Showing 1 words to 3000 words out of 72389 words

Chapter 1 - MOHAN HAUSA NOVEL

bintou   

27 Jan 2025

4904

https://chat.whatsapp.com/LktP8sXbLIK8zYRtUl6s37

*MORHAN*

_Bismillahir rahamanir Raheem, Da sunan Allah mai rahama mai jin 'kai_

                 *_SADAUKARWA_*
_Gabadaya littafin nan sadaukarwa ne ga aminin arziki Sani M Naseer Allah ya biya maka bukatunka na alheri Ameeen_

               *SHIMFI'DA da GABATARWA*
Tabbas a cikin rayuwar kowannenmu akwai duhuwa wanda idanuwa baya iya ganinta. Kullum nitsawa cikin duhuwar muke a yayinda haske ke bayyana a gare mu bayan mun yi nitso a cikinta. Kaman haka 'kaddara yake, ba mu sanin haskenta sai mun nitsa a cikinta sannan. Hmmm... Masu yawan bibiyan al'kalamina zasu yi tambaya a nan, "Bintou me yasa kike yawan jefo kalmar 'kaddara a cikin rubutun ki?. Amsar ita ce "'kaddara ce tayi sanadin komai, sanadin da na fara ri'ke al'kalami, 'kaddara ita ce mafari, ita ce silar rubutuna, sannan ita ce zaren da ke bibiye da rayuwar kowannen mu.

Ban ce tafiya ce mai sau'ki ba, labari ne da ta 'kunci, tsantsar soyayya da sadaukarwa, amma ban muku alkawarin zallar soyayyar ba. Akwai 'kunci, da damuwa wanda su suka na'kasa farincikin MUHAMMAD NASEER (Morhaan), sannan akwai farin cikin da ta kasa zama zahiri a gare shi.

(Labarin Zakiyyah, Muhammad Sani, da Ahmad).

MORHAN Labari ne da ya ta'bo wani 'bangare na rayuwar Muhammad Naseeer( Morhan ).  Masana soyayya sun misalta soyayyar uwa da garkuwan da ke tattare da tasirin nagartar mutum, hadida hasken da ke 'kara karfafa mutum a raye a takaice ma soyayyar uwa ya wuce tunanin mutum.

Ya rayuwa zata kasance idan mutum ya rasa soyayyar mahaifiya?, shin mutumin da ya rasa soyayyar uwa zai iya samun garkuwan da zai yi tasiri wa nagartarsa?, ta ina zai samu hasken da zai haskaka rayuwarsa?, Shin ya addiction yake?, Ina nufin sabo da abu, kaman addiction na shaye shaye, ya rayuwar irin mutanen nan yake kasancewa musamman ina sun yi niyyar dainawa?.

Meye mafari?, Wa zai maye masa wannan gurbin da ya rasa?, wane illa hakan zai jawo masa?, yaushe bakin ciki zai gushe daga rayuwar sa?, Sai yaushe kuncinsa zai yanke?...

October 1944

*Maaarautar khindar*

"Ayari zai motsa!, Wanda baya kan dokin sa ya hau, Wanda ke wani uzurin ya katse za mu fita ta 'kofar gabas!, Ayari zai motsaa Wanda baya kan dokin sa ya hau, Wanda ke wani uzurin ya katsee!! Ayari zai motsaa Wanda baya kan dokin sa ya hau, Wanda ke wani uzurin ya katse za mu fita ta 'kofar gabas!!!"

Cewar daya daga cikin bayin dake bisa tawagar da suka yi ayari cikin Shirin barin garin. Cikin 'kankanin lokaci tafiya ta soma bayan kowannen su ya kara duba kayan sa gudun mantuwa..



KINDHAR babbar ƙasace a tsakkiyar wani babban tsibiri a wani ƙarni , ƙasace mai yawan arziƙin ma'adanai da kyawun kasar noma, yankin na gabas da nahiyar Africa. Ƙasar KINDHAR na da karamar Daular mulki da ke ƙunshe da sarakuna masu ɗunbin tarihi da labaransu bazai taɓa gushewa a duniya, duk da kasancewarsa 'karamar 'kasa sun yi gwagwarmaya da dama wanda ya sa a yanzu suke zaune da 'kafafun su . Ba arziƙin ma'adanai da kasar noma ne kawai suke da shi ba, su na da baiwar kiwon nau'ukan dabbobi kala kala, Wanda Hakan ya 'kara ha'bbaka arzukan su fiye da 'kima. Su kan fita da kayayyakin su ƙasashe daban-daban ko'a shigo da su cikin ƙasar Kindaar, sannan su kan yi hijira zuwa wata 'kasar domin zuwa neman ilimi, ko tafiya ta harkar kasuwanci. Kaman yadda wadannan ayarin suka yi, bayan daukar shekaru da dama suna shiriyawa wannan tafiya, domin tafiyar ta kunshi kasuwanci ne da neman ilimi, hakan ya sa suka ha'da kusan duka dukiyar waje 'daya da aka damka rikonsa ga amintaccen bawan sarkin yankin wato sunusi. Tafiya tai tafiya, rana ta shige, duhu ya fara mamaye gari, sai suka nemi waje suka kafa rumfa, bayan sun 'daure dawakan su. Cikin dare Sunusi ya laluba ajiyar dukiyar da aka bashi, sai ya ga wayam, ya dawo cikin rumfar su, Yana tambayar matarsa ko ta sauya masu mazauni, yayi tambayar a daidai shigowar 'kanin sa Ahmad Bako. Ahmad ya rafta uban salati yana kallon sa.


"Yaya kar ka ce min kana nufin amanar ayari ya 'bata?"

Cikin tashin hankali sunusi ya ce
"Ban gan shi ba...."

Ahmad ya rafka uban salati Wanda ya jawo hankalin sauran jama'a, suka firfito daga bukkokin su kaman masu jira. Su ma jin abin da ke fita a bakin Ahmad ya sa suka rike baki wasu na salati, yayin da ahalin sullu'bawa suka fara 'daga murya suna neman tada jijiyan wuya, hayaniyar su ya ankarar da dakaran da ke bangaren rumfar shugaban tawaga, ya aika a kira su, suka gurfana a gabansa, zuwa wanna lokacin fitsari ne kawai Sunusi bai yi ba, don iya firgici ya gama firgicewa.

"Wallahi Allah shine shaida na bani da masaniya akan yanda akayi dukiyar nan suka bata. Kowa a nan shaida ne lokacin da aka bani dukiyar a bayan ra'kumina na 'daure, Kuma da ita muka taho.. ko.. ko Kuma wata 'kila faduwa yayi a hanya ban sani ba"

"Yi mana Shuru munafukin Allah, idan har ka daure a bayan ra'kumin ka kwanto mana shi mana fada mana inda ka boye mana dukiya kawai"

" Ni dai ban boye a wani wajen ba sai dai ku jira ni.... Wata 'kila ya fadi ne, a bani dama na koma na duba tun da bamuyi nisa ba, wata 'kila fa'duwa yayi"

Sunusi Bako ya fada cikin tsananin tashin hankali. Sati daya kenan da aka dam'ka amanar rabin dukiya a hannunsa yayi wa dukiyar kyakkyawar adana don kafin yau an sha kawo masa farmaki don a farauci dukiyar, amma ko da wasa bai taba bada dama ba. Dukiya ne a dun'kule damin 'danyen zinare wanda idan aka kasafta adadin kudin shi zai kaiwa dala Miliyan dari biyu. Cikin kaduwa Talbah da tasa dukiyar ta fi ta kowa yawa ya ce

"To Sunusi kai da kanka kace ka 'daure a bayan ra'kuminka kuma kafin tahowar tawagar ayari daga masarauta ka tabbatar mana da cewan kayan suna inda suke Kuma yanzu kace mana baka da masaniya a kan inda suke?, Kenan bayan ka 'daure ni na zo na kwashe ko kuma me kake nufi?"

Sunusi ya kalli Talbah da ke masa magana cikin zafin Rai, ji yake kaman ya sa hannu ya 'daukeshi da mari, ya kauda kansa yana cizan la'bensa. Ya san da a masarauta ne, cikin su babu Wanda ya isa ya masa kallon banza balle a tuhumesa da laifin da ake zargin ya aikata, saboda shaidar da aka yi masa, yana da rikon Amana sosai, hakan ya sa mai martaba da kansa ya na'da shi a matsayin amintaccensa babu wani sirin mai martaba da bai sani ba.

  Sunusi ya hadiye yawu muqut saboda yanayin fuskar Talban da ya gani, ba ma shi ka'dai ba, har da mutanen da ke wajen matayen su sai turo baki suke suna  gunguni 'kasa 'kasa don ba dama su tanka suna matukar ganin girman shugaban Ayari, dukda kasancewan batu ake na ma'kudan dukiya da suka 'kare rayuwar su suna ha'ka  suka tara domin jiran ranar yau a ce lokaci guda an neme su an rasa?.

Sai da Sunusi ya daidaita nutsuwarsa kafin ya kalli Talba da ke jiran jin ta bakinsa yace

"Talbah, ka yadda da ni, bani da abin fa'da na gama magana, ban san ya aka yi ba?, Ban San inda suke ba, na tabbas na taho da su, a bincika ko wani ya hada da kayansa a rashin sani, amma tabbas na taho da shi sai kuma in faduwa yayi"

"Sharri zaka mana?, A bincika kayan wa?, Tun da muke ba'a taba samun 'barawo a wannnan ayarin ba, don haka kai ka san Inda ka 'boye munafukin Allah ta'ala"

"Talba ka yadda da ni..."

ya qarasa muryarsa na rawa zufa na keto masa, fargaba yake yi da mamakin yadda aka yi ya rasa su, tabbas koda rana lokacin da suka sauka don yin sallar azahar ya gani, to me yasa? Ya aka yi ya rasa su a yanzu kuma?, Kuma shi Shaida ne a kan babu Wanda ya zo kusa da rakuminsa, don gudun hakan... Yana da tabbacin wata 'kila fa'duwa yayi a hanya....

A yadda suka dauki burin duniyar nan suka 'dora a kan zinaren, ya san idan ya tabbata zinaren sun 'bata  abu biyu ne dole daya ya faru, ya sani a wannan wajen, abu ne mai sauki su gasa namarsa su binne 'kasussuwansa ba tare da wani ya sani ba. Idan ya tabbata zinaren nan sun 'bata tabbas ba zasu yafe ba, sai sun dauki mataki , a yanzu ko shi aka mayar zinar baza'a hada adadin abin da ya 'batar ba.

"Maganar wani kila wa'kala duk bata taso ba, dukiya ce iya dukiya fa... ko shi mai martaba da ya amince da kai, sirrinsa kawai ka sani na alaka da zamantakewa, Amma bai barka ka san lamurran dukiyar sa ba, don haka, babu wani munafurcin da zaka mana a nan, ka ga kudaden da baka taba gani ba, ka shirya kitumurmura don ka mallake su Kai kadai, ka fito fili kawai ka fada mana inda ka 'boye su, in ma da wasa kake mana batun 'batan su, ka ga sai mu fahimci inda ka dosa cikin ruwan sanyi baki alaikum ba sai zancen tayi tsayi ba"

Attahiru Babban 'dan sarkin Tsullubawa ya fada yana wani zazzare masa ido kaman zai Kai masa tafi, sai a lokacin sauran suka magantu.

"Nima dai abinda na gani kenan, idan kuma yayi taurin kai ranka shi dade ina ganin a barshi da jami'ai su Yi aikinsu nasan su zasu tunasar da shi inda suke" 

"Ai ni tun da can ban yadda da shi ba, ku ne dai kuka ga dacewar a bar masa kayan..."

"Dama ai mai martaba ne ya dage sai an bar mashi, abu sai kace dukiyar ta uwarsa ce"

Cewar Idi yana 'kara wa miyar gishiri. Ganin haka tuni kowa ya shiga tofa albarkacin bakinshi.

"Yo wa ya sani ma 'kila hadin baki aka yi don a cuce mu?"

"Wallahi ba zata sa'bu ba, uban kuturu yayi ka'dan, na rantse da rabbil izzati sai dukiyar nan ta fito don ba zai yiwu jaki da aiki' kato da kwashe kaya ba, kai in fa ta kama har shi mai martaban sai abin ya shafe shi, don ba wani ya ce muna bu'katar mai ajiya ba, ba mu ce mun Gaza ba, wa ya sani ko duk shirin su ne"

cikin Sunusi ya kada, ya ringa raba ido tsakanin mutanen da suka kewaye shi, duk da kasancewan sun kasance ahali a gare shi, amma tun lokacin da mai martaba ya mai da shi amintaccen bawansa sai suka fara nuna masa hassada a Fili.

Abu kaman wasa sai guri ya kaure da hayaniya, babu mai kare shi, dama kaman da can haushin sa suke ji, ita kou matar sa banda kuka babu abin da take yi, gata da tsohon ciki.

A karo na farko Shugaban tawaga Halliru ya motsa laɓɓan sa, cike da izza da ƙasaita irin ta masu karamin mulki yayi magana.

“ Duk na ji bayanan ku kuma a bar komai a hannuna"

Yay maganar yana kallon sunusi Wanda a yanzu hawayen tashin hankali sun fara sauko masa.

"ina so daga yanzu zuwa wayewar gari na ji kyakkyawan labari a kan dukiyar bayin Allahn nan, ban damu da yadda zaka nemo su ba, ina so in san ta inda aka kwana a ragaya"

yana gama fadar haka ya tsuke bakinsa yana kallonsu , ya ce

Baya so a sake tada maganar, sannan ya umurci masu gadi biyu su yi masa rakiya su bi hanya su koma.

Sunusi ya sauke ajiyar zuciya me nauyi, jiki da bakinsa suna rawa ya sake gurfana a kan gwiwowinsa yana godiya cike da ya'kinin zai gani.

 

Talbah da Indo matarsa wa'danda faruwan hakan yayi musu dadi, suka 'daga kai a fakaice suka kalli juna tareda 'dage gira daya suna murmushi.


Sannan cikin zafin ran dake nuna ba'kin ciki da hassada 'karara Talbah yace

"A'a Ranka ya dade, ba za mu yadda ya tafi shi kadai tare da wadannan masu gadin ba, dole 'dayan mu ya bisu domin mu muka san azabar da muka sha kafin mu tara dukiyar, in banda rainin hankali ma taya za'a ce mana dukiya ta 'bata?, Sai kace allura?, Yo ai ko amanar allura aka baka baka Isa ka gaya mana ya 'bata ba, don haka ya zama dole mu bi shi, ka bani dama ranka ya dade ni zan bi bayan sa...."





Arziki kala kala ne
Wasu Allah yana basu arzikin lafiya, wasu Kuma Allah ya basu na 'ya'ya, wasu Kuma Allah ya basu na tsantsar dukiya, wasu na ilimi, wani na farin jini wani na iya mu'amala.

Sai dai duk Wanda Allah ya baka, ba zai hana tawaya tunkarar sa ba.

Shin me ya kawo batun 'batan zinare muna labarin Muhammad?.

Shin da gaske 'bacewa zinaren yayi?.



Shimfi'da kenan daga littafin Morhan.

In Sha Allah Asalin labarin zai zo maku a ranar shida da watar Nuwamba 2024.


Ina fatan zaku kar'bi labarin fiye da yadda kuka Saba kar'bar sauran.

Na gode

Bintou ce.

Nayi gabas🚶🏾‍♀️
22 oct 24.
*MORHAN*
(love beyond addiction)

_Dedicated to Problem S_

_Disclaimer_
*In the name of thy lord almighty..All right reserved. Wannan labarin gaba dayan ta mallakin *Zakiyyah Bintou ishaq* ce, any resemblence of story or lifestyles should pls be considered as a plagiarism. Ban yarda a dora shi a kafafan siyarw ba, karantawa bugawa ko a juya min shi ba tare da izini na ba.

_Shafin farko sadaukarwa ce ga Khadijah Shehu Haruna_

Kowace gauta.....

*001*
"FUNTUA...!,, KANO, KADUNA, ABUJA MAIDUGURI JALINGO, BIRNIN YERO...!"
"Kaduna mutum 'daya"
"Katsina ciko..."
Duk da girma irin na garajin 'dan magaji, babu lungu da sak'on da zaka kurd'a sautin muryar masu lodin mota da matafiya daga Zaria zuwa garrurruwa mabanbanta bai zagaye ba. Sannan ga mutane nan birjik! tun daga yan talla, na cikin gari har zuwa matafiya masu baza nasu hajojin.

Duk inda zaka duba mutane ne ke kai kawo, kowa da abin da ya kawo shi tashar.
A cikin wannan hayaniyar Zakiyyah na can tsaye jikin wasu motocin da suke lodi zuwa abuja. Hannunta rik'e yake da wani kwando cike da wasu manyan gorunan Popcola, fanta, da biscuits sai kokarin tura kai tsakanin motocin take tana nuna musu don su saya.

"Pop cola...!, Ranka ya da'de Pop cola, akwai fanta mai sanyyi, akwai biscuits wane kala za'a baki, akwai wafer, fantasiya, bakers speedy da cabin, hajiya a kawo?, 'dan yalo kana kallon biscuit ne?, yunwa kake ji ko?, ka ce mama ta siya ma"

Ta fada tana kai dubanta da matar da ke rike da yaronta, shi kuma idanunsa na kan biscuits din hannunta. Matar ta ha'de girarta biyu alamun rashin fahimtarta.
"Shi ya ce zai ci biscuit?"
"No hajiya if him mouth is not talking him face is saying it, hajiya kada ki shiga hakkin yaron nan, aradu yana son biscuit din nan ki siya kawai ba tsada, just handred naira"
Ta fada tare da fito da Speedy biscuit mai 'ya'ya tana karka'dawa. Maganar ta sa mutanen da ke cikin motar dariyar da basu shirya ba a lokaci guda, matar ta girgiza kai ta fito da kudi cikin purse dinta tana dariya.
"Kin dai rantse sai kin ci kudina to gashi bani 'daya ki ban canji"

"Hajiya 'daya kuma?, Ke fa? ba zaki ci ba?"
"Ba zan ci ba, ban canjina''
"Allah ya baki hakuri, daga gani bakanuwa ce, uwar ma'ko sai ki ci a cikin na 'danki ai"
Ta furta tana mi'ka mata chanjin, sannan ta yi gaba tana
"Poop colaaa, fantasiya, speedy, akwai fanta''
"Mai fanta akwai mai sanyi?"
Muryar wani mutumi ya dakatar da ita.
"Gidan ku akwai nepa ne hala?"
Ta bashi amsa ba tare da ta juyo ba, tana ji yana fadin bakaken maganganu irin na yaran tasha masu jiran a kula su, bata kula shi ba ta yi gaba don ba shi ne a gabanta, ba shi kadai ba duk mutanen da ke tashan kama daga manyan har direbobi babu wanda ya Isa ta tsaya tana musayar yawu da shi, kasuwanci ya kawota tasha kuma shi take yi ta kama gabanta, duk maganganun da zaka fada a kan ta in dai ba siyan kayanka zaka yi ba to ko kallo baka isheta ba. Hakan ya dasa tsanarta a zukatan wasu daga cikin su don a cewan su tana da girman kai.

Karfe biyu na rana ta baro tashar bayan ta gama siyar da lemuka da biscuits da ta saro tun daga kaduna. Daga tasha kasuwar sabon gari ta nufa shagon wata tsohuwar makociyar su Mama Ijeoma inda take sana'arta ta siyar da kifi a duk sanda ta dawo weekend. A nan ma kasa kifayenta tayi wadanda take ajiyan su a fridge din Mama ijeoma, idan bata nan ta kan siyar mata sai su raba ribar, idan tana nan kuma ta samu waje ta siyar ta rike kudinta.

Tana shagon aka kaure da ruwa mai karfi hakan ya sa bata baro kasuwar ba sai yamma. Ran ta cike da farin ciki, don cinikin yau ya zarce na kullun.
Garin yayi luf-luf kasancewar yanayi ne na anyi ruwa an ɗauke. Duk inda ta wuce a bakin titi nan garin ruwa ne a kwance yana gangarawa, wani kuma ya maƙale a bakin ramin da titinan suka fara fiddawa saboda yawan wucewa ta kansu da ake yi.

Kallo 'daya zaka yi mata ka fahimci tafiya kawai take, amma hankalinta sam baya tare da ita.
fuskarta kaman kullum amurtu'ke babu annuri ko kadan. Kunnuwanta rufe yake da earpiece, tana sauraron motivations na *Muniba Mazari* wanda a kullum suke da'da zugata take jin cewa babu wanda ya isa da ita, kuma babu wansa ya dakatar da ita daga cikar mafarkinta, ta gudu daga rayuwar kulle kuma, za ta yi gudu iya iyawanta domin mallakan duk wani buri nata.

  Kyakkyawace amma ba lallai ka fahinci hakan a karon farko ba, ba'ka ce sai dai ba duhun da zai sa a kirata da sunan ba'ka 'kirin ba. Fuskarta a zagaye take, tana da tsayi sosai,  idanuwanta manya ne da suke ɗauke da zara-zaran gashin ido wanda ya ƙara ƙawata kyan idonta, haka kuma gashin girarta a cike yake sosai, gashi baƙi siɗik da shi. Dogon hancinta da kuma ƙaramin bakinta mai kalar pink ya taimaka wajen ƙawata kyakkyawar fuskarta, da a ce mai yawan murmushi ce da a ko yashe ana iya ganin haɓarta da ke lomatsa ta tsakiyarta, gefen fuskarta kuma akwai kwantaccan gashi akanta.
   

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login