Showing 78001 words to 81000 words out of 299804 words
ina, dan ina jirane sai jaridu sun fidda shi kafin in watsashi kafafen yaɗa labarai na duniyar gizo-gizo".
Cikin tsananin jin daɗi suka jinjina wa basirar Laminu.
A can sashin Gimbiya Aminatu kuwa, kekyawar tsohuwar bafullatana ƴar kimanin shekaru 61 sosai hankalin ta ya tashi jin labarin abinda ya samu jikanta mafi soyuwa a gareta. Cikin rawan jiki ta miƙe tare da juyawa zata nufi Side ɗin ta.
Da sauri Lamiɗo yayi gyaran muryar dake mata nunin ta zauna ta nitsu.
Cikin tashin hankali ta koma ta zauna tare da cewa.
"Allah Rane zanje in duba halin da yake cikine".
Cikin ƙasaita da bada umarni yace.
"Koma ki zauna ki nitsu kin ga magriba ta ƙara to. Bawai zan hanaki zuwa bane, ki bari ayi sallan magriba da isha'i sai ki aika Jakadiya ta dubo miki in idonshi biyu sai kije".
Ba don ta soba ta amince da hakan.
Hajia Mama kuwa, tana jin lbrin abinda ya faru daga bakin Abba, kai tsaye daga sashinsa sashin Jabeer ɗin ta nufa.
A falo ta samu Haroon kadai zaune cikin shigar kakanan kaya. Cikin tashin hankali da kiɗima da firgici ta nufi hanyar side ɗin. Jabeer ɗin ido na zubda hawaye.
Da sauri Haroon ya miƙa tsaye cikin sanyi yace.
"Mama ya samu bacci ne, kuma Dr Aliyu yace kada a tadashi, jikin da sauƙi ma sosai ki kontar da hankalinki".
Ina hankalinta bai konta da hakanba, saima ƙara kutsa kai cikin falon side ɗin shi takeyi.
Cikin sanyi ta tsaya jin Haroon na ce mata.
"Dan Allah Mama kiyi haƙuri, Allah kuwa jikin da sauƙin, Abba da Lamiɗo da kansu suka kula dashi, yanzu haka bacci yakeyi."
Cikin tashin hankali murya na rawa tace.
"Haroon hankali na ya tashi sosai, ina tsoron kada a cutar min dashi kamar yadda akayiwa Jafar."
Hannunta ya kamo kana yaja suka dawo falo, cikin sanyi yace.
"In Sha Allah babu wani abinda zai sameshi, in Allah ya yarda an gama samun nasara a kansu, yanzu warakace ke kusantosu, in sha Allah duk sarƙaƙiyan dake sarƙafe cikin masarautarku da mutanen cikinta zai worwore, za kuma ayi walƙiya kowa zai ga kowa!".
Wani irin lumshe ido tayi tare da cewa.
"Allah yasa haka".
Cikin kontar mata da hankali yace.
"Amin Amin. Umaymah ma tace tana nan tafe".
Cikin tarin mamaki da baiyana tsantsar jin daɗin ta tace.
"Alhamdulillah kai naji daɗin wannan mgnar ko ba komai in tazo ai zan samu wacce zan tattauna damuwar raina, sabida hirar waya bata wadatar wa".
Murmushi yayi tare da nuna mata hanyar fita cikin tsokana yace.
"Wato kun san ɗan naku ragone shiyasa duk kuka tashi hankulanku."
Cikin share hawayenta tace.
"Haroon yayanka nefa".
Tura baki yayi tare da cewa.
"To naji Hajia Mama je kiyi salla lokacin salla yayi, kinji an fara kiran salla".
Da haka ta fita.
Shi kuwa Haroon a hankali ya nufi cikin ɗakin, kamar yadda yabar Ya Jafar zaune a tsakiyar gado yasa Jabeer a gaba, yana karatu tare da gyara mishi rufuwar shi.
Haka ya sameshi yanzuma,
Kuma har zuwa yanzu idonshi bai daina zubda hawaye ba.
Kana ganin fuskarshi zaka hango zazzafan so da ƙanan da tausayin ƙanin nashi cikin ƙwayar idonshi.
A hankali Haroon ya matsosu.
Cikin sanyi yakai hannunshi ya kamo hannun Ya Jafar ɗin.
Kanshi ya ɗago ya zuba mishi ido.
Murya cike da rauni Haroon yace.
"Ya Jafar tashi kazo muje masallaci lokacin salla yayi. Muje muyi salla muyiwa Sheykh Jabeer Addu'o'in samun lfy".
Kanshi ya gyaɗa sabida in dai abu na ibadane to bai kasance jiɓeɓɓe a kanshi ba.
Sunkuyo wa, yayi ya sumɓaci goshin Jabeer kana, ya sauƙo kan gadon.
ƙofar Bathroom Haroon ya nuna mishi da yatsa.
Shiga yayi bayan ya fitone, shima Haroon ya shiga ya sabunta al'wala kana, suka fita.
A babban falon suka samu, Aunty Juwairiyya da Jakadiyarsu suna shirya musu abinci bisa dinning table.
Cikin kula Aunty Juwairiyya ta kalli Haroon murya a sanyaye tace.
"Haroon ya jikin nashi dai?".
Ɗan tsayawa yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah gsky zama muce ya worke, sabida ya amayarda duk wani dafin dake jikin bilalin yanzu naga shatin kunaman ma duk sun ɓace a jikinshi, ya zama sai shatin bulalin".
Murmushi Jakadiyarsu tayi tare da cewa.
"Suma nanda kwana uku in sha Allah babu tabonsu a jikinshi. Na gaya muku ai jinyar Shaɗi ba abu mai wuya bane a masarautar Joɗa, yanzu da asibiti aka kaishi, koda ko ƙasar waje za'a fiddashi a ƙalla sai anyi watanni uku ana jinyarshi, in yanada nisan kwana ya worke da kyar in kuma kwananshi sun ƙare ya cika a can. Amman yanzu yana tashi bacci zaiji sauƙin sosai".
Cikin mamaki suka zuba mata ido.
Jalal da Jamil da yanzu suka shigone suka haɗa bakin wurin cewa.
"To wai Ummiy meyasa naga kamar farin cikin, abun kikeyi keda ko ruwan sama bakya son ya taɓa lfyarmu mu bare ɗan gatanki".
Kanta ta ɗan jijjiga tare da cewa.
"Abune mai duhu shekarun ku baiyi yawan da zaku gane haskenba, su kansu magautan Jabeer duk basu san ƙarfin iko da sani da shaharar wannan masarautar akan al'adun Shaɗi bane,."
Jafar ne yayi gaba bayan ya duba agogon hannunshi ganin hakane duk suka bi bayanshi.
A can Rugar Bani kuwa, bayan anyi sallan bamgrib, anyi Isha'i.
Shatu, Rafi'a, Ummey, da kuma Bappa sai Autar gidan Junainah dake konce gefen Ummey duk sunyi shiru.
Suna jin Bappa yana basu lbrin yadda komai ya faru a wurin gasar cikin sanyi yaci gaba da cewa.
"Tabbas akwai abinda Allah yake nufi da wannan bawan, haƙƙun nasan Allah bazai bari a zalumceshi haka nan banzaba, inaji a jikina akwai wani babban al'amari mai girgiza zuƙatan mutane da zai faru a nan gaba".
Cikin sanyin murya Rafi'a tace.
"Bappa meye sunan jikan sarkin ne?".
Cikin sanyi Bappa yace.
"An faɗa amman na mance sunan".
Sallamar da wani yaro yayine ya sasu maida hankalinsu kanshi, bayan ya rusuna ya gaisa Bappa ne yace.
"Bappa ana sallama da Shatu wai tazo".
A hankali Shatu dake zubda hawaye ta juyo ta kalleshi. Bappa kuwa cikin girma yace.
"Waye ne?".
Wani irin azabebben ajiyan zuciya Shatu ta sauƙe jin yaron yace.
"...!
By
*GARKUWAR FULANI*
"Ya Salmanu ne yake kirantan, yace tayi haƙuri tayi sauri ta fito."
Cikin sanyin jiki Shatu ta manna kanta jikin kafaɗar Rafi'a.
Shi kuwa Bappa, gyaran murya yayi tare da cewa yaron.
"To je kace mishi tana zuwa."
Jin haka yasa yaron ya juya ya fita.
Miƙa Bappa yayi kana ya kalli Shatu murya a sake yace.
"Shatu tashi kije, kiji dame yake nemanki".
Cikin sanyi tace.
"To". Kana a hankali ta miƙe dan cika umarnin Bappa.
Rafi'a kuwa, miƙewa tayi ta shiga cikin ɗaki, gyara musu wurin konciya tayi, sannan tazo ta shigar da Junainah kana ta cewa Ummey su shiga, jiki a saɓule Ummey ta miƙe suka shiga.
Bappa kuwa turakanshi ya shiga.
A can ƙofar gidan kuwa.
Bisa ɗan dakalin ƙofar gidan nasu, suka zauna.
Tunda suka zauna tayi shiru, kanta na sunkuye tana wasa da ƴan yatsunta, kana hawaye na ɗigowa kan tafin hannunta.
Shi ma Ya Salmanu shiru yayi, tamkar bazaiyi mgna ba.
Farin wata kuwa ya fito ras ya haska ko ina, alamun yau watan ya kai kwana tara ko goma.
Kanshi ya ɗan juyo ya ɗan kalleta cikin tsananin tausayawa ya fidda numfashi mai zafi tare da cewa.
"Shatu!". Shiru bata amsa mishiba sai dai ɗago kanta tayi tana kallonshi hawaye na kwaranya, wani irin murmushi yayi cikin sanyi da harshen fillanci yace.
"Bazan hanaki kukaba, Shatu, sabida koni kaina nakan zubda zafafan hawaye a duk sanda na tuna yayuna ƙannena makusantana, abo kaina da aka kashe, wanda basujiba basu ganiba.
Nakanji zuciyata na tafasa, tafasar da nakejin bazai taɓa gushewa ba sai na ɗauki fansa."
Cikin rawan murya tace.
"Ya Salmanu fansa kuma?".
Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa.
"Uhum fansar dai, tunda hukuma da gwamnatin da masarautun gargajiya basu ɗauki mataki kan abinda akeyi mana ba. To mu zamu ɗaukarwa kanmu."
A hankali tace.
"Ta yaya ɗin bayan duk an kashe matasa majiya ƙarfin. Cikin kaso goma na mutanen Rugar Bani an kashe kaso 6 huɗune suka rage. Me amfanin ramuwa, wlh da zan faɗa aji da mun bar musu garinsu kawai mu koma wani wurin".
Gyara zaman shi yayi ya fuskanceta da kyau cikin sanyi yace.
"Ko wani ɗan adam ina ya shiga dumuwa, ire iransa ke shige mishi ya magance matsalar.
Yanzu da ɗan jarida ɗaya aka kashe zakiga zakiji yadda ƙungiyoyin yan jaridu zasu magantu, sai ya zama babu wani rahoton da zasu buga sai na kashe ɗayansu da akayi.
Hakama da za'a kashe police officer ɗaya zakiji yadda hukumar zatayi ta bincike da ɗaukar mataki har sai sun gano wayene sun kuma ɗauki mataki.
Da za'a ƙona kamfani ɗaya ire irensa kamfanoni sama da dubu zasu iya shiga fadan.
Hakama in da za'a taɓa ɗan kasuwa to zakiji yadda duk yan kasuwa zasuyi ta kumfar baki.
Da za'a kashe manomi ɗaya to zakiji yadda gungun manoma zasuyi rubdugu kan mgnar.
Da za'a taɓa bafaden wata masarauta zakiji duk masarautun ƙasarnan sun amsa.
Haka abin yake. Duniyar ta zama waka sani? waya sanka? Mu kuwa Fulani bamu san kowa ba bayan Allah da Manzonsa, bamu da wani namu a siyasance.
To tunda haka abin yake, muma da wannan salon zamuyi amfani.
Muna nan munata raba goron gaiyata wa duk al'ummar fulanin makiyaya a duk inda suke a cikin duk faɗin duniyar nan, in dai sunada damar zuwa to su zo!.
Su kawo mana agaji, wlh in sha Allah da izinin ubangiji sai mun yaƙi kafuran Bonon sai mun kashe dodon tsafinsu Bonon mun hallakashi a doron ƙasa,
Shatu mun kai matakin da wallahi babu mahaluƙin da zai dakatar damu.
Sai mun kauda Shirka da waɗannan mushirkan a wannan yankin."
Ido ta rumtse wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata.
Cikin muryar dake nuna ƙunar ranta tace.
"Ya Salmanu wane mataki ake ɗauka kan neman su ya Giɗi kuma?".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Yana cikin matakin shiga cikin ƙabilar mu yaƙesu, mu kuma bincika ko sun ɓoye su Giɗi a cikin garin nasu".
Ajiyan zuciya taja tare da cewa.
"Allah ya taimaka".
Amin Amin.
Murmushi yayi kana yace.
"Kinji batun gasar da akayi ko da nasarar dake tinkarar rayuwarki ko?".
Cikin sanyi tace.
"Kaiya ya Salmanu ina kake da tabbacin nasara mutumin da bamu san irin fansar da zai ɗaukaba, naso ace kaine kai wannan nasarar da nafi kowa farin ciki".
Murmushi mai ciwo yayi a ranshi kana yace.
"Nan ɗin ma muna zaton farin ciki, duk da akwai tarin ƙalubale, mu dai in mun samu wani ya ci Ba'ana a gasar Shaɗi kin san yayi al'washin zai bar ƙasar nan gaba ɗaya ko?".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Uhum in bai sauya salon ba dai".
Cikin jin daɗi yace.
"Ba zai sauya saloba, dole zai bar ƙasar sai dai shiri zaije ya ƙara, kafin ya dawo kuma, an aura min ke, shi kuma jikan sarki.
Muyi musu mubaya'a, mun yarda su masarauta Joɗo fulani ne".
Cikin tsananin jin daɗi tace.
"Allah ya tabbatar da haka ya Salmanu yasa kuma a samo su Ya Gaini cikin Bonon don Ni dai nafi zaton can suka kaisu.
In anyi gasar an cishi, ya bar kasar, a ɗaura aurenmu a ranar".
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamun jin kunya,
Shi kuwa Salmanu murmushi yayi tare da cewa.
"Iye yan Matana an girma, me ma za'ayi mana?".
Cikin kunya tace.
"Ban saniba".
Murmushi yayi kana yace.
"Ni ai bazan manceba tunda yanzu burin mu na kusa da cika, ayi mana aure, nima haka ne tsarina ana watsewa gasar suna tafiya, za'a ɗaura mana aure.
Kinga gashi dama na samu aiki a babban birninmu.
Sai mu tafi can abinmu ko Wannan mugun saurayin naki ya dawo bazai samemu ba".
Murmushi tayi shi kuwa ido ya zuba mata yana jin tarin farin ciki.
*DAN ALLAH DA MANZONSA DA DARAJAR IYAYENKI DA SUKA HAIFEKI SUKA BAKI TARBIYYA, KADA KI FITARMIN DA LITTAFINA DAN AL'FARMA ANNABI DA AL'ƘUR'ANI, KU DENA FITAR MIN DA LITTAFI DAN ALLAH🙏🏻😭😭😭 Especially ku ƴan SPG na roƙeku da Allah🙏🏻😭😭
Da sauri ta gimtse dariyarta, cikin sanyi da tsoro ganinshi tamkar gilmawar walƙiya sai gashi a gabansu.
Wani irin azabebben tsorone ya rufe Salmanu amman sai ya dake, cikin ƙarfin hali da kalato jarumta ya kame jikinshi dake rawa.
Cikin ɗan rawan murya yace.
"Me haka, zuwa babu sallama?".
Wani mugun kallo ya watsa mishi tare da cewa.
"Kiyaye bakinka idan maza suna wuri."
Cikin dakiya Salmanu yace.
"Ina mazan!? Ai ni banga wani na miji a nanba sai mata maza. Ai namiji shi zai iya sa namiji ɗan uwanshi zubda hawaye ko tsuma da faɗuwa, a dai yanzu ai babu wani namiji a Rugar Bani da kewaye sama da Jarumin da bulalar SHAƊI bata sashi zubda hawaye ba Sheykh nake nufi".
Wani irin zabura Ba'ana yayi ya nufi kansa alamun zai shaƙeshi.
Da sauri ya tsaya jin Shatu ta saki ihu tare da cewa.
"Bana so ya Ba'ana in dai kana son farin ciki na, to kada ka dakeshi ko ka cutar dashi da komai".
Wani irin kallo ya mata mai cike da tuhuma da razana da kuma karaya,
Ita kuwa Shatu cikin rawan murya tace.
"Ya Salmanu ka tafi, bana so kaje ka bar koya min komai".
Cikin sauƙe ajiyan zuciya na tsoro.
Salmanu ya juya ya tafi.
Shi kuwa Ba'ana, zama yayi inda Salmanu ya tashi, cikin taraddadin ko dai Shatu bata sonshi ne, ya nuna mata gefenshi.
A hankali ta zauna, shiru tayi tana sauƙe shessheƙan kuka.
Cikin ƙuna da baƙin cikin rashin sa wancan ɗan birni mai fata kamar ta jariri kukanne ya sakar mishi fargaba,
cikin sanyi yace.
"Mata!".
Bata kalleshi ba kuma bata dena shessheƙan ba.
Kiranta ya kuma yi a karo na uku.
"Mata!".
Cikin disashewar muryar tace.
"Na'am".
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau a hankali yace.
"Mata bakya so nane!?".
A bazata tambayarshi tazo mata,
ta ina kuma ta yaya zatace mishi bata sonshi, bayan tasan abin da yayi mata shekarun baya, dama fansar shi ta soshine kuma ta aureshi, da wanne bakin zatace mishi bata sonshi.
wasu zafafan hawaye masu ɗumi ta zubda.
Haƙiƙa ya Ba'ana mugune amman a iya saninta a kanta ya zama mugun, tunda sai wanda ya nuna baya sonta dashine yakewa mugunta,
Babbar matsalarshi mushirkine kuma baya salla.
Cikin rawan murya da kuka tace.
"A a Ya Ba'ana Ni bance bana sonka ba".
Da sauri yace.
"Uhhmmm to meyasa bakya ganin laifin Salmanu akan duk abinda yake min, ko dai shi kikeso ne Mata!?".
Da sauri ta jujjuya mishi kai sabida sanin ko jinkirin bashi amsa tayi zai iya yiwa Salmanu illa.
Cikin rawan murya tace.
"Bana son ka cutar da shine sabida, shi ya janye batun soyayyarsa gareni. Ka kuma sani karatu yake koya min amatsayinshi na wanda ya samu karantarwa a wata jami'a,
Yana sona da al'khairi kai kuma kana ƙinshi, ko dai ka manta ka ce min zaka so duk wanda yake sona da al'khairi yake kuma taimaka min".
Jiki a mace ya gyaɗa mata kai,
sai kuma ya rumtse idanunshi da yakejin suna cikowa da hawaye yace.
"Lokuta da dama sai inga kamar bakya farin cikin ganina, a madadin farin ciki sai inga tsorona cikin ƙwayar idonki."
Juyowa tayi gareshi da kyau cikin kuka tace.
"Ba kai ke bani tsoroba, abinda kakeyi ne yake sani tsoronka, ya Ba'ana ka bar wannan asirce-asircen babu kyau shirka ne, wanda yake ɗaya daga cikin manyan zunuban da Ubangiji ya haramtawa mumini yin tsafi haramun ne".
Kanshi ya jingina da jikin gini yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta,
A hankali ya fara mgna cikin muryar da bata taɓa jin rauninta a muryarsa ba yace.
"Mata ina sonki, wallahi Allah kenan rantsuwar musulmai, ina sonki, son da ni kaina bansan adadinshi ba,
Duk abinda nakeyi a kanki nefa, Shatu ki min uzuri, na roƙeki kiyi min ɗa'ar riƙe tukuicin abinda nai miki a baya,
Ki soni koda rabin yadda nake sonki ne.
Kiji tausayina Shatu ina jin tsoron kada ƙaddara ta rabamu,".
Kekkyawar fuskarshi ta zubawa ido, tana gani. Irin kyan da Allah yayi mishi sai dai sam babu kyan hali ya zama kyan ɗan maciji.
Cikin sanyi tace.
"Ya Ba'ana tsoro kuma?".
Kai ya gyaɗa mata cikin sanyi yace.
"Eh sabida muddin aka rabamu, zan zamewa fulani babban ƙalubale a rayuwarsa, kuma duk wanda yayi sanadin rabuwata da ke, wallahi zaiga toskun rayuwar duniya, zaiyi dana sani, zan zama mugun zahiri. Na san ke Kum bakya son hakan.
Yau kuma fargaba na, yafi na baya yawaita da wannan jikan sarki ya iya daurewa azabar bulalina baiyi ƙollaba."
Wani irin ajiyan zuciya taja tare da cewa.
"Babu komai ya Ba'ana Ni dai ina tayi mana addu'an ALLAH yayi mana zaɓi mafi al'khairi a rayuwata, ya kuma shige min gaba a dukkan motsina".
Ido ya zuba mata babu ko ƙebtawa, cikin sanyi yace.
"Nine mafa al'khairinki Mata".
Da sauri tace.
"Baka saniba".
A zafafe yace.
"Na sani mana".
Cikin tsoro tace.
"Kai masanin gaibu ne kenan?".
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
"Ehh kusan haka tunda nayi duba a kanki".
A hankali tace.
"Wa'iyazubillah. Duba ba gsky bane, zai iya maka ƙarya".
Hannu ya ɗaga mata da sauri kana ya nuna mata hanyar shiga gida.
A hankali ta tashi tsaye cikin sanyi tace.
"Allah ya baka haƙuri ya shiryeka".
Ta ƙarishe mgnar tana ƙoƙarin yin kuka.
Da sauri ya juyo cikin sanyi yace.
"Kada kiyi kukan mata, nayi haƙuri.
yanzu na fasa jiran Sai kin gama karatu ayi mana aure.
Duk randa wancan malamin ya dawo ya rama gasar Shaɗinsa. Za'a ɗaura auren mu a ranar, domin
Koda duk bulalin duniyar nan zai zabgeni dasu wlh bazaici nasara a kainaba domin idona ba idon da zai zubda hawaye a kanki bane bilali ɗaya nake tsoro kuma babu wanda yasan inda suke.
In kuwa aka samu wani akasin dama bazai samuba, to zan bar ƙasar nan zan koma ƙasar Cameroon can babban birnin Yahunde, inbi cikin Rugar wasu fulanin.
Sai dai ko bana nan duk wanda ya aureki ya auri ajalinsa."
Bata iya tanka mishiba, a haka ya juya ya tafi.
Kana ita kuma ta koma cikin gida.
A cikin masarautar Joɗa kuwa.
Sai da akayi sallan isha kafin.
Su Haroon suka dawo gida.
Suna tafe,
Abba da Lamiɗo da Galadima, da Dr Aliyu da kuma Sarkin Shaɗi.
Suna biye dasu a baya.
Kai tsaye wucewa sukayi har bedroom ɗin Jabeer har yanzu bacci yakeyi.
Sai dai tunda lokacin salla yayi yaketa jin baccin ba daɗi sai dai kuma Allah bai bashi ikon farkawa ba.
Dubashi sukayi tare da ƙara shafa mishi wasu magunguna kana suka fita suka tafi.
Hakama Gimbiya Aminatu tazo itama har ɗaki sai dai samunshi yana bacci yasa ta tafi.
Bayan fitanta ba daɗe Barrister Kamal da ɗan sa Sulaiman sukazo.
Suma har ciki suka shiga suka dubashi.
Kana suka tafi.
A ranan a daren gaba ɗaya mutanen masarautar kowa yaji lbrin abinda ya faru.
A falon su Jafar duk sukaci abinci.
Ganin dare ya tsalane yasa Juwairiyya jan hannun Jafar suka tafi.
Jalal, Jamil, Ya Hashim kuma sukayi musu saida safe kowa ya tafi side ɗin shi.
Jakadiyarsu kuwa