Showing 114001 words to 117000 words out of 299804 words
tace.
"Bari inje inzo da Angon."
Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
"To kuyi sauri dai".
To tace kana ta fita.
A can sashin Sheykh Jabeer, kuwa.
Da alamun wonka ya fito, a nitse yake kimtsawa, cikin wani fitinenne yadi mai taushin gaske.
yadin Royal blue ne mai masifar kyau.
rigar half jomfa yar tsukekkiya,
tsaki ya ɗan ja lokacin daya gama dai-dai-ta zaman rigar a jikinshi sabida tayi kib-kib a jikinshi har kamar ta ɗan matseshi.
Wondon kuma irin mai iya kuibin sawune, irin sakun wondunan ahlul sunna.
a hankali ya iso gaban drower'n da hulunanshi da hirami da baƙin abun saman hiramin ke jere a ciki.
Har yasa hannunshi bisa wani farin hula, sai kuma ya sunkuya ya ɗan kalli. Kanshi.
Fuskarshi ya ɗan tsuke, sai kuma ya ɗan juyo jin muryar Haroon yana cewa.
"Wow masha Allah, gsky kayi kyau, Please ka fita haka mana, ka ganka ɗan saurayi mai jini a jika, amman in kasa al'kyabbar nan, sai kwarjininka yayi yawa yaseen.
Ni kaina sai inji ina shakkarka,".
Kai ya ɗan shafa kana yasa hannunshi ya zaro hiraminshi fari da baƙin zagayen.
ɗaya marfin drower'n ya buɗe tare da zaro wata dakekkiyar al'kyabbar fara mai ratsin blue na zaren aiki gaba da bayanshi.
Gaban gado ya dawo yana warware al'kyabbar tare da cewa Haroon.
"In na fita a haka ai ji zanyi kamar babu tufafi a jikina, sabida sunyi min kaɗan."
Ya ƙarishe mgnar yana zura al'kyabbar a jikinshi.
Masha Allah, Haroon yace.
Kana ya matsoshi yana tayashi gyara zaman al'kyabbar yana cewa.
"Duk shigar da kayi tana maka kyau, in na ganka ba al'kyabbar sai inga kamar kafi kyau.
In kuma kasa al'kyabbar sai inga kafi kyau".
Baice dashi komaiba yaci gaba da gyara sakun hiraminshi,
saida ya gama dai-dai-ta hiramin sai ya juya ya nufi, wannan drower'n da hulunanshi ke jere a steps biyu na sama.
Biyu na ƙasan kuma jerin takalmanshi ne.
Fararen takalma masu taushi ya saka ƙirar Gucci,
Zara-zaran yatsunshi sarari sabida ba sau ciki bane ba kuma half cover bane.
turare ya fesa, tare da sa hannunshin ya shafa sajenshi.
Kana ya kalli Haroon daketa ɗaukar shi hoto.
Cikin tura baki Haroon yace.
"Na bari, nasan yanzu zakayi ƙorafi, yanzu ina zakaje?".
Yana fita yace.
"Valli Hospital, akwai yaron da zan duba aikin da akayi mishi".
Bayanshi ya biyo tare da cewa.
"To sai ka dawo".
Ni zamuje wurin Budurwar Jamil taga babban yayanshi.
Wani kallo ya mushi tare da cewa.
"Allah ya shiryeka babban kobo".
Dariya Haroon yayi tare da cewa.
"Eh naji na yarda, zanje yaro ya samu matsala da ita tanata wahal dashi ba dole inje in dai-dai-ta musu matsalar ba".
Juyowa yayi jin abinda Haroon yace cikin sakin gajeren murmushi yace.
"Uhumm yaushe ka zama luwali, bani da lbri, to kai taka matsalarma yaushe ka warware ta, kun iya cikamu da zancen ku ƴan soyayya ne, kuma bakuma san yadda ake soyayya da magance matsalolin ta da tattalinta gudun ta lalaceba".
Wani irin dariya mai sauti Haroon yayi tare sara mishi.
Da sauri ya juya, da nufin tafiya,
sai kuma yaga Umaymah na tsaye a gabanshi.
Hannunta tasa ta kamo nashi tare da janshi suka fara tafiya.
Cikin sanyi yace.
"Oh Umaymah ina zamuje?".
Haroon kuwa baki ya taɓe tare da cewa.
"Wlh gobe zan koma in sha Allah, komai sai an nunawa mana ƴan ubanci".
Dariya Umaymah tayi tare da cewa.
"Allah kiyaye hanya".
Da sauri yace.
"To na fasa tafiya".
Suna gab da fitane yace.
"Umaymah sakeni karmu fita a haka".
Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"To taho".
To yace mata kana yabi bayanta.
Suna tafiya cikin ƴar faffaɗan hanyar da bishiyoyin namijin gwanda yayi musu ƙawanya,
shiyasa wurin yayi sanyi.
A hankali ya kalleta lokacin da suka iso.
Bakin ƙofar Gimbiya Aminatu.
tare da cewa.
"Umaymah me zanyi a ciki?".
Hannunta tasa ta kamo nashi.
Kawai ta kutsa kai ciki. Dole ya bita a baya.
Yana saka ƙafarsa cikin falon yaji zuciyarshi ta buga,
da ƙarfi, lokaci ɗaya ta fara harbawa da sauri-sauri.
Cikin sanyi yace.
"Umaymah barni a nan".
Bata kulashi ba taci gaba da janshi tayi har bakin ƙofar falon Lamiɗo.
wani irin rumtse idanunshi yayi yin yadda zuciyarshi ke barazar fashewa.
Da sallama a bakinta, suka shiga.
Yayinda Lamiɗo da Abbanshi suka amsa mata.
Cikin wani irin azabebben bugun da zuciyarshi keyi, yasa ƙafarshi cikin falon.
yayinda Umaymah ke riƙe da hannunshi tana mishi jagora har zuwa gaban Lamiɗo da Galadima da Abbanshi da kuma Malaminshi Malam Abubakar.
Kana ta tsaya dashi kusa da Aysha tare da rusunawa.
Yayinda shi kuma cikin fargabar yadda ƙirjinshi keyi ya rusa a hankali ya zauna bisa tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a wurin.
Dib, dab, dib, dab, dib, dab. Haka zuciyarshi keyi.
yayinda itama Aysha da bai lura da ita Bama haka zuciyarta keyi,
sabida jin an mutun ya zauna kusa da ita.
A hankali ya lumshe idonshi, sabida bugawar da zuciyoyinsu keyi a tare yasa, ƙarfin nashi bugun ya ɗan ragu kaɗan.
Cikin nitsuwa ya kalli Abbanshi kanshi a sunkuye yace.
"Barka da safiya Abba".
Cikin kula yace.
"Barka dai".
Sai ya kuma kalli Malamin nashi cikin kamala yace.
"Allah hokke sabbugo, Malam Barka da zuwa ya gida?".
Cikin nitsuwa Dattijan yayi murmushi tare da cewa.
"Alhamdulillah Sheykh Jabeer ya hidima".
Alhamdulillah yace, kana ya kalli Lamiɗo da Galadima.
sai kuma ya kauda kanshi.
murmushi Galadima yayi tare da cewa.
"Mu bazaka gaishemu ba kenan?".
Ɗan tsuke fuskarsa yayi tare da cewa.
"Gaggawa dai aikin shaiɗan ne".
Murmushi Lamiɗo yayi sabida ya fahimci duk abinda zasuyi,
sai ya cisu gyara ta kuma fuskar gsky.
Galadima ne yace.
"To ni bari in gaisheka Ina kwana".
Kanshi ya jinina mishi tare da cewa.
"Kayiwa kanka tanadin lada ashirin, a madadin kaɗan da zaka samu in ni na ɗaga maka gaisuwar.
Lfyta lau Alhamdulillah."
Ya ƙarishe mgnar da amsa gaisuwar.
Dariya sukayi kana, ya kalli Lamiɗo a daƙile yace.
"Ina sauri dan inada aikin yi, menene kasa aka jawoni nan".
Ya ƙarishe mgnar a hankali yadda Abbanshi da Malaminshi bazasu jiba.
Kana ya ɗan muskuta ya matsa gefe yayi nesa da Aysha sabida wani tsalle da yakeji zuciyarshi nayi, a madadin bugun da takeyi kafin ya zauna kusa da ita.
Cikin zuba musu ido.
Lamiɗo yayi murmushi sabida sunyi masifar dacewa da juna, shigarsu da ta zamo iri ɗaya tayi matuƙar yi musu kyau.
Cikin wasa irin na kaka da jika yace.
"Ga amaryar taka baku gaisaba, ku gaisa sai ka kaita kuje ka gabatar da ita".
Fuskarshi a haɗe yace.
"Hakan addinine ko al'ada?".
Da sauri Galadima yace.
"Al'adace kuma sai kayi ta".
Ta gefen ido ya kalli Galadima tare da cewa.
"Da ba Galadima za'a bakaba, da sarkin raya al'adu za'a baka".
Shiru yayi jin Abbanshi na cewa.
"Allah ya bamu nisan kwana, kaima watan watarana a gabanka yaranka zasuyi min haka Muhammad".
Cikin yin ƙasa da kai cikin girmamawa da karrama mgnar mahaifin nashi yace.
"Sun isa! Suyi maka haka in barsu".
Murmushi Malam Abubakar yayi tare da cewa.
"Kamar yadda ka isaba".
Shiru yayi gane manufarsu.
Jin duk sunyi shiru ne, yasashi ɗago kai ya kallesu.
Suma shi suka zubawa ido, da sauri yayi ƙasa da kanshi.
Ita kuwa Aysha shiru tayi tamkar ruwa ya cinyeta, tanajin yadda suke musayan kalamai. Sai dai bata fahimtarsu domin, tuno nata ahlin.
Gyaran muryan da Abbansa yayine yasashi ɗago kai ya kalleshi.
Cikin bada umarni Abba ya nuna mishi Aysha tare da cewa.
"Kama hannunta kuje, ka gabatar da ita, ka fara daga sashin ƙannen Lamiɗo, sai na Mamanku, daga nan kuje wurin Gimbiya Saudatu,
dama sauran matansu Babanku Nasiru".
Bisa dole yace.
"To kana ya yunƙa ya miƙa,
da sauri Umaymah ta miƙe tazo ta miƙar da Aysha.
kana ta kamo hannunta ta miƙa mishi alamun ya riƙe hannunta.
Cikin tsuke fuskarsa da kwaɓeta tamkar zai ɗaura hannunshi a ka ya kurma ihu.
Ya zuba mata ido. Muryar Abbanshi ce ta katse tsayuwar da yayi kamar an dashi.
"Riƙe hannunta ku je". A hankali ya ware tafin hannunshi da Umaymah ta kamo
kana lokacin guda yaji zuciyarshi tana tsalle da harbawa, kamar dai tana mararin wani abu.
Hannun Aysha Umaymah tasa mishi cikin nashi tare da meda yatsunshi ta rumtsesu.
Dam-daradam-dam haka zuciyarshi tayi wani masifeffen bugun mai kama da na aradu kana tafara wani irin tsalle.
Ita kuwa Aysha, wani irin tsuma jikinta ya fara lokacin da taji tattausan yatsun hannunshi da fatar tafin hannunshi ya rumtse nata.
Hannun wani irin masifeffen tsoro da kunyane suka diro mata, a lokaci guda.
Shi kuwa Sheykh wani irin asirtace kuma ɓoyeyyen dogon ajiyan zuciya ya sauƙe mai sanyi, jin gaba ɗaya zuciyarshi ta koma ta nitsu tabar wannan tsinkewar da bugawar da tsalle tayi lib a cikin ƙirjinsa.
Jin muryar Jakadiya ne yasa, Sheykh Jabeer, yin ƙarfin halin ɗaga ƙafarshi ta dama.
Jin ya ɗan yi gabane yasa itama, ta ɗaga ƙafarta ta hagu, sai hakan ya bada wata dama ta musamman, ya zama suna ɗaga ƙafafuwan su, a tare kana suna taku a jere.
Sai dai shi ɗin ya ɗan kereta kaɗan.
"Masha Allah. Tabarakallah,". Sune kalaman da Umaymah ke Maimaitawa, lokacin da take biye dasu a baya.
Lamiɗo da kanshi da Galadima sunga wani irin dacewa na musamman a tsakin Muhammad Jabeer da Aysha.
Abba kuwa murmushi yakeyi mai baiyana jin daɗi.
Malam kuwa, Addu'o'in yaketa jero musu na fatan al'khairi da zaman lafiya da nitsuwa da samun zuriya ɗayyiba.
A hankali suke taku yayinda kowa zuciyarshi ke bin takun sawunsa,
A haka suka fito babban falon Gimbiya Aminatu nan suka samu Ummi. Tana ganinsu ta miƙe da tsauri tayi gabansu, hadimai hudu cikin na Gimbiya Aminatu kuwa, sukayi bayan Umaymah dake bayansu.
Shi kuwa Sheykh Jabeer suna fitowa yayi wani irin saurin sake hannunta tare da janye nashi,
Sabida shi ji yake tsikar jikinsa na tashi tamkar ya riƙe wutan lantarki ne sabida masifar tsuma da yaki naman jikinsa nayi.
Murmushi Umaymah tayi ganin still dai suna tafiya a jere a jere suna wani irin taku mai ƙayatarwa.
Suna fitowa, suka samu sallama a bakin mashigar wurin.
Nan ya shaida musu, duk sashukan gidajen anje anyi sallama dasu an kuma basu daman shiga.
Tafiya kaɗan sukayi daga sashin Gimbiya Aminatu, ta gefen hagunshi,
suka ɓullo farfajiyar wani babban part,
Jakadiyarsu na gaba suna biye da ita a baya, Umaymah na biye dasu.
A hankali suke taku cikin ƙasaita hadimai da fadawa na mara musu baya.
Suna shiga ciki, suka samuwa wata dattijuwar tsohuwa mai tarin shekaru.
Cikin murmushin da muryar tsufa tace.
"Malamai magada annabawa, lallai yau inada babban baƙo da babbar baƙuwa."
A hankali suke tafiya har zuwa gabanta, inda take zaune bisa tattausan carpet hadimanta na kewaye da ita.
wanda biyu daga cikinsu, suka tashi da sauri suka kawo ababen motsa baki suka jera a gabansu.
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya kalli tsohuwar da take matar ga Galadima.
Cikin kula yace.
"Barka da safiya Innano". Cike da kula tace.
"Barka dai Malam Muhammad, mun samu ƙaruwa ko".
Kanshi ya gyaɗa mata a hankali haka yasa duk basu ganiba sai ita da yake gabanta.
"Cikin muryar tsufa tace.
"Allah ya sanya al'khairi. Ya baku zaman lafiya. Yasa matarkace iya rai da mutuwa. Ya azurtaku da zuriya ɗayyiba."
Da Sauri Umaymah ta amsa da Amin Amin hakama sauran baki ɗayansu.
Ita kuwa Shatu, cikin saisaita nitsuwarta ta ɗan kalli tsohuwar tare da cewa.
"Ina kwana".
Murmushi tayi tare da kai hannunta ta kamo hannun Shatu, tafin hannunta ta buɗe ta zuba musu ido, na yan wasu ɗakiƙu kana tace.
"Lafiya lau, ya baƙu ta?".
A hankali tace.
"Alhamdulillah". Jakadiyarsu ce ta ɗan rusuna tare da cewa.
"Mun barki lfy".
Kai ta gyaɗa kana tayiwa hadimanta umarni su miƙo kyautar da take gadon masarautarsun ce farin gyale ne mai kyau da taushi.
Umaymah ce ta amsa ta miƙa hadiman dake bayanta.
Kana suka miƙe suka fita.
Daga nan sashin wani sashin na kusa dashi suka shiga.
Wanda yake sashin ƙannen Lamiɗo ne.
Saida suka gama da sashukan manyan masarautar.
Kana suka nufi sashin Hajia Mama.
Tuni tasan da zuwansu.
haka yasa ta kimtsa ta tsara komai na tarban surkar tata.
A matsayinta na uwar ango.
Har can cikin bedroom Ummi ta wuce, su kuma suna biye da ita a baya.
Suna shiga suka sameta, zaune bisa kilishi,
Batool na gefenta, wacce son ganin amaryar ne, ya hanata tafiya.
Hadimanta kuma na zagaye da ita.
Suna shigowa ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi.
Cikin tsananin baiyana farin cikin ta, ta nunawa Jabeer kusa da ita.
a hankali suka iso suka zauna gabanta.
Umaymah kuwa gefenta ta zauna.
Ummi ko na bayansu hadiman kuma suna can falo.
Hannunta tasa ta kamo hannun Jabeer.
Cikin fara'a tace.
"Alhamdulillah Muhammad Jabeer, Allah ya sanya al'khairi ya baku zaman lfy".
To shifa suna ɗaure mishi kai, da tarin addu'o'insu na al'khairi, shi dai ba sonta yakeba ba kuma zama da ita zaiba,
to me zai wahal dashi da zaice Amin Amin.
Umaymah da Jakadiyarsu ne suka amsa da Amin Amin kamar dai yadda sukayi a sauran wuraren.
Batool ce ta kalli Shatu cikin isa tace.
"Amarya ki ɗago kanki mana kinga gaban uwar mijine kike".
Duk da taji mgnar Batool sai tayi kamar batajiba,
Abubuwan ci da sha dake gabansu ne,
Hajia Mama ta jawo wani ɗan ƙaramin tray da cups biyu ke kanshi.
Gyara zama tayi da kyau, tana murmushi ta kalli Shatu dake mgna a hankali.
"Ina kwana Mama".
Cikin kula tace.
"Lfy lau ɗiyata ya baƙun ta".
Alhamdulillah tace, tare da tsurawa madara da zumar da Hajia Mama ta zuba musu cikin kofu nan ido.
a hankali ta ɗan muskuta kaɗan tayi baya, tare da ƙara yin ƙasa da kanta.
ita kuwa Hajia Mama, kofin ta ɗauka ta miƙa mata.
Tare da cewa.
"Gashi ɗiyata amshi kisha."
Cikin sanyi murya can ƙasa ta girgiza kanta tare da cewa.
"Alhamdulillah".
cikin nuna kulawa da so Hajia Mama ta ƙara miƙo mata kofin tare da cewa.
"A a ɗiyata, amshi kisha, wannan al'adace ta masarautar Joɗa, dole in marabceki dashi."
Kai ta kuma girgiza alamun ya isheta.
da sauri Umaymah ta matso kusa da ita tare da cewa.
"A a Shatu amshi kisha kinji ko?".
Cike da mamaki ta ɗan kalli Umaymah ta gefen idonta.
jin Umaymah na ƙoƙarin matso da kofin kusa da itane yasa tayi mgna cikin ɗan ɗaga murya tace.
"Bana shan madarar".
wani irin kallo mai cike da damuwa Hajia Mama tayi mata tare da cewa.
"Subahanallahi, bakya sha, kuma, amai yake sakine? Ƙa'idane da dole kishi".
Ta ƙarishe mgnar cikin damuwa.
Ita dai Shatu shiru tayi idonta na bisa kofunan madarar.
Ummi ce ta matsota tare da cewa.
"Shatu amshi kisha koda kurɓa ɗaya ne".
Cikin rawan murya tace.
"Bana sha".
Jin alamun rawan murya irinta an takura mutum ne, yasa duk sukayi cirko-cirko suna kallon Madarar.
Zuwa can Hajja Mama ta sauƙe wani bahagon ajiyan zuciya, kana ta ɗauki ɗaya kofin ta miƙa Jabeer tare da cewa.
"To gashi kai kam kasha naka".
Zamanshi ya ɗan gyara tare dasa hannun damansa ya amshi kofin.
Wani irin zaro ido Shatu tayi.
Kallon kofin takeyi tamkar zata maida kwayar idanunta cikin kofin.
duk jikinta tsuma yakeyi, wani irin masifeffen bugawa ƙirjinta yakeyi da ƙarfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer zaune yake riƙe da kofin, ya fuskanci Hajia Mama da kyau.
Ita kuwa Hajia Mama hannunta tasa ta kamo ɗaya hannun Jabeer da baya riƙe da kofin.
Kana ta miƙowa Shatu hannun alamun ta miƙo mata hannunta.
Ƙara runsunar da kanta tayi tamkar bata gane me take nufiba.
Cikin murmushin Hajia Mama tace.
"Kawo hannunki ko ɗiyata".
A hankali ta ƙara maida hannunta baya,
dai-dai lokacin kuma Jabeer ya ɗago kofin ya kai saitin bakinshi da niyar zai sha.
cikin hikima ta muskuta ta ƙara matsowa jikinshi da sauri ta ɗago hannunta kamar zata miƙawa Hajia Mama hannun.
sai kuma ta ɗan kaikaice, ta buge c...!
Ƙaƙa tsara ƙaƙa
By
*GARKUWAR FULANI*
Ta bugi kofin madarar, ba zato ba tsammani, Jabeer yaji kofin ya tsumbce mishi.
ya faɗi gefenshi.
Tass ya fashe madarar ta kwaranye a ƙasa.
Cikin sauri da tsuƙe fuskarshi ya juyo ya kalleta.
Itama ɗin shi take kallo.
Ido cikin ido sukayi da ita a karo na forko a rayuwarsa duk da yasan sun taɓa haɗuwa.
Kallon kwaɗayye mai irin bakin Junainah, tayi mishi.
Sai kuma ta janye ƙwayar idanunta cikin nashi da sauri.
Sabida wani irin kallon da taga yanayi manata.
Umaymah da Ummi kuwa, kallon junansu sukayi, cikin yanayin son gane ya akayi kofin ya faɗi dan basuga sanda ta ta ɗan buge mishi hannunta.
Hajia Mama kuwa cikin tashin hankali da kiɗima ta kalli Umaymah tare da cewa.
"Akwai matsala, ita batasha, shi nashi ya kwaɓe."
Sai kuma ta maida dubanta ga Shatu cikin alamun damuwa tace kawo hannunki na dama."
Still maida hannun nata tayi baya, ba tare da tace komaiba.
Ummi ce ta ɗanyi ƙasa da murya tare da cewa.
"Miƙa mata hannunki ku gaisa".
Murya can ƙasa tace.
"Yana ciwo". Ta ƙarishe mgnar da jin haushin kanta da ƙaryar da suka satayi.
Batool ce ta kalleta sama da ƙasa kana cikin gyatsine tace.
"Umaymah ai wannan ba irin matar Sheykh bac."
Sai kuma ta haɗiye ragowar mgnar dan ganin wani irin kallon daya watsa mata na alamun.
Ki kama kanki da kiran sunana a bakinki.
Wani dogon ajiyan zuciya Hajia Mama ta sauƙe cikin fargaba tace.
"Tashi Kuje ku gaida sauran. Allah yayi muku al'barka ya baku zaman lafiya.
In sha Allah babu komai".
Kamar jira Shatu takeyi a basu izinin tashi tayi fit ta miƙe.
Da tarin mamaki Umaymah da Ummi suka miƙe, dan abubuwan da suka faru da yanayin Shatu, ya tsaya musu a rai.
Shima Sheykh Jabeer miƙewa,
yayi kana suka jere suka fita.
Sai dai Shatu na ɗan sassarfa.
Cike da mamakin wannan abun suka nufi Side ɗin Gimbiya Saudatu.
A falonta suka sameta tana hakimce bisa kujerar ikonta,
ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana karkaɗa ƙafar cike da izza.
Ummi na gabansu suna bayanta Umaymah na bayansu.
Cikin rusunar da kai Jakadiyarsu ta durƙusa gefenta tare da cewa.
"Barka da safiya Gimbiya Saudatu, ga Sheykh Jabeer ya kawo miki da amaryarsa!".
Cike da izza ta ɗan kallesu sama da ƙasa, kana ta nuna musu gabanta.
Alamun su zauna, cikin sanyi Shatu ta rusuna tare da sunkuyar da kai ta zauna gabanta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin kallo yayi mata, mai cike da ma'anoni,
gefen ta ya kalla inda wata kujerar ke kusa da tata komansu iri ɗaya.
Taku yayi cike da ƙasaita ya isa gaban kujerar, kana ya juyo ya zauna kan kujerar.
Hakan yasa ya fuskanci Shatu da Umaymah.
zaman ƙasaita da isa yayi.
wani mugun kallo take binshi dashi har ya zauna.
Ita kuwa Shatu kanta a duƙe tana murzam ƴan yatsunta.
Umaymah ce ta ɗan taho zata zauna kusa da ita, a hankali ya jujjuyawa Umaymah kai, alamun. A a kada ta zauna a ƙasa.
gane manufarsa ne, yasa ta zauna bisa kujera.
Shiru kakejin falon, sai takun sawun hadimanta dake kawo ababen motsa baki, suna ajiyewa gaban Shatu.
Suna gama jerawa suka koma can gefen.
Jin shiru-shirun yayi yawane yasa Shatu ɗan ɗago kwayar idanunta, ta kallesu.
A ranta take mgnar zuci.
"Ikon Allah, ohoho ni Shatu wannan wanne irin bahagon gidane, mai cike da sarƙaƙiya da tubkar baƙin zare,
To ko dai ita wannan ɗin kurmace."
Muryar Gimbiya Saudatu ce ta ƙatse mata tunani ta,
cikin isa da izza ta kalli Sheykh Jabeer, kana ta juyo