Showing 15001 words to 18000 words out of 67530 words

Chapter 6 - SHIRYAYYAR-ƘADDARA HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4357

?in na ?auke da parlor biyar harda wannan wanda ya kasance shine babba a cikin su kuma yake a tsakiyar su, daga cikin parlorn zaka iya hangen sauran falukan dake floor ?in,masu karatu ba ?aramar dukiya aka kashe a wajen ha?a wannan parlorn ba idan nace sai na fayyace maku komai dake cikin shi to tabbas anan book one zai ?are,kawai ku ida ?issma sauran a zuciyar ku.


ma'aikata ne ke kai komo a cikin parlorn, zubewa su ka shigayi akan gwiwowunsu suna kai gaisuwa gareta, ko kallon in da suke ba tayi ba.


glass elevator su ka nufa,?an yatsanta tasa a jikin na'ura dake jikin ?ofar elevator nan take ?ofar ta bu?e, ciki ta shiga tana lumshe idanunta alamar gajiya,mara mata baya ma'aikatan su kayi,?aya daga cikin ma'aikatan ce ta danna wasu madanni dake ?auke da nombobi a jikin su,?ofarce ta shiga zuge, sama elevator tayi da su, daga ta ciki zaka iya hangen manya manyan parlor kan da suke wuce masu matu?ar kyau wanda tsayawa fayyace su har littafin ya ?are ba'a gama fa?ar kyawu da ha?uwar su ba, tsayawa elevator yayi da alama sun kawo in da za su tsaya, ?ofar ce ta shiga zugewa,sai data gama zugewa tas tukun tasa kai ta fice ma'aikatan na biye da ita kamar wasu jela.


nan ma wani katafaren parlorn ne su ka shigo wanda yafi na farkon ha?uwa sai dai bai kaishi girma ba,ma'aikatan ne nan ma ke kai kawo, take su ka shiga zubewa ?asa suna gaishe da ita, hannu kawai ta ?aga masu yayin da take yin gaba, a bakin wata katafariyar ?ofa su ka dakata, ?aya daga cikin matan ce tayi saurin mi?a mata wayarta dake hannunta, amsa tayi yayin da take ?aura tafin hanunta saman na'urar dake jikin ?ofar, zanen hannunta ne ya fito a jikin na'urar ,scanning hannunta na'urar ta shigayi na tsawan secon biyar kafin na'urar ta fara magana kamar ta ?ofar da su ka fara shigowa yayin da ?ofar ke zugewa.


sai da ?ofar ta gama zugewa tas tukun ta kunna kai zuwa ciki yayin da matan guda biyu ke biye da ita sauran su ka kama gaban su, wacce ke ?auke da backpack ce ta bi bayanta sai ?aya wacce take ri?e da towel ?in data goge mata jiki.

wani irin katafaren bedroom su ka shigo a ?alla girman shi ya isa ayi ?an ?aramin plat house saboda girma da fa?in shi, bedroom ?in yana ?auke da king size bed light golding, gadon na shimfi?e da tattausan bedsheet da ?aton blanket mai azabebben taushi ga jerin pillows wanda su ka kusa cinye kwata gadon,
gefe da gefen gadon nightstand ne mai ?auke bed sides lamps daga gaban gadon ottoman table ne mai ?auke da drawer chest a jikin shi daga saman shi anyi mashi kwalliya da wasu stones masu she?i an mamman a jikin shi.


daga ?asan gadon wani ha?a??e rug ne mai gashi gashi a jikin shi tsabar taushin shi har bacci mutum zai iya a kanshi ba tare da ya fahimci ba'a katifa yake ba,idan ka kalli saman ?akin wani irin ?aton chandeliers ne,daga hannun dama na ?akin glass sliding door ce wanda nan ma wani bedroom ?in ne sai dai komai na cikin shi white color ne, daga ?ayan ?angaren kuma wani ha?a?en stairs case ne can ma saman wani bedroom ?in ne sai dai bai kai wannan dana kusa da shi girma ba, daga ?angaren haggun ?akin wasu ?ofofi ne guda uku a jere ?aya bathroom sai spa and saloon wanda yake ha?e massege spa sai ?aya ?ofar dressing room ne wanda idan ka shiga cikin shi zaka ?auka boutique ne.


wacce ke goye da back pack ?in ce ta nufi laundry room,?ur?usawa ?ayar tayi a gabanta takalamin ?afarta ta shiga cire mata, zama tayi saman ?an stool hakan ya bata dama wurin cire mata takalmin, bayan data gama cire takalmin,sama nailarh ta ?aga hannunta hakan yaba matar damar cire mata rigar dake jikinta tayi ta barta daga ita sai bra ta ajiye gefe kafin ta koma kan wandon, wandon shima zame mata shi tayi shantala shantalan cinyoyinta ne su ka bayyana farare tas da su sai she?i su ke kai kace haske rana bai ta?a ratsasu ba,kwashe kayan matar tayi ta nufi laundry room da su,a tare su ka fito daga laundry room ?in ita da wacce ta fara shiga sallama su kayi mata su ka fice daga ?akin.



A kasalance ta shiga taka ?afafunta tana nufar ?ofar toilet, tafiya take kamar bata son gaka ?asa tana tafiya ko ina na jikinta na juyawa musamman ?ugunta da zanen rose flower na tattoo ya ?arama fatar bayanta kyau,tun kafin ta ?araso bakin ?ofar ta shiga zugewa kutsa kai tayi ciki,wani irin bathroom mai girman gaske komai na cikin shi expensive ne,harda silver bed mai ?auke da rober mattress mai ha?e da pillow sai daga jikin bangon toilet ?in glass drawer ce mai girman gaske an rarrabata gida gida wanda bakomai ne a cikinta ba sai tarin shower gels,soaps,shampoos, towels, bathrobes,sponges da flip flops.




?ofa biyu ce a toilet ?in da wadda ta shigo sai wata dake can ?ayan ?an garen , silver bed ?in ta nufa kwanciya tayi rub da ciki tana sauke ajiyar zuciya,wasu irin abubuwa ne a jikin ?ayar ?ofar masu kama da bulbs haske su ka shiga kawowa suna fitar da wani irin sauti can kuma su ka daina suna sanar da isowar lolah da larah,a hankali ta furta open ba tare da ta ?ago ba, zugewa ?ofar ta shiga yi, wasu matan turawa ne su ka shigo manya da su kamar ?an wrestling,ba?in mini skirt ne a jikin su tare da farar shirt ajikin rigunan su an rubata sunayen su da wani irin style, haka shigar ma'aikatan gidan take.


in da take su ka ?araso gaishe da ita su kayi suna ?an rissinawa,bata amsa masu ba hakan bai dame su ba idan da sabo sun saba da halin uwar gidan ta su,lolah ce ta nufi glass drawer ?in nan, bu?ewa tayi ta ?auko shower gel tare da soap da shampoo da sponge,a saman wani ?an table mai ?afafu ta ?aura, maida ?ofar drawer tayi ta rufe turo table ?in tayi zuwa gaban bed ?in, ?aukar shampoo larah tayi, bu?e marfin tayi ta shiga tsiyayama Nailarh shi a kai, bayan data gama ne tashiga cu?a mata kan sai data tabbatar ya wanku tukun ta jawo hand shower ta shiga wanke mata kan, bayan data gama ne ta ?auki shower gel ta shiga zubawa a ko ina na jikin Nailarh,sponge sock lolah ta saka a hannun ta larah na gama zuba shower gel ?in ta shiga mulka mata mashi a ko ina na jikinta, ko motsi Nailarh ba tayi kamar matatta su ke juyata yanda su ke so dan su wanko ko ina na jikinta.


sangarta da gata ne yasa Nailarh ko wanka bata ma kanta ba wai dan bata iya ba isa ce kawai da lalacewa tasa bata iya yi da kanta musammusam ta ajiye lolah da larah dan su ri?a yi mata wanka wanda aikin su ke nan a gidan, daga wankan ta da yi mata massege sai gyaran jiki babu abun da su ke iya aikin su kenan.


ta ?auki tsawan lokaci tana cu?a mata jikinta sai data tabbatar ko ina na jikinta ya wanku tukun larah ta jawo hand shower ta shiga wanke mata jikin bayan data gama ne ta ?auko hairdryer ta shiga busar mata da gashin kanta bayan data kammala busar mata da kan ta nufi glass drawer ?in nan ta ?auko bathrobe da flip flops ta dawo a bakin bed ?in ta ajiye mata, a kasalance Nailarh ta sauko daga saman bed ?in,flip flops ?in ta zura a ?afarta, mi?a mata bathrobe ?in tayi , ?ar?a tayi da kanta ta zura kafin ta cire hook ?in bra ?in dake jikinta ta ciro a ?asa ta yarda ita kafin ta warware igiyar pant ?in shima nan ?asa ta sake shi, igiyar bathrobe ?in ta ?aure ?ofar fita ta nufa ba tare da ta ko kalli ?aya daga cikin su ba.


bra da pant ?in lolah ta kwashe ta nufi dustbin ta saka Nailarh tana da wata ?abi'a ta rashin maimaita sutura idan har kaga ta maimaita sutura to ba ?aramin sonta take ba bra da pant dama su daga idan ta cire su to sun zama wasted bata ?ara amfani da su,gyra toilet ?in su kayi su ka maida komai mazaunin shi sannan su ka wanke toilet ?in duk da ba datti yayi ba bayan da su ka gama ?ofar da su ka shigo su ka nufa tun kafin su isa ?ofar ta bu?e alamar an basu izinin fita, ficewa su kayi.


Nailarh tana fita daga toilet ?in wannan sliding glass door ?in ta nufa tana isowa ?ofar na bu?ewa, ciki ta kutsa kai sai wani lumshe ido take, nan ma bedroom ne komai na cikin shi white color ne , babu wata hayaniya a cikin shi bed ne sai nightstand dake ?auke da bedside lamps sai rug mai taushi dake shimfi?e a ?asa sai chaise lounge chair dake bakin wata ?atuwar glass sliding door wacce da an bu?eta zata sadaka da ?yataccen swimming pool wand kusan ha?e yake da ?akin ?ofar ce kawai ta raba su sai ruwan da suke a kewaye daga bakin swimming pool ?in lounger chairs ne guda biyu suna fuskantar juna sai daga can ?an nesa da su ball chair ce daga gabanta ?an madaidaicin glass table ne.


nightstand ?in ta nufa ear phone ?in dake ajiye ta ?auka tare da eye mask,bed ?in ta dawo a kune ta sa ear phone ?in kafin ta rufe idonta da mask ?in, fa?awa tayi saman bed ?in ta ?aura kanta saman pillow tana saka ?aya tsakankanin cinyoyinta yayin da ta rungume ?aya a haka bacci yayi awan gaba da ita yayin da wa?ar data kunna a ear phone take ratsa ?wa?walwarta, Al'adarta ce bacci tana sauraron sauti.



_*ABUJA . NIGERIA*_


_*G J I ESTATE*_


momy da laatifa ne zaune saman sofa da alama fita za su yi,momy ta ?au wankan swiss lace maroon color ta yafa mayafi saman kanta, wayace kare a kunenta da alama waya take laatifa na daga gefenta zaune saman sofa mai mazaunin mutum ?aya ta ?au wankan black abaya tayi rolling da gyalenta simple make_up ne a fuskarta sai medical glass ?inta dake ?arama kyakyawar fuskarta kyau,wayar tace ri?e a hanunta tana aikin latsawa, janye wayar momy tayi daga kunenta tana ?an jan tsaki


"du kace zaka fita tare da Balqis sai ta ?ata maka lokaci,gaskiya tafiya zanyi na barku ni driver ya kaini idan ta gama shiriritar kun ta ho"

momy ta fa?a tana mi?ewa tsaye ta ?auki hand bag ?inta, tashi laatifa tayi itama tana ?aukar hand bag ?in ta "baza ki tafi ki barni ba momy, tare zamu tafi ita driver ya kaita

"gani nan bama sai an tafi an barni ba" Balqis ta fa?a yayin da take taka stairs case tana nufo parlorn, Abaya ce a jikinta tayi rolling gyalen kamar yanda laatifa tayi tana ri?e da hand bag a hannunta fuskarta tasha uban make_up ba ?aramin kyau tayi ba.



harara momy ta watsa mata tana nufar ?ofar fita daga parlorn, murmushi Balqis ta saki yayin da ta ?arasowa cikin parlorn, bin bayan momy su kayi,a parking space su ka sameta har ta bu?e back seat na wata ?akar Acura ta shiga,?arasowa su kayi laatifa ta shiga driver seat yayin da Balqis ta bu?e front seat kusa da laatifa ta shiga, babu ?ata lokaci laatifa tayi ma motar key ha?i da reverse, cikin Estate ?in su ka nufa tafiya su kayi mai ?an nisa, parking space ?in gidan dady su ka nufa, parking laatifa tayi ha?i da kashe motar, momy ta fara fitowa sannan sai Balqis, momy bata tsaya jiran su ba ta nufi main entrance ?in villa ?in,fitowa laatifa tayi a tare su ka jera zuwa entrance ?in a lokacin da su ka ?araso har ?ofar ta bu?e alamar an basu izinin shiga.


a tare su ka kutsa kai, babu kowa a parlorn sai jefi jefin ma'aikata dake kai kawo, gaishe da su su ka shiga yi cikin kulawa momy da laatifa su ka shiga amasawa yayin da Balqis ko kallon banza ba su isheta ba, glass elevator dake parlorn ta ?angaren mom su ka nufa,laatifa ta danna nombobin dake jikin elevator ?in,zugewa ?ofar tayi, momy ta fara shiga kafin su ka bi bayanta rufewa ?ofar tayi elevator tayi sama da su.


ba su samu kowa a main parlorn mom ba hakan yasa su ka nufi ?ayan parlorn,yumnah da fa'iza su ka samu zaune a parlorn kowacce ta tasa waya a gaba sai aikin latsawa take ba su jima da dawowa daga prison ba duba jikin mahaifiyar nainarh, bakin su ?auke da sallama su ka ?arasa ciki, ?agowa su kayi suna amsa masu sallamar da gudu yumnah ta taso ta nufi momy fa?awa tayi jikinta tana fa?in oyoyo, murmushi momy ta saki tana shafa bayanta.


"sannu da zuwa momy, ina wuni , yanzu mom ta shiga ciki"
"lafiya lau Alhmdllh ya hutu" da Alhmdllh yumnah ta amsa yayin da take raba jikin su gaishe da momy fa'iza tayi cikin kulawa momy ta amasa mata tana fa?in
"yan hutu, shine har yau banga ?afarku ba ko" sunnar dai fa'iza tayi tana sakin murmushi

yumnah da sauri ta nufi laatifa bu?e mata hannuwa laatifa tayi tana sakar mata murmushi da sauri ta ?arasa gabanta fa?awa tayi jikinta tana fa?in


"nayi missing ?inki sosai Aunty laatifa" murmushi laatifa tayi tana shafa bayanta
"nima nayi missing ?inki, ya hutu"
"hutu ya kusa ?arewa" yumnah ta fa?a yayin da suke raba jikin su, ta?e fuska Balqis tayi tana nufar ?ofar bedroom ?in mom yayin da take fa?in


"ni bari nayi ciki tunda babu wanda yayi missing ?in na dama banyi na mutum ba" dariya gaba ?ayan su ka saki saboda sun san bakomai yasa Balqis fa?in haka sai tsabar kishi saboda babu wanda yayi mata oyoyo



"Aunty Balqis ai ni mun ha?u a court shiyyasa ban yi maki oyoyo ba" yumnah ta fa?a, murmushi fa'iza ta tayi tana fa?in "ke nan dai wannan fa?an dani ake, to Allah ya huci zuciyarki ?ar uwa nayi kewarki ya ki ke"


ya mutse fuska Balqis tayi tana fa?in "lafiya" dariya gaba ?ayan su suka saki ganin yanda ta amsa bayan abun da take so kenan, girgiza kai momy tayi tana nufar sofa ta zauna, ?ofar bedroom ?in mom Balqis ta bu?e ta shiga,zama laatifa da Yumnah su kayi fa'iza itama zama tayi yayin da take gaishe da laatifa, cikin kulawa ta amsa mata, fira su ka shiga ta?awa.


Mom ce ta fito hannunta ri?e dana Balqis dake sakin murmushi, da sauri laatifa ta mi?e sakin hannun Balqis mom tayi tana bu?e ma laatifa hannuwanta alamar ta zo gareta, laatifa ba tayi ?asa a gwiwa ba ta ?arasa ga mom ?in, hugging ?inta tayi fukarta ?auke da murmushi
"mom ina wuni, mun same ku lafiya"


"lafiya lau agogo sarkin aiki" mom ta fa?a yayin da take raba jikin su, ?ata fuska laatifa tayi tana fa?in "mom kema haka za ki ce"


dariya Balqis tayi tana fa?in
"wallahi mom gaskiya ki ka fa?a Aunty laatifa bata saurarama aiki" momy na daga zaune,murmushi ta saki a ranta tana fa?in sarakai za ku fara
"ai ba sai kin fa?a ba Balqis na santa ne" mom ta fa?a


"shikenan mom tunda kema haka za kice" laatifa ta fa?a tana komawa mazauninta
"wasa nake maki laatifa ai aiki abu ne mai kyau" murmushi laatifa ta saki jin mom wasa take mata itafa babu abun da ta tsana sama da ace mata ta cika nacema aiki.


sofa da momy take zaune mom ta nufa, tashi momy tayi su kayi hugging ?in juna kafin su ka raba jikin su fuskokin su ?auke da murmushi, gaishe da juna su ka shiga yi cikin kulawa yayin da suke samun wurin zama su ka zauna,masu aiki fa'iza ta kira dan su kawo ma su momy abun sha ta hanyar landline ?in kitchen.


fira sosai su ka shiga yi a tsakaninsu momy na jajanta ma mom abun da ya faru da aminiyarta hajiya Asma'u,tambayar mom momy tayi ina ?iyar hajiya Asma'u take
"tunda mu ka dawo daga prison wajen mahaifiyarta ta shige ciki bata jin da?i,yumnah je ki kira man ita" mom ta fa?a, har yumnah ta mi?e fa'iza tayi saurin tashin tana fa?in "bari na kira ta"ta fa?a tana nufar corridor da zai sada ka da bedroom ?in yumnah, tura ?ofar bedroom ?in tayi ta shiga bakinta ?auke da sallama.


bedroom ?in yana da girma sosai, king size bed ne a cikin shi mai matu?ar kyau gefe da gefen shi nightstand ne mai ?auke da bedside lamps,daga saman headboard ?in bed ?in ?ar rumfa ce mai ha?e da sparkling bulbs,sai ?aton dressing mirror an cika gaban shi da body lotion da perfume masu dadda ?an ?amshi da tsadar gaske, tsakar ?akin shimfi?e yake rug carpet.


daga bakin sliding door glass balls chairs ne guda biyu suna kallon juna, daga wajen door ?in ?ar baranda ce mai ?auke da chairs guda biyu tsakiyar su round table ne daga nan kana iya hangen cikin estate ?in da swimming pool dake cikin garden ?in gidan.


A kwance fa'iza ta hangota saman makeken gadon ta rufe jikinta da duvet, bakin bed ?in fa'iza ta ?arasa pillow da take kwance ta ?an bubbuga tana kiran sunanta, a hankali ta shiga bu?e idanuwanta da su kayi mata ?auyi ga wani irin azabebben ciwo da kanta yake yi mata

"ki tashi mom na parlor tana kiran ki"pro khaki eyes ?inta ta sauke akan fuskar fa'iza da tayi maganar,eyes ?in sun ?anyi jajja jajja saboda baccin data fara ga ciwan kai.


A hankali ta tashi zaune hanunta dafe da kanta, matsawa fa'iza tayi tana bata hanya dan ta samu damar saukowa, a hankali ta zuro da fararen ?afafunta ?asa,rober gown ce a jikinta ,rigar ta kamata ta bayyanar da surar jikinta,kanta babu ?an kwali, water

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login