Showing 45001 words to 48000 words out of 67530 words

Chapter 16 - SHIRYAYYAR-ƘADDARA HAUSA NOVEL

08 Nov 2024

4354

kamar ko wane lokaci zaka samu fuskarta da makeup,sofa dake kusa da su Hajiya fatilah ce matar uncle mutallaf tare da Hajiya Halima matar Uncle Ubaid sun ?au wankan tsadadden less mai shegen kyau,fuskarnan ta su tasha makeup hannuwan su a cike su ka da ?an hannu da zobba na zallar zinari.


Mama Ameena ce hakimce saman sofa mai mazaunin mutum biyu dake kallon ?ofar shigowa parlorn,super atamface a jikinta anyi mata ?inkin riga da zani kalar na su na tsaffi,ta dafka uban ?aurin ?ankwalinta kamar koda yaushe.


cikin parlorn su mom su ka nufo bakin su ?auke da sallama,tsuke fuska mama tayi lokacin da idanunta su ka sauka kan mom,ta?e baki mamy tayi tana kauda kai.


Amsa masu sallamar su kayi in ka cire mamy dake cin ?aci sai wani bu?ar hanci take,
har gaban sofar da mama take zaune mom ta ?ara so,cikin girmamawa ta gaishe da ita,cike da izza tana wani yamutse fuska ta amsa mata a ta?aice,lamarin yaba Nainarh mamaki ita da abun ya zama sabo a idonta amma duk wanda ke parlorn yasan cewa babu jituwa tsakanin mama Ameenah da mom kwata kwata bata sonta.


Mama Ameenah matace ga Abbah,ita ta haifi Aunty Adama,ita ka ?ai ta rage a matan Abbah,kwata kwata bata ?aunar mom.


"mun same ku lafiya?"
"ga zahiri kuwa kin gani" mama Ameenah ta fa?a tana nuna kanta da hannu, murmushi ne ya bayyana akan fuskar mamy da su Hajiya fatilah da alama abun yayi masu da?i.

shiru mom tayi ba ta sake cewa komai ba,gaishe da mama su Yumnah su kayi, a ta?aice ta amsa masu tana sauke idonta kan Nainarh da duk tasha jinin jikinta.

"ita kuma wannan ina aka sameta?" mama Ameenah ta fa?a tana nuna Nainarh da hannu,fa?uwa gaban Nainarh yayi,gaba ?aya parlorn duban su suka kai ga Nainarh.


"?iyar Aminiyata ce Hajiya Asma'u" mom ta fa?a,jinjina kai mama tayi
"ziyara ta zo maki ko mi?"
"A'a wani iftila'i ne ya fa?ama mahaifiyar ta,to shine na daw..." bata ?arasa ba mama tayi saurin dakatar da ita
"to sai aka yi yaya,zama mi take cikin zuri'ata,ita mahaifiyar ta ta bata da dangi ne da bazaki barta a hannunsu ba,?"


"ba haka bane mama,zaman..."
"dan Allah dakata mana Zulaihart, wai sau nawa zance karki sake kirana da mama,banda jaza masifa ina ni ina haihuwar dangin she?an wanda Allah ya tsinemawa,ko nayi maki kama wannan tsohuwar banzar mai yawo ?wauri waje??"

?ar dariya mamy tayi tana kallon su Hajiya gaje
"Allah ya huci zuciyarki" mom ta fa?a tana tashi, ta nufi ?ofar fita daga parlorn, Yumnah idanunta har sun cika da hawaye bakomai yasa bata son zuwa part ?in Abbah ba idan ba ranar Friday ba sai dan saboda wannan cin mutuncin da mama kema mom,tashi tayi tana kama hannun Nainarh da duk jikinta yayi sanyi.


Fa'iza ma ranta ba ?aramin ?aci yayi ba,tashi itama tayi ta bi bayan su da kallon mamaki mamy tabita har ta fice daga parlorn.

rai a ?ace Aunty Adama ta kalli mama Ameenah
"gaskiya wannan abun mama da ki ke a gaban ?a?a da jikokin ki bai dace ba,haba dan Allah da shekarunki zaki zauna yara na zugaki kina abu irin haka"


"kamarya yara na zugata, mi kike nufi Adama?"mamy ta fa?a rai a ?ace
"da mahaifiyata nake magana ba dake ba,karki ?ara sa man baki,kuma duk abunda take akwai mai zugata sama da ku ne?"


tsantsar mamaki ne ya bayyana a kana fuskar mamy wai yau ita Adama ke fa?ama haka "lallai Adama Ni kike fa?a ma haka saboda Zulaihart?"


"fiye da haka ma sai ta fa?a maki mabaruka,gaba ?aya ku babu mai hankalin data san abun da ya kamata,mama shekarunta sun ja tunaninta baya yake komawa,maimakon ku zama masu bata shawara idan kunga za tayi abun da ba dai dai ba amma saboda son zuciya kullum cikin birkita mata tunani kuke,babu wanda yafi bani haushi a cikin kuka sama da ke Safeenah" Aunty Mariya ta fa?a rai a ?ace tana kallon Aunty Safeenah


"ni mi nayi Aunty mariya,babu ruwana fa a cikin wannan abun?"
"dama zaki ce haka mana,akwai wanda ya ?aure masu gindin yin abunda su ka ga dama sama dake,kina ?anwar mazajensu ko kunya bakiji"



"da Allah ya isa haka mariya,ni ya kamata Ku rufe da fa?a ba su ba,kune za ace ma ko kunya ba kuji,kun fifita bare sama da ?an uwanku musulmai,ko da yake ke barewa ai baza tayi gudu ?anta yayi rarrafe ba"


"ko mi zaki ce mama a shekarunki wanan abun da ki ke bai dace ba" Aunty Mariya ta fa?a tana nufar wata ?ofa,da harara mamy ta bita har ta shige ?akin,tsaki Aunty Adama taja tana bin bayan su mom.


"aikin banza dana wofi, kullum da an ta?a wannan dangin she?an ?in sai su rufe mutane da fa?a kamar wasu ?a?an cikin su" Hajiya Gaje ta fa?a tana sake jan wani tsaki
"gaba ?aya zanyi maganin su ne daga su har ita" a cewar mama Ameenah


"wallahi mama karki bari yarinyar nan ta zauna,ta maidata can dangin uwarta,haka kawai zata jajubo ma mutane gayyar tsiya inji ba uwarta bace ta kashe mahaifinta ba" Aunty Safeenah ta fa?a sai wani huci take.

"rabu da ita ai Tahir ?in zai zo ya same ni,zanji idan shi ya bata damar ajiye wanann annobar a gidan shi"



mamy ranta fes kamar ta zuba ruwa a ?asa tasha,dama ta san muddin mama Ameenah taga Nainarh sai tasa an koreta daga Estate ?in gaba ?aya.



first floor mom ta koma, bedrooms ?in dake floor ?in ta nufa, toilet ta shiga yayin da Yumnah da Nainarh su ka zauna saman arm chairs ?in dake bedroom ?in, Nainarh hankalinta duk a tashe yake da abunda ya faru a part ?in mama Ameenah,tunaninta yanzu wace irin rayuwa za tayi idan ta koma hannun dangin mahaifinta,kwata kwata basa sonta musamman yanzu da suke zargin mahaifiyarta da kashe mahaifinta,bare ace dangin mahaifiyar ta da ba nan suke ba,yanzu ita ya za tayi kenan...?? _*Ep 21_22*_



*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*?????


______________________________



sosai tayi nisa a duniyar tunani har mom ta fito daga toilet yumnah ta shiga bata sani ba,prayer mat Fa'iza ta shimfi?a ma mom ?in, wurin da Nainarh take ta nufo.


dafa kafa?arta Fa'iza tayi, saurin kallon fa'izar tayi,murmushi Fa'iza ta sakar mata " ina ta magana kinyi nisa a tunani baki ji,karki damu da maganar mama Ameenah babu in da za kije kina nan a tare da mu, ki kwantar da hankalin ki kinji"


murmushi kawai Nainarh ta sakar mata ba tare da tace komai ba, turo ?ofar ?akin Aunty Adama tayi ta shigo,duban su suka kai gareta, cikin ?akin ta ?araso, zama tayi kan chair ?in da yumnah ta tashi tana fuskantar Nainarh, fuskarta ?auke da murmushi tace


"kiyi ha?uri da halin kakar taku wasa take babu in da za kije, kina nan tare da mu har Allah ya kubutar da mahaifiyarki kinji"
murmushi Nainarh ta sakar mata
"nagode sosai Aunty, Allah ya bar zumunci"
"kar ki damu,ai yanzu munzama ?aya, zansa yumnah ma ta kawoki gida ki zo man ziyara, ai zaki zo ko"
"Eh in sha Allah, nagode sosai Aunty"



"shikenan, tashi ki shiga toilet ki ?auro Alwala ki zo kiyi sallah" da to ta amsa mata, tashi tayi ta nufi toilet ?in, kusa da Yumnah ta zo ta kabbar sallah, bayan fitowar Nainarh Fa'iza ta shiga,?aya bayan ?aya su ka shiga gabatar da sallar zuhur, bayan da su ka kammala ne su Yumnah su ka fice aka bar mom da Aunty Adama a ?akin.


main parlorn su ka nufa,a zaune su ka samu kairiyyah da Noor,?arasawa su kayi cikin parlorn, kusa da kairiyya yumnah da Nainarh su ka zauna.


suna a nan zaune parlorn Aunty Nafeesa da Aunty Nadiya su ka shigo,sun ?au wanka Abaya maroon color yayinda Enaaya da Aneesarh su kayi ankon Pakistan dress riga da wando white color ,rigar da wandon sun sha adon sparkling stones,sunyi rolling Veil ?in kayan a kan su,simple makeup ne a fuskarsu, kamar ko da yaushe eyes ?insu manne suke da sunglasses mai shegen kyau.


basu jima da shigowa ba Laatifa da Balqis su ka shigo tare da mom maryam da mom maimunatu, suma ankon Abaya su kayi yayinda mom maryam da mom maimunatu suka ?au wankan tsadadden Swiss less naji da fa?a.



mom maimunatu ta so su shiga part ?in mama Ameenah Amma mom maryam tace babu inda za ta sai dai mom maimunatu taje ita ka ?ai,duk yanda mom maimunatu ta so su shiga su gaishe da mamah ?in zuwa mom maryam tayi sai ma tashi da tayi ta nufi bedroom ?in da su mom su kayi sallah, itama sallah tayi.




*Queen Kainart??*



A jere dan?ara dan?aran motocinsu su ka shigo cikin estate ?in yayinda motocin securitys Armys ?in su suka sako su a tsakiya,katafaren parking space ?in dake part ?in Abbah suka nufa, daidaita parking ?in su kayi, durowa security Armys ?in su ka shiga yi daga motocin su,cikin girmamawa su ka shiga bu?e masu car doors, motar farko
Abbah ne ya fitowa hannunshi ri?e da sandarshi mai shegen kyau sai ?ayan ?agaren dady ya fito, motar bayan su dady Ahmad ne da dady mustafa su ka fito bayan ta su sai tasu Uncle ubaid da Uncle mutallaf su ka fito daga nan sai Uncle hashim.



bayan motocin su sai na jikokin Abbah,a mota ?aya ya Naeem da zaabith su ka fito motar bayan su ya Adnan da ya usman, ya Ahmer ne su ka fito bayan tasu ne sai ta su Irfan da Waseef su ka fito waseef ri?e da hannun Jamal a front seat na motar da su ka fito Aman da Ammar su ka fito su ukku sun sha ankon white jallabiya harda Arb turban a kansu ba ?aramin kyau su kayi ba kamar ka sace su ka gudu, motar bayan su Fa'iz da Yazdan ne su ka fito sun ?auki wankan farar shadda kamar sauran, kawunan su a sanye su ke da huluna hakan ya ?oye tarin sumar dake kansu.



gama fitowar su kenan daga motocin su motocin her excellency salima suka kunno kai cikin estate ?in,da katawa su kayi har motocin su ka ?araso parking space ?in, sai bayan da su ka gama daidaita parking ?in tunkun ?aya daga cikin securitys ?in ya bu?e mata car door ta fito,masha Allah na furta a sanye take da lafaya white color ta yafa gyale saman kanta, fuskarta ?auke take da simple makeup kyawawan eyes ?inta a manne su ke da farin shade mai shegen kyau.



wurin Abbah ta nufo cikin takun ?asaita yayinda PA ?inta ke take mata baya, cikin girmamawa ta gaishe da Abbah, da kulawa ya amsa mata
"ina ki ka baro man Amaryata na ganki ke ka ?ai?"
" bata jin da?i ne"
"subhanallah, mike damunta?"


"ta dai ceman zazza?i na damunta, da tare zamu zo to sai da muka shirya kuma taji bata iya zuwa jikin ya ?anyi zafi"
"ya salam, to Allah ya bata lafiya, Allah yasa kaffarane" gaba ?ayan su da Ameen su ka amsa


"dr ya dubata kuwa?" uncle Mustafa ya fa?a
"eh dr James ya dubata"
"mike damunta yace?"
"zazza?in ne kawai" mom salima ta fa?a
"zazza?i kawai ne a wajenki?,ni dama na san Zaabith bazai iya kula man da ?ata ba,idan baza ku iya kula da ita ba ku dawo man da ita zan sa ?wararren likita ya duba man lafiyar ?iyata" ya fa?a yana zaro wayar shi daga Aljihun wandon shaddar shi.

Uncle Ahmad har ya bu?e baki zaiyi magana Abbah yayi saurin dakatar da shi dan ranshi ya ?aci ya rasa miyasa Almustafa yake mashi haka, kullum gazawar su yake gani a wajen kula da ?arsa,gaba ?aya zuba mashi ido su kayi suna kallon ikon Allah, Zaabith duk yasha jinin jikinshi yasa bazai wuce rashin mutuncin da yayi mata bane ya haddasa mata zazza?i.



dialing number dr fawar yayi, bugu biyu yayi picking "hello fawar kana hospital ne?" on the other handa dr fawar ya amsa mashi da "Eh sir, kana bu?atar wani Abu ne?"
"kainart ce ba lafiya nake son kaje ka duba man ita"
"ok sir"
"thank u" ya fa?a yana rejecting call ?in.


"amma kasan cewa gidan gomnati ba wurin shigar kowa bane haka kawai ?" Uncle Ahmad ya fa?a yana kallon Uncle Mustafa da yayi kicin kicin da fuska


"Irfan kaje kayi mashi rakiya zuwa Villa ?in,idan kun isa ka kira ni ina son na san mike damunta da gaggawa"
"in sha Allah Uncle" Irfan ya fa?a yana nufar ?aya daga cikin motocin da suka dawo,driver seat ya shiga, suna anan tsaye yayima motar key ya nufi main gate ?in estate ?in.


babu wanda Uncle Mustafa ya kalla a cikin su ya nufi ?ofar shiga katafaren garden ?in gidan, murmushi kawai hajiya salima ta saki,Uncle Mustafa yanda mata?ar tsaurin akan ?a?an sa, bai ha?a soyayyar da yake masu da komai ba, zai iya ?atawa da kai saboda ?a?an shi shikuma tashi ?addarar kenan son ?a?a,shiyyasa Kainart ke mugun tsoron ya san irin zaman da suke da Zaabith dan ta san muddin ya sani abun bazai yi kyau ba.



"bari na shiga ciki Abbah"
"to salima" Abbah ya fa?a, enterence ?in shiga part ?in Abbah ta nufa
"muje ko Abbah"dady ya fa?a
"kuje gani nan zuwa" da to suka amsa mashi,?ofar shiga garden ?in su ka nufa, dakatar da Uncle Ahmad Abbah yayi.


"zo Ahmad" dawowa yayi in da Abbah yake tsaye, kamo hannunshi Abbah yayi cikin nashi, wata ?ofar shiga garden ?in su ka nufa daban da wacce su dady su kashiga,wasu irin shuke shuke ne a wajen masu matu?ar kyau da ?aukar hankali,ga wasu tsuntsaye masu ban sha'awa dake kai komo a cikin garden ?in.



wasu ?ayatattun benchs dake ?ar?ashin wasu rukunin bishiyu su ka nufa,zama su kayi suna fuskantar wasu killatattun ruwa,kai tsaye baza'a kira su da swimming pool ba ga wasu tsuntsaye dake shawagi saman ruwan abun gwanin ban sha'awa.


"na san ba kaji abunda ?an uwanka yayi maka ba,amma ina so kayi ha?uri kayi mashi uzuri" Abbah ya fa?a
"Abbah amma mi yasa kullum Al'mustafah yake ganin gazawata akan ?ar sa,ina iya bakin ?o?arina wajen ganin wani abu bai faru da ita ba"


"haka ne Ahmad,amma kafi kowa sanin halinshi,yanada saurin fushi ga zuciya musamman akan ?a?anshi shi kalar tashi ?addarar kenan shiyyasa nake son kuri?a yi mashi uzuri idan yayi wasu abubuwan,yanzu na san yana can hankalinshi duk ba'a kwance ba saboda rashin lafiyar ?iyarshi,da ?yar yau yayi bacci mai da?in,kayi ha?uri da ?addarar ?an uwanka"



"shikenan Abbah komai ya wuce a wajena, Allah ya bashi ikon cinye ?addarar shi"
"Ameen ya Allah,ya fama da mutane,ina fata komai yana tafiya daidai??"


"Alhmdllh Abbah komai yana tafiya yanda ya kamata"
"masha Allah,labari yana samuna har gida daga mutane daban daban,suna kawo man labarin yanda komai ke tafiya,kuma Alhmdllh naji da?in yanda kowa daya bu?e baki yake fa?in Alkairi a kanka,Na yarda da tarbiyyar ka da gaskiyar ka da ri?on amanarka,nasan yanda kake da tausayin talaka ina so Ahmad ka ?ara fiye da haka, kazama adalin shugaba kamar ?an uwanka,ina fatan yanda ?an uwanka yayi ya gama lafiya har yau ?asar nan bata manta da ayyukan Alkairin sa ba,ina so kaima kowa ya bu?e baki ya fa?i Alkairin ka ko bayan saukar ka"


"in sha Allah Abbah zaka sameni fiye da yanda kake tunani"
"haka nake son ji,Allah yayi jagora"
"Ameen ya Allah" fira su ka shiga yi Abbah na ?arfafa mashi gwiwa akan mulkinshi da bashi shawarwari.



Idan muka koma ?an garen su dady wani ?aton dinner hall su ka nufa dake cikin garden ?in,gaba ?aya zagaye yake da glass daga waje kana iya hangen abunda ke ciki,wasu irin zungura zunguran luxury dinner tables ne guda biyu masu ?auke da chairs guda ashirin akan kowane table,daga saman floor ?in wasu irin manyan crystal chandelier ne masu shegen kyau dogayen da su kamar za su sauko ?asa,gaba ?aya hall ?in a zagaye yake da manyan curtains masu matu?ar kyau an zuge su.



hall ?in an ?awatashi da wasu tukwanan ?asa dake ?auke da furanni masu matu?ar jan hankali,chefs ne maza da mata da a ?alla zasu kai su goma sai aikin jera warmers suke a saman tables ?in,cikin hall ?in dady su ka shigo bakin su ?auke da sallama.


da sauri chefs ?in su ka dakata da abunda su ke,cikin girmamawa su ka shiga gaishe su,da kulawa suke amsa masu,tunda su ka shigo suka sauke idon su a kan uncle Mustafa dake can zaune saman ?aya daga cikin kujerun dinner table ?in,ya ?aura ?afa ?aya kan ?aya sai aikin jijjigata yake,bini bini yake kallon wayar shi ha?i da jan tsaki.



dinner table ?in su ka nufa kwanansu kujera yaja ya zauna dady ne kawai bai zauna ba ya nufi uncle Mustafa,kujerar dake kusa da wacce ya zauna yaja ya zauna,dafa kafa?arshi yayi,saurin kallonshi uncle Mustafa da baisan da zuwanshi wajen yayi ba.


"yanzu Mustafa duk dan saboda ?arka ka shiga wannan yanayin?,
rashin lafiya ne ba wani abu ba amma duk kabi ka tada hankalin ka?"
"bazaka gane bane ya Tahir,ni ka ?ai na san yanda nake ji"
"taya zan gane tunda ni ban haifa ba, Al'mustafa ka rage wannan mugun son ?a?an da kake,duk kabi ka ?aurawa kanka damuwa saboda ?a?a sai kace kai ka?ai Allah yaba ?a?a,akan ?a?anka ba kaji baka gani,haba!?" ?an dakatawa dady yayi yana kallonshi kafin ya ?aura da cewa


"yanzu abunda kayi ma matar Ahmad kana ganin ka kyauta kenan,karka manta yanzu kainart ta tashi daga ?ar?ashin kulawarka ta koma hannunsu,sun fika iko da ita,sannan ina so ka sani ko babu Aure a tsakanin su Ahmad mai iya ri?e kainart ne haka Zaabith,ka zamo mai kawaici a kan ?a?anka"



tunda dady ya fara magana ?ala Uncle Mustafa bai ce ba sai yanzu
"kayi ha?uri ya Tahir in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba,hankalina ne ya tashi ban san wane irin ciwo take na"
"koma wane irin ciwo take Adu'a ya kamata kayi mata ba abunda kayi ba"
"in sha Allah zan kiyaye,kayi ha?uri"
"shi zaka ba ha?uri ba ni ba" Dady ya fa?a,waige waige uncle Mustafa ya shiga yi ko zaiga Uncle Ahmad


"yana waje tare da Abbah,kaje ka bashi ha?uri"
"to" uncle Mustafa ya fa?a yana mi?ewa ya fice daga hall ?in.

tun suna ?ananansu suna matu?ar girmama umarnin dady har kawo yau da su ka mallaki hankalin su kuwa.


tashi dady yayi ya nufi in da su uncle Ubaid su ke ya zauna,matan ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login