Showing 33001 words to 36000 words out of 67530 words
zaice mashi daga islamiyya yake da irin wannan shigar ya yarda,ta ina ma yayi kama da mai zuwa islamiyya.
"saboda ka ?auke ni shashasha kamar kai ko"
"wallahi ka tambayi yazdan daga can muke mun shiga gida ne muka canza kaya"
"in tambayi abokin cin
mushenka ko,zan kamashi ne shima"
"Allah ba ?arya muke ba"
"to naji, karanta man abun da aka koya maku yau ko ka kwana kana frog jump"
da ?yar ya ha?e yawu jin abunda ya naeem ?in yace,raba ido ya shiga yi kamar wanda yayi ma sarki ?arya
"oya kai nake saurare" ya naeem ?in ya fa?a fuska a tsuke yana har?e hannuwanshi a ?irji
nan fa ido ya raina fata,?an kame kame ya fara,ran ya naeem ne ya fara ?aci,cakumo kwalar rigar shi yayi yaja shi ?iiii zuwa waje,yazdan na ganin haka yayi saurin kwanciya cikin motar sai zare ido yake.
?aya daga cikin sojojin dake shawagi cikin Estate ?in ya Naeem ya kira,da sauri sojan ya ?araso,?ato ne bana wasa ba,daga bakin parking space zuwa bakin main entrance ?in shiga gidan ya Naeem ya nuna ma sojan
"ka sashi frog jump ko sau ?aya ya tsaya ka kirani"
"ok sir" sojan ya fa?an yana sakin murmushi dama rana irin wanann yake jira saboda yaron ya raina su kwata kwata baya ganin su da ?ima ya raina su.
barin wurin ya Naeem yayi ya nufi motar shi,shiga yayi,key yayi ma motar ya bar wurin.
"amma wallahi second father ya gama dakai FA'IZ,ya rasa wa zai sa ya hukunta ka sai wa?annan ?an iskan sojojin, tir wallahi" yazdan ya fa?a yana bu?e marfin motar ya fito
"oya start,ko yanzu na kira shi" sojan ya fa?a yana kallon Fa'iz ?in dake tsaye yana binshi da kallon ?as?anci
"an gaya maka tsoron shi nake ji ne?"
"wannan kuma matsalar kace,zaka fara ko sai na kira shi?" sojan ya fa?a yana zaro wayar shi daga Aljihu
"kai dallah malam dakata,ce maka a kayi bazan yi ba ne?"
"to fara idan ba so kake na kira shi ba"
tsaye Fa'iz yayi sai ?an kalle kalle yake,yana tsoron ya Naeem amma bai son ajinshi ya zuba a gaban securitys ?in gidan.
yazdan ne ya ?araso wajen shima sai layi yake kamar zai fa?i ?asa,kayan jikinshi iri ?aya ne dana Fa'iz sai dai shi kanshi kitso ne sa?anin Fa'iz dake da aski
"malam ai sai ka tafi ko" yazdan ?in ya fa?a yana ma sojan kallon rainin wayau.
"na tafi saboda kai ka sani ko?"sojan ya fa?a ,kallon fa'iz yazdan yayi su ka kwashe da wata ?ar iskar dariya "cewa za kayi na shan fura kake so,ai da kayi magana"
Fa'iz ne ya zura hannu cikin Aljihu ya ciro bandir ?in dollers ya watsama sojan yana jan hannun yazdan "zo mu tafi kaji"
ran sojan ne yayi matu?ar ?aci hakan yasa ya fisgo rigar Fa'iz ?in "kai har ni zaka wula?anta?" sojan ya fa?a
"an wula?anta ka,dama can kai ba wula?antaccen bane,maza ka sauke hannunka saman jiki na ko ranka yayi mummunan ?aci yanzu" Fa'iz ya fa?a dai dai jiniyar motocin sojoji na tunkaro gidan,da sauri Yazdan ya du?a ya kwashe ku?in.
mota biyu ce ta security guard ta nufo parking space ?in yayin da su ka sako wata ba?ar Nissan a tsakiyar su, parking motocin su kayi,da gudu security guard ?in su ka shiga fitowa suna nufar ba?ar Nissan ?in dake tsakiyar su, ?ack seat ?in motar ?aya daga cikin security ya bu?e.
Wata kaykyawar mata ce ta fito cikin shigar lafaya fara mai adon flowers ja,tasha adon zobba da sar?a na gold, high hills ne a ?afarta,cikin takun izza ta nufo in da su Fa'iz ?in su ke ,sojan na ganinta ya saki Fa'iz ?in yana ?an rissanawa ya gaisheta,ta?e baki Fa'iz yayi yana fa?in matsiyaci kawai.
murmushi su saki shida yazdan suna ?arasawa in da matar take, hugging ?in su tayi itama fuskarta ?auke da murmushi,raba jikinta tayi da nasu tana fa?in " 5 and 6 lafiya na ganku tsaye nan,mike faruwa??"
kallon sojan dake tsaye yazdan yayi "wannan matsiycin ne ya Naeem wai yasa yasa Fa'iz tsallan kwa?o" kallon sojan matar tayi "wai haka ne?"
"eh ranki ya da?e" sojan ya bata amsa,dubanta ta kai ga Fa'iz
"laifin mi kayi mashi yasa a hukuntaka?"
"momy babu abunda nayi mashi,kawai kin san ya tsaneni ne" girgiza kai matar tayi
"babu yanda za'ayi Naeem yasa a hukuntaka haka nan Fa'iz dole a kwai abun da kayi mashi,jeka kawai wajen aikin ka" ta fa?a tana kallon sojan
"to ranki ya da?e" sojan ya fa?a yana barin wajen,bai so Hajiya ta zo ba yaso yau ya koyama Fa'iz hankali amma idan ba yau ai akwai gobe.
cikin gidan su ka nufa ita da su Fa'iz ?in securitys ?in ta da PA ?in ta har sun biyo su ta dakatar dasu,ciki su ka shiga su yazdan sai zuba mata ?arya su ke wai sunyi broke gashi kwana biyu dady bai basu ko sisi ga motar su babu mai a ?asa suke takawa zuwa school,murmushi kawai tayi tana girgiza kai ta san ?arya su ke mata,hannu ta zura a jakar ta ciro bandir ?in ?an dubu dubu har guda shidda ta basu kowa uku uku,godiya su ka shiga zuba mata kamar tsaffin maro?a.
A main Parlor su ka rabu ta nufi part ?in mom su kuma su ka nufi part ?in mamy.
tun daga first parlorn mamy Fa'iz ya shiga ?wala mata kira
"mamy! mamy!! mamy!!!,wai ba kowa ne a gidan nake magana anyi man banza??" masu aikin gidan najin maganar shi su ka nemi wajen ?uya dan sun san muddin ya gansu sun shiga uku baijin kunyar ta?a jikin su a gaban kowa ko da kuwa mahaifiyar shi ce .
kitchen ?in part ?in ya fara le?awa ganin babu kowa ne yasa shi jinjina kai yana fa?in "?ana nan ?an iska basa nan kenan" ya fa?a yana nufar ?ofar bedroom ?in mamy.
A bakin ?ofa yaci karo da mamy doguwar rigar less ce a jikinta kanta babu ?an kwali gashin Attachment ?in ta har gadon bayanta kamar dai kullum,daga sama har ?asa ta shiga ?are mashi kallon kafin ta sauke idonta kan fuskarshi da sawun hannun ya Naeem ya fito ra?au.
"mamy wai ina ki ka shige ne sai ?wala maki kira nake?" ya fa?a yana layi kamar zai fa?o mata,saboda tsa?ar shaye shaye ko bai sha komai ba baya iya tsayuwa dai dai sai ka ganshi yana layi
"kai Ni da Allah karka fa?o man a ka,daga ina kake haka?"
"daga yawo"ya bata amsa a gadarance
"yawon iskanci ko, a can ma ka samu wani ya ?auke ka da mari ko?,wallahi Fa'iz ka shiga hankalinka dani,kai kullum burinka kaja man abun zagi ko dan ubanka"
shafa kumatun shi yayi "nifa ba abun zagin da nake ja maki,kuma wannan sawun marin da ki ka gani Naeem ne ya mare ni dan kawai na bigeshi ban gani ba"
"mari fa kace, wai tsayama wane Naeem ?in??"
"akwai wani Naeem ?in ne banda wanda ki ka sani"
"ya mareka dan kawai ka buge shi?"
"eh" ya bata amsa
"yana cikin gidan ko ya fita"
"ya fita" ya bata amsa
"idan ya fita ai uwar shi na nan" mamy ta fa?a tana dam?ar hannun Fa'iz ?in ta ja shi zuwa part ?in mom,dan suyi saurin isa ta corridor da zai sadaka da duk wani part dake second floor tabi,cikin ?an ?anin lokaci su ka iso part ?in mom Fa'iz sai fa?i yake ta sake shi amma ina...
_*Ep 15_16*_
*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*?????
______________________________
A saman sofa suka samu mom da matar data shigo,fizge hannunshi Fa'iz yayi, babu sallama babu Nocking mamy ta hau surfa masifa
"wallahi bazata sa?u ba bindiga a ruwa,bazai yiwu ko wane ?an iska yari?a dakar man yaro ba ehe" kusan a tare mom da matar data shigo su ka kai duban su ga mamy dake fama sirfa masifa, Yumnah da gudu ta fito daga ?akin mom.
"naga dai iskanci babu wanda baiyin shi,Allah na tuba akwai wanda akafi sani da iskanci sama da soja,wane irin iskanci ne nasu Bama gani a gidanan, ko kuwa wanda ke matse ?a?an mutane a office da sunan aiki ne ba ?an iska ba, ko wanda ya hai?e ma tsarar haihuwar shi da ?ananun shekaru ya kuma wanke ?afa ya koma can cikin nasara masu jan kunne dangi she?an ne ba ?an iska ba, ko mai yawan mashaya duk daren Allah ne ba ?an iska ba!!???"
daga mom har matar data shigo zuba mata ido su kayi kawai suna kallonta kamar wata mai ta?in hankali.
"to wallahi bazan yarda ba tunda ba wani yasha man wahalar haihuwa ba ehe" clapping hand taji anyi daga bayanta.
Da sauri gaba ?ayan su ka kai duban su ga dady dake tsaye can sama tun ?azu ya dafa handrail,tunda mamy ta shigo yake tsaye yana kallonta,wani irin mummunan fa?uwa gaban mamy ya shiga yi duk a tunaninta baya gidan.
parlorn dady ya nufo yana fa?in "da kyau uwar ?a,da kyau wacce ta iya haihuwar ?an kirki" ya fa?a yana ?arasowa in da suke.
Fa'iz shan jinin jikinshi yayi ganin irin kallon da dady ke mashi,yana ?arasowa in da yake ya ?auke shi da lafiyayyun maruka har sau biyu,da sauri ya dafe kuncin shi.
Mamy gabanta ne ya fa?i,nan ta shiga ?an kame kame da nufin ba dadyn ha?uri,wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata wacce ba ita da yayi mawa ba hatta su mom sai da ?an hanjin cikin su suka ka?a "yanzu ni na mareshi ko zaki rama mashi??"
Ya fa?a yana sake saukema Fa'iz ?in wani lafiyayyan marin "haba janar taya za kaita dukan yaron haka,ba fa shi yayi maka laifi ba"
"na sake marin shi dan na gwada maki iskancin soja kamar yanda ki ka fa?a"
dadyn ya fa?a a karo na uku yana sake ?auke fa'iz ?in da wani marin har sai da ya saki fitsari a wando, yumnah bata san sanda ta fashe da dariya ba, da sauri tasa hannu ta toshe bakinta gudun kar wani yajita.
"dan Allah janar kayi ha?uri, wallahi ba haka nake nufi ba"
"haka ki ke nufi mana,ai gwara na gwada maki iskancin sojan"
"dan Allah dady kayi ha?uri ba dan ni ba" fa'iz ?in ya fa?a hawaye na zobo mashi shar
"yiman shiru ko nayi ?asa ?asa da kai a wurin nan shashasha" da sauri fa'iz ?in yasa hannu yan kama bakin shi, kallo mamy dady yayi
"Mabaruka!!!" dady ya kira sunanta da kakkausar murya,jiki na ?ari tace
"Na'am"
"wannan ya zama na farko kuma na ?arshe da ?afarki zata sake takowa zuwa ?angaren zulaihart da sunan tujara ko rashin mutunci, Naeem yaya yake ga Fa'iz ya isa ya hukuntashi akan kowane laifi da yayi,daga yau idan ki ka sake tada jijiyoyin wuya akan Naeem ko wani a cikin ?a?ana ya hukunta ?anki, ina mai tabbatar maki zaki gamu da fushina wanda hakan bazai ta?a maki da?i ba kinji na fa?a maki"
"naji in sha Allah hakan bazata sake faruwa ba" mamy ta fa?a kamar da gaske,hanyar fita dady ya nuna mata ita da Fa'iz ?in
"maza kija ?anki ki ba mutane wuri"
kama hannun fa'iz ?in tayi sumi sumi su ka fice
kallon dady matar data shigo tayi "ina wuni ya Tahir, na sameku lafiya?"
"lafiya lau Salima ya mutanen gidan, ina ki ka baro man ?anina" murmushi matar ta saki tana fa?in " yana can yana fama da jama'a"
"ai dole ne, Allah dai yasa a gama lafiya" dady ya fa?a
"Ameen ya Allah"
"ki gaishe man da shi" dadyn ya fa?a yana nufar part ?inshi
"zaiji in sha Allah" matar ta fa?a tana kai dubanta ga mom
"ba mu gisaba, na same ku lafiya?"
"lafiya lau hajiya salima, ya kuma fama da jama'a"
"lafiya lau Alhmdllh,ashe kuma abunda ya faru da Asma'u kenan, to Allah ya kyauta gaba"
"Ameen ya Allah" mom ta fa?a
"da tare zamu zo da Kainart bata jin da?i ne shiyyasa bamu zo tare ba amma tana maki jaje"
"Ayya Allah sarki, ina amsawa Allah ya bata lafiya"
"Ameen summa Ameen"
?arasowa yumnah tayi cikin parlor
"momy shine baki zo man da su Ammar ba?"
"suna school ne yumnah"
"ke ki ka ma biye mata idan tana son ganin su ai ta san in da zata same su"
"ai kuwa dai, dan tunda yalla?ai yaci za?e ina jin zuwan yumnah Villa sau ?aya shima bata wani jimaba ta dawo"
?ata fuska yumnah tayi "school bata bari na saketa, kuma dokokin gidan gwamnatin ne momy sunyi yawa"
"kaji ja'ira banza lokacin da ku kuna gidan gwamnatin ai ba suyi maki yawa dokokin ba sai yanzu ko, kawai baki son zumunci"
"ba haka bane momy"
"to yaya ne?"
"ina nan zan zo kafin muyi resuming school"
"ina nan ina saurare Allah ya kawo ki lafiya"
"Ameen" tashi matar tayi tana fa?in
"bari na shiga ?angaren mabaruka mu gaisa"
"to nagode Allah ya bar zumunci, a gaishe man da Kainart ?in"
"za taji in sha Allah"
"momy sai na zo" yumnah ta fa?a
"Allah ya kawo ki lafiya" da Ameen ta amsa, har main parlor mom ta rakata, part ?in mamy hajiya salima ta nufa.
Mamy a lokacin da su ka fito daga part ?in mom, fiszge hannunshi yayi daga ri?on da tayi mashi
"mamy ai ga irinta nan sai da nace ki ?yale ni gashi nan yanzu kin ja man shan maruka, na san yanzu hankalin ki ya kwanta?"
"wallahi Allah ne ya ceceta da ace janar baya gida yau data gane kurenta"
ta?e fa'iz yayi " kullum haka ki ke cewa,kin ta?a ?aukar mataki a kan mom ?in ne ko da sau ?aya, wallahi mamy ina guje maki randa dady zai shuka maki rashin mutunci saboda matarshi"
"wane shi, ya dai shuka mata rashin mutunci"
"ai yanzu naga fa?an da yayi maki ita yayi mawa,wallahi mamy ki rage shige mata wallahi ko ?a?anta ba raga maki za suyi ba, ki bar ganin kowa ya zuba maki ido a gidanan kamar ana tsoronki, wallahi lokacin biye maki ne basu dashi amma duk randa ki ka kaisu bango abun bazaiyi kyauba"
"fa?a mata gaskiya fa'iz kullum abunda nake so ta gane kenan amma ta?i, wallahi mamy wannan abun da ki ke ida sirema dady ki ke, dan zubarma kanki da mutunci ki ke a gaban kowa muma kina ja mana" Fa'iza ta fa?a wacce fitowarta kenan daga bedroom ?in ta
baki mamy ta saki ta rasa har yaushe tayi lalacewar da Fa'iz da Fa'iza su ka rainata irin haka "ni ku ke fa?a ma haka dan uwarku?"
"gaskiya ce kuma daga ?inta sai ?ata, kai yazdan zo mu tafi muje kawai restaurant muci abincin a can" Fa'iz ya fa?a yana jan hannun yazdan su ka fice, Fa'iza ma shigewa tayi ?akin ta da kallo kawai mamy ta bisu.
duk wannan hargagin da take tana yi ne saboda su amma basa gani
"Allah ya wadaran naka ya lalace" ta fa?a tana nufar ?aya daga cikin sofas ?in parlorn ta zauna, masu Aiki dake la?e suna sauraron abun da ke faruwa ban da Allah ya ?ara babu abun da su ke.
hajiya salima ta shigo parlorn bakinta ?uke da sallama, da sauri mamy ta kai dubanta gareta,tashi tayi ta nufeta fuskarta ?auke da murmushi, hugging ?in juna su kayi.
"saukar yushe?" mamy ta fa?a tana jan hannunta su ka nufi sofa su ka zauna
"dama yaushe zaki ganni kinje kina tsula tsiyarki" mom salima ta fa?a
"wai da ke ce a parlorn, ni inama na lura da wacece ido a rufe suke ne raina ya ?aci"
"ai naga alama, wai dama mabaruka har yanzu baki daina hargagi da zulaihart irin wannan ba?"
"yaushe kuwa zan daina, ai idan kinga na daina to na sake sender ta ?asar su kamar shekarun baya" kallon baki da hankali matar ta shiga binta dashi.
"ke har yanzu kina tunanin zaki iya raba Tahir da zulaihart ne, to wallahi idan ma bacci ki ke tun wuri ki farka kar kije garin tsige igiyar Aurenta ke ki tsige taki a banza"
"ban gane ba, mi kike nufi"
"ko wannan matakin daya ?auka yau akan fa'iz a gabanki saboda zagin ?a?anta da ki ka yi ya isa yasa kiyi hankali kisan cewa da da yanzu ba ?aya bane"
"ni wallahi Hajiya salima kin barni a cikin duhu,dan ban gane inda maganar ki ta dosa ba"
" kin manta bala'in da ki ka shiga lokacin baya?, da ba dan mama Ameena ba da yanzu kina wani gidan ba wannan ba, idan zaki canza salon kishin ki ki canza idan kuma haka ki ke ganin ya fiye maki tam, shi dai ya?i ?an zamba ne"
jinjina kai mamy ta shiga yi alamar gamsuwa da maganar hajiya salima "shikenan naji zanyi ?o?arin ganin na sauya"
"hakan dai shi ya fi, ni na shigo ko gaisawa ba muyi ba,kin wuni lafiya?"
"lafiya lau, ya yau ban ganki da tawagarki ba?"
"ki bari kawai ni na hana su biyo ni nace suyi zaman su jaje zanje ba ?abbaka siyasa ba, ko security cewa nayi su jira ni a waje"
"kina sha'aninki ta wajen Ahmad, ai wallahi ni lokacin da janar na kan kujerar shugaban ?asa duk in da zani da tawagata nake zuwa ai shine girman"
"ban manta ba" matar ta fa?a, mai aiki mamy ta ?walama kira dan ta kawo ma hajiya salima ruwa da lemu.
"ai barshi kawai mabaruka nasha a part ?in zulaihart tafiya ma zanyi"
"nifa kinga abun da ke ha?ani dake kenan,dan mi zaki sha ruwa a wajenta"
"ni dai yanzu idan na sake dawowa na sha, amma yanzu kam gaba nayi"
"shikenan Allah ya nu na man lokacin da zaki sake dawowar" da Ameen hajiya salima ta amsa, a tare su ka mi?e ita da mamy.
har parking space mamy ta rakata, sai da taga tashin motocin ta tukun ta koma ciki.
*ASO VILLA*
Kusan a tare motocinta da motar da aka ?auko su Ammar daga school ta shigo.
A bakin main entrance ?in shiga part ?in su motocin su kayi parking, drivern da yayi driving ?in su ne ya fito ya bu?e masu,da gudu su ka fito suna nufar motar kakar tasu,suna isowa security na bu?e mata ?ofa ta fito.
da gudu suka fa?a jikinta "oyoyo granny,shine ki ka fita bama