Showing 123001 words to 126000 words out of 318746 words
kowa maganaba.
Papa da yasan minene fushin Yoohan yay saurin bin bayansa yana kiransa. Amma ko kallonsa baiyiba balle ya saka ran amsawa. Ya buɗe murfin motar a fusace ya shiga baya, shima Papa ɗayan gefen ya zagaya ya shiga yana cigaba da kiran sunan sa. Hakanne ya saka drivern sa da Solomon saurin shiga suma, sauran guards ɗinsa da su Emanuel da suka sami mafita suma suka nufi nasu motocin batare da suncema baba malam komaiba.
Nannauyan numfashi baba malam ya sauke lokacin da mitocin suka harba kan titi. Yayinda can ƙasan zuciyarsa ke mamaki da jinjina al'amarin UBANGIJI. ‘Yoohan ɗan Pastor Goshpower ne da gaske? Lallai UBANGIJI mai yin yanda yaso, a lokacin da yaso, ga kuma wanda yaso’. Baba malam ya faɗa a fili. Yasan tabbas UBANGIJI shike fidda rayayye a cikin matacce, ya kuma fidda matacce a cikin rayayye. Amma al'amarin akwai ɗunbin ban al'ajabi a cikinsa, dan yasan abubuwa masu yawa game da papa tun shuɗaɗen lokaci kafin yakai haka.
Da wannan tunanin baba malam ya koma cikin gidan, inda ya tadda duk jama'ar gidan sun fito sunata tararrabin abinda akace ya faru da Nu'aymah. Su Abban Abdallah ma shirin shiga mota suke zasubi bayansu asibitin.
Ganin baba malam ya sakasu dakatawa, duk suka nufesa hankali tashe suna tanbayar yaya Nu'aymahn.
Tausayinsu ne ya kamashi. dan haka cikin taushin murya ya kwantar musu da hankali, tare da sanar musu shima yanzu zai bisu. Basu zauna ɓata lokaciba suka ɗunguma a mota ɗaya Omar ya jasu, akabar su Umm a gida na binta da addu'a.
Yoohan da tunda suka tafi ya ƙi kula papa daketa so yayi magana yay kwance jikin kujera hannunsa dafe da goshinsa cike da tsananin takaicin abinda ya faru tsakaninsa da Nu'aymah yauma. Yarasa mike jan hankalinsa ga aikatama yarinyar nan wannan banzan ɗabi'ar?. Abinda ba halinsa ba amma yana ƙoƙarin ɗabi'antar da shi a gareta. Saima yaji na yau yafi masa zafi a rai fiye da na jiya.
Da sauri ya kwanto jikin papa saboda wata hajijiya-hajijiya dake neman kwasarsa. Sake rikicewa papa yayi. A matuƙar ruɗe ya shiga girgiza Yoohan kai kace gani yay baya numfashi.
Sosai takaici da hayaniyar papa ta sake rufe Yoohan ɗin, amma sai ya daure cikin taushin murya da sanyayata yace, “Papa Please relax. Ina lafiya fa”.
Da sauri ya rungumeshi yana sauke numfashi a jajjere. Su dai su Solo suna kallon ikon ALLAH daga gaba. A haka suka ƙarasa hotel ɗin da har yanzu akwai sauran yaran Ema... Da taimakon papa Yoohan ya fita, shine ya kamasa har ɗakin da yake. Su kuma su Solomon suka dakata wajen manager ɗin hotel ɗin suna musu bayani akan anga Yoohan ɗin su kwantar da hankalinsu.
Papa na zaune kusa da Yoohan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama rasa wane kalar tunani ya dace yayi akan matsalarnan guda biyu. Alaƙalar Papa da Baba malam. Abinda ya aikatama Nu'aymah a karo na biyu. Buɗe idanunsa yay a hankali kan papa da yay shiru shima yana wani tunani can daban, sai da yay masa kusan kallon sakan goma kafin cikin nuna kulawa ya kamo hannunsa cikin nashi da faɗin, “Papa!”.
Firgigit ya dawo hankalinsa tare da kallonsa. Yoohan ya sake lumshe idanu ya buɗe a kansa. “Papa dama kasan malamin nan ne?”.
“Yoohan! Wannan tambayar taka bata da muhimmancin samun amsa. Kai ya kamata nasan minene alaƙarka da shi?”.
Kamar Yoohan ya faɗi ainahin gaskiya sai kuma wata zuciya ta gargaɗesa dayin hakan. Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai ya jingina da fuskar gadon. Hannunsa ya sake maidawa cikin na papansa, cikin kwantar da murya yace, “Papa akwai abinda nake buƙata a wajensa, shiyyasa na kwantar da kaina nake binsa a sannu harna cimma burina. Sai dai kuma gashi kai kazo cikin mintuna goma kacal kana shirin rusamin shiri na. Miyasa zaka biyema su Solomon da shirmensu? Ai koda suka sanar maka na ɓata ko tunanin inda za'a'a sameni kamata yayi ka jira harna dawo kaji ta bakina. Haba papa da girmanka a ƙasarnan amma kake abu tamkar wani mara.......”
Saurin katsesa papa yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. hakanne ya saka Yoohan haɗiye sauran maganar tasa. Papa ya gyara zamansa sosai da cewa, “Naji nayi kuskure, amma kaima harda laifinka. Miyasa tun tuni baka sanarmin ba, bayan kasan niɗin mai baka goyon bayane akan kowanne irin business naka musamman a wannan yakin”.
“Nima naji nayi kuskure to. Amma ina da dalilin ɓoyewar ai. Da ace na sanar maka mi nake shirin yi zaka iya ɓatamin aiki dan kanada gaggawa papa. kai kafi son komai da zafi-zafi a lamarinka. Hakan kuma na taɗiyeka daga nasarorinka. Yanzu da ace bakazo ba da cikin satin nan zan kammala aikina. Amma yanzu kaga ka kawo min togaciya dan zai fara kokwanto a kaina. Kaga kenan saina sake sabon ginin da zai ƙara yarda dani hundred percent kamar farko”.
Cikin tsananin jin daɗi papa ya rungume Yoohan yana faɗin, “I am sorry my sweetheart, kai ɗinne ba'a gane kanka sai kaso. Yanzu dai na maka alƙawarin da kaina zan gyara abinda na ɓata a yau ɗinnan kaji”.
Ɗagowa Yoohan yay da sauri, yace, “Papa da gaske kakeyi?”.
“Ƙwarai kuwa my dear son”.
Wani lallausan murmushi Yoohan ya saki najin daɗi. Dan ya fahimci lallai sai ya nunama papa akwai manufa a tafiyarsa da baba malam sannan zai samu nutsuwar samun damar fahimtar ilimin addinin islama da zai kare kansa anan gaba a wajensu dama duk wani dake a cikin ahalinsa da yasan zai kawo masa togaciya. Amma a yanzu yasan duk yunƙurin da zaiyi sai sun taɗesa saboda rauninsa na kasancewa sabo cikin addini mai ɗunbin haske irin musulinci. A yau kawai daya kasance a ciki jinsa yake tamkar sabon mutum. Tamkar darajarsa ta ƙaru. Duk wani nauyin zuciya da ƙunci da yakan tsinta kanshi a ciki a baya yau sai yaji tamkar ansa kwano an kwashesu tas.
Jikin papa ya sake lafewa tare da lumahe ido. Papa ma dake jin daɗin Yoohan ya fara ɗaukar huɗubarsa ya shiga shafa kansa cike da jin daɗi da annashuwa. Dan shima har zuciyarsa ta gama shirya masa babban aiki akan baba malam tsaf............✍
Tofa masu karatu. Yanzu za'a fara wasan😎 dan haka kumuje zuwa filin daga😉😱🚶🏻.
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/23, 10:10 AM] +234 816 133 8078: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
*_BARKA DA JUMA'A. ALLAH yasa muna cikin bayin da zasu sami gafara a cikinta😭🙏🏻_*
No. 33
..........Koda suka isa can ɗinma wasu jerin motocinne sukazo tarbarsu tare da bodyguard ɗin papa. Haka suka nufi gida zuciyar Yoohan sam babu daɗi.
Sun sami tarba da ga ahalin nasu, musamman ma Yoohan da ya jima dama baya ƙasar. Shima yaji daɗin ganinsu sosai, musamman kakarsa data haifi Papa da ƙannen papan su uku mata da yaransu da ya gani sunzo musu, ga kuma kakarsa data haifi Mom itama dai bata komaba har yanzun.
Madam Chioma sai tattalinsa take kamar ta haɗiyesa dan farin cikin ganinsa, gashi taga ya wani ƙara mata ƙyau da kwarjini da cikar haiba kamar wanda akaima wankan iji.
Haka dai ya daure yana biye musu sama-sama dan kamar ko yaushe fuskar dai babu walwala. Ƙasan ransa ma basusan cike yake da tashin hankalin ganin yanda suka cika gidanba tamkar masu biki, musamman da ya san baƙar ƴar tsamar dake tsakanin kakanninsa guda biyu. A yanzu ma haka ya tabbata wannan zuwan na kakar tasu yanada nasaba da zaman mama Deborah Abujan.
Da ƙyar ya iya zaman mintuna goma a falon ya gudu sama a cewarsa zai watsa ruwa ya dawo. Yana shiga ya ja tsaki tare da dafe kansa. Zama yay cikin kujerar dake ɗakin ya zaro wayarsa a aljihu, sai faman yamutse fuska yake dan har yanzu ransa a ɓace yake akan dawowar dole da papa ya sakashi yi. Wayar ya shiga sarrafawa cike da ƙwarewa. Kansa tsaye yay kiran number baba malam dan yana buƙatar yin magana da shi. Cikin sa'a kuwa bugu uku ya ɗaga.
Sai da suka gaisa Yoohan yace, “Uncle mun iso gida, amma nifa gobe zan dawo kano”.
“Alhamdulillahi, barkanku da hanya. Amma mizaisa ka dawo Yahya?”.
Fuska ya ɓata kamar yana gaban baba malam ɗin, cikin nutsuwarsa da taurin kai irin na samari masu ji da lokacinsu yace, “Uncle ina buƙatar neman sani akan addinin musulinci. Ta wannan hanyarne kawai zan iya yaƙar duk wani ƙalubalen da nake hange da ga ƴan uwana. Ta hanyar neman ilimin ne kuma kawai zan bautama UBANGIJINA. Ba tsoro nake duk wanda ya sanni yasan na zama musulmi ba. Kawai ina buƙatar kwankwaɗar madarar ilimine nima cikin kwanciyar hankali”.
Sosai baba malam yay murmushi har Yoohan na jiyo sautinsa. “Yoohan karka damu kaji, bama sai ka dawoba, inason kabi komai a hankali kamar yanda ka faɗa. Akwai ƙanina dake anan zaune abujan amma yana nan basu koma bikin salla ba, dama na shirya masa magana kawai zaka ringa ɗaukar karatu a wajensa tunda anan kafi zama fiye da nan kano, kaga zaifi maka sauƙi ko kuwa?”.
Ɗan jimm Yoohan yayi alamar tunani, bawai hakan bai masa baneba. A'a tunaninsa shine yanayin aikinsa, dan ya tabbatar a nan abujar ma ba samun zaman yake ba. Yanzu haka kwanaki biyar kawai zaiyi ya wuce Lagos. daga can kuma zai shiga Maiduguri. Yana da tabbacin kuma da wahala ya ƙulla wata guda bai sake barin ƙasarba ma........
“Yahya ko akwai damuwa ne?”. Baba malam ya katse masa tunaninsa.
Ajiyar zuciya ya sauke, tare da miƙewa ya taka jiki a sanyaye zuwa bakin gadonsa ya sake zama. “Uncle babu komai. Kawai dai ina duba yanayin aikina ne da baya barina zaman waje ɗaya, sai nake gani kamar hakan zaiyi wahala a gareni. Inba dai ajiye aikin zanyiba kawai na fuskanci karatun.....?”.
“A'a Yahya bazai yuwuba, duk da bansan ya aikin naka yake ba bazan baka shawarar ajiye aikinka ba. Dan mu musulinci addini ne dake son mutum mai neman na kanka. Ta hakane zaka kare mutuncinka da tarbiyyarka, ka kuma nema halalinka harka tausayama na ƙasa da kai da marayun ALLAH. Yahya karka manta kaifa bawan ALLAH ne mai yawan hidima, sannan bayane goya marayu. Idan ka ajiye aiki yaya masu jira daga garekan zasu kasance kuma?. Kaf Annabawan ALLAH tun daga farkonsu har zuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gareshi, tarihi ya nuna mana nauyin dake kansu na yaɗa kalmar ALLAH baisa sun rayu a rashin neman na kansuba, balle ai tunanin zama daga jiran na wani ko taskar masu mulki. Dukansu sunada sana'oinsu. To inhar mutane masu daraja irinsu sun yi gwagwarmayar neman halalinsu mu su wanene da bazamu tashi munema na kanmu ba”.
Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke. Murya a sanyaye yace, “Hakane Uncle. Tunanin hakan baizo min a rai ba shiyyasa”.
“Karka damu ALLAH yana tare da mu. Insha ALLAHU mafita zatazo daga UBANGIJIN rahama da jinƙai”.
“To shike nan Uncle nagode sosai. ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai. Bara na barka ka huta dan yanzu na sami nutsuwa, ɗazu kam hankalina a tashe yake sosai”.
Ƴar dariya baba malam yay masa sukai sallama ran Yoohan fes. Da ƙarfin zuciyarsa kuwa ya miƙe ya fara zame kayansa dan son watsa ruwa.
★★★
Tunda suka ajiye wayar baba malam ya shiga dogon nazari, harga ALLAH yana jin son Yoohan cikin ransa. hakan har mamaki yake bashi wani lokacin. Duk da yasan UBANGIJI kan jefa soyayyar wani a zuciyar wani batare da wata alaƙa ba a tsakaninsu
Har yanzu baisan abubuwa da yawa ba dangane da Yaron ba, amma sai ya keji zuciyarsa na tsananin ƙyautata masa zato akan abubuwa da dama na rayuwar yau da gobe. Haɗuwarsu ta uku kenan kacal. Amma ya fahimci wasu ƙyawawan halayya da ko a cikin musulman ma ba kowane ke da su ba. Ga ƙyauttawa da yarda da yaron ke bashi ɗari bisa ɗari.
Numfashi ya ɗan sauke wani gefen zuciyarsa na sake ƙarfafa masa gwiwa akan alkarin da yake shirin aikatawa. Yayinda can kuma wata ke gargaɗarsa musamman akan ahalin da Yoohan ɗin ya fito.........
“Malam lafiya kuwa ka zurfafa a tunani haka?”. Umm data shigo tun ɗazun tanata sallama bai jiba ta faɗa tana mai katsesa.
Ajiyar zuciya ya sauke da sauri tare da kallonta. Gefensa ya nuna mata da hannu alamar ta zauna. Batare da tayi musu ba ta zauna kuwa idanunta a kansa. Hannunsa ya saƙala cikinnata yana ɗan sake furzar da huci. “Jannat wani al'amarine yanzun nan UBANGIJI ya saƙaminshi a cikin tunanina akan yaron nan dana sanar miki jiya ya musulunta. Sai dai kuma wani sashi na zuciyar tawa yana gargaɗina dason jefani a kokwanto game da al'amarin”.
“Tom nidai a nawa tunanin sai naga kamar shaiɗanne Malam. mizai hana ka bama al'amarin wani ɗan lokaci haka, sai ka duƙufa neman zaɓin ALLAH akan yuwuwarsa ko barinsa”.
“Eh tabbas kinzo da shawarar hankali Jannat. Insha ALLAHU kuma zanyi amfani da ita. Amma kema inason ki tayani dan ALLAH”.
“Insha ALLAHU zan tayaka Abban Nu'aymah, ALLAH ya tabbatar mana da alkairinsa”.
“Amin ya rabbil-alamin”. Ya faɗa cike da jin nutsuwa da gamsuwa akan shawararta”.
______________★★★
Kwanakin Nu'aymah uku a asibiti aka sallamota. Alhmdllh jikinta yayi ƙyau sosai, sai dai haɗarin da Doctor ya tabbatarma iyayenta tana a ciki akan iya fuskantar loosing mamory shine ya jefasu a cikin matuƙar damuwa.
Yayinda ita kuma da batasan mike faruwa ba sai tata matsalar ta zama Naser. Dan a kwanaki biyun nan daya ɗauka da zuwa gaba ɗaya ya takurama kowanne irin motsinta. Duk da daga gaisuwa babu abinda ke sake haɗasu sai magana kamar kowa. Amma kallon da yake jifanta da shi da tarewa a asibiti da yayi ya tabbatar mata cewar zuwan nasa akwai manufa.
Tun bayan dawowarsu gida Umm ta taimaka mata tai wanka taci abinci da magungunanta ta kwanta danta huta. Shine ta samu damar yin tunani akan Naser ɗin. Kamar daga sama ta dinga jiyo hayaniya na tashi a gidan, sosai mamaki ya kamata, duk da ta tabbatar hayaniyar bata faɗa bace tasan wannan ba ɗabi'ar mutanen gidansu baceba hakan. ‘To minene ya faru?’ ta faɗa a fili cikin sake zurfafa mamakinta.
Kusan mintuna ashirin sai kuma taji hayaniyar ta lafa. bata ko motsa ba balle ai tunanin zata fita ta ganoma idanunta, haka ta cigaba da kwanciyarta tun tana tunani har barci mai nauyi ya ɗauketa saboda a maganin nata akwai na barci daman.
Kiran sallar magriba ne ya saka Umm shigowa ɗakin Nu'aymah ta tadata. Da ƙyar ta samu ta tashi dan barcin nata yayi nisa sosai. Taimaka mata tayi tai alwala kafin tai yunƙurin fita zata barta.....
“Umm wai hayaniyar mi naji anayi ɗazun?”. Ta faɗa cikin katse hanzarin Umm dake ƙoƙarin fita.
Batare da Umm ta juyo ta kalleta ba tace, “Su Abdallah ne, sunma shigo dubaki kina barci”.
Sosai gaban Nu'aymah ya faɗi, sai dai kafin ta sake cewa wani abu Umm ta fice abinta. Shiru tai tsaye hannunta riƙe da hijjab, dan zuciyarta cike take da tambayoyin miya kawo su Yah Ab ɗin gida a yanzun bayan kuma shine da kansa yacema Hajjo sai bikin su aunty Hajarah daya rage saura kwanaki ashirin cif yau ayi. Ganin bata da mai bata amsarta sai ta saka hijjab ɗinta ta kabbara salla kawai.
Koda ta idar bata fitaba tai zamanta a ɗaki, sai da tai sallar isha'i da shafa'i da wutiri sanna ta fito falonsu danta ɗansha iska. Umm kawai ta tarar zaune. Ta zauna kusa da ita tare da ɗora kanta a gefen kafaɗarta.
Ɗan kallonta tayi, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta ɗaura hannunta a wuyanta. Jin jikinta babu wani zafi ya saka Umm sauke ajiyar zuciya da janye hannunta.
“Umm nafa warke”. Nu'aymah ta faɗa tana murmushi dajin ƙaruwar ƙaunar mahaifiyar tata a cikin rai. Itama Umm Murmushin tayi, ta shafa kumatun ɗiyar tata da faɗin, “Ai haka muke fata Nu'aymah, ALLAH ya ƙara miki lafiya dai damu baki ɗaya”.
“Amin Umm”. Ta amsa mata zuciyarta cike da damuwa. tasan iyayenta suna cike da damuwar halin data tsinci kanta, basu da damuwa sama da lafiyarta, basu kuma da burin da ya wuce su wayi gari suga ta warke.........
Sallamar Adawiya ta katse tunanin Nu'aymah. Ta ɗan ɗago daga kafaɗar Umm tana amsawa. Sai dai ganin harda Yah Abdallah ya sata maida kan ta sake kwantarwa zuciyarta najin zafin kishi a kansa.
Rungumeta Adawiya tayi cike da munafincin data saba nunawa idan suna a gaban mutane. Itama sai Nu'aymah ta tarbeta fuskarta fes. Umm dai cike da jin daɗi take dubansu. Yayinda Abdallah kam kallonsu kawai yakeyi.
Bayan sun gaisa da Umm, Nu'aymah ta gaida Abdallah batare data yarda sun haɗa ido ba duk da