Showing 273001 words to 276000 words out of 299804 words

Chapter 92 - GARKUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

17 Jul 2024

111373

sa tsuntsuwar Boleru a gaba Magauta na musu dariya.

Sai da asubane sun kabbarta yin salla asuba, tsuntsuwar ta tashi ta fire, Bata tsaya cikin masararutar Joɗa bama ta fuskanci ƙasar Cameroon ta nausa tayi can yankin Yahunde.

Ɓacewar tsuntsuwar nan shi yafi tada musu hankali.
Anyi neman duniya har an gaji.
Ba ita ba dalilinta har dai aka ruggumi ƙaddara.

Sai dai Lamiɗo da Galadima da Jadda da Umaymah sunci gaba da bincikawa da neman mafita.

Lokacin da Sheykh ya kammala digirin sa na farko yazo.
Nigeria nan ne ake faɗa masa abin da ya faru a lokacin tashin hankalin da kiɗimar rayuwar daya faɗa ciki baya misaltuwa wani babban tashin hankalin kuwa shine daya iske ya Jafar baya magana sai addu'o'in da yin karatun al'ƙur'ani mai girma da kuka, dakuma ya buƙaci yaje yaga Mamey'n shi a yadda take ɗin a tsuntsuwar ta ɗin, nan ake faɗa masa ai tun lokacin da abun yafaru da kwana ɗaya rak ta fire tabar cikin masarautar Joɗa.

Ranar Sheykh kuka kamar karamin yaro ya rungume Jamil Jalal Yah Jafar da tun isowarsa Jafar ɗin ke ƙanƙame da hannun sa yana karatun yana kuka haka sukayi ta kuka Hajia Mama na tayasu.
Ranar tazamo musu tamkar sabuwa.

Tun daga wannan lokacin kuma sai yazamo kamar an cire hankalin Abba'n su a kansu madadin a lokacin ya janyosu jikinshi yazame musu Garkuwa dan suɗan sami sassaucin kunar dake cikin zuciyarsu sai yariƙa nisanta kanshi dasu.
Shi kansa bai san dalilin hakan ba,
duk wannan kuma acikin shirin Hajia Mama ce, kwana ɗayan da tsuntsuwar tayi tafire ma ita takoma gun bokanta tace tanaso tsuntsuwar tabar cikin masarautar gaba ɗaya dan taga sun dage da magungunan.
Dariya bokan nata yayi tare da cewa.
"Ke shar-shar banza da kika samu ma ba Addu'o'inku na musulmai sukeyiba ai da tuni sun karya sihirin".
Cikin jin daɗi tace.
"Aini gaba ta kaini da hankalin su baije ga canba".


Lamiɗo kuwa lokacin ya ƙara jan Sheykh a jiki sosai.
Sabida bayanin da Malam Musa yayi musu na cewar a sanadin aurensa da ba fulatanar daji mahaifiyarsu zata dawo.
Haka yasa part in da a ka bashi kusa da Garden inda tsuntsayen suke.
aka buɗe mishi wata kofa taciki in da daga cikin part ɗin direct zai sadashi da cikin Garden ɗin.

Bai wani jima sosai a Nigeria ba yakoma Madina sabida jin yakeyi ya tsani ƙasar Nigeria Especially Masarautar Joɗa.
Koda ya koma sosai ƴan uwan Sitti suka ga canji a rayuwarsa saida aka dage da addu'a kafin ya dawo hayyacinsa.
Daga nan suka ƙara kula ta musamman a kanshi suka zame mishi uwa uba ƙanne yayu sukeyi mishi komai.
Yakanyi shekara uku huɗu bai zoba.
Sai dai yana yawan sawa Jadda yazo mishi da Jamil Jalal Yah Jafar da Affan yawanci duk shekara zasu zo sau biyu hajji da umra wani shekaranma sau uku.
Ya maida hankali sa kan karatunsa da addu'a Allah ya baiya mishi Mameynshi a duk inda take ko a tsuntsuwar Boleru shi zaici gaba da rainonta da kula da ita iya rai da mutuwa.

Daga nan yayi master's madadin ya dawo ya haɗe. PHD ɗinsa. daga nan yadawo Nigeria'n bisa tirsasawar Lamiɗo da Jadda da Galadima da Umaymah dake matsayin Uwa.
Dole ya yarda ya dawo ya sanyawa ƙannensa ido wajen kula da su dakuma tarbiyyan su dakuma neman hamaifiyar su da kula da yayansa yakuma zame musu Garkuwa Da kuma bincikar Magautansu wanda dalilin haka ya samu matakin SS wanda dama shine burinsa to kuma Alhamdulillah ya gane komai Especially da ya samu damar aikin SS wanda dama burinshi kenan a dole Lamiɗo ya sashi karantan likitancin.

A kwai sabo ƙauna tausayi da shaƙuwa da tsama tsakaninshi da kakanun nashi sosai.

Hajia Mama kuwa da gayya ya barta da wayonta ita tanayi mishi kallon biri shi yana mata kallon ayaba.

Dama kuma malam Musa.
Ya faɗa musu cewa sanadin Sheykh ɗin ne Mamey'n zata dawo yabasu lbrin iya abinda Allah ya sanar mishi cewa bata rasuba tana raye kuma tajuye daga tsuntsuwar dasuke tunani tadawo mutum tuntuni tun bayan tafiyarta da watanni.

(Rayuwa kenan takan iya sauyawa a duk san da Allah yaso domin shi yake juya daƙuƙu i zuwa sa'a wuni zuwa dare kwana zuwa shekara ya fidda matacce a cikin rayayye ko ya fidda rayayye a cikin matacciya)

Ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe baki ɗayansu da suke cikin falon.
Bayan ya Jafar yagama basu labarin yadda akayi da abinda ya sani har Mamey'n su ta juye ta zama tsuntsuwa da kuma yadda akayi shima yakoma baya magana sai kuka da karatu.

Gabaki ɗaya parlour'n ya kaure da ambaton sunan Allah da yiwa uban giji tasbihi.
Ita kam Mamey sai murmushi takeyi tare da maimata.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah alakulli halin".

Affan kuwa kuka yakeyi tamkar ransa zai bar gangar jikinsa.
Cike da rauni Sheykh ya jawoshi jikinshi ya ruggumeshi suna masu zubda hawaye baki ɗayansu.
Cikin rauni da tausayin irin kukan ƙuncin da Affan keyi Lamiɗo ya gyara zama tare da yin gyaran murya kana ya juyo ya kalli Bappa tare da cewa.
"Ka bamu labarin yadda akayi.
Aishatu tashigo hannun ku".

Ai kuwa kaf hankalin jamar parlour'n yadawo kan Bappa dan kowa nason jin yadda akayi Mamey'n tashigo hannunsa gaba ɗaya shi suka zuba ido.

A hankali yayi Bappa gyaran murya tare da gyara zamanshi kana ya ɗago hannunshi ya nuna Shatu da yatsarsa manuniya kana yace.

"Shatu itace sanadin.
Dan a lokacin da tashigo hannun mu mu muna mata kallon tsuntsuwar Boleru ne tsawon kusan wata bakwai muna tare da ita muna ganinta Giɗi yarona shike kula da ita saida ya zama tare suke cin abinci.

To Shatu itace ta fara ce mana ba tsuntsuwar Boleru bace mutunce ita a ranar wata jumma'a da tazo tare da mahaifin ta Alhaji Abboi wanda ni makiyayinsa ne.
Nan taga tsuntsuwar yara na son kamata su yaran damu manyan duk muna cewa tsuntsuwa ce.
Ita kuma tana cewa mutum ce.
Wanda haka yasa dole basu koma cikin birnin Yahunde a ranarba ita da mahaifinta suka kwana a gidana a Rugar Arɗo Babayo wanda nanne asalin mahaifata.
haka ta kwana tana gaɗin tsuntsuwar har dai Allah yanuna mana ikon sa da asuba tajuya ta dawo mutum a gaban idonmu,
Sai dai tana cikin larurar naƙuda.
Cikin ikon Allah ta haifu ta sauƙa lfy ta haifi ɗiyarta mace.

To lokacine mukaga sarƙar dake wuyanta.
Mai ɗauke da tambarin masarautar Joɗa kasan cewar masarautar fulɓe ce kuma mahaifin Alhaji Abboi abo kine ga Lamiɗo akan ɗan ziyarci juna kaɗan kaɗan to sanadin hakane Alhaji Abboi ya gane tambarin dake jin sarƙar na masarautar Joɗa ce.

Tofa anan muka gane cewa duk yadda akayi ita ahalin masarautar Joɗa ce.
Kuma Sarkin bakanmu ya tabbatar mana ita mutunce aikin sihirine to sai dai babu yadda za'ayi mu fuskanceku da mgnar kai tsaye tunda bamu san komai nakuba."

Ɗan tsakaita maganar yayi yaɗan ja numfashi kana yaci gaba da faɗin.

"Ni banine mahaifin Shatu ba Alh Abboi shine mahaifinta ga kuma mahaifiyarta.

Ni makiyayin mahaifinta ne.
inayi masa kiwone yana biyan.
Mafi akasari duk karshen wata suna zuwa tare da ita nan Rugar Arɗo Babayo.
To ita Shatu tanason yanayin daji rugarmu shiyasa duk sanda zaizo da ita zai zo, in zai koma kuma wasu lokutan yakan koma yabarta anan Rugarmu da yake ranar Jumma'a yake zuwa, to sai ranar lahadi da yamma Al'ameen ko wani daga cikin yayunta yazo ya ɗauke ta su koma.
Yawan zuwasu shi yasa tasaba da da yarana sosai da mai ɗakina.

To amman zuwansu da Allah ya ƙaddara lamarin Ummey ta juye a gabanta fir babu yadda ba'ayi da ita ta komaba taƙi bin mahaifinta fir taƙi tace ita zata zauna da Ummey ita ta zaɓa Junainah suna.
Wannan yasa dole mahaifinta ya koma ya barta.

To lokacin da Ummey'n Shatu'n ta faɗo hannunmu muka kuma ga wannan sarkar dake wuyanta na masarautar Joɗa shine Alh Abboi yace mu ƙaura mu dawo nan.
Nigeria kusa da masarautar Joɗa cikin Rugar Bani dan tasami kusan ci da masarautar.
to nan fa muka dawo Nigeria har da ita Shatu'n dan taƙi yar da a raba su da Ummey'n ta ashe rabo ke jawota nan.
dole iyayenta suka haƙura suka barta tare dani.
Muna dawowa nan muka sata a makarantar cikin Shikan".
Nan yaci gaba da basu labarin duk wani bayanin gwa-gwar mayar da
Shatu tayi a ka Ummey
duk sai da ya basu labari.
Ya ƙara da cewa.
"Lokacin da muka zo Nigeria da Ummey
wato (Mamey) Ba'ana naɗan shekaru sha takwas a duniya, lokacin (Parvina) wato Shatu kenan ita kuma du-du shekarun ta takwas ne,
to kafin mu dawo ma Mamey bata dawo daga haiyacin taba bata fara magana ba, lokacin da mukazo.
Nigeria Rugar Bani sai Ba'ana yace zai bata mgnin zata fara mgn kuma zata zama dai-dai sai dai zaiyi wuya ta tuna baya,
Amman zata dawo tayi mgn amman da sharadi. kasan cewar fatanmu ta tuna baya mu maidata ga ahlinta yasa mukace mun amince da sharaɗinsa wanda bamu san menene sharaɗin ba.

Shi saida ya fara bata mgnin kuma yace sai da sharaɗin in Ummey ta worke ta fara mgn muyi al'ƙawarin aura mishi Shatu.
To lokacin mu baƙine bamu san halinsa na ɓoyeba kuma burinmu da fatanmu ta worke mu maidata hannun ƴan uwanta sai muka amince mukayi mishi wannan al'ƙawarin bisa rashin sanin halin daga ranar Mata yake kiran Shatu.

Kullum Shatu ita ke zuwa gidansu Ba'ana da safe tana karɓawa Ummey magani a gunsa, dan shi tun tashin sa yake wannan cacube-cacuben nasa, so kullum.
Shike bawa Shatu magani ta kawo wa
Ummey tana sha har Ummey tadawo tafara magana sai dai bata iya tuna baya ba nan. Ba'ana'n ke ce mana duk randa taga wasu nata ko ƴan uwan ta ko wani abu nata zai yiwu tunanin ta
yadawo ta iya tuna baya."

Sai kuma ya ɗan tsagaita tare da sauƙe numfashi kana a hankali yaci gaba da cewa.
"Toh tun daga ranar ne muka fara neman hanya da dalilin da zai haɗamu daku mutanen masarautar Joɗa.
Sabida munsan aikin sihirine dole akwai Magauta sannan a gefen Ba'ana kuwa ya addabemu ya hana Shatu salama duk mai sonta sai yaga bayanshi.

To sai marigayi Cuɓaɗo ya bamu tabbacin bulalin Shaɗin masarautar Joɗa ne kawai zai karya duk wani sihirin jikin Ba'ana to kasan cewar yana sonta so na gsky bai cutar da ita in hankalinmu ya tashi kan muna tsoron ya aureta takan ce mana.
"Abinda in na gama karatuna zamu koma Yahunde sabida ita bamu sanar mata mun gano asalin Ummey ƴar ina bane gudun ita yarinyace kada tai ta gayawa wasu.

To munata son yadda alaƙa zata haɗamu sai kuma ga ƙabilar ɓachama su tasomu gaba.
Ran da muka zo nan na forko da muka ga Jamil sosai muka ƙara ƙarfafa guiwar ita ahlin masarautar Joɗa ce dan akwai kamar jini tare dashi da ita.
To da akayi faɗa kukaje mana jaje da gayya Arɗo Bani ya gaggayawa mai martaba Lamiɗo mgn dan ya tunzurashi ayi Shaɗi mu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan.

Mun dawo da ita, mu kuma samu mgnin Ba'ana to kuma Alhamdulillah duk abin neman ya samu.

Sai kuma yayi ƙasa da kanshi murya na rawa yace.

"Sai dai sanadin faɗan ni na rasa kowa nawa".
Bappa ya ƙarashe mgnar cikin rauni da zubda hawayen tuno matarsa da zaratan yaranshi.


Cikin raunin tuno ahlinshi kuka mai rauni ya rufeshi yayinda Shatuma kuka mai ƙarfi ya kubce mata hakama Ummey sabida ita dai gata ta dawo ahlinta shi kuma garin dawo da ita cikin ƴaƴanta ya rasa nashi yaran.

Cikin tsananin jin daɗi
Sheykh ya ɗan muskuta cikin tsananin farin ciki da jin daɗin da godewa Allah daya bashi damar kuɓutar dasu ƴaƴan Bappa su Gaini shima zaisa Bappa farin ciki kwatankwacin yadda ya sashi.
Cikin sauri da bada umarni ya kalli Jamil tare da cewa.
"Jamil tashi maza kaje kazo dasu".
"To". Jamil yace kana ya miƙe da sauri yafita batare da ɓata lokaciba sabida ya gano su waye Gaini.

Yana zuwa yace.
"Yah Gaini taso taso kuzo ga Bappanku da Shatu da Junainah".
Ai kafinma ya rufe baki duk sun muƙe cikin tsananin zaƙuwa suka biyo bayanshi.

Shi kuwa Bappa da Arɗo Bani da Alhaji Haro da Alhaji Umaru rauninsu ya rigada ya dawo tuno irin kisan gillar da ƙabilar ɓachama sukayi musu.

Shi kuwa Sheykh dasu Lamiɗo shiru sukayi sabida son yi musu ba zata.

Da sauri Jamil yasa hannunshi ya tura ƙofar suka shigo tare da cewa.
"Assalamu alaikum Bappa share hawayenka gasu Yah Gaini Seyo da Giɗi".

Duk sauran mutanen falon duk suka ɗago kansu.

Ido cikin ido Shatu tayi da Yah Giɗi'nta abokin tsamarta.
Wani irin yunƙura tayi ta miƙe tsaye tare da cewa.
"La'ilahaillaha Muhammadu rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam Alhamdulillah Bappa gasu Yah Gaini".
Jin kalaman Shatu ne yasa Bappa dayake sunkuye ya ɗago kanshi yana kalli bakin ƙofar shigowa ya sauƙe kwayar idanunshi kan.....!



Kuyi haƙuri da typing errors ina cikin ciwon kai nayi typing ɗin a daddafe.



Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300.
A yawan posting ne babban cinsu 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa in kin tura sai kiyi screenshort na Debit Alert ki turo min ta whatsApp 09097853276 ƴan 3oo in naki da halin biya ta Account zaki iya sayan katin mtn na ɗari uku ki copy numbers ɗin ku turo min ta whatsApp ɗin 09097853276.




By
*GARKUWAR FULANI*
[4/3, 8:39 PM] +234 806 559 0880: Ya sauƙe idanunshi kan Giɗi Seyo Gaini.
Cikin wani irin yanayin tarin farin ciki mai sanya rauni.
Wasu zafafan hawaye suka kwaranyo mishi.
Da sauri ya yunƙura ya juyo ya fuskanci al'ƙibila. Sujjadar godiyar Allah yayi kana ya ɗago yana mai zubda hawaye.
Ita kuwa Shatu da sauri ta ƙarasa garesu, kawai sai ta faɗa jikinsu baki ɗayansu, tare da sakin raunataccen kuka.
Cikin rauni da yanayin kula Seyo wa mai tausayi kamar uwa yace.
"Shatu dena kuka, mu godewa Allah".
Sai kuma ta kalli Yah Giɗi cikin sanyi ta ruggume shi tare da cewa.
"Tunda na rasaka kusa dani na rasa abokin faɗa da tsama, shiyasa lokuta da dama ina jin daɗin inyi taƙaddama da Gimbiya Saudatu dan sai yana tunamin ta ƙaddamar mu, da Yah Giɗi na abokin faɗana".
Cikin zubda hawaye shima Giɗi yayi murmushi tare da janyeta jikinshi kana yace.
"Nayi kuka a lokuta ma banbantan da bazan iya ƙididdiga ba sabida tunoki da rayuwarmu".
Hannun tasa ta share hawayenta kana ta kalli Yah Gaini wa mai matsayin Uba cikin kulawa da yanayin rayuwarta yace.
"Shatu ina Ba'ana ko mun samu nasarar rabuwarki dashi".
Da sauri tace.
"Yah Gaini Allah ya rabamu da Yah Ba'ana".
Cikin tarin jin daɗi yace.
"Alhamdulillah".
Dai-dai lokacin suka isa gaban Bappa daketa zubda hawaye.
Zama sukayi a gabanshi gaba dayansu huɗu.
A hankali Giɗi ya sunkuyo ya kwantar da kanshi bisa cinyar Bappa tare da sakin sassayan kuka a hankali yace.
"Bappa mun ganka kaida Shatu ina Innarmu ina Ummey ina Junainah ina Yah Lado?".
Da sauri Ummey tasa hannunta ta rufe bakinta jin kuka zai kubce mata.
Sai dai tuni sautin kukan ya fito.
Da sauri Giɗi ya rarrafo gabanta murmushi yayi still Ido na zubda hawaye a hankali yace.
"Alhamdulillah Ummey Junainah ina Innarmu da Yah Lado".
Cikin kuka Junainah ta faɗa jikinshi tare da cewa.
"Arnan Ɓacama sun kashe Innarmu sun kashe Yah Lado sun kashe mutane da yawa na rugarmu".
Da sauri Giɗi ya juyo ya kalli Ummey cikin tashin hankali da kubcewar kuka.
Gaini da Seyo suma kuka mai rauni suka sake ganin Bappansu yana jinjina musu kai alamun zancen Junainah hakane".

Shiru falon sukayi baki ɗayansu sai sutin kukan Giɗi, Shatu, Junainah, Ummey, Seyo, Gaini. Raunin da kukansu ya sauƙar a zuciyar Bappa ne yasa shima sakin kuka dan yau sai sukaji gaba ɗaya rasuwar Yah Lado da Inna ta dawo musu sabuwa.

Sosai Shatu keyin kuka tana durƙushe ta tanƙwashe sawunta, hakama Ummey.

Gaba ɗaya kab falon saida idon kawa ya ciko da ƙwalla.

Cikin Rauni Sheykh ya matso inda Shatu ke durƙushe gaban yayun nata, cikin sanyi ya kalli Bappa Ummey murya a raunace yace.
"Tabbas bansan irin ƙunar da kakaji a cikin ranka ba Bappa amman nasan kwatankwacin kamannin ƙunan rashin ɗa, a suman da Afreen tayi naji ciwo da ƙuna a zuciyata tamkar ban taɓa farin cikiba, nasan zafin rashin uwa, amman ban san zafin rashin mataba dan kamin gatan bani Mar'atussaliha ta zame min GARKUWA tana sani farin ciki a duk lokacin da nake cikin baƙin ciki."
Shiru yayi sai kuma ga hawaye shar-shar a idanunsa cikin rauni yace.
"Na samu komai da nake nema a rayuwata daga gareka ka bani mata ta gari, Allah ya azurtamu da samun ƙaruwar arzin haihuwa sanadinka Ummey na ta dawo.
Inama! inama! ace Inna da Lado ɓata sukayi ba rasuwa ba, da tabbas zanyi iyakar iyawata in dawo maka dasu da izinin ubangiji.
To amman wannan hurumin ubangijin sammai da ƙassaine.
Kayi haƙuri Bappa Allah ne ya baka Inna matsayin mata ya ɗauketa ya sauyama da ƴar uwarta kuma Allah shi ya baka Lado ya ɗauke shi kuma ya killace maka Seyo Gaini Giɗi, wanda wata ƙil da suna Rugar ba'a sacesu ba da an kashesu.
Gashi yanzu Allah ya dawo maka dasu.
Bappa kace Alhamdulillah ka godewa Allah da ni'imar da yayi maka sai ya ƙara maka wata a kai.
Kayi haƙuri ka bar kuka kaga kukanka na ƙara ingiza nasu".
Ya ƙare mgnar yana sa hannunshi cikin tafin hannun Shatu yana murza a hankali.
Cikin gamsuwa da jin sanyi a ransa Bappa yace.
"Alhamdulillah".
Da sauri Su Giɗi suma sukace.
"Alhamdulillah". Hakama su Lamiɗo kab falon sai suka fara mai-mai-ta hamdala.
Ai kuwa cikin ikon Allah duk ƙuna da ƙuncin da zuƙatansu keyi a take Allah ya sauƙaƙa musu shi.
Cikin gyaran murya Lamiɗo yace.
"Alhamdulillah komai yayi forko zaiyi ƙarshe duk abinda yayi tsananin tabbas zaiyi sauƙi Allah mun gode maka daka ara mana rai da lfy".
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Sheykh dake kallon agogon hannunshi sabida jin anyi kiran sallan azahar.

Cikin tarin jin daɗi Abbansu Sheykh ya matso kusa da Bappa da Abboi murya cike da tarin jin daɗi yace.
"Bappa Abboi dama duk al'ummar Rugar Bani da Rugar Arɗo Babayo ngd matuƙa Ubangiji yayi muka sakayya da gidan al'ljanna mafi ƙololuwa girma.
Shatu Allah ya dafa miki ya tsareki dake da ahlinka".
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Shi kuwa Bappa Sheykh ya kalla tare da cewa.
"Muhammad Ngd

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login