Showing 27001 words to 30000 words out of 69951 words

Chapter 10 - MIKIYA Book One Hausa Novel

18 Nov 2024

8178

a cikin zuciyarta. Saida Anne ta share hawayenta da bayan hannu kana ta ɗago fuskarta, ɗago MEERAH daga jikinta tayi cupping
fuskarta a raunace cikin muryan kukan ta furta.
"Yi kuka! Kiyi kuka MARYAM yi kuka!!!. Kana ki ɗauki hakan kamar haɗuwar hadarin kakane ya haɗa ,kuma ya baje ya ɓace ɓatt kamar komai ba'aiba. Karki bari abinda ya faru dake yayi tasiri a ranki dahar zai yi pinning ɗinki down. FIGHT DIDINA fight the feeling and move on!" Ai kuwa Atake ta fashe wani irin kuka me ƙona zuciya. Ɗauke guntuwar kwallar data saƙƙo masa malam Abdullahi yayi wanda yake tare da Isa Manu tare da Salman. Wanda ya kafe MEERAH da masifaffun idonsa ko kyaftawa babu, kaddai ace wannan zazzabar beb ɗin itace yarinyar da zasu yi Auren manufa da ita. Wllh Idan itace kuwa idan har aka aura masa ita babu shegen daya isa ya raba shi da wannan zazzafar bebyn.





_DOWN_

_catafares_

_Slow motions_


_AK K he's going to shikenan


*BY AMMEY LAYLERH



08104493215




*🦅 MIKIYA 🦅*


*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page23&24

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# Treason
# Strong love
# Right
# Women's travel
# The Secret Society
# Oppression

# KIDNAPPER'S
# Informants
# DEEP
# BEST LOVE

🤍🔥✅

★★★★

Da Wani kallon ka shiga hankalinka Isa manu yabi salman dashi don ganin irin mayataccen kallon da yake bin meerah dashi, Kasan Keyarsa yadan shafo yana waskewa abinsa. Kallo daya tama mutanen dake tare da baffanta ta dauke kanta daga garesu tamkar bata gansu ba, duk da kuwa ta gane isa manu don ita ba mutum bace mai yawan mantuwaba.
A mutumce cikin salon girmamawa isa manu da salman suka shiga gaida Anne da tambayar me jiki.
"Jiki alhamdullih da sauki wllh"
Anne ta amsa itama a mutumcen kamar dai yadda suka gaida tan, ta dayan gefen da kanta yake salman ya koma don bai gama morewa kallonta ba.
"Baby ya saukin jikinki?"
Ta tsinkayi muryarsa me kama da anyi bari an kwashe, ba tare data ko kalli inda yake ba taja idanunta ta kulle abinta domin haka kawai taji ta tsani mutumin farat daya. Shima daga haka ya kama kansa domin be kamata ya fara bata aikinsu tun daga yanxun ba.
Sallama sukama su baffa bayan sun ajje katuwar ledar da suka shigo da ita, duk da baffa beso hakan ba amma be ya kyalesu kawai.
Kwananta daya da wuni daya amma daga gidansu meerah babu wanda ya leko da sunan dubiya bare taya Anne murnan bayyanar da tayi.
Hajiyar salman ma tazo dubiyar haka manyan yan siyasa suka dinga zarya a cikin hospital din domin nuna karamcinsu da girmamawa wa Isa manu.
Karfe biyun rana aka basu sallama lokacin baffa baya hospital din yaje gida, suna fitowa harabar hospital din wata rantsatstsiyar black Toyota Camry 2024 ta sha gabansu, duk tsaiwa sukayi a tare suna jiman moton ya wuce ya basu hanya su tari napep ya mikasu gida ga zafin rana da yake dakar ko wannensu. Kokarin kauce may suke ganin yaki basu hanya, sake shan gabansu yayi tare dayin qasa da glass din motar yana sakin murmushinsa me kama dana muna fukai tare da fitowa yana fadin.
"Mama barka da rana Ku shigo nine fa"
Yayi maganar yana kokarin bude musu Motan domin shiga, "0'oh ba ayi haka ba salman daga haduwa kuma sai dawainiya ai nauyin saiya ma yawa"
Amma ta fada cikin hakikanin gaskiyarta, Saida yadan saki wani shegen murmushi kafin ya furta. " Haba mama dawainiyar miye zaiyi yawan matar dazan aura CE fa Insha Allah "
Da sauri ta dago kanta tare da watsa mishi wani banzan kallo, domin ita sai yanxune ma ta tuna shi, tasha ganinsa a inda bai dace ba ta dalilin aikinta da irin aikinsu na jonalist (JARIDA) babu inda baya kai mutum. "Halan kai babu zuciya a kirjinka? Nifa a duniya na tsani mutum Mara fashimta OK"
Kin dauke nasa idon yayi akanta duk kuwa yadda take jifansa da muggan kalamanta hadu da mummunan kallon da take jifansa dashi, amma shi hakan bai dameshi ba saima sake watsa nashin da yayi cikin natan, hannun Anne ta sake damka tana yin gaba abinta, da sauri yasha gabanta cikin maraitacciyar murya ya furta.....Pls mana babe don Allah Ku shiga"
Tana kokarin sake Jan hannun Anne'nta ne taji annen taki biyo bayanta, ita kuwa annen ganin yadda hankulan mutanen dake compound din ne ya Sanyata tsaiwa chakkk. Da ido tama Merrah din alamar data kalli yadda hankula ya fara yowa garesu, kamar ance kalli side din dake damanki idanunta suka shige cikin nasa kyawawan idon, yana tsaye jikin wata mahaukaciyar baka wulik din Ralls rayce car yayi crossing kafafunsa yana buga games da tsadaddar waya abinsa hankali kwance cikin nutsuwa.
Wani irin matse hannun Anne tayi tare da dan mutstsikar idonta kadan waiko gizo ya mata, still dai shi din ne tsaye cikin shigar riga da wando na long sleeves sawayensa sanye cikin wasu hadaddun snickers shoe sai idonsa daya to she su da wani mahaukacin luxary shade. Amma hakan bai hanata gane shi din bane *AK* ta furta. (Me wannan abin yake anan?) Ta fada acen kasar zuciyarta.
"Didi wai kodai kin hadu da cutar kurumta ne?"
Anne data riga ta zauna a cikin motar ta jeho mata tambayar, da sauri ta dauke kanta a kanshi tare da kokarin sanya kanta cikin motar.
*"Ashe kedin me arha CE haka ban sani ba tunda har zaki Iya shiga cikin ko wacce tarkacen shara right?"*
Haka taji saukar wucewar kalamansa har cikin tsakar kanta dap da ya kawo kansa kamar zai wuce ne.

Ahankali ta saki murmushin daya kara kawata kyawun fuskarta a karo na farko tana tsayawa chark. Sai kuma ta dan tabe bakinta tare ta sakin wani murmushin takaici kafin cikin maganarta ta kai tsaye ba tare da jin shakku ko tsoron komai ba, Idonta cikin nashi ta shiga furta.
”Ai abu me tsadane yake birge kowa koda kuwa mutum yasan bazai same shiba yakan Iya tsayawa yayi tayi duk da yasan zaren ba kalan yadin bane, amma zeso ya dandali arziki yakuma bar arziki a inda arziki yake SBD farinjini halittane metarin baiwa wadda duk tsadar Abu seyanada farinjini yake birge kowanne halitta, just if u been a black stomach man ok tell me now but u are very amazing me for ur talked”
Tunda ta fara motsa lips nata ya zuba mata kyawawan idonsa, kafin ya saki wani shegen murmushin nan nashi da mutane kema lakabi da na mugunta.
A fusace ta shige cikin motar da Sam bata da ra'ayin Shiga 5 minutes da suka shude, harta shiga kuma ta juyo again. ”Remember kasani ayau zaka kara tabbatarwa mutum crismatic ako' Ina nadabanne kuma yanada wuyar samuwa” da karfin masifa ta buga murfin motor'n.
Wanda hakan ya sanya salman kwasarta a guje suna barin kurarsu.

★★★
Har bakin kofar gida salman ya kawo su Meerah,bakin baffa na zaune cikin barantar dake kofar gidanshi suna zaune da mutanen da suke karatu duk bayan sallar asuba da kuma isha'i, dake yau kuma ranar alhamis ce karshen sati duk alhamis din duniya sau uku suke daukar karatu. Da farko be kawo su annen bane saida yaga fitowar Annen kafin merrah ta biyo baya. Da dan hanzarinsa ya nufo su har wasu daga cikin mutanen na Mara mishi baya.
Shi da kansa ya dauki yan kayayyakinsu da basu da yawa bayan ya dada musu sannu, sallama sàlman ya musu yana cewa da baffa sent xuwa dare Insha Allah, sosae baffa ya dade masa godiya yana fadin. ”Allah ya kaimu min gode sosae”
Cikin gidan suka shige shi kuma bayan sun gaisa da jama'ar dake tare da Baffan, shi kuma salman ya dauki hanya yana barin cikin anguwar baki daya.
”Assalamu Alaikum!”
Anne da meerah suka hada baki wajen ma jama'ar dake zaune gaban bishiyar setline suna shan iska, amma tari babu Wanda yayi tsakanin matan gidan da kuma tarin yaransu. Saima hayaniyarsu da sukaci gaba dayi suda yaransu wanda ba'a raba gidanmu dashi.
Da gudu Affan daya fito daga toilet yayo wurinmu cikin murna sosae yana fadin. ”Oyoyo aunty meerah dinmu ta dawo bayan mamanmu tace bazata sake dawowa ba wai”
Wani irin fisgar hannun affan maman Saude tayi cikin fushi ta shiga sirfa masa masifa. "Ance ba zata dawo ba din dan ubanka, affan zanci ubanka a gidan nan wllh shege marar zuciya ban hanaka kula wannan yadin magen ba @ gidan nan”
Kuka yake yana ta kokarin kwatar kanshi daga mahaifiyarsa, wata uwar tsawa ta daka mishi tana jan hannunsa kiiiiiii suka shige daki.
Ahankali ta dauke kwallar da suka tarum mata, tana jin wani Abu da batasan ko miye shiba yana tokare kirjinta, tana bakin cikin irin wadan nan abubuwan da suke faruwa a rayuwar gidansu.
Daki suka shige duk kuwa yadda take jin kukan affan yana ta kuka yana fadin wllh saiya rataye kansa, tanajin sanda maman saude tana fadin ya rataye mana idan bashi da hankali. Da haka suka shige dakinsu kwanciya tayi ita kuma Anne zama tayi don ta huta.
***Bayan an shiga sallar la'asar affan dake labe yana ta faman sauke ajiyar zuciya, satab satab ya leko saida ya tabbar babu kowa a tsakar gidan kana ya fito tsakar gidan. Gyalen mamansa dake rataye a kan window ya dauka da gudu yabar dakin yana yin gaban bishiyar setline din tsakar gidan.
Gyalen ya cilla ya hada ya masa daurin azar gagi, turmi ya taka ya zira kansa cikin daurin azargagen da yayi tare da shure turmin da kafarsa. Ji kake zug kansa ya zuge.
Bacci tasha sosae Wanda har batasan iyakar shi ba, ihun maman saude shine ya farka da ita sama sama take jin ihun tana fadin.
”Jama'a Ku temake ni affan ya rataye kansa, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Wayyo affan, wayyo jama'a, yanxu dama Ashe da gaske kake rataye kan naka zakayi affan?”
Da wani mugun gudun bala'i na fito har inacin tun tube, kaff matan gidanmu suna tsaitsaye an rasa Wanda zai sinto affan. Hakan yasa na janwo drow din da muke tara ruwa na taka zan sinto shi.
Drow din da nake kai naji an ture da karfin masifa, ji kake *tummm*
na fado daga kan drow din.
”Shegiya mayya wllh kema saikin mutu tunda kece sanadiyyar kashe min da”
Sune kalamai na karshe da kunnawana suka jiyo min na tafi duniyar somewa......kan kace meee gidan harya cika da mutane ko nace samarin gidan, jikin baffa kuwa rawa kawai yake don kowa a gidan ya shaida irin girman shakuwar dake tsakanin baffa da kuma affan din, Yaya Ibrahim ne ya sinto affan kan yay jale alamar a karye yake,wani irin kuka maman saude ta kece dashi ta fadi kasa tana mututuwa tana tunballo ta ratayo wuyan affan din tana kuka, Anne kuwa wani irin rumtse ido tayi tana jin wani irin dacin da bata San na miye ba na taso mata.
”Innalillah wa'inna ilaihir raji'un²”
Ta fada tana jin wani zafaffen hawaye na karyo mata.
Yaya Auwal ne shida Sapwan sukayi saurin Ciro affan daga jikin maman suna fita dashi don kaishi hospital.
”Ibrahim miye haka kuma zakuy? Kulli nafsin za'ikatul mauti! Dukkan mai rai mamacine saida muce ubangiji ya jikan Nasiru (Affan) ya kuma Sa mace tane”
Cewar baffa da baki daya jikinsa yayi sanyi, su kansu manyan hawaye zubar musu yake domin affan irin yaran nan ne masu azabar shiga rai, dadi da kari akwai shi da nutsuwa,hankali, biyayya Sam shi babu ruwansa da yadda tsarin gidan nasu yake duk da kasan cewar yaro me dan bazai zarce irin shekara biyar din nan ba xuwa shida.
Kan kace me makwafta sun cika gida harma da sauran yayan gidan aurarru duk sun iso, duk wannan fadi tashin da ake babu wanda ya sake bi takan meerah. Tana cen palon baffa da yasa Ibrahim ya maida ta cennnñ, bayan yayyafin ruwa da yasa aka mata ta farka amma alhamdulillah kuma ta sami bacci.

Cikin kankanin aka suturta gawar affan aka meka shi xuwa gidansa na gaskiya. Sisae ya sami jama'a kasan cewar Sa yaro na kowa, har a manyan masallatu da gidan radio aka sheda rasuwar.
Sai bayan sallar isha'i wajajen goman dare kana malan Abdullahi ya shigo, har xuwa lokacin kuwa meerah na palon Baffan, da kansa ya tada ta ruwan tea din da aka kawo masa ya hada mata da kansa, tare da bread saida ta wanko bakinta da fuskarta kana ta zauna tana tonkoshe kafafunta a gaban baffan.
Haka badan taso ba ta shiga tura ruwan zafin zuwa cikinta amma sammm taki cin bread din, xuwa lokacin idanunta sun fada sosae sunyi zuru² duk da cewar dama tana a halin jinya be. Maman Auwal CE ta shigo dakin da sallama kasan cewar itane da girki yau, wani mugun kallo ta wullawa meerah a fakaice tare da Jan kwafa.
Ita kuwa a tsanake ta mike tana ma maman Auwal sannu, ciki² ta amsa ta ita kuwa ta kwashi tarkacen tana yin woje bayan ta sake baffanta gaisuwa a karo na biyu.

★★★
*Armstrong*

Gurfane yake gaban manyan police din dake kewaye da dakin, jikinsa duk jini ya jigata iyaka jigatuwa.
Wata uwar tsawa dpo ya kwatsa mushi yana furta. "Tell me know zaka fada mana inda sauran suke ko sai yanke ma yatsun hannuwa?”
Dago kansa yayi Wanda yake sharkaf da zufa, kafin a galabaice ya dago ya dubesu tare da sakin murmushin daya kusan haukata zukatan police din.
“Wai kuna son na baku batu akan Boss ne¿”
Ya fada tare dabin su da jajayen idonsa, da badan boss yaki bashi dama ba da tuni ba wannan batun ake ba wani ake.
”who is ur boss master' who is he?”
Dcp ya fada cikin zafi yana cakumo wuyar rigar Armstrong.
*”AK”*
Ya furta cikin wani jahilin sautin daya sanya dcp sakinsa yana yin baya a mugun tsorace, jikinsa na wani irin mazari dpo kuwa wani irin yanka yaji zuciyarsa tayi. A kuma daidai lokacin manyan soldiers suka danno Kansu cikin babban dakin horaswas.
A zafafe Ajmaal ya wani irin cakumi wuyar rigar Armstrong hada shi yayi da jikin gini yana furta.
”INA YAKE?”
Hhhhhhhhhhhhhh sautin dariyar Armstrong ya karade dakin kafin cikin wani sauti ya shiga furta.
”Ganinsa kawai kansa kafafu su dau mazari, zuciya ta fara bugawa tamkar kazar da tagaji ta kwanta a cikin mai sai gata a kafe. Kunsan waye AK kuwa?
_Shine mugun da yake lalata mugyayen kasa!!!, shine me tsince kazantar cikin al'umma! Kuma shedanin shedanun cikin al'umma, a shirye nake da in bada rayuwata ga *AK* wanda nake kallonsa a matsayin uwa uba Yar uwa Dan uwa”
Dogo kansa yayi tare da bin Ajmaal da wani dan iskan kallo hannunsa yakai gefen bakinsa dake disar jini ya goge, duk kuwa da cewar hannunsa na cikin handcuffs ne.
Cikin dangerous voice nashi ya furta.
”kodan sabo da mutuwa ta tai ma'ana shekeni!!!, zoka harbeni. Ko zaka rage radadin dake sukar zuciyarka domin shi kasan *BA YA MUTUWA*”
Wani irin damkar wuyar rigar Armstrong Ajmaal yayi tare da bashi wani mugun naushi a gefen fuskarsa, saida ya dan dakata kafin still ya sake damkar wuyar rigar nashi yana sake furta.
”Idan har baka fada min inda yake ba na rantse sena sheke ka kafin nabi ta kansa shima na karkkarya kasusuwansa a gaban idonka”
Wani shegen dariyar bazatane ya kwacema Armstrong.
”AK is too hard for me to break, diamond ne shi kafin a narka shi sai an yi amfani da ice da fire I have used the ice. Ta ya kake tunanin karamar kwakwalwarka ya gaya maka daidai? Ko dai ka manta *SARKI NE SHI A DAWA?*"
A matukar fusace Ajmaal ya daga bindigarsa ya dana akan Armstrong yana shirin d'ana kunamar binfigar nashi.
”Ajmaal stop!!!”
Mr president da shigowarsa kenan ya furta cikin rawar jiki, da dacin murya amma ina tuni Ajmaal yaaaaaaa........

★★★

AK POV
Fitowarsa cikin takun nan nasa na isa da izza tamkar babu wani abinda ke damunsa ya saka uban guards din dake harabar gidan nutsuwa. Cikin Tsananin kwarjininsa da gizagon da kullum ke sanya zuciyar magauta nutsuwa, lullebe a akan kyakykyawar fuskar dake nan tamkar hadarin daya kunshi ruwa yaki ya fashe.
Sanye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login