Showing 234001 words to 237000 words out of 299804 words
tayi sama tamkar zata faso boxes ɗin shi ta fito woje.
Da sauri ta juya da gudu ta nufi ƙofar fita, sabida ganin yadda abun ya miƙe fiye da yadda ya miƙe na farin.
Juya kwayar idanunsa yayi tare da binta da ido.
Ganin ta fice a guje.
Uhummm yace a bayyane kana cikin zuciyarsa kuma yace.
"Zakiyi bayani ne yarinya".
Juyawa yayi ya kifu rub da ciki.
Daƙiƙu biyu tsakani, ya kuma juyowa rigingine tare da jan dogon tsaki.
gefen damansa ya kuma juyowa amman ina duk yadda yayi babu damar kwanciya domin, ya rigada nitsiwarsa ta bar jikinshi.
Ta gama hautsuna mishi lissafi.
Ta birkitashi, ta tsokano mishi bananarsa ta hanashi salama.
Da sauri ya miƙe tsaye, bathroom ya shiga.
Yana shiga kuwa ya sakarwa kansa ruwan sanyi wai ko zaiyi ƙasa da fitinenneyar sha'awar data yunƙuro mishi, uwa zata kaishi ƙiyama.
Madadin ta kwanta sai ƙara ƙarfi da miƙewa da cika takeyi.
"Shehhhhyyt".
Ya faɗa cikin hautsunewar kwanyarsa.
A hankali ya fito, kana ya sauya boxes ɗin.
Sannan ya fito.
Komawa yayi ya kwanta amman ina abunfa yama wuce zatonsa.
Haka ya rinƙa juye-juye bisa gadon.
Kamar zaiyi hauka, to abin ya haɗe masa da yawa ga fushin da bai husheba, muddin ba ya samu ya kekketa wani abunba.
Sabida shi in ya fusata koda abincine in zaici zakaga yana taunarshi da ƙarfi kamar dai yana hucewa a kansa.
To yau kuma ga fushi ga Sha'awar data addadabeshi wacce yasan Aysha ce ta tsokano mishi ita.
Gashi kuma in a fushi yake duk abinda zai yaken mishi da ƙarfi, hakane ya ta'azzara bukatarsan.
Aysha kuwa tana fita kai tsaye ta wuce.
Ɗakin Ummi sabida ta samu ba kowa a falon alamun su Affan duk kowa ya tafi uzurin gabansa Jalal wurin aikinsa ya wuce, hakama Jamil.
Kwance ta samu Ummi a bisa gado tana bacci.
A ƙasa ta kwanta, bisa carpet,
Tana zazzare idanunta sabida gani take in ta shiga ɗakinta kamar zai biyota,
sabida sosai ya firgitata da jarumtarsa.
numfashi take fiddawa a hankali tare da lumshe idonta.
Duk da bai taɓa nuna zaiyi wani abu da itaba.
Taji tana tsoronshi yau, ko dan ganin fusatarsa da fushin da yake cikine. Oho.
Ta faɗa a hankali.
A haka dai itama bacci yayi gaba da ita.
Shi kuwa Sheykh Jabeer karo na forko a rayuwarsa da sha'awar ta gigitashi ta sashi, fita haiyacinsa.
Yayi wonka kusan sau huɗu tsakanin azahar da la'asar, sabida masifar da yakeji.
Ƙishin da yakeji yasashi fitowa falonshi, Dinning area ya nufa.
Fridge ya buɗe, babu ruwa ko ɗaya, sai madarar ruwa ta goggoni,
Ɗaya ya ɗauka, mai sanyi kana yazo gaba show glass ɗin da cups da sauran ababen buƙatarsa suke ciki,
Ya buɗe.
Bula gongonin yayi yasa a cup kana ya ɗauki ɗan galan ɗin zuba dake wurin, ya cika cup ɗin.
Spoon ya ɗauka ya jujjuya, kana ya zauna bisa Dinning chair.
Kafa kanshi yayi ya shanye shi tas.
Sannan ya miƙe ya koma bedroom.
Bathroom ya wuce.
Al'wala yayi bayan ya kuma watsa ruwan.
Yana fitowa ya buɗe drower'rsa wani sabon boxes da yasan zai matseshi ya zaro, ya saka kana yasa wani gajeren wondon a kai sabida su danne mishi Sheykh ɗinsa dake son nunawa duniya a yunwace take.
Farar jallabiya ya zura, kana ya ɗauko al'kyabba irin mai shara-sharan nan ita kuma Sky blue ya saka, sannan yasa hiramin ya fesa turare.
Kana ya fito.
Shiru falon ba kowa, haka yasa ya fice. Da ɗan sauri sabida lokacin yayi.
Kiran salla ne ya tada Ummi daga baccin da ta ɗan yin.
Da mamaki take kallon Aysha dake kwance itama tana baccin.
Sauƙowa tayi ta tsaya kana ta gyara ɗaurin zaninta sannan, ta sunkuyo kan Aysha ta tasheta daga baccin.
Da sauri ta tashi zaune tana waige-waige.
"Tashi kije kiyi salla lokaci yayi".
Ummi ta faɗa tana shiga bathroom.
To tace tare da miƙewa ta nufi ɗakinta.
Bayan sun idar da salla ne, suka fito a tare.
Kitchen Suka nufa.
A nan suka samu Sara tana jajjaga kayan miya.
Ummi kuwa tukunyar data ɗaura tun kafin taje tayi bacci ta buɗe, bul-bul haka yake bararraka a hankali sabida ta rage wutan sosai yadda ko zata kai magriba ruwan bazai kare ba.
Ƙara wutan tayi, tare dasa ludeye ta ɗan motsa ƴan ƙananan mulmulen tunkusa, wanda suketa bararraka da jan nama mai kyau da tantaƙwashi, sai ƙamshi yakeyi tuni saman ruwan ya cika da mai naman kab ya diddige ya marmashe.
Juyowa tayi ta kalli Aysha tare da cewa.
"Me zaki dafawa Sheykh?".
Matso tayi kusa da ita tare da cewa.
"Ba miyar kase za'ayi ba, ai yanaci".
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
"Eh yanaci kam, bare an kwana biyu ba'ayi ba.
Yanzu ɗebo nama mai ɗan yawa ki haɗa kifi kizo.
Ki saka.
Ke kuma Sara gyara min ganyen yakuwar nan."
To sukace baki ɗayansu.
Sara ta fara gyara yakuwar.
Ita kuwa Aysha naman tukunyar dake gabanta ta buɗe wanda sulallen naman ke ciki.
Juyewa tayi cikin tukunyar miyar, kana ta juya ya shiga Store bandan kifi ta ɗebo manya masu kyau.
Ruwan ɗumi ta zuba a ciki ta wonke ta gyarasu fes.
Kana tasa a cikin tukunyar.
Ummi kuwa tukunyar tuwo ta ɗaura.
A masallacin Masarautar Joɗa kuwa, ana idar da sallan la'asar duk, aka fara fitowa.
Affan shi cikin gari ya wuce wurin aminansa Yusuf da Aryan.
Jalal kuwa amsa kiran uban gidansu ya tafi.
Jamil da Ya Jafar ne suka dawo gida.
Suma Side ɗin su Jamil ɗin suka wuce.
Ƴan tsirarun mutane ne suka rage a masallacin wanda Sheykh yana cikinsu.
Mafiya yawa karatun al'ƙur'ani mai girma sukeyi.
Wasu kuma tasbihi sukeyi wasu kuma a kwance suke suna sauraron sautin murya.
Sheykh dake Karatun Alqur'ani cikin sassanyan murya.
Biyar dai-dai Sheykh ya fito cikin masallacin da sauran mutane.
Sabida wani irin duhu da ya fara yiwa illahirin garin Ɓadamaya ƙawanya.
Bisa alamu wani babban hadarine ke ketowa tun daga ƙasa.
Dimmmmmmm haka garin yayi, koda tsuntsaye baka ganin suna shawagi.
Gaba ɗaya kowa hanyar gidansa ya nufa.
Cikin nitsuwa bakinshi ɗauke da tasbihi yake tafiya.
A Lamiɗo da Galadima suna gabanshi.
A haka ya isa farfajiyar Side ɗinsa.
Ya kai hannu zai tura ƙofar kenan yaga an buɗe.
Gefe ya ɗan koma yana jiran mai fitowa.
Sara ce ta fito riƙe da kuloli a hannunta da alamun sun gama girki kenan.
Da sauri ta wuce saboda ganin hadarin.
Batama lura dashi ba.
A nitse ya shiga falon da sallama a bakinshi.
Ummi ce ta amsa tare da juyowa ta kalleshi.
Windows ya fara rurrufewa yana gyara labulayen.
"Hadari ne a garin namu ko?".
Ummi ta tambaya tana kallonshi.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Mai ƙarfi ma kuwa Ummi, ku rurrufe windows ɗin falon can da ɗakunan ku.
"To". Ummi tace tare da miƙewa ta nufi falon.
Gefen Aysha ya ɗan ratsa ya nufi kitchen.
Zagayawa baya yayi, ya dudduba ko ina kana ya dawo.
A inda ya barta a nan ya sameta.
Tana ta danna waya.
"Nace kije ki rufe windows ɗinki ko".
Ɗan juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"A rufe suke".
Kanshi ya gyaɗa kana ya wuce ya barta a wurin.
Lib-lib haka gari ya ƙara ɗibkewa da duhu.
In dai wuri babu hasken ƙwan wuta to ko tafin hannunka bazaka gani ba.
Da sauri ta nufi ɗakin Ummi.
A zaune ta samu Ummi tana gyara carbinta daya tsinke.
Gefe ta zauna ta fara tayata.
Shi ko Sheykh Windows ɗinsa ya rurrufe,
tare da kashe komai na wuta dake falonshi da Dinning area,
hasken wayarshi ya kunna kana ya wuce bedroom.
Wutan ya ɗan kunna guda ɗaya hasken yayi dai-dai misali.
Umaymah ya kira bayan sun gama mgna ya katse kiran.
Sai ya zauna bakin gadonshi tare da jawo system ɗinsa.
Gaba ɗaya hankalinsa ya meda kanta, shiyasa baima san lokacin ya tafi ba.
Shida dai-dai, hadarin ya gama haɗa gangaminsa tako ina gabas da yamma kudu da arewa da tsakiyar sararin samaniya yayi baƙiƙƙirin
Sai wani irin walƙiya mai masifar haske da akeyi tako wani sashin.
Wani walƙiyane da a haska yazo tare da wani razanenne tsawa mai firgitarwa ne yasa Aysha wani irin zabura ta takure kanta cikin cinyoyinta tare da cewa.
Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Itama Ummi abinda ta maimaita kenan sabida ta razana matuƙa.
Sheykh kuwa hannunshi yasa ya rufe system ɗinsa tare da cewa.
"Subhanallazee yusabbihu ra'adu bi hamdihi wal Mala'ikatu min khifateeh".
Ya maimaita sau uku. Wani irin kumshe idonsa yayi lokacin aka kece da ruwa tamkar da bakin kwarya.
"Allahumma saiyiban nafi'an".
Ya kuma fara mai-maita wa.
Aysha kuwa da sauran matsorata irinta ajiyan zuciya ta sauƙe, tare da cewa.
"Kai ya Allah kasa mucika da imani, wlh Ummi ina tsoron walƙiya da tsawa a rayuwata, ina son yanayin damuna amman ina tsoronshi".
Jingina kai da jikin gado Ummi tayi tare da cewa.
"Tsawa abin tsorone ƴar nan. Nima kaina naji tsoron".
Kai ta gyaɗa jinjina tare da cewa.
"Tab Ummi kema kina tsoro".
Sosai ma kuwa tace. Dariya suka sa.
Ruwane fa ake tsulawa da iya ƙarfin shi.
Miƙewa Sheykh yayi tare da kallon time a wayarshi.
Shida har ta wuce.
Gab ake da kiran sallan magriba.
Gashi kuwa ruwa aketa fesawa babu kama hannun yaro.
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
"Da ban dawo bama sai nayi salla a masallaci".
Bathroom ya wuce. Al'wala yayi kana ya fito.
Turare ya fesa, a jikinshi kamar yadda yakeyi koda yaushe.
Falonshi ya fito, dai-dai lokacin aka kuma danna wata tsawar da ta kece da ruwa mai ƙarfi.
"Ya ilahi". Yace lokacin da ya fito babban falon, shiru ba kowa sai hasken wuta.
Sanyin dake ratsa jikinshi ne yake sashi cikin wata fitinar kuma.
Baka iya jin sautin komai sai na ruwan shuuuhhhh.
Ƙofar falon ya nufa, a hankali ya buɗe.
Jingina kanshi yayi da jikin ƙofar yana kallon ikon rabbil samawati.
Ruwane tako ina yake kwaranya.
Ƙasa tasha ruwa ta ƙoshi.
Tabbas in matsoraci zai gani zaiyi zaton ƙasar ma tsastsafo da ruwa takeyi.
Magadanan ruwan duk sun cika tambul.
Dole ya maida ƙofar ya rufe, sabida.
Ruwan yayi yawanda in ya shiga kafin ya isa masallacin zai iya cutar dashi Allah ya sani baya son yayi salla shi ɗaya ba cikin jam'iba, gashi su Jalal ma yau duk basa nan ɗin.
A nitse ya juyo.
Falon Aysha ya nufa.
Shiru ba kowa sai TV'n da suka bari a kunne.
Kanshi ya ɗan juya ya kalli ƙofar ɗakinta,
TV'n ya kashe sannan ya nufi ɗakin.
Da sallama a bakinshi ya shiga,
tsayuwa yayi a tsakiyar ɗakin, ganin ba kowa.
juyowa ya ɗan yi kana, ya fito falon,
ƙofar ɗakin Ummi ya nufa,
a bakin ƙofar ya ɗan tsaya tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
Da sauri Ummi tace.
"Wa laikassalam, Sheykh ka shigo".
Kanshi ya ɗan shafa tare da yin jim kaɗan kana yace.
"Umm Aish tana nanne?".
Da sauri Ummi tace.
"Eh gata nan muna tare".
Ta ƙare mgnar tana nunawa Aysha hanyar fita alamun taje.
Shi kuwa Sheykh ɗan juyawa yayi tare da cewa.
"Ummi magriba ta kusafa".
Miƙewa Ummi tayi tare da cewa.
"To Sheykh".
"Aish". Ya kira sunan a mutunce.
A hankali tace.
"Na'am".
"Kizo".
Yace yana mai juyawa.
Miƙewa tayi ta fito.
Da ɗan sanɗa ta isa gefenshi tare da cewa.
"Gani".
Juyowa yayi ya ɗan kalleta sama da ƙasa kana yace.
"Je kiyi al'wala kizo ɗakina muyi salla, bazan samu zuwa Masallaci ba".
Cike da gamsuwa da mgnar sa ta ɗan karya wuya tare da cewa.
"To amman zanyi wonka kafin nan".
Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa.
"To Kiyi sauri kada lokacin yayi baki fitoba".
To tace kana ta nufi ɗaukinta.
Shima ya wuce ya nufi Side ɗinsa.
Kai tsaye bedroom ya wuce.
Babban sallayarshi ya shimfiɗa musu a tsakiyar ɗakin kana ya zauna a wurin, tare da lumshe idonsa ya fara bita.
Ita kuwa Aysha Kai tsaye bathroom ta wuce.
Ruwa mai ɗan zafi sosai ta haɗa, bayan tayi Brosh wonka ta farayi mai rai da lfy.
Sosai ta cuccuɗa jikinta lungu da saƙo kamar ko wani lokaci tana gama wonkan tayi al'wala kana ta fito.
Tana fitowa ta wuce gaban dreesing mirror, gashin kanta ta taje ta gyarashi ta tubkeshi a ƙeyanta sabida saurin da takeyi bata tsaya kitse jelarba.
body lotion mai ɗan karen ƙamshi ta shafa a jikinta, kana ta shafa humranta mai sassanyan ƙamshi.
Kasan cewar yanayin Weather'n garin ya sauya ko ina yayi sanyi iska mai sanyi nata busawa tana kaɗawa da sassayan ruwane yasa.
Ta saka dogon wondon blue jeans sai kuma tasa wani Baby top fari wanda ya lafe a jikinta yayi mata cib-cib kana ta ɗaura wani pink jacket wuyanshi da tattausan suma fari, sai dai jacket ɗin ba irin ƙattin nan bane ƴar cafalce dai-dai da jikinta kuma ya tare mata sanyin.
Gaban dreesing mirror ta koma wasu turaruka masu ƙamshi guda biyu ta fesa.
Kana ta zato wani ƙaton hijabinta Black blue mai ɗan karen kyau da sheƙi, ta zurashi har ƙasa ko idon sawunta bazaka iya ganiba.
Sallayarta ta ɗauka kana ta fito da ɗan sauri ta nufi Side ɗinsa.
Ganin baya falone yasa ta wuce bedroom da sallama a bakinta.
"Wa laikissalam".
Ya amsa mata lokacin da ta turo ƙofar ta shigo.
A gogon hannunshi ya kalla tare da cewa.
"Iso muyi lokacin na tafiya."
To tace tare da ƙarasowa tsakiyar ɗakin.
Sallayan dake hannunta ya kalla tare da taɓe fuska kana yace.
"Duk sallayan dake ɗakin nan bazasu isheki bane sai kinzo da naki?".
Girgiza kai tayi alamun a a.
Hannunshi yasa ya amshi sallayar, kana ya juya ya fuskanci gabas.
Ita kuma ta ɗan matso gefenshi ta tsaya daga bayanshi kaɗan. Ganin ta kimtsa ta nitsu yasashi tada kabbara.
Masarautar Joɗa kuwa, an dai kira salla amman ba'a samu mutane da yawa ba sabida laruran ruwan sama.
Bayan sun idar da sallan ne, sukayi addu'o'in kana sukayi nafila raka'a biyu, sannan suka zauna.
Tasbihi ya ɗanyi kana ya gyara zamansa da kyau, Al'ƙur'ani dake kan durowar dake gaban wurin da yake sallan ya dauko,
juyowa yayi ya fuskanceta kana ya miƙa mata.
Kallonshi tayi tare da amsar ƙura'an ɗin.
"Ki karanta inji yadda kira'arki take".
Ya faɗa idonshi na kanta.
Shiru ta ɗanyi tare da kauda idonta daga kan nashi.
Cikin sanyi ta miƙo mishi ƙura'an ɗin".
Ba tare da ya amsaba yace.
"Bazakiyi ba, inji ki samu lada ba?".
Kai ta jujjuya kana a hankali tace.
"Zanyi".
Cikin kauda kanshi daga kanta yace.
"To bismillah".
Miƙo mishi ƙura'an ɗin ta kumayi tare da cewa.
"Ka riƙe min sai inyi kana duba min haddana yayi ko da gyara".
Wani irin sassanyan numfashin da bai shiryawa bane ya subce mishi.
Cikin nitsuwa yace.
"Ba sai na duba mikiba, kada ki damu kiyi inaji in kin ɓata zan gane ba sai ina duba surar ba".
Cikin sanyi ta ɗan ɗago idanunta ta kalleshi kana ta ruggume ƙura'an ɗin a ƙirjinta.
Lumshe idonta tayi tare da cewa.
"Wacce sura zan karanta?".
Kanshi ya jingina da jikin gado kana ya zubawa fuskarta dake zagaye da hijabin ido a hankali yace.
"Surar da kikafi jin daɗin haddarsa".
Cikin nitsuwa tace.
"Suratul Noor".
Kanshi ya jinjina mata tare da cewa.
"Bismillah".
Kai ta rausayar ba tare da ta buɗe idonta ba, ta gyara zamanta kana a hankali tayi gyaran murya tare da cewa.
"Aaoozubillahi minashaiɗani rajen.
Mismillahi rahmaniraheem.
(Suratu anzalnaha wa farad'nahah wa'anzalnaaa fihahhhhhhhhhhh Aayati baiyinati la'allakum tazakarun."
Ida nunshi ya lumshe a hankali tare da sauƙe numfashi jin yadda ta bada taƙib a wurin fihahhhhhh, kana ta rufe ƙarshen ayar da bawa Wawun iya damarsa.
A hankali ya buɗe idanunshi ya zubawa lips ɗinta su, sabida jin taci gaba da aya ta biyu.
Karatun takeyi cikin sanin ƙaidarsa da bawa ko wanne harafi haƙƙinsa tsakanin ɗauri da wasalin sama dana ƙasa da kuma wurin ja mai shida da huɗu da uku.
Sosai yake jin sautin zazzaƙar muryarta na ratsa mishi kunnuwa har zuwa ƙahon zuciyarshi.
Kanshi ya jingina da gado yana jin yadda take fitar da Tajwid da kyau da fidda Qalqala, iglab, idgham, ikhfa'a Ghunna.
A hankali ya ɗan ɗago kanshi lokacin da ta iso aya ta 31 gyaran murya ya ɗan yi,
wanda yasa ta buɗe lumsassun idanunta da sauri.
Kallon alamun tambaya ta mishi.
Kanshi ya jujjuya tare da mata alamun taci gaba.
Nannauyan numfashi ta sauƙe tare daci gaba.
Kai ya sake ɗagowa lokacin da tazo aya ta 61 still yayi gyaran murya.
Ci gaba tayi da karatun dan ta fahimci alama yake mata.
Kasan cewar suratul Noor ayoyi 64 gareta.
Aya uku ta kara kan na 61 da ya mata gyaran murya tazo ƙarshen ayar.
Da sauri ta buɗe idonta jin yace.
"Sadakallahul azeem".
Kanshi ya jinjina tare dayin murmushi.
Ita kuwa cikin sanyi tace.
"Ɓata nawa nayi?, Yah Sheykh a gyara min?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Baki ɓataba kinyi ƙoƙari sosai".
Cikin sauri tace.
"To kuma naji kayi gyaran murya".
Gyara zamanshi yayi ya fuskanceta da kyau kana yace.
"A aya ta nawa da ta nawa nayi gyaran murya?".
Hannunta tasa ta tallaɓe fuskarta tare da cewa.
"Aya ta 31 da 61".
Hannunsa yasa ya ɗan shafa gemunsa kana yace.
"Ayoyin sun kasance ɗaya daga cikin dogin ayoyin da aka ƙiyasta tsawonsu dake cikin al'ƙur'ani mai girma".
Kai ta jinjina alamun gamsuwa kana tace.
"Ayyah, wato shiyasa lokacin da nake haddarsa aya ta 31 saida na kusan sati a kanta, bappa yayi ta faɗa wai nasa wasa a gaba".
Kanshi ya jinjina kana yace.
"Sosai ma kam gskyar Bappa kinyi wasa".
Cikin sanyi tace.
"Kai a kwana nawa ka haddaceshi?."
Murmushi yayi tare da cewa.
"A kwana bakwai sati ɗaya na haddace suratul Noor".
Cikin ware ido tace.
"Kai ai ƙwaƙwalwarka ta musamman ce Yah Sheykh."
Miƙe tsaye yayi yana cewa.
"Ko?".
Eh tace tana kallon dunduniyar ƙafarshi.
Wayarshi ya ɗauka, ɗan daddan nawa yayi kana ya kara a kunne jim kaɗan ya fara mgna.
"Ayyah Ummi zanci gashinki".
Murmushi Ummi dake zaune bisa sallaya tayi tare da cewa.
"Kaza ko zabuwa?".
Juyowa yayi ya ɗan kalli Aysha kana yace.
"Zabuwa, Ummi ta gasu da kyau".
Cikin sakin fuska tace.
"To Sheykh bari inyi sallan isha'i".
To yace kana ya katse kiran.
Ya dawo ya zauna.
Ummi kuwa
har ta zauna sai kuma ta tashi.
Ta nufi kitchen a cewarta kafin tayi sallan zabuwar ta sulala.
A gudanta haka ta wonketa fese.
Kana tasa a tukunta, sannan tasa al'basa, kanamfari citta tafarnuwa kaɗan sai kurry, sannan tasa Maggi da gishiri kaɗan, sannan ta ɗaura a wuta kana ta wonke hannunta ta koma ɗakinta.
Ruwa kuwa har yanzu tsugashi akeyi kamar ba gobe.
Tana gab da shiga falon ne ta jiyo muryar Jalal.
"Ummi".
Da sauri ta juyo tare da cewa.
"Yauwa Jalal ɗaukar muku abinci tun ɗazu ku nake tunawa".
Kanshi ya sunkuyar yana kallon yadda yake ɗigan ruwa.
Dinning table suka nufa.
Foodflaks ɗin ya ɗauka tare da plate kana ya juya ya fita da sassarfa.
Yana fita Ummi ta meda ƙofar ta rufe kana ta koma ɗakinta.
A can ɗakin Sheykh kuwa.
Kallonta yayi tare da cewa.
"Bappa ya baki tabsir a kan surar ne?".
Da sauri tace a a.
A gogon hannunshi ya kalla kana yace.
"Kina son ki san abinda Allah madaukakin sarki yake cewa a Suratul Noor ɗin?".
Da sauri tace.
"Eh sosai ma."
"To tashi muyi sallan isha'i sai in fassara miki ita ko a taƙaice".
To tace kana ta miƙe.
Bayan sun idar da sallan isha'i sukayi addu'o'in kana ta miƙe tayi shafa'i da wutri".
Sannan ta zauna tana tasbihi.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta kana ya meda kai yaci gaba da Addu'o'in.
Ummi kuwa tuni ta fita tazo kitchen.
Gashin tukunya mai masifar daɗi da ƙamshi tayiwa zabuwar.
Bayan ta kwashe robon, ta sake sata ta hasata da kyau.
Gaba ɗaya gidan ya cika da ƙamshi mai tada yunwa.
A wani kekyawan Foodflaks tasa dangwaleliyar zabuwar kana tasa, romon mai cike da ɗan-ɗano