Showing 291001 words to 294000 words out of 318746 words
Abdullahi, tare da shirinku na bayan mutuwar Zainabu zai aureta. Hankalina ya tashi, dan zan iya cewa wannan shi e sanadin girmama samuwar hawan jini na ma. Na riƙe komai a raina na kasa faɗa har ƴar uwata tazo diba ni (Ananah) banso faɗa mataba. amma na fahimci dolene na samu shawara daga wani kafin lokaci ya ƙure. Dan wannan abune mai matuƙar sarƙaƙiya. haka na samu lokaci a wani dare mukai maganar. Itama hankalinta yayi ƙololuwar tashi dajin wnanan zance. Itace ta kawo shawarar ai tunda SARAN ƁOYE kukeyi muma yakamata mubi ta ZAGON ƘASA mu kamaku a hannu dumu-dumu. Itace ta kawo shawarar sace Zainabu ranar daren aurenta, dan hakanne kawai zai wargaza auren cikin sauƙi. A cikin shirinmu Ameer ya shigo rayuwar Zainabu matsayin abokin Abdullahi. Ameer kuwa abokin Naser ne, dan Naser shine mukaba aikin a hannunsa. Nice da kaina na shiga na haɗo kayan Zainabu a ɗakinta, na kuma jajjefa wasu ta taga. Ina cikin yi Yusrah ta shigo ɗakin da alama banɗaki zata shiga. Na tabbatar taga mutum, sai dai ban saniba kota gane waye ko bata ganeba. Abdullahi yaso lalata mana shiri a ranar saboda jan ra'ayin Zainabu da yay tayi akan suyi hira. Sai dai kuma ta dalilin Adawiya hirar batai tsaho ba. Naser ya samu damar ɗauke Zainabu ya kaita wani gida. Bamu dawo da itaba sai bayan sati biyu. Daga haka muka cigaba da bibiyar duk wani taku naku. Hatta da sace Number likitan da zaima Zainabu aiki naji a raina wani a cikinkune ya saceta, sai dai banida hujja shiyyasa nai shiru. Ina kan sani na amince da aurama Abdallah Adawiya saboda ɗana tarkon farko a gareku, inason kuma tabbatar da hannun Abdallah akan shirinku, kokuwa kuna amfani da shi ne kawai batare dashi kansa ya sani ba?. Na kuma hana Yusrah tarewa dan dama bazan yarda ta tare ɗinba. Tafiya da Zainabu Umrah yanada nasaba da son sake tabbatar da komai. Na kuma tabbatar ɗin. Waya da aka ɗagama Khadijah na hana Abdullahi zuwa Nigeria duk a cikin shirinmu ne. Munsa Nasiru ya dawo rayuwar Zainabu ne daman dan ya sake wargaza magar auren da Abdallah keta naci da son sake ganin ya ƙullu tsakaninsa da ita. Da kuma sanin da nai duk cikin shirinkune”..
“Maman Aaida data zama ƙawar Adawiya a saudia duk a cikin shirinmune itama. Mune muka sakata samun kusanci da Adawiya da ɗorata mataki-matakin kasancewa da Abdallah, a tunaninmu ko zaku dawo hayyacinku ku yarda da ƙaddara. Amma sai kuka sake tura kanku a cikin ramuka. A tarayyar maman Aaida da Adawiya ne ya bamu damar sake fahimtar bada sanin Abdallah kuke wani abunba. Dan ba komai kuke sanar masa akan shirinku ba, sannan lallai da gaske yana son Zainabu duk da ya raba hankalinsa biyu akan soyayyarta da dukiyar mahaifinta da kuka ƙwaɗaita masa a rai. Ta kuma hakane muka fahimci banzar sana'a da Abdallah yake ƙoƙarin jefa kansa a ciki. Amma Alhmdllh munyi ƙoƙarin maidosa hanya ta dalilin mijin maman Aaida ɗin, wanda ta hannunsa mukejin duk wani motsin Abdallah a yanzu haka. Maganar cikin Zainabu shine ya hautsina min tunani, saboda batare kukai aikinba yasa ban fahimci komaiba a ciki ba, duk da ina zargin kuɗinne duk da haka. Koda na tabbatar Zainabu takai mutuncinta gidan aure wannan ruɗanin na maganar ciki bai barniba sai yanzu da Fauza ta warware komai akan samuwar ciki da fitarsa. Na kai Uwaliya aiki Abuja ne dama dan Lurwanu yay yunƙurin yin amfani da ita kamar yanda Nasiru ya gano mana hanyar da sukebi wajen aamfani da Rabi itama. Na tabbatar alwashin da yahya ya ɗauka akan gano ko wanene bazai tashi a banzaba. Bakuma zai samu sauƙin ganowarba sai da wani a tsakani. Shiyyasa na tura Uwaliya ta fara sauka gidan Lurwanu ta kwana biyu sannan aka kaita wajen Zainabu. Ita kanta batasan amfani zamuyi da itaba, na ɓoyene saboda fahimtar idanunta a buɗe suke dasan kuɗu itama. Ko nawa Lurwanu ya bata lallai zata amince tai masa aikin daya buƙata akan Zainabu. Ankoyi sa'a shirinmu ya tafi dai-dai saboda Nasiru ma mutumne mai ƙwaƙwalwa da hikima. Hatta da yawan shigowa Najeriya da Abdallah ke yawan yi suna ganawa da Lurwanu duk mun sani dan duk inda yasa ƙafa Nasiru na biye da shi batare da yasani ba. Kai hatta binmu da Abdallah yayi ƙasar da akaima Zainabu aiki nasani. Dan ko a randa Yahya ya gansu suna magana shi da Lurwanu nima na gansu, sanin da nayi babu ta hanyar da zasu iya cutar da Zainabu saboda tsaron da take samu a wajen yasa na watsar da al'amarinsu. A yanzu haka mijin maman Aaida shine ya taso mana ƙeyar Abdallah zuwa Najeriya harya halarci wannan bikin duk da yazone a makare”.
Ta ƙare maganar da nuna inda Abdallah ke zaune kansa a duƙe tamkar munafuki. Harga ALLAH da yawan mutanen dake falonma sai yanzu sukasan da zamansa a falon. Hajjo ta sake gyara zamanta tana duban kowa.
“Nasan wasu zasuce miyasa duk nasan wannan amma na ɓoye matsayina na mahaifiya ga waɗan nan yara su duka?. Amsarku itace duk da ni mahaifiyace a garesu fitowa da lamarin kai tsaye dasa sabuwar fitinace da zatafi wadda muke ciki girmama. Dan inhar da tun a wancan lokacin na fiddo komai zasu kare kansu akan ba haka bane, su jefa zuciyarmu a ruɗani mu duka kokuma su canja salo, ko komai ya ɓaci duniya tasan halin da muke a ciki maƙiyanmu dake a waje su sami ƙofar yin kutse cikin wannan zuri'a su ƙarasa ɓarar da sauran abinda ya rage daga garemu. Ƙyaƙyƙyawar rayuwar da aka gina tsahon shekaru zata wargatse ta lalace kowa ya fita a hayyacinsa. Idan hakan ta kasance banci riba ba. Sannan wahalar da malam ya sha akan son gina zuri'arsa baici riba ba kenan shima. Dukansu ni na haifesu, tun a ƙuruciya nasan halin kowannensu. Dama can Lurwanu hatsabibine tun yana ƙanƙaninsa, a cikin ƴan uwan nan nasa babu wanda baisha wahalarsaba. Kaifin addu'a ne kawai ya ladabtar da shi, sai kuma kawaici da iya zama da su da ɗan uwansu yayi. Na yarda inhar ka samu ƙyaƙyƙyawar tushiya a cikin yabanyarka da izinin ALLAH zaka azurta da ƙyaƙyƙyawar albarka. Kasancewar ɗan malam ɗa nagari, mai haƙuri da kawaici, mai juriya da riƙe girmansa matsayin babba ga ƴan uwansa shine ya taimaki wannan zuri'a da kaiwa haka batare da mutanen waje sunyi tunanin samun ɓarakar shigowa cikinmu su wargazamuba. ALLAH yayima ɗan malam baiwa da ƙyautar abubuwa da yawa. Ilimi, hankali, dattako, dukiya, sanin ya kamata, nasaba. Sai dai hakan ba yana nufin zai more rayuwarsa ɗari bisa ɗari ba tunda ya haɗa komai. Shiyyasa ALLAH ya jarabcesa da atsabibancin Lurwanu dana matar ɗan uwansa Mustapha. Suka dinga wajiga rayuwarsa saboda UBANGIJI ya gwada ƙarfin imaninsa. Koni da nake mahaifiya a garesa inajin sha'awar koyi da halayensa na haƙuri da juriya duk da zuciyarsa na ƙonuwa shi da matarsa da ƴaƴansu. Wannan kawaicin da uziri shine ya kaimu ga matakin nasarar da a yau gashi su da sukecin dunduniyar sane a gabanmu suna faɗin tsiyatakun da suka aikata da bakinsu, miyafi wannan nasarar daɗi ga bawa kuwa?”.
Abban Adawiya ya share hawaye da fadin, “Babu inna, wlhy babu makamancin wannan nasara kuwa, dan hakan yana nuna mana duk mai haƙuri da tsayawa akan gaskiya, da adalci gana ƙasa da shi, ma'abocin bautar UBANGIJI, ALLAH bazai taɓa taɓar da shi ba, ALLAH bazai taɓa ƙasƙantar da shi ba. ALLAH bazai taɓa wulaƙanta rayuwarsa a hannun azzalumai ba. Ni shaidane akan hakan, dan Lurwan yaso jan ra'ayina sosai akan lamarin Yaya, kullum zancensa shine Yaya cutarmu yake a ɓoye. wai tayayama za'ai ace a raba mana gado tare, amma yazo ya fimu komai. Yafi kowa kaso mai tsoka a duka kamfanonin mu. Ga wasu harkoki da yakeyi kuma a gefe masu bala'in bashi kuɗi. Sannan kuma wai ai muduka munada ilimin addini amma tayaya za'ace kowa yafi sonsa da ƙaunarsa dajin maganarsa. Hatta mahaifiyarmu sai abinda Yaya yace takeyi a gidannan. Acewarsa wai Yaya ya asirce kowane kawai amma yake fakewa da malanta. Da farko na fara bin ra'ayinsa. Sai dai ba'ai nisaba ALLAH ya soni da rahamarsa ya fargar dani, danni dai ban taɓa ganin wani abu saɓanin ƙyautatawa ga yaya ba. Da kuɗinsa na gado ya tsaya mana mukai karatu duk da kuwa muma muna dasu. Da kuɗinsa na gado ya dinga mana hidimar rayuwa tamkar mahaifi. Idan mukai kuka shima sai kaga ƙwalla a idanunsa. Idan mukai ciwo shima sai kaga raɗaɗin a fuskarsa. Idan mukai dariya sai kuga tashi fuskar faɗaɗe da murmushi mai tsada. Shine ya nuna mana hanyar tashi mu nema na kanmu, dan shine ya fara shan wahalar kafa dukkan kasuwancin da ayanzu sune suke riƙe da duk wani motsinmu. Shine ya tsaya akanmu mukai karatu tuƙuri bayan ya tattare martabar mahaifinmu ya riƙe mana bai bada ƙofar da zamuyi sakacin da zata kufce mana ba. To miyasa son zuciya zaisa zamuyi sakaci ya sargafe tunaninmu?. Hakan yasani janye jikina daga wannan mummunar a ƙidar naita istigifari akan zargin da aka sakani nai masa babu gaira babu dalili. Ashe ya koma sun ƙulle da matata suna cutama yaya da zuri'arsa da basujiba basu ganiba. Minene laifin waɗan nan ƙananun yaran da basuma gama sanin rayuwarba balle daɗinta. Basai nace komaiba, dan Fauza azabarma da kike ciki ta isheki. kai ko Lurwanu ka jira naka sakamakon kaima, dan duk wanda yaci zalin gwani rabbi zai saka masa da alkairi a duniya ko a lahira”.
Abba Musbahu yace, “Tabbas haka zancenka yake Yaya Mustapha. Dan koni ma yaso jan ra'ayina. Sai dai fa ka sanni ni, a zuwan farko na shata masa layi duk da kasancewar sa yayana. Shine dalilin da yasa zama waje ɗaya a Lagos ya nema gagararmu sai da yabi ya lallaɓa yaya malam ta ƙarƙashin ƙasa aka maidasa Abuja aka buɗe masa company wanda ALLAH kaɗai yasan irin ɓarnar da yake a cikinsa shi da abokan aikin nasa. Domin a duk lissafin ƙarshen shekara idan mukayi sai mun tsamo yawan cuwa-cuwa da akai da kuɗaɗen company. Shi Yaya cayake daga ma'aikatanne. Niko nasan Yaya Rudwan ne dama wlhy. Nayi shiarune kawai dan ina fatan Yaya Malam ya kamashi da hannunsa dumu-dumu. To ashe aikin nasama ba anan ya tsayaba duk bala'in da ake kunnama Yaya malam da ƴan ƴaƴansa biyu da suka rage yanada hannu aciki. Wlhy ko alhakin ƙananun yaran nan bazai barku ku zauna lafiya ba balle kuma haƙƙin yaya malam da Umm-Muhammad da a kullum burinsu su ƙyautata rayuwar ƴaƴanmu a gidan nan. Kaɗanma kuka fara gani yanzu kuma”.
Momyn Abdallah daketa kuka tun ɗazun tace, “Lallaikam yanzu suka fara gani Musbahu. Wannan wace irin cin amanace haka? Wane kalar son zuciya ce?. Ba yaya kaɗai kuka cutarba ai, muma kammu iyalanku kun cutar damu, kun shiga haƙƙinmu. Wace irin ni'ima ce ALLAH bai baku ba a rayuwa amma ku gaza gode masa har sai kun ɗaura ɗammarar shiga haƙƙin wani. Alhalin dukiyar da kukema zarin ma kunfi mai ita amfana da ita ku da iyalanku. Wai miyasa ɗan adam ɗin da ALLAH yayma ni'ima shike fin tsaurin idon rashin gode masa? ALLAH ya baku ilimi alhalin ga wasu can jahilai ko yanda zasu bauta masa basu saniba. Ya baku lafiya, ga wasu can a gadon asibiti kwance basu da kuɗin neman lafiyar. Ya baku muhallin zama. Ga wasu can suna raɓe-raɓe basu da ko kangon da zasu raɓa. Ya muku sutura. Ga wasu can tufafin da zasusa su rufe tsiraicinsu bai wadacesu ba. Ya baku mutunci da daraja a idon duniya, bayan akwai dubunku da suka fiku shekaru a ƙasƙance. Ya baku dukiyar da bama kuda iyalanku ba, waɗanda suka raɓu da ku zaku iya ciyar da mutum sama da ɗari a kowanne yini. Ga wasu can iyalansuma basa iya wadatawa. Ya azurtaku da ƴaƴa maza da mata, ga wasu can suna nema da miliyoyin kuɗaɗe basu samu ba. Ya azurtaku da iyaye na gari, bayan ga wasu can iyayen nasu a gidajen baɗala. Duk waɗan nan ni'imon kuka gagara godema ALLAH a kansu, to mikuke jira UBANGIJI ya muku kafin ku gode masan? Mi kuke nema kukuwa a duniya bayan duk waɗan nan tarin ni'imomin da yay muku. Bafa kunfi waɗanda basu da shi bane, ba kuma tsoronku yasa aka baku ba. Ba kuma ƙoƙarin ibadar kuce tasa aka baku ba. Kai jama'a kaicon hannu mai butilcin amsa ga mai bashi. Kaicon zuciya mai baƙin cikin cigaban mai ƙyautata mata, Kaiconku Rudwan, tabbas bazan yafe muku ɗoramin yaro akan mummunar aƙida da kukayiba........”
Kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana. Shi dai Abban Abdallah ya kasa koda ƙwaƙwaran motsi, kansa duƙe a ƙasa ya gagara kallon kowa. hakan yasa babu wanda zai iya cewa ga a yanayin da yake.
Baba malam ma dai kansa a ƙasa yake duƙe. Babu mai shaida yanayinsa. Umm kam ganin al'amarin take tamkar a mafarki zuwa anjima zata farka. Zuciyarta ta kasa gaskata komai akan Abban Abdallah da Fauza. Mutanen da sukafi kowa kusanci da su a gidan. Kai jama'a duniya ina zaki kaimu?.....
Jin kowa bai ƙara cewa komai ba yasa Jay yin gyaran murya. Kusan duk kallonsa sukayi. Ya furzar da numfashi na takaici da faɗin, “To inaga idan kun gama da su zamu kaisu station mu haɗa bayanansu sai mu miƙasu kotu su amshi hukunci kamar yanda shari'a ta tanadar”.
Tari Addah ta fara kaɗan-kaɗan, hakanne ya saka baba malam ɗagowa ya kalleta ya maida dubansa ga Jay. “Muhammad Jawaad mubar zancen zuwa kotu kaji. Ita wannan kuma miya rage mata a duniyarma gaba ɗaya. Ai wannan izayar da take ciki kawai ta isheta izina. Sai dai mu taimaketa mu miƙata asibiti kawai....”
Murmushi Jay yayi yana jinjina kai. “Duk da haka malam ai ya kamata su fuskanci shari'a kodan hakan ya zama ilimi ga ƴan baya masu sha'awar sake aikatawa. Duk da tana cikin halin ciwo bashi ke nuna zata mutu ba, mutuwa ta ALLAH ce, takanzo a sanda taso ga wanda taso. Dan haka zamuje asibitin taga likita amma bisa ƙarƙashin kulawar hukuma. Shi ko zamu wuce da shi station”. Ya ƙare maganar yana nuna inda Abban Abdallah yake zaune.
Baba malam zai sake magana Hajjo ta katsesa da cewar, “Ɗan malam hakan shine dai-dai kuma ya kamata. Kaga idanma da mai sha'awar aikatawa a nan gaba sai ya bada himma”.
Tarin Addah daya ƙara ƙarfine ya sakasu duk maida hankalinsu gareta. Da wannan damar Abban Abdallah ya samu ya sulale a hankali yabar sashen. Sauran jami'an dake a waje basusan yaya aka ƙareba shiyyasa basu hana Abban Abdallah bi ta gabansuba ya wuce sashensa yaje ya haɗa duk wasu abubuwa nasa masu muhimmanci ya zuba a ƙaramar jikka ya fito. A gaban jami'an ya shiga motarsa maigadi ya buɗe masa gate ya fita batare da shima yasan mike faruwa ba.
Daga ciki ma babu wanda ya farga da rashinsa sai bayan an fito da Addah daketa faman zuba aman jini aka saka a mota domin kaita asibiti. Suna wucewa su Jay suka koma kan Abban Abdallah sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye. A take suka hau cigiyarsa a lungu da saƙo na gidan, sai daga baya sukeji daga bakin maigadi cewar ya fita a mota tun kusan mintuna talatin da suka shuɗe.
A razane Jay yace, “What?!!, shine kuka barsa saboda baku da hankali?!”. Yay maganar wa yaransa. Duk rawa jikinsu ya kamayi suka hau rantse-rantse su basusan mai laifi bane. Ai kota kansu Jay baibiba ya shiga motarsa shi da Bily da Little. Suma duk suka shiga a wacce sukazo. sai da suka tambayi maigadi motar daya fita a ciki da lambarta sannan suka fice a guje.
Wayar Jabeer Jay ya kira, yana ɗagawa ya ce, “Jabeer inason a baza zami'ai a kowacce hanyar fita garin kano domin tsaidamin mota mai Number..... Ruwan toka”.
Jabeer na amsa masa ya yanke kiran, C.P ya kira shima dan ya taimakesu.
__________★★
A gidan su Nu'aymah kam musalta muku halin da suke ciki ɓata lokacine. Dan motocin su Jay na fita a gidan Umm ta yanke jiki ta faɗi. Hakama Malam ƙarami shiɗe musu yayi. Ga kukan da su Adawiya keyi ya taru ya ƙara ɗaga musu hankali. Baba malam kansa dauriya kawai yakeyi dan gaba ɗaya jinsa yake kamar kansa zai tarwatse dan ciwo. Gashi su Yoohan sun wuce da Addah asibiti. Hakan yasa dole aka kwashi su Umm ma zuwa asibitin.
Ɓangaren Abban Abdallah kam tunda ya fito anguwarsu kai tsaye hanyar Katsina ya ɗauka, shi kansa baisan mi yake shirin aikatawaba. Ceton kansa ko gudun kunya? Ko tsoro?. Gudu ya ke na hauka babu wasa a cikinsa. Musamman daya kasance ta gefe-gefen gari yake tafiyar, dan bai yarda yabi ta cikin gariba sam. Yana fara ɗaukar hanyar Ktn bayan ya gota Dawanau kaɗan ko mintuna goma baiyiba ya ga motar ƴan sanda na binsa a baya. A take ya ƙara ƙarfin gudun motar tamkar ya manta da kasancewarsa Dattijo. Abu kamar a film suka fara rere tsakaninsa da jami'ai.
ALLAH sarki rayuwa, duk iyawarka baka isa zarce ƙaddarar UBANGIJI ba. Dan kuwa dai wannan ƴar tsere na Abban Abdallah da ƴan sanda sunansa gudu akan igiyar ƙaddara. Dan kuwa bisa tsautsayi sukau taho mu gama da wata mota dake nufo cikin kano. A take waccan tayi gefen titi, shiko ta Abban Abdallah sai ta kife ta fara wuntsil-wuntsil daga titi ya gangara cikin gona. Tun suna jin yanda yake neman ɗaukin UBANGIJI har sukaji tsit, motar kuma ta bugi bishiyar dalbejiya ta tsaya cak.
Cikin sauri ƴan sandan da dama tuni sun fito a mota suka nufi motar domin bashi taimako. Da ƙyar kuwa akayi kama-kamar ɗaga motar aka zarosa a ciki. Gaba ɗaya jikinsa yayi face-face da jini har ba'a iya gane inane ya bugu koma yanada rai ko ya