Showing 306001 words to 309000 words out of 318746 words
zufa ta jiƙesa a take duk da uban sanyin da ake zubawa a garin. Yace, “Shima sunansa Goshpower, shi ɗin twin brother ɗinane. Wannan kuma matarsa ce”.
“Yayi ɗan gari, haka nake buƙatar jinka. Omar a cire masa bullets ɗin nan”.
Da sauri Omar yace, “Okay Uncle ”.
Tsabar son azabartarwa Umar sai ya ɗauki giyar da papa yasha ya rage ya zuba masa akan harbin. A take kuwa ya saki wata wahalliyar ƙara ya suma. Ko a jikin Omar. Ya amshi First aid box a hannun wani jami'i da sukazo da shi ya cire bullets ɗin cike da rashin tausayi. Sai da ya kammala komai sannan aka zubama papa ruwa ya farfaɗo.
Sai da suka bashi damar hutun kusan mintuna biyar ya daidaita sannan ya fara bada labari.
“Ni da shi twins ne. Muna tsananin kamanni har takai jama'a basa iya banbantamu inba mahaifiyarmu ta faɗa ba. Duk da itama wani lokacin rikicewa takeyi. Suna ɗaya iyayenmu suka saka mana wato Goshpower. Takai inhar ka kira ɗaya a cikinmu sai mu amsa maka mu duka. Mamanmu ta taɓa faɗa mana kaifin basira da muke da shi da farar fata tasa har ana dangatamu da wasu sunaye. Wasuko na tsoronmu da faɗin mama debora ta haifi waɗanda ba mayu. Wannan ba sabon a bu bane daga hallayar mutanen ƙabilarmu da yankinmu wajen danganta mutum mai fari da ƙyawun jiki da suna na tsoro. Mutane basu fara samun basirar banbantamu ba sai da muka fara girma halayenmu suka fara banbanta tsakanina da ɗan uwana. Mu duka munada kaifin basira da wayo, sai dai kowa da yanda yake gudanar da tashi. Duk inda gaskiya take zaka samu ɗan uwana a wajen, niko saɓanin haka shine zaɓi na. Kullum cikin takalo rikici nake wa iyayenmu, ɗan uwana kuma bai gajiya da bayyana gaskiya idan an tambayesa. A duk lokacin kuma da nai niyyar cutar da shi akan wannan abu da yakemin sai bana samun nasa. Dan ko faɗa zamuyi yafi ƙarfina. A haka dai muka kammala primary, akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninmu, amma bamu cika zaman lafiya ba da zama waje ɗaya na dogon lokaci. Bayan secondary skull muka wuce jami'a, inda anan mabanbantan halayenmu suka sake bayyana. Duk da mu duka muna karatu ni a koda yaushe hankalina nakan mata, sannan duk wani abokin banza zaka samu nawane. Hakan na ɓatama ɗan uwana rai, tun yanamin nasiha da faɗamin gaskiya har yayi zuciya ya daina, daga ƙarshema muka raba ɗakin kwana, dama ba department ɗinmu ɗaya ba. Haka dai muka cigaba da tafiya, kafin mu kammala jami'a na zama riƙaƙen mara jin magana dan har harkar ƙwaya na fara, sannan na shiga cikin ƴan Cult. Mun kammala degree ɗinmu na farko, ta hanyar ogan babanmu muka samu taimakon tafiya ƙasar Italy ƙaro karatu. Daga nan ne labarin canjawar komai ya fara. Dan watanninmu biyar kacal a makarantar na sake canjawa daga duk yanda aka sanni. Idanuna sun sake buɗewa sosai harna fara harkar cocaine. Ta hanyar wanda na fara harkar Cocaine ne idanuna suka sake bushewa. Ya kutsa dani cikin manyan mutane konace tantirai dake juya duk wani iya shege na duniya. Nasha wahala ba kaɗanba wajen karɓar horo daga garesu har takai makaranta ma na daina shiga duk da yawan damuwa da kirana da ɗan uwana keyi, tare da yawan ƙoƙarin son sanin abokan mu'amulata. Muna shekarar ƙarshe daya kamata mu kammala degree ɗinmu na biyu ɗan uwana ya haɗu da matashiyar Balarabiyar saudia mai suna Anum. Itama karatu tazoyi, wannan kuma shine zangonta na farko. Sun fara rayuwa kamar abokai a hankali suka rikiɗe zuwa masoya. Sam bansan da wannan soyayya tasu ba sai da tai nisa, muna ma gab da kammalawa. ko nace ɗan uwana na gab da kammalawa. Danni tuni na yaye kaina daga zuwa makaranta. Sai dai nakan shigo lokaci-lokaci saboda harƙallar dake tsakanina da ɗalibai ta kayan shaye-shaye. A wani shiga da nai cikin makarantar ne na haɗu da Anum, wadda ina cikin tafiyata tazo tasha gabana, a zatonta ɗan uwana ne. Da farko na harzuƙa matuƙa, sai dai ƙyawunta yayma idanuna barazana da danne fushina. Cike da tsokana take kallona tana dariyar wai yaushe nasai kayan jikina?, ita dai basu mata ba. Naji haushin kalamanta amma saina fuske na barta akan ɗan uwan nawa ne. Kiran wayata da ogana yayine yana min neman gaggawa yasa na sulale nabar Anum da nufin zan dawo gareta. Daga haka bansan yanda ta ƙareba bayan taga ɗan uwana. Shin ya warware mata mu ƴan biyu ne, kokuwa ya karɓa mata matsayin shine ni?. Kwana biyu da yin haka na dawo cikin skull neman Anum sai dai na samu labarin cewa sun wuce saudia ita da ɗan uwana. Samakon zuwa da yayunta biyu sukai suka ganta da ɗan uwana daba musulmi ba”.
“Duk da bana shiri da shi hankalina ya tashi matuƙa, dan kodai babu komai shiɗin ɗan uwanane ai. Duk zatona ko zasu cutar da shi ne? Naso binsu duk da bansan ina suka nufaba sai kuma wani aiki ya sake taso mana zuwa ƙasar Germany. Haka na tafi al'amarin ɗan uwana na damuna a cikin rai. Kamar wasa sai ga wannan tafiya ta jani tsahon wata huɗu, lokacin da muka dawo ƙasar Italy saina samu munyi graduation, course mate ɗina duk sun kama gabansu har ɗan uwana. Na bincika Anum sai na samu wai itama tabar makarantar. Daga jin haka sai kawai na nufi Nigeria, a zatona ɗan uwana ya koma gida. Amma kash sai na iske saɓanin tunani. An dai tabbatar min yazo wata biyu da suka gabata wajen rasuwar mahaifinmu, nima anta nemana amma ba'a sameniba. Ko damuwa banyi da mutuwar babanmu ba, sai dai jin ogan babanmu ya bama ɗan uwana maƙudan kuɗin aikin da mahaifinmu yay aiki a ƙarƙashinsa dan yaje ya juya hankalina ya tashi na bukaci sanin ina ɗan uwana yake?. Mamanmu bata saniba, abinda kawai ta sanarmin shine ya sake barin ƙasar, bakuma susan ainahin ƙasar daya tafi ba. Yadai bar musu kuɗin da zasu ishesu, tare da musu alƙawarin nanda shekara guda zai dawo musu da daddaɗan labari. Nayi ƙwafa kawai bance komaiba. Daga haka na tattara kayana zan koma. Sai dai kafin na wuce na haɗa harƙalla da abokaina akan zanke turo musu kaya insha ALLAHU suna saidawa su tura min kuɗin. Sunko amince tare da min alƙawarin bazasu bani kunyaba. Daga haka na tattara na koma inda na fito, babu wani zancen nasarar da naci a karatuna dana zauna naima mahaifiyarmu. dan koma ban faɗaba nasan ɗan uwana ya gama tona mata dukkan zance a kaina”.
“Ban sake sanin ina ɗan uwana yakeba, ba kuma mu sake haɗuwa ba sai bayan kusan shekara, ana gab da zai cika alƙawarin daya ɗaukama iyayenmu na komawa garesu da daddaɗan albishir. A lokacin naje kai kaya ƙasar Syria ne. Kwatsam zamu shiga wani shopping mail ni da abokin tafiyata sai ga twin Brother ɗina tare da balarabiyar yarinya dana taɓa haɗuwa da ita a Italy a bazata. Da gani har shi babu wanda baima ɗan uwansa kallon mamaki ba. Hakama mafi yawan jama'ar wajen kallon mamaki suke mana da al'ajabi. A zahiri dai gashi muna tsananin kamanni, amma a shigar sutura da yanayi bama muyi kama da ƴan yanki ɗaya ba. Ni na fara sakin murmushi ina kallon jaririn dake rungume a kafaɗarsa, sannan na kalli Anum na sake kallonsa. Goshpower kaine anan kuma?”.
“Shima Murmushin ya saki a karo na farko yana girgiza min kai, yace my twin bro, wannan suna yanzu na bar maka. A yanzu sunana IBRAHEEM ne, wannan matatace Anum, ga yarona Abdul-Maleek. Woow!! Na faɗa ina dariya da tafa hannu, kafin na miƙa hannun ya ɗoramin jinjiri Abdul-maleek. Yaro ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kama da mahaifiyarsa, sai dai ya kwaso kamannina nima ni da ɗan uwana kaɗan. Ganin dai da gaske munsan juna abokin tafiyata ya barni tare da su yana faɗin mu gaisa shi zaije ya kai kayan zuwa anjima saimu haɗu. Na amsa masa da jin daɗi, dan koba komai ina buƙatar keɓancewa dama da ɗan uwana dan naji yaya batun kuɗin daya amso a Nigeria suke. Dan ko kaɗan banji wani damuwa da fahimtar ya koma musulmi ba. Kamar ya shiga raina kuwa. Sai ya buƙaci mizai hana muje gidansa kawai, ashe nan yake da zama yanzun. Mun shiga danƙareriyar motarsa dani da ke wahalar nema da shiga haɗarin rayuwa ko wadda bata kamitaba bani da ita. Wannan abu ya sosamin rai, amma sai ban nunaba muka shiga, suna gaba shida matarsa niko ina baya tare da jaririnsu a hannu. Al'amari bai kuma tadamin hankaliba sai da muka isa ƙaton gida da yaji kayan more rayuwa a matsayin wai nashine. Lallai nasha kallo, cikin mintuna kalilan kuma matarsa ta gama cika gabanmu da kayan ciye-ciye. Sai bayan munci mun ƙoshi mukai gaisuwa da tambayar bayan rabuwa. Bai ɓoye min komaiba daya shafesa bayan rabuwarmu”.
Yace, (Ɗan uwana kamar yanda na sanar maka wannan itace matata, mun haɗu a jami'ar Italy dakaƙi nutsuwa ka ƙarasa. Da farko tsakanina da ita abota ce, sai daga baya muka fahimci muna son juna. Sai dai ta tabbatarmin babu yanda aure zai kasance a tsakaninmu saboda addinimu ba ɗaya baneba. Hankalina ya tashi domin ina tsananin ƙaunarta. Nai alƙawarin inhar zata yarda mu zama ma'aurata zan koma addininta. Ta sake tabbatarmin indai saboda aurenta ko soyayyar da nake matane zan zama musulmi wannan bazaisa ta yarda ta aureniba. Na musulinta kawai domin ALLAH badan tarayyarmu ba. A hakanma na yarda na amince, a randa muke shirin zan karbi shahada aranar ƴan uwanta biyu sukazo dubata. Sun nuna mata tsantsar ɓacin rai nayin tarayya dani, harma yanda ake musalta musu a cikin makarantar mun zama tamkar wasu miji da mata. Dagani har ita hankalinmu ya tashi muma. Dan tunda nake da ita ko maganar banza bata taɓa shiga tsakanina da itaba. Bata taɓa yarda ko zama gab da juna munyiba balle akai ga aikata wani abu mara ƙyau. Ni bamma taɓa kawo wani mummunan al'amari tsakanina da itaba kamar yanda nasan itama hakanne daga gareta. Kawai dai ALLAH ya haɗa jininmune kawai, kuma ina koya mata karatu. Duk yanda mukaso su sauraremu sunki, daga karshe ma suka tattarata wai zasu wuce da ita. Banyi ƙasa a gwiwa ba wajen tattara duk abinda nake da shi na bisu batare da sun saniba. Sai da muka dira ƙasar saudi-arebia suka fahimci jirgi ɗaya ma muka shiga da su. Sun nuna jin zafin binsu da nayi, amma sai basu hanani na bisu har gidansu ba. Koda muka isa gidansu sunma iyayensu bayani akan dukkan alaƙar dake tsakanina da Anum. Maimakon nai zaton za'a koreni sai naga saɓanin hakan, dan kuwa sun yarda da bukatata ta zama mai salla. Amma babu zancen aurena da Anum, dan suncemin yarinyarsu karatu takeyi. Duk da na shiga tashin hankali saina amince a hakan zan musilinta ɗin. A take kuma na amshi shahada. Komawata musulmi ya sake canja komai, dan kuwa sunmin gagarumar ƙyauta maiban mamaki ta maƙudan kuɗaɗe wai na riƙe kaina, tare da haɗani da wani malami dazan dinga ɗaukar ilimi a hannunsa a ƙasar Italy. Satina biyu a saudia na dawo saboda karatuna. Amma daka ganni kasan bana cikin hayyacina saboda rabani da akai da masoyiyata. Duk na rame na fita hayyacina, amma hakan baisa nayi sakaci da karatuna ba. Na cigaba da neman ilimin addini da zana jarabawar ƙarshe data rage mana na tsahon watanni biyar. Har muka kammala jarabawa banji labarin kaba. Na bincika ance bakaje Nigeria ba. Hankalina ya tashi matuƙa. Amma yaya zanyi. Bayan yin graduation ɗinmu na tattara zan koma gida ƙasata. Amma maimakon nayi 9ja direct saina kasa haƙuri na nufi Saudia wajen Anum. Nayi mamakin tarbar dana samu daga iyayen Anum da ita Anum ɗin kanta daya kasance tazo hutu, dan lokacin karatunta ya dawo nan ƙasar Syria. Albishir na farko da suka faramin shine bani auren Anum, ashe dama sun gwadanine dan suga da gaske nakeson komawa addinin islama kokuwa dan son ƴarsu?. Shiyyasa suka haɗani da malamin dake koyar dani batare da nasan bayanai yake basu ba a kaina. Nayi farin ciki nayi kuka dan daɗi. Sai dai da aka nema na gabatar da iyayena na fito fili na tabbatar musu akwai matsala. Dan nasan kaf danginmu babu wanda zai amshi canjawata matsayin musulmi balle kuma auren musulma kai tsaye. Naji tsoron Anum zata sake kuɓucemin sai gashi ba hakaba. Dan duk da abinda na sanar musu sai gashi sun amince sun bani aurenta. Bayan ɗaurin aurena da Anum an bamu wajen zama kafin ta koma makaranta. Watanmu ɗaya da tarewa ta koma makaranta, ni kuma naje gida Nigeria, sai dai kowa ya tambayeni ina kake sainace kanacan baka ƙarasa naka karatunba sai next year. Na tarar jikin babanmu yayi tsamari, amma sunki kaisa asibiti. Inada kuɗaɗe masu nauyi a accaunt dana samu saboda musilintar da nayi, dan haka nai amfani dasu wajen kaisa babban asibiti aka fara bashi kulawa. Sai dai kash, kwanakinsa huɗu a asibiti ya rasu. Bayan rasuwarsa da kusan sati biyu nace musu zan koma domin yin kasuwanci. Ananne ogan daddy ya bani kuɗaɗen daddy, wai yace a bamu idan munzo, tunda mune manyan ƴaƴansa maza. Na amsa kuɗi na basu wanda zasu wadacesu na koma saudia. Mahaifin Anum shine ya ɗaurani akan harkar kasuwanci acan ƙasar Syria, ya bani shawarar na koma can kusa da matata ina kasuwancina tana karatunta. Naji daɗin wannan shawara kuwa. Tafiyata Syria ta zama tushen nasarata, dan ina zuwa na iske matata na laulayin ciki. Nayi farin ciki matuƙa, harma bansan yaya zan musalta makaba. Haka na zauna kulawa da ita tare da fara kasuwancina. Cikin amincin ALLAH sai gashi dan danan na haɓaka. Saboda na farane da kuɗaɗe masu nauyi. sannan kuma ta hannun babban mutum irin mahaifin Anum. A haka cikin Anum ya shiga watan haihuwa, tana gab da haihuwa na sayi wannan gidan da nake ciki, tare da motar hawa. Sannan na zauna na banbance dukiyar da take matsayin mallakina, na kuma fidda wadda ta kasance ta mahaifinmu. Kwanaki uku da yin haka Anum ta haihu namiji, wanda yaci suna Abdul-malik. bansan yaya zan bayyana maka ɗunbin farin cikinaba ɗan uwana. Amma babu abinda zancema ALLAH sai godiya. A yanzu haka watan Abdul-maleek uku a duniya, muna shirin zuwa Saudia ne domin nunasa ga dangin Anum dan babu wanda ya taɓa ganinsa sai mahaifinta da yazo mana nan sanadin harkar kasuwarsa. Daga Saudia kuma zamu wuce Nigeria na nunata ga dangina, na kuma sanar musu na zama musulmi duk da a tsorace zuciyata take. Dan yanzu haka maganar da nake makama nayi cinikin wani gida a Lagos, idan munje can zamu ɗan zauna kafin hutun Anum na ƙarshen shekara ya ƙare. Waɗanan takardun sune takardun shaidar company na dana mallaka da dukiyata. Insha ALLAHU kuma zan mallakashi ga Abdul-maleek ne. Dan haka kaima inason ka zama shaida, kaimin signing anan wajen, a duk lokacin da yakai shekaru talatin na girma zan mallaka masa shi. Wannan kuma sune takardun dukiyar mahaifinmu, idan nazo Nigeria mu dukanmu zamu haɗu mu saka hannu alamar tabbatarwa da banawa bane ni kaɗai).
“Rungumesa nai a lokacin, na nuna masa tsantsar jin daɗina da wannan ƙoƙari nashi, tare da bashi goyen baya akan zamansa mai sallah. Yaji daɗin yanda na bashi goyon, hakama matarsa. Sai dai ni a cikin zuciyata ƙulla ta yanda zan kwashe waɗanan takardun nakeyi, tare da damfare duk wata dukiya da yake fankamar ya tara. Banbar gidanba sai dare, na tafi da ƙudiri kala-kala a cikin raina da zuciyata”.
“Washe gari ma naje na samesu, shine ya ɗaukeni ya zagaya da ni duk inda companys ɗin suke guda biyu. Na ƙara girgiza da wannan al'amari, dan dukiyace bata wasaba ɗan uwana ya tara. Tofa sai tunanina ya ƙara faɗi da girmama. Dan koda nabar wajensu a ranar kasa barci nayi, har takai na fito na bayyanama abokin tafiyata. Yace na bashi dama zaiyi tunanin ta yanda dukkan wannan dukiya zata zama tawa, amma sai nan da kwana biyu mun gama abinda ya kawomu zai faɗamin hukuncin daya yanke. Naji daɗi, na kumayi murna. Sai dai wayewar garin ranar al'amari ya canja salo, dan bamusan yaya akaiba aka kama wanda muka kawoma kayan cocaine. Har bincike yazo ta kanmu. Da farar safiya mukaji jiniyar motocin ƴan sandan ƙasar. Hankalina ya tashi matuƙa ni da abokin tafiyata, cikin zafin nama muka samu nasarar tserewa ta bayan gidan kafin ƴan sanda su gama shigowa gidan. Muna barin gidan muka rabu nida abokina, domin wannan gudune na ceton rai, kuma hakan abune da kowa ya sani daga tsagera. Idan bala'i ya tunkaro kowa takansa yakeyi. Ba'a sauraren dukiyar da aka tara balle abokantaka. Cikin kiɗima na nufi gidan ɗan uwana, dan duk da wannan bala'i da nake a ciki ban manta da batun takardu ba. Ina isa na samesu a tsakar gida suna hutawarsu cikin kwalliya. Dakewa nai daga ruɗanin da nake ciki na amshi jaririnsu, tare da faɗama matarsa nifa inajin yunwa. Dariyar tsokana suka dinga min, ɗan uwana na faɗin to nazo nayi aure, yafimin wannan gararin, danshi sofa yake na dawonan tare da shi mu haɗa ƙarfi wajen kula da kasuwancinmu. Murmushi kawai nayi, na shiga daga ciki ɗauke da yaron. Matar ta shigo ta bani abinci. Tana kammala haɗamin komai ɗan uwana ya shigo, kallonta yay cike da so da kauna, yace tunda ga bro yazo kizo muje muyi shopping ɗin nan da bamuyiba jiya, sai mubar Maleek tare da shi dan harmu dawo da wahala ya farka. A take ta amince da shawararsa. Yayinda ni kuma kaina ya kawomin wuta a take. Jacket ɗin jikina na cire jin yana faɗin bara ya karo riga a saman kayansa. Nace bro indai rigace ga wanann ka saka nasan zata maka ƙyau, dan yanzun nan dazan fito na ganta a wani shago na siya. Nama tambayi biyu akace babu. Cike dajin daɗi ya amsa, dan shi mutumne mai saukin kai. Sannan bashi da saurin zargi.