambatar sunan sa yakan sanya wasu girgizar ƙasa......
"ZAID!!!!.....
MANDOOD ya katse shi a matuƙar tsawace.
Ko inda yake bai kalla ba saima cikin elevator ɗin daya wuce Direct bedroom nashi ya wuce Cikin kwanciyar hankali.
Zaune yakai kan caution tare da jan table ɗin system nashi, cikin kwanciyar hankali yake danna laptop nasa ga sanyin Ac na ratsa shi sai faman cizan lallausan laɓɓan sa yake, ga lips ɗin nasa ya kara yin jawur kamar yasa lipstick saboda ciza su da yake duk wannan latsa laplop da yake hankalin sa na can duniyar wani tunani na daban.
Shiru yayi yana tunani abubuwan sun haɗu sun cakushe masa ya jima sosai akan system nashi kafin ya kashe yana fadawa bathroom.
_1:15am_
Ya fito sanye cikin haɗaɗɗun riga da wanda palazzo ride vizzon Loƙacin da ya fara sako ƙafarsa sa a benen sauƙowa palon ƙasa, ji kake tsit duk wani halitta mai rai dake cikin palon ya nitsu tsit sun sha jinin jikin su, wasu daga cikin bodyguards kam jikin su har kerma yake saboda tsoron mugun haɗe fuskar da yayi. Domin ZAID tamkar ICE and FIRE🔥 haka yake yakan rikiɗe a duk sanda yaso. wucewa yayi ko kallon in da kuyangain suke bai yi ba ya faɗa cikin wata Black jeep Wrangler. Duk kuwa da har haɗa baki suke wajen rige rigen ɗaga masa gaisuwa, bai amsa gaisuwar ko ɗaya daga cikin suba dan dama ba amsawa yake ba sai dai ya ɗaga musu hannu dan magana na masa a duk lokacin da yake cikin irin wannan yanayin.
Yana shiga kai tsaye ya basu umarnin *Flash dancing club* (gidan rawa) Amma baki ɗaya ya rufe ko ina na jikinsa.
Motocin su Zaid na fakawa a *TOWER'S IN KUWAIT. tawagar *GANG BANG* ɗin su na kewaye motar tamkar irin wanda suke Bechelor's Night ɗin nan. Wani irin ɗan iskan aski ne akawunansu. Wasu kuma sun fake Tulan sumar sune da band.
Sune suka buɗe masa car In da kansu tare da fito dashi woje baki ɗayansu, shigarsane kawai ya fita daban da sauran domin wasun su suna sanya ne da gajerun wanduna, wasun su kuma suna sanya ne da trouser sweetheart riga...... Wani babban ɗakin dake zagaye da Gellary DPY WELPAPER suka suna wurin sai walƙiya yake.
Lallai Abin mamaki baya ƙarewa suna shiga duk waɗan da hannuwansu ke riƙe wine 🍷 suka farfasheta, sai kuma suka shiga jona manyan na'urori tako ta ina.
Tawagar Manyan DDS kenan ta ƙasar Kuwait masu ɓadda kama domin duk wata ƙungiyar dake ji ta tantiranchi a garin Kuwait zaka taras su ZAID sune na gaba gaba. Mugwayen ƴan ɓadda kama ne tsabar Tantiranchinsu basa ayyukan su a ko ina sai manyan wuraren da suka fi ko ina tacewa.
A take ɗakin ya ɗauki sautin joing na'urorin cikin kwarewa da sanin makamar aiki suka shiga aiwukansu, Rankwafo da kansa yayi zuwa ga study table ɗin dake gaban Afif tajuddeen.
Baki suka juye cikin harshen larabci suka shiga wasu maganganun dana kasa gane musu. Saidai cikin labarcin suke yawan ambatar sunan *LION🦁*.
★★★★
_LAGOS-NIGERIA_
*Ak*
Sanye ya fito cikin wasu American suit blue black Winter Sports Hat ya sanya a kan sa, bayan ya ɗaure dark black curly hair sa da ɗan ƙaramin ribom's inda tulun sumar ya fito ta ƙasan ƙeyarsa, yayi kyau over ita ma hulan ta masa kyau sosai sai dai ya bar wannan ɗan guntun gashin gaban goshin nasa a waje bai shigar da ita cikin hulan ba, fuskar nan nasa a ɗaure take tamau kamar kullun sai dai na yau ma tafi na kullun, dan ina ga yau idan sukayi ido huɗu da mai karamain zuciya nan take zuciyar zata buga ya mutu awajen saboda tsoron yadda fuskar AK tayi yau abun ba'a magana ya wuce tunanin duk wani mai tunani. sai tashin fitinannen kamshi yake hannun sa na ɗaure da diamond watch kyawawan kafafun sa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal wadda a kalla kuɗin sa ya kai $96000, kasan cewar takalmin launin baki ne sai yayiwa farar kafar sa bala'in kyau na ban mamaki wayar sa da kuma laptop na sa ya ɗauka ya nufo waje, yana taku irin na manyan jarumai ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa kasan cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma lafiyayye kakkafa ne ke tinkaro ka.
Kai tsaye Restroom nashi ya shige domin wani muhimmin aikin dake gabansa. Akan stool ɗin dake gaban coffee table ɗin yakai zaune