Showing 54001 words to 57000 words out of 67530 words
earrings ?in bayan ta ajiye mata hills ?in a ?asa,zura ?afarta tayi a takalmin.
"baby kin yi kyau sosai" Aunty Sophia ta fa?a, murmushi Nailarh ta saki "thanks" locker ta ta nufa,?ofar fita Aunty Sophia ta nufa tana fa?in
"baby zan jiraki a parlor" Bata tsaya jin mi Nailarh za tace ba ta fice.
murmushi Nailarh ta saki ta rasa miye matsalar Aunty Sophi da gun kwata kwata bata son kallon locker ta bare akai da abunda ke cikin ta,bu?e locker tayi ta ?auki pistol,a ?ugunta ta soke ta tukun ta rufe locker.
jerin shades ?inta ta nufa,Black color ta ?auka ta zura a idonta,ficewa tayi daga dressing room ?in, wayarta dake ajiye saman makeken gadonta ta ?auka.
a parlor ta samu Aunty Sophia na jiranta,tunda suka shigo main parlor gidan masu aiki ke bin Nailarh da kallo ba?aramin tafiya da su wankan nata yayi ba.
russunawa suka shiga yi suna gaishe da ita,hannun kawai ta ?aga masu,a jere su ka samu motocin da zata fita da su a compound, jiki na rawa security guard ?inta suka shiga gaishe da ita,suma hannu kawai su ka samu ta ?aga masu,har gaban motar da zata shiga ?irar ACURA RDX black color Aunty Sophia ta rakata,da kanta ta bu?e mata back seat ?in motar ta shiga ta rufe,?aga mata hannu tayi tana juyawa ta koma ciki.
A jere motocin su ka fice daga gidan,babban titin da zai fitar da su gaba ?aya street ?in su ka hau,suna karya wata kwana motocin su Joseph suka kunno kai,ha?ewa su kayi da nata motocin su ka ?auki babbar hanyar da zata sada su da ?aton PORT dake RENO.
Tafiya su kayi mai ?an nisa tukun su ka iso PORT,?aton port ne iya ganinka,ga manya manyan truck dake kai kawo ?auke da containers,a parking lot ?in dake port ?in su kayi parking.
kusan a tare su ka bu?e cars door ?in su ka fito,motar Nailarh securitys ?in su ka nufa tare da Joseph,car door su ka bu?e mata ta fito,ya mutse fuska tayi tana kallon port ?in kafin ta kai dubanta ga Joseph.
"ina containers ?in su ke ne?" ta fa?a ganin tarin containers dake wurin ga wanda trucks ke ?awainiyar ?auka.
"sai mun fara zuwa office ?in C G tukun"
"ok mi kake jira"
"sorry boss" ya fa?a yana ?an rissinar da kai ha?i da nufar office ?in CG ?in dake cikin port ?in,tsaki taja tana komawa cikin motar ta zauna,bata rufe door ?in ba ?afarta ?aya a ciki ?aya a waje.
Bayan kamar 5 minutes Joseph ya dawo tare da wani mutumin dake sanye da uniform white color hannunshi ?auke da wasu takardu, bayansu matasan samari ne har su shidda suna sanye da overall orange color.
har gaban motar su ka ?araso, ?arasawa Joseph yayi bakin door ?in motar
"boss ga CBP nan,shine in charge na cargos ?in"
zame shade ?in dake fuskarta tayi tana kallon mutumin da tunda Joseph yayi magana yake washe baki
"?arasa" Joseph ya fa?a yana nuna mashi bakin door ?in motar,?arasawa mutumin yayi,fuskarshi ?auke da fara'a ya gaishe da ita cikin girmamawa.
glass ?inta dake hannunta ta ?aga mashi alamar amsawa, murmushi ya saki yana jin jina kai, takardun dake hannunshi ha?e pen ya mi?a mata
"CG ya sa hannu sai naki kawai ya rage"
yamutse fuska tayi tana kar?ar takardun da yake mi?o mata, sign ta shiga yi a takardun ba tare da ta ko karanta abun da su ka ?unsa ba.
mi?a mashi tayi tana fa?in "what next?"
"za muje ne kiga kayan"
"ba sai naje ba kawai su ?auko" ta fa?a
"please madam ganin yanada amfani,kuma zaki shaida adadin containers nawa ne su ka iso"
yamutse fuska tayi tana zuro ?afarta da nufin fitowa ringing ?in wayarta ne ya dakatar da ita,jawo wayar tayi tana duba sunan mai kiran nata Sweetheart shine sunan daya bayyana a screen ?in.
picking call ?in tayi ha?i da kara wayar a kunnenta,fitowa ta yi su ka nufi cikin inda containers su ke,cike da shagwa?a take waya da mahaifiyar ta ta data kira dan taji ya abun yake tafiya.
a gaban wani ?aton container ship dake bakin ruwa, trucks na jidar containers su ka tsaya, Nailarh na can bayan su tana waya,nuna ma Joseph containers ?in su da trucks su ka ?auka har guda biyar yayi.
jinjina kai Joseph ?in yayi
"aikin ka yayi kyau,fatan kayi waya da Madam?"
"eh tun kafin ma ku ?araso ta kira ni"
"ok good,muje ko" Joseph ya fa?a yana nufar Nailarh harta kammala wayar.
Juyawa tayi ta koma inda su kayi parking,motar ta shiga security daya bu?e mata ya rufe door ?in,sallama Joseph yayi ma in charge ?in ya shige motar shi, a jere su ka fice daga port ?in trucks ?in containers ?in su na biye da su...
A jere su ka fice daga port ?in trucks ?in containers ?in su na biye da su, wata hanya su ka ?auka daban, tafiya su kayi mai ?an nisa kafin su ka iso wani ?aton orphanage, daga yana yin ginin zaka san cewa bana ?ana nan mutane bane,yanada girma sosai.
horn su kayi a bakin gate ?in, can cikin bacci masu gadin orphanage ?in su ka ji ?arar horn ?in, ba suyi mamakin jin horn da tsohun dare nan ba saboda mamallakan orphanage ?in sun saba yi masu shigar dare irin haka.
?aya daga cikin securitys ?in ne ya le?o ta ?ar ?ofar dake jikin gate ?in,kallo ?aya yayi ma motocin ya fahimci ko su waye, a hanzarce ya koma ciki, gate ?in ne ya shiga zugewa zuwa gefe guda, da gudu motocin su ka danna kai zuwa cikin orphanage ?in,da sauri securitys ?in su ka shiga motocin dake bakin gate ?in su ka bi bayan motocin.
wasu irin gine gine na zamani su ka shiga wucewa ba laifi Orphanage ?in yanada girma sosai, a bakin wasu manya manyan store har guda biyar su ka yi parking,fitowa su ka shiga yi daga cikin motocin su, wani matashin saurayi ne ya fito daga motar Joseph tun ?azu sai yanzu ya fito,black American ne, neck ?in shi yasha zanen tattoo kallo ?aya zaka mashi ka gane ri?a?en ?an duniya ne.
motar da Nailarh ke ciki Joseph ya nufo, back seat ya bu?e mata, fitowa tayi a dai dai lokacin da securitys ?in ke ?arasowa, da sauri su ka nufeta, gaishe da ita su ka shigayi cikin girmamawa, ko arzi?in kallo basu samu daga gareta ba, trucks ?in ta nufa umarnin a bu?e su ta bada,fitowa drivers ?in su ka shigayi,kowace truk mutum uku ne su ka fito daga cikinta, babu ?ata lokaci su ka shiga bu?e bayan truck ?in, wasu irin tarin kwalaye ne a bayan truck ?in, da hannu tayima Joseph alama da ya zo, da sauri ya nufo in da take, wayarta ta mi?a mashi,da sauri yasa hannu ya amsa,video ya shiga ?aukar kayan.
truck ?ayace ba'a bu?e ba kallon drivers ?in tayi "wannan fa?" ta tambaya tana nuna masu truck ?in, Joseph ne yayi saurin fa?in
"ina tunanin itace wacce madam tace kar a shiga da ita"
cike da bada umarni ta furta "ku bu?eta" da sauri Joseph yace "ba kuji ana magana" a hanzarce su ka shiga bu?e truck ?in, wani irin mummunan fa?uwa gabanta yayi a lokacin da tayi arba da abunda batayi tunanin gani ba, da tsantsar mamaki take kallon matasan ?an mata da samari dake bayan truck ?in an rufe masu bakunansu yayinda hannayen su ke a ?aure.
da sauri Joseph ya sauke wayar ?asa, da mugum mamaki tashiga kallon drivers ?in kafinta sauke idanunta akan Joseph, cike da tuhuma ta furta"miye wannan?"babu wanda ya iya bu?e baki a cikin su ya bata amsa, suma sun shiga ru?an, sunyi matu?ar mamakin ganin yaran, wata irin gigitacciyar tsawa ta daka masu kamar ba Nailarh ba.
"tambayar ku nake miye wannan, ina aka samu wannan yaran??"
?aya daga cikin drivers ?in ne yayi ?arfin halin bata amsa "mu ma bamu sani ba kawai dai mun samu truk ?in a cikin jadawalin da miss m..." kasa ?arasawa yayi saboda tsawar data daka mashi, bashi da tayima tsawar ba hatta Joseph sai da ?an hanjin cikinsa su ka ka?a.
gaba ?aya fuskarta ta riki?e da tsantsar ?acin rai, a fusace ta bu?e baki da nufin magana amma sai ringing ?in wayarta ya dakatar da ita, da saurin Joseph ya mi?a mata wayar, picking call ?in tayi ba tare da ta ko duba sunan mai kiran nata ba.
muryar mahaifiyarta ce ta daki dodon kunnenta daga cikin wayar "hello baby har kun kammala" saurin maida kiran tayi zuwa video call, back camera ta kunna ta saita wayar dai dai inda truck ?in take.
"momy wannan container ta waye?" ta fa?a ranta a matu?ar ?ace, a kwance take saman hammock chair a bakin beach daga Ita sai bra da wani matsiyacin pant mai igiya gefe da gefe kusan rabin mazaunanta a waje,ta rufe idonta da ba?in shade hannunta a ri?e da coconut drink tana sha.
cike da bariki irin bata fahimci mi Nailarh take nufi ba tace "wace container baby?"
"wacce idanunki su ka nuna maki" ta bata amsa dai dai da tambayarta dan ba ?aramin ?aci ranta yayi da ganin yaran ba.
"sorry baby na manta banyi maki bayani ba,marayu ne basu da gata, gashi suna fama da wata lalura na turo su nan ne saboda suna bu?atar emergency treatment"
maida front camera tayi tana jifar mahaifiyarta ta da wani kallon rainin wayao
"amma momy kwata kwata yaran nan basuyi kama da patient ba kama suke da wanda a kayi kidnapping, momy ina ki ka samo yaran nan?" ta kai ?arshen maganar babu alamun wasa
"baby kin fi kowa sanin mahaifiyarki ko dabba bazata iya sacewa ba bare mutum, ki yarda da ni yaran nan taimakonsu kawai nake son yi"
"idan taimakonsu ki ke son yi mi yasa baki turosu a Flight ba amma ki ka turo su a container bakunan su a rufe,mi hakan yake nufi?"
"ki yarda da ni baby taimakonsu nayi" ta fa?a cike da shagwa?a kamar bada ?arta take magana ba
"gaskiya banji da?in yanda ki ka sa aka ?aure su ba,kamar wasu dabbobi"
"sorry baby na amshi laifin hakan bazai sake faruwa ba, sorry" ta fa?a tana ?an kama kunnenta, tsaki Nailarh taja tana rejecting kiran.
umarni ta bada akan su fito da yaran bayan ta tura securitys ?in orphanage ?in sun kira doctors ?in dake hospital ?in orphanage ?in, ?aya bayan ?aya su ka shiga fito da yaran sai layi su ke kamar za su kifa ?asa da alama wani abun aka basu wanda ya gusar masu da hankalin su.
doctors da nurses dake ?auke da stretcher ( gadon ?aukar marasa lafiya) su ka ?araso wasu sun su sai hamma suke da alama daga bacci su ke, cike da girmamawa su ka shiga gaishe da Nailarh bata wani amsa masu ba ta bada umarnin a ?auki yaran, babu ?ata lokaci su ka shiga ?aukar yaran a gadon ?aukar marasa lafiya suna nufar hospital ?in, bayan su Nailarh tabi, ganin haka ne yasa Joseph bin bayan su.
cikin gaggawa likitocin su ka shiga ba yaran emergency treatment dan ganin sun dawo cikin hayyacin su, sun shafe awanni da yawa suna abu ?aya sai da ?yar su ka samu yaran suka farfa?o amma sun gagara gane ta?amaimai abunda ke damun yaran.
kallon Nailar dake zaune saman waiting chair Joseph yayi, idanunta a lumshe bacci ne sosai a idonta amma saboda san ta san mike damun yaran ta?i tafiya gida, cike da tausasa murya joseph yace "boss ya kamata ki tafi gida ki huta"
"bazan tafi ba sai na san abunda ke damun yaran nan"
"am sorry boss, da dai kin tafi har yanzu bincike doctors ke yi kuma na san idan suka gama bincike har gida za su kawo maki result ?in"
"kana ba kanka wahala Joseph babu in da zan tafi bansan abunda ke damunsu ba"
lallashinta ya shiga yi shida securitys ?in amma babu wanda ta saurara a cikin su sai ma cewa tayi idan ba so suke suyi ta aikin su ba to karsu sake mata magana.
ganin dai da gaske ba amincewa za tayi ba ne yasa Joseph yanke shawarar kiran mahaifiyarta, number mahaifiyarta ya shiga dannanama kira amma ba tayi picking ba, canza akalar kiran yayi ga Aunty sophia, baiwar Allah tunda Nailarh ta fita bata rintsa ba, ta kasa zaune ta kasa tsaye hankalinta duk a tashe yake saboda inda Nailarh ta tafi, kiran Joseph na shiga wayarta har sai da gabanta ya fa?in, jiki na rawa tayi picking ko da ya sanar da ita dalilin kira ba ?aramin kwanciya hankalin ta yayi ba.
"please bata wayar" ta fa?a, da sauri ya mi?a mata wayar"boss miss sophia na son magana dake" a hankali ta bu?e ido tana jifanshi da harara, saurin sadda kanshi yayi ?asa, kauda fuska tayi gefe ba tare da ta amshi wayar ba, kara wayar yayi a kunnenshi "ta?i kar?ar wayar" ya fa?a
"sata a speaker" shine kawai abunda Aunty sophia ta fa?a,ok ya furta yana sa wayar a speaker
"hello baby kina jina?" Aunty sophia ta fa?a
da wata kalar kasalalliyar muryar ta wanda bacci ke neman fin ?arfinshi ta furata "Aunty sopei "
"baby mi yasa baki son ki dawo gidan, kin san yanda hankali na ya tashi da fitar da ki ka yi, tunda ki ka fita ko bacci na kasa yi please ki dawo gida"
"zan dawo Aunty sopei kawai ina son na san abunda ke damun yaran"
"karki damu har gida doctor zai kawo maki result ?in su kuma nayi maki al?awarin tare da ni zamu zo duba su idan doctors sun kallama bin cike amma yanzu ki dawo gida"
"shikenan sai na dawo"
"yawwa ko ke fa keda na sanki babu ruwanki da shiga abunda bai shafeki ba?"
"ke ki ka fara koyaman damuwa da damuwar mutane" murmushi Aunty sophia ta saki da alama taji da?in maganar Nailarh.
"sai kin dawo" da ok ta amsa mata, rejecting kiran Joseph yayi yana sauke ajiyar zuciya, harara Nailarh ta watsa mashi murmushi kawai ya saki, tashi tayi ta le?a ?akin da yaran suke kafin ta nufi ?ofar fita,har inda motocin su suke doctors ?in suka rakata kafin sukayi mata sallama.
a guje motocin su ka fice daga orphanage ?in, tun a hanya su ka rabu da su Joseph su kuma suka kama hanyar gida, Nailarh bata san sun iso gida ba saboda tun a moto bacci yayi awana gaba da ita, sai da Aunty sophia tasheta tukun ta san sun ?araso,fitowa tayi su ka nufi cikin gidan, direct bedroom ?inta Aunty sophia ta nufa da ita, suna shiga ta fa?a kan bed ko takalman dake ?afarta bata cire ba.
murmushi kawai Aunty sophia ta saki, da kanta ta shiga rage mata kayana jikinta, rigar suit ?inta ta zame mata ha?e da earring ?inta da wristwatch tukun ta zame mata takalman ?afarta, idanunta ta sauke akan gun ?in dake suke a ?ugunta har zata wuce sai kuma tasa gefen suit ?inta ta zame gun ?in, a cikin rigar ta na?eta,dressing room ?inta ta nufa, maida komai tayi a mazauninshi, a saman locker ta ajiye mata gun ?in saboda bata san password ?in locker ba kuma Nailar tafi amfani da eye I D, ficewa tayi daga dressing room ?in ta koma bedroom ?in, gyara mata kwanciya tayi kafin ta fice daga ?aki baki ?aya.
*ABUJA NIGERIA*
Nainarh da yumnah ne suka fito daga bedroom ?in mom,less ne a jikin yumnah ?inkin bubu ta yafa mayafi saman kanta yayinda Nainarh ke sanye da riga da skirt na atamfa hijab ne a jikinta sa?anin yumnah dake da gyale, hannunsu ri?e da na su Ammar, Aman da jamala da alama fita za suyi.
Part ?in dady su ka nufa,da sallama a bakin suka shiga a parlor su ka sameshi shida mamy,ciki suka ?arasa, kallo ?aya mamy tayi masu ta ?auke kai dady kuwa da fara'a sa yake kallon su, a saman rug carpet su ka zauna cike da girmamawa su ka gaishe da su dady kawai ya amsa masu amma mamy yi tayi kamar ma bata san da zaman su a parlorn ba.
"my friends sai ina haka?" dady ya fa?a yana kallon su Ammar, Aman ne ya bashi amsa da
"gidan papah" ?aure fuska dady yayi "shine za ku fita ba tare da ni ba, kodai mun dai abotar ne ban sani ba?" jamal ne yayi saurin cewa "A'a ka tambayi Aunty Nainarh idan tace aje da kai shikenan" gaba ?ayan su suka kai duban su ga Nainarh da
kwata kwata hankalinta baya kansu tunda su ka shigo idanunta suka sauka akan wani ?aton photo dake manne a bango,sosai ta shagala da kallon photon, tayi mamakin ranar da su ka shigo bata ganshi ba tunanin ta fara yi to kodai ba'a jima da sashi ba.
?an ta?o ta yumnah tayi "dady na magana" da sauri ta kai dubanta ga dady "Aunty Nainarh jamal yace sai kin amince za'a tafi dani, za kuje dani kuwa?" saurin sadda kai ?asa tayi tana sakin murmushi, murmushi shima dadyn ya saki yana le?a fuskarta "idan na fahimta wannan shirun alamace ta ba'a zuwa dani" da sauri ta ?ago tana fa?in "A'a dady zamuje da kai"
"wasa nake maku sai kun dawo ina gaishe da mutanen gidan"
tashi yumnah tayi tana kama hannun Nainarh
"za su ji in sha Allah, ku tashi mu tafi"sallama su kayi masu suka fice, ta?e baki mamy tayi tana kallon dady "wai ni kam Janar da sanenka wannan yarinyar take zaune a gidan nan?"
"wace yarinya kenan" dady ya fa?a yana kai duban shi gareta dan bai fahimci akan wa take magana ba
"wacce su ka fita yanzu da yumnah"
"wai kina magana ne akan Nainarh"
"ni ban ma san sunanta ba amma ita nake nufi"
"da sani na take zaune gidan akwai matsala ne?"
"ni gaskiya bana son zamanta a gidan nan"
"miye matsalar ki da zamanta a gidan yarinyar da ba'a kanki take ba"
"kamarya miye matsalata, gidan mijina ne fa,kawai sai mu zuba ma zulaihart ido tayi ta yin abunda taga dama, hakanan zata kwaso mana yarinya idan ta cutar damu fa??" tunda ta fara magana dady ya kafeta da ido tsantsar mamaki ne akan fuskarshi ko miye abun masifa