Showing 30001 words to 33000 words out of 318746 words

Chapter 11 - saran boye complete by Queen meenali

01 Jul 2024

41583

mu bazai saka na kasa cigaba da rayuwa ba na barwa Naseer wasika Akan ya sakeni bazan iya ba Zan koma garinmu ko wanke wanke na ringa Yi Ina ciyar da yarana Dan bazan tab'a barin yarana da Naseer mahaifiyarsa ta kasheminsu ba Wlh mmn Mannir banji Ina nadamar matakin Dana dauka ba wlh nesa ma danayi daga gidan bakiji iskar danake shak'a Mai kyau ba nidai kawai ki Tayani da Addu'a watarana insha Allahu zamu sake had'uwa"

Mmn Mannir kasa magana tayi sabida kukan da take dak'yar na kwace hannuna na Shiga motar Ina shiga muka samu Karin passenger daya Yana shiga motar mu ta d'au hanya

Haka kawai naji wani Abu ya tsayamin a mak'oshi tambayar da Zahira ta Kara jefomin Akan tafiya zamuyi mu bar abbansu yasa na kifa kaina akan hannuna na fara kukan danake ta dannewa tun lokacin Dana shirya rabuwa da Naseer.

Allah yasan ba Haka naso ba Dan mijina Yana Sona Yana Kuma iya kokarinsa Dan yaga ya kyautata Min nida yayana Amma mahaifiyarsa ta daka tsalle tace sai mun rabu bansan Umma tsanar da takemin har ya tashi daga kaina zata iya tab'a min Yaya ba
gaba gaba kila wuka zata d'auko ta caka musu ni har mamakin halinta nake Dan wlh ko dabba bazan iya cutar dashi ba ko ragon layya a da idan zaa yanka tausayi yake bani sai da akacemin babu kyau na daure na daina Dan bana ma tsayawa Inda ake yanka d'abba Amma Wai Umma ita ce take zuba wanann zalincin har Yara kanana Bata Bari ba idan dai har zata iya yiwa Nadeeya Haka na tabbata ma Naseer Bai tsira a wajenta ba.


Addua kawai nake Allah yasa na Gane hanyar garinmu Dan shekaru dayawa rabona da can toh waye ma nawa acan ne inama Ina zuwa Naga Yaya Aliyu yazo shima Yana nemana inama na samu wasu suzo suce sune dangina inama na tambaya Mahafina ko Mahaifiyata.wani nasu da yanzu na samu wajen zuwa Amma ba komai Haka zanje ko makotammu na da idan na samu na tambayesu game da gidan da mahaifina ya Bari dan nasan kila yana hannun Mai unguwa idan Allah yasa basu siyar Mana ba sun ajiye Mana kayanmu sai na zauna nida yarana na nemi sana'a.


Biscuit da ruwa na siyawa su Nadeeya da sai Dana tashe su daga bacci.

Zahira ce kawai batayi bacci ba ta Yi jigum da biscuit dinta a hannu ta kasa ci Dan sai data karamin tambaya na daka Mata tsawa akan ta kyalleni naji da iya damuwar da nake ciki.


Sai da mukayi nisa da Kano Naji wani irin tausayin Naseer ya rufeni ko ya zaiji waya sani ma ko har yaje gidan yaga wasikar abinda nakejin Kuma nadamarsa Bai wuce ce Masa danayi na tafi garin kaduna ba Dan nasan kila ya tafi can neman mu alhalin ba can mukayi ba.


Ahaka nayi lamo Ina kallon Motocin dake ta tsere a titi Ni nasan Umma sai ta kusa taka rawa sabida murnar tafiya ta.


Naseer kuwa tunda ya bar gida yake Jinsa kamar Mai zazzabi ahaka ya daure yayi ta zama a katon shagonsa daya bud'e dake sabon gari dake d'auke da kayan electronic Dan Naseer Kam fanin arzki sai daya ce alhamdulillah dan shagunansa zasuyi uku a sabon gari shidda kenan har Dana kofar gidansa.


Yanzu Haka ma Yana Gina wani katon gida a kasan layinsu ko Naeema Bai gayawa da ace mahaifiyarsa Bata Sako shi a gaba ba da ace mahaifiyarsa ta rungumi Naeema a matsayin matar danta da ya ce shi kam ya samu rabon duniya sai dai Kuma na lahira.

Sam yaji zaman shagon ya gundureshi ba Kuma yajin dadin jkinsa hakane yasa duk da yawan mutane dake zuwa siyayya ya Sallame su akan bayajin dadin ya rufe shago ya nufi gida.

Ganin lokacn tashinsu Zahira ya kusa yasa ya tsaya a makarantar su Dan saura Yan mintina su tashi

Kansa tsaye ya shiga cikin makarantar ya nufi office din headmistress din tana ganinsa ta hau gaishe shi tana Masa gaisuwar rasuwan da aka musu

Cikin mamaki Naseer yace Bai Gane ba


Itama headmistress din cikin mamaki ta Kora Masa zuwan Naeema makaranta da Sunan an musu Rasuwa ta tafi da su Zahira.

"Kin tabbata Mahaifiyarsu ce tazo ta d'auke su"?


"Itace Mana Alhaji Naseer yanzu ma wajen awa biyu kenan"


Naseer Bai tsaya jiran sauran bayananta ba ya fita da Sauri gabansa na fad'uwa Mai ke faruwa Naeema tazo ta dauki su Zahira lokacin tashi baiyi ba ko Ummansa ce ta Kara musu wani Abu


Da ikon Allah ya Kara sa gida ko parking Mai kyau baiyi ba ya hau sama g da balain sauri.

Naeema ya hau kwallawa Kira Yana kiran sunansu Zahira Haka kawai gabansa ya tsinke ya Fadi daya shiga d'akin naeema.ya duba koina Bai ganta ba fitowa yayi da Sauri.ya fada Kitchen nan ma Bata nan.

Da sauri ya fito ya Kara sauka kasa.

Yana sauka ya hau tambayarsu lukman ko sunga Naeema da Zahira.

Dukansu girgiza Masa Kai sukayi sai Mai Zama a dayan shagon ne yace yaga ta sauko ita da Minal da Humaira a goye a baya tayi hanyar titi.

Naseer Bai tsaya ya Gama Jinsa ba ya da dan gudu ya nufi gidan mmn Mannir daya San Nan kawai take zuwa Sosai yaji Yana tsoron darsa tunani a Ransa akan ko wani abun ne ya faru addua kawai yake.Allah yasa tana gidan mmn Mannir.

Tsabar tashin hankali Bai tsaya Sallama daga waje ba ya fada cikin gidan da Sallama a bakinsa


Mmn Mannir dake zaune ta buga tagumi tunda ta dawo ta mik'e da Sauri tana sallati ganin Naseer a rude yasa jikinta ya hau rawa cikin jarumta tace.masa.lafiya

Naseer da Sauri ya hau tambayarta inda take ita da Yara.
Ita kuwa tace masa Bata ganta ba sosai taji wani irinn tausayinsa daya zaro Ido Yana sallati.

Ya juya da Sauri ya bar gidan

Sosai hankalinsa ya tashi ya koma gidan a hargitse

Yana Kara kwallawa Naeema Kira Dan gani yake.kamar Tana gidan..

Sai a lokacin tunanin shiga d'akinsu Umma ya Fado Masa.

Da Sauri ya fada d'akin suka dago suna kallonsa

"Umma Mai Kika yiwa Naeema Dan Allah Banga Naeema ba Banga yarana ba Umma Mai Kika musu Dan Allah ki gayamin kimin komai Umma Banda rabani dasu"


Wani irin kallo umma.ta hau yi.masa Hindatu kuwa ta fara zuba Mai harara cikin kishi a ranta tana ayyana Allah yasa ma Naeema ta mutu

Umma kuwa taja Tsaki ta Kau da kanta.

Fitowa ya Kara Yi daga d'akin Yana sallati
Ya Kara Shiga d'akin Naeema tsabar rudewar da yayi ya hau daddaga Kaya ahaka ya d'ago pillow har zai mayar ya Ajiye yaga farar takarda

Baisan lokacin daya dauka ba Yana bud'ewa numfashinsa ya fara barazanar d'aukewa

"Kafin kaga wasikar Nan munyi nisa Naseer Kayi hakuri da matakin da na dauka Naseer nagaji da ace Umma iya Ni takewa Zan iya jurewa Amma yanzu ta fara tab'a min. Yaya daga ni har Kai munsan ita ta d'auke Nadeeya duk sabida kiyayyar da takemin na rasa Mai na Mata idan bamu rabu ba Naseer watarana zaka rasani ko ka rasa yayanka Wanda nasan hakan sai yafi maka ciwo akan dai rabuwar mu banida kowa sai Allah sai Kai Amma Umma ta dage sai mun rabu na dauka auren data saka kayi zai saka na samu sassauci daga wajenta Amma bansamu sassauci ba sai Karin azaba hakane yasa na yanke guduwa da yayana muje garin kaduna ko Allah zai kawo Mai taimaka Mana rabuwar mu sai yafiyemin alheri Naseer kayiwa Umma biyaya ngd da alherinka a gareni dafatn bazaka.....

Wani irin sallati Naseer ya doka cikin fitar hayyaci Bai ma iya karasa.karantawa ba ya fita aguje ya nufi d'akin Hajara takarda rik'e a hannunsa Yana "Umma shikenan kin kasheni Umma Naeema ta gudu ta barni ta tafi da yarana sabida azabar da kikee gana Mata Umma kalli takardar Nan kiga mai tace Umma Naeema ta shiga duniya da yayana innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"


Hajara duk da batayi karatu ba karbar takarda tayi ta mik'e zaune Dan Dama a kwance take "Mai kace Kara maimaita min naji kace Naeema ta gudu da Yara"?

Umma Naeema ta gudu da Zahira da Nadeeya da Minal da Humaira Umma tace ta gaji da azabar da kike gana Mata Umma Mai na Miki kika tarwatsa.min rayuwa? Mai na Miki kika rabani da farincikina"?Umma Naeema fa Bata da kowa sai Ni Umma Mai yasa kikemin Haka idan wani Abu mahaifina ya Miki kike San ki dau fansar hakan akaina ki gayamin na nemi yafiyarki Umma uwa da tausayi aka santa umma uwa Bata cutar da dan data Haifa Umma ban miki komai ba kina ta cutar Dani Ina Miki biyayya daidai gwargwado Naeema tana Miki bansan Mai yasa Kika dage sai kin rabamu ba gashi dai ta tafi min da yara har su hud'u"

"Rufemin baki shasha lusari Kai yanzu akan mace kake kuka ka dagawa kanka hankali Haka?Kai yanzu Sabida Naeema ta rabu da Kai kake wanan surutan?anya Naseeru Haka yarinya Nan ta barka?Naeema kadai ce mace a Duniya ko sai akace ma Dan ta rabu da Kai rayuwarka tsayawa zatayi? Karka manta fa kana da kudi kana da damar da zaka auri duk kalar macen da kakeso ta kuma Haifa maka maza"


"Ni kuma Mai matsayina a wajensa kenan da kike cewa zai auri wacce Ransa keso"?

Hindatu tace tana jifan Hajara da harara

"Ga Hindatu Nan dame Naeema ta fita Naseeru"?

"Ya kake Abu kamar ba Ni na Haifeka ba"?

Naseer kallon Hajara kawai yake hawaye na zubo Masa shi kadai yasan halin da yake ciki shi kadai yasan Mai yakeji a zuciyarsa.

Juyawa yayi a hankali ya fice daga d'akin Yana dafa bango Dan sosai yake Jin jiri na neman kayar dashi


Yana fita Hajara ta hau rawar murna rabonta dataji ta a farinciki Haka har ta manta gaskiya tafiyar Naeema da yaran ya balain faranta mata take ta fara addua Allah yasa Naeema ta lula duniya Tama hadu da ajalinta ita da yaran Dan batasan Nasser ma ya kalli wani Abu da zai tuna Masa Naeema.

Palon ta fito tana washe baki ganin Bata ga Naseer a palon ba yasa ta zauna a kujera palon tana zai Gama koke kokensa ya gama ne.

Zamanta da Yan mintina Naseer ya fito daga d'akin Idonsa ya kad'a yayi jawur.hannunsa rik'e da mukullin mota yayi hanyar waje.

"Ina zakaje"?

Ko kallonta baiyi ba ya fice waje.

Gidan mmn Mannir ya Kara komawa da takardar a hannunsa Dan gani yake kila tana da masaniyar Inda Naeeema taje

Yana k'ok'arin Sallama mmn Mannir ta fito cikin tashin hankali ya Mik'a Mata takarda Yana
"Dan Allah Mmn Mannir idan kinsan wajen Wanda Naeema taje a kaduna ki gaya min nasan bazata ki Gaya miki ba sai dai kawia ki boyemin Dan darajar Allah ki gayamin idan kinsan Inda zata a kaduna ki taimakamin sabida kananan yaran data tafi dasu Naeema kanta Bata gama mallakar hankalinta ba ba kuma ta da kowa babu Kuma Wanda ta sani karki boyemin Dan Allah idan kin sani ki gayamin"?

Sosai ya kashewa mmn Mannir jiki bare data ga Yana ta hawaye

Tayi wa Naeema alkawarin bazata gayawa kowa ba Amma a yanzu Anya zata iya cika alkawarin data daukar Mata bayan taga halin da Naseer yake ciki

"Dan Allah kigayamin mmn Mannir Kar ta fada hannun mugayen mutane"?


"Naseer a gaskiya Mahaifiyarka ta takurawa Naeema Mahaifiyarka tana cin zalinta sabida tana ganin Bata da kowa mai Naeema ta Mata Haka data tsaneta nidai bansan Inda Naeema taje ba ta dai cemin zata gudu Amma bansan dgaske ta gudun ba sai yanzu da kazo kana tambayata Amma a gaskiya bansan Inda taje ba da nasani Zan Gaya maka"

Mmn Mannir tace tare da kau da kanta data tuna girman Alkawarin data daukarwa Naeema

Naseer cije lebb'ensa yayi batare da sake cewa komai ba ya tafi.

Motarsa ya bud'e ya Shiga ya zauna ya rufe Ido yana tunanin ta Inda zai fara neman Naeema wa ta sani a kaduna da zata tafi wajen wa zataje ?Mai yasa Naeema zata Masa haka ta gudar Masa da Yaya shi akaran kansa akwai abinda yake tsara musu Gaya Mata ne kawai baiyi ba Dan ya Kara shirya su gudu zuwa wani garin na Dan lokaci kafin suga ko Umma zata hakura ta kyallesu.

Amma sai gashi Naeema.ta gudu da yayansa tashin hankalinsa Bai wuce Ina zata je ba wajen wa Kuma zata sauka Bai San har Naeema tayi wayo yin wanan tunanin ba Naeema daya sani tana da tsoro Mai yasa zata Masa Haka yanzu idan sun Isa kaduna Ina xasu kwana ita da yaran tunani iri iri Haka ya ringa yi kirjinsa na Masa nauyi.

Take zazzabi Mai zafi ya rufeshi

Sai su lukman ne Suka Gane bashida lafiya Suka Kira likita a kasan layinsu yazo ya duba Naseer ya mishi allura ya Sha magani.



Dak'yar ya koma cikin gida Inda Yana Hawa sama.yaga Umma taci kwalliya ita da Hindatu fuskarsu kamar gonar auduga sai cin kaza suke Bai kallesu ba ya Shiga d'aki a ranar ko runtsawa baiyi ba washegari da sassafe ya dau hanyar kaduna.

A takaice sai daya kwana uku a kaduna Yana bulayi duk da Bai San takaimaimai Inda zai ga su Naeema ba a cikin kwana uku ya zama kamar mahaukaci Dan ko wanka baya yi balle ya samu cikakken bacci.

A ranar daya kwana biyar a kaduna Yana yawon nemansu Naeema Tasha tasha.unguwa unguwa ya yanke zuwa garin su Naeema Dan Haka kawai yaji kuma zuciyarsa ta karkata can.


Naeema


Duk da sauye sauyen da aka samu a garin na cigaba hakan Bai Hana ni Gane unguwarmu ba rabona da garin tun rasuwar mahaifina da Mahaifiyata kaina tsaye gidan Mai unguwa na nufa da su Zahira da har kuka suka ringa min da Sunan sun gaji.

Sosai na ringa adduoi a Raina Akan Allah yasa Kar Mai unguwa ya canjamin sabida Yana ganin iyayena sun rasu.

Ga mamakina muna Isa ya.gane Ni Suka Kuma Mana tarb'a Mai kyau Inda naji wani irin kwanciyar hankali da nutsuwa Wanda rabona ma danaji Haka Zan iya cewa tun kafin na auri Naseer.


Sai da muka huta daddare ya aika a kirani Inda ya hau tambayata mahaifinsu Zahira dafatan lafiya yagani da Yara.

Kuka na fashe dashi na tsinci kaina da karyar Naseer s'akina yayi

Sosai ya nunamin baiji dadin abinda ya faru ba ya min nasiha akan na rungumi kaddara zasu rik'eni tunda banida kowa sun Kuma Yi zaman mutunci da mahaifina Amma fa sai.na mayar dasu Zahira Dan bazai iya rikesu ba baima Kamata na taho da yaran gabadaya ba.

Anan hankalina ya tashi danaji abinda yace kuka na fara yi.masa inaso na Gaya masa gaskiya abinda ke faruwa bakina yamin nauyi Kamar an dinke inaji Ina gani yace na tashi na tafi idan an kwana biyu zai saka a cikin yaransa wani ya rakani na mayarwa Naseer yayansa.


Sosai hankalina ya tashi na hau nazarin abin yi Inda a karshe na yanke kafin ya karamin magana gwara na Gaya masa gaskiya ko da zai iya taimakamin tunda Naga gidanmu na Nan a kulle Dan har maganar gidan yamin akan mallakina ne gwara na gyara na zauna a ciki nida yarana Dan canjin hannuna na ringa juyawa.


Ranar da muka cika kwana biyar a garin washegari.na karbi mukulin gidan nace Zan je na Dan gyara.

Na tafi da yarana gabadaya shigata gidan ya hau fad'omin da irin Rayuwar danayi da.iyayena cikin so da Kauna da kwanciyar hankali.

Haka kawai na samu waje na zauna na hau bawa yayana labarin iyayena da yayana da ya tafi soja har yau banji labarinsa ba da irin San da sukemin.ina basu labari Ina kuka Inda mahaifina yake yawan Zama nake nuna musu Ina murmushi kamar ance na juya na kalli bakin kofa Naga Naseer a tsaye ya zubomin Ido Yana kallona badan nasan Naseer ba danace mahaukaci ne a tsaye a bakin kofa.......


Iabarin na da Dan tsayi shiyasa nake typing kullum na matsu Nazo. Ta tsakiyar labarin Dan haka inaga Zan Dan daddatse sabida mu fara Dan bana shiri da novel Mai tsayi Nan da Nan nake gajiya😃😃😃
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 19*



Cikin fad'uwar gaba na d'auke kaina banji dadin yanda mmn Mannir ta karya alkawarin data daukar min ba ba yanzu naso Naseer ya ganmu ba naso sai mun Dade na samu hutu kafin ya ganmu kasan Raina Kuma tausayinsa ne ya cike min zuciya amma kuwa saman fuskata hade Rai nayi Dan bazan tab'a binsa ba nafi jina cikin kwanciyar hankali tunda na baro Garin Kano

Jiki ba kwari ya daga Minal Ya Dan matsar da Zahira da Nadeeya da suka kankameshi suna ihun murnar ganinsa.

Ina Jinsa suka karaso gefena ya sauke Minal ya saka hannu ya dauki Humaira Dana kwantar da ita a gefena
Ya sauke wani irin ajiyar zuciya.

Har lokacin ban yarda na kalleshi ba duk da Yana ta lallubar kwayar idona Dan mu had'a Ido daga ni har shi ba Wanda yayi magana

Ni kuwa sosai na Kai zuciyata nesa wajen ganin na danne hawayen tausayinsa dake neman fitowa ta k'arfi da yaji ko ince tausayinmu gabad'aya.


Shi kuwa ganin naki kallonsa yace "Taimakamin da ruwa in Sha Naeema"

"Mik'ewa nayi nayi hanyar waje Dan babu komai a gidan.

Cikin gidan Mai unguwa na Shiga na d'ebo Masa ruwa a kwanun Sha na rufe na kawo masa na ajiye a gabansa.

D'auka yayi ya kafa baki sai daya shanye tas ya Ajiye anan na saci kallonsa Naga yanda yayi wurjan wurjan lebb'ensa duk ya bushe.

"Naeema Mai yasa Kika min Haka a ganina bai Kamata ki dau matakin guduwa da yaran ba da kin fadamin da na San Abunda ya Kamata nayi Sabida ki wahalar Dani Kika cemin Kaduna Kika tafi sai danayi kwana hudu a can kafin tunanin zuwa Nan yazomn haba Naeema Mai na Miki Dana cancanci ki zabi rabuwa dani"?

Cikin hade Rai Dan yasan dagaske nake bana San komawa gidansa marairaicewar da.yake bashi zai Saka na bishi da yarana ba

"Idan na Gaya maka Naseer hakuri zaka bani kace mu cigaba da Addu'a kullum kalmar kenan alhalin sababin abubuwa Umma ke kara bijiromin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login