Showing 18001 words to 21000 words out of 67530 words
wave hair ?inta har gadon bayanta ya sauka, gashin duk ya ?an yamutse saboda bai samu gyara kwana biyu ba,sannu fa'iza ta shiga yi ma mata yayin da take binta da kallon ba ?aramin tafiya da ita kyan nainarh yayi ba yarinyar ce Allah ya zuba mata kyau ko mace ?ar uwarta ta kalleta sai ta sake kallon, hijab ?in ta dake kan bed ?in ta ?auka ta zura a jikinta.
"muje"fa'iza ta fa?a, gaba nainarh tayi fa'iza na biye da ita, a hankali take taka ?asa kamar zata fa?i saboda rashin ?warin jikinta,tunda su ka shigo parlor momy da laatifa ke bin nainarh da kallo har su ka ?araso ciki, wurin mom nainarh ta nufa tana fa?in mom gani, momy ta nuna mata tana fa?in "ga momyn su laatifa nan kun gaisa" sai a sannan nainarh ta kai dubanta ga momy.
gaishe da ita tayi cikin kulawa momy ta amsa mata tana fa?in" ya jikin ki naji ance ba ki jin da?i"
"da sauki Alhmdllh" ta fa?a, gaishe da laatifa tayi cikin kulawa laatifa ta amsa mata Balqis tunda su ka shigo parlorn kallo ?aya tayi ma nainarh ta ?auke kai
"amma kin sha magani kuwa?" laatifa ta fa?a cikin nuna kulawa
"A'a" nainarh ta fa?a tana nufar rug carpet zata zauna saboda wani jiri da take ji, da sauri momy ta nuna mata kusa da ita tace ta zauna.
sannu su ka shiga jera mata mom na fa?in"bari idan IRFAN ya shigo ya duba ki, yumnah kira man shi a waya kice nace idan ya taso daga aiki ina son ganin shi"
da to yumnah ta amsa tana ?aukar wayar ta ta shiga contact, number Irfan ta shiga nema, dialing number tayi ringing ta shiga yi har ta katse bai ?aga ba, sake kira tayi sai da ta kusa katsewa ta samu sa'a yayi picking,sallama tayi tana gaishe da shi babu wanda ya amsa mata daga ciki sai cewa yayi" lafiya ki ke man irin wannan kiran?"
shagwa?e fuska yumnah tayi kamar tana a gaban shi
"dama mom ce tace idan ka ta so daga aiki ka shigo gida tana son ganinka" rejecting kiran yayi kawai ba tare da yace komai ba, ta?e baki yumnah tayi.
masu aiki ne su ka shigo hannun su ?auke wooden tray, soft drinks ne da ruwa masu sanyi ha?e da glass cups, cikin parlorn su ka ?araso bakin su ?uke da sallama, amsa masu sallama su kayi,ajiye tryas ?in su kayi saman glass round table ?in dake parlorn, ficewa su kayi, fa'iza ce ta shiga zuba masu ruwan da lemu ta mi?a masu.
masu aikin suna fita daga parlorn ?aya kitchen ta nufa yayin da ?aya ta nufi elevator, da sauri ?ar uwarta tace"munirat ina za kije?"
"part ?in mamy "wacce aka kira da munirat ta fa?a, girgiza kai wacce ta kira munirat ?in tayi tana fa?in
"munirat ina rabaki da kiwan kyalla kina akuya ta haihu, wallahi ki daina shishige ma mamy, dan wallahi za kiyi da kin sani dan ita ba'a mata gwaninta ina guje maki ranar da zata shuka maki rashin mutunci"
"banji bakin ki ba, kuma ni bani ke shishige mata ba itace ke jana a jiki"
"na dai fa?a maki dan idan baki san abun da ya faru da baaba jummai ba gara tun wuri ki sani"
"ni dai naji,yanzu zan dawo" ta fa?a tana daddana madannan dake jikin elevator, girgiza kai kawai ?ar uwar tata tayi tana nufar kitchen...
_*Episode 9_10*_
*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*?????
______________________________
A kishingi?e take saman makeken king size bed ?inta ta ?auki wankan rantsatsiyar shadda white color anyi mata aiki da red color ?in zare, fuskarta tasha make_up a ko wane lokaci zaka samu hannuwanta da wuyanta da ?afarta cikin adon gold ko zinari, kanta babu ?an kwali gashin Attachment ?in dake kanta ya sauka har gadon bayanta,wayarta ce a hannunta tana aikin daddanawa.
Nocking ?ofar bedroom ?in a kayi,yamutse fuska tayi cike da izza tace "waye?"
?an ?aga murya munirat dake tsaye bakin ?ofar tayi "munirat ce mamy"
"ke da waye ne?" mamy ta fa?a
"ba kowa ni ka?ai ce"
"ok shigo"mamyn ta fa?a.
a hankali munirat ta turo ?ofar ta shigo bakinta ?auke da sallama,?aremata kallon mamy ta shiga yi tun daga sama har ?asa, a bakin bed ?in ta tsaya,cike da girmamawa ta dur?usa har ?asa ta gaishe da mamy.
?in amsa mata mamy tayi sai ma cewa tayi "ina sauraronki mi ya kawoki ?akina?"ta fa?a tana wani yamutse fuska.
"dama zuwa nayi na sanar dake hajiya maimunatu matar yalla?ai hashim ta zo ita da ?a?anta suna part ?in madam zulaihart"
"mi su ka zo yi"mamy ta fa?a tana wani tsuke fuska
"nima ban sani ba amma ina tunanin sun zo yima madam jaje ne"
jinjina kai mamy tayi"naji da?in jin wannan labari da ki ka zo man dashi, abunda nake so dake ki sa man ido akan kowa dake part ?in komai ki ka gani ki sanar dani, komai ?an?antar abu ki sanar da ni"
"in sha Allah madam" jinjina kai mamy tayi"yawwa haka nake son ji, tashi ki tafi bana son janar ya shigo ya sameki, zan tura maki sa?on ki ta waya" mi?ewa munirat ?in tayi "nagode sosai Allah ya ?ara girma"ta fa?a tana nufar ?ofar fita ta fice.
tsaki mamy taja tana fa?in"munafuncin banza ko miye abun zuwa jaje in ba tsabar tsugudidi ba" mamyn ta fa?a tana sake jan wani tsakin.
wayarta ta ?auka tayi dialing wata number, bugu biyu a ka yi picking, murmushi ta saki yayin da take kara wayar a kunenta.
"Allah ya taimaki first lady,hutawar ki lafiya hajiyar yalla?i Ahmad"mamy ta fa?a ta na sakin dariya,on the other hand ta cikin wayar itama dariya ta saki.
"kullum da kalar tsokanar da ki ke zuwa MABARUKA, yau kuma ni ki ke ma wannan kirarin?"
"ai kin can canta ne, ya ki ke ya kwana biyu?"
"Alhmdllh, fatan kema kina lafiya, ina madam ?inki take?"
ta?e baki mamy tayi "tana nan kamar yanda ki ka santa,ban ma baki labari ba"
"ina jinki mi ya faru?"
"uhmm ina wannan shari'ar da suke akan ?awarta wannan munafukar hajiya Asma'un?"
"eh na gane ,?azu naji WASEEF na mata jaje wai an yankema hajiya Asma'u hukuncin ?aurin rai da rai"
"eh ashe kinji?"
"naji waseef na mata jaje kin san ni ba ma'abociyar bibiyar labarai bace"
"ai kuwa kamar yanda ki ka ji an yanke mata hukuncin ?aurin rai da rai"
"tab! Allah ya kyauta gaba,ki ce yau ku baku ba walwala"
"bata ba walwala dai, kema kin san babu abun da zai hanani walwala dama abun da na da?e ina jira kenan dan wallahi ba ?aramin jin haushin Asma'un nan nake ba"
dariya mai ?an sauti ta cikin wayar ta saki "duk da haka da kinyi mata kara ai zaman tare baice haka ba"
"wa ni? Allah ya ki ya ye dama ta dawo magana na samu na nannausa mata na san sai ta da ?e tana damunta"
dariya ta cikin wayar ta sake saki "gaskiya mabaruka baki da kir ki, mai makon ki taya ta ja je shine zaki ?ige da gaya mata magana"
"Allah ya ki ya ye ai ga abokan cin mushenta can ?ayar har ta zo wai ja je ?ayar munafukar ma na san tana nan zuwa anjima"
"baki da dama mabaruka, nima anjima ko gobe zan shigo nayi mata ja jen"
ta?e baki mamy tayi"ai da yake ke akwai kara a tsakanin ku"
"to ya zanyi tunda Allah ya ha?a Auratayya a tsakanin ?a?an mu dole ne zumunci ko bama so"
"Allah ya kawo ki lafiya" da Ameen ta cikin wayar ta amsa, sallama su kayi.
wata number mamy ta sake dialing, ringing wayar ta shiga yi, sai da kiran ya kusa katsewa sanann a kayi picking, murmushi mamy ta saki tana fa?in
"kaga abun gidan janar, halama bacci ki ke nake kira ba'a picking in time"
on the other hand ta cikin wayar tace "ina fa na shiga kitchen ne wurin masu aiki, kin san idan baka sa masu ido sai suyi maka shirme"
murmushi mamy ta saki" kice kina can kina gasa masu aya a tafin hannu dan na san halinki ba sau?i ne dake ba"
"duk rashin sau?ina na kai ki ne?"
"ai wallahi masu aikin ne sai da jan ido, idan kayi sanya sai su kawo maka raini"
"haka ne kam,to ya gidan, ya kwana biyu fatan kina lafiya??"
"lafiya lau Alhmdllh, ya naki gidan"
ta?e baki mamy tayi" yana nan yanda ki ka san shi sai ma abunda ya ci gaba" murmushi ta cikin wayar ta saki
"ki ce kina nan kin hana dangin nasara masu jan kunne sakat"
"mi za'a fasa, ai in dai ina raye ta shiga uku"
"Allah ya shirya man ke ?awata, ki zo ki samu mata a har gidan mijinta ki hanata rawar gaban hantsi"
"tama isa, wanda yace tayi sakacin da mijinta yayi mata kishiya"
"kina sha'aninki ta wajena, wai ni kam ?azu nake gani a TV an yanke ma ?awarta hukuncin ?aurin rai da rai"
"eh Allah yayi maganin ?ayar munafukar saura manyan, kin san kuwa ?ayar harta kwaso ?afa ta zo jaje??"
"wa ki ke nufi?"
"wacece kuwa ban da uwar ?an tausayi maimunatu" tsaki ta cikin wayar taja
"munafukan banza kawai, na san ?ayar munafukar ma tana nan zuwa"
"wannan a rubuce take sai ta zo"
"wallahi haushi hajiya maryam ke bani, sai girman kan masifa"
"ai wallahi bake ka?ai take ba haushi ba, wani lokacin idan tana hura hanci tanama mutane kallon banza ji nake kamar na rufeta da duka"
"ke dai ki bari mai abun duniyar ma batayi ji da kai ba sai ita"
"za ki shigo anjima?" mamy ta fa?a
"mi zan zo nayi"
"ai nayi tunanin ko zaki zo mata ja je"
"wa ni? Allah ya ki ya ye, lokacin da hajiya Asma'un zata kashe mijinta shawara tayi dani da zan zo mata ja je, ai in kin ganni lahira to kaini a kayi"
dariya mamy ta saki "shiyyasa nake sonki ?awata, yanzu na gama waya da hajiya SALIMA ta ce zata zo"
"ita ki ka ce ji tayi zata iya"
"ai kin san so akwai ala?a mai ?arfi a tsakanin su"
"wace ala?a?, daga ?anta na Auren ?iyarta shikenan ko dan IRFAN na hannun mijinta, ni ba NAEEM bane ke Auren NAFISAT, ke ni bazan iya ba ala?ar Aure ma dake tsakanin nafisat da naeem dan bani da yanda zanyi ne amma wallahi da ba'ayi Auren ba"
"nima dai haka na gani"
"rabu da ita kawai sai mun ha?u ranar juma'a a part ?in Abba"
"ok Allah ya kaimu" da Ameen matar ta amsa sallama su kayi.
?????????? ????????????????
Mom da momy ne kawai babu a parlorn, Yumah na kusa da laatifa sai zuba mata zance take yayin da balqis da fa'iza ke zaune saman sofa suna firar yaushe gamo.
tashi Nainarh tayi ta nufi bedroom ?in Yumnah,da sannu su laatifa su ka bita balqis kuwa banda binta da kallon tsana babu abunda take, haka nan taji bata son Nainarh ita kanta bata san dalili ba amma taji ta tsaneta.
Sallama su ka ji daga bayan su da sauri su ka kai duban su ga matar dake shigowa, ta ?au wanka ba?ar Abaya tayi rolling da gyalenta,da gudu Yumnah ta nufeta hugging ?inta tayi tana fa?in"momy kema ashe kina hanya" murmushi matar ta saki tana raba jikin su
"wani ya zo kenan da har ki ke tunanin nima ina hanya" murmushi Yumah ta saki "momy ma ta zo tare da su Aunty laatifa" ta fa?a yayin da su ke ?arasowa cikin parlorn, cike da girmamawa su laatifa su ka shiga gaishe da matar tana amsa masu cikin kulawa yayinda take hugging ?in su ?aya bayan ?aya.
"su mom na garden ita da momy" Yumnah ta fa?a
"ok bari na ?arasa wajen su" ta fa?a yayinda take nufar sliding door dake parlor wacce daga nan kana iya hangen cikin garden ?in da kusan zagaye yake da gidan.
shuke shuke ne a cikin a garden ?in masu matu?ar ?aukar hankali da ban sha'awa,ga grass carpet dake malale a cikin garden ?in,?aton swimming pool ne a cikin garden yayinda aka ?awata gafe da gefenshi da lounger chairs da deck chair masu kyan gashe domin zama,ducks ne ke shawagi a cikin swimming pool ?in farare tas da su,daga can gefen swimming pool ?in wasu rukunin bishiyu ne masu matu?ar ?aukar hankali sunyi rukuni,peacocks ne masu kyan gaske ke yawo tsakanin bishiyun,babu kalar tsuntsun da babu a cikin garden ?in.
A tsakiyar bishiyun mom Maryam ta hango mom da momy kishingi?e saman rug sun yi matashi da tum tum yayin da aka cika masu gaban su da fresh fruit cikin kwandon kaba ha?e da snacks da soft drinks masu sanyi.
Momy ka ?aice ta ?an gatsi Apply yayin da mom ta zuba ma ducks ?in dake shawagi cikin ruwa ido,damuwar halinda Aminyarta take ciki ce duk ta isheta ,bata so duniya ta juya mata baya lokaci guda ba.
"ki kwantar da hankalin ki barisster in sha Allah babu abun da zai faru da Asma'u,ina sha Allah zata ku?uta su kuma wanda su kayi silar jefata cikin wannan halin da izinin Allah asirin su zai tonu"
Ajiyar zuciya mom tayi
"babu abunda yafi ?aga man hankali sama da yanda jami'an tsaro da mutanen gidan su ka kafe akan ita ta kashe shi, ni na san wacece Asma'u ko dabba bazata iya kashewa ba bare ?an Adam"
"nima a iya sani na da ita bazata iya aikata wannan babban laifin ba amma in Sha Allah gaskiya za tayi halinta"
"ina fatan haka"
fuskarta ?auke da murmushi ta ?araso in da suke, sallamarta su ka ji daga bayan su ,da sauri su ka kai duban su gareta, murmushi su ka sakar ma juna yayinda su ka mi?ewa, hugging ?in juna su ka shiga yi cike da kulawa suke gaishe da junan su,kalar ta su gaisuwar kenan a duk lokacin da su ka ha?u da juna.
saman rug ?in su ka koma su ka zauna,sake gaisawa su kayi
"ya kuma mu ka ji da abun da ya faru da Asma'u" mom Maryam ta fa?a
"sai godiyar Ubangiji" momy ta fa?a
"Allah ya ku?utar da ita"
"Ameen ya Allah" mom ta fa?a yayin da take ?aukar sherry glass cup ta zuba ma mom maryam drink mai sanyi, mi?a mata tayi , murmushi mom Maryam ta saki ya yinda take amsar cup ?in.
shiru ne ya gitta a tsakanin su,kowa da abunda yake sa?awa a ranshi ba kamar mom da kwata kwata bata cikin walwala,mom maryam ce ta katse shirun na su.
"amma barisster kin ?auki wani mataki a kan shari'ar nan?" ta fa?a ya yinda take ajiye cup ?in dake hannunta.
"ban fahimci ya ki ke nufi ba ,wane mataki zan ?auka??"
mom ta fa?a cikin rashin fahimtar Abun da mom maryam ?in take nufi.
"ai nayi tunanin zaki sa ayi maki bincike na daban akan case ?in,idan Allah yasa aka dace kinga ba sai a tada shari'ar ba tunda hukuncin ?aurin rai da rai ne"
"wane bincike zan sa ayi bayan wanda barisster Hashim yayi"
yana yin fuskar mom maryam me ya canza "uhmm barisster hashim fa ki ka ce?"
"eh shine lawyer dangin marigayi ,duk wani bincike da ya kamata ayi yayi"
"kenan kin yarda ita ta kashe mijinata?"
"A'a sai dai na san barisster ba zai fa?i abunda ba shikenan ba, kuma bana zargin zai ha?a kai da kowa dan kawai yayi nasara a kaina"
girgiza kai mom maryam tayi,mom Maimunatu na kallon su ?ala ba tace ba
"am sorry hajiya Maimunatu ba wai ina zargin barisster ba ne" murmushi kawai mom Maimunatu tayi ko zargin barisster su ke ya za tayi halin mijin nata ne dole a zargeshi.
"mu duka mun san cewa barisster baya ?aunar zulaihart tun fil'azal, ni bana zargin zai iya ha?a kai da wasu dan dai kawai ya cika burin shi akan barisster,amma ?ara binciken da za kiyi yanada matu?ar amfani ni a nawa tunanin amma ya ku ka gani"
shiru mom tayi tana tsunduma duniyar tunani ta wani ?an garen hajiya maryam na da gaskiya sai dai bata son ta binciko ma kanta abunda zai hanata zaman lafiya duk da har zuciyarta bata zargin Aminyarta zata aikata laifi makamancin haka.
"maganarki gaskiya ce hajiya maryam,?ara binciken yanada amfani,sai dai waye zaiyi binciken?" mom Maimunatu ta fa?a
"haka ne ?ara binciken yanada amfani, Allah yasa ya zama sanadiyyar tonuwar asirin duk wanda ke da sa hannu,sai dai ta maganar Maimunatu wa zan sa yayi man binciken?" mom ta fa?a
"yawwa burina dama ku fahimce ni, maganar kuma wanda zaiyi binciken ba matsala bace karku manta gidan nan cike yake da jami'an tsaro kala kala samun wanda zaiyi bincike ba abun bane mai wahala NAEEM ma zai iya tunda dama aikin shi ne"
jinjina kai su kayi da alama sun aminta da maganar mom maryam
"shikenan zan samu lokaci mu zauna da shi,zanyi mashi bayanin yanda case ?in yake" mom ta fa?a
"yawwa hakan yayi ,sai dai fa ya zamana cikin sirri zaiyi shi, kuma kar ya sanar a wajen aikin su yayi shi parsonal,duk da na san aikin su dama na sirri ne sai dai wannan ya ?auke shi a matsayin na gida bana aiki ba" mom maryam ta fa?a
"in dai wannan ne ba matsala"a cewar mom , murmushi mom Maimunatu ta saki
"shiyyasa nake sonki hajiya maryam akwai kawo shawara mai ?ullewa" murmushi su ka saki gaba ?ayan su
"abun ne wallahi ya ta?a zuciyata,baiwar Allah nan babu ruwanta amma ace lokaci guda wani ya dabaibayeta da sharri,su barta mana taji da zaluncin kashe mata miji da su kayi mana ba sai sun manna mata kisan a kanta ba"
"gaskiya ko waye ba ?aramin cutar da ita yayi ba" firar su suka shigayi suna alhinin abunda ya faru da ?awar mom.
?????????? ????????????????
A tsaye take a gaba motar ta ?irar honda Black color, blue black ?in Abaya ce a jikinta ta yafa gyalen saman kanta,hand bag ?inta ce ri?e a hannunta,cikin fa?a fa?a take fa?in
"Enaaya wai zaki fito ne ko sai nayi tafiyata?"
daga cikin motar naji Muryar yar ?aramar yarinya tana fa?in "momy gani nan fitowa hand bag ?ina zan ?auka"
tsaki matar taja "ko uwar mi za kiyi da hand bag,ni kinga tafiyata idan kin gama kilibibin naki