Showing 288001 words to 291000 words out of 318746 words

Chapter 97 - saran boye complete by Queen meenali

01 Jul 2024

41631

kuwa. Da farko ta hanyar malami kawai nake samun nasara akan Firdausi, amma haɗuwata da kai ya sani hutawa daga zuwa wajen kowanne irin malami, dan kai kafi malamin hatsabibanci ma. Yau ranace mai kama da ranar hissabi, yanda nasan cewar ayyukanmu bazasu ɓoyu ba a wannan rana dake jiranmu to ina tabbatar maka yau ɗin nanma tun a duniya zan fara fallasasu dan kowa ya yaji. Dan wlhy yanda duniya tasan waceceni a yau, ƴaƴana sukaji shukar danayi, mijina yaji, dolene kaima uwarka da yayanka da matarka da ƴaƴanka da sauran ƴan uwanka susan kai wanene a cikinsu”.
       Sake zabura yay kanta kuwa da ƙarfin tuwo ya fisge hannunsa a cikin na hajjo, amma sai Dawood yay azamar shan gabansa da bindiga. “Ka kama girmanka, inba hakaba zan maka irin tabon dake a ƙafarta kaima. Ka nutsu ka riƙe sauran mutuncinka”.
      Jikin Abban Abdallah rawa yakeyi sosai, dan bai taɓa kawowa a ransa tone-tonen Addah zai iso kansaba musamman da yasan irin gargaɗin da yay mata kafin ya yarda su fara aiki tare, da kuma kalaman datai amfani dasu a yau wajen shimfiɗa labarinta. Yayi zaton zata rufa asirinsa ne.
            A hankali baba malam ya yunƙura ya miƙe hawaye na sakko masa akan fuska. Yasa babbar rigarsa ya share sannan ya dubi jama'ar falon. “Inaga dan ALLAH mubar maganarnan gaba ɗaya, wannan tone-tonen a ganina sam bashi da amfani. Sun aikata abinsu a ɓoye sai mu barsu kawai da nauyinsu suje can su ƙarta. Bana buƙatar jin abinda Rudwan ya aikata ku barni haka, n.......”
      “Dolene kuwa kaji ɗan malam, dan haka koma ka zauna”. Hajjo tai maganar cike da bada umarni. Baya iya ƙetare maganar mahaifiyarsa. dan haka ya koma jagwab ya zauna yana mai dafe kansa da hannaye biyu saboda jirin dake kwasarsa.
       Addah tai murmushi mai ciwo da cigaba da faɗin, “Lurwanu shiya canja tunanina daga fushin rasa masoyi zuwa na mallakar dukiya, dan huɗubarsace ta fahimtar dani cewa ina dukan taiki ne kawai ina barin jaki, haukana kawai nake akan nafi Firdausi ƴaƴa nafita nasara yanzun. sai dai ashe dukiyar da mijinta ya mallaka a cikin ƴan uwansa ta ninka wadda nawa mijin ke da shi sau fiye da bakwai. Kaso biyu na dukiyar gidan nan mallakarsace, kaso ɗaya ne na mazajenmu da Hajjo. Gaba ɗaya komai ya susuce min a lokacin nama nema rasa makamar tunani da hankalina. Amma sai ya dinga kwantarmin da hankali ta hanyar nunamin inhar zan taimakesa muyi aiki tare to lallai dukiyar baba malam zata koma ƙarƙashin ikonmu ne. Nace masa ta yaya kenan?. Ya bani tabbacin ta hanyar Abdallah. Tunda akwai shaƙuwa sosai tsakanin Nu'aymah da Abdallah hakan na nufin nangaba kaɗan soyayya zata iya bayyana a tsakani duk da ƙuruciyarsu.  Dan bazaiyi wasaba wajen ɗora Abdallah akan matakin daya kamata game da Nu'aymah. Ɗari bisa ɗari na yarda da hakan a wancan lokacin. Saboda a yanda ya faɗaɗa min bayanansa na fahimci inba ta wannan hanyarba babu ta inda zamu mallaki wannan dukiyar. Wannan shine sanadin dunƙulewarmu waje guda ni da Lurwan muka fara aiki tare. Amma wlhy kullum hankalinmu cikin ƙara tashi yake gameda haɓaka da dukiyar Sooraj keyi abun tamkar roƙo. Shima kuma sake ɗaukaka yakeyi fiye da sauran ƴan uwansa akan ilimi da soyayyar mutane. Wanda ɗaukakar tasa itama tana ɗaya daga cikin abinda ke ƙara ɗora Lurwan ga son cutar da shi. Haka muka cigaba da tafiya munama Sooraj *SARAN ƁOYE* da iyalinsa harma da duk wanda tsautsayi ya sakko a tarkonmu. Dan kuwa dai Rabi na ɗaya daga cikinsu. Mun sakata tana mana wasu ayyukan akan dole wasu ko bama tasan muna amfani da ita munayiba musamman ta wayarta. Akwana a tashi mun cigaba da tafiya wataran muyi nasara akan aikinmu wataran su tsallake tarkonmu. A haka maganar soyayyar Abdallah da Nu'aymah ta fito, har takai Nasir yayi zuciya yabar gidan nan dan shima yana sonta. Da gaske Abdallah tsananin son Nu'aymah yakeyi, kamar yanda itama sonsa takeyi saboda tsananin shaƙuwar dake a tsakaninsu, amma a hankali muka fara canja tunanin Abdallah muna kwaɗaita masa dukiyar Sooraj. Tun yaron nan baya fahimtar mi muke nufi yana bijire mana harya hau kan hanya saboda ɗaukesa da iyayensa sukayi zuwa wajensu. Dan mun fahimci zamansa da Firdausi ne ke mana illa komin masa huɗuba itake wargaza mana komai ta hanyar ƙaunar da take nuna masa ta gaskiya. Gaba ɗaya mun tattara shirinmu ne akan auren Nu'aymah da Abdallah, shiyyasa duk likitan da aka samo da tabbacin zai mata aiki akan matsalarta sai munbi duk hanyar da zamubi wajan daƙile hakan saboda wani likita ya tabbatar mana da wahala ai mata aikin nan ta tashi, mukuma burinmu muyi amfani da wannan damar sai bayan aurenta da Abdallah aimata aikin ta sheƙa mu samu abinda muke buƙata, dan inhar muka gama da yarinyar kauda ƙaninta abune mai sauƙi a garemu. Har ALLAH yasa burinmu ya cika aka tsaida ranar auren Abdallah da Nu'aymah. Sai dai Abdallah baisan da shirinmu akan bayan aurensa da Nu'aymah so muke ta mutu ba. Wannan daga ni sai mahaifinsa ne muke shirinmu. Amma kash tarihi sai ya nema maimaita kansa tsakanin Adawiya da Nu'aymah tamkar ni da Firdausi. Dan kuwa dai Adawiya soyayyar Abdallah ce tai mata shigar sauri, tanata ɓoyewa har takai ta gagara hakan lokacin data tabbatar zai kubuce mata. Na jima da fahimtar tana sonsa amma sai na ɗauka kawai ƙuruciyace, sai da aka tsaida rana na fahimci yarinyata da gaske takeyi. Shine fa na samu Abban Abdallah da zancen kozamu samu mafita. Kai tsaye ya nunamin hakan bamai yuwuwa bane. Na harzuƙa matuƙa, dan ina buƙatar farin cikin ƴaƴana, dan haka nace to kuwa sai dai kowa ya rasa. Da dai ya fahimci zan lalata komai bayan nasara dake tunkaromu sai ya lallasheni akan to na fahimcesa mana, mu bari ayi auren Nu'aymah da Abdallah. bayan komai ya faru Aymah ta mutu wajen aiki duk yanda zaiyi zaiyi a aurama Abdallah Adawiya. Na zauna nayi nazari sosai kafin na yarda da tsarinsa, dan nima a nawa hangen dukiyar da zamu mallaka ɗin idan Abdallah ya auri Adawiya zata sake dawowa wajenane tunda jikokina sune zasu zama magadan Abdallah, daga haka muka cigaba da shirye-shiryen biki, sai dai kash ana gobe matakin cikar burinmu zai tabbata aka sace Nu'aymah. Ina mai tabbatar muku munfi iyayenta shiga tashin hankali a wannan lokacin, duk da ni ɗaura auren Adawiya da Abdallah ya ɗan min daɗin da har tashin hankalina ya sassautu. Amma bayyana muku kalar ruɗanin da Lurwan ya shiga a wannan ranar ba'a magana. Dan har sai da muka samu matsala kanmu ya rabu, ni haushina ƙiyayyar da Abdaallah ya nuna akan yarinyata, shi kuma Lurwan takaicinsa suɓucewar damarmu. Daga baya dai muka dai-daita muka tafi shirya filan b. Iya bincike kuma munyi mun rasa gano yaya akai? ta wace hanya hakan ta faru? Sannan wanene ya aikata mana hakan? Da gaske mun fara zargin asirinmu ne ya tonu, sai dai har ƙura ta lafa bamuga wani alamar hakanba sai hankalinmu yaɗan kwanta”.
        Karan farko Hajjo tai murmushi mai ciwo. Amma batace komaiba.
       Addah ta cigaba da faɗin. “Mun sake son ƙulla auren Abdallah da Nu'aymah a karo na biyu. Sai kuma ga Naser ya dawo wai shima da soyayyar ta. Da alama kuma tayi shirin amsarsa. Sannan hajjo da Ananah sun goya masa baya a wannan karon. Shi kansa Sooraj mun fahimci so yake ya bama Naser ɗin. Dan yanda suke takun saƙa da Abdallah baisa wani ya taɓa nuna goyon bayan Abdallah ba. Muna tsaka da neman mafita Abdallah ya saki Adawiya da Yusrah. Wannan saki shine ya kawo saɓani mai girma a tsakaninmu. Dan nikam dai na tabbatar musu sai Abdallah ya maida Adawiya zan cigaba da basu goyon bayan cigaba da aiki tare. Amma sai Abdallah ya tubure, ƙarshema ya gudu ya bar gidan saboda takurawar da mukai masa ni da Abbansa. Sai dai ya tabbatar mana shifa da gaske yanason Nu'aymah ya kuma gaji da biye mana. Hankalinmu duk ya tashi, dan tabbas da gaske munga soyayyar yarinyar a cikin idanunsa. Mun kuma tabbatar da ya daina mana biyayya kenan”.
       “Ana tsaka da wannan rikicine ciwon da nake yawan ji ya takura mani, batare da sanin kowaba Mustapha ya kaini asibiti, a gwaje-gwajensu aka tabbatar mana da ina ɗauke da ciwon kansar jini, ga kuma ciwon zuciya daya ci jikina sosai shima, wanda na tabbatar yanada alaƙa da hana kaina zaman lafiya danai akan ƙadarar da ban isa canjataba tunda rubutacciyace daga littafin Firdausi da Sooraj. Lallai jikina yayi sanyi, duk wani kaushina ya sulale, adadin watanni da likitanci sukai ƙiyasin bazan zartaba ya ruguza dukkan burikana da zalamata. A karan farko zuciyata ta kwaɗaitu da son yin ƙyautatawa ga Firdausi koda sau ɗaya ne a rayuwata”. Kuka yaci ƙarfinta da tari. Yanzu kam gaba ɗaya ta cire ɗan-kwalin ta tare jinin dake fita da tarin, sai da ta tsagaita da ƙyar sannan ta cigaba da faɗin,
         “Na roƙi Mustapha ya rufe zancen ciwona harga ƴaƴana saboda banason ɗagama kowa hankali, da farko bai aminceba, amma da naita lallaɓasa da hujjoji sai ya fahimta. Son kuɓutar Nu'aymah daga tarkon Lurwan ya sakani sakebin hanyar wani malami aka sakar mata jini. Ni da kaina na zuba garin magani a zoɓo na kai sashensu saboda a gabana Firdausi tasa Rabi ta dafama Sooraj zoɓi shima. sai nayi amfani da wannan damar kawai, ni na kwaɗaitama Rabi kaima Nu'aymah zoɓon ɗaki lokacin dana shigo sashen da nufin neman cucumber. Sai na aiketa ta faɗoma Firdausi zan ɗauki cucumber ɗin. Tana fita na zuba maganin. Ina laɓe ta bayan kitchen lokacin da Rabi ta tafi kaima Nu'aymah zoɓo sai ma suka gamu a falo. Inajin Nu'aymah tace bazatasha zoɓon ba na shiga damuwa. Inata ƙulla yaya zanyi kuma sai ga Rabi ta dawo kitchen ɗin ta ɗaura shayi. Dabarar bugar glass ɗin Windown nayi, Rabi ta kalla wajen ta ɗauke kai. Na sakeyi har sau biyu, shine ta leƙo, bataga komaiba da alama, shine na sake bugarsa. Shine fa tai tsaki ta fito domin dubawa. Nikuma nai amfani da wannan damar na shigo na zuba maganin na fita ta falo. Inda na wuce Aymah na kallo, sai  hankalinta bai kau kainaba harna fice da sauri. Na bada awa guda sannan na sake dawowa na laɓe jikin window ɗinta, banbar wajenba harta fara ciwon ciki wanda na tabbatar magani ya fara aiki. Nabar wajen cike da farin ciki. Kafinma na isa sashena ihunta ya karaɗe gidan. Malam ya tabbatar min dama kowanne irin bincike likitoci zasuyi ciki kawai zasuyita gani ya zube a jikinta, hakanne kuma ya faru. Da wannan damar zancen ciki na sakeyin amfani na tursasa Hamisu bisa tsoratarwar zan kashe mahaifiyarsa ya kawo hotunan da ni na ɗauki Yoohan da Nu'aymah su ba shiba, ba kuma Kubrah ba kamar yanda nasan Nu'aymah zatai zargi. Nayi amfani da Hamisu ne saboda kusancinsa dana sani da Sooraj sosai, na kuma san Sooraj ya yarda dashi. Duk da Sooraj da Firdausi sun bani tausayi sosai a wannan halin na danne zuciyata na cigaba da aikata shirina dan nasan shine kawai zai kuɓutar da Nu'aymah daga sharrin Lurwan akan kwaɗayin dukiyar mahaifinta...............✍


Turƙashi😭🚶🏻


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 74

............“Dabarata ta jingina ciki ga Nu'aymah, da kawo hotonta ita da Yoohan shine burina Sooraj yay fushi yace sai Yoohan ya auri Nu'aymah. Ta hakanne kawai aurenta da Abdallah ko Naseer zai gagara. Duk da bana zargin Nasir da komai, amma inhar shi Nu'aymah zata aura tsugunne bata ƙareba kenan. Amma indai ta auri Yoohan inada yaƙinin zai bata kariya. Saboda alwashinsa na ranar da aka kirashi akan wannan batun ya birgeni. Ko bayan babu raina ina fatan ya zama garkuwa ga ahalin Firdausi. Sannan Nu'aymah ma zata samu lafiya ta dalilinsa tunda shine likitan da dama aka basu Number sa muka sace ni da Lurwan. Alhmdllh naci nasara, dan kuwa da bakinsa ya furta son auren Nu'aymah, duk da Sooraj bai bashi goyon bayaba a lokacin saboda jin nauyin ƴan uwansa akan su Abdallah na tabbatar yanason bashi. Lurwan ya shiga ruɗanin ganin zai rasa dama ta biyu, hakan ne ya sakashi sake dawowa gareni mu haɗa kai a wannan karonma. Ya kuma bani haƙuri da tabbacin zaisa Abdallah ya maida aurensa da Adawiya da zarar anyi aurensa da Nu'aymah. Na nuna masa na amince dan na samu a gama maganar auren Nu'aymah da Yahya cikin kwanciyar hankali. Daga haka na cigaba da gayama ALLAH dan agareshi kawai nake hangen samuwar nasarar kubutar da Nu'aymah daga tarkon Lurwan. Hidimar aurar da ƴaƴa kawai nake a zahiri, a baɗini kuwa ba wannan bane a gabana sam, shiyyasa na samu Firdausi da shawarar duk yanda zatayi tayi kar Sooraj ya bama Abdallah ko Nasir Nu'aymah, gara a auramata Yahya bisa wasu dalilan dana lissafa mata a lokacin waɗanda Alhmdllh sunyi tasiri a gareta. Sai da ina shirin fitowane naga Sooraj tsaye bayanmu alamar yaji komai da muka tattauna kenan. Hakan yamun dadi, dan insha ALLAHU koba komai inada yaƙinin samun nasara”.
      Ta share hakawayenta ga murmushi a fuskarta. Cigaba tai da faɗin,
       Jin tabbatuwar ɗaura auren Nu'aymah da Yahya shine nasarata ta farko da kobayan nabar duniya inason ƴaƴana su tuna suyi farin cikin aikin alkairi dana taɓa ƙullawa a rayuwata ta zaman gidan nan. Ko murnanr aurar da ƴaƴana guda biyu a ranar banyi murnarsa da tsananin farin ciki ba kamar yanda nayi na Nu'aymah. Amma a baɗini nabar wannan nasarar tawa. A zahiri kuwa na shiga jerin masu shiga ƙololuwar tashin hankali kamar su Abdallah da Lurwan da rayuwarsu ke a gigice. Dan wlhy aranar da aka ɗaura wannan auren kaɗan ya hana zuciyar Lurwan bugawa a gidan nan. Ya kuma sake ɗaukar alwashi kala-kala akan koma ta halin ƙaƙa saiya samu cikar burinsa. Wannan furici nasane ya sakani saka ƙanwata bin ƴan tawagar kai amarya. Sai da na tabbatar Nu'aymah ta shiga ɗakin mijinta lafiya ta hanyar ji daga gareta sannan hankalina ya kwanta. Duk da na tausayama yarinyar inda ƙaddara ta jefata. Amma sai nai mata fatan samun kariyar UBANGIJI da nasarar canjasu dalilin shigowar tata cikinsu. Daga haka na cigaba da ɓoyayyar jiyyar da mijinane kawai yasan inayi da duƙufa neman gafarar UBANGIJINA ko zan samu sassaucin raguwar zunubaina. Abinda yasa nabiku Austria ganin Nu'aymah saboda kozan samu na nema gafarartane. Ban saniba ko kafin ta dawo ƙasar ni na rasa raina. Ta ɗayan gefen kuma inason sakama Lurwan idone. dan a yanzu na daina sanin komai daga shirinsa saboda ya fahimci bana tare dasu a yanzu. Ko amincewa da zaman Adawiya da nai gidansa tanamin aikin sakamasa idone. Dan duk wani motsinsa itace ke kirana tana sanarmin batare da ita kanta tasan aiki takeminba dan ban fito fili na sanar mata manufataba”.
      Wannan shine labarina, shine ƙaddarata, shine kuma son zuciyar SARAN ƁOYE dana aikata muku Firdausi, nasan bazaki taɓa yafeminba ke da zuri'arki, shiyyasama bazan matsaba wajen neman yafiyarku. Kai koma ke kin yafemin ALLAH bazai yafemin ba, dan nasan na cutar daku iya matuƙar gaya ta hanyar SARAN ƁOYE. na aminta ku kaini kowace irin kotu a yankemin hukuncin daya dace dani kafin naje na fuskanci babbar shari'ata ga babban alƙali”.
     Ta ƙare maganar da fara tari mai tdanani. Sosai yanda take tarin guda gudan jini na faɗowa ya tada hankalin kowa a falon. Umm ta matsa gareta ta riƙeta sosai jikinta tana kuka. Da ƙyar aka samu tarin ya lafa. Duk da Yoohan najin zafinta har yanzu, dan shi baiji wani tausayin taba, duk da ƙoƙarin ƙulla aurensa da tai da Nu'aymah a ƙarshen ɓarnakun data tafka, amma sai ya bada shawarar a kwantar da ita zata samu sassauci daga yawan tarin. Da shawararsa akai amfani wajen kawo ƙaramar katifa aka kwantar da ita ɗin. Aiko sai tarin ya lafa sosai.
     Murmushi tayi tana kallonsa, murya na rawa tace, “Nagode Yahya, ALLAH ya azurtaku da ƴaƴa nagari da zasuji ƙanku, ALLAH ya sauki Nu'aymah lafiya naga gudan jininku kafin nabar duniya”.
     Uffan baiceba, baima nuna yaji mita faɗaba, amma jama'ar falon sun amsa mata da amin, duk da wasuma irin zuciyar Yoohan garesu basuji tausayin nataba.

          Abban Abdallah da keji kamar ya tashi ya ƙarasa rayuwarta saboda zuciya data kumesa ya yunƙura zaiyi magana Hajjo ta dakatar da shi ta shanyar ɗaga masa hannu. Dole kuwa ya koma ya zauna yana zare idanu.
        Tai gyaran murya sannan ta gyara ƙafarta mai ciwo da dubansu ɗaya bayan ɗaya ta fara faɗin, “Karma ka wahal da kanka wajen ƙaryata abinda duk Fauza ta faɗa Lurwanu. Idan bakai tunanin ana kallonku ba yau zan sanar maka cewar na jima da fahimtar kai da ita su wanene a cikinmu. Na barkune saboda na muku talalar zuwan wannan ranar. Na jima ina zargin akwai wani abu a zuciyar Lurwanu game da ɗan uwansa, dan yasha kawomin sukarsa akan miyasa kaza da kaza dole sai da umarnin ɗan malam akeyi a gidan nan?, sai dai ina nuna masa ɓacin rai. Amma ban sake tabbatarwa ba sai bayan tsaida ranar auren Abdullahi da Zainabu. Da kunnena naji dukkan abinda kuka tattauna akan soyayyar da Adawiya kema


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login