Showing 171001 words to 174000 words out of 299804 words
da rumtse idanunta tace.
"Wash hannuna".
Cikin sauri Ummi tace.
"Sannu hannun ya gaji ko".
Kai kawai ta gyaɗa mata.
A haka suka fito falon. Kai tsaye bedroom ɗin ta ta nufa.
Shi kuwa Jamil yayiwa Ɗalha jagoro,
Suka shiga suka gyara wurin da aka fasa ɗin fes.
Kana Ummi ta share wurin ta goge, sannan suka tura gadon suka maidashi.
Nanma ta ƙara gyara ɗakin Jamil kuwa ya ɗauki Ɗalha ya maidashi wurin aikinshi.
Ummi na gamawa taja ƙofar ta rufe tana al'ajabin wannan abu da ta gani da idonta.
Kitchen ta wuce ta ɗaura musu Lunch tana kiran Umaymah ta gaya mata duk abinda ya faru.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kaɗan daga cikin mafarkan da nakeyi kan Sheykh ya auro ba fulatar daji sun fara tabbata.
Ya Allah kasa abinda zai faru a sanadin shigowar Shatu masarautar Joɗa ne kake nunamin a mafarkaina".
Umaymah ta faɗi lokacin da Ummi ta mata bayanin abinda ya faru.
"Amin Amin, Ummi tace kana ta katse kiran jin muryar Aunty Juwairiyya da Hibba."
Umaymah kuwa da sauri ta kira Lamiɗo ta gaya mishi abinda ya faru.
Murmushi yayi irin nasu na manyan sarakuna yace.
"Alhamdulillah warakafa nan shigowa masarautar Joɗa baki ɗayanmu zamu rabu da mugun iri a cikinmu, kada ki gayawa kowa Khadijatu kinji ko".
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
"In sha Allah kuwa ko Jadda bazan gaya mishi ba".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Masha Allah, Allah ya miki al'barka Khadijatu da ace duk ƴan uwa haka suke riƙe ƴaƴan yar uwarsu da zumunci ya ƙara ƙarfi kin musu abinda mahaifiyarsu bazata iya musuba".
Amin Amin tace kana ya katse kiran.
A cikin ɗakin Shatu kuwa.
Wani irin...!
By
*GARKUWAR FULANI*
Ya ruggumeta da kyau a jikinshi.
Jinyadda taketa fizge-fizgen zata kwance kanta.
Wani irin tsuma jikinshi ya rinƙayi can cikin naman jikinshi yake jin tsuman.
A hankali ya manna kanta, kan faffaɗan ƙirjinshi,
hannunta mai ciwon data ɗaura a tsakiyar kan natane ya zubawa ido.
Sosai hannun yayi jazir sai kelli yaki, alamun kumburin da yayi.
A hankali yasa hannunshin ya tallabo hannun.
Wani irin ihu tasaka da ƙarfi.
Sai dai bai bari ihun ya fito daga bakinta ba, yayi maza ya rufe mata baki da tattausan tafin hannunshi yana ta mai-maita.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Tabbas da in ya barta ta kurma ihun shike nan ta tabbata zautacciya,
yin ihun da take son yi dai-dai yake da sihirin ya gama shiga jikinta ya ratsa zai kuma haukatata.
Shiru tayi tana zazzare idanunta da hawaye ke zuba babu ƙaƙƙautawa, shi kuwa Sheykh a hankali ya janye hannun nata data aza a kai ya tallabeshi da tafin hannunshi.
Sannan ya manna ƙirjinshi da nata ƙirjin da kyau.
Har suna iya juyo bugun zuciyar juna.
Sunkuyo da kanshi yayi tsakanin kafaɗarta da wuyatan
Bakinshi ya saita cikin kunnenta.
Hure gashin daya baje kan kunnen yayi ya matsa,
sannan ya kawo bakinshi gab da kunnenta har tattausan lips ɗinshi na taɓa tattausan kunnenta.
Lumshe idonshi yayi tare da gyara tsayuwar nasu da kyau.
Ita kuma sai fiffizgewa take sonshi jikinta duk yana karkarwa ga zufar dake tsiyayo mata.
Hannunta dake cikin hannunshi ya kalla yadda yaketa rawa, gashi zafi jau kamar wuta.
A hankali yayi gyaran murya tare da yin bisimilla.
Cikin ɗan-ɗaga sauti ya fara karanta Suratul Baqra cikin kunnenta cikin fidda harrufan da karsashin yadda zai ratsa kunnuwanta.
Yanashi yana cire tafin hannunshi dake bakinta,
wani irin manna kanta tayi da ƙirjinsa,
ta lumshe idonta wasu hawaye masu ɗumi suka fara kwaranya.
hannunta na hagu dake da lfyar tasa bisa kafaɗanshi ta zagayo wuyanshi da kyau.
Shi kuma hannunshi da ya janye daga kan bakinta ya maida kan ƙugunta ya ruggumeta tsam a jikinshi.
A haka yaci gaba da karatu, in yazo wasu ayoyin yakan maimaita karshensu kafin ya kuma kama forkon na gaba.
A hankali ta fara sauƙe wasu tagwayen numfarfashi, ji takeyi azaba da raɗaɗin yana ɗan lafawa.
*Al'farma Annabi da Alqur'ani kenan.*
A hankali ta daina duk fizge-fizgen ta dawo sai kukan da takeyi mai sauti amman sautin a hankali ne.
Kuka take sosai ganin hakane, ya gyara tsayuwar tasu.
Kana ya tallabo kanta ya kalleta.
A hankali ya girgiza kanshi tare da jawota suka nufi bakin gado.
Yana cewa.
"Uhummm baku samu wurin zamaba a kanta in Sha Allah bazamu zauna inuwa ɗaya dani da kuba, zaku bar jikinta."
Ajiyeta yayi kan gadon kana shima ya hau ya zauna.
da sauri ya riƙo hannunta da take son maidashi tsakiyar kanta ɗin.
Karatu ya fara yanayi yana ɗan hura mata sassanyan iskan bakinshi.
Tub, tub, tub, haka yake ɗanyi tare da fesa iskar, kana ya zuba mata ido cikin idanunta.
A hankali tayi ƙasa da kanta.
Shi kuwa haɗe fuska yayi tare da cewa.
"Ɗago ki kalleni mana".
Kai ta girgiza alamun a a.
Shikuwa hannunshi ɗaya yasa ya tallabo haɓarta, dan ta kalleshi da sauri ta rumtse idanunta.
Cikin kausasa murya yace.
"Buɗe idon ki kalleni!".
A hankali ta buɗi baki cikin irin Muryar da yaji tayi mgna kwanaki dashi tace.
"Bazan iyaba, kunyarka nakeji!".
Watsa mata wani kallo yayi tare da cewa.
"Ƙarya ne, bakiji kunyan Allah'n daya haliccemu ya halicceku ya kuma yi mana iyaka a tsakaninmu ya hanaku cutar damu, ta hanyar mazonsa ya ƙaiyade muku dukkan motsinku, ya hanaku cutar da bani Adam.
Duk bakiji kunyarsu ba, kika shiga jikin yarinya ƙarama, kina sata yin wasu abun da ba halinta ba,
bakiji tsoron Allah daya hanakuba.
Bakiji kunyar iyayenta ba, kina cutar musu da ɗiyarsu sai ni?".
Cikin sanyi murya cike da alamun tsufa, tace.
"Ni bana cutar da ita, Ni ba muguwa bace, ban taɓata cutar da ita ko wani nataba duk tsawon shekarun da nake tare da ita".
Da sauri cikin faɗa yace.
"To meyasa zaki shiga jikinta".
A hankali cikin zubda hawaye tace.
"Ni tun tana jaririya nake jikinta, kuma ni makaran gadone na ahlinsu daga wurin kakarta mahaifiyar mahaifinta".
Da sauri yace.
"Rufe min baki, makaran gado,
Ku kuɗine ko wata kadara ce, ku cikin kadarorin da Allah (S.W.A) ya lissafa cikin jerin jadawalin abinda za'a gada?.
Ko dan kinga ina binki a hankali ne yasa zakiyi min zancen banza na mutanen banza".
A hankali tace.
"Jikana ka kontar da hankalinka muyi mgna".
A fusace yace.
"Waye jikan naki, kina Jinnu ina bani Adam ta ina na zama jikanki.
An ƙi a kontar da hankali tsohuwa dake kinzo kin liƙewa yarinya kina ƙoƙarin sata tana yaye suturar jikinta tana shirin yin ihu.
Ko baki san cewa matar aure bace, baki san daraja da kimar dake cikin aure bako?".
Cikin fushi itama tace.
"Ni bani nasata yarda kallabin kanta ba, zafin ciwo da takeji ne ya gigitata yasata yarda kalkabinta.
Sannan batun ihu da kakeyi kuwa.
Aikin da mugayen Masarautar Joɗa sukayi data taɓane yake shiga jikinta.
Ni kuwa na zone sanadin karatun Rugyan da kayi ta mata, amman duk wancan abun da takeyi ni bana kusa ma.
Kuma ni ba mai cutarwa bace.
Batun darajar aure kuma na fika sani.
Kai kama tsaya inda takene bare ka raya auren ka tabbatar da ita matarka ce kai mijinta ne?.
Kasa sabgogi a gabanka, kana sane da magautanka sun saka a tsakiya kayi, burus dasu, suna neman rabaka da rayuwarka.
Ita kuma dole in taimaketa sannan dama Aysha in dai bata da lfy ko zazzaɓi ne tana kuka haka ciwonta yake."
Cikin haɗe fuska yace.
"Eh wato da ban ƙonaki bane, kikemin baki ko. T taimako bana son taimakonki ki fitamin a jikin matata, bana so, zakisa tayi ihu ta fita tsakiyar masarauta bayan kin san inada magautan to meyasa zaki nemin abinda zaisa magautana farin ciki.
Tai mako kuma bama so, muda mukeda ubangijin taliƙai wanda yasan zahiri da baɗinin shi yake taimaka min, ba tare da yasa mana ciwon kai ko fita haiyaci ko kukaba dan haka fice min a jikin matata".
Murmushi tayi tare da jinjina kai kana tace.
"Matarka kuma yau".
A hatsale yace.
"A a matarki ce, in ba matata ba?."
Sai kuma yayi bisimilla zai fara karatu da sauri tace.
"Tsaya Muhammad Jabeer ɗan Habibullah jikan Nuruddee, Bubayero, Joɗa, Sule Usmanu jinin sarki Muhammad Bello, ni bazanyi faɗa da kaiba kafi ƙarfin haka duk da ni ba cutar daku nakeyi ba. Naga ranka ya ɓaci ina jinin.
Wai matarka kace ko?".
Wani irin kallo yayi mata tare da ɗago hannun shi zai shararamata mari yana cewa.
"Wai ne ma ko?".
Da sauri tayi murmushi tare da cewa.
"Kamar gibtawar ido zan gudu jikinta, ka kwaɗa marin a kanta".
Ai fa a kufule ya kai marin.
Hannunshi na isa fuskarta tana yin atishawa.
Zafin marin ya sauƙa kan fuskarta cikin azaba ta ɓare baki tare dasa kuka tana mai shafa haɓarta ido na zubda hawaye a gigice idonta na ganin duhu sabida zafin marin bata gama dawowa haiyacinta ba murya na rawa tace.
"Wayyo Allah na me nayi maka zaka mareni, ka barni inji da ciwo ɗaya mana".
Hararanta yayi tare da miƙewa ya sauƙa gadon yana cewa.
"Mutun jiki duk al'janu, sai hegen bakin rashin kunya mutun in ba lfy bazaiyi addu'a ba sai kuka".
Ya ƙarishe mgnar da juyawa ya nufi falo.
Ita kuwa Aysha wani irin bacci ne yayi awon gaba da ita,
tana mai jin zafin hannun ya ɗan lafa sai kuma raɗaɗin marin.
A can falon kuwa, wayar Aysha ne dake hannun Hibba yayi ringi.
Bappa am.
Shine sunan da ta gani a rubuce.
Da sauri ta nunawa Ummi shi tare da cewa.
"Ummi ana kiranta".
A hankali tace ki ɗaga.
Kai ta gyaɗa tare da amsa kiran ta kara wayar a kunnenta.
Cikin nitsuwa tace.
"Wa alaikassalam". Sai kuma tace.
"A a Bappa ba Aysha bace.
Hibba ce, Aunty Ayshan tana ɗakin Hamma Jabeer".
Cikin dattaku Bappa yace.
"To Hibba ya jikin nata?".
A hankali tace.
"Bappa hannunta kam yana ciwo sosai, ya kumbura yayi ja, in an taɓashi zafi kamar wuta, bata iya bacci".
Da sauri tayi shiru ganin Ummi na girgiza mata kai alamu.
Ta daina faɗa mishi hankalinsa zai tashi.
Ila kuwa hakane, cikin tashin hankali da kiɗima yace.
"Yanzu kai mata wayar maza, kai mata inji muryarta".
A hankali ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi wai in Kai mata wayar".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Jekiyi sallama ki kai wayar".
To tace kana ta juya ta nufi falonshi.
Tana jin Bappa na cewa.
Yi sauri".
A falo ta samu Hamma Jabeer ɗin cikin sanyi tace.
"Hamma Jabeer gashi Bappa am, na son yin mgna da Aunty Aysha".
Hannunshi ya miƙa ya amshi wayar ba tare da yace komaiba.
Ganin kiran bai yanke bane.
Yasa ya zubawa number ido cike da mamaki ganin code number ɗin bana ƙasar Nigeria bane, na ƙasar Cameroon ne.
a hankali ya kai wayar kunnenshi tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
"Wa alaikassalam Jabeer ne?".
A hankali cikin nitsuwa yace.
"Eh Bappa nine, ina kwana ya gida".
Cikin jin sanyi yace.
"Lafiya lau Alhamdulillah. Ya jikin Shatu?".
A hankali yace.
"Alhamdulillah Bappa jiki da sauƙi sosai ma yanzu hakama tana bacci ne".
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah to Allah ya ƙara lfy, amman me yake faruwa da hannun ne?".
Cikin sanyi ya miƙe ya nufi bedroom.
A gaban gadon ya tsaya tare da cewa.
"Hannun ya ɗan kumbura amman ba sosai ba, sai kuma yayi ja, sannan jikin hannun yayi zafi sosai".
Cikin tausayawa ɗiyar tasa yace.
"Amman kada ayi mata allura, sannan a nunawa masu maganin gargajiya hannun, ko dajine".
A hankali yace.
"Bappa ba daji bane an gwadata babu wani ciwo a jikinta.
Kuma inma dajin ne yanzu akwai alluran shi.
Matsalar hannun yana ɗan lafawa ya kuma tashi ne.
In ya tashi kuma ihu take son yi.
Kuma sai tayi ta kuka.
To kukan ne ke sa mata zazzaɓi da ciwon kai".
Cikin sanyi yace.
"Allah sarki Shatu, haka take in bata da lfy.
Zan zo jibi in sha Allah."
Cikin hikimar nuna mishi ya fahimci inda yake tace.
"To Bappa Allah ya kawoka lfy, daga gobe zaka taso ko?".
Cikin nitsuwa yace.
"In sha Allah".
Kontar mishi hankali yayi kana suka katse kiran.
Ba'ana kuwa duk abinda ke faruwa da Aysha yana gani a ƙwaryar tsafinshi.
Amman muddin Sheykh yana wurin sai yaga wani haske ya rufe ƙwaryar gaba ɗaya sai ya kasa ganin komai a kanta.
Yanzuma zaune yake yasa yaranshi a gaba.
Da kuma sabon uban gida daya samu.
Cikin fargaba da tausayawa Mata abinda ke damunta ya kalli ɗaya daga cikin yaransa wanda ɗan ƙabilar ɓachama ne, cikin waɗanda suka koro shanayen Bappa ne da Alhaji Haro.
Cikin Ɓacamancin yace.
"Barun zaka tafi ƙasar Nigeria ka wuce jihar Ɓadamaya kai tsaye har cikin masarautar Joɗa".
Cikin tsoro Barun yace.
"Masarautar Joɗa kuma, ta yaya to?."
Numfashi ya fesar tare da cewa.
"Duk magungunan da Sarkin bakan masarautar Joɗa yake saka mata da wanda zai sa mata nan gaba, duk na ruruta ciwon ne, sabida shi magautan Jabeer yakewa aiki, to kasan cewar bawai sihiri bane shiyasa Mata bazata ganeba, kawai maganin ingiza ciwon yake shafa mata.
Sannan makarin ciwon Ni kaɗai nake dashi.
To zan kira Bappa da layinka.
In mishi jawabin ciwon da mgnin sannan zance mishi kai yau zaka kama hanya,
dan taimaka mata, amman fa sai in zasu biya kuɗin jinyar da shanu hamsin".
Cikin mamaki Barun yace.
"Shanu hamsin mutumin da muka kwashewa komai ko ɗan tinkiya bamu bar mishiba, ina zai bada shanu hamsin".
Murmushi Ba'ana yayi tare da cewa.
"Uhumm baka san waye Malam Liman ba kenan Bappa baka san da waye yake tareba, baka san komai game da shiba. Kai dai bani inkirashi yanzu kaji."
Da sauri ya miƙa masa wayar.
Shi kuma ya dannawa Bappa kira.
Yana katse kiranshi da Sheykh yaji wani kiran ya shiga wayarshi.
Amsa kiran yayi tare da kara wayar a kunne.
Sauya murya ba'ana yayi tare da cewa.
"Ina mgn da Malam Liman ko baban Aysha mai ciwon hannu".
Da mamaki Bappa yace.
"Waye ne?".
Ciki kaurara muryarshi yace.
"Sarkin bakan nufe ne, bincike nane ya nuna min ciwon hannun yarka tana can masarautar Joɗa.
An kawo wani sarkin baka yana mata mgni sai dai mugune magautansu yakewa aiki.
In har zaku biyani ni Shanu hamsin zan je kuma zan mata aiki a take zataji sauƙin".
Cikin sanyi Bappa yace.
"To yanzu kai ina kake".
A nitse yace.
"Ni yanzu haka ina bakin iyakar ƙasar Nufe da Nigeria ne.
Yau zuwa gobe zan shiga ƙasar".
A hankali cikin sanyi Bappa yace.
"To ba matsala, nima jibi zan shigo.
Mu haɗu a can in dai kayi mata mgnin ta warke a take zan biyaka da abunda kace".
Cikin jin daɗi yace.
"To sai mun haɗu."
Katse wayar yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah Shatuna zata samu lfy. Zan kuma samu shanu hamsin. Sannan zanji lbrinta, zaka kuma isarmin da manufata.
Kunga na jefi tsuntsu biyar da dutse ɗaya."
Jinjina mishi sukayi kana ya shiryawa Burun komai nagnin ya nuna mishi yadda zaiyi da yadda zai isar mishi da saƙonshi wurin Aysha.
Bappa kuwa Murmushi yayi dan ya gane Muryar Ba'ana.
Dama ya sani bazai rabu dasu haka a sauƙaƙeba yasani yanzu duk motsin Aysha yana tafin hannunshi.
Abinda yasa ya yarda su haɗu kuma yasan ba shi da kanshi zai jeba.
Sai dai ya wakilta wani.
Ya kuma sani tabbas yanada makarin ciwon taɓen sihiri wato ƙetare.
Yakuma san bazai cutar da Aysha ba yasan tabbas taimaka mata zaiyi dan baya son abinda zai cutar da ita.
A haka shima ya kira Arɗo Bani suka tattauna kana ya fara shirin tahowa.
Ko Ummey bai gaya mata abinda ke faruwa ba.
A can jihar Tsinako kuwa sha ɗaya dai-dai jirginsu Umaymah ya tashi ya nufi jihar Ɓadamaya.
A cikin Rugar Bani kuwa. Tun shekaran jiya su Junaidu suka dawo gida.
Alhamdulillah duk sun worke kuma har gida aka dawo dasu.
Sosai Arɗo Bani da sauran dattawan sukayi mamakin jin Sheykh ne ya kaisu sibitinshi ya kuma kula dasu har suka samu lfy.
Kana yayi musu komai ya dawo dasu lfy.
Alhamdulillah kuma yanzu Rugar Bani basu da matsalar komai.
dan ya rigada Allah yasa tsoron fulanin a zuƙatan Ɓacamawan.
Yanzu kowa harkar shi yake ba kare bin damo.
Suyi kiwonsu lfyta shanayensu nata habaƙa.
Yanzu kuma sun maida hankali kan shuke-shuke amfanin gonakin su.
Sabida shigowar damuna.
A cikin masarautar Joɗa kuwa.
Sheykh yana gama mgna da Bappa ya shiga bathroom.
Cike da mamaki ya ɗan sunkuyo ya kalli boxes dake jikinsa,
wanda dashi zaiyi wonka.
hannunshi yasa ya damƙi bnnarshi da tun jiya da safe data harba ta miƙe ta tsaya ta rinƙa kumbura da cika da miƙewa tayi tsawo.
Har yau har yanzu harbawa takeyi babu ƙaƙƙautawa yadda zuciyarshi ke harbawa haka itama.
Kuma tana tsaye gam tamkar zata faso boxes ɗin ta fito woje.
Shiyasa yake jin tsikar jikinshi yana zubawa.
A hankali ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, wanka yayi kana, ya fito ya kimtsa ya shirya jikinsa cikin manyan kayan.
A falon kuwa Lamiɗo da Galadima da Sarkin bakan.
Ne suka shigo bayan. Sallama yayi musu jagora.
A bisa kujera Lamiɗo da suka zauna sarkin baka kuma a ƙasa.
Hakama Ummi da Hibba.
Jalal da Jamil kuwa tun ɗazu suka fita, suka tafi Side ɗin Mama.
A can suka samu Ya Affan.
Cikin girmamawa Ummi ta ɗan rusunar da kanta tare da cewa.
"Barka da isowa Lamiɗo shugaba mai adalci".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Barka dai Jakadiya mai gsky,
ya jikin ɗiyar taki, ina take".
Cikin ƙara rusunar da kai tace.
"To jiki dai da asuba da sauƙi amman kwana mukayi babu bacci.
To rana na fitowa kuma ciwo ya harzuƙa ya zarta na baya".
A hankali Lamiɗo da Galadima sukace
"Subahanallahi".
Sarkin baka kuwa.
sunkuyar da kanshi yayi tare da sakin murmushin mugunta,
kana ya gyara riƙon da yayiwa wayarshi yadda, waɗanda suka sashi aikin zasuji bayanin komai da kunnensu.
da kiransu da ya haɗa.
A can kuwa magautan dariyar jin daɗin lbrin.
Sukayi.
A hankali ya kalli Ummi yace.
"Sauƙi a hankali yake samuwa, zai nayi yana lafawa har yazo ya bari gaba ɗaya".
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa.
A hankali ta miƙe bayan Lamiɗo yace mata.
"Jeki kira min ita tazo".
To tace kana ta nufi shashin Sheykh.
Shi kuwa Sheykh yana cikin fesa turare kenan.
Ya juyo ya kalli Aysha da ta tashi zaune da sauri tasa hannu a kanta tana yarfa ɗaya tare da cewa.
"Wash! Wash! Wayyoooooooo Allah na!'.
A hankali ya ajiye kwalban turaren kana yazo gaban gadon.
Tare da cewa.
"Sauƙo". Cikin rawan jiki ta sauƙo tana yarfa hannunta.
Cikin haɗe fuska yace.
"In zakiyi kuka fice min a ɗaki".
Cikin rauni tace.
"Yah Sheykh zafi! zafi!! zafin nakeji yana dawowa".
Da sauri ya juyo ya kalli ƙofar ɗakin jin ana bugawa.
Jiyo muryar Ummi ne yasa ya juya ya nufi ƙofar.
Yana buɗewa tace.
"Sheykh, Lamiɗo ne yazo yana son ganin hannun nata".
Kanshi ya ɗan gyaɗa kana yace.
"Fito kije, Ummi a kawo mata ɗan kwali ta ɗaure wannan dogon gashin da kitseshi ma aikine shiyasa ko yaushe kai a tsefe ai kuwa al'janu kam sayi ta shiga lodi-lodi".
Da sauri Ummi ta miƙo mishi ɗan kwalin doguwar rigarta dake hannunta tun sanda ta wurgar dashi.
Kanshi ya juya tare da cewa.
"Fito".
Cikin zubda hawaye ta fito.
Gaban Ummi ta tsaya tana cewa.
"Wayyo Ummey na".
Cikin tausaya mata Ummi tace.
"Sannu ko". Ta ƙarishe mgnar tana yafa mata ɗan gyalen.
Kana ta kama hannunta na hagu suka nufi falon.
Shi kuwa Sheykh hiraminshi yasa ya dai-dai-ta komai.
Sai dai abin da ya sashi jin kunyan kanshi da kanshi ganin.
Har yanzu bnnarshi a tsaye ƙiƙam