Showing 168001 words to 171000 words out of 318746 words
ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._
_LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._
_”Wait... Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”_
_”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta’kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_
_Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa😢yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA🙆🏻♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba🤔yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,🤦🏼♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki😫 ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._
“_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi.. Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_”
_”Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account🤲🏻kamar yadda Za’a faranta maku a littafin UNCLE NE_
_(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)_
____________
No. 46
.............Washe gari ƴan biki duk suka kama gabansu. Ciki kuwa harda ƴan kano su aunty hibba. Dan cikin sa'a sun sami jirgin safe. Sun tafi kuma da ɗunbin alkairi daga Yoohan. Sai dai kuma zukatansu cike da tausayin Nu'aymah da ƙaddarar aure ta kawo tsakkiyar waɗan nan mutane. Amma zasu cigaba da tayata da addu'ar zama mai nasara a cikinsu.
Nu'aymah kam bama tasan wainar da ake toyawaba a cikin gidan. Babu wanda ya nemeta a jama'ar gidan, itama kuma bata damu da son ganin kowa ba ma. Dan kukan data raba dare tanayi jiya ne ya ja mata komawa barci mai nauyi yau da safe. Bata farka ba sai wajen sha ɗaya. Haka ta tashi jikinta zau da zazzaɓi. Cikin dauriya tai wanka da ruwa mai zafin gaske. Tana fitowa anayin knocking ƙofar. Sai da ƙirjinta ya ɗan harba kaɗan, dan zatonta ko Yoohan ɗin ne. Jin an sake knocking ɗin ya sakata rumtse idanunta da sukai mata nauyi, hijjab ta ɗauka ta zira, sannan tazo ta buɗe ƙofar tana faman cin magani.
Victoria ce tsaye da tray a hannu, Destiny a bayanta ɗauke da flask ɗin shayi madaidaici. Ganin yanda yaran keta washe mata fuska ya sata sassauta fuskarta data ɗaure. Baki suka haɗa wajen faɗin, “Good morning Aunty!”.
A taƙaice Nu'aymah tace musu, “How are you?”.
“Fine Aunty, dama Aunty Blessing ce tace mu kawo miki breakfast”. (Kukun gidan).
Matsa musu tayi suka shiga cikin ɗakin batare data sake cewa komai ba. Ɗakin sukebi da kallo cike da sha'awar yanda ya haɗu. Bayan sun ajiye Destiny da bakinta baya iya yin shiru tace, “Aunty ɗakinki yayi ƙyau”.
“Thanks you”. Aymah ta sake faɗa a taƙaice. Dan ta kula shegen surutu yaran zasu dameta da shi idan ta basu fuska. Ilai kuwa sai Victoria ma ta buɗe baki zatai magana aka turo ƙofar ɗakin. Basai an faɗa ba, ƙamshin turarensa ma kawai ya isa amsa garesu. Da sauri suka miƙe daga zaman da sukayi akan sofa. Cikin ɗan rawar baki suke gaishesa. Janye idanunsa yayi akan Nu'aymah data ɗauke kanta bayan ta masa kallo ɗaya ya maida garesu. A taƙaice ya amsa musu yana cigaba da takowa cikin ɗakin. Saurin nufar ƙofa sukai suka fice.
Duk abinda sukeyi Nu'aymah na kallonsu ta cikin mirror, sai dai ta basar tanata shafa mai a ƙafarta kamar batasan da zamasu ba. Sai dai a ranta ji take kamar taje ta shaƙesa. Amma zata daure taga iya gudun ruwansa na yinin yau kawai......
Yanda bata tanka masa ba shima bai tanka matanba. Wayar dake a hannunsa yana latsawa ya matsa ya ajiye mata saman mirror ɗin, batare da yace komaiba ya juya zai fice. Cike da jin haushi Aymah ta bisa da kallo, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta murguɗa baki da harar bayansa.
Shiko haushin ƙin gaidashin da batayi bane ya sakashi ƙinyi mata magana. Duk da daman dai yau ya tashi ne da rashin ƴan son maganar saboda barci dake cike da idanunsa.
Yana ficewa Aymah ta maida dubanta ga wayar tasa mai azabar ƙyau, baki ta taɓe, harta ɗauke kanta sai kuma ta sake duban wayar. ba komaine yazo mata a rai ba sai kiran su Umm. Kwana ɗaya kawai har taji kewarsu, ji take kamar ta shekara babu su tare da ita. Sannan koba komai tanason sanar musu abinda take ganin basu sani ba, dan ta tabbata akan rashin sani iyayenta sukai wannan gamin gambizar. Ita dai tasan mutumin nan da aka aura mata kafiri ne, kuma tana da tabbacin iyayenta bazasu aura mata arne ba tunda sunsan haramunne a musulinci. Shin ko dai ya ɓoye musu ainahin kansa ne? Tabbas Aunty Kubrah ta cutar da ita, tunda har ta ɗauki hoton abinda ya faru a kuskure ta bama Hamisu ya kawo gidansu, (dan harga ALLAH tasan Kubrah ce ta saka hamisu yin hakan, sai dai shi tarasa miyasa ya amince ya aikata?) gashi nan ta silar hakan taja an aura mata kafirin da baisan ALLAH ba, danginsa mushiri kai. Dolene a yau tai gaggawar sanarma baba malam abinda ke faruwa..
Hawayene masu zafi suka sake gangaro mata, harga ALLAH ta gwammaci zaman gidansu akan wannan gidan da babu komai sai shirka a cikinsa. Gashi bazata ɓoyeba tana son Yah Ab har gobe a cikin zuciyarta. Tana danne soyayyarne kawai dan gudun shiga tsakanin alkairin iyayensu da zumincinsu. Taji daɗin ganin wayar babu wani lock. Daga Number baba malam harta Umm da hajjo a cikin kanta suke tsaf. Dan haka babu wani shan wahala ta saka Number Umm ta kira. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ba. Ta sake kira nanma ba'a ɗaga ɗinba. Ta baba malam ta saka. Tunkan ta karasa ma *Uncle S* ya bayyana. alamar da haka yay sebin lambar kenan. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ɗaga. Jikinta har rawa yake najin daɗi. Hawayen da take maƙalewa suka sake silalowa jin muryar Abbanta ya rangaɗa sallama da muryarnan tasa mai tarin kamala.
“Abba na!” ta faɗa kukanta na ƙwacewa da sauti.
Murmushi baba malam yayi daga can, cike da tsokana yace, “Anya mamana bata girmi kuka ba yanzun?”.
Ai kamar ya sake zugata ma, saita ƙara sautin kuka nata. Baba malam daketa ƙoƙarin danne kewar ƴar ɗiyar tasa yace, “Tom ya isa haka kuka. Inba hakaba kuma zan yanke wayata.....”
“A'a Abbah, dan ALLAH karka kashe. Ina kwana?”.
Murmushin ya sakeyi sannan ya amsa mata. Bayan sun gama gaisawa ta tambayi kowa da kowa na gidan nasu. Ya tabbatar mata da duk lafiya suke harsu Ananah da tuni sun isa gida.
“Amma Abbah shine basu sake zuwa nan ba?”.
“Ai kinga da safe sosai suka taho mamana, kinga idan sunce sai sunzo nan zasu makara. Mijinki ne ma da kansa yaje ya kaisu airport”.
Hawayene suka sake ziraro mata. A ranta tace, ‘Mugu shine yaki tashina muje tare’. a fili kuwa sai ta saka hannu ta share hawayen nata. Murya na rawa tace, “Dama na kiraka ne muyi magana Abbah”.
Zamansa ya sake gyarawa da ƙyau yace, “ina jinki mamana”.
“Abbah dan ALLAH ka fahimceni, wlhy ba ƙazafi nake masa ba. Mutumin nan fa kafirine, ya ɓoye muku ne kawai har kuka bashi aure na.......”
“A'a Mamana shi ba kafiri baneba a yanzu. Ki nutsu ki saurareni za miki bayani yanzun nan kinji”.
Kanta ta ɗaga masa tamkar tana a gabansa. cikin nutsuwa baba malam ya sanar mata komai game da musulintar Yoohan, ya kuma nuna mata muhimmancin zama da shi da dalilin aura mata shi dansu raba gardama tsakanin Abdallah da Naseer gudun kar zuminci ya samu giɓi. Itama kuma zata huta idan tayi nesa da su. Harga ALLAH taji daɗin jin cewa Yoohan ɗin yanzu musulmi ne, sai dai bawai hakan na nufin zata so shi bane ba, zataima iyayenta biyayya har lokacin da UBANGIJI zai iyakance mata zama tare da shi. Dan bataji zata iya rayuwar dindindin ta aure da shi ba balle waɗan nan dangin nasa masu kama da ojuju.
Baba malam ya mata doguwar nasiha mai ratsa jiki da ɓargo. taji kuma tayi ɗammarar yin amfani da ita, amma bata ɗauki alƙawarin haƙurin zama da Yoohan ba tabbas. A ƙarshen wayar ta roƙa baba malam a kawo mata koda ƴar aiki ce daga nan kano. hakan zaisa ta samu abokin hira kafin ta saba da jama'ar gidan.
Baba malam baiƙi karɓar alfarmar tata ba. Dan koba komai yasan hakan zai bata nutsuwa ta ɗan kwantar da hankalinta yanda yake bukata da fata. Sai dai yace sai mijinta ya amince sannan.
Koda suka ajiye wayarma tashi tai tana sharɓar hawaye. Batare data cire hijjabin data zumbula ba balle ta nema kayan sakawa ta faɗa saman gado ta cigaba da kukanta da batasan na minene ba. Jitai zazzaɓin na sake lulluɓe ta. Taja lallausan bargon dake saman gadon ta kudundune zuciyarta fal ƙunci.
Yoohan dake can ɗakin Momy da itama babu lafiyar bayan ya lallaɓata tasha tea ya saka mata ƙarin ruwa. Sai da yaga barci ya ɗauketa ne ya zare hannunsa dake cikin nata a hankali ya lulluɓa mata bargo ya fito. A corridor yaci karo da Miracle. Kallo ɗaya yay nata ya ɗauke kansa saboda shegun kayan barcin dake a jikinta bata da maraba da tsirara. Da alama ma yanzu ta tashi barci. Cike da kishi tace masa “good morning”. Batare daya amsata ba ya wuce abinsa ya barta da ƙamshinsa.
Sashen sa ya koma. Inda ya iske Solomon a falo yana goge-goge. Gaidashi yayi cike da girmamawa kamar yanda ya saba.
Amsa masa yayi yana tura ƙofar ɗakin Nu'aymah ya shiga. Solo ya rakashi da kallo tamkar idanunsa zasu zubo ƙasa. Oho baimasan yana yi ba, danshi tuni ya shige.
Shashshekar kukanta daya faracin karo da ita cikin kunnuwansa ne ya sashi lumshe idanunsa a hankali ya buɗesu a kanta, cigaba da tsaiwa yayi a bakin ƙofar kawai yana kallonta kamar ya samu television. Ita kam bama tasan da shigowarsa ba, dan gaba ɗaya hankalinta da tunani yana kan ta yanda zata samu mafita akan wannan auren ne. Sai ɗunbin kewar iyayenta da ƴan uwanta dake gaba-gaba wajen tunzura kuka nata.
A hankali ya sauke numfashi da zura duka hannayensa cikin aljihun baƙin wandonsa. Ya fara taka farar ƙafarsa dake fes babu wani datti a jikinta saboda tsabar saka kwaba shu da yake a koda yaushe ya ƙarasa har gaban gadon dai-dai saitin inda fuskarta take. Har fuska ta rufa bargon. Kaɗan yaja gajeran tsaki a maƙoshi, a ransa ko rayawa yake, ‘Sai shegen tsiwa a bakinta da ƙuruciya’. A fili kam sai ya ɗan ranƙwafo da zare hannunsa daga cikin aljihu ya yaye bargon daga fuskarta. Bai kai ga kaishi kafaɗa ba ta riƙe gam. Idanu ya zubama farar fuskarta da tai jazur musamman saman hancinta da idanunta. Dai-dai da ɗago nata kumburarrun idanun ta zuba cikin nashi. Sai dai sam kwarjininsa ya hanata iya cigaba da kallon tsakkiyar idanun nasa. Hakan ya sakata azamar janyewa tana kumbura baki fal da iska. “Malam ka daina shigamin rayuwa bana so”. Cikin yin ƙasa da murya yanda bazaiji ba tace, ‘Haka kawai a ringa shigoma mutum kai tsaye babu neman izini’.
Baiji maganar data faɗa ba a ƙarshe dan da hausa tayi, ta farkoce dai tayi da turanci. Amma a yanda tai maganar yaji a jikinsa rashin kunya ce a ciki. Amma sai ya shareta bai kulata ba, sakin bargon yayi ya ɗora yatsunsa biyu a saman goshinta saboda ganin yanda jijiyar kanta tai ruɗu-ruɗu.
Saurin ja baya tayi hawaye na sakko mata, “Nifa a daina taɓa ni bana so”. Ta faɗa tana hararsa ta ƙasan ido da murguɗa baki kaɗan.
A karan farko da abin nata yaso bashi dariya, dan haka ya ɗanyi luuu da idanunsa tamkar zai lumshesu amma sai ya buɗe yana kauda kai gefe da sakin murmushi. Barin gaban gadon yayi batare da ya sake magana ba. Abincin da aka kawo mata ya bubbuɗe. Irish ne da ƙwai, sai farfesun kayan ciki, da gasashshen burodi da yaji haɗin salad a tsakkiya. Maidawa yay ya rufe sannan ya miƙe ya fita.
Nu'aymah da duk tana kallon abinda ya keyi ta raka bayansa da harara tana faɗin, ‘Mutum babu abinda ya iya sai son taɓa jikin mutane dan kwartanci’. (Hhhhhh🤣 Aymah tamu ta mutunci, mutum ya sauke sadaki ki kirashi kwarto dan ƙarfin hali irin naki😂).
Bai fi mintuna huɗu da fita ba ya dawo hannunsa ɗauke da kofin tea ruwan hanta, yanda turiri keta fita ta samansa zai baka tabbacin shayi ne..
A gefen gadon ya zauna daf da ita. Hakanne ya sakata matsawa da sauri. Baki yaɗan taɓe, batare da ya kalleta ba yace, “Oya tashi”. “Na maka mi?” ta bashi amsa tana satar kallonsa. Kofin tea ɗin kawai ya miƙa mata batare da ya sake cewa komai ba.
“Tab, toni nace maka zansha tea ne? Na ƙoshi”.
“Silly girl”
ya faɗa yana hararta a karo na farko. Ya sake tsuke fuska da faɗin, “Malama tashi kiyi breakfast kona juye miki shayin nan ta hanci”.
Tuni idanun Aymah suka ciko da ƙwalla, cikin rawar sanyin da yake ƙaruwa mata tace, “To ana dole ne? Nace na ƙoshi ba sai ka barni ba”. Komai bai sake ce mataba, sai dire kofin yayi a saman bedside drawer ɗin ya miƙe. Fita yay da ga ɗakin. Da sauri Aymah tace, ‘ALLAH ya hanaka ikon dawowa mai zubin masu jajayen kunne, da wani kansa kamar sheƙar angulu’. (Wlhy ke da shi Aymah ni dai ba ruwa na😂).
Ganin abinda ya dawo da shi a hannu ya sakata miƙewa zumbur jikinta na rawa. Shiko ko kallon inda take ya ƙiyi sai ƙoƙarin ɓare syringe ɗin daya shigo da shi ya keyi. Ya sake zama a bakin gadon yana ɓalle bakin kwalbar maganin, tare da saka kan allurar jikin syringe ɗin ya zuƙe ruwan allurar da ya kusa rabin syringe ɗin. Ajiyewa yay a gefenta bayan ya gama, sannan ya ɗakko kofin shayin ya miƙa mata batare da yace komai ba.
Da iya gaskiyarta take ziraro da hawaye, zuciyarta sai bugawa take da sauri-sauri. Tabbas a rayuwarta allura na ɗaya daga cikin abinda take tsoro fiye da hasashen mai karatu, sai kuma duhu. Waɗan nan abubuwan ko a tunani batason tunasu suna tayar mata da hankali. Hakan yasa hannunta har karkarwa yake wajen miƙa hannu ta amshi kofin shayin. Nanma baice da ita komai ba ya sakar mata. Tiren kayan breakfast ɗin ya ɗakko gaba ɗayansa ya ajiye saman gadon a gabanta. Bayan ya buɗe mata koma ya ɗago ya kamata tana jan allurar daya ajiye alamar so take ta ɓoye.
Da ƙyar ya iya danne dariyar data zo masa a maƙoshi. ya sake tsuke fuska yana balla mata harara. “Idanma kin ɓoye inada gomanta a ɗakina, kinga kenan kinyi na banza. Na baki 20minutes kacal naga tray ɗin nan empty”.
Hannu tasa ta sake share hawayen da suka ciko mata idanu, cikin ƙunƙunin da bazaijiba tace, ‘Tunda ga jaka rumbu uwar zira lauma an kawo maka ko’. A fili kuwa duƙar da kai ƙasa tai kamar ta ALLAH😂.
Hannunsa ya ɗora saman nata da har yanzu ke riƙe da syringe ɗin ya zare abarsa. Gefensa ya ajiye tare da gyara filos ɗin dake birjit a saman gadon ya kwanta rigingine. Wayarsa ya ɗauka ya hau dannawa tamkar ya manta da ita a ɗakin.
Ɗagowa goma Aymah zatayi harara ashirin take antaya masa. Baƙar magana kuwa da gorin hawa mata gado da yay tayi yafi sau ɗari babu ɗaya tana tunzura baki gaba. Daka ganta kasan tsoro ne fal ranta kawai da neman faɗa da tafi ƙwarewa a yi. Shi dai bai sake bi ta kanta ba duk da yana jin ƙunƙunin da takeyi da harar da take masa. Sai dai kasancewar hausa takeyi bai damu da abinda take cewarba. Da yake dama yunwar ta keji sai gashi ta shanye tea ɗin duka dan ya mata daɗi. Harko da ayyanawa take a ranta ‘Wai buzun nan ashe ya iya haɗa shayi’ (Kai wagga ɗiya ta baba malam ALLAH dai ya gyara😆😂). A sauran abincin kuwa bread kawai taci, dan yanda aka haɗashi ya mata ƙyau a ido da daɗi a baki. Wai saida ta gama ci kuma sai cewa tai, ‘ALLAH dai yasa ba arnakun nan suka yishiba na wage baki ina turawa kamar a haɗiɗiya’. (Ke dai kika sani🤣).
Ganin ta kammala Yoohan ya miƙe zaune sosai yana ajiye wayar hannunsa. Trayn ya sauke ƙasa, batare da ce mata uffan ba ya matso daf da ita sosai har suna jin saukar numfashin juna. Zabura tayi da sauri zata matsa ya riƙota. Baya buƙatar hayaniyarta a yanzu saboda jikinta yay masifar zafin zazzaɓi, shegen taurin kanta ne kawai ya hana bakinta da