Showing 291001 words to 294000 words out of 299804 words

Chapter 98 - GARKUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

17 Jul 2024

111390

sun fitone.
Ya kalleta da kyau ganin yadda ta lafe ta kwanta lib, da’alama ta ɗan gaji ne.
Murmushi yayi sannan ya fice daga cikin dakin, Dinning area yaje.
Tea mai kwauri ya haɗa da zafi ya cika ɗan babban kofi kana ya dowa daƙin.

Hannunshi ya miƙa mata, ganin haka yasa ta kama hannun,
Ɗagota yayi ta zauna, kana shi kuma ya zauna agefenta.
Cup ɗin tea din ya kai bakinta.
Babu musu kuwa ta buɗe bakin sabida wani irin masifeffen yunwa da takeji, shikansa yasan dole ne ma,
taji yunwa, sabida yanda yayi heaven sex da ita yau din, is so special.

Tasha tea din sosai, saida ta kusan shanyewa ne kuma ta janye kanta ahankali, tare dayin gyatsa asanyaye tace.
"Alhamdulillah".
Hannunshi yasa bisa cikinta a hankali ya shafa cikin kula yace.
"Shanye shi ko mangana".
Ya ƙare maganar yana sa mata cup ɗin tea din abaki.
Shanyewa tayi kana ya aje cup ɗin bisa bedside.

Sannan yazo ya kwanta ya jawota jikinshi.

Washe gari ranar Monday kotu ta yanke wa Ba'ana hukuncin kisa ta Hanyar rataya.
Sabida hujja da shaidar daya bayar a kan kanshi.
Kana yayi bayanin duk shanayen da yake sacewa daga wannan ƙasar zuwa waccar ƙasar.
Ya bada tabbacin duk suna nan.
Ya kuma sa yaranshi sun medawa kowa nashi.
Domin suma sun musulunta.

Bayan kwana biyu aka shirya rataye shi.

Bayan anyi komai an fito da shine.
Ya kalli taron fulanin Rugar Bani.
Cikin zubda hawaye yace.
"Dan Allah ku yafe min".
Wani irin raunine ya rufesu mai sa zubda hawaye.
Kusan a tare sukace sun yafe mishi.
Cikin sanyi yace.
"Ngd". kana ya juyo ya kalli Sheykh dake gefensa, murya na rawa yace.

“Ga dai ƙarshena ni kam, Allah bai nufa zan rayu da Shatu ba.
Allah ya ƙaddara matarka ce.
Dan Allah ka kula da ita Shatu mace mai rauni da tausayi."
Cikin zubda hawaye Sheykh yace.
"In sha Allah".
Sai kuma ya kalli Bugulu cikin rauni yace.
"Mama kin tuna kin min al'ƙawarin zaki musulunta kuma zaki bar sata".
Cikin kuka tace.
"Nayi al'ƙawari".
Da sauri ya kalli Sheykh a hankali yace.
"Dan Allah bawa mahaifiyata ƙalmar shahada, a gaban idona in samu in mutu da farin ciki".
Cikin zubda hawaye Sheykh yace.
"Toh".
A nan ya musuluntar da Bugulu.
Nan aka rataye shi gaba ɗaya mutane na kuka.
Sosai Sheykh da kanshi yayi ta kuka sabida.
Amanar kula da Shatu da Ba'ana ya bashi amana.

Bayan an rataye shi ne.
Droo yayi musu bayanin cewa fa.
Ya musulunta tun da dadewa.
Hakane yasa Sheykh da kansa yayi masa wonka kana ya limanci sallan gawanshi kana aka kaishi gidansa na gsky.

Rayuwa kenan.

Shatu kuwa sai dai ta buya tayi kuka, Ummey da kanta tayi tashan kuka.

Alhamdulillah bayan rasuwarsa da wata ɗaya.
Lamiɗo da kanshi ya shiryawa Sheykh da Shatu da Ummey da Dr Aliyu da Baba Basiru da Galadima su tafi ƙasar Cameroon dan yiwa iyayen Shatu godiya da kuma nemawa Jamil auren Khadijah, dan yana son ranar auren a kuma naɗa Sheykh a matsayin Sarkin Masarautar Joɗa.

Alhamdulillah sun gama shirinsu,

Washe gari zasu tafine.
Batool ta kira Sheykh.

Suna zaune da Shatu kiran ya shigo bayan ya ɗagane ta mishi bayani ta ƙara da cewa.
"Affan ne ya bani number ka.
Alhamdulillah aurena next week Ina gayyatarku ɗaurin aure".
Cikin ɗan sake fuska yace.
"Masha Allah, Allah ya kaimu in Sha Allah zanzo nida Affan".
Cikin jin daɗi tace.
"Toh ngd matuƙa Hamma Jabeer".
Daga nan sukayi sallama.
Da sauri ya sauƙe numfashi ganin Shatu bata kallonshi ma.

Ranar litin da yamma jirginsu ya sauƙa cikin ƙasar Cameroon birnin Yahunde.

Wasu irin motoci masu tsadar gaskene sukazo suka ɗauke su zuwa gidan Abboi.

Suna isa bayan sunyi parking sun firfito gaba dayansu Jamil ne ya ɗan juya....!







By
*GARKUWAR FULANI*
[4/6, 7:36 AM] +234 806 559 0880: *Lamiɗon Adamawa, Dr Aliyu Mustapha jama'ar Adamawa duk suna a gaisheka.😭😭😭 Allah ya jiƙanka da Rahama Lamiɗon Adamawa Dr Aliyu Mustapha. Wannan shafi gaba ɗayan shi sadaukar wane gareka.
Jinjina da godiya ga Sarki mai ci Muhammad Barkinɗon Aliyu Mustapha. Allah ya taya riƙe!.!..




Ya juyo ya kalli Shatu dake sauƙe numfashi tare da yin murmushi mai cike da jin daɗin ganin gida.

Yah Al'ameen ne ya matso gabansu Sheykh da sauri tare da cewa.
"Bismillah mu isa ciki".

“Masha Allah”
Galadima yace tare da bin bayanshi kai tsaye parlon Abboi na musamman suka nufa.
Kana suma saura duk suka bi bayansu.
Shatu da Mamey da Ummi da Sara kuwa cikin gida sukayi.

Tarba mai cike da mutuntaka akayi musu tare da Kekkyawar mu'amala.

Kwana su biyu rak. Suka juyo suka dawo Nigeria, bayan sun gama tsaida batun auren Khadijah da Jamil. Hafsi da Salmanu. Rafi'a da Yah Al'ameen Jalal da Hibba.
Bisa mutuntakan da kimar Lamiɗo da tsarin su, na son a ranar za'a naɗa Sheykh a sarautar Sarki Joɗa, yasa duk aka tsara batun ɗaurin auren a Masarautar Joɗa za'ayi shi.

Sosai angwayen keta rawar ƙafa abun.

Bayan sun dawo da wata biyu.
Sosai Afreen ta girma dan yanzu watanta biyar, in ka ganta kace ƴar wata bakwai ce.
Rarrafenta ya nuna ko ina zataje, tayi kuɓul-ƙubul gwanin burgewa da ban sha'awa.

Kuma yanzu aurensu Jalal saura watanni shida cus da izinin ubangiji.

Yau asabar ne, tun safe Sheykh yana gida.
Kiran sallan azahar ne yasa ya ɗan miƙe zaune bisa kujerar 3 str da yake kwance.
Cikin lumshe ido ya kalli Afreen dake wasanta a tsakiyar falon.
Shatu kuwa nata binta zata kamota, ta tubke mata gashin kanta.

A hankali ta zauna tare da cewa.
"Allah na gaji in biki, nan ki zille can in biki can ki zille nan, na lura sam bakya son a taɓa miki kanki".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Waya sani ko ke ta gado".
Da sauri tace.
"Sai dai in Junainah ta gado".
Miƙewa tsaye yayi yana murmushi.
Sai kuwa yayi sauri ya koma ya zauna Kamar wanda aka ture ya faɗi.

Da sauri ta miƙe tare da matsoshi cikin kula tace.
"Subahanallahi Yah Sheykh lfy kuwa?".
Hannun yasa ya dafe kanshi da kai, tare da rumtse idanunshi.
Da sauri ta zauna ta jawoshi jikinta, kanshi tasa bisa ƙirjinta cikin sanyi murya tace.
"Yah Sheykh baka da lfy ne".
Manna kanshi yayi da ƙirjinta murya can kasa, kana ido a lumshe yace.

“Ba komai fa Aish kontar da hankali ki".
Cikin rau-rau da ido tace.
"Ta yaya zan kwantar da hankalina kuma, in ka tsaya kai ɗaya kana shirin faɗuwa na lura da hakan da daɗewa".
Ajiyan zuciya ya sauƙe kana a hankali yace.
"Lfya ta lau Aish bakiga ma, yadda nake yawan cin abinci ba, bini-bini naci abinci, toh amman kuma wannan karon laulayin da jiri yazo min, musamman in na daɗe a zaune, toh in na tashi tsaye sai inga har duhu yana rufe min ido".
Cike da mamaki tace.
"Laulayi kuma?".
Ta ƙare mgnar cikin zaro ido.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
"Eh mana".
Da sauri tace.
"Waye mai cikin?”
Tashi zaune yayi tare da cewa.
"Kece mai cikin mana nine kuma mai laulayin".
Da sauri tace.
"Na shiga uku Yah Sheykh ciki kuma?nifa tun jinin biƙi ban sake yin jiniba".

Kiss ya sakar mata a goshi kana a hankali yace.
"Toh kafin wani jinin yazone kuma ciki ya shiga".
Cike da al'hini tace.
"Yah Sheykh ban ganeba".
Cikin tsananin jin daɗi yace.
"Allah kuwa Aish kinada ciki, na kimanin watanni uku har ya shiga na huɗu, yana ma gab da fara motsi".

Da sauri ta ɗan ja da baya ɗage rigarta sama kaɗan tayi tare da zubawa cikinta ido, ya ilahi ya mujibadda'awati ta faɗa hawaye na kwaranyo mata murya na rawa tace.
"Innalillahi Dr.
Afreen na da watanta biyar kacal kuma ace ina da ciki, yarinyata zata sha wuya, na shiga uku".
Da sauri ya jawota jikinshi ya ruggumeta tsam cikin kwantar mata da hankali yace.

“Baki shiga uku ba Aish, al'janna zaki shiga da izinin Ubangiji, aihuwa rahamace Shatu, wasu suna nema ido a rufema Allah bai basuba mu kuma ya bamu.
Kuma Alhamdulillah batun Afreen nima da fari hankalina ya tashi so da naga.
Ba abinda nonon yayi mata sai ban damuba, ni yamin ma ko kin sani kawai kina ɓoye min ne, sabida kada in sani in nuna farin cikina har Magauta su gane shiyasa baƙi in gaya miki na gane".
Cikin zubda hawaye tace.

“Yah Sheykh daga haihuwa da kwana arba'in fa kenan na samu ciki".

Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
"Ance miki ni ɗin wasane, bugu ɗaya nakeyi ƙollo ke shiga raga.
Gashi kema ɗin ma zalamemmiyace da an baki saiki karɓa.
Toh mu godewa Allah kinji ko Mar'atussaliha, muyi farin ciki da abinda Allah ya azurtamu dashi, kiyi Sujjadar godiyar Allah kiyi hamdala sai mu roƙi Allah yasa tagwaye ne, ina kina son ƴan biyu?”

Cikin jin sanyi da daɗi tace.
"Uhumm sosai ma kuwa Yah Sheykh".

Kai ya ɗan ronƙofa ya sumbaci lips ɗin ta kana yace.
"Toh Allah ya bamu".
Amin Amin tace.
Kana yaje yayi al'wala ya wuce masallaci.
Ita kuma ta ɗauki Afreen ta wuce da ita.
A falo ta samu Junainah ta miƙa mata ita kana ta wuce.


Bayan kusan wata biyu kenan lokacin cikin ya cika wata biyar.
Sosai ya ɗan fito cas sai kuma tayi yar ƙiba.
Afreen kuwa yanzu tana dafa abu ta miƙe tsaye.

Aurensu Jalal saura wata 4.
Alhamdulillah tana fama da karatunta, kuma wanda yanzu suke shekarar ƙarshe ita da Rafi'a shiyasa ma aka kai bikin da nisa dan Rafi'a ta ida.

Tana ruggume da Afreen ta shiga Part ɗin Mamey, dawowarta daga makaranta kenan.
Da sauri Mamey tasa hannu.
Ta amshe Afreen sai kuma ta kalli Sara dake biye da ita a baya tace.

“A'a Sara ya haka, kin barta da jaka da wannan lukutar ƴar tasu".
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Wlh Mamey Afreen na min son inna a soka asha jinin jikinka, wai sai taƙi Sara ta amsheta dole sai ni zan riƙeta".
Ta ƙare mgnar tana dungure kanta.
Dariya ta karketa kanar tasan abinda akace..ita kuwa Mamey da sauri tace.
"Toh Sara ɗauko mata abinci."

To tace kana taje ta ɗauko mata.
Bayan ta ɗauko ta ɗauki nata ta tafi.
Ita kuwa Mamey serilac ɗin Afreen ta dama kana ta fara bata.
Tana bata tana kallon Shatu.
Sai kuma ta ɗan yi gyaran murya tare da cewa.
"Da sauƙi ma ai duk da wahalan karatun da rainon bai sa kin rameba".

Kanta ta ɗan sunkuyar ta kalli cikinta cikin yin ƙasa da murya tace.
"Toh ba cewa yayi wai inada cikiba".

Da sauri Mamey ta danne dariyarta tare da cewa.
"Wai ne ma Shatu? Har yanzu a wai yake?".

Cikin ɗan jin kunya tace.
"Uhum".
Nan dai sukayi ta hira daga bisani ta miƙe ta koma Part ɗin ta.


Alhamdulillah shirye-shiryen aure nata kan-kama.
Tare da shirin naɗin sarauta.
Tako ina tako wani lungun da saƙon masarautun gargajiya na Arewacin Nigeria da kudancin, dama maƙotan mu kamarsu Niger, Cameroon, Chadi. Da dai sauransu duk takardar gayyatar naɗin sarautar sabon sarkin masarautar Joɗa ya riskesu.
Shiri iya shiri akewa bikin da yake haɗe da ɗaurin auren mutane shida.


Cikin Shatu kuwa ya girma ya fito ras, sabida yayi watanni takwas.
Afreen kuwa Alhamdulillah tana gudu ko ina yanzu ga gwarancinta ras.
Watanninta goma sha ɗaya amman in ka ganta zakayi zaton Yar watanni goma sha biyar ne.

Alhamdulillah su Shatu sun kammala karatun su lfy, komai yayi yadda ake buƙata.

Hajia Mama kuwa duniya tayi mata atishawar tsaki.
Sabida kuturta ya kuma shiga yatsunta na tsuntsayen.

A hankali take tafiya Afreen na riƙe da yatsarta.
Tana ta gwaranci.
"Abba! Abba! Abba!".
Murmushi yayi tare da buɗe mata hannunshi da sauri ta tsaki yatsar Shatu ta nufi inda Sheykh ke tsaye, cikin tarin farin ciki yace.
"Oyoyo Mamina".
Kana ya ɗagata sama.
Murmushi Affan yayi tare da cewa.
"Afreen sarkin wayo ita kowa natane".
Jamil ne yace.
"Hmmmm ai ni jiya ta bani mmki.
Wai Ance Abbanmu na kiranta zai bata sweet wai sai tace.
“Bata so Abbanta a kawo mata".
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Kuma daga baya ta bishi da gudu tana Abba cha ciwiut".

Murmushi Sheykh yayi kana ya sauƙeta, tare da kallon Shatu dake zaune ta tasa cikinta gaba.
Cikin wasa ya kalli Jalal daya shigo yanzu yace.
"Jalal ko dai zamu ɗaga bikin kun nanne sai Aish ta haihu zatafi sakewa".

Da sauri ya katse wayar da yakeyi da Hibba tare da cewa.

“A'a me yayi zafi, tasha zamanta a ɗakinta mun hutasshe ta zuwa bikin".

Jamil kuwa kwaɓe fuska yayi tare da cewa.
"Uhumm wai a ɗaga".

Dariya Affan yayi tare da kallon Sheykh dake musu murmushin wasa nan dai sukaci gaba da tattaunawa kan bikin.


Alhamdulillah yau bikinsu Jalal saura mako ɗaya rak.
Komai ya kankama.
Tuni baƙi sun fara cika masarautar Joɗa tako wani yanki.
Hotels din Ɓadamaya Lamiɗo da Sheykh sun kama fiye da rabinsu sabida, sauƙar baƙin da suke tsastsafowa tako wani yanki.

Yau jumma'a wanda ya kama sauran kwana bakwai cin a nawa Sheykh rawani jumma'a mai zuwa kenan.
Wanda ya kama kuma ranar za'a ɗaura aurensu Jalal tuni su Umaymah da tawagarta sun iso.

Tun da safe kuwa yau Shatu ta tashi da ciwon mara, kaɗan-kaɗan.

A haka take ta sabgoginta, sabida tana tare da amare duka uku.

Sha ɗaya dai-dai na safe Allah ya sauƙeta lfy ta haifi ɗanta na miji santalele.

Farincikin a ahlin Sitti ba'a mgn.
Bayan an gama kimtsa mai jego da jaririnta kato fari ƙal dashi.

Suna kwance Sheykh ya shigo.
Cikin tarin farin ciki dan yana gidan Malam Abubakar ne Yah Jafar ya kirashi ya masa al'bishir.

Cikin jin daɗi ya zauna gefen Shatu.
Tare da miƙawa Safiyyah hannu ta miƙa mishi jaririn murya cike da zallan farin ciki yace.
"Alhamdulillah masha Allah. Allah na gode maka, da wannan kyauta da kaimin. Ya Allah kasa baɗi iwar haka mu samu tagwaye".
Dariya sukayi baki ɗayansu ganin yadda Shatu ta zaro idonta cikin alamun tsoron tace.
"Wayyoooooooo Allah na. Yah Sheykh sai kace wata inji".
Aunty Rahma ce tace.
"Ato ai da alamar hakan zakuyi tunda gashi a shekara ɗaya an samo irin tagwayen Nana Faɗima".
Ummi ce dake gefe tana fifitawa Shatu tea tace.

"Ko ƴan ukune Allah ya kawosu akwai masu tayaki rainon su.
Inji gashi yanzu Afreen tunda aka yayate, sai dai tazo ta leƙaki tayi gaba abinta".
Da sauri yace.
"Uhumm yauwa Ummi na gaya mata dai".
Ya ƙare mgnar yana sumbatar goshin yaron cikin tsananin farin cikin da son yaron.
Sai kuma ya kalli Mamey dake shigowa yace.
"Mamey da waye yake kamane?".

Matsowa gabanshi tayi ta kalli fuskar jaririn kana tasa hannunta ta tallabo tashi fuskar.
Cikin jin daɗi tace.
"Da kai yake kama".
Cike da jin daɗi yace.
"Alhamdulillah".

Nanfa akaci gaba da hidima.

Yau kwana biyu da haihuwar Shatu.
Zaune yake agaban Mamey da Abbanshi, kai ya ɗan ɗago ya kalli Abbanshi tare da cewa.
"Ummm Abba nace wanne suna za'a sawa yaron?".
Murmushi mai cike da jin daɗi Abba yayi tare da cewa.
"Na baka zaɓi zaɓawa ɗanka sunan da kafi so".
Murmushi mai cike da jin daɗi yayi tare da cewa.
"Mamey kefa, ko Jadda kikeso inyi mai suna".
Yayi mgnar cikin raha.
Da sauri tace.
"Mutun da ɗan shi mun baka damarka a matsayinka na uba".
Kanshi ya sunkuyar tare da cewa.
"Ngd matuƙa da wannan damar".
Daga nan ya sallamesu ya miƙe ya fita.

Bedroom ɗinsa ya wuce.
Yana shiga ya kira Shatu a waya, ta kawo mishi ɗan.
Yayi mishi huɗu ba.
Ido ta ɗan zuba mishi tare da cewa.
"Me sunanshi?."
Murmushi yayi tare da kashe mata ido a hankali yace.
"Sai ranar suna zakiji".
"Abinma sirrine kenan".
Ta faɗi tana murmushi.
"Ina da wani sirrine bayan ke, Y.M.D.G na".
Ido ta zuba mishi tana mai nazartar baƙaƙen da yake yawan faɗi wasu lokutan.
Kiranshi da akayi a wayane yasa ta bar zancen.

Ranar jumma'a, da safe bayan an fito sallan asabu, aka raɗa sunan yaron kana suka nufi cikin gida kowa na mamakin sunan da Sheykh ya sawa ɗansa.
A tare suka shiga falon shida ƙannensa.

Da sauri Mamma tace.
"Affan me sunan ɗan naku?".
Murmushi Affan yayi tare da nuna Sheykh dake wucewa Side ɗinsa Haroon da Ibrahim na biye dashi a baya.
Da sauri Umaymah tace.
"Affan me sunan ana tambayarka kayi shiru".
Cikin dariya yace.
"Uhumm Yah Sheykh da abun mmki sunanshi fa ya sawa ɗan, duk zuriyar mun nan ya rasa wanda zaiwa takwara sai yayiwa kanshi".

Cike da mamaki su Ummi sukayi salati, shi kuwa Sheykh murmushi yayi tare da juyowa jin yadda suke salati yana dariya yace.
"Yoh duk zuriyar mu, nuni wanda sunanshi ya kai nawa daɗi Muhammad Jabeer, kuma kafin in burge wani gwara in burge kaina da kaina. Kuna ina son yaron yaji daɗin da nakeji a duk sanda naji an kirani da sunan sabida iyayena sunmin kekkyawan zaɓi".

Murmushi Mameyn tayi tare da cewa.
"Allah ya raya Muhammad Jabeer ƙarami yasa ya gaji halayyar mahaifinshi".
Amin Amin sukace baki ɗayansu.

Ita kam Shatu murmushi takeyi tana shafa kan jaririn.
Tare da kallon Afreen dake zaune gefenta.
Oh Allah mai iko wai itace dai Shatu da yara har biyu.

Nan dai sukaci abinci.
Kana duk mazan suka fara shirin fita ɗan sha biyu dai-dai za'a naɗa Sheykh.

Ƙarfe ɗaya saura.
Duk illahirin manyan Masarautar Joɗa, da baƙin sarakuna.
Da duk maza ahlin masarautar Joɗa, hatta Jabeer da yau aka fita sunansa.
Jalal yazo dashi.
Gaba ɗaya ɗakin rantsawar ya cika maƙil da bani Adam.
Babu abunda ke tashi sai sarewa da tambura da al'gaita da kakafi.

A hankali Lamiɗo ya tashi bisa kujerar, kana ya matsa.
Sarkin naɗi, ya kamo hannun Sheykh dake cikin shiga ta al'farma shigar limancin.
Ya matso dashi gaban kujerar, kana a hankali yasa hannunshin ya zare hiramin kansa.
Sannan ya sunkuyo ya amshi.
Rawanin da Lamiɗo ke miƙa mishi.
Yana daga tsayen ya naɗa mishi.
Kana ya juyo bayanshi da niyar zare al'kyabbar jikinshi.
Da sauri Lamiɗo yace.

“A'a barshi da shirgarsa ta limancin, shigar sarauta bazata kori ta limancin ba.".
A hankali Sheykh ya lumshe idonshi yana mai jin wani irin masifeffen nauyi dake ratsa kanshi nauyin rawanin mulkin Masarautar Joɗa.

Shi kuwa Sarkin naɗi kai ya gyaɗa kana ya zaunar da Sheykh bisa asalin kujerar masarautar Joɗa da sunan Allah a bakinsa.

Kana aka miƙa mishi sandan ya amsa ya riƙe, sarkin fada ya matso kusa dashi.
Hakama ɗan zagi.
Sauran fadawa kuwa duk sai suka matsa suka janye labulen da sukayi musu da manyan garunan su.

Lokacin ɗaya gaba ɗaya mutanen cikin hall ɗin duk suka zauna
Tare da jinjina kai, dan ko kai sarkine in kazo Masarautar wani sarkin to shine a sama.

Sabida kalmar nan ta bahaushe.
(Kare ma a gidansa zaki ne)
Bare kuma sarki.
Nanfa makaɗa da mabusa duk suka ɗauki amo.

Cikin wani irin rauni Sheykh ya lumshe idanunshi tare da ci gaba da tasbihin da yake abokin rayuwarsa.
Sabida wani irin tashi da tsikar jikinshi keyi.
Sarautar tana ratsashi.

Bayan an gama naɗa shi ne, aka naɗa Baba Basiru a matsayin Galadima.
Wanda dama anfi son Galadima yafi sarki shekaru.
Nan kuma aka naɗa Affan Chiroma.
Kana Jalal Wambai, Jamil Durbi.

Yah Jafar kuwa Majidaɗin Masarautar Joɗa.

Masha Allah komai dai ya tafi yadda ya kamata.
Nan aka naɗa duk sauran hakimai.
Kiran sallan Jumma'a ne ya tadasu a taron.
Nan kuma aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login