Showing 114001 words to 117000 words out of 318746 words

Chapter 39 - saran boye complete by Queen meenali

01 Jul 2024

41639

murya na rawa. Wata wawiyar tsawa papa ya sake daka masa daga can, tare da sakin wani irin ihu tamkar zai fasa gidan.
       “Solo!!!!!! Inhar yarona ya shiga wani hali na rantse muku da ALLAH duk sai na kasheku da hannuna, na baku awa biyar kacal akan nemansa. Idan har kuka bari na iso kano kuyi kuka da kanku!!....”
    Ƙit ya yanke wayar batare da ya bari Solo yay ko ƙwaƙwaran numfashi ba.

        Sosai hankalin Solomon ya sake ƙololuwar tashi, hakama na sauran ƴan uwansa. Dan sunsan wanene Pastor Goshpower, sun san kuma abinda zai iyayi, musamman ma akan Yoohan da duk duniya bai haɗa sonshi dana kowa ba.
       Suna cikin tashin hankali da tararrabin mafita sai ga ƴan sanda kusan mota uku sun iso hotel ɗin bisa jagorancin D.p.o Emanuel.
     Su masu hotel babban tashin hankalinsu kar sunansu ya ɓaci. suko su Solomon sune sukasan babban tashin hankalin da zai iya samunsu da su kansu masu hotel ɗin indai har ta tabbata anyi kidnapping ɗin Yoohan a hotel ɗin ne, kamar yanda kowa yake tunani da hasashe.............✍
[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.



No. 30

................Lokacinda su Solomon ke acan cikin tashin hankalin tsoron cikar lokacin da papa ya basu akan sanin inda Yoohan yake, shi yana nan suna shirin tafiya massallacin juma'a shi da su baba malam.
      Kowa ya kalli baba malam ɗin a yau zai fahimci yana cike da tsantsar farin ciki. A cikin nishaɗin daya shiga da shi cikin gidan nasa ya sake fitowa shi da Umm data taimaka masa yay shirin massallaci.
    Ƴar tsokanar da ya kema Umm yasa Nu'aymah dake zaune a falon tana gyaran fruit ɗin da Umm ta sakata ɗagowa tana kallonsu. Cikin washe baki tace, “Abbah yau dai kana cikin farin ciki ALLAH, naga tun safe fuskarka sai annuri takeyi”.
      Da ga Umm har baba malam dariya sukayi, ya matsa kusa da ita tare da kai hannu ya shafa kanta. “Tabbas yau ina cikin farin ciki mamana, saboda wannan farin cikin yau har ƙyauta ta musamman na shirya miki ke da Muhammad, dan haka kafin na dawo ki shirya faɗa mini abinda kike so”.
         Sosai farin ciki ya sake kamata. Ta shiga jera masa godiya da addu'ar fatan dawowa lafiya. Daga shi har Umm amsa mata suke cike da kulawa. Kowannensu najinta a ransa sosai, dan daga Umm har Baba malam ba ƙaramin so sukema Nu'aymah ba. Suna dannewane kawai saboda ƙarfafama kansu tarbiyarta. Ga ɗunbin tausayinta dake mamaye da ruhinsu game da matsalarta. Dan har yau da muke ɗin nan baba malam bai gajiya ba wajen cigaba da neman likitan nan, yana kuma gayama UBANGIJI da neman taimakonsa a kowane daƙiƙa.

     Bayan Umm tama baba malam rakkiya ta dawo. A inda tabar Nu'aymah nan ta sake isketa tana ƙalular gyara fruit ɗin.
      “Nikam naga takaina da wannan hali naki Nu'aymah! Mutum yayta abu sanyi-sanyi tamkar bazai ƙaresa ba. Yanzu maimakon ki zauna kiyi aikin nan a kitchen shine kika taho nan kuma dan salon neman ɓata guri?”.
       Baki ta tura gaba tana ɓata fuska, “Yoni Umm idanfa na zauna a kitchen wlhy Rabi damuna zatayi da surutun ta, kin sani dai ko redio haka ta ganta ta ƙyale akan zanc........”
      Bammm!. Umm ta make mata baki, hakanne ya hanata ƙarasa faɗa. Da sauri ta saki wuƙar hannun nata hawaye na taruwa mata a ido. Umm dake hararta tace, “Saunawa zan faɗa miki karna sake jin wannan maganar banzan a bakinki Nu'aymah? Rabi bata girmeki ba? K wai yaushe ne zaki bar tsiwa da rashin kunya? Itaɗin sa'arki ce?”.
       “Kiyi haƙuri Umm bazan sakeba ALLAH ”.
      “Kima sake mana, mara wayau kawai”. Umm ta faɗa tana hararta da barin wajen. Harta kusa ƙofar sashen baba malam ta juyo. “Kiyi ki tashi a wajen nan kuma kafin na fito, ga man-shanu can a kitchen ki ɗauka ki kaima Addah, kuma idan kinje ki zauna shiririta karki dawo ki ƙarasa aikin dana sakaki kinji ko”.
        Sake ɓata fuska Nu'aymah tayi hawaye na zirara mata. Sai dai batace komaiba har Umm ta shige ciki. Dan zuciyar gadon tazo mata wuya.
     
       Duk yanda Umm tace tayi haka tayi, sai dai data shiga kitchen Rabi tasha harara, dan a ganinta saboda itane Umm ta Mammangare ta. oho ita batama san tanaiba, dan aikinta takeyi koda ta shigo bama ta kalli inda Nu'aymahn takeba tunda tasan basa doguwar magana lafiya sai sunyi faɗa.
       Manshanun ta ɗauka zuwa sashen Addah. Sai da tai sallama kusan sau uku kafin a amsa mata ciki-ciki. Bata damuba ta shige tana ɗaure fuska dan har yanzu akwai haushin faɗan Umm tare da ita. Kubrah kawai ta iske zaune a falon, tunkan ta ƙaraso ciki take jefo mata harara.
       Jitai kamar ta juya dan haushi, amma sai ta daure ta ƙarasa da faɗin, “Aunty Kubrah Umm ce ta aikoni wajen Addah?”.
     Banza tai mata tamkar bata jitaba, har Nu'aymah ta fara yanke shawarar juyawa sai ga Hajarah ta fito daga ɗakinsu hannunta ɗauke da Al-qur'ani.
       “A'a Aymah ce a wajen namu?”.
Ajiyar zuciya Nu'aymah tayi da maida kallonta gareta. Fuskarta da ɗan damuwa tace, “Aunty Hajarah Umm ce ta aikoni wajen Addah. Amma ina tambayar Aunty Kubrah tamin banz.....”
           Kafin ta ƙarasa taji saukar duka a bakinta, Kubrah da tai dukan ta nunata da yatsa cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “K dan uwarki ni sa'arki ce ko?”.
       “Kai haba Aunty Kubrah daga tambaya, yanzu dan ALLAH mita miki zaki dakar mata baki? Minene abin laifi anan to?”. Hajarah ce mai maganar dai-dai tana ƙarasowa inda suke ta kama hannun Nu'aymah dake hawaye, dama bakin bai gama mata zafiba akan dukan da Umm tai masa yanzu. Ga kuma Kubrah ta ƙara mata wani.
    Cikin masifa Kubrah ta kalli Hajarah, “Kozaki rama mata ne?”.
     “Bazan rama mata ba, amma ALLAH zai saka mata. Tunda duk wanda ya zalinci wani ALLAH na kallonsa. Nu'aymah jeki Addahn na ɗakinta kinji ko”.
      Kai Nu'aymah ta ɗagama Hajarah tana share hawayenta. Batare datace komaiba ta nufi ɗakin Addah zuciyarta na mamakin yanda Aunty Kubrah kejin zafinta a ƴan kwanakin nan, duk da dai dama ita babu wani shaƙuwa sosai tsakaninta da ita tun da can. Sai dai bata taɓa nuna mata banzan hali irin na wannan karonba. Tana gab da shiga ta tsinkayo muryar Kubrah na faɗin, “Ƴar iskar yarinya ki taka a sannu dan a tafin hannuna kike wlhy, inba hakaba saina tona asirin iskancinki a gaban kowa yasani a gidan nan”.
     Sosai gaban Nu'aymah yay bala'in faɗuwa, dan tasan inhar Kubrah ta faɗi abinda ta gani tsakaninta da Yoohan ranar tata ta ƙare. Da ƙyar ta iya haɗiye kukan daya taho mata.
        Da mamaki Hajarah ta kalli Kubrah, “Haba Aunty Kubrah wace irin maganace haka? Wai nikam minene ya haɗaki da Nu'aymah mai zafi a kwanakin nan dan ALLAH?”.
      “Ki shaƙeni in faɗa miki mana”. Kubrahn ta faɗa a harzuƙe.
      “ALLAH ya baki haƙuri”. Hajarah ta faɗa tana barmata wajen ranta fal tunane-tunane kala-kala akan ƴar tsamar yayar tata da Nu'aymah data gaza fahimtar tushenta a kwanakin nan sam.

       Sai da Nu'aymah tai sallama Addah ta bata izinin shiga sannan ta shiga ɗakin. Tsaye ta isketa tana ninke abin salla alamar sallar ta idar. Ganin Nu'aymah na sharar hawaye yasa fara'ar fuskar Addah gushewa lokaci guda. “Lafiya Nu'aymah? mi akai miki?”.
       “Babu komai Addah, Umm ce tace na kawo miki wannan”.
    Sam Addah bata yarda da maganar Nu'aymah ba, dan haka tai shiru tana cigaba da kallonta kawai batare data amshi man-shanun ba. “Nu'aymah bana son shirme, faɗamin gaskiya mi akai miki?”.
      “Addah wlhy aunty Kubrah ce ta dakar mata baki dan hawai tacemin ta tambayeta kina ina ta mata banza”. Hajarah dake shigowa ɗakin ta bama Addah amsa.
      Cikin ɓacin rai Addah tace, “Kubrah?!”.
       “Eh wlhy Addah, ni bama dukan ya ɓatan rai ba, bakiji yanda take faɗama Nu'aymahr maganar banza ba. A kwanakin nan dama na kula tana matsama yarinyar nan a gidan nan, haka ɗazun a islamiyyar asuba dan kawai Nu'aymah ta fiddo Fahad ɗin maman Sadiya daga aji saboda suna faɗa da wani yaro wlhy bakiga abinda tai mataba. Alhalin baikamata taima Nu'aymahn maganaba tunda yaran duk ƴan ajintane, ta fita sanin halin kowa a cikinsu”.
      Kama hannun Nu'aymah Addah tayi suka fito ranta a ɓace. Hakan yasa Hajarah biyo bayansu da sauri itama.
         “Kubrah!!”. Addah ta ƙwala mata kira ganin bata a falon.
    Da sauri ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da plate ɗin abinci.
     “Ubanmi Nu'aymah tai miki kika daketa?!”.
        Sake tsuke fuska Kubrah tayi, ta kalli Nu'aymah data duƙar da kai tana hawaye har yanzun. Wani ɗan murmushin mugunta tayi kafin ta kalli Addahn. “Addah catai na daketa?”.
       “Ni na faɗa ba ita ta faɗaba, tunda a gabana akai komai”. Hajarah ta bata amsa kafin Addah tai magana.
      “Mtsooow!! Munafuka kawai. Addah ni ban daketa haka kawaiba, rashin kunya zataimin shiyyasa........”
     “To amma shine zaki ce mata ƴar iska, kuma sirrinta a tafin hannunki yake. Idan kinso zaki tona mata asiri agaban kowa”.
       “Wlhy Hajarah zan sauya miki kamanni, wai ni sa'ar wasanki ce?”.

         “Kai!! Ya isheni haka, banason rashin mutunci. Bazan ɗauki wannan wawancinba kunji na faɗa muku. Shin kuɗin yaran goye ne da kullum baku da wani buri sai na samin ciwon kai? Kusani daga yau na sakejin makamancin wannan banzan al'amarin wlhy sainayi ƙololuwar ɓatama mutum rai a gidannan. Banda k kullum girma kike kinacin ƙasa Nu'aymah ce kuma ta zama abar tozartawarki Kubrah? To daga yau na ji wani abu ya sake fitowa makamancin wannan zakiyi nadama a gidannan kinji na faɗa miki”. Ta ƙare maganar da matuƙar zafin rai tana sake yima Kubrah gargaɗi da hannu.
   Sai kuma ta juya ga Nu'aymah dake sauke ajiyar zuciya a jajjere. “Nu'aymah jeki wanke fuskarki kinji  kuma kar naji wannan maganar a wani waje, kiyi haƙuri”.
     Kai Nu'aymah ta jinjinama Addah, babu musu ta shiga toilet ɗin dake a falon ta wanke fuskarta ta fito. sallma tai musu ta fice batare data sake yarda ta kalli sashin da Kubrah take ba. Harga ALLAH hankalinta a tashe yake matuƙa da kalaman Kubrah.
           Koda ta koma sashensu ɗakinta ta shige ta shiga raira kuka, Nu'aymah yarinyace da bata da tsoro sam. Amma yanda tai matuƙar damuwa da faruwar abin nan na jiya daya kasa barin ransta saita baka tausayi. Tasan tabbas wannan laifin na jiya yasha banban da kowane irin laifi, kuma duk wanda zaiji abinda ya farun sai yayi ALLAH wadai da ita, ƙilama baba Malam da Umm su tsine mata albarka.
     Sake rushewa tai da kuka kamar zata shiɗe wajen jan zuciya. A haka ta tsinkayo muryar Umm na ƙwala mata kira. Da sauri ta miƙe ta shiga share hawayen, harta nufi ƙofar fita sai kuma tai saurin dawowa. Toilet ta shiga ta sake wanke fuska tazo gaban mirror tasa hoda da kwalli sannan ta fita.
         Zaune ta iske baba malam da Umm a falo. Cikin raunin murya taima baba malam sannu da dawowa. Duk kallonta sukai shi da Umm, baba malam yace, “Lafiya kuwa? Naga idonki kamar wadda tai kuka? Mamana!”.
    Kafin tayi magana Umm dake hararta tace, “Saboda namata faɗa akan rashin kunyar data iya”. (dan ita tazata faɗan datai matane ya sakata fushi har yanzun).
      Baba malam baice komaiba sai maida kansa da yay ga tv kawai. Fuska a ɗaure Umm ta nuna mata trayn dake a kan centre table. “Ki ɗauka ki kaima baƙo a falon baba”.
     Kai kawai ta jinjina mata ta koma ɗakinta ta ɗakko hijjab. Batare datai maganaba ta ɗauka tiren ta fice. Sai da ta fice gaba ɗaya sannan baba malam ya ɗauke kansa daga kallonta. maidawa yayi ga Umm da itama take kallon nata.
       “Addu'a ya kamata ki cigaba da mata bawai nuna fushinki da zafi fiye da kima ba. Har yanzu Nu'aymah yariyace ƙarama, sannan kinsan lalurar dake tare da ita sam bata buƙatar yawan takura. Ki fahimci ita wannan tsiwar itace tata ƙuruciyar”.
        “Amma Malam ka tunafa ƴa mace ce ita. Gidan wani fa zataje. Bandama ƙaddara daba yanzu tana ɗakin miji ba. Wlhy sam bana son tsiwarnan tata, bansan a ina ta kwaso wannan banzan halinba nikam”.
     Murmushi baba malam yayi yana miƙewa, “To ayi haƙuri zata daina insha ALLAH, nima zan zauna da ita anjima ALLAH ya huci zuciyarki”.
       Yanda yay maganarne ya saka Umm yin murmushi, dan ta sake tabbatarwa yau mijin nata yana cike da nishaɗi sosai kam, musamman data san yafi kowa ƙin jinin tsiwar ɗiyar tasu.

★★★★★★

             Murya a sanyaye tai sallama a ƙofar falon har kusan sau uku. jin shiru ba'a amsaba ya sakata tura kanta ciki da haushi. Takaicin rashin amsa mata sallamar da ba'ayiba ne ya sakata ƙin kallon baƙon ma balle tasan wanene.
      A gabansa ta dangwarar da trayn, murya a cinkushe batare data kallesa ba tace, “Ina yini”.
       Shiru yanzuma ba'a amsaba, wani sabon takaicin ya sake lulluɓe ta. Har tayi niyyar dubansa ta sauke masa takaicinta saita tuna yanzufa Umm ta gama mata faɗa harda duka akan tsiwa, sannan kuma bai kamatama tayi wani abun rashin hankali ba tunda batasan wanene baƙon nasu ba. Zata iya yuwuwa babban mutumne sa'an baba malam ko cikin yayunta. Haɗiye haushinta tai ta nufi hanyar fita zata bar falon.
          Yoohan da tun shigowarta idonsa nakan wani littafi da baba malam ya bashi ya duba ya ɗan ɗago kansa dan sam baiji sallamarta ba balle shigowartaba ma shi, sai gilmawarta kawai ya gani yanzu da take ƙoƙarin fita. Cikin tsautsayi ta bigi ƙaramar jakkar dake gefensa da ƙafa. baya tai taga-taga zata faɗi cikin sa'a yay saurin saka mata ƙafa dan son kareta bisa tsautsayi sai gata a cinyarsa ɗare-ɗare.
     Duk da ya canja kayan jikinsa mayataccen ƙamshin turarensa na nan manne da shi. Shaƙa ɗaya Nu'aymah tayi tai azamar ɗagowa cikin tashin hankali da tsantsar takaici.
       Idanunsu ne ya shige cikin na juna, cike da firgici Nu'aymah ta sake waro masa idanunta da kware baki zatai ihu saboda harga ALLAH ta tsorata da ganinsa.  Saurin saka tattausan hannunsa yay ya rufe mata bakin ruf yau ma, tare da sake manneta a jikinsa sosai shima a cikin ɗan firgice.
        Wani irin mugun bugawa ƙirjinta ya sakeyi, jikinta ya hau ɓari tamkar wadda aka jefa cikin garwashin wuta ko akan wayar lantarki. Ta shiga mutsu-mutsun ƙwace kanta tana kai masa duka.
          “Oh my God! Just relax. Please calm dawn”. Ya faɗa yana janye hannayensa duka daga jikinta.
       Cikin rawar jiki hawaye na zirara ta miƙe, sake bigewa tai da kujera ƙafarta ta tuzguɗe ta sake yin gaba kuma zata kifa yay azamar riƙo mata hannu ta sake dawowa jikin nasa.
      “Wayyo Abbana ɗan isk.........” ta wage baki da iya ƙarfinta zata faɗa yay azamar saka hannu ya sake toshe bakinta da manneta sosai a jikinsa yanda bazata iya ko motsawa ba.

        “Wa'iyazubillah!! Iskancin naku da rashin tsoron ALLAH yau har a falon malam?” Kubrah data shigo falon tamkar an jehota ta faɗa hannu bisa kai tana mai waro idanu waje..   
          Tashin hankali, tsabar ruɗewa Nu'aymah harda guntun fitsar ta saki a wando, batama san ta saka gwiwar hannunta ba ta kai ma Yoohan duka. Sai ko ya sauka a gefen cikinsa.
      Saurin sakinta yay yana faɗin “Ouch!!!” dan harga ALLAH yaji zafi. Yay saurin ɗoura hannun nasa bisa cikin ya riƙe yana watsa mata mayun idanunsa masu haske da cikar gashi.
       Nu'aymah dake ja da baya tana hawaye da kallonsa da kallon inda Kubrah take tsaye tace, “Ɗan iska kawai, ALLAH ya isa ban yafeba. Wlhy daga yau ka sake ƙoƙarin taɓamin koda hannu sai na illata maka wannan fuskar taka mai kama da jan ƙosai, na tsane ka wl........”
        “Hhhhhhh! K! Ƴar iska bar wani pretending kinji!”. Kubrah ta faɗa tana ƙarasa shigowa cikin falon sosai.
      Nu'aymah dake kuka tamkar ranta zai fita tace, “Aunty Kubrah wlhy ba abinda kike tunani bane. Wlhy tallahi kinji na rantse by mistake ne hakan ya sake faruwa yau ma, shine fa y.....”
        “K dalla saurara mani! Mahaukaciya kika maidani irinki komi? Na ganki da idona saman cinyarsa kuna tsotsar bakin juna sannan ki hau mini wani rsantse-rantsen banza. Kinsan ALLAH, inhar kika sake faɗin tak saina kwarara ihu yanzun nan kowa yasan halin da kuke ciki”.
     Ƙasa Nu'aymah ta durƙushe tana ƙara sakin kuka maiban tausayi. Yayin da Yoohan da sam bai fahimci mi Kubrah ke faɗa ba ya zuba musu idanu kawai yana kallonsu.
     Juyowa Kubrah tayi garesa, sai dai wani shegen kwarjini da cikar haibarsa tai bala'in cika mata idanu. Muƙut ta haɗiye maganar tata ƙirjinta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Cikin suɓutar baki ta firta ‘Tsarki ya tabbata ga ALLAH’.
         Sake ɗaure fuska Yoohan yayi fiye da da, dan a rayuwarsa ya mugu-mugun tsanar kallo, musamman ma irin wanda Kubrah ke masa na ƙurulla a yanzun. Duk da ma bawai yaji mi take faɗaba ne ɗazun, sai dai ya fahimci ba magana mai daɗi takema Nu'aymah ba. Dan haka ya watsa mata wani mugun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login