Showing 48001 words to 51000 words out of 67530 words

Chapter 17 - SHIRYAYYAR-ƘADDARA HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4368

su ka fara shigowa hall ?in,Mama Ameenah ce a gaba yayinda su mamy ke biye da ita a baya,sai da su ka gama shigowa mom da mom maryam da mom Maimunatu su ka shigo bayan sun shigo ne yaran su ka fara shigowa.


Su Yumnah ne su ka shigo hannunta ri?e da hannun Ammar da Aman yayinda da Jamal ya ma?al?ale hannun Nainarh sai turo baki yake shi adole fushi yake yumnah bata ri?e hannunshi ba.

?aya bayan ?aya su ka shiga shigowa, kowannan su ya shigo wajen zama yake nema ya zauna, table ?in da su dady ke zaune su mom su ka zauna, kowaccen su na fuskantar mijinta yayinda mamy da su hajiya fatilah su ka cure waje ?aya su da Mama Ameenah bako ta mazajen na su suke ba, sai hura hanci su ke sunama mutane kallon tara saura kwata.

?ayan Table ?in su Yumnah su ka zauna da sauran jikokin Abbah, a tare Abbah da Uncle Ahmad da Uncle Mustafa su ka shigo, suma wajen zama su ka nema su ka zauna,saida kowa ya gama samun wurin zama ya zauna tukun chefs su ka shiga serving ?in su, cika masu gaban su su kayi da Abinci kala kala na Alfarma.


tunda su ka shigo Aunty Safeenah ta kafe mom Maryam da kallo,wani irin kallon mamaki take binta dashi,tsaki taja tana kallon mama Ameenah


"dan Allah mama dubeta,sai wani hura hanci take kamar wani ta fi,mai Abun duniyar ma ba tayi ?afafa ba sai ita"

"ai ni wallahi lamarin Maryam mamaki yake bani,wai ni baku lura da ita ba yanzu tafi ?arfin zuwa ta gaishe da mama bare mu data gama rainawa mu samu arzi?in da za tayi mana magana" A cewar hajiya halima


"rabu da ita kawai zanyi maganinta ne"acewar mama Ameenah



firarsu su ka shigayi wacce banda zagin su mom ba abunda su ke, Hajiya Salima na cikin su amma kwata kwata bata saka masu baki ba haka mamy ma tunda ta zauna hankalinta na can wani waje daban,bamata san akan mi su ke magana ba,ta ?urama waje ?aya ido,suma da su ka gaji shiru su kayi hall ?in yayi tsit banda ?arar spoon da plate baka jin komai.



Noor tunda ta zauna dinning ?in Banda juya spoon babu abunda take gaba ?aya ta kasa cin abincin saboda rashin shi a kusa da ita duk tabi ta damu,kallonta laatifa dake kusa da ita tayi.


"lafiya dai ko Noor?" murmushin ya?e ta sakar mata tana fa?in lafiya.
"mi yasa baki cin abincin,ko dai wannan baiyi maki ba chefs su canza maki wani??"


girgiza mata kai Noor ?in tayi
"A'a, bana jin da?i ne "
"Ayyah!,sannu mike damunki?"
"jikina nake ji babu da?i" ta bata amsa, murmushi Kairiyyah ta saki dan ta san ba komai yasa noor fa?in haka ba sai dan saboda Irfan.



Ringing ?in wayar laatifa ne yaja hankalin mutane da dama dake hall ?in har da dadyn ta,wani kallo ya shiga watsa mata,kwata kwata bata lura da irin kallon da yake mata ba, ganin sunan mai kiranta nata ne ya sata saurin mi?ewa daga saman chair ?in da take zaune,?ofar fita daga hall ?in ta nufa yayinda take picking call ?in.


a bakin ?ofar shiga hall ta tsaya tana amsa wayar
"hello sister,kamar kin san duk ina nan na damu da rashin zuwanki" laatifa ta fa?a,on the other hand ta cikin wayar tace

"bana jin da?i ne ?ar uwa shiyyasa ban zo ba"
"subhanallah! mike damunki naji ma muryarki wani iri, fatan dai ba wani abun ba ne ya sake faruwa ba dan naga ya Zaabith na gari"
"please sister ki zo idan babu abun da ki ke"


"wai mike faruwa ne,duk kin sa hankalina ya tashi"
"babu komai ki zo dai Please"
"ok gani nan zuwa"
"sai kinzo" rejecting call ?in tayi,hanyar fita daga garden ?in ta nufa ba tare da ta koma cikin hall ?in ba,daga inda dadynta yake cikin hall ?in yana hangen ficewar ta.



mi?ewa yayi ya fito daga hall ?in,bayanta yabi, parking space ?in gidan ya nufa,yana isa motar ta na ficewa daga parking space ?in,wayar shi ya zaro daga cikin Aljihu yayi dialing wata number, bugu biyu a kayi picking.


"gata nan ta fito ina son kutabbatar da in da taje" on the other hand wata irin kakkausar Muryar ce mara da?in jin ta daki dodon kunnenshi
"angama ranka ya da?e" rejecting call ?in yayi ba tare da yace komai ba.



yana a nan tsaye kamar daga sama yaji anyi hugging ?in shi ta baya tightly, murmushi gefen fuska ya saki ba tare da ya juya ba dan ya san bazai wuce ita ba ce dan babu mai mashi irin wannan rungumar idan ba ita ba.


"ai nayi tunanin sai na kira ki zaki fito?" ya fa?a cikin wani irin yanayi kamar ba barisster ba
"ni na isa, kawai jiran damar da zan fice nake ba tare da wani ya lura da ni ba"


ta?e baki yayi yana fa?in "fushi nake dake,yau wajen kwana nawa da al?awarina amma baki ciki ba"

"kafi kowa sanin halin yayanka kwata kwata baya bani damar da zan matsa daga gidan,yanzu ina sa ?afa na fita zaisa abi masa diddi?in in da na tafi,kuma nasha fa?a maka ka ri?a zuwa gidan babu mahalu?i da ya isa ya zargeka akan zuwa gidan yayanka,kuma har ka gama abun da ya kawoka ka fice ba tare da ya san ka zo ba.



hannunshi yasa ya jawo hannunta ta dawo gaban shi, ?are mata kallo ya shiga yi tun daga sama har ?asa kafin ya tsaida lumsassun idanunshi a kanta, wani irin shai?anin kallo ya shiga binta da shi,ba ita da yakema kallon ba hatta ni dake la?e sai da naji kunyar irin kallon da yake mata.



kasa jure kallon da yake mata tayi,tafin hannunta tasa ta rufe idanuwan shi
"barisster irin wannan kallo haka, sai ka sa gaban ya fa?i" murmushi ya saki yana janye hannunta daga idanunshi,baki ta bu?e da nufin yin magana amma yayi saurin manne bakinshi da nata.


*Tashin sense Barisster Hashim,mamy ????????*


Zagayo da hannayenshi yayi ya ri?e ?igunta,itama ?an?ameshi tayi kamar za su koma abu guda,a ?alla sun shafe tsawan five minutes a haka kafin ya raba jikin su,jan hannunta yayi su ka nufi ?aya daga cikin motocin dake parking space ?in,front seat ya bu?e mata ta shiga,zagayawa yayi ya shiga driver seate,Key yayi ma motar su ka nufi cikin estate ?in.



*ASO VILLA*



Bata sha wata wahala ba wajen shiga, saboda ita ?in sannance a idanun securitys ?in kuma bayan haka sun san ala?arta da mazauna gidan.



A katafaren parking space ?in Villa ?in tayi parking, kusan a tare su ka fito da wani matashin ba indiye dake zaune a cikin motar shi,bai jima da parking ba tayi parking.



in da take ya nufo hannunshi ?auke da briefcase, fuskarshi ?auke da fara'a ya ?araso,murmushi itama ta sakar mashi.

"Dr fawar dama kana ?asar?" ta fa?a da almun mamakin ganinshi, murmushi ya sakar mata cikin hausar shi da bata gama daidaita ba yace
"ina za ni, Ina nan hajiya laatifa, dama yaran irin mu na ganin ku?"


dariya ta fashe da ita wacce ta ?ara fito da ainihin kyawun fuskarta "da?ina da kai zolaya fawar, in da ka so gani na ai ka san in da zaka same ni"
"kina son dadyn ki yayi ?arata kenan?" ya fa?a,dariya kawai laatifa tayi ba tare da tace komai ba.


juyawa su kayi da nufin barin wajen zuwa ciki, horn ?in da a kayi a bayan su ne ya dakatar da su,parking space ?in matu?in motar ya nufo, parking yayi, zuba ma motar ido su kayi dan ganin wanda zai fito.



Irfan ya fito,da sauri ya nufo su yana fa?in "sorry Dr, na san na ?ata maka lokaci" ?an hararar shi dr fawar ?in yayi
"haba Irfan ka san yanda tsarin gidan nan naku yake amma ka barni a tsaye a bakin gate da ba dan nayi hausar kiran Zaabith ba da tuni ina can rana na duka na"



"sorry na tsaya amsar wani sa?o ne, muje ko, Aunty Laatifa ina wuni"

"lafiya lau Irfan, kwana biyu" da Alhmdllh ya amsa mata yayinda su ke shiga cikin gidan,babu kowa sai masu aiki dake kai komo, direct part ?in Zaabith su ka nufa, parlorn su tsit yake babu kowa sai masu aiki dake ?an hidindimun su, gaishe da su masu aikin su kayi, a saman sofa fawar da Irfan su ka zauna yayinda laatifa ta nufi bedroom ?in Kainart.



bakinta ?auke da sallama ta tura ?ofar ta shiga tana ambaton "my own sis gani na ?a..."
dakatawa tayi da maganar ganinta a kwance saman bed harda su rufa,?arasawa tayi bakin bed ?in.


"Kainart lafiya?" ta fa?a tana ?an yaye blanket ?in data rufa,tashi tayi zaune ta jingina da head board ?in gadon.


wani irin mummunan fa?uwa gaban laatifa yayi ganin sawun duka a saman neck ?inta gana mari da har yayi ba?i saboda hasken fatar ta.


"kainart mi ya same ki haka, kardai kice har yanzu ya Zaabith bai daina dukanki ba??" Laatifa ta fa?a da tsantsar damuwa
"har yau Laatifa ya Zaabith ya?i ya canza halinshi"
"kainart idan har da laifin ya Zaabith naki yafi yawa, ni banga amfanin zaman nan da kike da shi ba, mutuminnan baya sonki amma ke har yau kin kasa ganewa, so ki ke ki salwantar da rayuwarki a banza?" Laatifa ta fa?a ranta a ?ace.



"bazaki gane bane Laatifa"
"dama taya zan gane tunda soyayya ta rufe maki ido har kina shirin salwantar da rayuwarki a banza, wallahi Kainart ko ni da nake fuskantar tsangwama daga dady gara ni dake, duk ranar da Allah ya bani miji mai sona nayi Aure shikenan, amma ke fa?, karki manta zaman Aure ba zama ne na ?an lokaci ba zama ne na har abada, kuma tuda har ya Zaabith bai sonki ko kun ?au tsawan shekaru tare ba ganin mutuncinki zaiyi ba, gara tun wuri kisan Abun da ya dace??"



"ina sonshi ne Laatifa shima yana sona bazaki gane ba, kuma idan na barshi ya ki ke so nayi da su Ammar?"

"matsalar ki kenan soyayya,wlh ya Zaabith baya sonki da yana sonki bazai ri?a wula?antaki ba, sannan su Ammar da ki ke magana, karki manta ko babu Aure tsakaninki da ya Zaabith zai iya ri?e abun da ki ka haife barema ?a?an sa ne, kuma kin san cewa duk tashin hankalin da za'ayi dady bazai ta?a bari a rabaki da su ba hakama Abbah, ki nemama kanki mafita Kainart,ba kiga yanda ki ka koma ba kamar ba ke ba duk kinbi kin lalace"


"wace mafita zan nema Laatifa?" ta fa?a da alamun son ?arin bayani daga Laatifa
"na san zaki ce bazaki iya rabuwa da shi ba, amma ya zama dole dady ya san irin zaman da kike a gidanan"
girgiza mata kai tayi "gaskiya Laatifa bazan iya sanar da dady ba kin san halinshi, muddin ya sani ya Zaabith ya shiga uku"



"to ya shiga ukun mana ina ruwan wani, ke sau nawa yana saki a ukun" Laatifa ta fa?a a hassale da alama dai ranta ba ?aramin ?aci yayi ba
"bazan iya ba, ina tausayin hukuncin da dady zai yanke mashi,zanta kai kukana wajen ubangiji, in sha Allah wata rana zai daina"


"ai shikenan sai ki tashi dr fawar na nan dady ya turoshi ya dubaki" wani irin fa?uwa gabanta yayi, saurin dafe saitin zuciyarta tayi

"na shiga uku! waya fa?a mashi bana da lafiya?"

"kema kin san dole yaji ba'asin abunda ya hanaki zuwa gidan Abbah,may be mom salima ce ta fa?a mashi baki da lafiya, kin san kuma komi a kayi maku idan ba shi yayi ba baya ganin daidain shi, ki tashi kawai kije"


"amma bata fa?a mashi dr James ya dubani ba?"
"kinfi kowa sanin waye dady, kawai ki wuce kije" hijab ta ?auka ta zura a jikinta, ficewa tayi zuwa parlorn, gefen bed ?in Laatifa ta zauna.


A zaune ta same su saman sofa kamar yanda laatifa ta barsu masu aikin sun kawo ma Dr fawar abun motsa baki.


cikin girmamawa su ka gaishe da juna ita da Dr fawar,bayan da su ka gaisa ne ya shiga yi mata ?an tambayoyi tana bashi amsa.


duk wani abun da ya kamata yayi mata yayi mata,baisha wahala ba saboda duk wani da zai bu?ata wajen duba patient ya zo da shi,sallama yayi mata akan idan ya kammala binciken zai ba Irfan sakamakon ya kawo mata,godiya tayi mashi sosai.



sallama yayi mata su ka fice shida Irfan,a parking space yana shirin shiga motar shi uncle Mustafa ya kira dan yaji mike damunta,sanar da shi yayi zazza?i ne dai yanzu sai sakamakon test ?in da yayi mata ya fito sannan ya san ta?amaimai abunda ke damunta.


godiya sosai uncle Mustafa yayi mashi kafin su kayi sallama,ficewa su kayi daga Villa ?in motar Irfan na gaba yayinda ta Dr fawar ke bayan shi.


Estate Irfan ya koma lokacin har sun kammala lunch suna part ?in Abbah,Noor tayi fushin tayi fushin har ta gaji,sai da ?yar ya samu ya shawo kanta.


Barisster Hashim da mamy da su ka fita ba sune su ka dawo ba sai da yamma li?is ana gab da kiran magrib,sai ma da suka dawo sannan wasu su ka fahimci ba sa nan.


Bayan sallar isha su kayi dinner kowa ya kama shirin tafiya gida,Ammar tunda lokacin tafiya suka fara murnar yau a gidan big daddy za su kwana Jamal ma rigima yasa shima dole ya bisu,wayau Aunty Nafisat ta so yi mashi kan ya bari idan sun koma gida dadyn shi zai kawo shi amma fir ya tubure shi dole yanzu yake son bin su duk yanda ta so ya bari sai wani week ?in amincewa yayi dole tasa su ka ha?ura.


motar su na bayan ta Irfan daya ?auko mom,Yumnah na back seat tare da yaran yayin da Nainarh ke front seat kusa da Fa'iza dake driving.


Yumnah tun kafin su ?arasa ta kira Ishrat ta sanar da ita zuwan su Ammar saboda su gyara masu bedroom ?in dake kusa da na Yumnah,sosai Ishrat tayi murna da zuwan su Ammar yaran na matu?ar burgeta.


A tare motocinsu su kayi parking,a tare su ka shiga fitowa daga motocin,cikin gidan su ka nufa su Ammar na ri?e da hannun Yumnah, Jamal ma Nainarh ya ma?alemawa tunda Aunty Yumnah ta yadashi,?aya daga cikin security ?in gidan ne ya shigo da kayan su Ammar.


Irfan har bedroom ya raka mom da jakatar a hannunshi mom har mamaki take miye ala?ar Irfan da son ri?e jaka,duk za su fita tare baya barinta ri?e jaka ko kau ina za su je haka zai ri?e jakarta,Fa'iza har iya shage take mashi saboda ri?e jakar mom.


Basu wani jima su ka fice shida Waseef da alama sauri suke zuwa wani waje, bedroom da Yumnah tasa aka gyara masu ta nufa da su Ammar, bedroom ?in yana da girma sosai dan yafi na Yumnah girma ?aton king size bed ne a cikin shi.


ruwa Yumnah tasa su ka watsa su ka shirya cikin pajamas ?in su,a nan ?akin su kwana harda Nainarh dan rigima su ka masu akan sai sun kwana tare da su...


_*HEART OF VEGAS CLUB AND CASINO*_

*12:00 AM*


_*HEART OF VEGAS CLUB AND CASINO*_


?arfe shabiyu na dare daidai motar su tayi parking a ?aton parking space ?in dake club ?in, ma?il yake da motoci kasancewar yau Friday duk wani mashahurin da yake ganin ya shahara ayawan club zaka same shi a nan.


Kamar yanda sunan ya kasance iri ?aya haka tsarin ginin ma iri ?aya ne,banbanci kawai wacan yafi girma sai dai ba wani sosai ba,gaba ?aya photocopy wacan ne.


Kusan a tare su ka fito,jeans da T_shirt ne a jikin Waseef yayinda Irfan ke sanye da shirt ha?e da short iya gwiwarshi,kanshi a sanye yake da Ivy Cap idanunshi a manne su ke da ba?in shade mai shegen kyau.


Entrance ?in shiga club ?in su ka nufa,wasu irin jibga jibgan security guard a gaban katafariyar ?ofar shiga club,tun kafin su ka ?araso securitys ?in su ka rissinar da kai alamar girmamawa a gare su,kallon in da su ke babu wanda yayi tsakanin Irfan da Waseef,bakin ?ofar su ka ?arasa, Waseef ne ya ciro card ?in shi daga cikin aljihu,a jikin na'urar dake jikin ?ofar ya zura card ?in,zugewa ?ofar ta shiga yi bayan na'urar ta kammala acknowledging card ?in.



ciki su ka kunna kai Irfan na baya yayin da Waseef ke bayan shi,tsarin club ?in ?aya ne dana US duk abunda ke a wancan a kwaishi a wannan banbanci abubuwa ka?an ne, mata da maza ne ta ko ina kowa na harkar gaban shi, wasu na rawa wasu na shaye shaye,babu wanda ya lura da shigowar su har su ka isa bakin galss elevator dake club,maddanan dake jiki Waseef ya danna nan take ?ofar ta bu?e,ciki su ka shiga,sama elevator tayi da su zuwa floor ?in ?arshe.


fitowa su kayi bayan ?ofar ta zuge,a bakin wani office su ka tsaya,wasu nombobi dake a jikin na'urar dake jikin ?ofar ya danna,nan take ?ofar ta bu?e,ciki su ka shiga, katafaren office ne kamar ba'a niger ba komai na cikin shi extraordinary ne, Executive chair ?in dake gaban ha?a??en glass desk Irfan ya nufa,zama yayi yayin da Waseef ke jan ?aya daga cikin chair ?in dake gaban desk ya zauna.



mac book ?in dake ajiye saman desk ?in ya bu?e,babu ?ata lokaci ya shiga operating ?in ta.


"wai yaushe Muhsin yace maka Boss zai dawo ne,akwai kayan da babu ga tarin customers da muke da su?"Irfan ya fa?a ba tare da ya ?ago daga abunda yake ba

"kasan ba kowa ke sanin lokacin tafiyar shi ba haka lokacin dawowarsa" jinjina kai Irfan ?in yayi
"gashi Muhsin ?in bai shigo ba,amma bari na kira wayar shi naji" ya fa?a yana zaro wayarshi daga aljihu,number Muhsin ya shiga dialing, ringing wayar ta shiga yi har kiran ya katse ba'ayi picking ba, Yana ?o?arin sake kira aka turo ?ofar office ?in.


"ina jin gashi nan" Waseef ya fa?a yana kai dubanshi ga ?ofar dan ya san idan ba Muhsin ?in ba to Boss ne su ka?ai keda lasisin shigowa ba tare da na'ura ta dakatar da su ba.

Wani matashin saurayi ne ya shigo cikin shigar ?ananan kaya,?a??arfa ne na gaske,cikin office ?in ya nufa, kujerar dake kusa da wacce Waseef ke zaune yaja ya zauna,hannu ya mi?a masu su kayi musabaha


"kamar kuwa kasan nemanka nake"irfan ya fa?a
"shigowata kenan naga kiranka,neman mi kake man fatan dai lafiya?"
"dama tambayarka zanyi yaushe boss zai dawo, akwai tarin customers a gaban mu"

"ka san halin yaya idan zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login