Showing 186001 words to 189000 words out of 299804 words

Chapter 63 - GARKUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

17 Jul 2024

111417

safe.

Sheykh ya kuma ɗauko wani zam-zam ɗin da ganyen magarya guda bakwai,
Yazo yana mata tofin cikin ruwan.
Yana mgnar zuci.
"Uhum jiki yayi sauƙi zamu huta da koken masifa da shogoɓar tsiya".

Koda ya gama yaje ya ajiye a Fridge kana yazo.
Ya shiga wonka kasan cewar yau Monday ne tushen aiki ko nasara na tsoronta.

Ya fara kimtsawa.

Ita kuwa a falon bayan sunyi breakfast,
suka dawo nan cikin falon, juyowa tayi ta ɗan kalli Umaymah dake shigowa falon tace.
"Uhum Umaymah ruwan fa ya ƙare".

Shigowa tayi ta zauna gefenta kana ta kalli hannun ya saɓe sosai.
"To kije ki gaya mishi mana, ai bai fitaba, tashi kije da sauri kada ya fita baki gaya mishi ba".

To tace kana ta miƙe ta nufi can.


Tana shiga yana fitowa.
A hankali ta koma gefe ta tsaya.
"Ina kwana". Tace mishi ido a ƙasa

Ta gefen idonshi ya kalleta tare da cewa
"Lfy ya jikin?."

"Da sauki". Tace kana ta ɗan kalleshi tare da cewa.
"Yah Sheykh!".
Ido ya ɗan zuba mata kana yace.
"Na'am!".

hannunta ta ɗan sa ta shafi fuskarta kana tace.
"Uhum dama maganin nawa ya ƙarene shiyasa nace bari in gaya maka".

Hannunshi ya miƙo tare da cewa.
"Inga hannun".

Ɗago hannun tayi ta miƙa mishi.
Amsar hannun yayi kana ya juyo ya nufi tsakiyar falon.
Tana biye dashi abaya.
Bisa kujera ya zauna tare da nuna mata gefenshi.
Zama tayi, duk yana riƙe da hannun,
ɗan sunkuyowa yayi ya fara karanta Suratul Baqra yana tofa mata, yana sa yatsunshi biyu yana ɗan murza hannun a hankali-hankali, ido ta ɗan rumtse tare da motsoshi jin yana ɗan jan hannun.

Wash tace a hankali.
Ɗan ƙara murza hannun yakeyi yana tofa mata.
Hannun hagunta tasa ta damƙi damtsen hannunshi na dama.
bai kulata ba yaci gaba da jujjuya mata hannun dan ya lura tana barin hannun a ƙage wuri ɗaya ko yaushe tana naɗe dashi.
Murza hannun yakeyi da ɗan janshi yana miƙar dashi da ɗan ƙarfi.
Wani irin bubbuga sawunta tayi tare motsoshi da kyau.
Tsakanin sawunshi tasa cinyarta ta dama.
kana tasa hannun hagun nata ta maƙaleshi.

duk ta kanainayeshi tako ina.
zuface ta fara keto mata tako ina na jikinta,
Ajiyan zuciya ta fara sauƙewa jin ya sake mata hannun.

Kanta ta manna a damtsen hannunshi tana maida numfashi.

Shi kuwa shiru yayi yana jin yadda take maida numfashi.
Kusa 6 minute kana a hankali yace.
"To ɗan sakeni in kin gama hutawa ko".
A kunyace ta ɗan zame jikinta ta janye cinyarta.

Miƙewa tsaye yayi yana gyara al'kyabbar jikinshi.
goran ya ɗauko a Fridge ɗinsa kana ya miƙa mata.
Amsa tayi kana suka fito a tare.

Affan suka samu da matarsa Mami.

Suna fitowa Affan ya miƙa tare da miƙa wa Hamman nashi hannu bayan sun gaisane yace.
"Ya mai jikin dai?".

"Alhamdulillah jiki da sauƙi".
ya bashi amsa

Mami kuwa a hankali ta zame ta ɗan rusuna cikin girmamawa tace.
"Barka da safiya Hamma ya mai jiki".

Hannunshi ya kai ya ɗan shafi kan ɗansu Karami Aliyu tare da cewa.
"Lfy lau Alhamdulillah jiki da sauƙi. ya yaran?".

Suna lfy tace tare da kallon Aysha dake murmushi jin Affan na cewa.
"Aunty Aysha ya jikin dai yanzu kam hannun bazai faɗi bako".

Murmushi tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah da sauƙi".

Sallaman su Umaymah Sheykh yayi ya tafi.

Murmushi Mami tayi cikin son matar Hamman nasu tace.
"Ina kwana Aunty Aysha".

"Lfy lau".

"Ya jikin naki". Tace tana kallon hannunta.

"Alhamdulillah jiki da sauƙi sosai ma".
Ta bata amsa.
Tana zama kusa da ita, tasa hannun hagun ta amshi Aliyu wanda Dr Aliyu sukayiwa mai suna.

Affan ne ya ɗan kalleta tare da cewa.
"My Aunty ga iyalin nawa.
Ƙanwar Yusuf aboki nane yayar matarshi Zahra ce kuma."

Cikin fara'a da son Mami tace.
"Ayyah yayi kyau Allah ya ƙara zaman lfy da zuriya mai Al'barka".

Murmushi yayi tare da cewa.
"Amin tare daku, mu yanzu wannan na uku fa, ai munyi ƙoƙari ko Umaymah".
Cikin dariya Hibba tace.
"Kai Ya Affan abinma ƙoƙari ne kenan".
Dariya sukayi duka kana sukaci gaba da hira.
Aysha tana jin gamsuwa da gskyar Mami fiye data Aunty Juwairiyya.
Ranan dai anan Mami ta wuni.

Haka dai taci gaba da amfanin da ayatul shifa da zam-zam da ganyen magarya.

Cikin ikon Allah da izininshi.
Cikin kwanaki goma sha biyar hannun nan ya warke ya koma garau.
Har tana shiga kitchen ayi aiki da ita.

Hakane yasa Umaymah ta fara shirye-shiryen komawa tana mai jin sanyi kaɗan a ranta.

Yau kwananta ashirin da zuwa, kuma yaune zata koma.
To fa batun ƙomar da zatayi da Hibba ne yasa.
Aysha taji babu daɗi.

Allah yasani ta saba da Hibba sosai.
Ganin yadda ta koma ne yasa Umaymah ta ɗan zauna kusa da ita cikin lallami tace.
"Kiyi haƙuri Aysha kinga badon makarantar Hibba ba dana bar miki ita.
Yanzuma duk an gama mata komai na karatun zata tafi SS1 harma yan uwanta sun fara zuwa.

Kuma kema an kusa janye yajin aikin da University's Suka tafi, nayiwa Jazlaan mgna ana komawa kena zaki koma kici gaba da karatunki kewan zai ragun miki.
Rafi'anki zata dawo itama".
Cikin sanyi tace.
"To Umaymah ki bar mana ita mana, sai in gayawa Yah Sheykh ya sama mata wata makarantar a nan".
Murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
"Abbansu bazai yarda ba Aysha".
Cikin sanyi tace.
"Uhumm Allah sarki to shikenan Umaymah.
Amman wlh gidan zai mana babu daɗi ko Ummi".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Gsky kam Aysha zamuji kewar Hibba".

Ita kuwa Hibba tana tsaye gefen Jalal ne.
Da alamu wani abun yake nuna mata a wayarshi.

Jamil kuwa murmushi yayi tare da cewa.
"Uhum in tayi tsami dai maji".
Hararanshi Jalal yayi tare da cewa.
"Namu ƙamshi zaiyi ba tsamiba, ko Hibba".
Murmushi ta ɗanyi tana share hawayenta, duk da rarrashinta da yakeyi kan kada tayi kuka.
Har yake nuna mata text message ɗin daya turawa Hamma Jabeer ɗin su cewa.
"Yana son Hibba".

Kowa yasan Hibba na masifar son Ya Jalal ɗin.
Duk abinda yakeyi burgeta yakeyi.

Tun yana kaucewa har dai shima ya gane yana sonta ne.

Shi kuma Jamil sarkin latsi yaje can yace, i love You yaje can ya kuma cewa haka har yau bai tsaida matsaya ɗaya ba.
Kuma soyayya ta hanashi maida hankali kan aikinshi.

A hankali Aysha ta sunkuyar da kanta ganin hawayen Hibba na zuba.

Shi kuwa Sheykh Jabeer ido ya zuba mata.

Lokacin da taga Umaymah ta miƙe tace.
"To Ummin Jabeer Allah ya sadamu da al'khairi".

Amin Amin Ummi tace cikin kewarta tun kafin ta tafi.

Hibba kuma ruggume Aysha tayi tare da cewa.
"Aunty Aysha zanyi kewarki sosai".
Ta ƙarashe mgnar murya na rawa.
Tuni hawaye suka tsinkowa Aysha.
Aunty Juwairiyya ma sai ga hawaye.
cikin danne zuciya Umaymah tace.
"Ha Juwairiyya harda ke a kukan so kuke in tafi nima ina kukan ko".

Kai Juwairiyya ta jujjuya.

Ya Jafar kuwa shiru yayi yana kallonsu.

Shi kuwa Sheykh idonshi ya maida kan tab ɗin shi dake hannunshi.

Aysha kuwa.
Cikin son danne kukanta tace.
"Nima haka Hibba zanyi rashinki sosai.
Sai yaushe zaki zo kuma".

Cikin zubda hawaye tace.
"Aunty Aysha auren Ya Haroon ya kusa, ai zaki zo, bai cika wata biyu ya rage bama".

Cikin sanyi tace.
"Allah ya kaimu".

Amin Amin sukace kana suka fita suka tafi.

Suna fita Aysha ta koma ɗakinta.
Tana kuka.

Ummi da Aunty Juwairiyya da ya Jafar kuwa a falon suka zauna.

Sauran kuma duk yan rakiya ne sun fita.

Daga Side ɗinsa, sashin Hajia Mama taje ta sallameta kana ta wuce sashin Lamiɗo suma ta sallamesu sukayi mata fatan isa lfy kana ta tafi.

Ummi da Saratu suka shiga kitchen.
Ita kuwa Aunty Juwairiyya ta koma sashinta itama.

Koda suka dawo rakiyar bata fitoba.
Kasan cewar magriba tayi ne,
sukayi al-wala suka tafi masallacin.

Itama Ummi taje ɗakinta.

Ita kuwa Aysha yau tana hutun sallan.
Dan haka taci gaba da konciya.

Har akayi isha'i tana konce.

Koda suka dawo kai tsaye Side ɗinsa ya wuce.
Jim kaɗan ya fito yacewa Ummi.
"Bari inje Lamiɗo na nemana".

"To sai ka dawo".

To yace ya fita.

Ita kuwa Aysha, kiran da akayi mata a wayane yasa ta ɗanyi murmushi.
Muryar Junainah taji tana cewa.
"Adda na ya hannunki".
Cikin jin daɗi tace.
"Alhamdulillah ƙanwali ya worke yanzu kam ina Ummey na".
Cikin jin daɗi tace.
"Gata nan".
A hankali tace.
"Ummey na nayi kewarku, ina jina kamar bani da kowa nawa a duniya.
Gashi Hibba ma yau ta koma".

Murmushi Ummey tayi tare da cewa.
"Ke kuwa kikeda kowa naki a duniya, gaki ga salihin mijinki da Al'amin ya dawo yana yaba mana kamalarsa kowa naki sun gamsu da zaɓin da Bappanki ya miƙi.
Gani ga Bappanki ga Abboi ga Ninnanki gasu ya Ahmad sannan ga dengin mijinki masu sonki
Gashi kuwa munji lbrin su Ya Gaini".
Ta ƙareshe mgnar dan son kontar mata da hankali.
sabida basu wani ji lbrin su Gaini ba.
Cikin jin daɗi ta gyara konciyarta tare da share hawayenta.
"Alhamdulillah Ummey na godewa Allah. Ina suke?".
Cikin sanyi tace.
"Suna wata rugar FULANI dake ƙasar Senegal, yanzu ana ƙoƙarin a tabbatar ki cire damuwa a ranki ki sasu a addu'a kinji ko".
Cikin sanyi tace.
"To Ummey na ina sha Allah zan sasu.
Kuma zan roƙi Yan Sheykh ma ya samin su a addu'o'in shi".

Cikin jin daɗi tace.
"Yauwa to yafi. Ga Bappanki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Bappa na ina wuni".

"Lfy lau Shatuna ya jikinki".

"Alhamdulillah Bappa na worke".

"Masha Allah, to Allah ya ƙara mana lfy".

"Amin Amin tace."

Kana sukayi saida safe.

Tana katse kiran Ummi dake zaune gefenta tace.
"Taso muje kici abinci kinji ko kije ki gayawa Sheykh damuwarki ya saki a addu'o'in shi.
Domin addu'ar miji ga matarsa bata da hijabi".
Kanta ta gyaɗa cikin gamsuwa kana ta miƙe ta fito.

Kaɗan taci abincin. Sannan taje tayi wonka, tasa doguwar rigar bacci kana ta zurma hijabin ta.
Ta nufi falonshi.

Shi kuwa Sheykh lokacin ya dawo daga wurin a
Lamiɗo
Inda yake gaya mishi, akwai zagayen rangadin da zaiyi rugagen Fulanin ƙasar gaba ɗaya.

A cikin wata mai kamawa.

Koda ya dawo wonka ya shiga,
Ya fito ɗaure da towel a ƙirjinshi zuwa saman guiwarshi.

Mai ya shafa tare da fesa turare.
Kana yasa wani tattausan gajeren wonɗo mai ɗan faɗi amman ƙasamshi robar a tsuke take.
Yana riƙe da rigar bai saba.
Yaga kiran Umaymah ya shigo.

Wayar ya ɗaga bayan sun gaisa ne take ce mishi sun isa lfy.

A hankali ita kuma Aysha ta turo ƙafar bedroom ɗin ta shigo.

Ido ta zuba mishi sama da ƙasa a karo na forko kenan da ta ganshi babu riga a jikinsa.
Damatsan hannunshi ta zubawa ido zuwa kan ƙirjinshi da tattausan gargasa tsilli-tsilli ya mishi ƙawanya a farar fatarshi.

Shi kuwa ido ya zuba mata dan rabonta da shigowa ɗakinshi yafi kwana goma.

Umaymah kuwa cikin murmushi mai sauti tace.
"Ina ɗiyata, tanata kuka ko?".

A hankali yace.
"Gata".
Wani irin farin cikine ya rufe zuciyar Umaymah tasan burinsu bazai tabbataba muddin babu shaƙuwa da kusanci tsakanin Sheykh da matarsa.

Cikin jin daɗi tace.
"Bata wayar".

Uhum yace kana ya miƙo mata wayar.
A hankali ta iso gabanshi kusa dashi gab-gab ta tsaya.
wayar ya miƙa mata yana kallon yadda take matsoshi.
Amsar wayar tayi ta kara a kunne tare da yin sallama.
Kana idonta kuma yana kan zanen macijiyar dake konce har kan cikinsa zuwa saman haƙar-ƙarinshi.

Da Ido yabi wurin da take kallon.
Fuskarshi ya haɗe tare da ɗaga ƙafarshi zai ja da baya.

Sai kuma ya tsaya cike da mamaki ya kalli hannunta da tasaka ta kamo bakin robar gajeren wondon dake ƙugunshi.

Hannunshi yasa ya bugi hannunta,
Amman sai ta ƙara matsoshi.
Cikin sanyi ta....!




Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta number nan da nake whatsapp da ita, 09097853276 ba hoton katin zaki turoba, ba kuma TRANSFER ɗin katin zakiyi minba, ba kuma BTU ba, numbers ɗin katin zaki rubuto ki turomin. In kuwa special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min screenshort na shaidar biyanki ta wannan number tawa ta whatsapp 09097853276.
Kada kiyi min TRANSFER ko BTU na kati wlh in kinyi ba ruwana.


By
*GARKUWAR FULANI*
Ta ƙara matsowa gabanshi.
A hankali tasa ƴar yatsarta ma nuniya dai-dai inda taga kan macijin.
Wurinda shi kuma yake masifar yimishi ƙaiƙayi.

Hannunta ɗayan kuma ta maidashi ta riƙe bakin robar gajeren wondon dake ƙugunshi.

Ido ya zuba mata, cike da mamaki da kaɗuwa, da al'ajabi to me hakan me zatayi.

A hankali ta fara bin zanen kan macijiyar tana danna yatsarta, tanayi ƙasa da yatsar.
Wani irin yam-yam haka tsikar jikinshi ke tashi tana zubawa wani irin abu yakeji yana zir-zir-zirrrrr cikin jikinshi gaba ɗaya, abune da bai taɓa jin makamancinsa ba a rayuwarsa.

Cikin wani irin masifeffen da kasala daya diro mishi ya buɗi bakinshi a hankali yace.
"M.. me h hakan.".

Manna kanta tayi da ƙirjinshi ta kife kunnenta dai-dai kan ƙahon zuciyarshi dake harbawa da sauri-sauri dib-dib dib-dib.

Cikin wata muryar data ganar dashi,
ba ita bace, bata haiyacinta mutanenta ne a kusa tace.
"Kayi shiru da Allah".

Kanshi ya sunkuyar a hankali.
Idonta a lumshe hawaye na zuba.
Cikin raunin muryar tace.
"Wurin yanayi maka ƙaiƙayi wasu lokutan ne?".

"Uhummmmmm". shine abinda kawai ya iya furtawa.

Ita kuwa ƙara shigewa jikinshi tayi.
tare da cewa.
"To kayi wa kanka jinyar wurin mana.
wannan zanen yana daga kan babbar yatsarka har zuwa nan.
Yana bin jikinka, kayi ma kanka aikin irin wanda kayi wa Aysha a ciwon hannunta.
Kana sha kana shafawa a wurin.
Zai bar jikinka zai ɓace duka.
Yanzu dai baya ci gaba da tafiya,
tunda Aysha ta tone aikin".
A hankali yace.
"Yau kuma zuwa kika sakeyi kenan? Bazaki bar jikinta ba kenan kike nufi? Sai ki biyota har ɗakina dan baki da tsoron Allah".
A hankali tace.
"Inada tsoron Allah wlh nima musulmace Kamarku.
Kafurun iska ko mugu bazai taɓa iya ratso cikin sashin kaba.
Sabida ka wadata wurin da ambaton Allah.
Ko yaushe madadin kallace- kallacen tv na banza da wofi karatun al'ƙur'ani kake sawa.

Duk sashin gidanka majigine na ƙura'an.
Ni ba muguwar iska bace.
Bana sata faɗuwa, ko kuka bare ihu.
Bana samata koda ciwon kai.
Ina kuma kareta ne ga wasu ababen cutarwa
wasu lokutan idonta kan iya ganin abinda ba kowa ke ganiba. Wanda wannan baiwar tace tun tana ƴar ƙaramarta"

Cikin dakekkiyar murya yace.
"Ki bar jikinta bana so.
Kina sata yin abinda in tana haiyacinta ba yinshi zatayi ba."

Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Shike nan na tafi, amman in buƙatar zuwana yayi zaka gane nazo.
abinda ma babu wanda ya taɓa gane ina jikinta sai kai daga nayi mgn sai ka gane.
Zan tafi, amman tanada buƙatar daya kawota wurinka.
Zata roƙekasa yayunta a addu'o'in kane.
sabida sun ɓata tsawon lokaci har yau babu lbrinsu."
Cikin haɗe fuskarshi yace.
"Na sani ai, ba sai kin gaya minba, Ni nan nasan komai a kan matata, nasan abinda ya faru da yayunta jeki kawai".

Atishawa tayi a hankali.
Sai gashi ta narke a jikinshi tayi lib ido a lumshe alamun tayi bacci.

A hankali ya gyara tsayuwarshi.
Tallabeta yayi da kyau.
Hannunshi yasa ya cire hijabin jikinta.

A ranshi yake mgna.
"Na fahimta kenan iyayenta ma, basuma san tanada wata iska a jikinta ba.
Shiyasa basu sanarba kafin a ɗaura auren".
Ido ya lumshe yana goge wannan ayar tambayar da ya bugawa Bappa cikin ƙoƙolwarshi na ya aurar da yarshi ba tare daya sanar musu tanada al'matsutsaiba kamar yadda shariya tace.

A hankali ya zauna bakin gadon da ita.

Yana nazartan abubuwa da dama.

Ya fara fahimtar wasu ababen a kanta musamman da yake Junaidu ya labarta mishi komai abinda ya sani a kan Shatu da Ba'ana lokacin da suke asibitinshi Valli.
konciya yayi a gefen daya kwantar da ita.

Kana yasa hannunshi ya kashe wutan ɗakin.

Ido ya lumshe ba tare da yayi baccinba.

Ita kuwa Aysha a hankali ta farka daga baccin, ido ta ɗan buɗe.
tabbas kam tasan tazo ɗakin shi kuma tasan ta ganshi babu riga daga nan kuma bata kuma sanin meke wakana ba.
cikin sanyi take juya kwayar idonta.
A hankali ta kalleshi yana konce yayi rigingine, cikin sanyin murya alamun baccin tace.
"Yah Sheykh! Yah Sheykh!".
A hankali ya ɗan juya kwayar idonshi ya kalleta.
cikin sanyi yasa hannunshi ya jawota jikinshi.
Kan ƙirjinshi ya kwantar da ita.
Yana mai jin wani irin baƙon yanayi yana game dukkanin sasan jikinsa gaba ɗaya.

Shiru tayi jikinta na wani irin sassanyan tsuma can ciki-ciki.

Cikin sanyi tace.
"Zan kwanta".

Cikin sanyi murya can ƙasa yace.
"Yanzu a tsaye kike ai".

Ya bata amsa a daƙile, shirun ta kumayi.
Shi kuwa gyara kwanciyar tasu yayi.
Tare da jawo blanket ya rufesu.
kana ya fara Addu'o'in yanayi yana tofawa a tafin hannunshi yana shafawa a fuskarta da sassan jikinta.
Idanunta ta lumshe yanaji sanyin tattausar fatar hannunshi.
A haka sukayi bacci, ɗaki ɗaya gado ɗaya borgo ɗaya pillow ɗaya a liƙe a jikin juna.
Karo na forko kenan da wannan kusancin ya samu tsakaninsu.

Washe gari kuwa.
Lamiɗo ya ƙara neman Sheykh akan batun tafiyar da dole zaiyita.
Shi kam yace zai tura wasu.
Dan yana son zuwa aikin haji,
Amman fir tsohon nan yaƙi.
Ya haɗashi da Abbanshi dole ya haƙura.


Washe gari da safe.
Mami matar Affan tazo, ita da Zahra'n Hamma Yusuf.
Bayan sun gaisane tace.
"Ga ƙanwata Zahra matar Yusuf".
Murmushi Aysha tayi tare da cewa.
"Ayyah ai kuna kama fa".
Da sauri Mami tace.
"A a na fita kyau duk gidanmu itace mummunar mu fa".

Dariya Zahra tayi tare da cewa.
"A daba".

Nan Aunty Juwairiyya ta shigo sukaci gaba da hira,
Ummi da Saratu suna kitchen.

To haka dai mafi akasarin lokuta Mami kanzo susha hira.

Tofa nan kewar ke ɗan raguwar mata, wani lokacin kuma ta kira Bappa susha hira ko ta kira Rafi'a ko Junaidu taji lbrin Rugar Bani.

Yau sallan layya saura sati biyu.
Kuma gobene Sheykh zai fita.
dole kuma tafiyar da motace bazai yiwu ta jirgiba.
Tunda rugogin manyan Arɗaɓe zai ziyarta wanda cikin dazuka suke.

Yana zaune a falon Lamiɗo shida Abbanshi da Galadima.
"Ka gama shiryawa ko Muhammad?".
Abba ya tambayeshi cikin kula.
Kanshi ya ɗan gyaɗa tare da cewa.
"Eh".
Lamiɗo ne ya ɗan shafi kan shi tare da cewa.
"Itama iyalin taka ta gama kimtsawa ko?".
Da sauri ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
"Ta kimtsa taje ina ɗin?".
Abba ne ya bashi amsa cikin bada umarni yace.
"Ta kimtsa ku tafi tare, dole tare zakuje".
A hankali yayi ƙasa da kanshi tare da cewa.
"Dan Allah Abba tafiyar da nima ba sonta nakeyi ba, a kuma sake haɗani da wani jidalin".
Fuska a haɗe Abba yace.
"A bayanka akace ka goyeta ku tafi ne?".
A hankali ya jujjuya kai.
Cikin yanke hukunci yace.
"To ku tafi tare Muhammad bana son musu a kan yarinyar nan duk abinda akace kayi dan Allah kayi tunda ba wanda ya saɓawa shariyar musulunci za'ace kayi ba.
Baka san abinda muke zaton samu ta sanadinta ba.
Muna ganin nasarori kan matsalarmu. Kaje da matarka kaji ko Muhammad na".
A hankali yace.
"To Abba ba komai in dai zakayi farin cikin hakan zanje da itan".

Kanshi ya shafa tare da cewa.
"Allah yayi maka al'barka".
Amin Amin yace cikin jin daɗi.

Kana ya sallamesu ya fita.
A falo ya samu Ummi ita ɗaya tana kallon wata tashar da aka saka wa'azin shi.
Cikin sanyi yace.
"Ummi gani gaki sai kin kalleni a tv".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ina ƙaruwa ne ai".
Kanshi ya jinjina tare da ɗan kallon gefe da gefe kana yace.
"Ummi ina take?".

Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"Tana ɗakinta".
Kanshi ya gyaɗa kana yace.
"To Ummi Lamiɗo yace wai dole da ita zamuyi tafiyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login