Showing 147001 words to 150000 words out of 318746 words
mai ƙarfin imani da ƙwaɗayin rahama ne kuma kawai ke iya juriyar cinyesu komai tsanani da zafin da sukazo masa da shi. UBANGIJI ya fimu sonta ai, bai kumayi shawara damu ba sanda ya bamu, idan ya ƙarɓeta a yanzu sai dai mu gode masa da ni'imar da yay mana na samunta tsawon shekaru sha bakwai a gabanmu. Dan haka faɗamin kawai”.
Baki Yoohan ya cika da iska ya fesar, zuciyarsa da ruhinsa na ƙarajin ƙauna da son baba malam har cikin jini. A komai nasa yana fatan yin koyi da baba malam. Cikin harshen turanci yace, “Uncle tanama da ranta, sai dai dama bawai mun mata aikin ainahin matsalarta bane kamar yanda nai maka bayani ɗazun kafin mu taɓata. Aikin da mukai mata zai bata taimakone kawai wajen hana ƙwaƙwalwarta goge komai da take barazanar yi, sannan zai sassauta mata raɗaɗin da takeji a duk lokacin da matsalar ta motsa, insha ALLAHU zai hana ta iya rasa hankalinta. Nayi tunanin aikin zai bata kariyar da zamu iya ɗaukar kamar watanni biyar kafin ai mata aikin gaba ɗaya, dan dole sai an fita da ita waje, a ƙasarnan bamu da isassun kayan aikin matsalarta, koma muna dasu zaka samu bana zamani bane tunda shuwagabannin namu bawai hankalinsu nakan abinda ya dace suyi bane. To a yanzu dai matsalar dana fahimta dolene ai gaggawar yimata aikin koda nan da wata ɗaya ne insha ALLAH, inba hakaba zata iya loosing memory ɗinta a koda yaushe”.
Ɗan rumtse idanu baba malam yay yana ambaton sunayen ALLAH, muryarsa da ƙoƙarin jarumta yace, “Shikenan Yahya, duk yanda kake ganin ya kamata akai kayi tunda aikinka ne, yanzu zamu iya zuwa mu ganta?”.
Ɗan jimm Yoohan yayi, kafin yace, “Eh to amma karkuzo da yawa dai”. “Babu damuwa”. Baba malam ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya.
Batare da kowa ya saniba a gidan Umm da baba malam da Hajjo suka tafi asibiti duba Nu'aymah. Yoohan da yake wani irin jin kunyarsu da nauyinsu ne yay musu rakkiya har ɗakin da Nu'aymah ke kwance. Ba ƙaramin tashi hankalinsu yayiba ganin yanda aka jajjone kan Aymah da na'urori, Hajjo da Umm harda hawayensu. Basu wani jimaba suka fito. Office ɗin Yoohan suka sake komawa. Inda ya sake musu bayanin komai dalla-dalla a nutse. Sosai suka gamsu da bayaninsa, wanda a take duk murmushi ya baibaiye fuskokinsu, suka shiga saka masa albarka da jera masa addu'oin fatan alkairi. Har wajen mota ya rakosu, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki, dan yau a asibitin zai sake kwana saboda Nu'aymah zata iya farkowa a kowane irin lokaci.
Zamansa babu jimawa Solomon ya shigo ɗakin ɗauke da takeaway da yayo masa acan hotel ɗin da suke sauka. Dan idan yazo kano abincin can kawai yake ci, sai ko yanzu da suka haɗu da su baba malam. Ganin yana waya ya saka Solomon komawa gefe ya tsaya yana sauraren yanda Yoohan ɗin ke wayar a nutse.
Magana suke da wani likita abokinsa dake a ƙasar Canada. Yana buƙatar a aiko masa da wasu allurai ne masu matuƙar tsada da zaima Nu'aymah amfani da su. Kuma yana buƙatar sune da gaggawa daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu. Shine suke maganar ta yanda za'a kaisu airport ɗin ƙasar a damƙawa wani abokinsa matuƙin jirgi da Yoohan ɗin yasan kayan zasu iso yanda yake fata. Sai da suka kammala maganarsu har Yoohan ɗin yayma Dr Androi transfer ɗin kuɗaɗen allurar take anan masu yawa daga asusunsa sannan ya ajiye wayar.
Solomon dake kallonsa cike da takaici da mamakin ganin kuɗin daya biya na alluran tamkar baisan ciwonsu ba yay saurin faɗin, “Good evening sir! Ga abinci na amso maka, naga bakaci komaiba tun breakfast ɗin safe”.
Ɗan luuuu da idanu Yoohan dake miƙewa yayi, kamar zai lumshesu sai kuma ya buɗe su akan Solomon ɗin. “Karka damu banajin yunwa. Haɗamin coffee kawai is ok for me”.
Ganin yanda ya tsuke fuska sosai ya saka Solo amsa masa da “To” kawai. Cikin bin umarni yayi masa yanda ya buƙata, acan rukunin kujerun office ɗin daya koma yana aiki a lap-top yaje ya kai masa coffee ɗin. A hankali yace, “Thanks”. Shiru office ɗin yayi na wasu mintuna, Yoohan nata aikinsa da shan coffee kamar ya manta da Solomon. Sai kuma ya ajiye kofin ya ɗago yana kallon solo ɗin. “Kaje ka kwanta, basai kazo nan da safe ba, inaga zuwa dare zamu wuce Abuja, sai ka mana booking ɗin jirgi”.
Cike da girmamawa yace, “Okay sir”. Daga haka yay masa sallama ya fice.
Solomon na isa hotel ɗin wayar Papa ya fara kira. Ba a ɗauki lokaciba kuwa ya ɗaga. Bayani ya shiga yimasa da yarensu wanda sam ban fahimci akan minene ba. Sunja lokaci mai tsaho suna wayar sannan ya kira madam Chioma itama. Itama ɗin dai magana sukai ta tsahon lokaci da wani yaren ba irin wanda sukai da papa ba. Batun yau ba na fahimci Solomon najin yare ba ɗaya ba. Kamar yanda na kula shima Yoohan ba yare ɗaya kawai yake jiba bayan turanci. Shiyyasa a lokuta da dama nakan gaza banbance shin su wane yarene wai?.
*_WASHE GARI_*
Washe gari da safe ƴan gidan su Nu'aymah sukaje asibitin suka duba Nu'aymah data sake farfaɗowa. Sai dai har suka gama abinda zasuyi suka taho basuga Yoohan ba. Yana office yana duba marasa lafiyar da suke da tsananin buƙatarsa duk da da da farko baiyi niyyar hakanba.
Suna dawowa gida kuma suka iske baƙin da basu san da zuwansu ba. Kakar Nasir data haifi babansa ce tazo daga katsina mai suna Hajiya Hassana. Sai dai suna kiranta Ananah, yayar Hajjo ce uwa ɗaya uba ɗaya, wadda ita kaɗai ce ta rage mata a duniya. Hajjo na tsananin girmamata dan itama tana ƙaunar hajjon, batason abinda zai taɓa hajjo da zuri'arta, ta zame mata tamkar uwa da uba. Itama ta tsufa sosai fiye ma da Hajjo, sai dai da yake ALLAH ya basu lafiya sosai ga jin daɗin rayuwa, ko ina suna zuwa, garama hajjo tana fama da ciwon ƙafa. Ananah kuma idanuntane dan sai da galashi take gani da ƙyau.
Tare take da jikokinta da yaranta biyu ƙannen mahaifin Nasir ɗin mata. Dama duk babbar salla anan take salla kano, ita kuma hajjo sai gab da azumi take zuwa mata can katsina tai kamar wata guda. Hakan na sakasu farin ciki sosai.
‘To yanzu kuma Nasir ya ɗaɗɗago Ananah akan batun Nu'aymah. Ko yaya zata kasance?. saimu bisu muga wane mai rabo ne zai ɗauki wannan allurar ta cikin ruwa😉?’.
Ba ƙaramin farin ciki hajjo dama duk jama'ar gidansu Nu'aymah sukaiba da zuwan Ananah. Dan yanda take son kowa a gidan haka kowa ke sonta da ƙaunarta har surukan Hajjo. Take gidan ya rikice da murna dan duk tunaninsu ta iso da wurine saboda bikin su Kubrah nan da kwanaki goma. Ciwon Nu'aymah ne ma yaɗan sanyaya shirye-shiryen da akeyi.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka shirya abinci gabansu kala-kala daga kowanne sashe. Da mamaki Ananah tace, “Wai ni banga ƙawalliyata ba ita?”. Kowa yasan Nu'aymah take nufi. dan suna shiri sosai-sosai da Ananah, saboda Nu'aymah nada sunan hajjo ma take cemata ƙawalliya.
Rufaidah ce tai caraf ɗin cewa “Ananah tana asibiti babu lafiya” a rikice Ananah take tambayar, “Asibiti kuma? Miya sameta ni Hassana ɗiyar malam Haruna”. Shiru kowa yayi ya gaza bada amsa. Sai hajjo ce tai ɗan murmushi da cewar, “Ciwonta ne ya motsa, amma Alhmdllh da sauki ma”.
Cikin jimami Ananah ta share ƴar ƙwallar data taru mata a ido, tace, “Kai duk wanda yay sanadin shigar wannan yarinya a bala'innan yayi asarar rayuwarsa wlhy, ALLAH ya saka mata, ko wanene kuma ALLAH ya hanashi farin cikin duniya dana lahira”.
Kusan a tare duk falon suka amsa da amin.
★★
Bayan sallar magriba Ananah sukaje asibiti suma suka duba Nu'aymah, a lokacin Yoohan yaje airport amso saƙon da aka aiko masa daga ƙasar canada. Hakan yasa har suka kammala suka wuce yanzunma basu haɗu da shi ba. Sai bayan wucewarsu da kamar awa guda ma ya dawo.
Kansa tsaye ɗakin da Nu'aymah take ya nufa. Solomon biye da shi ɗauke da wata madaidaiciyar bag. A ciki ya samu Nurse ɗin data gama gogema Nu'aymah dake barci jiki.
Da girmamawa ta gaida shi, Solomon kuma ya ajiye bag ɗin ya fice. Matsawa yay gaban gadon lumsassun idanunsa akan Nu'aymah da fuskarta tai wani irin fayau. Sai uban haske data ƙara tamkar mai yaron ciki. Ya kafe Laɓɓanta da sukayi wani irin jajur gwanin sha'awa, gashi taɗan tsuke bakin ya sake komawa mitsitsi.
Huci ya ɗan furzar ya janye idanunsa daga kallonta, yana faɗin ‘Bakin tsiwa’ a zuciyarsa. ya gyara kujerar gefen gadon ya zauna tare da ɗaukar bag ɗin da Solo ya ajiye ya buɗeta. Madaidaicin abu ya fiddo cikin kwali mai kama da kula, ya buɗesa sai ga ƙanƙara a sama tanata huci. a ƙasan ƙanƙarar ya zaro kwalaben alluran kusan guda guda bakwai ƴan ƙananu, yanda kwalaben suke ƴan mitsitsi sai ka ɗauka wani tarkacen banza ne. Nanko kuɗaɗene masu shegen nauyi zaune da ƙafafunsu. Sai da ya gama duba takardar dake a cikinsu kafin ya maidasu ciki ya fiddo ɗaya kawai.
Miƙama Nurse ɗin dake a ɗakin yayi, murya a daƙile yace “Kiyi mata allurar nan yanzun nan”. Amsa tayi da girmamawa. A gabansa ta buɗe syringe ta kwashe ɗan ruwan allurar da ko ganinsa bama ayi sosai cikin syringe ɗin. Shine ya nuna mata a inda zatayi. (A raina nace da idon Aymah biyu sai anyi ƙaramin yaƙin duniya na uku kafin ayi allurar na kuwa🤣).
Mintuna uku ba'a rufa dayin allurarba wani irin mahaukacin zufa ya fara tsatstsafowa a kowacce ƙofar gashi ta jikin Nu'aymah. Kafeta da kallo Yoohan dake zaune ƙafa kan ɗaya ya harɗe hannayensa a ƙirji yayi. Yanda take wani irin mutsu-mutsu kamar macijiya mai tsohon ciki ne ya sakashi sakin wani tattausan murmushi daya ƙawata cikar haibarsa da kwarjinin bautar UBANGIJI. Ya ɗan lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta yana jan ajiyar zuciya.............✍
‘Saura naji wani yace ɗan kaɗan ne😣😒. Da gobe saina ƙara rage mudu🚶🏻😑😚’.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
*Ga breakfast nan aci a hankali har dinner ɗin gobe idan ALLAH ya kaimu sai ku ɗumama😎😁⛹🏻♀️*.
No. 40
............Ƙarfe sha ɗaya na dare Yoohan da Solomon suka bar kano zuwa Abuja. Tafiyar da bata kulle awa guda ba jirginsu ya sauka. Sun iske guards ɗinsa tuni suna a airport ɗin ma, dan haka basu ɓata lokaciba wajen wucewa gida.
Kamar yanda yay tsammani ya iske gidan nasu shiru, alamar duk sun kwanta, madam Chioma kawai suka iske a falo zaune cikin kwalliyar riga da wando da sukai mata ƙyau sosai. Yanda ta zubamasa ido haka shima kallonta yake babu yabo babu fallasa. Cikin takun nasa ya ƙarasa gareta, itama sai ta miƙe tana mai buɗe nasa hannayenta alamar yazo gareta.
Gabanta yaje ya tsaya batare da ya shiga jikin nata yanda ta buƙata ba. Ya kamo hannunta ɗaya yana ɗan shagwaɓe fuska kaɗan. Cikin sanyin muryar da tabbatar da agajiye yake, da yarensu yace, “Mom na girma ni”.
Ɓata fuska tayi itama cikin wani yanayi, muryarta na harɗewa wajen fita tace, “Please my boy”. Karan farko ya saki lallausan murmushin da ya nema sumar da ita a wajen. Ya ɗora hannunsa na haggu saman tattausan sajensa ya shafa yana ɗan kauda idonsa daga gareta zuwa ƙafar benen dake a falon inda Miracle ke tsaye cikin kayan barci, ƙirjinta rungume da madaidaicin teddy bear ta wani kafesa da idanu tamkar zata haɗiyesa ta huta.
A hankali ya janyesu gareta yay wani luuuu da su kamar zai rufe sai kuma ya buɗesu yana sakin hannun Mom yaja baya. Hannayensa duka biyu ya ɗaga mata da faɗin “Sweet mom gudnit”. Kafin tace wani abu harya fara hayewa upstairs ɗin da ɗan sauran kuzarinsa batare da ya sake duban Miracle ba ya raɓa ta gefenta ya wuce.
Su duka da kallo suka bisa harya ɓacema ganinsu, mira ta share ƙwallar data cika mata idanu ta juya da gudu zuwa ɗakin barcinsu ita da joy. Wata malalaciyar harara Mom ta raka Mira da ita. Kafin ta taune lip ɗinta na ƙasa da ƙarfi zuciyarta na ƙuna fiye da yanda gangar jikinta ke tsuma.
Yoohan daya iske ɗakinsa kamar yanda yay fata komai fes bai wani zauna ba ya shige toilet. Bayan wasu mintuna masu ɗan tsaho ya fito jikinsa na ɗigar da raɓar ruwan wanka. Da sauri yaja ya tsaya ganin Mom zaune bisa sofa. A ɗan daburce yace, “Mom lafiya kuwa?”. Saurin ɗago idanunta dake akan wayarta tayi ta dubesa, dai-dai shi kuma yana ƙoƙarin saka farar t-shirt ɗin daya ɗauka. Miƙewa tai ta nufosa tana wani sakin tattausan murmushi, ta ɗauka ƙaramin towel ɗin daya fito da shi a hannu ta nufi sumar kansa alamar zata tsane masa gashinsa dake ɗigar da ruwa. Da ɗan hanzari yaja baya kaɗan yana tsuke fuska.
“Mom!!”
Ya faɗa aɗan tsawace. Jin a yanda yay maganar ne ya sakata tsayawa cak daga yin abinda tai niyya.
Da ɗan shagwaɓa yace, “Haba Mom! Miyasa kike son maidani baya ne kullum? Nifa ba Abraham bane ko Victoria Please”.
Ƙanƙance mayatattun idanunta tayi tana ɗan matsosa, cikin muryarta dake wani irin rawa tace, “Kaine kake ɗaukar kanka babba John! Ita uwa ɗanta kullum yaro ne a gareta. Ina sonka Yoohan fiye da yanda kake tunani, kai ɗin farin cikinane fiye da sauran ƙannenka”.
Ɗan lumshe idanu yay ya buɗe a kanta, ya ɗan sassauta muryarsa da fuskarsa dake a tsuke. Dan shi harga ALLAH bai fassara maganarta da komaiba face soyayyar ɗa da uwa. “Na sani Mom, nima ina sonku da ƙaunarku fiye da zato ke da papa da ƙannena. Amma Please ki ringa rage cewa zakimin wasu abubuwan. Bama ni ba ko Abraham ɗan shekara goma ba komai zaiso kimasa ba yanzun. Mun rigada mun girma, hidimar da kikai mana muna ƙanana ta wadatar uhmyim?”.
Yanda yay maganar cike da lallashi ne ya sake narkar da ita a wani irin yanayi mai wahalar fassara. Ta buɗe baki zatai magana aka turo ƙofar aka shigo. Gaba ɗayansu ƙofar suka kalla. Papa ne cikin kayan barci da alama ma ya fara barcin tashi yayi.
Cikin ƴar shagwaɓa Yoohan yace, “Yauwa papa Please kwashi matarka ku wuce dama ta sakani a gaba nikam”.
Papa dake bin Mom da wani irin kallo ya haɗiye yawu da yin guntun murmushi yana maida idonsa akan Yoohan ɗin da ya sake ƙwaɓe fuska. Muryarsa da alamun barci ya tashi yace, “Yaushe ka dawo?”.
Mirror Yoohan ya nufa yana faɗin, “Yanzun nan babu jimawa nazatama baka gida ai”.
Komai papa bai ceba ya kama hannun Mom suka fice yana faɗin, “Huta abinka sai da safe”. Suna fita Mom ta fisge hannunta da ga na papa tana kumbura kumatu. Baice mata komaiba yay gaba abinsa dan jin Yoohan yana sakama ƙofarsa key. Yasan ko mi zatayi bazai sake buɗe mataba kuma. A ransa kuwa mamakin yanda Matar tasa ke nuna tsananin so ga ƴaƴansu yakeyi. shi bai taɓa ganin mahaifiya mai ƙulafucin ƴaƴa irin Madam Chioma ba.
Yoohan kam koda ya kammala kimtsawa falo ya fito ya haɗa tea ya koma bedroom ɗinsa. Zaman sha yay zuciyarsa da tunaninsa duk na wajen Nu'aymah. Ji yay yana buƙatar sanin yaya take yanzun, dan haka yaja wayarsa ya nema Dr Aysha a karo na farko a rayuwarsa.
Ita kanta Dr Aysha ba ƙaramin mamaki tayi ba ganin kiran Dr Yoohan a wayarta. Abinda bai taɓa faruwa ba. Jikinta har tsuma yake wajen saurin ɗauka. Ta kara a kunne murya a narke tace “Hello! Doctor good evening”. Maimakon ya amsa mata sai cewa yay “Assalamu alaiki”. Idanu taɗan zaro waje jin sallama yayi, saɓanin da da sai dai ya ce maka hii. Itafa dama gaba ɗaya a wannan zuwan nasa abubuwa da yawa taga idan yanayi tamkar ba shiba. Shekaranjiya ma har ganinsa tai kamar ya fito massallaci......
Sallamar da ya sake maimaita matace ta katse mata tunaninta. “I'm sorry sir. wa'alaikissalam. Kunje lafiya?”.
“Humm”
ya faɗa a taƙaice yana lumshe idanu da kai kofin tea ɗin bakinsa. Sai da ya kurɓa ya haɗiye kafin yace, “Ya yarinyar nan ta farka ne?”. Ta gane Nu'aymah yake nufi, dan ita kaɗaice patient ɗin daya kwantar dai. Cikin sanyaya muryarta tace, “A'a har yanzu tana barci, amma an saka mata drip ɗin daka ce ɗin yanzun babu jimawa”. “Okay night” ya faɗa a taƙaice da yanke wayar batare da ya ƙara komai ba.
Nannauyan ajiyar zuciya Dr Aysha ta sauke tana ɓata fuska kamar zatai kuka. Akan laɓɓanta ta furta, ‘Ɗan wulaƙanci’.