Showing 12001 words to 15000 words out of 67530 words
motar ?afarta ta zuro kafin ta fito gaba ?ayanta,iska ta sha?a ta fesar, hannu ta zura ta ?auko hand bag ?inta, main entrance ?in duplex ?in ta nufa bayan ta rufe motar, sai ya mutse fuska take alamar ta gaji.
Wani madanni ta danna jikin ?ofar, nan take ?ofar ta bu?e, ciki ta kunna kai,mash Allah na furta a yayin da nayi arba da ha?a??en parlorn data shigo, komai na cikin shi ya kasance light brown, fa?a maku ha?uwa da tsaruwar parlorn ?ata lokaci ne,babu kowa a parlorn sai mai aiki dake ?an goge goge,jin ?arar bu?e ?ofa ne yasa mai aikin ?agowa, ganin wacce ta shigo ne yasa ta nufota da sauri,hannu ta mi?a da nufin amsar jakar dake hannunta tana fa?in
"good Afternoon ma" wani ?an iskan kallo mai ha?e da harara ta watsa ma mai aikin, saurin sadda kai ?asa mai aikin tayi tana ja da baya,tsaki taja tana nufar stairs case dake parlorn.
da kallo kawai mai aikin ta bita har ta ?acce ma ganin ta,ta?e baki tayi tana komawa kan aikin dake gabanta, a bakin ?ofar wani ?aki ta tsaya, tura ?ofar tayi ta shiga,wani ha?a?eb bedroom ne ta shigo komai na cikin shi ?an dai dai babu haya niya, ciki ta ?arasa tana kiran sunan
"Aunty laatifa! am home where are u" matashirya mata ta hango zaune kan study chair yayin da laptop ke a saman desk tana operating.
"Aunty nah sarkin aiki,a gidan ma baki huta ba, gaskiya mijinki ya shiga shiga uku na san a daren ku ma nafarko kwana za kiyi kina aiki, shiyyasa momy ke ce maki agogo sarkin aiki"
juyowa tayi masha Allah na fa?a da ganin wannan madarar kyan, laatifa kyakyawa ce ajin farko,riga da wando ne a jikinta masu taushi, kanta babu ?an kwali tayi parking gashinta a tsakiyar kai, medical glass ?in dake idonta ta cire.
"?anwata idan ban yi aiki ba mi ki ke so nayi?"
"gaskiya kina aje wa kina hutawa"
"shikenan, ya gajiyar aiki?" ya mutse fuska tayi yayin da take samun wuri bakin bed ta zauna
"aiki babu da?i" murmushi laatifa ta saki wanda ya ?arama kyakyawar fuskarta kyau
"gaskiya Balqis kin cika raki, miye abun gajiya a wannan aikin ke da kina bayan mota kina shan iskar Ac"
"haka za kice mana tunda ke kin saba, duk ranar dana sha court za kice haka"
"ba wai zan ce ba haka ne ma, kawai dai kin cika raki"
"shikenan naji ina al?awari na?"
"yanzun nan na gama tura mashi sa?o ta email kin san baya ?aukar kira ba tare da ka fara tura mashi sa?o ba"
"haka ne, amma ai ke naga kuna waya"
"wannan ai shi ke kirana, amma duk lokacin da ni nake son magana da shi sai na fara tura mashi sa?o tukun" ta?e baki Balqis tayi
"shi dai komai nashi na daban ne"
"classic boy ake fa?a maki dole komai nashi ya kasance unique,ke dai kawai ki dage da Adu'a dan akwai aiki a gabanki"
"ni kaina na sani Aunty laatifa abun har tsoro yake bani"
"karki damu nima zan tayaki da adu'a "
"in sha Allah, bari na tafi ?akin momy bata san na dawo ba, nan na fara shigowa"
"ok anjima zaki bani labarin yanda ?arar ta kasance"
"kin ma tuna man, wallahi dady ya ganni ba kiga harar da ya watsa man ba kamar ?an hanjin ciki na su fa?o" dafe ?irji laatifa tayi
"nashiga uku!! dan Allah da gaske ki ke"laatifa ta fa?a da tsantsar tashin hankali
"wallahi kuwa na san dole yaji ba'asin abun da ya kaini, amma zanyi duk yanda zanyi ganin bai gane ke ki ka tura ni ba"
"yawwa dan Allah kice ra'ayi ki ka yi ba ni nace kije ba"
"in sha Allah karki damu"
"yawwa na gode" ?ofar fita Balqis ?in ta nufa tana ?ara jaddadamata karta damu.
zama tayi bakin bed dafe kanta"ya Allah" ta furta,da alama hankalinta ba ?aramin tashi yayi ba jin dadyn su yaga Balqis.
Balqis tana fita daga ?akin wani ?an corridor ta nufa, wani ?an madaidaicin parlor ta shiga,a zaune take saman sofa mai mazaunin mutum biyu les ne a jikinta ?inkin half bubu da zani, hannunta da wuyanta sun sha adon zinari, wayace kare a kunenta da alama waya take
"lamari ai baiyi da?i ba, in sha Allah anjima idan Barrister ya dawo zan tambaye shi naje nayi mata jaje ai abun ayi jaje ne" murmushi Balqis ta saki tana ?arasawa cikin parlor.
fa?awa tayi saman jikinta"momy na dawo" da sauri ta janye wayar daga kunenta "ja'irar banza kin girma amma baki san kin girma ba, ba ki gani waya nake, karya ni ki ke son yi?" tashi tayi zaune tana turo baki"momy daga nayi kewarki zaki rufe ni da fa?a"
"an rufeki da fa?a, dan gidan ku haka ake kewa kina shirin karya ni"
"ke momy haka ki ke daga abun arzi?i sai ki rufe mutum da fa?a na san da dady ne bazai ce man komai ba"
"ai shi ki ka ce ?ashin shi ?wari ne gare shi" ficewa Balqis ?in tayi daga parlorn tana gungunai.
Mai da wayar tayi a kunne "kina jina da wannan ja'irar yarinyar tana neman karya ni"bana jin mi na cikin wayar ke fa?a
"to shikenan idan Allah yasa mun ha?u anjimar to shikenan, idan kuma bamu ha?u ba sai ranar friday kenan idan mun ha?u a part ?in Abbah" jinjina kai tayi kafin daga bisa ni su kayi sallama.
*UNITED STATE*
_*Las Vegas (Nevada)*_
_*Nailarh Racing Track (N.R.T)*_
?aton track ne gari guda wanda girmanshi zai kai girman wani babban ?auyen,kallo ?aya zaka ma wurin ka hango tsirarar dukiyar da aka kashe wajen gina shi,
ta ko ina ka duba mutane ne zazzaune a saman chairs gaba ?aya hankalin su naga wasan da ake gabatarwa,kowa burinshi nashi yayi nasara,duka mutanen dake wurin suna sanye ne da polo shirt white color wacce a gabanta a kayi rubutu da ?akin fenti in da aka rubuta QUEEN da manya haruffa daga saman shirt ?in logo ne na sunan center ?in ( N R T) sai p_cap da hat wanda suma aka rubuta QUEEN a jikinsu kamar na shirt ?in,maza ke sanye da p_cap yayin da mata ke sanye da hat wacce aka yi mata kwalliya da gashin tsintsaye a samanta, Al'adar wurin wasan ce duk wanda zai shiga sai an bashi wannan shirt da cap ya sa wanda kyauta ce daga mamallakiyar wurin wasan.
dawakai ne kyawawan gaske ke gudu a tsakiyar filin,yayin da mamallakansu ke saman su jikin su sai sal?i yake yana ?aukar ido,color uku ne dawakan wasu brown yayin da wasu su ka kasance ba?a?e doki ?aya ne a wurin ya kasance white color,daga yanayin tsarin dokin zaka san na musamman ne, a jere su ka fara gudun,cikin ?warewa da karsashi dawakan ke gudun abun gwanin ban sha'awa,abun dai sai wanda ya gani,rabuwa su ka fara yi da junan su, dawakai uku ne su kayi gaba yayin da su ka bar sauran a baya harda wannan farin dokin yama fisu yin baya sosai sama da sauran dawa kan,sosai su ke gudu dan kaiwa ga matsaya,mi?ewa tsaye mutane su ka fara yi da alama dawakan nan gudu uku na daban ne, mutane na da buri a kan su.
Wasa fa ya fara ?aukar zafi dawakan kansu su ukun sun rabu da juna yanzu biyu ne a gaba ?ayan a baya.
"da alama dai yau tarihin N R T zai canza, ban ta?a ganin wasa irin wannan ba" cewar wani bature dake zaune cikin ?an kallo, murmushi gefen baki mace dake gefen shi ta saki tana fa?in
"ba abu bane mai yuwuwa canza tarihin N R T cikin sau?i, a ko wane lokaci da sabon salo take zuwa, kana tunanin wannan baya bayan da tayi babu wata a ?asa?" ta?e baki yayi yana ?aga kafa?a
"i don think,tazarar tayi yawa duba kiga in da su Ryder su ke kalli in da king yake"murmushi matar ta saki
"dear sai kace yau ka fara zuwa kallon wasan N R T"
"ba yau na fara zuwa ba, but wasan yau ne ban ta?a ganin irinshi ba"
"to ka zuba ido za kace na fa?a maka"
"okay" ya fa?a yana mai da glass ?in shi daya cire.
ran wani magidanci ne daga cikin ?an kallo ya fara ?aci,sign matar wannan baturen tayi mashi, duban shi ya kai ga mata da majin
"bazan ta?a ?yale Anthony ba idan har ku?ina su ka lalace" ya fa?a da alamar ranshi ya ?aci"but why?" matar shi ta tambaya
"babu alamun zanyi nasara,kin kuma san dama ba da san raina na zuba ku?i na a wasan nan ba, idan har ku?ina su ka salwanta bazan ?yale shi ba"
"just bcox of five hundred thousand dollars kake wannan maganar akan brother nah?"
kallonta yayi da mamaki"its not a money?"
"no it's money, but ai kafi ?arfin su, kuma banyi tunanin zaka iya furta wannan maganar akan Anthony ba"
"it's not my concern,ku?ina kawai na sani"
"sai ka bari idan kaga ba kayi nasara ba sai ka fa?i duk abun da zaka fa?a,ai har yanzu wasan ake"
murmushi takaici mutumin ya saki
"oh wai kina nufin har yanzu kuna da sa rai a wannan wasan,?azamin tunani kawai" ya fa?a yana kauda kanshi gefe, ha?a ido su kayi da wannan matar da mijinta, a tare su ka sakar mashi murmushi suna ?aga mashi hannu, shima hannun ya ?aga masu yana maida kanshi ga wasan.
Murmushi matar tayi"mi na fa?a maka kowa ya san cewa canza tarihin N R T ba abau bane mai sau?i, ka dai ji wance magidanci ya saduda ta ?an ku?a?en shi kawai yake" ta fa?a tana sakin murmushi, murmushi shima mijin nata yayi yana jinjina kai da fa?in"na tabbata...
_*Episode 7_8*_
*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*?????
_____________________________
Murmushi matar tayi"mi na fa?a maka kowa ya san cewa canza tarihin N R T ba abau bane mai sau?i, ka dai ji wance magidanci ya saduda ta ?an ku?a?en shi kawai yake" ta fa?a tana sakin murmushi, murmushi shima mijin nata yayi yana jinjina kai da fa?in"na tabbata"
mai da hankalin su su kayi akan wasan,wasan ne ya fara canza salo kamar wal?iya sai ga dokin dake baya sama da ko wane doki ya zama shine a tsakiyar dawakai biyun dake gaba, kamar a mafarki masu kallon wasan ke kallon ikon Allah,tashi wannan magidanci yayi yana jan tsaki ya kalli matar shi
"kin dai ji abun dana fa?a maki sisi na ban yarda tayi ciwo ba" yana gama fa?a ya bar wurin gaba ?aya, ta?e baki matar tayi ita har a lokacin ba taga wani alamar rashin nasara ba tunda dai ba'a gama wasan ba.
fita dokin yayi daga cikin jerin dawakai biyun daya shiga ya zama shine ke biye da dokin dake gaba sai dai akwai ?ar tazara a tsakaninsu,sosai dawakan ke gudu cike da karsashi suna tunkarar matsayar wasan in da ya kasance nan ne ?arshe duk wanda ya riga isa shine ya lashe gasara.
hankalin mutane dake sa ran cin gasar ne yayi matu?ar tashi, tuni zufa ta shiga wanke wasu daga cikin su saboda ma?udan ku?in da su ka zuba wanda suke ganin suna gab da yin asara,seconds Biyar ya rage a kammala wasan,bai wuci taku ka?an ya ragema dokin dake gaba ya isa matsayar wasan, kamar wal?iya wannan farin dokin ya gita ta gabanshi ya riga shi isa matsayar, da sauri ma hayin dokin yaci birki rai a ?ace ga ci yana gani amma ya rasa.
Ihu da sowa ne ya fara tashi a wurin wasan ha?e da ki?e ki?e, a fusace ?ai ?ai kun mutane su ka fara tashi suna barin wurin wasan,birki dokin yaci cike da kuzari mamallakin dokin ya sauko, da sauri wasu matasan ?an mata su biyar suna sanye da riga da skirt iya gwiwar su, rigar white color yayin da skirt ?in ya kasance black color a?alla kowace a cikin su zata kai kimanin shekara 28 zuwa 30,cikin filed ?in su ka nufa a gaban wannan dokin su ka tsaya ?aya na ri?e da water bottle yayin da wata ke ri?e da ?an ?aramin towel wacce tafi kowa girma a cikin su ce take goye da backpack sauran biyu babu komai a hannun su sai sakin murmushi su ke, wani matashi sauarayi ne ya amshi dokin, helmet ?in dake kanta wacce aka rubuta Queen a jikinta ta zame tabarakallahu ahsanul kali?in na furta da ganin wannan ma?urara kyan.
fara ce tas doguwa kyakyawar gaske wacce idan akace kyau to fa anazuwa kanta an rufe babin kyau,tana da idanuwa masu matu?ar jan hankali launin Acme white grey sai she?i su ke ga zira ziran eye lashes ?inta da su ka ?ara ?awata su,tana da siraran la??a launin light pink masu matu?ar taushi tana da ?an tsayin fuska hancinta a tsaye yake kem,tana da cikar gashin gira sai dai ba sosai ba,kanta ta ?an girgiza yayin da take zame ?an ?aramin ribbon ?in data ?aure gashin kanta nan take wavy hair ?inta launin light golding brown ta tarwatse a gadon bayanta ,tana da shape mai matu?ar ?aukar hankali skin ?inta sai she?i take tana sal?i kamar hasken rana bai ta?a ra?arta ba.
kissing neck ?in dokin tayi tana ?an sakin murmushin gefen baki har sai da dimples ?inta su ka lotsa sosai murmushin ya ?arama kyakyawar fuskarta kyau
"madam water"?aya daga cikin matan ta fa?a tana mi?a mata water bottle ?in dake hanunta mai kyan gaske wacce a jikinta aka rubuta Queen, ya mutse fuska tayi ba tare da ta ko kalli in da matar take ba,wacce ke ri?e da towel a hanunta ce ta matsa kusa da ita dadda?an ?amshin turaren ta ne ya daki hancin matar har sai da ta lumshe ido duk da zufar da tayi haka bai hana dawwamamman ?amshinta fita ba, a hankali ta shiga goge mata zufar da tayi,jefi jefi mutane su ka shiga ?arasowa cikin field ?in suna mata congrat yayin da take ya mutse masu fuska ba tare da ta amsa masu ba hakan bai dame su ba saboda sanin halinta sunma samu sa'a yau da har ta tsaya harma take yamutse masu fuska.
barin wurin matashi yayi da dokin, ?aga ma dokin hannu ta shiga yi tana fa?in" i miss u" murmushi matan su ka saki,fly kiss ta ma dokin tana sakin murmushi,bata bar wurin ba har sai da ta daina ganin dokin tukun ta bar wurin yayin da matan ke biye da ita har gaban wasu motoci guda bakwai,guda shidda rang robbers ne yayinda su ka saka wata farar Rolls Royce tsakiyar su sai ?aukar ido take,body guards ne tsaye a bakin motocin A?alla za su kai su biyar ban da drivers ?in da da su kayo driving motocin,cikin girmama su ka shiga gaishe da ita suna tayata murnar lashe wasan, babu wanda ya samu arzi?in data amsa mashi sai ma nufar wannan fara rolls royce ?in dake tsakiyar motocin tayi, da sauri ?aya daga cikin su ya bu?e mata back seat ta shiga,komawa su kayi cikin motocin harda wannan matan,a jere su ka hau wani dogon titi a cikin wurin wasan.
A kishingi?e take a cikin motar ta lumshe idanunta yayin da sanyin Ac ke ratsata, tafiya mai ?an nisa su kayi kafin su ka nufo wani katafaren gate ga wasu irin jibga jibgan security guard a bakin shi, horn driver dake gaba yayi, babu ?ata lokaci security guard ?in su ka bu?e masu gate,da gudu motocin su ka kunna kai ciki security guard ne ke kai kawo ta ko ina na wurin, titi ne su ka sake mi?ewa shantal, wani ?an ?aramin gate na ?akin ?arfe wanda ya kasance shara shara kana iya hange ciki su ka nufo, wani remote driver dake gaba ya danna nan take gate ?in ya bu?e ciki su ka kutsa kai ciki.
masha Allah na furta da ganin irin ha?uwar wurin ,?atafaren luxury skyscraper ne iya ganinka, ta ko ina ka kallah a jikin ginin gilasai ne masu matu?ar ?aukar ido A ?alla yana da sassa guda shidda,harabar gidan kanta abun kallo ce lion water fall ne a tsakiyar gidan yayin da yake fitar da ruwa da styel daban daban, security guard ne ke kai kawo a ko ina na harabar gidan.
A bakin skyscraper ?in su kayi parking da sauri ?aya daga cikin security guard ?in ya fito ya bu?e mata car door,?aya bayan ?aya su ka shiga fitowa,gaba ?aya matan gaban motar da take ciki su ka zo su ka tsaya, a hankali ta zuro ?arta kafin ta fito gaba ?aya, security guard ?in dake kai kawo ne su ka shiga rissinawa suna gaishe da ita, hannu kawai ta ?aga masu kafin a hanzarce ta nufi gidan matan nan na take mata baya,a bakin main entrance ?in gidan suka tsaya,wata irin ha?a?iyar ?oface ta glass,sai ta fuskarta tayi a jikin wata na'ura dake manne jikin ?ofar wacce nake kyautata zaton face ID ne magana na'urar ta fara cikin harshen turanci
"welcome back home miss NAILARH"
zugewa ?ofar ta shigayi, kutsa kai su kayi ciki, wani katafaren parlorn ne su ka shigo,painting cikin shi sliver glod ne, an ?awatashi da manya manyan sofas jigunannun gaske masu matu?ar taushi da da?in zama set hu?u sai throw pillows dake kan ko wace sofa, daga tsakiyar parlorn round glass table ne an jera flower vase masu matu?ar kyau, daga saman ceiling ?in ginin crystal chandeliers ne golding color masu girman gaske an ?awata su da kwalliya, sai faskekiyar flat creen tv mai matu?ar girma ta mamaye kusan rabin bangon da take sai kayan sauti dake gefe da gefen tv, sparkling floor lamps ne ajiye a ?asa suna bada haske mai launika daban daban, ga dogayen curtains wanda aka ?awata da zanen furanni kewaye da parlorn an zuge su,idan ka kalli ?asan parlorn wanda ya kasance na glass wasu irin kifaye ne masu launika a jikin su suke shawagi.
komai na cikin parlorn golding color ne hatta stairs case ?in dake ciki,A ?alla floor