Showing 282001 words to 285000 words out of 299804 words

Chapter 95 - GARKUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

17 Jul 2024

116744

igiyoyin dake sarkafe gaban rigarta murya can ƙasa yace.
"Al'adar wai in mace ta haihu sai ta kwana arba'in kafin ta bari mijinta ya kusanceta.
Kullum a wahale nake kwana ke ko a jikinki kina sane dai al'adace ba addiniba amman kikayi tauye min haƙƙina".
Da sauri tace.
"Toh ai hakanma Al'adar masarautar Joɗa ne ni yamin ka sani ma".
Ta ƙare mgnar cikin gimtse dariyarta na ƙaryar da tayi na wai Al'adar masarautar Joɗa sai bayan arba'in za'a koma turaka, tayi ƙaryar ne kuma sabida ta samu ta ƙara cusa mishi tsanar al'adun da son kaudasu.
Ai kuwa cikin kwaffa yace.
"Zancen banza, ai wannan aikin jahilci ne ya za'ayi nida matata kuma ace sai wata Al'adar masarautar Joɗa ta bani izini da damar kusantarta".
Murmushi mai cike da ƙauna tayi tare da cewa.
"Toh ai shine muke fatan ka mulkemu ka kauda ire-iren waɗannan abubuwan".
Tayi mgn tana kai bakinta gareshi.
Wani irin dogon numfashi yaja tare dasa hannun duka biyu ya tallabe kanta.
Tare da fidda sautin.
"Shiyyyyyy Ahhhh Aishh".
Sosai ta gigitashi da salon da tasan yana masifar so.
Saida taga ya gama narkewa ta ɗan janye kanta kana ta ruggume shi a hankali ta kai bakinta kusa da kunnenshi murya can ƙasa tace.
"Yah Sheykh ka mulki masarautar Joɗa dan Allah da manzonsa dan son samar da gyara".
Cikin yanayin da bai san hali da duniyar da yake cikiba yace.
"Tohhhhh Aish".
Da sauri tace.
"Kayi al'khairi".
Jikinshi da muryarsa kab na rawa yace.
"Nayi al'ƙawarin".
Ai kuwa sai ta mirgina ta jikinshi da kyau.
Bayan ta cire rigarta.

Wani ɗan raunataccen ƙara ta saki sabida.
Zafin da taji yayin ziyartarsa wanda dole ta janye ta kwanta tare da cewa.
"Bazan iyaba".
Jikinshi na rawa yayi mata rumfa.
Da ƙarfi ta ɗan saki ƙara sabida ji tayi kamar yau ta taɓa sanin namiji dan gyaran da Ummi da Mamey da Umaymah sukayi mata ya haɗawa.
Hannunta ta ɗan yarfa cikin raki tace.
"Wash Honey".
Cikin yanayin shiga duniyar maji daɗi Yah Sheykh ya rinƙa sanya mata al'barka".
Cikin nitsuwa cikin sararin samaniya murya a narke tace.
"Yah Sheykh zaka mulki masarautar Joɗa ko".
Da sauri yace.
"Eh eh ehhhhhhhhhhhhhh Aishhhhh".
Sabida yana gab da jin numfashin sa na shirin ɗaukewa in bai buɗe bakinshi ba...

Bayan komai ya lafane sunyi wonka sun dawo suna konce.
Ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da shafa maransa kana a hankali yace.
"Alhamdulillah naji sakayau".
Sai kuma ya kai hannunshi bisa cikinta tare da cewa.
"Allah yasa ƙanwa ko ƙanin Afreen ya kasantu".
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Ai ni dai tunda ka yarda zaka mulki masarautar Joɗa ko duk shekara zan haihu ba matsala".
Da sauri yace.
"Toh yaushe kuma mukayi haka dake?".
Cikin kwaɓe fuska tace.
"Yanzu mana".
Juya mata baya yayi yana gyarawa Afreen kwanciya yace.
"Uhumm to ke waya ce miki al'ƙawarin a irin wannan lokaci yana aiki, ai ko al'ƙalai basa amsar shaida da al'ƙawarin mai fataucin kayan daɗi".
Da sauri tace.
"Yah Sheykh al'ƙawarin fa kayi".
Jawota jikinshi yayi tare da cewa.
"Kai sake wannan al'ƙawarin Aish, yoh ai sai ince miki na baki Makka da madina ma a cikin wannan yanayin ke baki san Y.M.D.G. bane".
Dariyar da take dannewa ne ta kubce mata.
Haka yasa ya lakace hancinta tare da cewa.
"Ja'ira wato dariya ma zakiyi min".
A haka dai sukayi bacci liƙe da juna.

Washe gari da asuba suna dawowa masallacin.
Abbanshi yake ce mishi.
Wai yayi maza fa ya fito su tafi shi ɗaya ake jira.

Sosai yayi mamakin ashe dama da gaske Lamiɗo yake yau zaiyi tafiyar.

Bisa dole bisa umarnin iyayenshi ya fito suka tafi.
Shatu nata bashi baki.
Ta kaicinsa ɗaya da aka hanashi tafiya da ita.


Alhamdulillah yayi tafiyar kai takardun murabus ɗin da Lamiɗo zaiyi ya bashi mulki ga masarautun gargajiya na Arewacin Nigeria.
Gaba ɗaya sunyi na'am da haka sun sa hannun.
Duk da shi baima san takardun me bane dan bai buɗeba.

Randa ya isa masarautar su Umaymah kuwa daɗi kamar zai kasheta.

Kwanashi goma ya gama zagaye kab masarautun ya dawo dasa hannun da buga hatimin dukkan masarautun.

Koda ya dawo da Lamiɗo ya gani saida yayi ƙwalla sabida zallan farin cikin ganin yadda ya samu haɗin kan kab masarautu har aka ƙara da yabawa sarki maijiran gadon.

Shida Shatun kuwa a ranar suka tabbatarwa juna.
Sunyi bege da kewar juna.

Kasan cewar ranar Al'hamis ya dawo.
Tun a daren Shatu ke ta masa batun.
Zuwa Rugar Bani.
Toh yace dai ba matsala ran asabar zai kaita.
Mamey ma da Ummi dasu Jalal duk sunce zasu je.


Ba'ana kuwa zuwa yanzu gaba ɗaya.
Ya zama wani irin al'ummar Rugar Bani kuwa sun cika da mamakin ganin yadda ya sauya jami'in salla baya wuceshi yayi sanyi ya sauya kamar ba shiba abu kaɗan sai hawaye.

Yauma kamar kullum yaje ya samu Bappa a garkensa bayan ya gama magiyar a bashi Shatunsa Bappa ya babbashi haƙuri.

Sai kawai ya jingina kanshi da jikin itacen nim dake gefenshi.
Murya na rawa yace.
"Zan sake barin Nigeria'n kuma tabbas da Shatu da duk dabbobinmu Rugar Bani zanyi awon gaba dasu muddin baku dawo min da ita cikin lumana ba."
Ya ƙarashe mgnar cikin alamun wai baraza zai mishi.
Ganin yadda Bappa ya zuba mishi idone yasa yaci gaba da cewa.
"Wlh Bappa mutuwa ce kaɗai zata rabani da Mata in haƙura, bayan mutuwa babu abinda zai rabani da ita na barshi.
Tabbas zan saceta.
Sabida itace cikon farin cikina Mata ce burin duniyata".
Ya ƙare mgnar hawaye na zuba.

Kai Sheykh ya jinjina tare da cewa.
"Uhumm da kuma ita zanyi maka tarko ka shiga hannun hukuma ba taƙadiri".

Shi kuwa Bappa da Baroon shiru sukayi suna jin yadda sautin kukansa ke tashi.

Washe gari ranar asabar.
Misalin ƙarfe goma na safe.

Tsaye suke gaba ɗayansu cikin shiga ta al'farma.
Jalal da abokanshi sojoji mutun huɗu su motarsu da ban.

Yah Sheykh kuwa shi yake jan motar da kanshi
Shatu na gefenshi Ummi da Mamey na baya.
Saratu kuwa tana motar Aunty Juwairiyya da Yan Jafar da yaransu.

Jamil da Affan kuwa motarsu ɗaya a haka suka nufi Rugar Bani.

Ƙarfe sha ɗaya dai-dai na safe tayi musu cikin Rugar Bani.

Cikin wani irin masifeffen zabura Ba'ana ya tashi zaune.

By
*GARKUWAR FULANI*


👆🏻

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
GARKUWA
Page 11


Tare da kallon zoben azurfan dake yatsarsa wacce irinta ya sawa Shatu a yatsarta wanda in suna kusa da juna zasuyi ta yin haske.

Wani irin dariya mai cike da jin daɗi yayi tare da cewa.
"Mata". Ya faɗi yana mai miƙewa tsaye ya nufi ƙofar gida.

Su Sheykh kuwa a hankali sukayi parking cikin nitsuwa suka fara fitowa.
Ummi na Ruggume da Afreen yar wata biyu tayi kuɓul-kuɓul da ita gwanin burgewa da sha'awa gashin kanta yana kwance lib-lib kamar ɗiyar larabawa.
Wasu irin tattausan kayane masu masifar kyau da taushi da tsada aka kimtsata a ciki rigar mai ɗan karen kyau.
Yellow and Pink color masu taushi sai ɗan banɗanan nashi mai kyau da akasa mata a kanta yayi cib dashi.
Sai Safar kafarta yellow sai takalmanta pink.
Kana towel din da aka ninketa ciki shima pink color.
Sai wani irin fitinenne ƙamshi mai daɗin shaƙa da takeyi.

A hankali suka fito baki ɗayansu.
Ajiyan zuciya Mamey da Shatu suka sauƙe tare da shaƙan daddaɗan iskan Rugar tasu.
Kowa ya bar gida tabbas gida ya barshi.

Da sauri Ummi da Aunty Juwairiyya da Sara suka matsosu.
Mamey ce a gaba duk suna biye da ita a baya.
Sheykh kuwa shine a gaba Yah Jafar da Affan dasu Jamil na biye dasu.

A cikin gidan kuwa, Junainah ce riƙe da hannun Yah Giɗi tana ɗan tsalle-tsalle tare da cewa.
"Yauwa Ya Giɗi muje lambu ka ciro min inabi mana".
Gyara riƙon da yayiwa hannunta yayi tare da cewa.
"Ba Junaidu ya kawo miki wani ba ɗazu".
Da sauri tace.
"A a ai na ajiyewa su Adda Shatu da Ummey na shi.
In sun iso zan basu".
Juyowa yayi ya ɗan kalleta tare da cewa.
"Toh ai kije kawai kici abunki, su tun jiya da yamma bappa yasa na ciro musu komai".

Dai-dai lokacin kuma suka iso ƙofar gida.
Da sauri Junainah ta saki yatsarsa tare da cewa.
"Oyoyo Ummey na Adda Shatu na".
Tayi mgnar tana nufar inda suke a guje.
Da sauri Shatu ta buɗe mata hannu ta faɗa jikinta.
Ruggume juna sukayi suna dariya.
Giɗi kuwa da sauri yace.
"Kai maraba lale sannunku da zuwa".
Ya ƙare mgnar yana isa gabansu Sheykh.

Da sauri Bappa ya fito jin muryar Junainah na cewa.
"Oyoyo Ummey na".
Ai kuwa a cikin zauren yayi kiciɓis dasu Ummey cikin jin daɗi yace su isa.

Kana ya wuce wurinsu Sheykh yayi musu jagora har barandar ƙofar ɗakin shi.

Shatu kuwa kai tsaye ɗakin Ummey ta buɗe musu suka shiga.
Inna Amarya kuwa daɗi kamar ta haɗiye haƙorinta Allah ya sani sun shaƙu da Ummey tayi kewarta ainun.

Bayan sun zauna ne ta kalli Shatu tare da cewa.
"Shatu taso kizo ki kaiwa su Sheykh ruwa".
Da sauri tace.
"Toh Inna Amarya".
Kana tabi bayanta.

Tiren saƙar kabar dake cike da fruits danginsu Ayaba, inabi, tupa, yazawa, goiba, mangoro, danino, masu masifar sanyi kasan cewar cikin tulu suka kwana.
Sai kuma ƙwaryar damemmen fura da nono da zuma.
Da fefeyin kayan ya'yan itatuwa ta rufe ƙwaryar kana ta ɗauki kananan ƙore da ludayayeyin suma masu kyau, ta riƙe, kana ta miƙe ta nufi ƙofar Bappa.

Ita kuwa Inna Amarya ta ɗauki sauran ta nufi cikin ɗakin Ummey dashi.

A hankali ta ratsa gefen Sheykh ta ajiye kwaryar a tsakiyar su.
Kana a hankali tace.
"Bismillah ga ruwa".
Murmushi mai yelwa Sheykh yayi tare da cewa.
"Mun gode".
Jalal kuwa hannunshi yasa ya ɗan tsinko gefen nonon inabi kana ya fara kaiwa bakinshi yana tsinka.
Ido ya lumshe tare da cewa.
"Wai ni kam Adda Shatu kuna da Fridge ne a garin nan".
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Bappa kuwa miƙewa yayi ya fita yana cewa.
"Toh bari inje nan kusa kafin kusha ruwa".
To sukace sanin bazai zauna ba.

Ita kuwa Shatu ruwa ta koma ta kawo musu cikin kwanon sha na asalin gargajiya.

Ajiyewa tayi tana kallon Affan da yake lumshe ido yana shan kindirmon.
Jamil kuwa Ayaba yakeci.
Yah Jafar ma nonon yake Sha.
Shi kuwa Sheykh dabinon yake ci.
A hankali ya kalleta tare da cewa.
"Ni zan sha nonon amman zumar bata ji minba a ƙaro min".
Da sauri tace to tare da miƙewa a nitse ta shiga cikin ɗakin Bappa.

Ido ya ɗan zuba mata lokacin data fito riƙe da akoshi ta ajiye a gabanshi tana buɗe wa.
Da sauri ya ɗan jawo akoshin ganin asalin farar zuma da sakarta, yatsarsa yasa ya laso yasa a baki.
Girarshi ɗaya ya ɗan ɗaga mata tare da cewa.
"Kefa baƙuwa ce, zaki shige musu har ɗaki".
Da sauri tace.
"Tab baƙuwa kuma ni da gidanmu".
Yana mai lasan zumar yace.
"Gidanku na can masarautar Joɗa".
Murmushi tayi kana ta miƙa ta koma wurin su Ummey.

Sosai suka sake anata hira da dariya ga sanyin safiya.
Ga yanayin garin ga farin ciki.

Junainah kuwa tana ruggume da Afreen tanata kiciniya da ita.

Ganin Inna Amarya ta koma Kitchen yasa Shatu Binta a baya.
"Inna Amarya me kike dafa mana ne?".
Juyowa tayi tana kallonta bayan ta sauƙe tukunyar kana tace.
"Tuwone miyar kase da man shanu.
Sai Danderun Zabbi".
Da sauri ta matso tare da cewa.
"Kai Inna Amarya kin biyani dama na dade banci miyar Kase ba".
Gefenta ta zauna tare da jawo akoshin dake gefenta babba da karami.
Danderun ne a ciki sai tururi da ƙamshin yake zubawa.
Da sauri ta rufe.
Kana ta buɗe manyan da sukafi wannan tuwon ɗanyar shinkafane anyi mata asalin kwasan gargajiya an lailaye samanshi da man shanu.
Rufewa tayi.
Tana kallon Inna Amarya data buɗe tukunyar miyar data sauke.
Murmushi tayi tare da cewa.
"Wannan miyar harda ta gobena".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Toh Shatu yanzu dauki tuwon da Danderun ki kai musu sai kizo ki kai musu miyar.
Da sauri tace to.
Ta ɗauka ta kai musu.
Ta dawo ta kai nasu Ummey kana tazo.
Ta zauna tana kallon yadda take zuba miyar.
Ƙwaryar dake gefenta ta buɗe.
Nanma tuwon ne da alamun na su Yah Giɗi ne.
Gefe kuma kwanukan Bappa ne.

Motsowa tayi tana cewa.
"Inna Amarya su Ummey duk basu wani damu da nama, Amman waɗan can kuraye ne.
Irin Jalal da Yayanshi sunfi son duk loma su tsakura da nama".
Dariya Inna Amarya tayi tare da cewa.
"Yoh kice irin Giɗi ne su".
Dariya tayi da sauri ta juyo jin Yah Giɗin nata dake Ruggume da Afreen yana cewa.
"Toh in banda irin Shatu wa zaiƙi nama, ko sunanshi mafa yana da daɗin ji".
Murmushi tayi tuno lokacin da ya dirka mata dundu a tsakiyar bayanta sabida ta hana a yanka tsuntsuwar Boleru wacce da Ummey aka yanka".
Ita kam inna Amarya naman ta kara musu.
Ita ta dauki nasu Ummey ta kai musu.

Ita kuwa Shatu ta kaiwa su Sheykh.
Murmushi tayi ganin tuni Jalal ya buɗe akoshin Danderun.
Yana ganinta yace.
"Yauwa Adda Shatu a kawo mana tray'n mana ko plate".
To tace.
Kana taje ta kawo musu tirurruka guda biyu.

Ajiyan zuciya Sheykh ya sauke tare da cewa.
"Wai anya kuwa kunci abincin safe?".
Da sauri Affan yace.
"Bamu ciba".
Murmushi Yah Jafar yayi tare da cewa.
"Koma dai munci ai yanzu hantsi ya duba ludeyi.
Dan haka Affan sa mana".
Allah sarki rayuwa mai daɗi ba girman kai.
Shatu ta raya a ranta.
Shi kuwa Sheykh dariya yayi.

Shi kuwa Affan ludeyin duma yasa ya zuba musu tuƙeƙƙen tuwon nan.
Kana ya zuba musu miyar kasen da yaji nama da kifi banda a saman tuwon.
Jalal kuwa ƙara min tray'n ya jawo.
Danderun ya juye a ciki fiye da rabi.
Ita kam Shatu juyawa tayi ta tafi.

Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Affan, Jamil, Yah Jafar.
Sun haɗa hannu cikin kono ɗaya suna cin abinci cike da gamsuwa da shaƙuwa da ƙaunar juna.

Haka nan yaji wani irin daɗi.
Jalal ne ya ɗan matso gabanshi da tray'n tare da cewa.
"Ni dai Allah ya sani ba cin tuwo zanyiba, Hamma Jabeer muci Danderun".
Jamil ne ya ɗan kalleshi tare da cewa.
"Manyan kuraye ba".
Eh ɗin Jalal yace kana sukaci gaba da ci suna hira.

Ita kuwa Shatu bakin kitchin ɗin ta koma.
Gefen Yah Giɗi ta zauna.

Tare da sa hannunta cikin akoshin abincin da yake cin.
Kana ta kalli Junainah dake gefenshi riƙe da Afreen tace.
"Junnu kaita wurin Ummi kizo muci mana".
Kai ta jujjuya tare da cewa.
"Ni na koshi naci da Ummey na a ɗaki".
A hankali ta ɗan juyo ta kalli ƙofar ɗakin Bappa jin Sheykh yayi gyaran murya.
Ido ya juya mata, alamun me takeyi.
Cikin jin daɗin yanayin tace.
"Ina cin abinci da Yah Giɗi na".
Murmushi yayi tare da juya kai.

Shi kuwa Yah Giɗi dama ya kaiwa abokan Jalal dake can ƙofar gida zaune kan taburma a gindin bishiya.
Suma sunci.

Haka dai sukaci suka sha sukayi haniƙan.
Kana Shatu ta tattare komai ita da Junainah.

Bayan sun gama ne Bappa ya dawo nan suka sake sabuwar gaisuwa kana suka ci gaba da hira.
Sannan sukaje sukayi sallan azahar a masallacin ƙofar gidan Arɗo Bani.
Kana suka dawo sukaci gaba da hira.

Shi kuwa Ba'ana yana fita.
Ya kalli Babanshi cikin zaƙuwa yace.
"Baba Mata tana Rugar Bani tabbas tazo".
Da sauri Bukar yace.
"A a Ba'ana banji lbrin ba".
Da sauri yace.
"Ga nan zobe na yana gaya min kana cemin a a".
Sai kuma kawai ya juya ya nufi.
Bakin garin inda yasan zai samu Baroon yana zuwa yace.
"Baroon taso muje gidan malam liman indan mun isa ni zan zagaya ta baya kai kuma ka shiga ta ƙofar gida.
Ina da tabbacin yau Mata
na nan kuma yau zan tafi da ita.
Yanzu bari in kira su Droo baki ɗayansu."
Da sauri Baroon yace to.
Kana sukayi maza suka nufi cikin garin.

Shi kuwa Ba'ana ya kira duk sauran yaranshi suka biyo bayanshi.
Ta bayan gidan suka zagaya.
Shi kuwa Baroon ya shiga cikin gidan kai tsaye sabida sanin Sheykh na ciki kuma zaije ya bashi bayani ne.

Yana shiga kuwa Sheykh ya yafi toshi da hannu da sauri ya iso.
Bappa kam ido ya zuba musu jin Baroon nayiwa Sheykh duk bayanin abinda Ba'ana yake shiryawa.
Murmushi Sheykh yayi tare da cewa.
"Yanzu yana bayan gidan nan kenan?".
Da sauri yace.
"Eh dashi da sauran yaran".

Da sauri Sheykh ya kalli Jalal tare da cewa.
"Ka gayawa su Khalid su kula da duk wani dake jikin gidan".
To yace kana ya kira su ya sanar musu.
Nan take kuwa suka miƙe suka fara ɗan zirya

Ajiyan zuciya mai nauyi Bappa ya sauke lokacin da Sheykh yayi mishi duk bayanin abinda ke faruwa.
Ya ƙara da cewa.
"Idan ban kamashi ba bazai daina bibiyar rayuwar Shatu ba, kuma zai iya ci gaba da yiwa mutane illa in ya rasata".
Cikin sanyin jiki Bappa yace.
"Hakane".

Dai-dai lokacin ita kuma Shatu ta fito cikin ɗakin.

Randunansu ta nufa.
Dai-dai lokacin kuma Ba'ana yana ta wurin ta bayan danga.
Tasa hannu zata ɗebo ruwa kenan taga zoben yatsarta ya kawo wani haske.
Da sauri ta miƙe tsaye.
Jin muryar Ba'ana cikin raɗa da leƙota ta tsakankanin karan da akayiwa danga a madadin katanka.
Da sauri ta dafe ƙahon zuciyarta jin muryarshi ras cikin kunneta murya cike da rauni yace.
"Mata! Mata!! Mata!!!".
Ta sani duk duniya mutum ɗaya rak ke kiranta da wannan sunan.
Murya na rawa tace.
"Yah Ba'ana".
Cikin rauni yace.
"Mata ina kika shiga kika mance dani.
Mata kika barni cikin ƙunci da ciwon rai da zuciya na rashin ki Mata wlh zan iya jure komai amman bazan iya jure rashin kiba".
Kar-kar haka jikinta ya fara rawa.
Da sauri ta juya, da nufin zata koma ɗakin Ummey sai kuma ta tsaya tare da rumtse idanunta da ƙarfi.
Ganinshi ya ɓace ɓat ya dawo gabanta.
Cikin rauni yace.
"Ina zakije? Tafiya zakiyi ki barni!".
Ya ƙare mgnar da rauni yana kuma ƙoƙarin kai hannunshi zai kamo nata.
Cikin tsananin ruɗani tace.
"A a, Yah Ba'ana kada ka taɓani ni matar aurece".
Sai kuma ta kauce.
Da sauri shima ya kauce ya bita.

Cikin tsoro tace.
"Dan Allah Yah Ba'ana ka bar fito min".

Da sauri Sheykh ya miƙe tsaye cikin tsananin tashin hankali jin furucin da Shatu keyi tare kuma da kakkaucewan da takeyi alamun ana binta.


Su Jalal ma kab miƙewa tsaye sukayi.

Shi kuwa Sheykh da sauri ya nufi inda take.
Dai-dai lokacin su Ummey ma kab Suka fito sabida karan da Shatu tasa.
Sabida riƙo hannunta da Ba'ana yayi ya fara ja.
A zahiri ita kaɗai ake gani amman a badini shike janta.
Cikin rawan jiki ta tashin hankali tace.
"Bappa Yah Ba'ana ne yake jana wai zai tafi dani.
Yah Sheykh zai tafi dani".
Ta ƙare mgnar da ƙarfi da kuma sakin kuka.

Shi kuwa Ba'ana shima kukan yakeyi cikin rauni da tsananin so yake cewa.
"Mata yanzu wani kike cewa yazo ya ceceki ya rabaki dani.
Shin bakya so nane?".

Dai-dai lokacin kuma Jalal ya iso gab da ita.
Da sauri duk suka buɗe baki tare kallon yadda Jalal yayi sama ya faɗi ƙasa tib sabida wani irin azabebben naushi da Ba'ana ya kima mishi.
Wanda su ba ganinshi sukeyi ba.
Cikin wani irin tafasan zuciya irin na sojojin Jalal ya miƙe tsaye tare da nufosu.
Jin Shatu na cewa.
"No Jalal kada ka iso zai illa taka".
Ina bai kulaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login