Showing 51001 words to 54000 words out of 69951 words
irin kwarjini mai tarin yawa kwarjinin da a kullum yake lullube da fushi da kuma fusata. Sai nose mark daya sanya wanda kai baka isa gane waye shi ba.
Wani irin daddaɗan ƙamshine ke tashi a jikinsa irin me ɗaukar hankalin nan. Ko yaya ka qara taqi kaɗan kusa dashi kana iya shaqar daddaɗan ƙamshin turarensa da ba lallai ka gane ainihin wanne irin turare bane,saidai yakan sanya nutsuwa ga duk wanda ya shaƙeshi ya kuma ƙara kwarjini ga ma'abocin ƙamshin.
Kyawawan fararen hannuwansa zube cikin aljihun tsadaddun riga da wandon dake sanye a jikinsa,Sake gyara zaman bindugunsu security'n sa suka sake yi a tsare cikin shirin kota kwanar karbar umarni daga gareshi. Wata zazzafar Iska ya ɗan furzar kafin ya taka zuwa gaba. Arms tare da wasu mutum biyu daga ciki sukayi gaba kamar masu masa jagora,sauran kuma suna biye dashi. Cikin takun cikakken gwarzon namiji yake takunsa har zuwa cikin ƙayataccen Royal parloun da yake ƙawace da wasu irin Italian Wikipedia chair. Daga nan duka bodygourd nashi suka tsaya a parloun shida arms ne kaɗai suka nufi entrance door ɗin da sai sadasu da duka sassan gidan.
A gaggauce suka wuce zuwa lipter da zai sadasu da dakin da zai sauka,cikin mintunan da ba zasu wuce 5 mint ba ya tsaya a parlou 3. Saida yayi scanning card a bakin qofar tayi qaramar qara alamun samun izinin shiga.
Palace tenpor room ɗin suka nufa kai tsaye Wanda ko ina na gidan Gellary odyssey ke walainiya tako ta ina.
Saida ya buɗe deep freeze ɗin dake makale da dab shiga asalin living room ɗin ya ɗauka kwallar wine ɗin sa. Nan ma Saida Gellary odyssey dpy ɗin yayi on locking up nashi kana ya suka shige Mahaukacin katon parloun da ma'adanar cctv footage ɗinsa yake. Wani irin matakan tsaron na'urori ne kawai ke magana a wurin.
Tanbuwal da tun da aka jeho hi aka garkamesa jiya be kuma sake jin motsi ba sai yanzu. Da wani irin sauri ya sanya hannunsa yana kare Mahaukacin hasken daya kusan ɗauke ganinsa, jikinsa rawa ya fara na tsabar azabar yunwar dake kwakular cikin sa.
Zaune yakai kan Chiar silinder caution ɗin dake facing da wannan mutumin. Ƙafarsa ya sanya tare da mirza ƙafar tanbuwal babu shiri ya saki wata ƙarar azaba cikin tsananin wahala ya furta.
"Pls kuɗin su waye ku? Me kuke nema daga gareni?, Kuɗi!?, Suna?, Mulki?, Ko kuwa ƙarfin Iko kuke da buƙata?"
Ya faɗa cikin muryan jigatuwa da wahala.
Shiru babu alamun amsa hakan ya sanya shi sake faɗin "please let me know waye kai?"
”Makwamishin guba! Mashekin rayuka matunzirin ruhi. Sannan kuma mai kare mabuƙata! Ni dabaibaiyi ne me harɗe duk kan wani azzalumi na kaishi har kasa ÆK”
Ya furta a fusace tare da kwance ɗaurin da akama tanbuwal ɗin. Wani irin mugun shock ne ya ziyarci ƙwaƙwalwar tanbuwal, AK AK AK haka sunan shi ya shiga masa amsa kuwa a tsakar kansa. Cikin Wata iriyar jarumtaka tanbuwal ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya kafin ya dakata. Cikin Wata irin dangerous voice ya furta.
"Ai baka cika cikakken NAMIJI ba tunda Saida ka hada hannu da mace kafin kawoni i zuwa gare ka,karkaga ina karkashin ikon ka ka zata zaka iya min wani abu.
duk da cewar zaki shine sarki a dokar daji amma karka manta damisa itace gwana wajen iya farauta"
Wani irin lalataccen kallo Æk ya wurgama tanbuwal tare da Crossing ƙafafunsa yana kora kwalbar wine ɗinsa. Cikin wani irin hosky voice ya ce.
"Ko wanne mafarauci garzone har sai sanda ya fuskanci ingarman zaki.
Wannan haushin ƙaramin kuykuyon kare kake! Ka sani haushin ɗan ƙaramin kuykuyon kare kuwa ba gurnanin damisa bace! Ammah Ka jira hasalin yadda gurnanin ta yake. Ka sani ABDOUL-MALEEK ba kamar sauran sharar daka saba takewa bane, wannan Asalin Cikakken fusataccen damisar daya fito domin farauta ne a gabanka"
Ya fadi tare da rotsa kwalbar wine ɗinsa kwalbar tai ratsatsa ta baje a wurin. Zuwa loƙacin babu komi a tare da Ak sai asalin fusatarsa kawai ake iya hangowa.
Armstrong dake tsaye ne ya tunkari inda tanbuwar ɗin yake tare da soka masa allura a gefen yuwansa Yana bin bayan Ak ɗin shima. Bai tarar dashi a main sequence parloun gidan ba, wayarsa ya fidda tare da tambayar su Boss ya fito ne?, Tabbacin be fito ba suka bashi hakan ya sanya shi sauke wayar tare da bin ko wanne entrance door da kallo.
Wani irin zafaffen numfashi ya fesar tare da tsananin tausayin uban gidan nasa. Kabar ƙasar ka kabar gidanku kabar danginka kazo ƙasar daba taka ba kana musu aiki da dukkanin zuciyarka da rai da ruhinka. Ko dan wannan abin ma bai ci ace gurɓatattun cikin ƙasar Nigeria'n sun sauya ba da kunya ma ace an rasa gwarzo zakwakurin da yake tsaye akan ƙasar sa. Kodan sun riga sun sanya tsoro ne a zukatan al'ummar OHO? Duk wani namijin da yake jin kansa da zafin kansa ta kawo akan ƙasar to kuwa Insha Allah sai an san yadda akayi aka kawar da wannan mutumin. Shin me masu kuɗin duniya da masu mulkarta suke son zama ne???. A kullum shine tambayar dake bisne cikin zuciyar Armstrong. Shi kikakken ɗan Nijeriya ne amma baya alfari da hakan saboda gurɓatattun cikin ta da ɓata garinta suka kewaye ko ina na cikin ta. Kasar data zamo koma baya ko lissafinta ba'ayi a cikin duniya.
A cikin gidanku ma babu adalci bare akai ga wani wuri me nisa, a gaban idonsa dangin mahaifinsa da suke ƴan uba suka sanya wuƙa suka yanke makogwaron mahaifinsa sa!, Akan dukiyar da guminsa ne shima ya bashi ba sata yayba ba kuma haram yabi wajen tara taba. To taya muke tunanin duniyar mu zata gyaru a cikin gidajenmu babu adalci? Sai tsananin azaba yakai tsanani mu dinga ƙiran Allah gyara. Tofa baya gyara ba dole muma sai mun gyaro ɓarnar dake cikin gidajenmu. Bawai Ƙasarce a ɓace ba mu al'ummar cikin ta mune a ɓacen mune ɓatattun dole kuma dama gyara ta cikin gidajenmu yake farawa. Idan muka gyara halayenmu sai Allah ya gyaramu Amma muma muna da kaso mafi girma akan tarin abubuwan dake faruwa da kasarmu uwarmu......
Wani irin zafaffen numfashi ya furzar tuno yadda ƙanwarsa ƴar shekaru uku a loƙacin take kuka tana dukan ƙirjinsa tana ƙiran mommy na daddy na. Gaba ɗaya jininsu ya ɓata jikinta. Wasu hawaye Masu zafin gaske ne suka zuba masa a lokacin daya tuna sadda mahaifinsa ke faɗin.
"Ka gudu! Ka gudu kai da ƙanwarka ka tabbatar kun rayu ABDOUL-MAJEED, ka reni zuciyarta akan gaskiya da gaskiya ka tabbatar ka kulamin da RIYYERNERTOU, ka zama gatan ta,haskenta, ita kaɗai ce danginka ƴar uwa ɗan uwa ku tafi ka tafi wata duniyar kaje zaka rayu tare da tsarkakkiyar zuciyar da zata reni taku zuciyar da irin tashi zuciyar da ɗabi'arsa.kamin alƙawarin zaka zamo mutum na farko da ƙasar sa zatayi alfahari da shi...
Wadannan sune kalaina na karshe da suka tsaya masa cakkkk acikin tsakiyar ƙirjinsa. Mahaifiyarsu kuwa ta mutu ne ba tare data iya furta masa komi ba sai idonta dake kan Riyya. "Ka gudu karsu dawo su sameku domin a zatonsu kuna makaranta ne, yanzu haka sun tafi ne da niyar su dauko ku kuma su kashe ku. Wannan kuma shine babban zunubi mafi girma da zasu aikata idan har suka taɓa lafiyar koda ɗaya daga cikin kun!........... Be ƙarasa maganar da yake shirin faɗar ma rai yayi halinsa haka ya ɗauki RIYYERNERTOU akan shoulder nashi ya gudu da ita. Sun sha matuƙar walahar gaske har tsawon shekaru uku a lokacin yana shekara na goma sha biyar ita kuma riyya tana da shekaru bakwai. A haka wani baƙin dare ya riski rayuwarsu shida ƙanwarsa.
Daga nan babin sabuwar rayuwarsu ta fara shida ƙanwarsa ta hanyar keta mata mutuncinta ta hanyar mata fyaiɗe Anyi Raping ɗin.
Masu iya magana sunce ko wacce ƙaddara tana da nara madubin,sudai nasu madubin Ak ne domin a lokacin da yake tsaka me wuya cikin mugun yanayin makauniyar ƙaddarar data riski ƙanwarsa. A daidai lokacin Allah ya kawo masa Ak shine ya shige masa gaba akan komi! Shine yake amsa sunan UWA UBA a gare su shida ƙanwarsa har kwanan gobe da safe. Ya basu tarbiyya ya inganta rayuwar da tarin ilimin addini da na boko. Ya shige musu gaba wajen ganin sun zama wani abu A koda yaushe Har abada abadan abada ABDOUL-MALEEK KUWAIT shine kashin bayansu.
Hawayen tausayin gwagwarmayar rayuwarsu da suka fuskanta ya share ya nufi entrance door ɗin da yake da tabbacin anan Ak ɗin yake. Shima ɗaya daga cikin room din ya fada yana kokarin ganin ya kawar da tunanin dake kokarin zeroying maid nashi.
Duk kokarinsa nason ganin ya kawar da tunanin dake neman addabarsa abin yaci tura, kansa ya jingina da jikin kofar tare da lumshe Idonsa. Numfashi yake fitarwa Ahankali yayinda yake furta kalmar. " Innalillahi wa'inna ilair raji'un,² Ya hayyu ya qayyum" daga cikin zuciyarsa domin kuwa tsabbb komai din da yake gudun ya faru ya rigada ya farun. A take kwakwalwar kansa ta nemi juyewa amma ambaton sunan Allah da yake hakan ya sanya. Ahankali nutsuwa ke saukar masa acikin zuciyarsa yayinda yaji tarin damuwarsa na gushewa.sosea yaji sanyi da cikakkiyar nutsuwa da salama acikin zuciyarsa.
Gaban fridge bottle water ya nufa kai tsaye tare da ɗauko bottle water ya ɓalle murfin, ya kafa bakinsa Saida ya tabbatar ya shanye ruwan dake ciki tsabbb kana yayi wurgi da gorar. Wata iriyar ajiyar zuciya yake saukewa tare da sanya hannu ya ya dafe kansa. duk yanda zuciyarshi taso sanya shi dogon nazari yaki aminta da hakan haka kuma yaki bama brain nashi daman yin tunani kamar yanda ya saba a wasu lokutan.
Ya jima a tsayen da yake kafin ya nufi bathroom, ya sakarma kansa ruwa Ya ɗebi mintoci kafin ya fito jikinsa na faman ɗigar da ruwa, mini towel ɗin dake rike a dayan hannunsa na aikin tsanewa.
Wani farin trouser ya zira da t-shirt ita ma farar directly ƙroom din daya tabbatar da ak din na ciki ya nufa, tare da danna door belt din bedroom din yana jiran a bashi umarnin shiga.
★★ÆK★★
Yana shiga bedroom din kayan jikinsa kadai ya cire tare da daura fari tass din towel wanda ya ma wani irin lago lagon dauri kafun ya wuce bathroom. Kai tsaye cikin bathtube ya shige wanda ya hada ruwa me dumi da fresh out din wankan daya zuba. Aqalla sai da ya shafe mintuna masu dama kafin ya fito,tamkar wanda yake sauya fatar jikinsa. Fatar nan sai uban daukar ido da walainiya take ta kota Ina Ak namiji ne tsayayye da babu abinda yake masa shamaki da cikar zatinsa.
Lafiyayyar fatarsa dake daukan idonsa ya kalla ganin wato shi Hutu da jika cikin arziki da nutsuwa Wani abu ne na daban da idan Allah yayika cikinsu basa taba boyuwa ko yayana.
kauda idanunsa da suka dan canza launi sakamakon shigar ruwa cikinsu ya mayar ga madubi yana qoqarin tsane sumarsa data jiqe da ruwa,abu guda daya tak da zai fara gaya maka AK din ba asalin bahaushe bane, kodan yadda farar fatar jikinsa take da kuma tulin gashin kansa da yake amsar kudade masu gwabi wajen gyaranta.
Tamkar babu wanda yake jiransa haka ya kammala shirinsa a nutse cikin wasu Ash din riga da wando Armless marasa kama jiki.wasu tausassan flip flops ya zura dogayen qafafunsa wadanda kamar basa taka qasa dan tsabar laushi da kuma taushinsu. kana ya kwashi wayoyinsa tare da daukar rimot ya danna kofar bedroom din ya bude. Waya ya fito yana yi cikin yanayin sakewa kadan.
Gaidasa Arms yayi tare da fada masa an shirya dining.
Bai ajiye wayar ba ya dan dago ya dan kalle shi kadan tare da amsa shi da kai, bai kuma janye wayan ba har zuwa lokacin.
Cikin ishashshen takunsa ya nufi dining din har kuma lokacin yana manne da woyarsa, Ba wasu abinci masu nauyi bane junk food ne kasancewar babu restuarent a kusa ga kuma a wannan gidan babu kuku's. Idan ka dauke sikuriti babu kowa dake rayuwa a gidan. Wannan kamar gidan horo yake.
A nutse ya jagali food din bame yawa ba yaci ya tashi har lokacin kuma woyarsa yake hankalinsa kwance. Kai tsaye coumpaund na gidan ya nufa da jikin railer ya jingina yayi crossing kafafunsa. Rigar nan da bata kama shima iska sai dade kwantar da ita a jikinsa take kan babu yar gadon fcarp.
★★★ ★★★
A dab plat din me napep ya sauke ta kamar kullum yauma sanye take cikin dogon shijjab har kasa, yau ba nikap ta sanya ba nose mark kadai ta sanya sai idonta data rufe da bakin glass. Rolex din skmee 2/1 din dake daure a hannunta ta sake dubawa da kyau don tabbar da nan din ne inda na'urar biyayar ta kawo ta.
Tun daga kan uban tight security'n dake zagaye da get din ta tsorata. Amma kasancewarta mutum bame nuna sarewarta a fili bane ya sanya ta nufar katon get din. Cikin rashin tsoro ta tunkari get din baki daya kawunansu a sama yake hakan ya sanya ta yin sadab sadab taje a sukwane zata shige suka farga da ita. Ko kafin su dago kuwa wata farar kwalbar dake rike a hannunta ta musu fesar turare da ita ji kake "fessssss" yuf tayi ta fada gidan.
Sadalaf, satalaf haka ta shiga kutsa kanta cikin gidan dayafi kama dana barayine ma zatace kome, gadai yadda hantar cikinta take kadawa a zahiri amma kuma ta danne tsoronta haka ma a yanayinta baka isa fuskantar a wanne yanayi take a ciki ba.
Kasancewar duhun magrib na dab da kawo karasowane ya sanya ta ringa bin jikin manyan flower's din coumpound na gidan. A haka har takai ga jikin katuwar railer din dake coumpound na wurin,Kamshin da bazata taba mancewa dashi bane taji sun kawoma kofofin hancinta ziyara. Kanta ta dago daga kokarin tafiyar da take shirin ci gaba dayi,Ido biyu sukai daidai Yana kammala wayar shi. Wani irin mugun tsoron kai tsayene yanzu kammm taji ya ziyarceta, Hannuwanta da suka shiga mazarine ya sanya ta dire Robar dake hannunta ahankali gudun kada ya subuce mata, wani shegen kallo ya jefeta dashi a kuma daidai ta sake dago kanta aikuwa yaja kyawawan fararen idonta masu kama dana mashaya a cikin nasa ta hanyar sarketa da nashi catizeen eyes dinsa.
Yau kam ta gama tabbatarma kanta tata kuma ta kare tunda ta kawo kanta da kanta gidan wannan me satar mutanen.
Muryarta na yankewan tsoro da mamakinsa cikin qaramin sautin ta furta "pah pa pls don Allah........
Wani shegen kallon daya jefa mata ne ya sanyata kimtse bakinta tayi shiru. Gashi kuma daf da juna suke sosai Kai tsaye hancinta babu Abinda yake shakar mata bayan mayen kamshinsa.
Wani numfashi taja ahankali tareda dauke idanuwanta daga kallansa gabaki daya saboda tsoransa da taji yana nema Kamata.
Jikinta ne ya fara mazari na tsatsanin tsoronsa ganin yana sake matsota, ja baya ta shiga yana sake binta yana ci gaba da jefa mata wannan dan iskan kallon nasa.
Kankame jikinta tayi wuri guda tare da toshe kunnuwanta ta fasa wata uwar kururuwar data sanya duka mutanen dake cikin gidan yowa wurin a guje.
Wani irin fusgarta yayi a fusace yana yin wata boyayyar hanya da ita. A daidai lokacin kuma harsu arms dake cikin gida sun kawo wurin, wulgawarsa kawai suka kalla ba tare da sun lura da Meerah ba.
Suna kaiwa wani wuri ya danna wata na'ura me kamar botton kai tsaye sai gasu a cikin wani fitinannen hadadde tsararren cumputer room. Gaba daya shiga dakin na'ura ta dauki shelar shigowarsa dakin tare da ambatar cikakken sunan meerah kai tsaye. Hakan ne ya sanyata kwatar hannunta daga kyakykyawan rikon daya mata tana bude idonta da niyar mata masa wasu maganganu masu irin myankar zuciyar nan. Ai kuwa bata sauka idonta a ko ina ba sai kan grey 11/in/21 rose glasses out din da kai tsaye hoton mutum yake irin rarrabewa nan, idonta bai sauka akan ko ina ba saikan hotonta daya rarrabe kusa ashirin da wani abin. Sai nashi daya juya baya iyaka lafiyayyar farar fatar jikinsa kawai take iya gani!, Ai bata san sanda ta tafi da wani irin mugun gudu ta fada jikinsa ba tare da kankamesa tana sakin wata gigitacciyar karar daya sanya baki daya nu'urorin dakin daukar karar itama. Wani irin kulle idanunsa yayi tare da sakar mata wata razananniyar tsawar da kai tsaye ya idasa tafiya da numfashinta, domin dama tana dab da somewar na a lokacinma numfashinta ma seezing yake sai tsawar ta idasa tafiya dashi kai tsaye.
"Ochhhhhh!"
Ya furta yana ma rasa yadda zaiyi da ita saiya saketa daga tsayen da yake, muguwar buguwan da kanta yayi ne ya sanya numfashinta dawowa. Ahankali ta shiga kokarin wara idanuwanta, Dashi dake zaune kan wata kafurar luzury caution