Showing 6001 words to 9000 words out of 67530 words

Chapter 3 - SHIRYAYYAR-ƘADDARA HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4363

daraja"

jinjina kai brisster hashim yayi yana fa?in "ita fa uwar ?akin taki, ya nata halayen su ke, bata da wasu ?abiu marasa kyau wanda baku jin da?in su???"

ran brisster zulaihat ne ya fara ?aci da irin tambayoyin da brisster hashim kema Aisha

"gaskiya babu"
"koda a ?oye bata da su?" ya sake mata tambayar, mi?ewa brisster zulaihat tayi rai a ?ace "objection my lord"

"sustained"Al?ali ya fa?a yana bata izini

"lawyer masu ?ara kamar yana son tursasa witness ?ina akan dole sai ta fa?i abun da bashi ba"

"brisster hashim ka kiyaye" jinjina kai brisster hashim yayi

"malam Aisha a ra'ayin ki ne ki ka tafi gida ko kuwa uwar ?akin kice ta nuna dacewar tafiyar ki a wannan lokacin?"

"Itace tace ya kamata na tafi na duba jikin shi , da tace man haka sai nace mata zan shirya ranar juma'a ko asabar naje amma sai tace na shirya gobe na tafi da farko na?i amincewa da tafiyar a washe garin nace kawai zan tura masu ku?in su fara amfani dashi kafin zuwa ranar juma'ar na tafi, amma sai ta zaunar dani ta nuna man dacewar na tafi a goben shine na amince"

"da tace ki tafi a lokacin ba kiyi wani tunani ba ko akwai dalilin da yasa tace kije?"

Mi?ewa brisster tayi tana ?an dukan table ?in dake gabanta "objection my lord"

"Overruled"Al?ali ya fa?a

komawa tayi ta zauna tana cizon yatsa na rashin bata dama da Al?ali yayi, side smile brisster hashim ya saki

amsar tambayar da brisster hashim yayi mata ta bashi

"banyi tunanin komai ba, saboda idan ahalina suna cikin matsala ta kan fini shiga damuwa akan halin da nake ciki,shiyyasa banyi zargin komai ba"

jinjina kai brisster yayi "mudi mai gadi ya sanar da koto cewa akwai wani matashin saurayi dake yawan zuwa wurin uwar ?akin na ki, baki ta?a tunanin mike kawoshi wajenta ba , ko miye ala?arta da shi ???"


"sunan sa Abid, ?an ?anwarta ne dake zaune a ?asar waje, yana yawan zuwa wurinta duk lokacin da yazo suna samu sa?ani da marigayi saboda kwata kwata jinin marigayi bai ha?u dana Abid ba, saboda Abid yaro ne mara tarbiya baya girmama na gaba da shi , gashi duk lokacin da yazo sai ya takura ma yarinyar su , hakan yasa marigayi baya son yana zuwa gidan, ita hajiya sai ta nuna ba taji da?i ba kan nuna kyara da tsangwama da yake akan yaron, a ranar da mu kayi magana kan tafiyata ya zo gidan har sa?ani ya shiga tsakanin shi da marigayi ya dake shi, abun yayi matu?ar ?ata ran hajiya har su ka samu sa?ani da marigayi, bayan mungama magana da ita naje ?akina na wanke kayan da zan tafi da su na zagaya baya zanyi shanya na hangesu ita da Abid suna tattauna wasu maganganu wanda ban san mi su ke tattaunawa ba, nayi ?o?arin naji abun da su ke fa?a amma abun ya gagara saboda tazara dake tsakanin mu,bayan na koma ?akina cikin dare naji Abid ?in yana waya a bayan ?akina kamar yana fa?ama wanda suke waya sa?anin da su ka samu da marigayi bana jin mi na ciki wayar ke fa?a masa na dai ji yana fa?in a cikin satinnan ya kamata suyi aiki a kanshi ko zai daina mashi shiga hanci da ?udindine, na tsorata da jin abun daya fa?a har na kasa bacci , washe gari tunda safe na samu hajiya da maganar amma sai ta nuna kar na damu da abokan kasuwancin shi yake waya"


tunda Aisha ta fara jera wannan jawabin gaban hajiya Asma'u ke fa?uwa bata ta?a sanin komai dake faruwa a gidan Aisha na sane ba sai yanzu.

"abokan ka suwanci, ko kin san wane irin ka suwanci yake?, sannan wane sa?ani ya shiga tsakanin shi da marigayi?"

"gaskiya ban san kasuwanci da yake ba, amma na ta?a jin labari a wurin mai gadi cewa yaron yana harkar kayan maye , kuma dukiyar da yake juyawa ta hajiya Asma'un ce "

jinjina kai brisster yayi
"wane sa?ani ne ya shiga tsakanin shi da marigayi?" ya sake maimaita mata tambayar
"gaskiya ban sani ba"

juyawa brisster hashim yayi ya kalli Al?ali "my lord , tun ranar da mai gadin gidan ya ba police duk wasu bayanai akan yaro suka tsaurara bincike sai dai kash bayan kwana biyu da fara binciken na su aka samu gawar shi yaron a cikin gidan shi anyi mashi kisa makamancin na marigayi,hakan na nufin hajiya Asma'u ta tura Aisha gida ne dan ta samu damar aiwatar da shirinta ba tare da wani ya ganota ba,sannan ta sallami ma'aikatan gidan dan kar su ga abunda zai faru,Abid ya ?i bata ha?in kai ne shiyyasa ta tura makasan da su ka kashe cp su ka kashe shi dan kar ya zame mata matsala"

"Objection my lord"
jinjina mata kai Al?ali yayi alamar amincewa

"my lord lawyer masu ?ara na son tabbatar da laifi akan wacce nake karewa ba tare da ?wararan hujjoji ba"
"brisster hashim ka kiyaye"
"tuba nake"

jinjina kai Al?ali yayi kafin ya ?auki pen ?in shi yayi ?an rubuce rubuce

"lawyer masu ?ara ko kana da sauran wasu tambayoyi da za kayi ma malam Aisha"

"su kenan tambayoyin da nake son yi mata" brisster hashim ya fa?a, tsaki brisster taja a zuciyarta tana fa?in
"ko ina amfanin wannan tambayoyin"

"lauyan wanda ake ?ara ko kina da wasu tambayoyi da za kiyi ma malam Aisha?"

mi?ewa brisster tayi "eh my lord" dama Al?ali ya bata, fitowa tayi brisster hashim kuma ya koma mazauninshi.

"malam Aisha a bayanan da hajiya Asma'u ta bada da kuma binciken da muka gudanar ya tabbatar mana da cewa kina a gidan a ranar da abun ya faru , hasalima kece ki ka fara sanar da su zuwa mugayen mutanen da su ka shigo gidan"

"wallahi brisster bana garin ita da kanta tace naje, munyi maganar da ita yau washe gari tunda safe na tafi"

murmushi gefen fuska brisster ta saki tana fa?in "?an uwan naki su su ka bada shedar cewa a ranar ba kije garin naku ba sai a washe garin ranar da abun ya faru"

shiru Aisha tayi ba tare da tace komai ba
"malama Aisha ke koto ke saurare?"
"ranar na tafi sai dai ban samu isa garin ba sai cikin dare,hakan yasa basu san da zuwa na ba sai washe gari"jinjina kai brisster tayi tana juyawa ta kalli Al?ali

"my lord malama Aisha ta sanar da koto cewa bata nan abun ya faru, a binciken dana gudanar ya tabbatar man da tana a cikin komai ya faru"

"binciken koto zai tabbatar da hakan, kina da sauran wasu tambayoyi da za kiyi mata"

"babu sauran wasu tambayoyi da zanyi mata"

"malam Aisha zaki iya komawa mazauninki kafin binciken koto ya kammala"
"godiya nake" ta fa?a tana ?an rissinar da kai,barin witness stand ?in tayi ta koma mazauninta ba tare da ta bari sun ha?a ido da brisster ba ko hajiya Asma'u.

brisster wurin zamanta ta koma itama,haka shari'ar ta cigaba da tafiya duk wasu jadawalin sunayen witness ( sheda) sai da Al?ali ya kira su gaban koto yana masu tambayoyi bayan ya kammala masu ya ba brisster's dama suma suyi masu nasu tambayoyi, ko wane sheda da kalar amsar da yake ba dawa a kan kisan marigayi CP,hajiya Asma'u tun tana sa ran ku?uta har ta sada?ata tasan bazata ta?a ku?uta ba daga yanayin amsoshin da shedun ke ba court,brisster ma gwiwowinta sun sage bata ta?a shari'a irin wannan ba tana shari'a akan kisa amma kuma bata ta?a rashin nasara ba amma wannan shari'ar na neman tafi ?arfinta , shedun da take ta?ama dasu gaba ?aya sun juya mata baya,duk wanda aka kira a cikin su abu ?aya su ke fa?i hajiya Asma'u ta kashe mijinta kuma suna bada ?wararan hujjoji wanda dole koto ta yarda .


brisster hashim kamar ya zuba ruwa a ?asa yasha yasan zaiyi wuya yau bai yi nasara akan brisster zulaihat ba abun da ya da?e yana jira kenan tsawan shekaru.

Magana Al?ali ya fara, tsit kotun tayi kowa na sauraron hukuncin da court zata yanke "binciken kotu ya tabbar da malam Aisha bata nan a ranar ashirin da ?aya ga watan biyar"

Ajiyar zuciya Aisha ta sauke tana dafe saitin zuciyarta, brisster wani mugun fa?uwa gabanta yayi hajiya Asma'u kuwa tuni hawaye sun taru a cikin idanunta

"bayan kammala ha?a duk wasu hujjoji da binciken koto dana likitocin dake kula da gawar marigayi CP ya tabbatar da hajiya Asma'u itce ta kashe CP" tunda Al?ali ya fara magana brisster hashim ke sakin murmushi, brisster zulaihat kuwa banda fa?uwa babu abun da gabanta ke yi.

"kotu ta yanke ma hajiya Asma'u hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da biyan tara ta naira milayan hamsin"

Wani irin murmushin farin ciki barisster Hashim ya saki yana kallon ?an uwan shi wanda hukuncin yayi masu dai dai,a ?ayan ?angaren kuwa barisster Zulaihart wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta tsinci kanta, da dama mutanen dake Court ?in abun yayi masu da?i yayin da wasu ke tausaya ma Hajiya Asma'un.

ana cikin jimamin hukuncin da court ?in ta yanke sai ga sa?o daga fadar shugaban ?asa na nemama Hajiya Asma'u sassaucin kotu daga rataya zuwa ?aurin rai da rai tare da biyan tara ta nera miliyan ?ari sa?anin hamshin.

Ran barisster hashim idan yayi dubu ya ?aci ba haka yaso ba yaso hukuncin kisa aka yanke mata ta hanyar rataya bai so ?aurin rai da rai ba amma idan ya tuna ba wai zata fito bane sai hankalishi ya kwanta, mom ta ?an ji sassauci da ba kisa bane ?aurin rai da rai ne sai dai idan ta tuna halin da hajiya Asma'u da nainarh za su shiga hankalinta na tashi.

wasu daga cikin mutane kwata kwata ba su so haka ba gani suke kamar wata ma?ar?ashiya ce ake ?ullawa.

Mi?ewa Al?ali yayi gaba ?aya su ka mi?e,?ofar office ?in shi ya nufa kamar jira a ke Al?ali ya fita koto ta ?auki haya niya kowa da abunda ke fitowa daga bakin shi,can compound ?in curt ?in kamar zai fashe saboda haya niyar mutane, mom tunda Al?ali ya fita ta kifa kanta saman desk ko motsin kirki ta kasa yi,matsowa wannan security guard ?in tayi tana bata ha?uri, mi?ewa brisster hashim yayi yana wani gyara zaman rigar shi fuskarshi ?auke da murmushin mugunta, ?aya bayan ?aya mutane su ka fara fita daga cikin kotun suna tofa albarkacin su.

hanyar fita prison officers suka nufa da hajiya Asma'u, da ?yar take taka ?afafuwanta suna zuwa tsakiyar court ?in ta yanke jiki ta fa?i a sume, salati mutanen da su ka rage a ciki su ka rabka da sauri mom ta mi?e kusan a tare su ka isa inda hajiya Asma'u ke yashe a ?asa ita da wasu mata guda biyu, amma kafin su ?araso ma'aikatan gidan yarin sunyi mata rumfa mom ka ?ai su ka bari ta ?arasa in da take, jijjigata ta shiga yi tana kiran sunanta amma ko gezau ba tayi ba, ?aya daga cikin prison officers ne ya mi?oma mom ruwa,a hannu ta zuba ruwan ta shafa mata a fuska, tayi hakan kusan sau ba adadi amma bata farfa?o ba mom bata san lokacin da ta fashe da wani matsanancin kuka ba,doctors ?in gidan yari ?aya daga cikin jami'an gidan yarin ya kira, ba'ayi five minutes ba sai gasu sun ?araso, nurses hu?u mata ne su ka kamata su ka ?aura saman stretcher,ficewa su kayi da ita daga cikin court ?in bayan su mom tabi tana goge hawayen dake zarya saman kumatunta, a hanzarce security guard ?inta tabi bayan ta har zuwa in da su kayi parking Ambulance,ganin fitowar mom ne yasa sauran security guard ?in nufota da sauri saboda mutane da ?an jarida da suka fara jefa mata tambayoyi harda na hauka, wasu ma a fakaice magana su ke gaya mata,bu?e Ambulance ?in ?aya daga cikin officers ?in yayi ciki su ka saka hajiya Asma'u,maganganu mutane ke jifa ma mom,tana jinsu amma tayi kamar bata jin mi suke cewa tana nan tsaye har sai da taga ficewar Ambulance ?in daga cikin court ?in tukun ta juya da nufin ta koma office ?inta, juwar da za tayi taga brisster hashim tsaye ya har?e hannuwa saman chest ?in shi, wani ?an iskan murmushi ya sakar mata yana tunkaro in da take tsaye, bashi hanya security guard ?inta su kayi da alama dai shima ba ?aramin mutum bane.

zuba mashi ido tayi har ya ?araso inda take, murmushi ya saki cikin wata irin murya kalar ta ?an duniya yace

"ya dai lawyer Al'ummah?, yau ina goyan bayan Al'ummar taki yake?"

?auke kai mom tayi wani ?ululun ba?in ciki na tokare mata ma?oshi, dariya brisster hashim ya saki
"see u next time" ya fa?a yana kashe mata ido ?aya, barin wurin mom tayi securitys ?inta su ka bi bayanta, da kallo brisster hashim ya bita har ta ?arasa inda su kayi parking motocin su,duk Abun da ke faruwa balqis na tsaye tana kallo,hawaye ne su ka taru a idonta ta rasa dalili rashin jituwar brisster hashim da mom, juyawa tayi ta nufi motocinsu ta shiga barin court ?in su kayi baki ?aya.


wannan lawyer ce ta nufo brisster hashim dake tsaye
"brisster na lura so ka ke ba?in ciki ya kashe brisster zulaihat a yau " ta fa?a tana sakin murmushi, martanin murmushi ya sakar mata yana
fa?in "yanzu ta fara gani in dai ni ne"

"Allah ya shirya ka, gaskiya baka kyautawa matar yayan ka ce fa"
"na tsaneta bana son ganinta" ya fa?a yana barin wajen, bin bayan shi lawyer tayi.

waya brisster ta ?auka tayi dialing number yumnah bugu ?aya tayi picking "ku fito ina parking space ku same ni" tana gama fa?a tayi rejecting ba tare da ta tsaya jin mi yumnah za tace.


mi?ewa yumnah tayi tana kallon nainarh data zuba uban tagumi, girgiza kai tayi tana nufar ta, dafa kafa?ar tayi firgigit nainarh tayi ta mi?e a tsorace har sai da gaban yumnah ya fa?in
"yumnah an gama shari'ar ne?" nainarh tajefa mata tambaya
"ban sani ba, amma dai mom tace mu sameta waje ban sani ba ko an gam...." tun kafin ta ?arasa nainarh ta nufi hanyar fita da sauri, bin bayanta yumnah tayi.


tana fitowa ?an jarida su ka yo mata caaa, sai jefa mata tambayoyi su ke marasa kan gado, ru?ewa tayi ta rasa in da zata dosa hawaye har sun fara zuba daga idanuwanta,ganin halin da take ciki ne yasa securitys ?in nufarta, zagayeta su kayi suna tutture ?an jaridar, in da mom ke tsaye tana jiran su suka nufa,maganganun mutane ne su ka fara ?aukar hankalinta da irin kallon da suke binta da shi

"itace ?iyarta ko kunya ba tajiba ta kashe ma yarinya ubanta saboda neman duniya kawai"

"ai hukuncin da kotu ta yanke mata bashi ya kamata da ita ba hukuncin kisa ne dai dai da ita"

"saboda brisster zulaihat yasa ba'a yanke mata hukuncin kisa ba, kasan suke da ?asar sai yanda su kayi da talaka" maganganun dake fitowa daga bakin mutane kenan, tunda ta fara sauraronsu gabanta ke fa?uwa.

bayan su yumnah ta biyo sai turo baki take kamar zata fashe da kuka,da sauri nainarh ta nufi mom hawaye na fita daga idanunta "mom ina ummah?" shine tambayar data jefa ma brisster, juyawa mom tayi ta shige motar ta ba tare da tace mata komai ba, motar da ke bayan wacce brisster ta shiga security guard ?in ya bu?e ma nainarh da nufin ta shiga, a masifance ta maida marfin ?ofar ta rufe tana juyawa zata nufi cikin court ?in, da sauri brisster ta fito tana fa?in "kar ku barta ta wuce"


umarnin mom su ka bi, duk yanda nainarh ta so shiga cikin court room ?in hanata security su kayi ?arshe data gaji zubewa tayi ?asa tana fashewa da wani matsanancin kuka,kamata mom tayi ta mi?ar da ita tana lallashinta su ka nufi mota, itama daurewa kawai take yumanh da yake saurin kuka ne gareta har ta fara matse ?walla abun tausayi, motar da su ka zo ita da nainarh ta shiga nainarh kuma a tare su ka shiga da brisster, kuka take kamar ranta zai fita tun brisster na daurewa har itama ta kaida zubar da ?walla, a tamanin security guard ?in su ka shiga motocin su, da gudun gaske su ka fice daga court ?in.



tun daga farkon shigowa anguwar zaka tabbatar da anguwa ce ta manyan mutane masu fa?a aji a cikin ?asa,manyan gine gine ne ta ko ina,tun daga nesa ?arar jiniyar motocin su ka cika anguwar,da wani irin matsiyacin gudu su ka shigo anguwar, mi?e titin su kayi shantal sai da su ka kusa kai ?arshen shi tukun suka karya kwana,tun daga farkon street ?in da su ka shigo check point ne na sojoji,kowanen su ?atuwar bindigace a hannunshi yayin da wasu ke soke a ?ugunansu, tun kafin motocin su ?araso sojojin dake zaune bakin ?an gate ?in da su ke sawa su ka bu?e masu, suna isowa babu jira suka wuce,tafiyar kusan minti goma sha biyar su kayi a ?alla sun wuce check point na sojoji da ?an sanda kusan guda goma kafin su ka kawo bakin wani ?atafaran gate,ba sojojin dake gadin gate ?in ba shi kanshi gate ?in abun kallo ne, wani irin zungureren gate ne ?aton gaske.


ga wasu irin manya manyan sojoji dake gadin shi, kwata kwata babu ?igon imani a fuskar su,sojojin dake zaune saman bench ne suka mi?e da sauri lokacin da motocin su ka ?araso bakin gate ?in,wani mahaukacin horn akayi da motar dake gaba da sauri wani soja ya danna wani abu dake hannunshi mai kama da remote nan take gate ?in ya shiga zugewa zuwa gefe ?aya,da gudun gaske suka danna kan hancin motocin zuwa ciki, masha Allah na furta a yayin da nayi ar?a da ?aton Castle ?in da su ka shigo,gidajene a cikin shi na alfarma hagu da dama a?alla za su kai kimanin guda hamsin kusan a jere suke sai dai akwai tazara mai ?an yawa a tsakanin ko wane gida, security guard ne ke yawo a cikin Castle ?in ta ko ina,babu abun da babu a ciki kama daga clinic ne sport center, garden babu abun da babu a ciki, duk wani abu na more rayuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login