Showing 21001 words to 24000 words out of 67530 words
kya shigo" matar ta fa?a tana nufar entrance ?in gidan.
da sauri wata ?ar ?aramar yarinyar ta fito, Black ?in abaya ce a jikinta tayi rolling da gyalen, simple make_up ne a fuskarta yayin da kyawawan idanunta ke manne da ?an sunglasses dai dai idonta mai butterfly,?ar hand bag ?inta ce ri?e a hannunta,highills ne a ?afarta ba ?aramin kyau tayi ba.
bayan mahaifiyarta ta tabi tana wani tako ?ai ?ai kamar wata uwar mata,a main parlor part ?in ta samu mahaifiyarta tana jiranta,glass elevator dake part ?in mom yarinyar ta nufa da sauri mahaifiyarta ta tace.
"ENAAYA ina kuma za kije?" ya mutse fuska yarinyar tayi tana fa?in "part ?in mom mana"ta fa?a cike da yanga
"muje mu fara gaishe da mamy tukun" mahaifiyar ta fa?a tana nufar part ?in mamy,juyawa yarinyar tayi tana fa?in
"ni gaskiya bazanje part ?in mamy ba,haka nan kawai ta rufe mutum da fa?a ba abunda yayi mata,kuma Ni dady nake son nunama wannan kwalliyar dan karma sister ta rigani,sai kin dawo kawai momy "
yarinyar ta fa?a tana nufar elevator part ?in mom.
girgiza kai kawai mahaifiyarta ta tayi tana fa?in "Allah ya shirya ki Enaaya"
A parlor ta samu mamy zaune saman sofa kayan ?azu ne a jikinta,bakinta ?auke da sallama ta ?arasa ciki.
fuskar mamy da fara'a ta amsa mata sallamar tana sannu da zuwa,wuri ta samu saman sofa ta zauna.
"in wuni mamy, ya gida"
"lafiya lau NADIYA, ya gida?"
"lafiya lau"
"masha Allah,Ina uwayen sanabe ko ana islamiyya?"
murmushi nadiya ta saki tana fa?in"A'a ta shiga part ?in mom ne" jinjina kai mamy tayi tana maimaita kalmar part ?in mom.
"watau ni tafi ?arfin ta zo ta gaishe ni,shine ta wuce wajen ?anwar uwarta, tunda ban haifi mahaifinta ba ai ba tazo ta gaishe ni ba,zata zo ta sameni ne" murmushi kawai Aunty nadiya tayi dafa gaskiyar enaaya mamy ba dai fa?a ba.
"tana nan zata shigo,na san duk saurin ta ha?u da dady ne"
"A'a tayi zamanta kawai ba sai ta zo ba"
"kiyi ha?uri mamy idan ranki ya ?aci"
uhmm kawai mamy tace mata ba tare da ta sake cewa komai ba.
sallama su ka ji daga bayan su ,Aunty nadiya ce kawai ta kai dubanta ga mai shigowa,riga da skirt na atamafa ne a jikinta ta yafa mayafi tun daga kanta fuskarta tasha make_up,manyan idanunta sun sha eyelashes na company, hand bag ?inta ce ri?e a hannunta yayinda yaranta ke biye a bayanta mace da namiji ,namijin ya ?au wankan jeans and t_shirt,hannuwan shi zube su ke cikin aljihun wandon shi kamar wani babban mutum, fuskar nan tashi a ?aure take, ?ar macen ce ke sanye da Pakistan dress riga da wando ta yafa mayafin kayan saman kafa?ar ta, anyi mata parking gashinta a tsakiyar kai,light make_up ne a fuskarta,?afarta sanye take cikin wedge shoe masu kyan gaske, itama sunglasses ne a fuskarta mai butterfly kamar Enaaya.
da sauri Aunty nadiya ta mi?e fuskarta ?auke da murmushi ta nufi matar dake shigowa, hugging ?in juna su kayi,gaba ?ayan su suna sakin murmushi.
"sister NAFISAT shine baki fa?a man kuna tafe ba ai dana jira ku" Aunty nadiya ta fa?a yayinda su ke raba jikinsu daga na juna.
"uhmm ki bari kawai nima ban san da fitar ba, ina zaune ya NAEEM yace wai mu zo,Ni ban ma san mi ke faruwa ba" ta fa?a tana ?an ya mutse fuska.
"tare ku ke dashi ne?"
"eh ajiye mu yayi yaje ya dawo"
zuba masu ido mamy dake zaune tayi tana kallon su,wurin mamy Aunty nafisat ta nufa, gaishe da ita tayi cikin girmamawa,mamy da fara'ar ta ta amsa mata,suma yaran gaishe da mamy da Aunty nadiya su kayi,ta?e baki mamy tayi
"miskili kafi mahaukaci ban haushi,yau kuma aljanun sun bari a zo a gaishe ni kenan?"
?an ta?e baki Aunty nafisat tayi tana dallama yaron harara da duk ya wani ?ata fuska shi dole an sa shi abunda baiyi niyya ba,da sauri ya kalli gefe ganin kallon da mahaifiyar tashi tayi mashi,tsaki taja.
"momy nadiya wai ina Enaaya ne?" ?ar macen ta fa?a
"tana part ?in mom" ko gama fa?a nadiya ba tayi ba ta juya da sauri ta nufi ?ofar fita,bin bayanta namijin yayi, da sauri Aunty nafisat ta daka mashi tsawa
"ina za ka ,ko kaima Enaayar ?awarka ce?"
"ai wajen Aunty Yumnah zan je" ya fa?a yana ficewa daga parlor ba tare da ya tsaya jin mi Aunty nafisat ?in za tace,jinjina kai Aunty nafisat tayi.
"wai shi mi a kayi mashi yake wannan kumbura fuskar?" mamy ta tambaya
"saboda nace sai mun fara shigowa nan shi baiyi niyyaba shine yake wannan cin ?acin"
"kaga ?an bantan uban yara sun raina ni,sai kace wata uwar nake masu da ba sa son zuwa in da nake"
"iskanci ne kawai irin na su" a cewar Aunty nadiya
"zanyi maganin su ?aya bayan ?aya ne"mamy ta fa?a.
canza fira su kayi,su Aunty nafisat Nama mamy jajen abunda ya faru da mom,ta?e baki kawai mamy tayi ba tare da ta ce masu komai ba.
?????????? ????????????????
?arar takun takalminta ne ya cika masu kunne,da sauri su ka kai duban su gaba bakin ?ofa,mamaki ne gaba ?aya ya cika su,dariya fa'iza ta saki tana fa?in
"?amshi duk ya cika mana hanci kace uwayen mata ne a hanya" tsayawa Enaaya tayi tana wani tsuke baki
"kar wanda yasa ran zanyi mashi oyoyo,saboda wannan kwalliyar ta dady ce" ta fa?a tana wani yi masu fari da ido ta cikin glass, murmushi su saki
"yanzu baby Enaaya ko ni baza kiyi ma oyoyo ba" Yumnah ta fa?a tana wani marairaice fuska.
"gaskiya yau sai dai kiyi ha?uri Aunty Yumnah kwalliyar nan ta dady ce,ki bari idan na dawo daga wurin shi nayi maki oyoyo"
tsuke fuska yumnah tayi tana ri?e ?ugu"ai kuwa bana so"
"shikenan tunda so ki ke su Aunty balqis suyi mana dariya" Enaaya ta fa?a tana nufar stairs case dake hannun daman parlor,tana tafiya tana wani jujjuya jiki.
murmushi kawai balqis tayi tana fa?in "manyan mata sun hallara kowa yayi ta kansa" dariya su ka kwashe gaba ?ayan su.
*KITCHEN*
Gaba ?aya masu aikin gidan suna kitchen domin lokacin fara aikin dinner yayi,a hankali take tafiya dan karma taji ?arar takalminta
alama tayi ma masu aikin dake ciki da kar suyi magana,da gudu ta nufi Eishrat dake tsaye gaban fridge tana jera drinks,kamar daga sama taji mutum ya fa?a saman bayanta, ?ara ta saki tana jefar da lemun dake hannunta,dariya ta fashe da ita.
"gaskiya chef Ishrat kin cika tsoro" ajiyar zuciya Ishrat ta sauke dan ba ?aramin tsorata tayi ba saboda bata san da shigowar ta ba sai dai kawai tajita a jikinta.
tsuke fuska Eishrat tayi tana
"amma baby Aneesah kin raina ni da yawa" dariya Aneesah ta kwashe da ita
"ba wani kin dai cika tsoro ne"
"to naji,saukar yaushe?"
yamutse fuska Aneesah tayi "yanzu muka zo da momy fatan kin ajiye man Al?awari na?"
yana yin fuskar Eishrat ne ya sauya "Ayyah! baby Aneesah ban san za kizo yau ba"
?ata fuska Aneesah tayi "chef Eishrat na fa sanar dake jiya, ko kin manta na kiraki da landline ?in kitchen?" Aneesah ta fa?a tana tsuke baki
"sorry baby Aneesah mantawa na yi,amma yanzu zan ha?a maki"
?ata fuska Aneesah tayi "har dady ya fita baki kammala ha?a man ba"
murmushi Ishrat ta saki
"wasa nake maki baby, tunda ki ka sanar da ni zuwan ku na ha?a maki"
da sauri Aneesah ta dafe saitin zuciyarta tana wani lumshe ido
"wai Allah! har kin sa hankali na ya kwanta,da yau kin sa sister Enaaya tayi man dariya, duk wannan saurin da nake dan kar ta rigani ba dady wani abu"
"Ayyah sorry,na san ta rigaki dan tun ?azu tana part ?in shi"
yamutse fuska Aneesah tayi "ita komai nata cikin sauri take yin shi,ai na san duk abun da zata bashi bazai kai wanda zan kai mashi ba"
"nima ina fatan haka, bari na shirya maki komai" Ishrat ta fa?a.
?aton wooden tray Ishrat ta ?auka, fridge ta bu?e fruit salad ta ?auko a cikin bowl sannan ta ?auko yogurt daga gani ha?in gida ne mara za?i da lemun wanda shima ha?ashi tayi da kanta sai chocolate cake.
Murmushi Aneesah ta saki ganin abun da tafi bu?ata,dish rag ta nufa cups ta ?auko da fork guda biyu ta ?aura saman tray,ficewa su kayi daga KITCHEN ?in Aneesah na gaba yayin da Ishrat ?in ke biye da ita.
bakin su ?auke da sallama su ka shiga cikin parlor,su Yumnah na nan zaune kamar yanda Enaaya ta barsu,Jamal na kwance saman sofa yayi pillow da laps ?in Yumnah.
murmushi su ka saki yayin da su ke amsa sallamar da su kayi,sama Aneesah ta nufa ba tare da tace ma kowa ?ala ba suma binta su kayi da ido dan sun san ba lallai ta tanka masu ba tana sauri taje wurin dady.
bin bayanta Ishrat tayi ,dariya fa'iza ta saki tana fa?in "yan bantan uban yara kowa zai ha?ura ya barma wani dadyn a cikin su?"
"rabu da ?an ?wal uba sun gama iskancin su su barma su mom majin su,yara sai kilibibin masifa"
a cewar Balqis, murmushi laatifa ta saki
"kar kuga laifin su,kuma da kune a matsayin su na san sai kunyi abun da yafi nasu"
"haba Aunty laatifa mu mi yasa ba mu yima Abbah haka"
"babu face ne shiyyasa" murmushi kawai su kayi ba tare da sun ce komai ba.
A kishingi?e yake saman rug carpet dake katafaren parlon shi, ya ?aura kanshi saman tum tum yayin da Enaaya ke gefenshi ,cike da salo da kisisina take bashi labarin school ?in su,ya ?afeta da ido sai sakin murmushi yake.
sallamar Aneesah da Ishrat ce ta katse masu firar da su ke, waro ido waje Enaaya tayi yayinda take mi?ewa tsaye
"wayyo Allah nah!, sister Aneesah dama za ki zo" Enaaya ta fa?a tana yarfe hannu
murmushi Aneesah ta saki tana ?arasowa ciki, da sauri Enaaya ta nufeta, hugging ?in juna su kayi sai sakin murmushi su ke,raba jikin su su kayi.
gaishe da junansu su ka shiga yi kamar wasu manyan mutane, Ishrat da dady ban da sakin murmushi babu abun da su ke.
cikin parlor Ishrat ta ?arasa a gaban dady ta ajiye tray
"barka da hutawa dady" murmushi dadyn ya saki
"lafiya lau Ishrat,sannu da ?o?ari" murmushi kawai Ishrat ?in ta saki tana nufar ?ofar fita
"thank u" Aneesah ta fa?a, alamar jinjina Ishrat ?in tayi mata tana ficewa daga parlorn.
wurin dady Aneesah ta ?araso tana sakar mashi murmushi ha?i da fari da idanu, murmushi kawai dadyn ya saki yana girgiza kai lamarin su Aneesah na matu?ar bashi mamaki.
a saman rug ?in su ka zauna, gaishe da dady Aneesah tayi yayinda take zuba mashi lemu a cup,cikin kulawa dady ya amsa gaisuwar yayin da yake ?ar?ar cup ?in lemun da take mi?a mashi.
a tare su ka shiga cin chocolate cake ?in banda dady saboda ciwan sugar
fira su ka shiga zuba mashi yan sauraron su.
Aunty nafisat sun jima a part ?in mamy kafin su ka shigo part ?in mom lokacin har su mom Maryam sun tafi ya rage saura fa'iza da Yumnah kawai, nainarh har time ?in tana kwance a bedroom ?in Yumnah.
bedroom ?in mom su ka shiga a zaune su ka sameta bakin bed ?inta tunda su mom Maryam su ka tafi take a nan zaune.
cike da girmamawa su ka shiga gaishe da ita tana amsa masu cikin kulawa,sosai su ka nuna alhinin su kan abunda ya faru da ?awar mom ?in.
tambayar su Aneesah mom tayi dan tun ?azu suna part ?in dady ba su fito ba, murmushi kawai tayi ko da su ka sanar da ita suna can.
fira su ka shiga ta?awa sama sama har aka fara kiran sallar magrib, bedroom ?in Yumnah su ka nufa domin yin sallah,sunyi mamakin ganin nainarh dan basu san da zamanta a gidan ba,kasa ha?uri Aunty nafisat tayi har sai da ta tambayi Yumnah wacece,fa?a mata ko wacece Yumnah tayi.
ta?e baki kawai Aunty nafisat ?in tayi Aunty Nadiya kuwa ko kallon in da su ke ba tayi ba tana sallame sallah ta fice daga ?akin zuwa na mom, anan ta samu Aneesah da Enaaya sai zubama mom fira su ke Jamal na gafen su zaune.
Aunty nafisat ma data gama sallah bedroom ?in mom ta koma,ko da lokacin sallar isha yayi a nan su kayi ta,suna zaune saman carpet sallame sallar su kenan a kayi nocking ?ofar bedroom ?in.
da sauri Enaaya taje ta bu?e, a tsaye suke su biyu ?aya suit ne a jikinshi yayin da ?ayan ke sanye da Army trouser da white ?in shirt.
Kamannin fuskar su ka ?ai zai tabbatar maka da su ?in jinin dady da mom ne ba kamar mai Army trouser ?in.
Da gudu Enaaya ta fa?a saman jikin mai Army trouser ?in wando tana fa?in "oyoyo dady NAEEM ashe da rabon mu gana yau"
dariya su ka saki gaba ?ayan su
"ai kuwa da rabon mu gana, ya school?" ya fa?a yayinda yake raba jikinsu
"Alhmdllh dady NAEEM,wai ina ka shige kwana biyu bana ganin ka?"
"aiki ne ya yi man yawa baby Enaaya,kuma ma ai idan kina son gani na kin san in da zaki same ni"
?an zaro ido tayi tana kallon wanda ke kusa dashi "wannan maganar tafi karfina dady NAEEM,ga dady nah nan ka tambaye shi" ta fa?a tana komawa cikin ?akin da gudu.
murmushi kawai su ka saki ya NAEEM na fa?in "kenan dai ADNAN kai ke hanata zuwa gida na?" ya fa?a yana ?an tsuke fuska.
"haba SECOND FATHER sai ka ce baka san sharrin Enaaya ba,ni ?arya take man"
cikin ?akin su ka ?arasa ya NAEEM na fa?in "yanzu dai maganar wa zan kama tsakanin ku?"
"tawa mana dady NAEEM" Enaaya ta fa?a tana wani marmar da ido.
da sauri ya NAEEM yasa hannu yana toshe bakin shi ha?i da ?an zaro ido kamar yanda Enaaya tayi ?azu, girgiza mashi kai ta shiga yi alamar kar ya fa?a tana zare ido.
dariya gaba ?ayan su suka sa dan sun san saboda mi ya NAEEM yayi mata haka watau dadyn ta ?arya yake.
da gudu Aneesah ta fa?a jikin ya ADNAN tana mashi oyoyo, Jamal ma nufo su yayi,Barka da zuwa yayi masu yana koma bakin bed daya ta so.
gaishe da ya NAEEM Aunty Nadiya tayi tanama ya ADNAN sannu da dawowa,hakama Aunty nafisat gaishe da su tayi.
ta shi su kayi su ka fice daga ?akin ya zama daga mom sai su ya NAEEM ?in,a gabanta su ka zo su ka zauna ?asa suna tan?washe gwiwowin su kamar masu neman gafara.
cikin girmamawa su ka shiga gaishe da ita tana amsa masu cike da kulawa.
"ya aiki" ta tambaye su da Alhmdllh su ka amsa mata ha?i da jajanta mata abun da ya faru.
"in sha Allah gaskiya za tayi halinta" ya Adnan ya fa?a, da Ameen su ka amsa.
sun ?an jima suna fira kafin su ka tashi zuwa part ?in dady dan su gaishe da shi,har sun kai bakin ?ofa mom tace ma ya NAEEM tana son magana dashi gobe idan ya dawo aiki ya zo ya sameta,da to ya amsa mata, ficewa su kayi zuwa part ?in dady.
su Aunty Nadiya na zaune parlorn Ishrat ta shigo ta sanar da su an kammala dinner.
"sannunki da ?o?ari Ishrat" fa'iza ta fa?a, murmushi Ishrat ?in ta saki tana barin parlorn.
a dinning room su ka hallara saman makeken dinning table mai mazaunin mutum shabiyu, Aneesah da Enaaya sun sa dady a tsakiya, Nainarh ka ?aice babu, itama ba bu yanda Yumnah ba tayi da ita ba a kan ta fito suyi dinner amma ta?i sai dai aka kai mata nata can,tsit ka ke ji sai ?arar spoon da plate dake tashi kowa na ba ciki ha??in sa.
hakan ya ba dady damar kafe su da ido yana kallon su cike da Alfaharin yanzu duk shi ke da wannan danma wasu basa nan,yana yin fuskarshi ne ya canza da alama ya tuna da wani abun,hawaye ne su ka taru a idanuwan shi saurin goge su yayi yana kawar da tunanin a ranshi.
sai wurin ?arfe goma na dare su ya NAEEM su ka bar gidan,har part ?in mamy Aunty Nadiya da Aunty nafisat su ka shiga yi mata bankwana harda su ya NAEEM amma ban da su Enaaya dan cewa su kayi basa zuwa da iyayen su ka matsa masu sai ficewa su kayi daga gidan da gudu.
murmushi kawai fa'iza da Yumnah su ka saki suna bin bayan su Aneesarh.
cikin girmamawa su ya NAEEM su ka gaishe da ita amma sai ta amsa masu tana wani ya mutse fuska,hakan bai dame su ba idan da sabo ai sun saba.
ba su zauna ba su ka fice a parking space su ka samu su Enaaya tare da su fa'iza,sallama su kayi ma junan su su ka nufi motocin su yayin da fa'iza da yumnah su ka koma ciki, barin gidan su kayi zuwa na su gidajen dake cikin Estate ?in...
_*Ep11_12*_
*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*?????
_____________________________
A main parlor fa'iza da Yumnah su kayi sallama fa'iza ta nufi part ?in mamy yayin da Yumnah ta nufi na su part ?in.
direct ?akinta ta nufa, a hankali ta tura ?ofar bakinta ?auke da sallama, a tsaye ta hango Nainarh bakin sliding door ?in dake cikin ?akin ta zubama cikin estate ?in da yake ?wanyar da haske kamar rana ido, jefi jefi take hange motoci na kai kawo a cikin Estate ?in.
A zahiri kallon cikin Estate ?in take a ?a?i kuwa hankalinta na can prison wajen mahaifiyarta, ko a wane hali take, wasu irin zafafan hawayen su ka wanke fuskarta lokacin data tuna irin kisan wula?ancin da a kayi ma mahaifinta.
Sosai take zubar da ?walla kwata kwata ko sallamar Yumnah ba taji ba, bakin door ?in Yumnah ta ?araso, a hankali ta kira sunan Nainarh amma bata amsa mata ba saboda hankalinta da baya tare da ita, dafa kafa?arta Yumnah tayi, da sauri ta kai dubanta ga Yumnah.
"nainarh dan Allah ki daina sa damuwa a ranki, komai zai wuce"
da sauri Nainarh ta fa?a jikin Yumnah tana sakin kuka mai sauti,jikin Yumnah ne yayi sanyi, wani irin tausayin Nainarh ne ya rufeta musamman yanda taji jikin Nainarh ya ?auki zafi.
?an bubbuga bayanta ta shiga yi tana lallashin ta.
"nainarh