Showing 183001 words to 186000 words out of 318746 words

Chapter 62 - saran boye complete by Queen meenali

01 Jul 2024

41668

zaunar bisa centre table da ke kusa da su. A gabanta ya durƙusa ya saka mata kofin a baki. Da sauri ta ɗora hannayenta duka biyu a saman nasa da ke riƙe da ruwan suka karasa da kofin bakinta a tare. jikinta sai rawa yake hawaye na zirara dan taji sarƙewar sosai. Ɗayan hannunsa ya ɗora a gadon bayanta yana shafawa. Kusan rabin ruwan tasha sannan ta janye, ta maida hannayen nata ta riƙe kumatunta tana ɗan murzawa da sauke wahalallen numfashi irin na wanda ya sarƙe. Cigaba yay da shafa mata bayan yana jera mata sannu.
        Kanta a duƙe ta tokare gwiwar hannunta da cinyoyinta ufan bata iya cemasa har tsahon mintuna kusan biyu. Sai a sannan ne madam Chioma ta taso inda suke. Hannunta ta ɗora akan nasa dake shafa bayan Aymah ta ɗan bubbuga ta wuce batare da tacema Nu'aymah sannu ba. Binta yay da kallo harta fice. Haka kawai ya samu kansa dajin haushin abinda tayin. A ganinsa ya dace ace tama matarsa sannu tunda a gabanta komai ya faru ai. Wannan halin na Momynsa ya fara damunsa shi kam. Ya kula batason kowace mace ta raɓesa a rayuwa daga ita sai ƙannensa. Kai su kansu ƙannen nasa wani lokacin fuskarta nuna ɓacin rai takeyi........
       Hannunsa da Nu'aymah ta janye a bayanta ne ya maidosa hankalinsa, saurin riƙota yay ganin zata tashi. “Ina kuma zakije?”.
      Cikin ɗan sanyin muryar da sarƙewar taja mata tace, “Zanje in kwanta barci nakeji”.
     “Da miya fito dake nan ɗin?”. 
Baki ta tunzira masa da faɗin, “To bahar na kwanta ba surutunku kai da Momynka ya tasheni”.
     “K ba momynki bace?”.
       “Bayan bata sona”. Ta faɗa da iya gaskiyarta.
      Tsatstsare ta yayi kawai da idanu ya kasa cewa komai. Ganin zata miƙe ya sake ruƙota, “Kinga muje kici abinci kafin kije ki kwanta ɗin”.
   “A'a ni na ƙoshi”.
“Mi kika ci?”.
      “Babu komai, kawai dai na ƙoshi”.
“Silly girl, kodai sauran kayana kika tattare kika cinye?”.
        A yanda yay maganar sai yaso bata dariya, amma saita gimtse abinta batayi ba, ta zare hannunta kawai daga cikin nasa tana miƙewa, “ALLAH ni barci nakeji ka barni na kwanta”.
        Bai sake ce mata komai ba ta raɓa ta gefensa ta wuce. Kallo ya bita da shi harta shige ta maida ƙofar ta rufe. Idanunsa yaɗan lumshe da sauke ajiyar zuciya sannan ya miƙe. Shima jiyay baya buƙatar cigaba dacin abincin, dan haka yay kiran Blessing ta telephone ya sanar mata tazo ta kwashe. Yana cikin haɗa tea a kofi Blessing ɗin ta shigo, ta tattare komai ta fice da shi, shi kuma ya nufi ɗakin Aymah da kofin shayin da biscuit guda ɗaya. Zaune ya sameta a gaban mirror tana ɗaure gashinta, ta canja kaya zuwa wando da riga na barci. Wandon ɗan fit ko cinya bai gama rufe mata ba, sai rigar itama dai babu wani girma da siririn hannu. Rikicewa tayi sosai dan batayi zaton shigowar tasa ba. Yanda taketa budum-budum ɗin neman hijjab ne ya bashi damar kallon abinda take ƙoƙarin son rufewar.
        Sosai ƙirjinsa ya harba. Ya ajiye shayin a kan mirror da biscuit ɗin yana faɗin “Gashi nan kisha kafin ki kwanta”. Daga haka yay ficewarsa dai-dai da ita kuma taja hijjab ɗin sallarta data samu nasarar gani a yanzu ta ƙudundune jikinta.

         Koda Yoohan ya fita da sassarfa ya rufe ƙofar falon ya kashe komai ya nufi nasa ɗakin shima. Ƙofar ya maida ya rufe ya jingina a jikinta da rumtse ido da ƙarfi. Tsaf Nu'aymah ta shiga dawo masa cikin idanu. ‘Ƴar 17years ce da wannan surar?, ko ina ya kai yanda ya kamata?’. Ya ayyana a ransa tsigar jikinsa na wani yamutsawa................✍

😜Ƴar yarinyace fa Dafta, ka bari sai ta girma kawai🤣🙄.


_______________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.




*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 50

____________

_Ina ma’abota karance karance littafin hausa? Wanda ke nishadantar wa ya fadakar? Kana ya tsunduma ku a kogin lobayyar kauna..?_

_*REAL FEEDO* hazikar marubuciyar nan ta zo muku da wani gangariyar littafi mai suna: *BA AMO...!* *BA AMO* wani nazartaccen littafi ne daya zo da wani irin salo na daban..._

_Labarin *BA AMO* ya faru akan wata yarinya da d'an sarkin garin su, yarinyar gidan su gidan yawa ne...Baban su yana auri saki ya tara 'ya'ya da mata da yawa. Tirqashi! To ita yarinya sunan ta KHAIRAT... Tun farko dangin mahaifin su sun tsani mahaifiyar tasu,Bayan ya auro ta, Ta haifi yara mata zallah suna kiran ta da uwar mata kuma kwata-kwata basa kaunar ita da 'ya'yan nata. To ita yarinya ta gama karatun ta.... wato KHAIRAT.. shekarun ta 22 matan gidan nasu suna mata gorin tayi kwantai tak'i aure. Kwatsam wata rana yarinyar ta samu labarin d'an sarkin garin su ya bude sabon company ya fara daukan sabbin ma'aikata, 🧚🏻‍♂️😍cikin ikon Allah ta zuwa ta samu aiki. Ta fara zuwa aikin ta, a karshe su kansu da suka fahimci kwazan ta da nutsuwar ta samu karin matsayi. To a lokacin ne kuma Yarima da PA dinsa suka sami matsala aka kore ta a ma'aikata sai aka daura ita Khairat d'in a matsayin P.A dinsa. Tafiyar tasu batama yi nisa ba! Aka yi makiya suka yi masu sharrin wai karuwar sa ce, har labarin yaje gun mai martaba. Itama Khairat d'in labarin yaje ga mahaifin ta har ya nemi korar ta daga gidan sa, da kyar aka lallashe shi ya hakura.._

_Tab rungutsumi din fa kenan🤮Ya zata kaya ne ga YAREEMAH GA KHAIRAT..a roof d’aya? Ya rabbi😢 labarin kauna yayi.. Amma fa Za’a sha rikici.. Karku manta khairat daga gidan yawa tafito🥺Ga basuda wani hali.. Shin sarki zai yadda da Khairat amatsayin personal assistant din yareemah ko kuwa.? Duk wannan ruguntsumi n REAL FEEDO ce kadai zata iya warware mana.._

_BA AMO::::: (Ba Labari...)_

_DOMIN MALLAKAR NAKI/‘NAKA TUNTUBE MU TA:_ +227 81 73 10 21


________________

No. 50

............Ya jima tsaye a jikin ƙofar wutar kansa a ɗauke. Kafin ya ja ƙafa da ƙyar zuwa saman gadonsa. Duk yanda yaso barci ya ɗaukesa hakan ya gagara, har kusan 2, daga ƙarshe dai ya miƙe zuwa toilet, ruwa ya sakarma kansa kafin ya ɗauro alwala ya fito. Daga haka yay nafilfilin daya saba, ganin ya kai har asuba saiya bari sai da yay sallar asuba ɗin sannan ya haye gadon ya kwanta ko azkar yau bai iya kammalawa ba saboda barcin dake cike da idanunsa.

          A ɓangarrn Aymah kuwa kanta ta dafe tare dayin jifa da hijjabin tana ballama ƙofar harara, sai kuma ta zabura ga ƙofar ta murza mata key wai karya dawo. Addu'a ta komayi akan ALLAH yasa bai ganta da ƙyauba, idanko ya ganta to bata yafe ba (dan ƙari😂). Da ƙunƙuni ta koma gaban mirror ɗin inda ya ajiye tea ɗin, babu kunya ta zauna ta sha dan dama ƴar yunwa na cinta ƙasa-ƙasa, alwashin data ɗauka na daina cin abincin gidanne kawai ya sata cewa ta ƙoshi. Sai da ta shanye tsaf taci rabin biscuit ɗin sannan taje ta sake yo brush tazo tai kwanciyarta.

★★★★

        A ɓangaren madam Chioma kam ta fitane da wani irin jin zafi da takaicin Aymah, dan ita duk a tunaninta da biyu tayi abinda tayi. Batasan ita Nu'aymah ko tarin farko da tayi, tayine kawai dan neman tsokana bawai danta kawo wani abu a ranta game da zaman nasu ba, tunda tasan sudai basu ɗauki taɓa jikin juna komaiba musamman ma ita dake a matsayin mahaifiyarsa. Ko kallon Victoria da Abraham dake rigima akan camara batai ba ta shigewarta ɗakinta ta banko ƙofa. Zama tai kan sofa zuciyarta tamkar zata tarwatse dan tsanar Aymah. Waya ta ɗauka kamar zata kira ƙawarta sai kuma ta fasa, a ganinta gara ta bari su haɗu a church jibi lahadi zasufi yin maganar yanda ya kamata ai.
      Hular gashin dake a kanta ta tuge ta ajiye, cirkuɗaɗɗen ainahin nata dake guntu ya bayyana. Fitowa ta sakeyi daga ɗakin zuwa sashen Papa. Baya falo, dan haka ta nufi bedroom ɗinsa kai tsaye. Saurin tura hoton hannunsa da lighter da zai ƙonashi yayi ƙarƙashin gado dan yazata cikin yaransa ne wani ya shigo masa. Amma ganin matarsa ne sai ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai dai hakan baisashi sake ɗakko hotonba duk da itama tasan wani abu akan hoton.
     Ita sam bama ta lura da abinda yayi ba, ta zauna a bakin gadon kusa da shi tana hawaye. Duk rikicewa yayi, ya shiga jera mata tambayaoyi da rungumota jikinsa. Bata iya bashi amsaba sai da tai kukanta ta more sannan ta labarta masa abinda ya faru. Murmushi yayi dan shi baiga wani abin fushi ba anan, a fili kam sai yace, “Uhm-uhm Darling cool down, ke mima ya kaiki sashensu yanzu? Kin sanfa yanzu yana da mata, duk kulawar da kike tunanin baya samu yanzu akwai mai masa”. Ɗan turesa tai ta tashi zaune sosai. Ya ƙyalƙyale da dariya yana riƙo hannunta, “Ah son ƴaƴa yamiki yawa Madam, karfa kice zaki ringa irin halin su mama akan matar John Please, dan indai kina nuna mata ƙi bazamuci nasara akan burinmu ba zaki rusa mana aiki”.
           “Honey yarinyar nan bata da kunya, ciwon da kaga Mira taji fa itace ta saka mata ƙafa ta faɗi saboda ta mata tsaki”. Idanu papa ya zaro waje sosai da faɗin, “Da gaske?”. “Na rantse maka kuwa Honey, abinda yasa nai shiru banyi maganaba saboda itama Miracle ɗin shegiyan kanta ne, danni tama isheni a gidan nan, ya kamata ta koma gidansu hakanan tunda ta kammala karatun ai”.
       Da sauri Papa yace, “No baza'ayi hakaba Darling, kawai dai zan mata gargaɗi karta sake shiga rayuwar matar John, inba hakaba kuwa shine da kansa zai koreta a gidan nan tunda tasan halinsa”. Wani shegen kallo Madam Chioma kema Papa mai cike da tuhuma. Amma sai ya basar kamar bai ganta ba. “Humm” ta faɗa tana haɗiye abinda ke a ranta. a ganinta inma hakanne ai zata saka idanu ta tabbatar. “Naji, yanzu dai inason kaima John magana, dolene idan yana garin nan ya ringa fita church bawai dole sai Sunday ba. Idan bamuyi hakaba yarinyar nan zata iya sakashi ya fara salla. Gara mu saka masa ido sosai itama kanta duk Sunday ya sata tana binmu tunda akwai addu'oin da ake masa, tunda kuma yanada mata kaima kasan a ƙa'ida dole saita ringa kasancewa a wajen”.
        “Eh maganarki gaskiyane kam, zan zauna da shi sai muyi magana”.
      Kanta ta jinjina masa alamar gamsuwa. Daga haka suka cigaba da hirarsu har ya manta da batun ƙona hoto ma.

*******

      A ranar gaba ɗaya Nu'aymah wasan ɓuya ta dingayi da Yoohan, gaba ɗaya taƙi yarda su haɗu har yamma duk da dai ya daɗe bai tashi a barci bane, sai gab da azhur ya tashi, yana yin wanka kuma yay shirin massallaci ya fita. A lokacinne ya isketa a falo tana kallo. Amma tanajin motsinsa ta tashi da gudu ta shige ɗakinta harda mirza key. Shi dariya ma ta bashi a lokacin, amma sai ya gimtse baiyiba yay ficewarsa dan ya kusa makara.

          Sai bayan sallar la'asar ya dawo massallaci ne ya ritsata ta fito zataje garden. Karo sukayi a bakin ƙofa, tai baya da sauri tana tura baki gaba da dafe goshinta. Uffan baice mata ba, sai idanu daya kafeta da shi. Dan doguwar rigar atamfar jikinta ta mata ɗas, daka ganta kaga cikkakkiyar bahaushiya ƴar arewaci.
        Jin yaƙi cemata sannu ta sake tura bakin tana tara hawayen ƙarya, ita a lallai dole taji zafin bigewar da tayi. Raɓashi tayi zata wuce yay azamar riƙo hannunta ya dawo da ita gabansa. “Kin gama gudun?”. Ya faɗa a hankali kamar bayaso. Yanda yay maganar muryarsa a sanyaye ne yasa kallonsa da sauri, kallon ido cikin ido sukaima juna, ya ɗan lumshe nasa dake da ja a ciki, gashi sun ɗan kumbure ya sake buɗewa a kanta.
      Samun kanta tai da faɗin, “Baka da lafiya?”. Kansa ya ɗan jinjina mata da yamutse fuska, kafin yace, “Kaina ke min ciwo”. Ya bata amsa yana sakin hannunta dake cikin nashi.
     A bazata yaji tace, “Dama likitoci na rashin lafiya?”. Tai maganar da waro idanunta manya waje sosai. A karan farko ya saki murmushi yana ƙoƙarin raɓata zai wuce, sai da ya shige falon sosai sannan yace, “Shi likita ba mutum bane?”.
         Harta buɗe baki zatayi magana sai ta fasa saboda hango Papa na sakkowa daga sama waya a kunnensa. Sai dai kuma idanunsa na kansu da ga ita har Yoohan ɗin. Juyawa tai ta fice abinta.

_______★★★★________

  *_KANO TA DABO_*

        Kamar yanda baba malam yayma Umm bayani akan ƴar aiki da Aymah ta buƙata daga nan, itama Hajjo ya sameta da zancen, Ɗari bisa ɗari hajjo ta bada goyon baya, sai dai tace ya kamata a tuntunɓi Yoohan idan ya amince, idan bai aminceba a haƙura kawai, a hankali zata saba da waɗanda ƙadadara ta kaita zama da su. Harma suna mata fatan cin riba akan hakan.
       Duk da baba malam ya riga da yayi magana da Yoohan akan maganar tun kwana biyu daya wuce sai ya amsama hajjo da cewar insha ALLAH a yau zai tuntuɓi Yoohan ɗin, yanda sukayi kuma zataji. A ransa kuwa da biyu yaƙi faɗa mata gaskiyar yanda al'amarin zai kasance. Ba komai ya jawo hakaba sai laɓe daya fahimci anai musu shi da Umm kwana biyun nan, inuwarnan daya gani a ranar da za'a kai Aymah Abuja. Sai kuma ya sake ganinta randa yakema Umm bayani akan wayar da sukayi da Nu'aymah. Sai dai yayi shiru da bakinsa ko Umm ɗin bai sanarmawa ba. Sai Yoohan da shima yay masa zancen ganin mutum a randa akai maganar cikin nan na Aymah,  dan randa Nu'aymah tai masa maganar mai aiki daga nan kano ya kira baba malam sunyi doguwar waya.
      A yanzu haka fatansa ALLAH yasa maganar da sukayi da hajjo an laɓe musu ɗin. Dan duk mai aikata musu SARAN ƁOYEN zaiso ace koma wace ƴar aiki za'a turama Nu'aymah ya samu dangantakar da zai ringa samin bayanai akan Aymah.
      Baba malam ya jima a wajen Hajjo da tunanin ko zai sake ganin inuwar mai laɓen nan. sai dai harya ƙaraci zamansa da kallon windows babu ko ƙyallin mutum balle wata inuwa. Hakan ya bashi mamaki amma sai ya share dan baya buƙatar hajjo ta fahimci komai tun yanzun, sai sun kammala ɗana tarkunansu tsaf sannan.

         Washe gari baba Malam ya sake samun Hajjo da maganar cewar Yoohan ya amince da maganar mai aikin. Fuskar Hajjo faɗaɗe da murmushi tace, “To to Alhmdllhi, madalla da ɗan albarka Yahya. Kaga bara na shiga nan gidan Iyami da kaina sai na mata bayanin a samo mai hankali ba yarinya irin Zainabu ba. Dan bazai yuwu a irin wannan zaman a haɗa ƙuruciya da ƙuruciya ba. Sai dai wadda taɗan tasa idan taga ba dai-dai ba ta nusar da ita”.
       “Eh gaskiya ne inna, hakan yayi kam. Dan mamana halinta kam sai ita, inba mai ɗorata a hanyar aka samoba sai aita samun matsala dan har yanzun hankali bawai ya gama isarta bane”.
          “Ai karka damu ɗan malam, wlhy duk abinda kaga Zainabu nayi nima nayisa, babu abinda ta bari na ƙuruciyata. Malam yasha fama dani bana wasa ba. Amma kaga ina fara haihuwa duk saina rage nawa. Garama Zainabu ai a shekarun da akai mata aure ta tasa fiye dani. Tunda ni ina sha uku aka aurama babanku ni, itako sha bakwai fa harda wasu watanni”.
          Baba malam dai kansa a ƙasa yanata ƙoƙarin haɗiye dariyarsa. Dan shima kafin mahaifinsu ya rasu ya taɓa bashi labarin ƙiriniyar da Hajjon tayi a gidansa. Da yake shi haka yake, duk randa ƴan labarin nasa ya motsa sai ya zaunar dasu yayta basu tarihin gwagwarmayar da yayi ta rayuwa harma da ƙuruciyarsu. Wannan ɗabi'ar ta mahaifinsu tana ɗaya daga cikin abinda basa iya mantawa a rayuwarsu su duka.

        Kamar yanda Hajjo tai alƙawari da yamma kuwa sai ta shiga gidan su Hamisu wajen mahaifiyarsa Iyami. Sosai Iyami ta dinga haba-haba da hajjo duk da kuwa kasancewar su maƙwafta. Amma da yake ba ɗabi'ar shige-shigence da suba inba da ƙwaƙwaran dalili ba, sai yazam duk randa akaga juna kamar baƙi.
       Bayan sun gaisa hajjo tasha ruwan da Iyami ta kawo mata duk da ba ƙishin take jiba, sai dai a cewarta ruwan zuminci yafi zuma garɗi. “Yauwa Iyami nasan kinata mamakin ganina da maraicen nan. To dama ba wani abune ya sani fitarnan ba ta gabannin magriba sai takwarata ƴar jikalleta Zainabu da aka kai Abuja”.
        Iyami dake murmushi tace,  “Oh ALLAH sarki Nu'aymah amarya zaki cemin, inadai fatan suna nan lafiya ko?”.
          “Ah lafiya lau suke sai alkairi kam. Mijin ne dama ya kira wai a nema mata mai aiki daga nan, shine nace to bara nazo da kaina wajenki ƙila ta hanyarki a samo wata mai hankali. Danni ƴan aikin gidan nan namu yanzu tsoro al'amarinsu ke bani wlhy Iyami. Kuma kinsan duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login