Showing 30001 words to 33000 words out of 67530 words

Chapter 11 - SHIRYAYYAR-ƘADDARA HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4356

taji saukar belt, dukanta ya shiga yi kamar ya samu jaka.



kuka take tana ambaton "dan Allah ya zaabith kayi ha?uri, na tuba bazan sake ba" ko saurarenta baya yi dukanta kawai yake kamar an aiko shi,bai ?yaleta ba sai da ya tabbar ya sauya mata kammani tukun ya jefar da belta ?in ?asa,wuyan rigarta ya cakumo yana manne bakinshi da nata,kamar zai cire mata baki haka ya shiga kissing ?inta,cikin rashin imani ya shiga yayyaga suturar dake jikinta, doguwar sumar kanta ya jawo kamar zai cire mata ita yayi jefa da ita saman gadon babu tausayi ko imani ya shiga biyan bu?atar shi da ita, sai da ya tabbar ya kusa kasheta tukun ya ?yaleta ya mi?e,yana tanga?i ya nufi wata ?ofa wacce nake kyautata zaton toilet ne.


wani sabon kuka ta saki ta rasa wannan wace irin rayuwa take, ko baiwar da aka siyo ba'a wula?antata kamar yanda Zaabith ke mata kuma a haka wai ita ?in matarshi ce ta sunnah wacce su kayi Auren soyayya bana ?iyayya ba,wasu zafafan hawayen ne suka sake wanke mata fuska.



da jan jiki ta sauko daga saman bed ?in,blanket ?in dake shimfi?e taja ta rufe jikinta,a daddafe ta nufi ?ofar fita, ficewa tayi daga ?akin, a hankali take tafiya tana ?an waige waige gudun karta ha?u da wani ko masu aikin gidan su ganta a irin wannan yanayin, Allah ya taimaketa har ta kawo bakin ?ofar wani ?aki bata ha?u da kowa a hanyar ba, tura ?ofar ?akin tayi ta shige,mai da ?ofar tayi ta rufe da key,a jikin ?ofar tabar key ?in,yara ne ?an maza guda biyu kwance saman makeken bed ?in dake ?akin cikin shigar PJ white color, sai sharar baccin su suke hankali kwance.



?ofar toilet ta nufa, tsarkake jikinta tayi,sannan ta gasa jikinta da yayi mata tsami, bathrobe ta zura a jikinta ta fito,zuwa tayi tsakiyar yaran ta kwanta bayan ta kashe light ?in ?akin,hugging ?in yaran tayi ajikinta yayinda hawaye ke sintiri zuba daga idanunta, tsawan shekara goma kenan da yin Auren su,shekara ?aya kawai su kayi suna shan soyayya amma tun daga nan komai ya lalace kullum cikin fuskantar azaba take daga Zaabith duk wasu munanan halayenshi babu wanda bai nuna mata ba, ya fita gida sai sanda yaga dama zai dawo,idan ya koma wajen Aiki Lagos sai yayi wata da watanni bai dawo ba duk ranar da zai dawo a buge yake dawo mata kuma a ranar ta shiga uku, iyayenshi sunyi fa?a sunyi fa?an sunyin jan hankalin amma a banza,duk da fara tara iyali da su kayi bai sa ya canza halayen shi ba.



tayi tunanin zaman su a gidan gomnati zai sa ya canza ?abi'un shi kodan gudun zubar mutuncin mahaifin shi da siyasarshi a idon duniya,amma a banza saima abun da yaci gaba gashi duk wannan u?ubar da take ciki ta kasa sanar da iyayenta duk dan gudun lalacewar zumunci dake tsakanin su saboda mahaifin Zaabith yaya ne ga mahaifinta uban su ?aya.



ta jima tana sa?awa da kwancewa har baccin wahala yayi awan gaba da ita rungume da ?a?anta, lokacin da ya fito daga toilet ?in ?ugunshi ?ure da towel, kallon gadon daya barta a kwance yayi, ganin wayam bata nan me yasa shi jan wani mahaukacin tsaki yana fa?in "zan kamaki ne yarinya".


?ofar fita shima ya nufa, ficewa yayi daga ?akin zuwa master bedroom ?in shi, yana shiga ?akin a saman gadon shi ya fa?a rub da ciki babu Adu'a babu komai,cikin ?an?anin lokaci bacci yayi awan gaba dashi.


*WASHE GARI*


Tunda Asussu ba ta koma ?akinta ta gyara gudun masu aiki su ganshi haka bata son su zargi wani Abu,duk da irin azabar da take sha a wajen shi har kawo wannan lokaci tana son shi tana kuma yi mashi kallon uban ?a?anta, Adu'arta a kullum Allah yasa ya gane kuskuren da yake aikatawa.


shaf shaf ta gama kauda komai,toilet ta shiga wanka tayi ha?e da Alwala,fitowa tayi ta nufi cloth set ?in ta,doguwar rigar Abaya ta ?auko ta zura a jikinta,da ?yar ta zura rigar a jikinta saboda ciwukan da taji a dalilin dukan da yayi mata duk ya faffasa mata baya,sawun duka har saman wuyanta ga marin da yayi mata, ta san dole sawun hannunshi ya fito.


a saman kai ta ?aura mayafin Abayar tukun ta ?auko hijab,ficewa tayi daga ?akin dan ta san a kowane lokaci zai iya dawowa.



Bedroom ?in yaranta ta koma,a kwance ta same su kamar yanda ta barsu, tashin su ta shiga yi domin lokacin sallah yayi,?aya bayan ?aya su ka shiga toilet su ka ?auro Alwala,jallabiya ta ?auko masu cikin kayan su, cire PJ ?in dake jikin su suka yi suka zura jallabiya.


"momy Dady ya dawo ko??"fa?uwa gabanta yayi dalilin tambayar da yaron yayi mata.

"Eh ya dawo tare ma za ku tafi masallaci,yana ?akin shi kuje ku same shi"

"momy shine ya dake ki ko" fa?uwa gabanta ya sake yi
"shine ko momy??" yaran su ka sake jefa mata tambayar
saurin ?a?alo murmushi tayi tana girgiza masu kai alamar A'a

"shi ne mana momy,ga sawun duka nan a fuskar ki"

"fa?uwa nayi Ammar ba duka bane"
"duka ne mana,gashi nan sawun hannunshi ne a saman fuskar ki"

"momy mun gaji da dukan ki da dady yake,sai mun rama maki dukan da yake maki yaji shima idan da da?i,kuma sai mun sanar da grandfa har yanzu bai daina dukanki ba"

duk yanda take daurewa kasawa tayi hawaye ne su ka wanke fuskarta,tun tana ?oye masu yanzu yaran babu abunda ba su sani ba game da irin zaman iyayen na su.

hanyar fita su ka nufa suna sai sun fa?ama grandfa Aman har ya fara zubar da hawaye,da sauri tabi bayan su,jawo su tayi zuwa jikinta, hugging ?in su tayi.

"kuyi ha?uri Aman kar ku sanar da dady Ahmad,dadyn ku bada gangan ya mareni ba ya bani ha?uri bazai sake ba"

"momy kullum haka yake fa?a,amma har yau bai daina ba,kinga da gangan yake dukan ki"

"duk da haka Ammar shi ?in fa mahaifin ku ne,idan baku rufa mashi asiri ba waye zai rufa mashi,kuyi ha?uri kunji ko,ku yafe mashi nima na yafe mashi"

sake shigewa su kayi jikinta suna sakin kuka,wasu hawaye ne itama su ka wanke fuskarta,?an bubbuga bayan su ta shiga yi

"ya isa haka ku daina kuka kun ji,zai daina wata rana" raba jikin su ta yi,hannu tasa ta shiga goge masu hawayen fuskar su.

"kuje yana ?aki ku same shi" ma?e mata kafa?a su kayi
"mu dai tare da grandfa zamu tafi da su uncle Waseef"
"ki bar mu kawai momy muje tare da grandfa"


"shikenan sai kun dawo,Allah yayi maku Albarka"
da Ameen su ka amsa suna nufar ?ofar fita,turo ?ofar ?akin da a kayi ne ya dakatar da su,gaba ?ayan su suka kai dubansu gare shi.


farar jallabiya ce a jikinshi,jikin shi da alamar danshin ruwan da yayi alwala,cikin ?akin ya ?araso,hannuwan shi biyu ya bu?e ma yaran alamar su zo gareshi fuskar shi a sake.


tsuke fuska su kayi suna bin shi da wani irin kallon tsana,lamarin yayi matu?ar ?aure mashi,da sauri ya kai duban shi ga kainart dake tsaye tana kallon su,saurin kauda kai tayi kamar ma bata ga abun da su Ammar ?in su kayi mashi ba.


ta gefen shi su ka zo za su wuce,saurin kamo hannun su yayi,wayancewa yayi irin kamar ma bai fahimci mi yaran su ke nufi ba " fushi ku ke da dady saboda bai dawo da wuri ba,kuyi....." bai ?arasa ba saboda fisgewa da su kayi daga ri?on da yayi masu,?ofar fita su ka nufa ba tare da ko sun kalli inda yake ba,baki ya saki kamar saka rai wai yau shine su Aman su kayi ma haka,mi hakan ke nufi mahaifiyar su ta fara hure masu kunne ke nan.



yana nan tsaye har su ka ?acce ma ganin shi,jinjina kai yayi yana nufo in da take,da sauri ta ?auki hijab ?in ta zata zura a jikinta,a zafafe ya fisge hijab ?in yayi jifa da ita,dam?ara sumar kanta yayi,rintse ido tayi saboda zafin daya ziyarci kanta.


"wato raini ya fara shiga tsakanin mu ko,har kin fara tara yara kina gaya masu ina dukan ki ko,a tunaninki dan kin sanar da su hakan zai canza wani Abu ne,ki sani a duk fa?in duniyar nan babu wani wanda ya isa ya hanani abun da nayi niyya ko da kuwa mahaifina ne,dan na san shi ki ke tunanin zai iya hanani??"



cikin ?unar rai tace "a tunanin ka ya Zaabith su Ammar ba su san abun da ka ke aikatawa ba ne?,ko a tunaninka ba su da wayan sanin abun da kake aikatawa ,karka manta kasha dukana a gaban su dan mi baza su ji haushin ka ba,nifa mahaifiyar su ce"

fisgar kanta yayi kamar zai cire shi gaba ?aya "to sai mi dan sun sani,ke baki isa ki shiga tsakani na da su ba saboda ni ?in mahaifin su ne ko suna so ko basa so"



fashewa tayi da kuka
"kaji tsoron Allah ya Zaabith,ka sani alhakin mu bazai barka ba,Allah zai saka m..." tsawa ya daka mata

"ya isa haka" ya fa?a yana sakin gashin kanta,idan da abun da ke tada hankalinshi ta furta Allah zai saka mata baya son tana barin shi da Allah, yana tsoron ranar da Allah zai tashi saka mata.


?ofar fita ya nufa,da kallo ta bishi har ya fice hawaye sai sintiri suke a fuskarta.


hijab ?inta ta zura, prayer mat ta shinfi?a,gabatar da sallah ta shiga yi,ta jima zaune tana kai ku kanta ga Ubangiji sammai da ?assai.


Tana a nan kwance a kayi Nocking ?in ?akin, tambayar waye tayi ba tare da ta tashi ba.


"saraj ce dama madam Salima ce tace ki fito time ?in breakfast yayi,takuma ce anjima za ku je can family house ?in ku"
"bana jin da?i sarah,ki kawo man nawa breakfast ?in nan kawai"

"to shikenan,ya zance ma Madam ?in?"
"ki fa?a mata bana lafiya"
"to shikenan" mai aikin ta fa?a tana barin wajen,bayan kamar minti biyar mai aikin ta dawo.

iznin shiga Kainart ?in ta bata,a hankali ta turo ?ofar ?akin ta shigo hannunta ?auke da tryan data ha?a mata breakfast ,saman ?an table ?in dake ?akin ta ajiye mata.


"sannu madam,Allah ya baki lafiya"
"Ameen sarah,su Ammar na wajen dady ne?"
"eh suna can harda yalla?ai Zaabith"
"ok shikenan zaki iya tafiya"
"ok Allah ya ?aro sau?i" da Ameen kainart ?in ta amsa,ficewa mai aikin tayi.




* Big Daddy's house*



Mom da ya Naeem ne zaune a saman gondola chairs dake cikin garden ?in gidan,?an madaidaicin glass table ne a gaban su an cika masu shi da fresh fruit ha?e da snacks, yayin da mom ke ri?e da wasu takardu a hannunta sai jujjuyasu take,
kallonta ya Naeem yayi "mom kinyi shiru ba kice komai ba?"


?an sauke ajiyar zuciya tayi tana kallon ya naeem ?in daya kafeta da idanu,takardun dake hannunta ta mi?a mashi

"ban san ta in da zan fara maka bayani ba ne naeem"

"koma ta yayane ki fara mom Zan fahimce ki in sha Allah"

jinjina kai mom tayi "wani taimako nake so kayi mana game da case ?in Asma'u"

"umarni za kice mom,Dan kinfi ?arfin neman taimako a gare mu,mi kike bu?ata nayi maki a kan case ?in?"

"yawwa,ina so ka sake wani sabon bincike a kan case ?in bayan wanda jami'an tsaro su kayi"

"amma mom saboda mi?"
"naeem zuciyata ta kasa yarda cewa Aminiyata zata iya aikata wannan laifin ,duk da ?an Adam yana canzawa akan yanda ka san shi amma ita ina kyautata mata zato"

"shikenan mom in Sha Allah zanyi yanda ki ke so ,amma dole sai na samu wasu ?arin bayanan sama da wannan da ki ka bani"

"wanann ba damuwa bace,ko a wajen yarinyar ta zaka iya samun wasu baya nan,sannan akwai masu aikin gidan da masu gadi duk da sun bada bayanan su a court da wurin ?an sanda sai dai bayanan na su ban gamsu da su ba, ina ji a raina kamar sun ?oye wani ko wanda su ke da alhaki a kan kisan su suka hansu fa?ar gaskiya"

"shikenan ba damuwa mom ko da sun ?oye wani Abu nayi maki al?awarin sai sun magantu dole za su fa?i gaskiya"


"yawwa haka nake son ji,amma ina so ya zama sirri kai ka ?ai nake so kayi aikin sai wanda ka yarda da dashi daga cikin yaran ka wanda kasan bazai yaudareka ba"

"karki damu da wannan mom,komai zai tafi yanda ki ke so in sha Allah"

jinjina kai mom ?in tayi "bayanan komai yana a cikin takardun nan"


"zaka samu komai a ciki,tun daga tarihin rayuwar su, sunayen mutanen da suke mu'amula da CP lokacin da yana raye da ita kanta Asma'u da duk wani ma'aikacin su,hatta ?asashen da su ke yawan zuwa da garuruwa da wurare da su ka fi yawan zuwa a fa?in ?asar nan zaka samu, Naeem kar kayi sakace da su duk da na san ba halinka bane amma ka kula da su sosai akwai baya nan da ko Court bata san da zaman su ba na?i bayyanar da su ne a gabanta saboda wasu dalilai nawa, dan Allah ka maida hankali a kan su Naeem"


?an dariya ya Naeem yayi "dama na da?e ina zargin tsakanin ke da dady wa SAM ya gado naci da bin ?wa?wafi case Ashe ke ce?"

murmushi mom ta saki "bana son shashanci Naeem,wannan case ?in karka manta Aminiyata ce a ciki kaga kuwa dole na nace akan shi"

"haka ne in sha zan baje gaba ?aya ilimina akan wannan case ?in,zanyi ?o?arin ganin munyi nasarar fitar da momy in sha Allah"


"haka nake son ji,ka ko yi waya da SAM?"

"A'a,mun kwana biyu ba muyi waya ba,kin san ?an naki sarki ne sai ya sha iska yake neman mutane gashi ko ka kira shi a banza idan ba yana free ba shine zai ?aga ko idan yaga missed call ya kira"


"nima kwana biyu bai kirani ba,amma Alyar da James sun kira ni kuma sun shaida man yana lafiya,aiki ne yayi mashi yawa"


"nima Alyar ya kirani harma ya ke sanar dani suna nan zuwa ?arshen shekarar nan shi da James,na dai ce su lalla?a SAM ?in nima zan gwada sa'ata ko za'a samu wannan karan ya biyo su"


"duk lokacin da mu kayi waya dashi sai na ro?i Alfarmar ya taimaka ko kiran dadyn ku ne yayi a waya ko ya tura mashi message ko da bai zo ba amma ina,ba?ar zuciyar dana rasa awajen wa ya gadota ta?i barinshi,harda momy da Uncle Jonas nasha ha?ashi saboda yafi jin maganar su sama da tawa amma a banza sunyi sunyi ya?i, ko da picking call ?in dadyn ku ne yayi idan ya kirashi amma ina"

"in sha Allah mom wata rana da ?afarshi zai tako ya zo har ?asar nan saboda dady,komai zai wuce"

"bana tunanin SAM zai yafe ma dadyn ku,ya ri?eshi sosai a zuciyar shi,tsawan shekara 18 fa kenan"

"mom ki daina wannan tunanin in sha Allah zai yafe mashi wata rana,koda shekara 50 ne,ke da ma yayi ma laifin ki ka yi ha?uri bare shi SAM ?in,zai dawo da kanshi saboda dadyn in sha Allah"


"Allah yasa haka Naeem"
"in sha Allah mom,wata rana komai zai wuce har jikokin SAM ?inki za ki gani a gabanki dan na san burinku kenan ke da Dady"


murmushi ta saki "Allah yasa haka,da kuwa nayi farin ciki mara misaltuwa"
"Ameen mom,ni zan wuce gida"
"ok muje nima zan koma ciki" tashi su kayi, jerawa su kayi a tare su ka nufi ?ofar cikin gidan.


part ?in dady su ka nufa,a kishingi?e su ka same shi saman rug carpet yana duba wani littafin addini,bakin su ?auke da sallama su ka ?ara da ciki,?agowa dady yayi yana amsa masu sallamar.

kusa da shi ya Naeem ya zauna mom kuma ta zauna saman kujera
kallon su dady yayi fuskarshi a sake yace "uwa da ?a daga ina haka,wani abun da?in ya faru ne"


murmushi ya Naeem yayi "barka da hutawa dady"
"barka dai Naeem,ya Aiki yau ba ku shigo tare da Adnan ?in ba?"

"Eh kila sai anjima zai shigo"
"Allah ya kaimu anjimar lafiya,na shiga wurin Abbah ?azu yace kwana biyu bai saka a idon ba ina fatan dai lafiya?"


"Ayyuka ne su ka ?an yi man yawa kwana biyu shiyyasa ban shiga ba na bari sai ranar juma'a"

"duk da haka Naeem tunda har kana samun lokacin shigowa nan ai ka ?an le?a ku gaisha ko da da dare ne"

"in sha Allah daga nan zan shiga"
"yawwa hakan yayi,Allah yayi maku Albarka"
"Ameen dady" ya Naeem ?in ya fa?a yana mi?ewa,sallama yayi masu ya fice.



*Main Parlor*


da sauri yaja baya saboda karon da yayi da mutum,duban shi ya kai ga matashin saurayin dake tsaye a gaban shi sai layi yake kamar zai fa?on mashi,da tsantsar mamaki yake bin saurayin dake neman ya ra?a ta gefenshi ya wuce,a wani zafafe ya fisgoshi baya,saukar maruka matashin saurayin yaji a saman fuskar shi wanda su kayi sanadiyyar dawowar shi cikin hayyacin shi,da sauri yasa hannuwanshi ya dafe kumatunshi.


?an uwan shi dake bayan shi ganin irin marin da ya Naeem ya sauke ma ?an uwan nashi ne yasa shi komawa baya cikin san?a ya koma parking space ya shige motar da su ka zo,mai da ?ofar yayi ya rufe a hankali,shiru yayi yana baza ido a hanya ko zaiga wucewar ya naeem.


tun daga kan crazy short ?in dake jikin shi da ?ar iskar shirt ?in dake jikinshi mai kama da rariya zuwa ?an iskan askin dake kanshi ya Naeem ke kallo,ga wani chain dake manne a wuyan shi kunnenshi ?aya a huje yake ya saka ear ring.


wani marin ya Naeem ya sake kifa mashi,dafe kuncinshi yayi sai ga hawaye shar da alama marin ya shige shi sosai
"dan Allah second father kayi ha?uri,wallahi bangaka bane shiyyasa na bigeka" saurayin ya fa?a yana watso ido kamar tsohun kwarto a kan ya Naeem.

"daga gidan ubanwa kake haka?" ya naeem ya fa?a yana cakumo wuyan rigar shi

cikin rawar murya yace "wallahi daga islamiyya muke Ni da YAZDAN,yazdan dan Allah ba daga can muke ba" ya fa?a yana waigawa bayan shi wayam ya gani babu yazdan


"wallahi daga can muke" ya sake fa?a yana kallon ya naeem,dariya ma maganar tashi ta so ba ya naeem in ba ya ?auke shi ?an iska kamar shi ba taya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login