Showing 267001 words to 270000 words out of 318746 words
9ja bayan haihuwar da kwana ɗaya yazo. Dan dama yaso Juliet ɗin taje Nigeria ta haihu taƙi. Yarinya dai taci suna biyu. Aysha & Lisa, Dan shi dai Omar duk abinda ya dace uba musulmi yayi akan ƴaƴansa shi yayi akan baby Aysha. Itako Juliet da yake dama bawani bidi'oin suna sukeba suna kawai ta sakama yarinyarta bayan wanda Omar ɗin ya saka mata. Saima yazam itama yanda Nu'aymah ke kiran sunan Aysha ɗin yana mata daɗi. Sai gashi tafi kiran yarinyar da Ayisha ɗin. Saboda daɗin da Omar yaji har ƙyauta yayma Nu'aymah da godiya. Tare da roƙonta dan ALLAH taita jan Juliet ɗin a jiki ko itama za'a dace ta gane gsky. Aymah ta amsa masa. duk da tasan hakan abune mai wahala ga baturen ba'amuruke irin Juliet. To amma komai ai na ALLAH ne.
_________________★
*_KANO NIGERIA_*
Anan kano ta dabo kam Umm najin daɗin zama da Afrah data ta fara aiwatar da aikinta cike da ƙwarewa da nutsuwa. Gaba ɗaya ta ɗauke musu kewar Aymah. Koda yaushe Muhammad inhar ba makaranta ya wuce ba yana nane da ita. Itama tana matuƙar son yaron, dan yana ɗauke mata kewar ƴan ƙannenta.
Haka ma tana matuƙar jin daɗin zama da baba malam da Umm. Dan mutanene masu dattako matuƙa. Ita da hajjo kam ai ba'a magana. Daka gansu tamkar jika da kaka. Kai gaba ɗayama al'ummar gidan Afrah nada ƙyaƙyƙyawar alaƙa da kowa. Dan malam ƙarami harya ƙyasa. Ita kuma taƙi sanar masa tanada mijin aurenta a hannu. Dan gab ma ake da saka musu ranar aure tunda iyaye duk sun shaida tuni.
A cikin dabarun da ALLAH yay mata a sashe su Nu'aymah ta manna cctv ɗin nan mai kama da stones. Hakama sashen hajjo da duk wasu gurare na cikin gidan batare da kowa ya farga da itaba. Bata da wata ƙawa mai shekarunta a gidan, dan haka taita jan yaran gidan jikinta sosai. Dan su Adawiya ma har yanzu suna Abuja. Admission ma za'a nemar musu su fara karatu tunda na Adawiya yasha kashi. Su baba malam sunso ta koma saudia ɗin ta cigaba hajjo ta hana hakan. Acewarta su jira dai suga iya gudun ruwan Abdallah ɗin.
A cikin kwanaki goma da Afrah tayi a gidan ta kammala aikinta na manna camaras a duk inda ya dace. Sosai Jay yaji daɗin ƙwazon ƴar tasa. Hakama Bily.
Sai kuma ta koma bama Dawood da little, Yoohan, Omar bayanai akan duk motsin ƴan gidan. Da wanna suka fara aywatar da aikinsu batareda jama'ar gidan sunsan sirrin ba. Hatta da Nu'aymah batasan hidimar da akeyiba. Dan koda Yoohan ya koma U.S bai sanar mataba. Takan dai gansa yayi serious a lap-top duk dare. kuma baya zama latse-latsen sai tayi barci. Inko har yazam ta farka to yabar aikin kenan. Dan duk dabarar da zaiyi ya ajiye abinda yake ya sani.
A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa har aka shiga watan azumin Ramadan. Wanda ya kasance na farko ga Yoohan da Omar. Sosai Aymah ta yabama ƙoƙarin Yoohan randa aka kai azumin farko. Dan ko irin nuna yau ya fara ɗin nan bai nunaba. Itacema sai da ta karya nata saboda jiri data dinga gani, daga ƙarshe kuma taita amai.
Omar U.S ya koma domin yin azumi. Hakan yasa kullum anan wajen Nu'aymah yake zuwa shan ruwa. Wani lokacin ma harda Juliet suke zuwa da Baby Ayisha.
Azumi nada kwanaki goma sha biyu hutun Afrah ya ƙare. Ta tattara ta koma Abuja cike da kewar su Umm. Dan ita dai taji masifar daɗin zama da waɗanan bayin ALLAH musamman cikin azumin nan. Su kansu duk sai da sukaji babu daɗi akan komawar tata. Sai dai babu yanda suka iya tunda zata koma kan aikintane.
An kammala azumin watan Ramadhan lafiya. Ansha kuma bikin salla a ƙasashen musulmai. Yayinda su dai su Aymah sai ɗan yawo sukai anan U.S, da ɗanyin nasu bikin sallar anan cikin gida.
Tsakanin Yoohan dasu papa har yanzu basu taɓa masa magana akan dukan Gebrail da yayiba. Dan komawar da yayi 9ja can gidan ma ya sauka abinsa. Sun kuma tarbesa kamar yanda suka saba. Ya iske su momy Destiny sun koma. Hakama maman Madam Chioma. Mama debora kawai ya iske da sauran ƙannensa sai guards ɗin gidan su Solomon daya koma gadin nadam Chioma yanzun. Gebrail kam tunda yaji Yoohan ɗin yazo gidan ya gudu. Har yabar ƙasar kuwa basu haɗuba. Daya sake komawama yay wajen kwana goma shima wasan ɓuya suka dingayi da Gebrail ɗin.
Wannan shiru da sukai ya bama Yoohan mamaki matuƙa. Badan dukan da yayama Gebrail ba. Sai dai maganar Solomon da baiji sun sake tayar masaba. Sai dai kuma shima baiyi magana ba ya bar Solomon ɗin cigaba da kasancewa da shi da sauran guards ɗinsa duk sanda ya shigo Nigeria. Duk inda ya shiga suna tare anan kam.
_____________________
A kwana a tashi babu wahala sai ga cikin Nu'aymah ya shiga watanni shidda. Tun cikin azumi kuwa ta fahimci ciki gareta. Murna taitayi zasu samu baby suma. saɓanin yanda Yoohan yay tunanin zata tayar da hankalinta. Aiki shima yaji daɗin yanda ta nuna murnarta akan Unborn ɗin nasu. Wata ƙaunarta mai girma na sake faɗaɗa masa a rai.
Ganin laulayin ya rage mata a lokacin sai kawai ya shiga ƙoƙarin nema mata admission. Wannan abu ya saka Aymah murna harda kuka. Dan tanason karatu sosai a rayuwarta. Addu'a ta dage ta dingayi babu dare babu rana akkan samun gurbin karatun nan. Su Umm ma sunsha addaba akan su tayata da addu'ar. Har Muhammad tasa ya faɗa a islamiyya wajen ƴan ajinta su mata addu'a.
To Addu'a dama takobin muminine ai. Balle gashi result ɗin Ayman da Yoohan ya amso a gida wani zuwa da yayi dama yayi ƙyau masha ALLAH. Sai gashi kuwa an dace. Ranar kowa yasan Aymah ta samu cikar burinta. Yoohan kam ai yafi kowa shan kallo dacin dariya a wannan rana, sannan kuma yasha tukuyci mai tsoka da ba'a bama yaro mai ƙiwa.
Da taimakon Juliet yay mata komai daya dace, dan itama tanayin wani course ma a cikin makarantar yanzu haka. Sai dai a online take ɗaukar lecture. Da wannan damar Yoohan ma yay amfani akan Aymah. Zata dinga ɗaukar lectures ta online. Idan kuma taso shiga school bai hanata ba bayan ta haihu. Yayi hakane saboda yanayin jikinta.
To da yake itama yanzu lallaɓa cikin take sai ta amince (wa yaga ba sabanba su Aymah za'ayi ƴaƴa😂).
Umm, baba malam, hajjo ne kaɗai sukasan da zaman cikin Nu'aymah a kaf jama'ar gidansu. Dan ko Addah Umm bata faɗamawa ba sam. Tabar abinta a zuciya wai randa Nu'aymah tazo kowa ya gani. To kuma anyi sa'a duk wautar Aymah da surutu ita bamai irin sakin zance ɗin nan bace ako ina. Dan ko su Umm ɗin ai ba fitowa fili tai tace musu tanada ciki ba. Sune suka fahimta ita da hajjo. Baba malam ma a wajensu ya sani.
Cikin ya mata ƙyau sosai a jiki, sai dai yasata ta ƙara ƙiba, kumatun sun fito masha ALLAH. Idan Yoohan najin neman magana yakan tasata gaba yayta dariya. Ita kuma taita hawaye dan yanzun dai kam bakin tsiwarnan duk ya mutu. ta kanta takeyi duk tazama wata shiru-shiru.
★★★★★
Akwai aikin da Yoohan zaizo yi Ƙasar ghana, daga nan kuma zai shigo Nigeria akan case ɗin gidan su Aymah. Dan zuwa yanzu sun tattara abubuwa da yawa ta dalilin Afrah. Sai bayanan sirrin da jay ya tattara ta hanyar camaras ɗin nan wanda shi da bily kawai suka san dasu. Amma suma ɗin basu duba komai ba a yanzu, dan sunbar komai ne ya tattaru, So suna son fara buɗe abubuwa a bayyane insha ALLAH a hankali. Sun san kuwa a wata uku kenan da zaman camaras ɗin a gidan sun naɗi abubuwa iri-iri, musamman daya kasance ansha shagalin bikin ƙaramar salla da babba, duk kuma ahalin gidan sunzo, idan ka cire Abdallah da yay hijira.
Shirinsu na farko dai yanzu shine fara kama Rabi. Daga haka sauran abubuwa zasu cigaba da tafiya a buɗe. Nu'aymah taso biyo Yoohan a wannan karon. Sai dai kuma ya lallaɓata akan ta bari sai hutun ƙarshen shekara idan ALLAH ya kaimu. Tunda baifi saura wata ɗaya da sati biyu ba. Batai masa musu ba, dan yanzu duk ta ƙara yin laushi, danma wahalar cikin ta mata sauƙi sosai zuwa yanzu Alhmdllh. Gashi kuma dama cikin fari. Ga kuma karatunta da ke mata matuƙar daɗi. Dan harya kaita da mantawa da wasu su madam Chioma. Lamarin papa ne dai kam sun tattauna da Omar sosai a wani zuwa da yayi U.S ɗin. Annan take faɗa masa gaskiyar lamari game da hoton data ɗakko a ɗakin papa ɗin, harma da waɗanda ta gani. Abin shima ya bashi mamaki sosai. Nan shima yake sanar mata abinda ya taɓa faruwa tsakaninsu da Jay kwanaki. Itama sai abin ya tsaya mata a rai. Har taji sha'awar son samun kusanci da zuri'ar Jay ɗin. A take Omar ya bata Number Afrah. Dama Afra ɗin ita tanada ta Aymah, kirantane dai bata taɓa yi ba. Dan sanda tana a gidansu sai dai su gaisa a wayar Umm ne. Tun daga sannan suke ɗan kiran juna a hankali, suna kumayin chart lokaci-lokaci kasancewar duk sunyi busy.
To yanzu dai sun ajiye magana akan duk sanda taje 9ja zata bashi hoton ya gani, daga nan sai su san tudun dafawa akan wannan al'amari. Daga haka suka ajiye batun.
Sai dai kuma abinda su Aymah basu saniba ita da Omar shine tun randa Jay yaga Yoohan bai hutar da kansa ba a bincike dabin diddigin papa. A hankali duk wani motsin papa ya kasance akan idon Jay batare da shi yasan hakan na faruwaba. Dan ya rigada yayi imani da cewar ya toshe duk wata hanya ta leƙen asirinsa daga wasu mutane koda jami'an tsarone. Sai gashi shi Jay yama kansa hanyar da yake kallon papan tsirara.
Dirar safe Yoohan yayma 9ja wannan karon. ya kuma sauka a Lagos ne. Sai da ya kwana uku sannan ya ƙaraso Abuja. Kamar ko yaushe ahalin nasa sunyi murna da zuwan nasa. Musamman ma madam Chioma da duk zuwa saita banka masa kayan tsibbunta a abinci yaci. Sai dai duk da bataga wani canjiba daga garesa tana ɗauka aikinta na tafiya dai-dai. Musamman da bata taɓa jin ya zauna yimata zancen Nu'aymah ba.
Tun isowarsa gidan Gebrail ya gudu kamar yanda yakeyi yanzun. Tun dukan da Yoohan yay masa bai sake yarda sun haɗu a inuwa ɗaya ba. da zarar yaji labarin zuwansa yake barin gidan, bakuma zai sake shigowaba sai Yoohan ya koma kokuma yaje wani jahan aiki. Duk da Yoohan na lure da Gebrail ɗin bai taɓa nuna yasan yanayi ba. Gaba ɗaya yi yake tamkar ya manta da wani halitta Gebrail a cikin ƙannensa.
Blessing da su Favour yasa suka gyara masa sashen nasa wannan karonma. Bayan ya watsa ruwa yaɗan miƙe a gado yanason ya huta. Sai da ya fara kiran Aymah suka ɗan taɓa hira sannan ya kwanta. A ƙanƙanin lokaci kuwa barci yay awan gaba da shi.
Madam Chioma da tun shigowar Yoohan gidan yau ta kasa zaune ta kasa tsaye ta fito wankan maganin da boka Bangaruta ya bata a gurguje. Zama tai gaban mirror ta shiga tsara kwalliya kai kace fita zatayi. Sai da ta tsuke cikin wando da riga da sukai mata matuƙar ƙyau sannan ta feshe jikinta da kalolin turarruka masu tsada da ƙamshi. Gashin Attachment ɗin nan sai uban walƙiya yake da ɗaukar ido kasancewar sa mai uban tsada. Cike da takun gayu da ƙasaita ta fito daga sashenta dan papa baya nan yayi tafiya yau kwana biyu. Mama debora dasu Victoria kuwa tasa sunbar gidan a cikin shirinta. Ta aika Blessing kuma kasuwa. Amma abinda bata saniba Blessing ɗin batakai da fitaba saboda toilet daya kamata. Kanta tsaye sashen Yoohan ta nufa, hakan yayi dai-dai da hawowar Miracle sama hannunta ɗauke da five alive da kofi. Waya takeyi da wata ƙawarta tana bata labarin zuwan Yoohan. Saurin ɓoyewa Mira tayi dan kar madam Chioma ta ganta, tare da jan wani shegen wawan tsaki dayin kamar zatai jifa da kwalin lemon. Sai kuma ta fasa saboda uban kuɗin data kashe wajen yima lemon haɗin magunguna saboda Yoohan. Itama kanta cikin gayun take na kece raini. da alama kuma sashen Yoohan ɗin ta nufa. Sai dai gashi Maman Yoohan ta ruguza lamarin. Ranta cike da ƙuna taje ta zauna a kan wasu kujeru biyu dake a upstairs ɗin tana huci da bama ƙawar tata labarin abinda Momyn Yoohan ɗin tai mata. Zugata ƙawar tata take famanyi daga can akan ya kamata Miracle tazo suyi duk yanda zasuyi wajan raba Yoohan da uwar tasa.
A ɓangaren madam Chioma kam ta shiga da dukanin gadaranta sashen ne. Key ta sakama ƙofar falon sannan ta nufi ɗakin Yoohan kai tsaye. Baisa a ransa kowa zai shigoba, musamman da yasan yanzu Momy ta bar masa ɗabi'ar banza na shigo masa sashema gaba ɗaya. Dan duk zuwannan da yakeyi bata shigowa, sai dai idan shine yaje sashenta gaisheta kosu haɗu a falon papa. Shiyyasa yake kwance abinsa daga shi sai boxer yana barci hankalinsa kwance. Ga iskar ac na shiga da ratsa masa ɓargo.
Nanma maida ƙofar tai ta rufe harda saka key. Kafin ta ƙarasa gaban gadon jikinta har tsuma yake saboda ganin a yanda Yoohan ke kwance. Duk da ma yayi rubda ciki ne. A hankali ta zauna a bakin gadon saitin kansa. Ta kai hannu kan sajensa da ke bala'in burgeta. Cike da ƙwarewa a bariki ta kwanto jikinsa tana sauke nannauyan numfashi, sai kuma ta shiga yin sama da hannun nata ta tura cikin sumarsa. Dan tasan tun yana yaro yanason a dinga masa wasa cikin kai. Yanda take da hannun nata a cikin sumarsa ya sakashi sauke ajiyar zuciya a cikin barci. GGashidama mafarkin matarsa yake. Sai abinda madam Chioma ke masa yay tasiri a garesa.
A hankali yay juyi gaba ɗayansa ya koma ringin gine. Kansa kuma ya ɗora akan cinyarta ɗaya dake a gadon. Wani irin daɗine ya kama Madam Chioma dan duk zatonta aikintane yay tasiri. Ranƙwafowa tayi da fuskarta daf da tashi tana wani lasar baki tamkar mayya. Yayinda hannunta ɗaya ke yawo a jikinsa. Tana gab da kai laɓɓanta kan nasa ALLAH ya bashi ikon farkawa a dalilin jin ƙamshi saɓanin na Aymahr sa. A wani irin matsanancin tashin hankali ya angizata daga ranƙwafomasa da tayi, danshi da farkoma yayi zaton Miracle ce............✍
*_Wayyo tazo kwartanci😱🏃🏃🏃_*
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[7/3, 3:48 PM] Queen Meenali👑: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 70
............Sai dai kuma ɗagowar da zaiyi cikin matsanancin fushi sai idonsa akan Momynsa daya yasar a ƙasa. A matuƙar razane yace, “What!!. Momy! Innalillahi wa'innalillahirraji'un”. Cikin karkarwa jiki ya shiga bin ɗakin da kallo, tabbas daga shi sai ita ne, hakan na nufin ba Mira ba. Ƙirjinsa ya sake bugawa da ƙarfi. Yay azamar jawo rigarsa dake gefe danya saka Madam Chioma da ALLAH yaba damar tashi tai saurin riƙe masa hannu. Dan ita haukanta gaba ɗaya bai nuna mata maganinta baya aikiba. Faɗa masa tayi ajiki tana faɗin, “Haba my boy ya kake abu kamar wani.......”
Ai kafinma ta ƙarasa ya sake hankaɗata da rawar jiki. “Momy kina lafiya kuwa? Ninefa Yoohan?! Kodai kinsha barasa ne?!”.
Duk da mamakin yanda yakeyi ya fara sata dawowa hayyacinta, ga zafin maguzar daya sake mata hakan bai hanata sake nufosa ba. Hankalin Yoohan ya sake kololuwar tashi, dan shi yafi tunanin Maman tasa bata a hayyacinta ne. Ta sake riƙe rigar daya ke ƙoƙarin sake kai hannu ya ɗauka tana wani narkewa hawaye na zirara mata. “My boy kaine mafarkina. Kai ne farin cikina. Tunda ka kai shekarun girma ka ɗauke hankalina ga kowanne namiji a duniya. Hatta da papanku baya birgeni gaba ɗaya duk da auren soyayya mukayi. Please masoyina kazo na baka zumar da wata a duniya bata taɓa baka itaba, na maka alƙawari........”
Duk yanda Yoohan yaso jurewa yama mahaifiyar tasa uziri ya kasa, dan haka ya fisge hanunsa data riƙe wani matsanancin tsoro na sake kamashi. Da sauri ya nufi hanyar ƙofa danya kuɓuta. Sai dai kuma ya sameta gam alamar ta kulle. Sunayen ALLAH ya shiga kira babu ƙaƙƙautawa, yay azamar kaucewa ganin ta sake nufoshi ido rufe. Dan har ta cire rigar jikinta tana ƙoƙarin cire wandon ma.
Wata azababbiyar ƙara da hatta Miracle da Blessing dake ƙasa a laɓe sai da suka jiyosa ya daka mata.
“Momy!!!! Are you mad?!!” Ya faɗa yana hankaɗata da iya ƙarfinsa da matsanancin fushi dan gaba ɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwa a tashi. Sai ko gata a ƙasa wanwar. Wata wahalalliyar ƙara ta saki saboda faɗawa datai akan hannun damarta.
Ya cigaba da magana cikin fushi na ficewar hayyaci. “Wane irin