Showing 162001 words to 165000 words out of 299804 words
Amman sai ta ji ya riƙeta gam-gam, yana ƙara cusa kanshi cikin jikinta yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren jikinta.
Cikin tsoro murya na rawa a hankali tace.
"Yah Sheykh!".
Karab sautin muryarta ya ratsa kunnuwanshi.
Sai dai ko motsi baiyi ba,
A hankali ta kuma ce.
"Yah Sheykh! Yah Sheykh!!".
Shiru babu amsa sai numfashin da yake fiddawa a hankali yana kuma shaƙan ƙamshin jikinta.
Cikin sanyi ta ɗan ɗago hannunta a hankali tasa taffin tattausan hannunta, ta ɗan rinƙa buge gefen fuskarshi a hankali a hankali tanayi tana cewa.
"Yah Sheykh! Yah Sheykh! ! Tashi wai Affan dasu Yusuf sunzo, shine Affan yace inzo in tasheka".
A hankali ya buɗe idonshi,
Yanayin yadda take ɗan marin gefen fuskarshi da hannunta wanda ke ɗaure da agogo.
A hankali ya ɗago hannunshi ya ɗan kan hannunta ya kamoshi ya riƙe, cikin tsoro ta fara kiciniyar kwace hannunta,
Sai kuma tayi zuru, jin ya ja hannun da ɗan ƙarfi ya kawoshi dai-dai saitin fuskarshi.
Idonshi ya zubawa yatsun hannunta da kullum in ya gansu da jan lalle yake tuna mishi baya.
Da sauri tace.
"Wash Allah na".
Jin ya murɗa hannun ya juyo da fuskar agogon inda zai gani.
Ƙarfe biyu da miti arba'in da ɗaya.
Du-du baccin 40 minutes yayi tazo ta tasheshi.
"Harda zuba min maruka".
Ya faɗa a ransa.
Ita kuwa kan tattausan suman ta ajiye sinsiyar hannunta.
tana jin kanta na sara Especially in ta kalli saitin ƙasan gadonshi."
A hankali ya sake hannunta kana ya yunƙura ya juya rigingine,
ya fuskanci sama, ita kuma tana zaune tana kallon ƙasa hakanne yasa suna fuskantar juna, cikin wani irin yanayi ya zuba mata ido na wasu sakanni.
Shigarta tayi masifar mishi kyau. Kodan tasa kalan kayan da yafi sone.
Cikin muryar bacci yace.
"Shine harda dukana? Meyasa ne ku mutanen garincan kuke son dukan mutun da kallon jikinsa?".
Cikin tura baki tace.
"Cinyana, nagaji kanka nauyi".
Bai janye idonshi a kantaba ya yunƙura ya tashi zaune tare da juyowa ya fuskanceta.
tanƙwashe sawunshi yayi tare da cewa.
"Me zaki kalla a jikina? Woto Kin zama kamar ɓarauniya ko? Me kike son gani? Wani abu kike sone?".
Cikin tura baki tace.
"Nifa tada kai a bacci kawai nayi".
Hannunshi yasa ya riƙo hannunta, yatsunta ya zubawa ido, cikin wata murya mai sanyi yace.
"Masha Allah, kinyi kyau."
Wani irin sanyi taji kalmar tashi tasa mata a ranta, ido ta ɗan ɗago ta kalleshi.
Shima ita yake kallo, ido ya lumshe jin sautin zazzaƙar muryarta a hankali tace.
"Nagode".
Tonƙoshe kansa yayi bisa kafaɗa kana hankali ya sake hannun nata.
Fuskarta ya kalla tare da taɓe baki yace.
"Waya koya miki irin sa lalle Mammeyyyyy nah!? Dan tafi ko wacce mace iya lalle".
Cikin sanyi da nazartar yadda ya kira sunan Mammeyyyyy da yadda lokacin ɗaya idonshi suka fara sheƙin tsastsafo da zafafan hawayen da ba zubowa zasuyiba.
Cikin son gano meke cikin zuciyarsa tace.
"Ummeyy nah ce ta koya min tun ina ƙaramar".
Yatsunta ya jujjuya kana ya miƙe tsaye.
A hankali ya juya ya nufi bathroom sabida baya son ta hango wutar ƙunar dake ransa.
Ita kuma binshi da ido tayi,
tare da langoɓar da kanta tana kallon sharabansa da gargasa yayi musu ƙawanya.
A haka ta shiga wani nazarin tana mai maimaita sunan da taji ya kira da cikekken so shaƙuwa ƙauna tausayi rauni shogoba *Mammeyyyyy.* Ta maimaita sunan a fili.
Shi kuwa Sheykh Jabeer al'wala yayi kana ya fito.
Yayi mamakin ganinta a zaune bata fita ba.
Hararanta yayi ganin yadda taketa kallonshi. Jallabiyar shi ya zura, kana yasa al'kyabbar, tare da sa Hiraminshi.
Sannan ya fesa turare.
Duk inda yayi tana binshi da ido.
Wayarshi da yafi yawan riƙewa ya ɗauka ya zura a al'jihunsa.
Sannan ya nufi bakin ƙofa inda takalminshi suke yana cewa.
"Wannan kallon maitan fa".
Da sauri ta janye idonta.
Cikin daƙilewa yace.
"Kada ki cinyeni da ido fa. Bana son kallo, ko kina bina bashine?."
a hankali ta miƙe tare da lumshe ido ta biyu bayanshi.
Tana gyara mayafinta tare da cewa.
"Ni ban kalleka ba".
"Uhummm." yace a taƙaice.
Kusan a tare suka fito.
Yana gaba tana bayanshi,
Suka fito tsakiyar falonshi.
Tsayawa ya ɗanyi ya gyara masaƙalin Al'kyabbar tashi.
Shiyasa ya zama a jere suke tafiya tana gefen damanshi.
A haka suka fito cikin corridor'n.
Suka doshi Falon cikin kwarjini da dacewa da juna sai ƙamshi da sheƙi zallan kyau sukeyi.
Da Sallama a bakinshi suka kutsa kai cikin falon.
Wani irin dariyar jin daɗi Affan da suke can Dinning area yayi, suna cin abinci da Ummi ta matsa suci.
Wani irin murmushi Yusuf da Aryan ma sukayi tare da miƙewa suka nufi inda uban gidan nasu ke tsaye da kekyawar tauraruwarshi mai haskawa.
Affan kuwa wayarshi ya zaro yana kekkebta musu hoto tare da cewa.
"Ga amarya, ga ango, suna carabki da zallan kyau da ƙamshi".
Murmushi sukayi dukansu, ita kuwa Shatu tana tsaye gefenshi.
A haka su Affan suka iso.
Suna Isa Affan ya ruggumeshi shima Sheykh ruggumeshi yayi tare da make ƙeyarsa.
Da sauri ya janye kanshi tare da cewa.
"Wayyo Allah na yanzu Hamma Jabeer na girma harda yaran nawama ban wuce dukaba".
Murmushi yayi tare da, Ruggume Yusuf da Aryan Allah ya sani yana masifar son yaran nan har gobe bashi da ɗalibai sama dasu yana sonsu so na musamman, duk sanda ya gansu yakan tuna ƙuruciyarsu tun suna yan shekara goma sha biyar-biyar yake tare dasu shi ya horas dasu.
Yana tura irin tarin ƙalubale da suka fuskanta a gasar Polo da kuma irin nasarorin da suka samu Especially Yusuf nashi yana tuna yadda yaran suke sheƙiyanci in sun haɗu, yana jinsu tamkar su Jamil.
Cikin murmushin ya shafa kansu tare da cewa.
"Sannunku da zuwa".
Cikin jin daɗi sukace to.
Bisa kujera ya zauna su kuma suka zauna a ƙasa a gabanshi kan carpet.
Ita kuwa Shatu a hankali ta juya ta nufi kitchen ganin Ummi ta nufi can.
Hibba kuwa na gefensu tana gayawa su Jalal ga Ya Affan fa.
Da gefen idonshi ya bita da kallo.
Har ta ɓacewa ganinsa, Allah ya sani yana son abu blue baya iya cire idonshi kan abu mai kalar shiyasa yake jin baya gajiya da ganinta, da zai samu kada tayi nesa dashi, dan tayi mishi kyau sosai farar fatarta ta fito fes kamar balarabiya ji yake tamkar ya bita duk inda tayi.
Cikin murmushin ya kalli Aryan yace.
"Aryan Ina su Yusuf ƙaramin".
"Alhamdulillah suna lfy Malam".
Kai ya jinjina tare da cewa.
"Masha Allah".
Sai ya kuma kalli Yusuf yace.
"Ina mai sunana baka zomin da shiba".
Murmushi Yusuf yayi tare da cewa.
"Malam baka tambayi Aryan ƙaramin ba da yakeso ya zama kamarka sai ka tambayi mai sunanka".
Dariya sukayi kana yace.
"Ayyah my Aryan, sun kusa tafiya ai in sha Allah Jami'atul Madina zaiyi karatunshi".
Da sauri suka juyo suka kalli Jalal da Jamil da suka shigo da sauri.
Ruggume Affan sukayi suna cewa.
"Oyoyo ya Affan".
Hannu ya basu suka tafa kamar sa'ao',insa ne su.
Cikin dariya yace.
"Tun ɗazu nake kiranku bakwa ɗagawa.
Nace waɗannan ana can cikin hayani ".
Murmushi Jamil yayi tare da miƙawa Yusuf hannu wanda ke cewa.
"Oh wato Affan kawai kuka gani mu ko oho ko".
Cikin ɗan sakin fuska Jalal yace.
"Afwan Hamma Yusuf ya Aunty Zahra da Mama".
"Suna lfy. Sun gaidaku". yace tare da bashi hannun.
Kana suka gaisa da Aryan.
Sannan suka miƙe sukace bari suje wurin Aunty Mami.
Cikin dariya Affan yace.
"Eh kujema kuzo da ita taga matar babban yaya".
Da sauri Jamil yace.
"A a ka kawota da kanka dai".
Ya ƙarshe mgnar suna fita.
Su kuwa cikin yin ƙasa da kai Yusuf yace.
"Uhum dama Malam zamu ɗan shiga wasan daba ne in batsala".
Murmushi mai faɗin Sheykh yayi tare da cewa.
"Wato ku dai har yanzu baku girma da batun doki ba".
Shiru sukayi sai Affan ne yace.
"Tab Yusuf kuma da in ya ga doki bai hauba jikinshi har rawa yakeyi".
Murmushi Sheykh yayi kana yace.
"To muje muyi salla. Tukun tunda sai anyi sallan la'asar za'a fara ko".
To sukace tare da miƙa ganin ya miƙa dan tuni uku da kwata ta wuce.
Affan ne ya kira Ummi tare da cewa suzo zasu tafi.
A tare suka fito kitchen.
Sabbin kuɗi rafa yan dubu-dubu Yusuf ya miƙawa Hibba ƙulli ɗaya dubu ɗari kenan yace.
"Gashi miƙa wa Ummi ta raba muku."
Affan ma ya basu.
Hakama Aryan.
Hibba sai tsalle take tana cewa.
"Yessss my brother's Allah ya ƙara buɗi Amin Amin sukace kana suka juya zasu fita.
Cikin tsare girma Shatu tace.
"Mun gode, a gaida gida".
Gida zaiji sukace kana suka fita suka tafi.
Suma su Ummi wucewa sukayi yin al'wala.
Ana idar da salla kuwa aka fara hawan daba, hawan sarki dama duk sauran shagulgula na gidajen masarautun gargaji yayin wurin taron bikin salla.
MASARAUTAR Joɗa ta cika tayi maƙil da bani Adam.
Haka dai akayi taron lfy aka tashi lfy sai kuma gobe in Allah ya kai rai.
Washe garin ranar da sassafe.
Sheykh ya tafi asibitinshi.
Ko karyawa baiba.
Sai kusan sha ɗaya ya dawo da alamun yunwa da gajiya tare dashi.
A falon ya zauna suna gaisawa da Ummi dan basu gaisaba ya tafi daga masallacin can ya wuce.
Ummi kuwa tasa Shatu ta kai mishi breakfast ɗin shi da yanzu kam in yacima ya zama lunch ne.
Hibba kuwa na can ɗauki tana ƙenƙesa ado.
Cikin isa da ƙasaita Gimbiya Saudatu ta shigo tsakiyar falon babu ko sallama.
Haɗe fuska Sheykh yayi tare da cewa.
"Wannan banzan ɗabi'a na arnatakun baya, dan ko arna yanzu suna cewa konkon, mutun kamar shanu ko mahaukaciya".
Cikin isa ta iso tsakiyar falon.
Dai-dai lokacin kuma Shatu ta fito falonshi.
Cikin shigar doguwar riga mai ruɓi biyu.
Kanta ta ɗago ta kalli Shatu kana ta kalleshi cikin yin dariyar mugunta tace.
"Eh kam tabbas tunda ka auro mahaukaciya dole kasan hali da ɗabi'un mahaukata ai.
Zuwa gaba kaɗan kaima zaka fara ihu da kuka da sume-sume irin na wannan al'janar fulanin daji daka auro ɗin".
Cikin tarin mamaki Ummi ta kalli Shatu ta kuma kalli Hibba da yanzu ta fito, cike da al'hinin ta yaya taji wannan batun ya fasa Masarautar Joɗa yes in dai Gimbiya Saudatu taji to ai shike nan kowa ma zaiji.
Shi kuwa Sheykh ba gane inda soki burutsunta ya nufaba yayi.
Ita kuwa cikin watsa musu kallon ku sakarkaru ne tace.
"Kuna mamakin ta ina naji, cewar ji shekaran jiya iwar haka dai wannan matar tashin tana yashe a sume da ido a wulkice tana ƙarkarwa farfaɗiya kamar mazari ne.
To ai Ni duk wanda yaci tuwo dani miya yasha.
Inada tawa a cikinku duk motsinku ina dashi a tafin hannuna.
Nan gaba kaɗan zamu samu riƙeƙƙiyar mahaukaciya a masarautar Joɗa".
Cikin tsuke fuskarsa yace.
"Yanzu ma ai muna da su mahauka ta kam, ke ɗin me banbancin ki da zararrun".
Shiru yayi ganin yadda Shatu keyin taku a hankali cikin isa ta nufi gaban Gimbiya Saudatu.
Ummi da Hibba kuwa miƙewa tsaye sukayi.
Shi kuwa Sheykh gyara zamanshi yayi tare da ɗaura ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya.
Ita kuwa Shatu a hankali ta isa gabanta.
Ido ta zuba mata tare da yi mata kallon tara saura kwata.
Cikin dakkeyar Muryar rashin tsoro tace.
"Toh *Bushiya* mai mugun baya, Bushiya mai bayan ƙayoyi masu kama da allurai, ki buɗe idonki da kyau ki kalleni Ni AYSHA ALIYU GARKUWA ba sa'ar yinki bace uwar mahassadan duniya, in kina cin ƙasa to tabbas ki kiyayi ta curi, ki bar min mijina ya sarara ki far masa rayuwa, ɗan shi ba sa'an yinki bane ki bar min mijina ya huta baya son ihun nan da kikeyi mishi, zan kuma iyan komai dan ganin na kauda dukkan abinda baya so."
Wani irin daɗi ne ya rufe zuciyar Ummi da Hibba Sheykh kuwa ƙafarshi kawai yake kaɗawa yana mai binta da wani irin kallo mai tarin ma'anoni kalmarta ta *Mijina* yake ji tana sa duk wani hudan gashin jikinsa na amsa amon kalmar yana ratsa jikinshi da zuciyarsa haka yasa bai san sanda wani yalwataccen murmushi ya subce mishiba, tabbas Shatu akwai ƙarfin hali.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu tsuru tai da ido.
Itako Aysha cikin karsashi tace.
"Na lura ke dabbace, sam bakya gane yarukan mgna na bani Adam, kinfi son sai an miki irin yarukanku na dabbobi.
Kina tsaye da farin yawu a bakinki kina zubda jini.
Yayinda wasu ke bayanki da jini a bakinsu suna fidda farin yawu.
Sokuwar rama mai tsami.
Ni nan da kike ganina da idona tar a buɗe na shigo Masarautar Joɗa, kada ki ganni haka Ni ɗan hakine da zaki iya renawa amman tabbas zan tsole idanun magauta ruwanshi ya tsiyaye.
In kin san fullanci to.
*MIN MI KURORI CITTA NFAMƊA NHEYAH* NI ```DAKKEN YAJIN BORKONE INYI KAƊAN IN KUMA ISHI MUTUN```
Ki tsumayeni tabbas zanyi daka inyi tankaɗe inyi rairaya a masarautar Joɗa!.
Ke ko kallo baki isheni ba domin bata ke akeyi ba da manyan Magauta nakeyi.
Ja mugun bakinki ki fice min a gidana!".
Rab-Rab.
Jalal da Jamil dake da Jafar shigowa ne, suka tafa mata da hannu bibbiyu.
Hakama Hibba. Ummi kuwa ƙasa tayi da kanta.
Shi kuwa Sheykh ƙanƙance idonsa yayi yana kallonsu yana kaɗa ƙafa ya watsa idanunshi cikin na Gimbiya Saudatu yana mata kallon itama ta isheki.
Aunty Juwairiyya kuma da tun ɗazu tana bakin ƙofar shigowa da sauri ta juya ta koma Side ɗin ta.
Ya Jafar kuwa sai murmushi yake tare da dunƙulawa Shatu hannunshi kamar haka👍🏻
Wani irin juyawa Gimbiya Saudatu tayi tare da jan al'kyabbar ta ta fita.
Har taje bakin ƙofa Shatu tace.
"Ki riƙe kalmar mahaukaciya tabbas zakiga mahaukata a masarautar Joɗa zasu baiyana bila'adadin."
Daga nan ta juya ta nufi Dinning area ɗin babban falon.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu ta juya ta fita.
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya sauƙe ƙafafunshi kana ya miƙa ya nufi falonshi.
Haka nan yaji murmushi na tsubce mishi.
Tabbas ya gamsu da ƙarfin halin Shatu da rashin tsoronta, sai dai yana jiye mata tuggun mutanen da bata san halinsu ba.
Yana shiga yaci abinci kana ya shiga yayi wonka.
Kana ya ɗauki wayarsa.
Jalal, Jamil, Hibba, Ya Jafar, Shatu kuwa zama sukayi a falon cikin mamaki Ummi tace.
"To wacece yar leƙen asirin Gimbiya Saudatu a wannan sashin?
Ya akayi tasan abinda ya faru da Shatu?
Waya gaya mata?
Bayan in banda muyamu.
Ni Juwairiyya, Hibba, Jalal, Jamil, Jafar. Wanda shi baya mgna, ita kanta Shatu bata san meya faruba batasan ya akayi ba.
To waya fitar da wannan zancen a cikinmu?."
Cikin gsky da gsky duk suka ce wlh babu wanda suka taɗawa mgnar Hibba harda ƙollarta tace.
"Wlh ita ko Umaymah ma bata gayawa ba".
To lallai kam akwai buƙatar bincike a tsakanin mu."
Ummi ta faɗa tana mai cike da al'hinin abin.
Ita kuwa Shatu uhummm. Kawai ta iya cewa tayi shiru bata ce komaiba.
Haka dai suka tashi taron.
Sheykh kuwa, number Umaymah ya kira bayan sun gaisa ne yace.
"Uhumm Umaymah wai me kika sani ne ya faru da wannan yariyar shekaran jiya?".
Cikin tsoro da son kauda batun Umaymah tace.
"Wacce yarinyar kuma?".
Fuska ya ɗan tsuke yace.
"Waccar yarinyar dai".
"To bata da sunane ita".
Ta kuma ce mishi.
Cikin gajiya da batun yace.
"To ni ba sanin sunanta nayiba, baku gaya min sunanta ba."
Wani irin murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
"Ban gane bafa Jazlaan".
Hannunshi yasa ya ɗan shafi sajenshi.
Yana mai son yasan meya sameta, meya faru da ita, shiyasa a hankali yace.
"Yarinyar dai da kike cewa ɗiyarki!."
Kai Umaymah ta jinjina tare da cewa.
"Laah ni nama mance bamuyi mgnarba, ran sallane tayi aiki ta gaji tunda safe bataci komaiba to ashe tanada olsa shine fa, ta shiga ɗakinka zatayi maka shara ta faɗi ta suma, da kyar aka samu ta farfaɗo suanta kuma Aysha".
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Shirme in banda sakarci da raki mutun ya bar kansa da yunwa da gajiyan aiki mutun har ya suma". Ya ƙarashe mgnar yana jinjina darajar sunanta a ranshi.
Cikin jin daɗin bai tsananta bincike ba tace.
"Akwai wani abune?".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Wannan mahaukaciyar Gimbiya Saudatunce tazo take cewa wai taji lbrin ta haukace".
Daga nan ya kauda zancen.
A hankali ya miƙe yana riƙe da wayar a kunne shi.
Dinning area ya nufa.
Murmushi yayi gano tabbas akwai abinda Umaymah ke ɓoye mishi.
Hannunshi yasa cikin zirin zirin igiyoyi masu duwatsu masu daraja sheƙin Daimond da sukayi Dinning area ɗinshi a madadin labule.
A hankali yasa hannunshin kan na'urar CCTV camera dake liƙe a gefen inda yake ajiye key, wanda duk abinda za'ayi a falon zai gani.
Cikin sanyi yace.
"Uhummm Umaymah kiyi mata faɗafa, ta dena hawan ƙawara kan mutanen masarautar Joɗa, ta kiyayi kanta da faɗa da magautana zasu ilatata.
Bata san komaiba a kaina ta tsaya matsayin baƙuwa Umaymah zafa suyi mata illa".
Ya ƙare mgnar a hankali.
System ɗinshi dake kan Dinning table ɗin ya jawo.
kana yaja kujera ya zauna ya fara haɗa na'urar.
Ita kuwa Umaymah a hankali tace.
"To ya zatayi tunda ƙaddara ta kasantar da ita matsayin matarka, ko ita kurmace dole sai sun nemi yi mata illa sun sabautata.
Dole kasata cikin jerin mutanen da ka zame musu GARKUWA a masarautar Joɗa, tunda ita dai matarka ce, amanarka kuma".
Shiru yayi yana jinta yana mai kallon fuskar System ɗinshi date ɗin shekaran jiya ya shiga.
ai kuwa Shatu ya fara cin karo da ita tana share falon da goge ko ina.
Sai kuma lokacin da suka shigo ita da Jamil da Hibba suka nufi bedroom ɗin sa.
A hankali yace.
"Uhmmm Umaymah sai anjima zan kiraki".
To tace kana ya katse kiran.
Ido ya zuwa System ɗinshi.
tsaki yaja karo na forko da yaji da ya haɗa na'urar da cikin ɗakinshi.
Gashi yanzu baya ganinsu sai dai ihun Hibba, da fitowa da tayi da gudu ta kira Ummi da yadda suka shigo da Aunty Juwairiyya.
Kanshi ya gyaɗa lokacin da yaga sun fito a hankali ya rufe System ɗinshi.
Dafe kanshi yayi yana nazari.
Ya dade a nan sosai kana ya koma ɗakin shi.
Da dare misalin karfe sha ɗaya na dare saura.
Shatu ta kalli Hibba dake konce tuni tayi bacci.
Yasa ta miƙa a hankali ta nufi ɗakin Ummi.
A bakin ƙofar ta tsaya a hankali tayi sallama.
Cikin mamaki Ummi dake zaune bisa sallaya ta idar da shafa'i da wutri kenan taji sallamarta.
Juyowa tayi tare da amsawa tace.
"Shatu".
A hankali tace.
"Na'am Ummi".
Cikin mamaki tace.
"Lfy kuwa shigo mana".
A hankali ta shigo tare da cewa.
"Lfy lau Ummi, nazo wurinki ne."
"To".
tace tare da nuna mata wurin zama bakin gadonta.
A hankali ta ƙaraso kusa da ita,
Gabanta ta zauna kan sallayan cikin nitsuwa tace.
"Ummi kiyi haƙuri ko zakiyi bacci na hanaki".
Da sauri ta girgiza mata kai alamar a a.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"To Alhamdulillah".
Sai kuma tayi shiru.
A hankali Ummi tace.
"Kina buƙatar wani abune?".
Cikin nitsuwa tace.
"Uhum Ummi dama tambayarki nake son yi".
Gyara zama Ummi tayi kana tace.
"Ina jinki".
Itama zamanta ta gyara a hankali tace.
"Dan Allah Ummi in ba damuwa, dan Allah da Manzonsa ki sanar dani abinda Allah ya sanar dake a kan masarautar Joɗa mana.
Ummi kaina na kullewa da mutanen masarautar Joɗa, ban gane banbanci su da dankantakarsu da kuma. Alaƙarsu ba".
Wani irin dogon ajiyan zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.
"To Shatu ai kin gama komai tunda kika haɗani da Allah da Manzonsa.
Kuma dama nace miki ki tambayeni duk abinda baki gane ba, zan gaya miki. To