Showing 102001 words to 105000 words out of 299804 words
bokina Hayatuddeen na kwana a can".
A hankali yasa hannunshin ya kamo kunnenshi tare da matseshi da yatsu sa biyu.
Da ƙarfi Jamil ya saki ƙara tare da cewa.
"Wayyo Hamma Jabeer bazan sakeba, na tuba".
Bai sakeba sai ma kauda kanshi da yayi yana kallon Umaymah cikin rauni yace.
"Kinji ba, shi kullum yana Club music sai kace ɗan ma kaɗa ko maroƙa, yaje ya kwana cikin yan iska azo ayi ta musu video ana yaɗawa duniya, ana liƙa sunana a ƙarshen sunayensu a social media kamar nine uban daya haifesu.
Haka kenan zanyi ta fuskar ƙalubale ina rasa yadda zan karesu ko in zagesu."
Ya ƙarishe mgnar rai a ɓace.
Ita kuwa Umaymah faɗa ta fara yiwa Jamil.
Shi kuwa gaban Jalal ya tsaya tare da kafeshi da ido.
Cikin tura baki Jalal ya fara bayani ba tare da an tambayeshi ba yace.
"Shiya shiga sabgata Ni kuma na dakeshi".
Cikin nuna ɓacin rai yace.
"Da yake kaine sarkin duka, ko kunyan Baba Kamal bakaji ba, ka kama Salis da duka kawai dan ka wuce da MP kana danna waƙe-waƙe da suɓale wonɗo shine tsokanar?".
Cikin yin ƙasa da kai yace.
"To ai zaginka yayi wai ilimi ka na banza tunda gamu a lalace bakayi mana wa'azi mun shiryuba, shiyasa Ni kuma na mishi aikin wanda ba shiryayyu ba".
Kwaffa yayi tare da cewa.
"Zagi kuma na nawa? Ba kune ke jazamin zaginba, kada ka yarda in sake jin ka taɓa shi Uhummm!".
Ya ƙarishe mgnar da kwaffa.
A hankali Jalal yace.
"Kayi haƙuri in sha Allah bazan sakeba".
Nan duk suka nufo cikin falon.
Suna isowa Hajia Mama na shigowa Batool na biye da ita a gefe.
Jafar kuwa da sauri ya koma bayan Sheykh tare da riƙe hannunshi ya fara ja alamun su tafi.
Shi kuwa Sheykh ƙara tsuke fuskarsa yayi ganin Batool cikin sauri ya gaida Mama, ta amsa fuska a sake tare da sanya masa al'barka.
Kana ya nufi hanyar fita, da sauri Jafar yabi bayanshi.
Umaymah kuwa da Ummi da Juwairiyya da Batool nan suka zauna suna ɗan hirarsu.
Jalal kuwa da Jamil a tare suka fita, shi kuwa Haroon falon Jabeer ya koma.
Yana shiga ya kira Jannart bayan sun gaisa take tambayarshi yaushe zai je masarautarsu nan yake ce mata.
Yana nan tafe a satin nan.
Shi kuwa Sheykh Jabeer yana fita kai tsaye Valli Hospital ya nufa.
Asibitinshi mai zaman kanshi.
Asibitin da duk nahiyar Ɓadamaya babu kamarshi.
Asibitin da in kana cikinsa zakayi zaton a ƙasashen turawa kake.
Haka lamarin yaci gaba da tafiya.
Babu mai yiwa Sheykh Jabeer batun Aysha.
Itama Aysha gani take kamar ziyara tazo ba aureba.
Tunda ita dai da idonta bata taɓa ganin mijinba, sai dai taji sunanshi.
Sosai ta shaƙu da Hibba da Umaymah, hakama Gimbiya Aminatu da Ummi.
Lokuta da dama takan shiga Bathroom tai ta kuka sabida begen ƴan uwanta.
Yau kwananta uku cur a gidan.
Idonta ma baiga ranaba.
Umaymah kuwa a sashin Jabeer yana fita.
Wata tirela ta iso har bakin Side ɗin shi.
Nan aka fara sauƙo da kayayyakin ɗaki na amare.
Ana shigarwa ciki. Kana masu aiki na ɗaure komai suna kimtsashi.
Sai kusan la'asar suka gama komai kafin.
Suka tafi kana su Umaymah suka taho.
Suna shiga asalin babban falon, Aunty Juwairiyya da Hibba suka haɗa baki wurin cewa.
"Wow masha Allah, Kai Umaymah ƙara so da sauri kiga falon nan yadda ya zama fadar masarauta".
Da sauri Umaymah da Ummi suka ƙara so.
Masha Allah! Masha Allah!! Masha Allah!!! Shine abinda kawai Umaymah keta mai-mai tawa, sabida kyau da tsaruwan falon yayi masifar kyau.
Kasan cewar falon irin ƙaton nanne mai faɗi da tsawo.
Wasu irin kujeru ne Daimond set masu masifar kyau da tsada, a shirya a cikin tamfatsen falon.masu Golding color mai ɗan karen sheƙi sai surkin Brown color mai sheƙin gaske da ratsin ruwan madara..
Kana haka ma kalan labuyen falon masu tsawo da faɗi da taushin gaske.sai wani table na glass mai Golding color da aka ajiye a tsakiyar falon bisa wani tattausan carpet mai azabar kyau.
Sai wani babban Tv dake liƙe a jikin bongon, kana gefen dama kuwa wani babban majigine manne wanda yake baiyana rubutun Kur'ani reras daki daki.
Can gefen kuwa steps ɗin hawa Dinning area ne,
wanda aka canza Dinning table and chairs ɗin,
Aka zuba wasu masu masifar kyau da tsadan gaske.
Ba'a wani cika falon da tarkace ba, amman yayi matuƙar kyau.
Tafiya kaɗan zakayi ta gefen hakun zaka ratsa cikin wani madaidaicin falo.
Yayinda na Jabeer yake hannun dama.
falon ɗakin da Umaymah ke tsauƙa in tazo kenan.
2 bedroom ne wannan falon yake dashi ko wanne da bathroom a ciki.
Kana sai Dinning area matsakaici daga nan gefen Dinning area kuma akwai ɗan ƙaramin corridor wanda zai sadaka da kitchen da store.
wasu irin datsa-datsan kujeru masu masifar kyau da ɗaukar hankali aka kimtsa a falon wanda komai na ciki.
Peach and white coffee ne mai ɗan karen kyau.
Hakama Dinning table and chairs ɗin.
Still labulayen ma hakane.
Sai kuma cikin bedroom ɗin wanda duk girmansu ɗaya, haka yasa aka shirya wasu tagwayen gadaje masu masifar kyau suma Golding color ne mai sheƙi da ɗaukar ido.
Saɓanin side ɗin Jabeer komai Sky blue and white ne, wanda hakan yasa kana shiga sashinsa sai kayi zaton a sararin samaniya kake rayuwa.
Komai yayi kyau.
Especially kitchen ɗin dake matsakaicin falon.
Domin wancan kitchen ɗin dake babban falon ba'a taɓa shi ba, hakama Side ɗin Sheykh.
Sai kuma sama wanda shi a rufe yakema, sam babu kowa a ciki.
Sosai fa su Umaymah suka yaba da kyan shirin da akayiwa wurin.
Nan suka zauna a falon.
Umaymah ce ta kalli Jakadiya cikin sauƙe numfashin tace.
"Alhamdulillah, gobe kuma zakiyi musu jagora shida matarshi su zaga ta gaida ahlin masarautar Joɗa, ta gansu su ganta su san juna, gudun kada a haɗu a wani wurin ba'a san junaba".
Wani gwauron numfashin Ummi ta sauke tare da cewa.
"A nan gizo ke tsakar ko ta ya zamu samu, Sheykh yayi wannan al'adar yadda ya dace ake kuma yinta, kinsanshi mutunne mai kunya, koda yana son abunma bare ba wani son abun yakeyi ba".
Cikin yarda da kai Umaymah tace.
"Kada ki damu yana ɗaya daga cikin dalilin da yasani, na zauna sai naga kamun ludeyin zaman nasu."
Haka dai suketa tattaunawa,
Suna nan zaune Gimbiya Saudatu ta shigo tare da hadimanta, kana da Laminu da Baba Basiru da Baba Nasiru.
Cikin isa da ƙasaita ta nufi kujerar da duk canjin da akayiwa falon ba'a canzashi ba sabida kujerace ta masarautar Jalaluddin, cikin isa take taku yayinda ta bawa ƙofar shiga baya.
Cikin gatsali ta kalli Umaymah data tsareta da ido. Kallon uku saura tayi mata kana tace.
"Duk mutun muna fuki abin tsorone. Amman munafurcin balaraben Mutun yafi na kowa muni da bada tsoro.
In banda salon munafurci ayi aure yau kwana uku a gaza fito da amarya a nunata ga mutanen masarauta, bare a fanshi idonta."
Ta ƙarishe mgnar tana kai mazaunanta bisa, Kujerar.
Sai kuma tayi maza ta miƙa, jin muryar Jabeer da yanzu ya shigo, ko mgnar ta, ta ƙarshe baijiba.
Cikin isa da ƙasaita da rashin tsoronta, da kuma tsare fuska alamun Ni bani da lokacin ki, kuma ni ba sa'an yinki bane ya nuna mata hanyar fita da yatsarshi tare da yamutsa fuska cike da ƙarfin zuciya ya kalleta ita da ƙannen Mahaifin nashi yace.
"Fice min daga gida, bacci na dawo zanyi so banda lokacin jin ihunku na kar...!
By
*GARKUWAR FULANI*
"Muhammad!". Ya kira babban sunanshi tare da jawo hannunshi, ya zaunar dashi bisa kujerar da ya tashi a kai.
Cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da tsoron abinda suke shirin aikatawa, ya kalli Mahaifin nashi, kana ya juyo ya kalli Lamiɗo da Galadima gefen damanshi ya juyo ya kalli Jadda cikin rauni ya kuma kalli mahaifin nashi tare dayin ƙasa da murya yace.
"Abba kada ka bari su ɗaura auren nan, dan Allah kace musu su bari, kada su ɗaura".
Ya ƙarishe mgnar cikin tashin hankali da ɓacin rai da tarin rauni a fuskarshi.
Cikin zuba mishi ido Abbanshi yace.
"Meyasa? Sabida me za'a bari!? Meyasa baka so!?."
Kanshi ya jujjuya tare da haɗe hannayenshi wuri ɗaya ya fuskanci mahaifin nashi cikin sanyi yace.
"Ni dai bana so. Abba dan Allah kada ka bari suyi.
Bana son garin nan bare mutanen cikinsa, kuma bawai haka banza naƙi auren nan ba, Abba inada matsala, Please Abba na tuba dan Allah kace su bari. In yaso a ɗaura da wani amman banda ni kam".
Lamiɗo ne ya kamo hannunshi cikin isa yace.
"Auren' nanfa, kamar ma an ɗaurashi an gama, domin babu wani abu ko wani mahaluƙin da ya isa ya hana wannan ɗaurin auren, gwarama ka kontar da hankalinka. Tunda ka iya jure bulalin aiko tabbas dole ka aureta, babu shakka dole sai ka aureta, bazai yiwu a dakeka a kantaba sannan ka barmusu itaba."
Cikin jin haushin wannan fitinenne tsohon ya kwace hannunshi daya riƙe tare da cewa.
"Haka kenan kullum zanyi ta wahala a bisa wasu dalilanka da bana addiniba, me ruwanka da dukan da akayi min, ba dai kai-kasa dole aka dakeni ba".
A hankali Galadima yace.
"Eh da kuma bakayi kukaba, baka guduba, yau kuma kasa yayi kuka ya gudu ai dole ka aure matar da a kanta aka haɗaku gasar, tunda mu dai ba sakarkaru bane, bare ace bamu san dokar gasar Shaɗi ba."
Wayyo Jabeer ji yakeyi tamkar ya mammake tsoffin nan dan tarin baƙin ciki. Rai a ɓace yace.
"Bakufa fini sanin kainaba, tunda nace muku bana son aure, bazan kuma yi aureba, to ku barni mana, rayuwata ce ko taku, ko dole ne duk wata matsalata da sirrin rayuwata sai kun sani! Nace muku bana son wannan garin na tsani garin bana son mutanen garin karankatab ɗinsu.
Bani babu su, in kuma kukayi gangancin cusa min wata muguwar yarsu, tabbas! lallai ilaihin! A kanta zan rama sauran bulali ashirin da wancan ƙaton gardin ya min, hamsin, ni a talatin ya gudu".
Kai Jadda ya girgiza tare da cewa.
"Ka rama mana kaida matarka, ka rama ka kuma jinyace ta".
Shiru sukayi sabida jin muryar Dr Aliyu da kuma Galadima da Arɗo Bani da Bappa suna tabbar wa juna lfyar yaransu, cikin Mamaki ya kalli Galadima dake cewa.
"Muma ɗanmu lfyarshi lau, Namiji ne".
Cikin sanyi Jabeer yace.
"Ji maƙaryacin tsoho, wai lafiyata lau, ko yaushe ya zama likita ya gwadani. Harda wani karkacewa yana zuba ƙarya ko farin gemunshi bai martaba-ba".
Jin Abbanshi ya daki gefen ƙafarshi ne yasashi yin shiru.
A nan a gabanshi a gaban mahaifinshi. A gaban dubban al'ummar fulani makiyaya daketa tsastsafo tako wani sashi na duniya, a kuma gaban Lamiɗo da tawagarsa hakama Jalaluddin da tawagarsa.
Aka ɗaura auren Muhammad Jabeer da Aysha. Bisa koyarwan addinin Musulunci.
Sosai su Jalal, Jamil, Hashim, Haroon, Sulaiman. Sukayi mamakin wannan aure na ba zata. Ba zato ba tsammani.
Bayan an gama dai-dai-ta komai an ɗaura auren ne, kuma.
Lamiɗo ya kalli Arɗo Bani, cikin girma da ƙasaita yace.
"Yanzu zai tafi da matarshi."
Cikin sanyi da al'hini Bappa yace.
"Allah rene yanzu kuma!?".
Galadima ne ya amshi zancen da cewa.
"Haƙƙun yanzu zamu tafi da ita!".
Arɗo Bani ne yayi murmushi mai cike da jin daɗin yace.
"To ba laifi ai, muje a fito muku da ita".
Shi kuwa Bappa ido ya zuba musu.
Dan shi a zatonshi ba yau zasu tafin mishi da Shatunsa ba.
Nan duk suka ɗunguzuma, suka shiga motocin. suka nufi ƙofar gidansu Shatu.
Ya Salmanu kuwa, tuni ya shiga cikin gidan su.
Ya shiga ɗakinshi yana ta kuka kamar yaro. Bai tsamci haka abin kan iya juyewa ba, Ba'ana ya rasa Shatu shima ya rasata.
Suna isa ƙofar gidansu, duk motocin suka tsaya.
A hankali Bappa da Arɗo Bani suka kutsa kansu cikin gidan.
A tsakar gidan suka samu.
Shatu na zaune dan dawowarta kenan, hannunta tasa ta tallabe haɓarta ta zubawa su Junainah ido, shigowarta gida kenan daga dawowarta.
Cikin Ɓadamaya su Binto suka shigo gidan a guje suna ce mata wai an ɗaura aurenta da ɗan sarkin da akayi gasar Shaɗi dashi.
Jin hakane yasata yin murmushi tare sauƙe dogon ajiyan zuciya na gajiyar tafiyar da tayi, ido ta lumshe tare da cewa.
"Auren kuma wasane, da zai zama an aura min wani wanda ba'a san halinshi ba, ko ƴar tsana ma ai ba'a aurar da ita a hakaba bare ni".
Ta faɗi mgnar cikin fargaban ganin yadda suketa rantse mata. Duk da bawai ta yarda da zancensu bane. Junainah kuwa dariya takeyi tare da ɗan tsalle-tsallenta tana cewa.
"Yeeh Auren Addana yazo, zanyi gayyan fati muyi gaɗa".
Cikin zuba musu ido, ta zauna gefen, Ummey dake ta Binta da ido, cikin sanyi tace.
"Ummey na dawo! Ya jikin naki!?."
Da sauri ta gyara zamanta tare da zubawa Ummey ido, cikin mamaki take kallonta ganin idanunta nata zubda hawaye ne, yasata cikin ruɗani da tashin hankali da fargabar abinda ke shirin faruwa da ita da rayuwarta.
A kiɗime tace.
"Ummey meya sameki? meya saki kuka? Jikin ne yake miki ciwo?."
Sam Ummey bata iya mgna ba, sai kukan da takeyi,
hakanne yasa zuciyar Shatu karaya, cikin rauni wasu hawaye masu ɗumi suka fara tsiyayo mata.
Hakan ya ƙara ingiza kukan Ummey hakama,
Junainah sai ta raɓa gefensu tayi, zurui a zatonta aure abun daɗi ne ba kukaba to gashi taga su kuma kuka sukeyi.
Sosai Shatu takeyin kuka mai tarin dalilai.
Suna isa Bappa yasa hannunshi ya kamo nata, cikin sanyi yace.
"Taso kizo".
Ido cike da hawaye ta mike tsaye bisa umarnin Bappa.
Shi kuwa Bappa cikin sanyi ya kalli Ummey da Junainah yace.
"Kada kuyi kuka, kuyi mata addu'o'in samun nasara a cikin wannan al'amari, muyi mata fatan aurenta ya zamo haske ne a rayuwarsa shi mijin da ahlinshin baki daya, fatanmu aurenta ya zamo ƙungiyar da zata jawo gskya cikin raminda aka binneta ya fito da ita kowa ya gani."
Shiru Ummey tayi sai hawayen da suke kwaranya.
Hakama Shatu hawayenta wani na korar wani.
Ita kuwa Junainah faɗawa jikin Ummey tayi sukaci gaba da zubda hawaye.
Bappa kuwa hannunta yaja suka juya suna nufi hanyar fita.
Da kayanta na ɗazu wanda taje Genaral Hospital Ɓadawaya dasu, hatta hand bag ɗinta na rataye a kafaɗarta wayarta na ciki.
Cikin mamaki take bin bayan Bappa, tare da yin taku a hankali tana bin bayanshi yadda yake jan hannunta.
Arɗo Bani kuma na biye dasu a baya.
Suna fitowa ƙofar gidan, Haroon da Jalal suka juyo suka kalli juna,
Cikin tarin mamakin ganin kamar yarinyar ɗazuce.
Shi kuwa Sheykh Jabeer yana zaune cikin motar, shi ɗaya dan duk sun fita.
Da sauri ya dafe saitin ƙahon zuciyarshi jin ta tsananta bugawar da yakeyi.
A hankali ya maida bayanshi ya jingina da sit ɗin tare da rufe idonshi.
Yana mai jin sanyin A/C na ratsa mishi jiki da jini da zuciya.
Amman duk da haka zuface ke tsastsafo mishi a jikinshi sabida bugun da Zuciyarshi keyi ya wuce misalin.
A hankali ya juya kanshi ya kalli gefen hagunshi inda yaga motar Jadda da kuma Dr Aliyu ne da Barrister Kamal ke jere a wurin.
Bappa kuwa a hankali yake taku, yana nufo inda Lamiɗo ke tsaye Dogari na riƙe masa da laima, Ɗanzagi da fadawa na zube a kasa.
Ita kuwa Shatu cikin rawan jikin jin idanun mutane na yawo a jikinta dan ma Allah yasa akwai niƙab a fuskarta.
Take bin bayanshi. Shi kuwa Sheykh Jabeer yadda suke ƙara matso inda yake haka bugun zuciyarshin keta tsananta.
Suna isa gaban Lamiɗo Bappa ya miƙawa Lamiɗo hannunta cikin sanyi da nitsuwa da taushin lafazi yace.
"Allah rene, ga Aishatu matar Muhammad Jabeer.
Gata amana bisa jagoranci ka, nasabarka da yardarka.
Da kamala da nitsuwa da na gani a fuskar yaron yasa naji ƙarfin guiwar baku aurenta.
Ba tare da fargaba ba, yanzu kaine kaka kuma jagora a gareta".
Sai ya kuma nuna Barrister Kamal da shima yana cikin wakilai, shi a zatonsa ma shine mahaifin Jabeer cikin sanyi yace.
"Kai kuma kaine matsayin mahaifi a gareta ku zame mata dangin ta data rasa, naso ace da mata a masu ɗaukanta, dan in danƙa amanarta a hannun macce yar uwarta.
Amman ba komai, na baku amanarta dan Allah kada a cutar da ita, domin nima ta kasance amanace a uwurina, domin ƴaƴan mu da muka haifama amanace Allah ya bamu kuma abun kiyayewa, bare kuma ɗiya irin Shatu ɗiyace da take da nasabobi masu yawa a gareni".
Cikin gamsuwa Lamiɗo yasa hannunshi ya amshi hannunta daketa karkarwa, tuni niƙab ɗin fuskarta ya jiƙe jilak da ruwan hawaye.
Cikin Dattaku Lamiɗo yace.
"In sha Allah zan kula da dukkan lamuranta tamkar yadda nake kula dashi Jabeer, kuma kada ka damu akwai masu meye mata gurbin uwa ƙanwa yaya dama duk danginta a cikin masarauta Joɗo, baƙoma baya kukan maraici bare kuma, matar sashin jinina".
Cikin sanyi da wasu hawaye Bappa yace.
"To Ngd matuƙa".
Arɗo Bani ne ya dafashi tare da cewa.
"Ka sanya mata al'barka a cikin aurenta ba zubda hawaye ba."
Sosai Haroon ya zuba mata ido.
Shi kuwa Sheykh Jabeer da mamaki yake kallon Bappa dake zubda hawaye.
A hankali su Bappa suka ɗan ja da baya.
Shi kuwa Lamiɗo ya juya ya nufi motar riƙe da hannunta.
Haroon ne yayi saurin buɗe musu marfin motar, suka nufoshi gadan-gadan.
Jalal kuwa ido ya zubawa yatsun hannunta da Lamiɗo ke riƙe dashi.
Shi kuwa Jabeer idonshi ya rufe da ƙarfi. Sai kuma ya buɗesu, dai-dai lokacin Lamiɗo ya kawota bakin ƙofar motar tare da cewa.
"Mamana kiyi bismillah ki shiga da ƙafar dama".
Cikin shessheƙan kuka ta gyaɗa kai tare da yin bisimilla kana ta ɗan sunkuyo, sai kuma kukan ya kubce mata.
Shi kuwa Jabeer da sauri ya buɗe marfin motar ta gefen hagunshi. Kamar gilmawar walƙiya ya fita cikin motar.
Dai-dai lokacin da Shatu tasa ƙafarta ciki.
da sauri yasa hannunshi ya buɗe motar Jadda tare da shigewa ciki yaja marfin ya rufe sabida ji yayi zuciyarshi zatayi bindiga, wani irin dogon ajiyan zuciya ya sauƙe mai ƙarfi.
Ita kuwa Shatu, a hankali ta shiga ta zauna, don batama lura da shi bane tabbas dai taga mutun ya fita cikin motar.
Tana shiga Haroon ya maida marfin ya rufe
Shida Lamiɗo suka koma sit ɗin bayan wannan sabida su a zatonsu Jabeer na ciki.
Ganin Lamiɗo ya shigane yasa duk kowa ya shiga motarshi.
Hakama Jadda ya shiga ya zauna hankalinshi na woje.
Sai da akaja motocin suka fara tafiya ne, ya juyo da sauri jin Jabeer na jan wani ja'irin tsaki mai tare da ajiyan zuciya.
Cikin mamaki Jadda yace.
"Haaahh kai kuma Meya kawoka nan? Yaushe ka shigo min mota!?".
Bai kula Jadda ba, asalima yi yayi tamkar bai jishiba.
Haroon kuwa cikin dariya ya ɗan bugi sit ɗin da yake zaton yana wurin cikin juya harcen Larabci yace.
"Masha ALLAH, gasar Shaɗi tayi mana rana mun rabaka da gwauranci".
Murmushi Lamiɗo yayi tare da kallon Haroon yace.
"Saura kai". Murmushi yayi tare