Showing 39001 words to 42000 words out of 67530 words
da part ?in shi,yayan dady ne?"
"granfa ?in mu ne, mahaifin su dady,duk ranar Friday gaba ?aya family ?in mu a can muke wuni,tundaga safe har dare a can muke lunch da dinner"
jinjina kai Nainarh tayi a lokacin da ?ofar ke bu?ewa, wani irin katafaren parlorn ne su ka shigo,launikan dake cikin parlorn Royal blue, light brown and white color ne, an ?awatashi da manya manyan sofas set biyu na gani na fa?a masu matu?ar taushi da da?in zama,sai throw pillows dake kan ko wace sofa, daga tsakiyar parlorn round glass table ne an jera flower vase masu matu?ar kyau, daga saman ceiling ?in wasu irin crystal chandeliers ne masu girman gaske , sai faskekiyar flat creen tv mai matu?ar girma sai kayan sauti dake gefe da gefen tv, sparkling floor lamps ne ajiye a ?asa suna bada haske mai launika daban daban, ga dogayen curtains zagaye da parlorn an zuge su,daga can bakin glass wall wanda daga nan kana iya hangen main entrance ?in shigowa part ?in daga compound ?in gidan,armchairs ne guda biyu ajiye daga tsakiyar su ?an madaidaicin glass table ne,idan ka kalli ?asan parlorn zaka ?auka mirror ne yanda yake ?aukar ido dan kana iya kallon kanka tsab.
Daga cikin parlorn kana iya hangen katafaren dinning room, wanda aka ?awatashi da ha?a?en dinning table,?yataccen glass table ne mai mazaunin mutum shidda,wasu ha?a?un chairs ne kewaye da table ?in,daga saman ceilling ?in dinning room ?in ?aton bulb ne ya haskaka ko ina na dinning room ?in,ga wata irin zungureriyar floor lamp.
cikin parlorn su ka ?arasa Yumnah na gaba yayinda Nainarh ke biye da ita tana ?arema parlorn kallo,tayi mamakin wannan part ?in wanene dan yafi ko wane part dake gidan ha?uwa da tsaruwa duk da ba ko ina na gidan ta sani ba,wayar landline dake ajiye cikin parlorn Yumnah ta nufa, number kitchen ta kira,daga can ?aya ?angaren a kayi picking call ?in.
"na bu?e part ?in ku nake jira" Yumnah ta fa?a tana rejecting ba tare da ta tsaya jin amsar da za'a bata ba,wata ?ofa Yumnah ta nufa ganin haka ne yasa Nainarh binta a baya,nan ma wani parlorn ne su ka shigo wanda yafi na farkon ha?uwa,komai na cikin shi blue White and gold color ne,glass door ne guda biyu a jere sai wasu corridor guda biyu dake hannu dama da hagu can ?an nesa da ?ofafin,wanda na hannun hagu ya kasance gym room ne ?ayan kuma wani part ne mai zaman kanshi.
?aya daga cikin ?ofofin dake jere Yumnah ta nufa tun kafin ta ?arasa ?ofar ta shiga zugewa da kanta,cikin ?akin ta kunna kai Nainarh na biye da ita a baya,wani irin ha?a?en bedroom ne su ka shigo komai na cikin shi black,white and gold color ne, bedroom ?in yana ?auke da Royal bed mai matu?ar ?aukar hankali,bed ?in a shimfi?e yake da tausassan bedsheet ga ?aton blanket mai gashi gashi a jikin shi,gefe da gefen gadon nightstand ne mai ?auke da bedside lamp,daga gaban gadon Ottoman table ne color ?aya da bed ?in,?asan ?akin shimfi?e yake da rug carpet mai taushi,wani irin ?ayataccen dressing mirror ne a cikin ?akin daga gaban shi stool ne mai taushin gaske.
cikin ?akin su ka ?arasa,dogayen curtains ?in dake a sake Yumnah ta shiga zugewa,kafin ta nufi wata ?ofa wacce nake kyautata zaton dressing room ne mai ha?e da bathroom, bu?e ?ofar tayi,shiga ciki tayi ta bar Nainarh nan tsaye tana ?arema bedroom ?in kallo ba?aramin tafiya yayi da ita ba duk da babu wasu kaya a cikin shi.
fitowa Yumnah tayi "gyaran ma bazai ?auki wani lokaci ba saboda babu datti da yawa" jinjina kai Nainarh tayi "eh gaskiya babu wani datti sosai"
"haka ne muje na duba sauran ?akunan kafin su Ishrat ?in su ?araso" da to Nainarh ta amsa mata,ficewa su kayi daga ?akin,?ofar dake kusa da wacce su ka fito su ka nufa itama ta glass ce kamar wacce su ka fito.
Nan ma wani bedroom ?in ne su ka shigo kusan duk abun da ke cikin wacan a kwaishe a nan banbancin color ne kawai shi wannan red and white color ne sa?anin wacan,mamaki gaba ?aya ya kashe Nainarh yanzu duk mutum ?aya keda wanann part ?in kuma ba zaune yake a ciki ba, zata so ganin wannan shalelen dady.
curtains ?in shi kawai Yumnah ta zuge ta duba dressing room da toilet Kamar dai yanda tayi a wacan bedroom ?in kafin su ka fice, corridor ?in dake hannun daman?ofofin su ka nufa,?ofofi ne guda biyu a wurin na glass daga in da su ke tsaye suna iya hangen komai dake ciki.
tura ?ofar su kayi su ka shiga ciki,wani irin azabebben parlorn ne su ka shigo wanda ya doke gaba ?aya falukan dake part ?in,yafi su komai nesa ba kusa furniture's ?in dake ciki ma kwata kwata ba irin tsarin su ?aya da wa?ancan ba,komi na cikin parlorn white color ne da ratsin gold,daga cikin parlorn kana iya hangen bedroom da swimming pool ?in dake part ?in ta hanyar glass wall dake mamaye da part ?in gaba ?aya.
bedroom ?in Yumnah ta nufa tana fa?in "gaskiya na fara kishi da shalelen dady" murmushin Nainarh ta saki tana biye da ita ba tare da tace mata ?alla ba sai raba ido take a parlorn kamar ba'a niger ba,kusan suman tsaye Nainarh da Yumnah su kayi a yayin da su kayi arba da makeken bedroom ?in da su ka shigo,ri?e ?ugu Yumnah tayi tana jinjina kai alamar mamaki tunda aka gina wannan sabon bata ta?a shigowa ba sai yau da dadyn yace su shiga a gyara,gaba ?aya bedroom ?in a mamaye yake da glass wall.
bedroom ?in yana da girma sosai dan tsab za'a iya gidan parlorn, bedroom, kitchen da toilet wadatattu a cikin shi,
wani irin makeken king size bed ne daga can ?an saman stape,a shimfi?e yake da bedsheet mai taushi gaske da blanket kafi mage taushi,gefe da gefen shi nightstand ne,bed ?in kusan rabi da kwatar shi a cike yake da pillows ?asan bed ?in na fitar da wani kalar haske,daga can gefen bed ?in sofa ce mai masifar kyau color ?aya da gadon itama ?asanta na fitar da haske kalar na bed ?in.
daga cikin ?akin kana iya hangen ha?a?en gym room dake can ?angaren hagu na ?akin,wasu irin expensive machines ne a cikin shi kamar a gym center,sai toilet da shima kana hangen komai dake cikin sa.
daga ?angaren dama sliding door ne wacce idan aka bu?e ta ?ar baranda ce,cuddler chairs ne guda biyu ajiye a wurin daga tsakiyar su round glass table ne ajiye.
jinjina kai Yumnah ta shiga yi tsarin part ?in ba ?aramin tafiya yayi da ita ba,wayar dake hannunta ta dannan, video ta shiga ?aukar part ?in,tundaga parlor har zuwa wannan yar barandar,babu in da bata ?auka ba har toilet tukun su ka fice daga part ?in su ka koma parlorn na biyu da su ka shigo.
tsaf tsaf yake part ?in saboda yawan gyarawa da ake duk da ba mai zama,?aya daga cikin sofas ?in su ka nufa su ka zauna,daga cikin parlorn suna hange parlorn da su ka fara shigowa ta hanyar glass wall dake mamaye da parlorn.
basu jima da zama ba Ishrat ta shigo tare da wasu masu aiki su biyar ha?i da ita su shidda kenan hannunsu ?auke da mop da tsintsiya da detergent,in da su Nainarh su ke suka ?araso,cikin girmamawa su ka gaishe da su,amsa masu su kayi Yumnah na fa?in "yawwa Ishrat sai kun mai da hankali,ki fara nuna masu in da za'a fara gyarawa,yau har sabon part ?in dady yace a gyara"
gya?a mata kai Ishrat ?in tayi,kasa masu aikin tayi gida biyu,biyu tace su gyara bedrooms da gym room,biyu kuma su gyara parlors ?in da dinning room da kitchens,ita da ?ayar kuma su ka nufi part ?in da su Yumnah su ka fito.
babu ?ata lokaci masu aikin su ka shiga gyaran ko ina a cikin gidan,main parlorn part ?in Yumnah da Nainarh su ka nufa, sliding door dake wurin su ka bu?e suka fita ?ar barandar dake wajen,a saman chairs ?in dake wurin su ka zauna,daga nan in da su ke suna hangen main entrance ?in shigowa part ?in da compound ?in gidan,suna iya hangen katafaren parking space dake wajen,rides ne da yawa a ciki an lullu?e su da alama an ajiye su ne kawai.
Kasa ha?uri Nainarh tayi har sai da ta tambayi Yumnah
"wai nan part ?in waye?,naji kina fa?in shalelen dady dama ba ke bace Auta ba,dady na da wani ?aramin ?a bayan ke?"
kallon Nainarh da tayi maganar Yumnah tayi tana sakin dariya
"wai dan kinji ina fa?in shalelen dady?,dady baya da wani ?aramin ?a ko ?a bayan ni,ni ce Autar sa"
"ok,amma nan part ?in waye,mi yasa ki ke ce masa shalelen dady??"
"part ?in ya SAM ne shi ne yaron dady na uku,daga ya Naeem sai ya Adnan sai ya SAM sai ya Irfan sai Aunty Fa'iza sai ya Fa'iz sai Yumnah Auta"
yumnah ta fa?a tana sakin murmushi, murmushi itama Nainarh tayi tana fa?in
"masha Allah,Allah ya Albarkace ku ya rayama dady ku" da Ameen Yumnah ta amsa tana fa?in
"tsawan shekara 18 kenan ya SAM baya ?asar,tun ina ?ar shekara 2 da haihuwa ya koma US wajen granny da zama"
"ikon Allah,yanzu zuwa zaiyi ne yasa dady yace a gyara part ?in?" girgiza mata kai Yumnah tayi
"babu wanda ya san ranar da zai zo,tunda ya tafi bai sake dawowa ba,kawai dai dady yana sa a gyara part ?in ne duk ranar friday"
"sorry kar kice na cika shiga abun da ba ruwana,amma miyasa ya tafi tsawan wannan shekarun bai dawo ba??"
murmushi Yumnah ta saki "nima ban sani ba,kawai dai na taso naga baya gidan kuma bai ta?a zuwa ba"
jinjina kai kawai Nainarh tayi ba tare da ta sake cewa komai na,amma lamarin ya bata mamaki wane irin ?a ne zaiyi nesa da iyayen shi tsawan wa?annan shekaru ba tare da ya waiwaye su ba,haka nan taji tana son sanin dalilin barin shi gida da rashin waiwayar iyayen shi tsawan wanann shekarun,wani ?angare na zuciyarta na garga?arta da shiga abun da babu ruwanta, Yumnah ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar fa?in
"next week fa muke komawa school,ni wallahi duk na ?agara next week ?in tayi dan na gaji da zaman gida"
yanayin fuskar Nainarh ne ya canza da alama ba tayi farin cikin da labarin komawar ta su makaranta ba
"ya dai,baki son komawa ne?" Yumnah ta fa?a tana tsareta da idanu, girgiza mata kai kawai Nainarh tayi ba tare da tace ?ala ba,itama Yumnah bata sake cemata komai ba dan ta san dalilinta na?i son a koma,amma ya za tayi dole tayi ha?uri ta koma komi ?an school ?in su za su ce.
*ASO VILLA*
Gaba ?aya a halin gidan sun hallara a katafaren dinning room dake villa ?in domin breakfast, Zaabith na zaune saman chair dake kallon wacce su Ammar ke zaune,sai Irfan da Waseef dake zaune kusa da juna,sun du?ar da kai,magana su ke ?asa ?asa idan ba kana kusa da su sosai ba ba zaka iya jin mi su ke cewa ba.
kallo Zaabith dake cikin abinci hankali kwance hajiya salima tayi
"lafiya ka fito kai ka?ai,ina kainart ?in take,ko har yanzu jikin ne??" da sauri ya ?ago yana kallon mahaifiyar tashi da tayi magana.
"zata fito,ta tsaya wani abun ne ciki" Zaabith ?in ya fa?a yan maida kanshi ga abincin da yake ci,wani ?an iskan kallo Ammar da Aman su ka watsa mashi ba tare da wani ya lura da su ba.
jinjina kai hajiya salima tayi tana kai dubanta ga sarah dake tsaye
"maza ki kira man ita sarah" da to sarah ta amsa tana juyawa tabar wajen zuwa part ?in Zaabith.
bayan kamar minti biyar sarah ta dawo "lafiya, tana ina??" hajiya salima ta fa?a tana kallon bayan sarah ganinta ita ka?ai
"gata nan fitowa ranki ya da?e"jinjina kai hajiya salima tayi
tunda ta tunkaro dinning room ?in ya kafeta da ido,da yake chair ?in da yake zaune tana fuskantar ?ofar shigowa dinning room ?in,ba?ar jallabiya ce a jikinta ta lullu?a mayafinta ta rufe rabin fuskarta da har yanzu sawun hannunshi na nan ra?au kamar yanzu ne ya mareta.
wani irin kallo ya shiga jifanta dashi wanda ita ka?ai ta san ma'anar shi,saurin kauda kai tayi kamar bata ganshi ba, murmushi hajiya salima ta saki lokacin da kainart ?in ta ?araso ciki.
da sauri Zaabith ?in ya mi?e yana ja mata kujerar dake kusa da shi,alama yayi mata data zauna yana sakar mata wani soft smile,?auke kai tayi kamar bata ga abun da yake nufi ba ta nufi inda su Ammar suke,tashi Aman yayi ya koma kujerar dake kusa da wacce ya tashi,murmushi ta saki tana shafa kanshi,zama tayi a tsakiyar su.
"ina kwana momy,kin tashi lafiya"
"lafiya lau Alhmdllh, kainart ya ?arin ?arfin jikin" da Alhmdllh ta amsa mata,da sauri sarah ta ?araso in da kainart ?in take tayi serving ?inta.
har time Zaabith na tsaye mamaki ne duk ya cika shi,kallon shi momy tayi "kai kuma lafiya kayi ma mutane tsaye a ka??"
"bakomai" shine kawai abun da yace ya koma mazaunin shi ya zauna.
"ashe baki jin da?i Aunty kainart?" waseef ya fa?a yana kai duban shi gareta
"naji sau?i waseef"
"Allah ya ?ara sau?i,amma shine baki ce na zo na dubaki ba" Irfan ya fa?a yana wani ya mutse fuska.
?an zaro ido tayi "irfan nace ka dubani,rufa man asiri in ka ganni lahira kaini a kayi" dariya Irfan ?in ya saki kamar ba shi ba
"nafa manta tsoron Allura ki ke"
dariya waseef ya kwashe da ita har da su Ammar
"gaskiya Aunty ya kamata ki rage wannan tsoron,akwai fa su Ammar a gabanki,amma kiyita abu sai kace farar kura" a cewar waseef.
jifar shi tayi da spoon ?in dake hannunta saurin du?ewa waseef yayi,hakan da yayi ba ?aramin dariya ya ba su,zuba masu ido kawai Zaabith yayi yana kallon su.
gyaran murya su kaji daga bakin ?ofar shigowa dinning ?in saurin kai duban su ga magidancin dake tsaye cikin shigar Jogging suit launin blue black,a tsarin hallita dogo ne,launin fatar jikinshi fara ce ba irin sosai ?in nan ba,sumar kanshi da gemun shi farare ne tas da alama rina launinsu yayi ba dan ya kai shekarun da za su koma haka ba,kunnen shi a manne yake da ear phone haka kyakkyawar fuskar shi a manne take ba?in glass.
Uncle Ahmad kenan, mahaifin Zaabith,Aunty Nadiya da Waseef,daga dady sai shi,shine President ?in Nigeria na wannan lokaci.
da gudu Ammar da Aman su ka nufe shi saurin zame glass ?in dake fuskar shi yayi ya tura shi a aljihun wando shi,fa?awa jikin shi su kayi suna mashi oyoyo, murmushi ya saki yana shafa sumar kansu,hannun su ya kama su ka ?arasa cikin dinning room ?in
"granfa shine yau ka fita ba tare da mu ba?" a cewar Aman
"bacci ku ke ne time ?in,amma gobe idan zan fita tare da ku zan fita"
"gobe ai muna gidan big daddy tare da shi zamu fita"
"au haka ne?"
eh su ka bashi amsa,jinjina kai grandfa ?in yayi
"shikenan idan kun dawo sai mu fita tare" ihun murna su ka saki suna koma mazaunin su.
gaishe dashi su Zaabith su ka shiga yi yana amsa masu cikin kulawa,sarah dake tsaye ma gaishe dashi tayi yayin da take matsowa domin tayi serving ?in shi,da katar da ita hajiya salima tayi ,da kanta ta shiga serving ?in shi.
"good morning" ta furta dai dai kunnen shi,kashe mata ido ?aya yayi yana sakar mata murmushi, mazaunin ta dake kusa da nashi ta koma ta zauna tana sakin murmushi.
kallon Zaabith dady yayi
"zaabith ka kuwa ha?u da Muhsin??"
"A'a dady,ya dai kirani jiya yace yau su ke sa ran isowar su Mubarak"
"kai yaushe za ka tafi can kenan?"
"?arfe ?aya su ke sa ran isowa,sai na tafi after Isha" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar kainart jin yau zai koma
"good" kawai dadyn yace ba tare da ya sake cewa komai ba,kallon Zaabith momy tayi
"yau zaka koma ne?"
"A'a,sai next week" ya bata amsa, kainart ba hakan ta so ba ta so ace tafiya zaiyi ko ta samu ta huta da u?ubar shi.
Dady da Zaabith ?in su ka fara tashi sai Irfan da Waseef,tashi kainart tayi itama ta fice aka bar momy da su Ammar.
*Big Daddy's house*
wajen awa biyu su ka ?ata wurin gyaran part ?in, gyara su kayi mashi na musamman ko ina ka shiga sai tashin ?amshi yake ha?e da sanyin AC.
"sannunku da ?o?ari Ishrat,wannan idan dady ya gani dole ya baku tukwici" murmushi kawai Ishrat ?in ta saki
"ai ina jin ku saki curtains ?in kawai a kashe bulbs,tunda an kammal"
da to su ka amsa mata suna nufar bedrooms da falukan dan ciki umarninta,duk wani kayan wuta da su ka san sun kunna sai da su ka kashe shi hatta AC ba su bari a kunne ba,kayan da su kayi amfani da su suka kwashe,ficewa su kayi daga part ?in bayan sun kammala.
?ofofin bedrooms ?in Yumnah ta rufe tukun suma su ka fice, direct part ?in dady ta nufa Nainarh kuma ta nufi bedroom ?in su,bata samu dady a part ?in ba har ya fice,key's ?in kawai ta ajiye ta fice.
A zaune ta samu Nainarh bakin bed,da kallon mamaki ta bita
"yanzu Nainarh maimakon ki shiga kiyi wanka sai ki zauna,ni ban san mi yasa ki ke haka ba komai sai nace kiyi sai kace wata ?aramar yarinya?"
"ba haka bane,naga ke sauri ki ke saboda fitar da za kuyi ,shine na bari idan kin fito sai na shiga"
wani ?an iskan kallo Yumnah ta watsa mata "mi ki ke nufi da fitar da za muyi,kina nufin ban da ke??"
"ha?uwa fa za kuyi da family ku ni miye nawa na zuwa"
"gaskiya Nainarh bana jin da?in irin wanann abun,ni kawai ki tashi ki shiga wanka karma su mom su shirya su fara jiran mu"
"yumnah gaskiya ni bazan je ba,taro ne na familyn ku, taya za ayi naje"
"wallahi sai kin shirya mun tafi kin ma ji na rantse,kullum naita fama dake kamar wata yarinyar goye" Yumnah ta fa?a tana nufar dressing room ?in ta.
tashi Nainarh tayi ta shiga wanka ta so Yumnah ta ?yaleta dan bata san wane irin kallo family ?in su za suyi mata ba ganin ta shigo cikin su,ba