Showing 135001 words to 138000 words out of 299804 words

Chapter 46 - GARKUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

17 Jul 2024

111372

shi ɗaya sai ya zauna da kima-kiman riguna, ganshi wata ƙil basa damunshi".
Haka taketa maganar zuci, har ya gama wayar da yakeyi bata, saniba.
shi kuwa baibi ta kantaba yaci gaba da ɗan aikin da yakeyi a wayar.
Jin shirune yasa ta ɗan kalleshi, ganin ya gama wayar da yakeyi ne yasa, cikin dakiyar murya tace.
"Uhummm dama so nake in ba matsala ko zamu rinƙa yin abin buɗa baki ana kaiwa masallacin, da kuma bawa bayi nasu daban".
Bai kulata ba, asalima yamutsa fuskarshi yayi, ya lura wannan abar bata gama iya sanin makamar mgna ba, ji yadda take mgn a kaikace.
Kamar ba ba fullatanaba, bayan anyi ittifaƙin bayan larabawa babu ƙabilar dake da luggar iya sarrafa harshe sama da Fulani.
Shiru tayi tare da tura baki kana ta ɗan murguɗashi, tare da cewa.
"Ayyah ka amince mana?".
kanshi ya sunkuyar tare da ɗaga system ɗinshi ganin biyu dai-dai ta cika.
Miƙewa tsaye yayi tare da motsa lips ɗinshi a hankali yace.
"Eh". Da sauri ta juya ta fita tana hararan bayanshi.
Shi kuwa bedroom ɗinshi ya wuce.

Rage kayan jikinshi yayi kana yasa hannunshi ya jawo pillow'nshi ya wurgar can gefe gaban gadon inda babu carpet,
a hankali ya kwanta a wurin,
Gudun kada daɗi gado yasashi yayi baccin da zai makara sallan la'asar, Yana konciya ba jimawa yayi bacci.

Ita kuwa cikin jin daɗin amincewar da yayi, tacewa Ummi.
"Ummi ya yarda yace muyi".
Miƙewa Ummi tayi tare da nufar kitchen a tare suka shiga.
Tana cewa.
"Yauwa to taho mu gayawa Saratu abinda za'ayi.

A tsaye suka sameta a tsakiyar kitchen ɗin kusa da kitchen table, tana gyara ganyen.
"Yauwa Saratu kin wonke shinkarfa masan ne?".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Eh na wonke,kuma mafa tun ɗazu da nazo kuna kuma bacci na jiƙa wani, sai dai hannuna ya zarce yayi yawa, yanzu ina gama tsinkar ganyen zan kai markaɗen ne in na dawo an kwaɓashin sai in fara firan Arish ɗin".
Ajiyan zuciya Ummi tayi tare da cewa.
"Mugamshin".
Babbar robar dake gefenta ta jawo tare da cewa.
"Gashi kinga yayi yawa wlh mancewa nai sai naga kamar na gidan Gimbiya Aminatu zan jiƙa shiyasa, kinga da na haɗa da wanda kika jiƙan yayi yawa sosai, ko zamu rabashi biyu".
Murmushi Shatu tayi ganin shinkafar tanada yawa, kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Ba matsala hakanma yayi dama mai yawan akeso".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Ga kuma ƙullun na dafa tun ɗazu har yayi sanyi, shiyasa nake sauri in kai markaɗen naga lokacin yayi nisa".
Motsowa tayi inda take tare da cewa.
"Ɗauki markaɗen ki kai bari in ƙarisa wannan aikin".
Cikin mamaki tace.
"A a bar".
Da sauri ta katseta da cewa, jeki".
To tace cikin mamakin sauƙin halinta ta ɗauki robar jiƙeƙƙiyar shinkafar da ta kai mudu biyar har ta ɗaura a kai,
Ta kuma sauke jin Shatu na cewa.
"Yauwa naga akwai murjejjiyar gyaɗa, ɗebo, da wata shinkafar kizo ga dabino da kwakwa a nan ki haɗa ki jikasasu ki tafi dasu, na kunune kafin a markaɗa wannan na masan shinma ya jiƙa sai a markaɗa miki shi.
Da sauri ta juya tayi yadda tace ɗin tanayi tana nuna mata dai-dai yadda takeso, saida ta gama kana rufe babban roban da marfinshi sannan ta ɗaura ƙaramin a kai ta tafi.

Ita kuwa Shatu matsowa tayi taci gaba da tsinkan ganyen, ita kuma Ummi freezer'n ta buɗe tare da ɗebo kayan ciki mai yawa, tazo.
Ta wonƙeshi fes, kana ta watsa al'basa mai yawa a ciki, Sannan tasa citta,kanamfari, cory tare da sauran kayan ɗanɗanon.
Gas ta kunna ta ɗaura tukunyar, sannan ta dai-dai-ta wutar.

Wani babban roba ta ɗauko kana ta nufi Store Arish ta ɗebo mai ɗan yawa tazo tana fereshi cikin ɗan injin ɗin firar lokaci ɗaya tayi nisa a fitar.
Ita kuwa Shatu tana gana gyaran ganyen ta ɗebo kayan miya tazo ta jajjagasu yadda takeso.
Kusan a tare suka gama da Ummi.
Wankeshi Ummi tayi bayan ta yishi tsillk-tsillk kana ta sashi a tukunya, tare ɗan yaryaɗa gishiri, ta rufeshi.
Ta ajiye gefe.
Ita kuwa Shatu cikin kula ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi me za'ayi da ganyen?".
"Miyan da za'aci masar dashi".
To bata amsa tana komawa cikin Freezer'n fruits ta ɗebo.
Tazo tana wonkesu tare da shiryasu cikin tray mai girma, kana ta shirya wasu kuma a wani ɗan madaidaicin tray mai masifar kyau.
rufesu tayi kana taje tasasu cikin Fridge.

It's kuwa Shatu can nama ta ɗebo dai-dai misali wonƙeshi tayi tasa a tukunya tare dasa kayan ƙamshi dana ɗanɗano.
ta ɗaura a wuta. Ummi kuwa ruwan tea ta ɗaura a ɗaya murhun dake gas ɗin babbane.

Naman na sulaluwa ta kwasheshi tasa mai saida yayi zafi tasa al'basa,
ya soyu yana ƙamshi kafin tasa jajjagen kayan miyar ta,
Ya soyu kana ta ƙara wonƙe ganyen miyar yazo tasa, ta soyashi da kyau.
kana ta zuba naman da sauran ruwan miyan.
Tasa duk sauran kayan hadin ta rufe tukunyar.
Sosai Ummi tayi mamakin yadda ta haɗa miyar, to sai dai bata damuba sabida sanin ko wacce mace da yadda take sarrafa girkinta, kai yadda kakeyi daban in wani ya gani yayi mamaki, yadda wani keyi da ban in ka gani kayi mamaki.

Cikin ƙanƙanin lokaci dai suka haɗa duk aiyukan da zasu iya ajiyesu ba tare da sun samu matsalaba.
Ita tayi miyar masan, ta kuma ƙarisa ferfesun kayan cikin da Ummi ta fara.
Ummi kuwa ta tafasa musu tea ta ɗuɗɗura a flaks,
Kana ta tafasa Arish ɗin.
Dai-dai lokacin kuma Saratu ta dawo.
Ita Ummi ce ta ɗan amshi ƙullun masar tare da cewa.
"Gskya mun ɗan makara aikin Masar nan gashi ni hannuna baya tashi da wuri".
Da sauri Shatu ta matso tare da miƙawa Ummi roban markaɗen kunun.
Tace.
"Ba matsala Ummi ni hannuna na tashi da wuri.
Yanzu tace mana marƙaden kunun bari in kwaɓa mana Masar."
Haka kuwa akayi Ummi ta fara tacewa.
Ita kuwa kulun dafaffiyar ɗanyar shinkafar ta murmusa cikin marƙaden Masar,
Kana tasa fulawa tare da yis kaɗan sannan ta tarfa gishiri kaɗan.
Kana ta rufeshi a robar dan babbace, motso da robar tayi kusa da Gas ɗin yana ɗan jin ɗumin wuta.
Gefen Ummi ta dawo wacce ta gama tace markaɗen
A babbar tukunta ta zuba shi kana ta ɗaura kan wuta tare da dai-dai-ta wutar tanayi tana motsa kunun.
tare da ɗan tarfa wanda ta rage, da surkin lemun tsami.
Cikin Sa'a ɗaya ta dama kunun shinkafar fari ƙal tamkar madara.
Sugar tasa ta juye a a ƙatuwar kula kana tasa a maidaciyar kula, Sannan tasa a flaks ɗaya, sai kuma tasa a Mug mai marfi duk ta kimtsasu gefe.
Tuni Side ɗin ya ɗin ke da ƙamshi miyar masan da ferfesun nan.
Buɗewa tayi ganin miyar tayine ta sauƙe ta maida gefe.
Kana ta kalli Ummi tace.
"Ummi je kiyi salla la'asar tayi, in kin dawo sai inje inyi".
To Ummi tace ta fita tana mamakin saurin aikin Shatu.
Koda taje tayi sallan ta dawo ta sameta tana sauƙe tukunyar ferfesun.
ganin Ummi yasa tace. "Yauwa Ummi komai yayi dai-dai yanzu kaskon tuya zamu daura kinga kullun ya tashi".
Cikin mamaki Ummi ta kalli Robar da taga har kullun na shirin zubewa.
Ita kuma ɗiba tayi a wata roba kana duk tasa yankekken al'basane a ciki Sannan tasa sugar ta gauraya,
sannan ta matso da kasko biyu,
juyowa tayi ta kalli Saratu tace.
"Yauwa Sara matso. Ke ki rinƙa yi kina sawa a wannan babban kulan in ya cika kisa a wannan shima.
Ummi ke kuma kisa mana namu anan suyanki mukeson ci".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"To jekiyi salla".
To tace kana ta fita.
Ita kuma Ummi ta juya ta kalli Sara tare da cewa.
"Kema kije kiyi salla".
Cikin ci gaba da aikinta tace.
"Ai nima nayi".
"To shike nan". Ummi tace kana sukaci gaba da tuyan.

A falo ta haɗu da Hibba da Jamil, sai dariya yakeyi cikin dariyar yace.
"Yauwa Aunty Shatu dama idonki nazo in gani, dan ga Hibba kam ta kusa kasawa".
Murmushi tayi dan bata da sauran ƙarfin yin dariya.
Cikin ɗan fito da idanunta da suka ɗan faɗa tace.
"Gani ras dani".
Dariyar ƙeta mai cike da alamun yunwa da ƙishi yayi tare da cewa.
"Inafa ras kalli yadda idonki ya fito kamar kinyi azumi goma".
Murmushi tayi kana tace.
"Um bari inje inyi salla".
Sai ta kuma kalli Hibba dake lankwabe tace.
"Sannu Hibba kwanta ki huta".
Jalal da yanzu ya shigone ya ɗan taɓe baki tare da cewa.
"To me tayi da zata huta tunda fa gari ya waya in anga ta tashi dai yin salla ne, tun tuni birgima take a tayis wai sanyi take nema".
Dariya sukayi mata baki ɗayansu,
Ita dai Shatu ciki ta wuce.
Salla tayi kana ta fito. Koda tazo kitchen ta samu Hibba na suya musu Arish ɗin, tayi mamaki.
Cikin wasa tace.
"Kawo in karɓeki jeki kwanta".
Cikin sanyi tace.
"Ai Hamma Jabeer ne yace min in ina aiki bazanji wuya ba, zanfi ganin lokaci ya gudu".
Dariya sukayi mata kana kowa yaci gaba da aikinshi.
Ita Shatu miyar sahur na asuba ta ɗaura musu.

Cikin ikon Allah shida dai-dai suka gam kan aikinsu.
Bayan Shatu'n ta taya Hibba suya kwai daban, ta jerasu a Foodflaks, in ta ajiye fefeyin soyayyan ƙwai da yaji haɗi da diddigin kifi, sai ta zuba soyayyan Arish a kai kana ta kuma rufeshi da fefeyin kwai haka ta rinƙa jerasu saida ta cika kulan.

Ummi kuwa ta sawa Saratu komai nata.

Sannan suka kimtsa wurin fes suka fito da komai suka jera a dinning table.

Nan duk suka wuce ɗauki.
Wanka sukayi, kana sukayi al'wala sannan suka fito falo. A nan suka samu Imran, Jalal, Jamil, Sulaiman.
Cikin gajiya Ummi tace.
"Yauwa Jalal ku ɗauki manyan kulolin nan ku kai masallaci.
Sauran madaidaitan kuma ku ajiyewa sarkin bayi.
A bawa bayi da hadimai".
Murmushi Jamil yayi tare da cewa.
"Eh lallai bana bayi sun samu uwar gijiyar data tuna dasu, bayan kuma anayi musu nasu na daban".
Cikin lumshe ido Shatu tace.
"Eh suma suci abinda muke dafawa da kanmu, ba sai na gandun nasuba".

Miƙewa sukayi suka ɗauki kulolin sun zo falon kenan Sheykh na shigowa, wani hadimi na biye dashi da manyan ledodi cike da ƴaƴan itatuwa.
Kusan a tare suke mishi sannu da dawowa.
Murya a bushe alamun ƙishi yake amsa musu kana ya nunawa Ummi leda ɗaya yace.
"Ummi a wonke wannan a haɗa da dabino mudu uku a basu su kai masallaci".
Ya ƙarishe mgnar yana wucewa.
Da sauri Ummi tace to.
Ta miƙe kenan Shatu tace.
"Ummi zauna bari in wanke sun".
To tace kana ta koma ta zauna.
Ita kuma taje ta wonke ta zubasu a tray kana ta ɗauko plates and cups masu yawa, tazo ta miƙawa Imran.
Da sauri suka amsa suka tafi.

Jim kaɗan suka dawo, cikin gajiya Jamil yace.
"Ummi ansha ruwafa mun samu Ladan na cin dabino".
Da sauri Hibba ta miƙa tare da cewa.
"Su ladanannan haka suke basa kiran salla sai sun sha ruwa."
Dariya sukayi mata kana suma suka miƙe sukabi bayanta.

Zama sukayi bisa kujerun kowa da abin yake hari.
Sai dai kab ɗibsu da dabino suka fara.
Ummi ce ta kalli Shatu tare da nuna mata babban tray'n da aka shirya komai na buɗa cikin Foodflaks guda 3 madaidata masu kyau, sai plate ɗin da aka shirya fruits masu ɗan karen sanyi, tupa, inabi ,kankana, abarba, gwanda, Lemu, ayaba, kana da dabino, da kwakwa,
Sai goran zam-zam madaidaci, kana sai cup da tea spoon a ciki, sai fork and knife a gefe da gefen plate ɗin dake cike da fruits ɗin komai biyu akasa.
Kulolin kuma ɗaya masane a ciki, ɗan namiyar kuma miyar Masar ne, sai ɗayan kuma, soyayyan ƙwai da dankalin, ɗayan kuma ferfesun kayan cikin ne.
Cikin nitsuwa Ummi ta ɗago tray ta miƙa mata tare da cewa.
"Yauwa gashi kai mishi lokacin shan ruwan na tafiya, yanzu zakiga ya fito".
Cikin sanyi da gajiya ta amshi tray'n kana ta nufi falon nashi, cikin nitsuwa take takun, a hankali tayi sallama tare da kutsa kai cikin falon.
A can bisa Dinning area ta hangoshi yana zaune, kan kujera ɗaya, ya kuma jawo ɗaya kujerar ya ɗaura sawunshi a kai ya miƙesu, System ɗinshi na bisa cinyarshi.
A hankali take takowa saman steps ɗin tare da ratsa cikin jeren ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar sheƙin Daimond sai sunkuyar da kanta tayi sabida ɗauke mata ido da suke.

A hankali ta isa kusa dashi, cikin tura baki tare da ɗan murguɗashi ta ajiye tray'n, a tsakiyar table ɗin.
ɗago kanta tayi da niyar ta ɗan juya, ta fita.
Wani irin buɗe idanin tayi gaba ɗaya tare da zubasu, bisa sharaban ƙafarsa ta dama, wanda sanaɗin zaman da ya ɗan yi ya miƙe ƙafafuwan nashi bisa ɗaya kujerar ne yasa suka ɗan baiyana, wani irin kallo mai cike da ɗimuwa takeyiwa zanen dake bisa ƙafarshi ta dama, da sauri ta rumtse idanunta tare dasa hannun hagun ta kama kanta sabida wani irin sarawa da ya farayi da ƙarfi.
Cikin sauri ta juyo tare da miƙa hannun damanta ta sauƙeshi kan...!





Akwai kayan gyara na amare da uwar gidaye da masu jego, ga mai buƙatar saya ga number ta 09097853276



By
*GARKUWAR FULANI*
Ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar sheƙin Daimond da yayiwa wurin labule.
Yayin da kuma hankalinta da idonta duk suke kan ƙafar tashi tana kallon zanen da take gani har kamar motsawa yakeyi a jikinshin, da kuma suffar macijiya.
A hankali ta ɗago ƙafarta tare da take step ɗin forko, hankalinta kuwa duk yana baya, har ta juya kanta gaba ɗaya sam ganinta baya gaba.
Cikin rashin sa'a kafar ta tsallake step ɗin forko bata isa kan dandamalin ta biyu ba, ta sauketa, cikin akasi ƙafar ta sule tare da yin shuuuuu tayi gaba.
Wani ƙara mai ɗan karfi irin na maiyin azumi ta sake tare da rumtse idanunta da ƙarfi tana jiran taji ta ina ɗin ta zai karye.
Wani irin ihu ta kuma sakewa, lokacin da taji ta faɗi gib a kan stpes ɗin kanta ya bugi dandamalin sama.

A hankali ya juyo kanshi ya kalleta a fakaice,
Ba tare da yace mata ko ƙalaba ya juyar da kanshi ya fuskanci tray'n data ajiye mishi, plate ɗin fruits ya ɗan buɗe kana, ya ɗauki Fork ɗaya, janye ƙafafuwan shi, yayi ya sauƙo dasu ƙasa kana ya gyara zamanshi ya fuskanci Dinning table ɗin da kyau.
Fork ɗin yasa ya fasa cikin dabino da yake irin na kwali nanne mai laushi ne,
ture ɗan yayi gefe kana ya soki dabinon a hankali ya kai bakinshi, bayan yayi addu'o'in buɗa baki.
Ido ya lumshe jin lokacin da sanyi da zaƙi da ɗanɗanon dabinon ya game mishi baki.

Ita kuwa Shatu kuka tasa tare da riƙe ƙugunta, da kanta cikin muryar kuka take cewa.
"Wayyo Allah na. Wayyo Ummey na, bayana ya karye ƙuguna ya ɓalgace, kaina ya fashe ƙeyana ya tarwatse".
Ta ƙasa Glass ɗin table ɗin ya ɗan kalleta, kana ya maida kanshi yaci gaba da cin dabino, yana maijin wani irin masifeffen dariya na taso mishi jin raki da Shatu ke zubawa.
Saida yaci ƙwaya bakwai, kana a hankali ya fara tsira Fork ɗin kan ƴaƴan inabi masu masifar sanyi da daɗi, ci yakeyi yana jin ƙishin daya addabi moƙoshinsa na wucewa.
saida ya tsinke nonon inabin kab ya cinye, kana ya fara soka kankana da akayiwa ƙaƙanan yanka kana aka barbaɗa garin madara a samansu, shima shanye rabinshi yayi.
Wani sassanyan gyatsa yayi tare da ture tray'n gefe.

Ita kuwa Shatu sosai taji zafin faɗuwan ga azumi ga gajiyan aiki ga faɗuwa ga haushin yadda duk ihun da tayi babu wanda ya kulata, bare a kawo mata agaji, abun ya haɗe mata sai hawaye share-shere ta tabbatar da a gidansu ne tayi wannan ihun da gaba ɗaya iyayenta da yayunta da ƙanwarta duk suna kanta, da tuni an ɗagata a wurin ma.
Bege da kewa da kukan rashin yan uwanta da watseman ahlinsu ne ya tunzura hawayenta.
Ta kasa tashi sabida jikinta duk rawan yunwa da gajiya yakeyi ba ƙarfi sam.

A hankali ya miƙe tsaye bayan ya sha ruwan zam-zam mai ɗan sanyi kan ƴaƴan itatuwan da yaci.
System ɗinshi ya ajiye kan Dinning table ɗin, tare da wayarshi.
Gefenta ya ɗan ratsa ya fara taka steps ɗin tare da kallonta a fakaice.
Yana gab da sauƙane ya ɗan motsa lips ɗinshi tare da cewa.
"Kaɗan kenan in dai baki dena samin ido a jikina ba,
Faɗuwa harda kareireyewa zakiyi in baki kiyayi yimin kallon ƙurillaba, na lura ku mutanen wancan dajin bakuda abinda kukafi so sama da kallon killataccen wuri na jikin mutun.
Muddin baki dena satan kallon jikina ba, sai waɗannan mayatattun idanun naki sun tsiyaye kin huta ki zama makauniya babu ɗan jagora.
Kiyi dai a hankali ko kya samu ki mutu da idonki,".
Ya ƙarishe mgnar yana tafi kamar bashi yayi mgnar ba.
Ita kuwa Shatu hannun tasa ta sharce hawayenta tare da rakashi da hararan kai mugune.

A falon ya samu su Ummi sunata dariya.
Cikin sauri ya kalli su Jamil yace.
"Kai wannan dariyar na menene, ku taso mu tafi masallaci".
Cikin dariya Jamil yace.
"Allah ko Hamma Jabeer ina zaton Hibba bata taɓa azumi ba sai bana.
Ga yadda ta dawo wuni ɗaya, wai a haka kuma har ta fara lissafin wai yauwa yau mun kai ɗaya mun rage".
Ɗan gajeren murmushi yayi tare da cewa.
"Muhibbata tashi kije kiyi salla sai ki ɗan konta ki huta kafin a kira isha'i ko".
Cikin sanyi tace.
"To Hamma MJ".
Jalal kuwa cikin yin ƙasa da murya yace.
"Gobe ma zakiyi ne ko zaki huta".
Cikin kwaɓe fuska tace.
"Zanyi Umaymah tace, bana ko ɗaya in nasha sai na biya".
Murmushi ya ɗan yi tare da cewa.
"Ashe dai kin girma".
Da sauri ta sunkuyar da kanta, shi kuwa yabi bayansu Jamil.

Duk sukayi gaba, Sheykh kuwa na bayansu.
har yaje tsakiyar falon sai kuma ya ɗan tsaya jin Ummi na ce mishi.
"Shetu fa".
Cikin saurin tafiya masallacin yace.
"Tana can ta faɗi wai ko ta karye ne naji tana cewa ban dai san mataba".
Yana kaiwa nan ya fita, ita kuwa Ummi da sauri ta miƙe cikin zaro ido tace.
"Karaya kuma? Innalillahi yaushe".
Tayi maganar tana nufar falonshi,
A bakin ƙofar shigowa sukayi kiciɓis da ita, da sauri ta tareta tare da tallabota, jin yadda jikinta ke rawane ta jawota suka fito falon cikin tausayawa tace.
"Sannu Shatu".
Cikin tausaya Hibba taketa jera mata sannu.
Ajiyeta bisa kujera Ummi tayi tare da cewa.
"Baki sha ruwan ba ma ko?".
Kanta ta gyaɗa mata alamar eh.
Hakane yasa Ummi tacewa Hibba ta ɗebo mata, abin shan ruwan a take kuwa ta kawo mata.

Bayan tasha ruwanne duk suka nufi cikin ɗaki dan yin salla.


Daga yin sallan magriba su Jamil suka dawo sukaci abinci kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login