Showing 84001 words to 87000 words out of 110620 words

Chapter 29 - FYADE COMPLT COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Sep 2024

8172

saki ƙayataccen murmushi yana takawa zuwa inda take . Ji tayi ya Rungume ta , ta baya yana kuma sarƙe da Hannun nata bai Saki ba . I'm sorry Kiyi Haƙuri ba zan sake ba ." Hummm sauke Numfashi tayi a hankali kamin ta juyo tana kallon sa , dai dai Door Bell din na ƙara . Yesss Yace cikin dan daga murya . Shigowa wani Bature yayi hannun sa dake da Wani Dogon Abu da taga yana gungurawa sai dai shi wannan flask ne da wasu Bowls da'alama Abinciwa ne cikin su . Dirning area ya nufa dake can Gyefe wanda duka basu bi ta kan shi ba . Shi dai Aaaryaan Hankalin sa na akan A'isha yayin da ita kuma A'isha Duka hankalin ta baya tare da ita . Duka a burkice take takasa natsar da zuciyar ta . Ji tayi ya hura mata iska a fuskar ta ,wanda jin haka yasa ta saurin kallon shi tare da Sauke Ajiyar zuciya . Daga mata gira yayi tare da Cewa " Tunanin Mama kike yi ?. Jin sunan Mama da Ya ambata yasa ta yin Rau rau da ido tana daga masa kai Alamun eh.

Yah Aaaryaan yaushe zamu koma Gida .? Tayi magana kamin yayi mata Wani magana . Hannun sa yakai yana Rungume ta tare da cewa " Zamu koma Amma sai na Kammala abun da ya kawo Ni , Na farko kin san Auren mu ne ." Shiru tayi masa tana bin bayan sa ganin ya nufi Dirning , A hankali ya fara zuba mata Ruwa yana miƙa mata sai kuma ya ɗan Lumshe idon ya budewa tare da cewa " Ruwa kike buƙata first ko Lemu?. Amsan Cup din tayi tana kauda kai tare da shan ruwan don tafi bukatar shi , tun saukar ta bata saka komai a cikin ta ba . Kallon Agogon Falon tayi karfe 6:40pm lokacin sallar magriba ta karato . Wani irin abinci ta gani kala² wanda ta rasa Gane wani kala ne , A zuciyar ta fadi take Wannan Wai abinci ne ?. Humm , Sauke Numfashi tayi ganin Talia a gyefen su yasha kayan Carrot da Wasu ganyayyaki da ta rasa gane suma Meye , amma Ganin Talia ce yasa ta saurin kai Hannu tayi tana kokarin daukar Plate din bowl din Talia.... Murmushi yayi yana kallon ta tare da Dauka daga gare shi yana matso dashi Gaban ta , Da kan shi ya fara zuba mata a Plate tare da haɗa mata da Pepe chicken ɗin suna fara cin Abincin Hankalin su kwance . Wow Gaskiya Ya Aaryaann babu laifi da dadi , Amma yaushe zamu koma Gida?.

A'isha Zamu koma na faɗa Miki , amma ...gimtse magana nasa yayi ganin Shigowar Kirar Haali . Lemu ya kurɓa tare da Daukar kirar , Ita dai A'isha ganin kira yasa ta dakatawa da cin Abinci a tunanin ta su Mama ne . Gani tayi yana murmushi wanda ta gama laƙantar shi indai yana kalon Wannan murmushin to wani mugun Abun zai maka Wanda sai kaji kaman kace Wayyyo Allah .!

Okay Haali Ina America ,eh Ku taho tare da Bie bie . Ok . Ita tasan inda nake sauka , ku taho tare goben . Ok.... Datse kirar yayi yana kallon yanda A'isha ta daura Fork akan cinyar kaxan ta tayi shiru Alamun tunani take yi .

Fork din Hannun sa yasa yana taimaka mata tana kaiwa bakin ta kamin tace " Ya Aaryan na Dauka su Mama ne ?. Kallon ta yayi yana ɗan kasa da idanun ta tare da ɗagosu yana sauke su akan Fuskar ta kana yace " A'a ba su Mama bane , ai na sauke layin da su Mama suka Sanni Dashi , Wannan fine babies dina ne , Zasu zo nan saboda sunyi kewata kuma suna buƙata na . Shiru tayi tana Kallon sa kamin ya saki mata Murmushi na bariki yana cewa " Kin ga ai idan na Rage zafi dasu ba wani matsala bane ,matata ma ta hanani su kuma nema na suke yi , Yau barcin rashin Dadi zanyi . Saboda ..... Kamin ya ƙarike Maganan ne tayi Saurin dakatar dashi tare da cewa" Ba komai na tsana a halin ka ba shine wannan halin naka , Sam baka tunawa da ALLAH . Bulalai ya kamata ayi maka a musulunci . Tsammm yayi don jikin sa yayi Wani iri duk da zuwan su Haali ba komai yake son yayi masu ba banda Tijara don ya ɗauki Alwashin masu tijarar da sai sun gwammaci Suyi shararar titin kasar America da irin abun da zai masu.....! Wani dariya yayi yana karawa tare da furta " Kowa sai ya tsaya a matsayin sa , A zuciyar sa kuma yana faɗin " Sai nasa an cire mun kayan jikin ta an sa mata na maza dama ai anan ne suka yi mata Surgery to zan yi maganin su duka .!
#MAMANT

```FƳAAƊE.!```
*(Erotic and Sympathetic Story)*

Ayshatou Mamanteddy
***46-47***
*SUFY'S PRINT GRAPHICS DESIGN*

🏷️ PROVIDING A RANGE OF CONTEMPORARY AND TOP NOTCH CREATIVE DESIGN.....

*📍 OUR SERVICES*
✒️LOGO DESIGN
✒️LOGO PACKAGE
✒️ FLYER DESIGN
✒️ BIRTHDAY FLYER
✒️ INVITATION CARD
✒️ADVERT VEDIO
✒️ DIGITAL INVITATION
✒️ STICKERS DESIGN
✒️AND LOTS OF
📝DM NOW....TO GET A TOP NOTCH ATTRACTIVE AND PROFESSIONAL DESIGN
Whatsapp:07045125150
Thanks you for choosing us nd we appreciate refferals 🥰🤗.
**
Shiru A'isha Farida tayi ran ta na mata babu Daɗi , A hankali take cin Talian Wanda tura shi kawai take yi , a fakaice Aaryaann ke kallon ta ko zai ga ga yanda reaction nata zai sauya ,Gani yayi ta miƙe tana kallon sa tare da cewa " Bara nayi Sallah Sai na ƙwanta barci nake son yi . Ohk Shine Abun da ya furta mata yana Kallon ta ,ta bar Wurin duk ta sauya a ƙwayar idon ta zaka ga Zunzurutun Kishi kwance . Murmushi yayi yana Ɗan yin Dariyar jin Dadi domin shi kullum burin sa bai Wuce yaga A'isha Farida a tare da shi ba . A da baya yana kokonton ko Soyayyar Aslaam da Aaaryaan ya samu masauki a zuciyar ta ,ya ture nasa amma kuma a yanzu ne ya gane Har yanzu shine Sarkin a zuciyar ta . Cike da Jin Dadi ya mike tana barin Dirning din don shima so yake yayi Sallah sai su Huta Gobe kuma su fita Shaƙatawa don dare ya fara daga Yanzu a can .

**
Lebanon
Tun bayar isar Aaslaam yake gashi nan dai babu Walwala Bare fara'a dama shi ba ma'abocin Fara'ar bane amma kuma a fuskar sa kana kalla zaka tadda damuwa na yi maka Sallama . Kullum kokarin Auntyn nasa Ɗaya shine taga ta sanya shi nishaɗi duk da ba yara take dasu sosai ba , Duka yaranta Biyu ne Mata ,ɗaya Tayi Aure Mubeena itace kaɗai a gaban ta a halin yanzu . A matsayin karatu kuma tana mastering deegre ɗin ta . A hankali Mubeena ta shigo inda yake ba tare da tayi masa Sallama ba ,don tasan Damuwar tasa baya Wuce Abu ɗaya shine tunanin A'isha Farida . Isowan ta ke da Wuya ta gan shi zaune Gaban Drowing bord Din sa , yana kallon Kyaƙyƙyawar fuskar A'isha Farida . A hankali Zuciyar Mubeena ya raya mata ,wannan itace A'isha Farida babu makawa. Cikin nuna Murna da zaƙewa Tace" Wow , Aslaam Wannan itace A'isha Faridan,?. Gaskiya tana da kyau sosai . ba tare da ya kalli Mubeena ba ,kuma ba tare da ya dauke idanun sa daga kallon Fuskar A'isha Farida ba ya sakin mata Murmushi tare da cewa" A zahiri ta fi haka ,ina ma zaki Haɗa . Amma kuma a yanzu tayi mun nisa , Na kasa jin zan iya daina Son ta a zuciya ta . Idanun sa ne sukayi Jah , Fuskar sa na sauya na nuna zallar damuwa da ɓacin Rai . Wannan yasa Mubeena kai Hannun ta tana ɗaukar zanen A'isha Farida tare da kaudarwa daga Gare sa . Mashaallh shine furucin da tayi a kuma karo na biyu da idanun ta ya sauka a kan Fuskar A'isha . Cikin tausaya ma ɗan Uwan nata kuma yaya A gare ta , ta furta " Aaslaam Kayi Haƙuri , Zan cigaba da Maka Addu'a Allah ya baka Wacce ta fita a zuciyar ka . Ita kuma Allah ya bata zaman lafiya tsakanin ta da mijin ta .

Wani irin banzan Kallo ya Watsa mawa Mubeena , yayin da zuciyar shi ke cewa " Wannan kaunar sa take yi ko Ƙin sa ?. Hannun da yakai yana amshe zanen Daga Hannun ta kamin cike da bacin rai da Tsawa yace " Ta shi ki fice mun Daga Ɗaki, Uban me ma ya kawo ki?. Jikin Mubeena na ne ya hau Rawa kar³ daga Addu'a ya zama mata matsala . Mara tunani ke kina ganin har akwai wata macen da zan so kamar A'isha Farida , To babu ita a rayuwa , a ganin farko Murmushin ta halayyar ta naji ta burgeni kuma tun daga nan ta samu kyaƙyƙyawar masauki a zuciya ta . Ba zan taba dai na Son A'isha ba har iya ƙarshen Rayuwa ta , Oya fita ki bani Wuri. jikin Mubeena na Rawa ƙwallah na ciko Ƙwarmin idanun ta ta mike tare da zummar fita , Sai jin Muryar sa tayi yana cewa " Ina bukatar Cofee kisa a kawo mun yanzu .! Tom . Ta furta tare da ficewa jiki babu karsashi . Idanun sa ne ya sauka akan screen ɗin Wayar sa , Wanda ran sa yaji yayi wani mummunar ɓaci Ganin sunan Nawaaz da yayi yana masa Kaikawo a saman Screen ɗin Wayar sa ,cike da Rashin mutunci ya daga kirar cikin Muryar marasa kirki ya furta " Yaaaaa......!



Mu karya da Wannan😜🕊️
#MMNTEDDY




*FƳAAƊE..!*

49-50

**

Maman Teddy!

I really congratulate you on your third anniversary as a Hausa novelist, specifically for your book "Bafulatanar Ruga" which has been widely read and appreciated. Today, we celebrate the first steps taken in your journey as a writer and the success you have achieved thus far.

I praise Allah for granting you the knowledge, resources, and perseverance to produce excellent literature that reflects the Hausa culture and language. Your work, "Bafulatanar Ruga," and all your other writings, have been a source of inspiration and enlightenment for many readers.

I have enjoyed reading your book and appreciate the way you have captured the essence of Hausa culture in your writing. I look forward to be reading more of your works in the future.

May Allah continue to bless you with good health, knowledge, and creativity in your writing career. I pray that your works will continue to touch the hearts and minds of many readers, and that you will remain a beacon of inspiration to aspiring writers in our community.

Congratulations once again on the third anniversary of "Bafulatanar Ruga" and all your other literary achievements!

Best regards from Fatima Muhammad Buba ( a future poet)

*Ina Godiya Ƙwarai bisa Ga Addu'oin ku na cikar shekaru uku da kammaluwar littafi na mai suna Bafullatanan Ruga, Na gode sosai Allah ya bar zumunci ya bar Ƙauna @muhammad fatima buba sai a yau na ga sakon ki ina godiya 🙏🏻🥰*

Yanda Naawaaz yaji Muryar Aslaam Sam bai damu da jin Hakan daga Gare shi ba ,don yayi expecting dama Jin hakan daga Garesa . Ya kwana biyu? . Naaawaaz yayi maganan cike da Share Maganan Aaslaam yana kawar dashi a zuciyar sa don komai yasan SO ne yasa Su aikata Hakan ,har rabuwar nasu da suka yi wanda basu taɓa kwana biyu ba tare da sunga junan su ba. Wani irin takaici ne Ya kama Aaslaam jin furucin Nawaaz da yake tambayar sa ya kwana biyu?. a zuciyar yana faɗin " Wato Kana morewar ka tare da shan Amarci da Wacce na kwadaita Aure shine ka kirani ka faɗa mun? To kirar na Meye karuwa zaka faɗa mun kun samu ko kuwa ya akayi?. Humm Sauke nannauyar Ajiyar zuciya yayi mai tattare da Ɓacin Rai yana danne Haushin sa kamin ya furta " Ya akayi .? I just call to greet.....Kamin Nawaaz ya Ƙare maganan nasa ne Aslaam yayi saurin katse shi tare da cewa " it's Okay bye. Kai dakata Aaaslaam Wallahi ka kashe mun Kira ran ka zai baci ,duk inda kake sai Nazo ." Dakatawa Aaslaam yayi daga kokarin datse Ƙirar da yayi niyya . Cikin Faɗa da Daga murya ya fara magana dai dai Mubeena na shigowa hannun ta dauke da Cup din Coffee . A kusa dashi ta zauna tana riƙe da Cup din tana kallon yanda Yake hura hanci tare da numfarfashi .

Kai wani irin dan Rainin Hankali, Ok ka kirani ne ka faɗa mun A'isha farida na Dauke da juna biyun ka , ko mene? Ko kuwa ka kirani kayi mun Albishir ne idan A'isha ta Haifo ma Yaro sunana zaka saka ? Oya I beg Mr Man kar ka sake kira na if not ran ka zai mummunan ɓaci . Huhhh Matsalar mu duka Rashin Fahimta . Nawaaz yayi magana yana kai Roban Swaan bakin shi don bai tsaya bi takan cup ba , kan sa ne yaji ya dau zafi Jin maganan Aslaam da yayi a yanzu . Ɓangaren Aaslaam kuwa wani irin tafasa zuciyar sa ke yi Jin Maganan da Nawaaz yayi a yanzu Wato matsalar su Rashin hadin kai ?. Yana tsaka da nanata maganan a kan sa ne yaji Muryar Nawaaz yana cewa " Ban Auri A'isha Farida ba .! What...? Aslaaam yayi maganan yana saurin sauke ƙafarsa da ya daura daya kan daya zuwa kasan tiles . Kallon Mubeena yayi wanda take kallon sa tare da cewa " Aaslaam me ya faru? A'isha ta mutu ne? . Ke ga mutuwa munafukar banza munafukar Wofi leave this place before I Open my Eyes , Mai mugun fata . Aje Cup din Coffee Mubeena tayi a gyefen table din dake kusa dashi , tana gunguni ta fice daga wurin ran ta ya ɓaci daga zafin kare dangin da yayi mata .

Shiru Naawaaz yayi kamin ya furta " Pls Aaslaam Calm down, me ye na wannan Faɗa haka?. Mtsw Dan tsaki Aaslaam yayi yana cewa " Okay Ina jin ka , ina A'isha take yanzu ? I know she's waiting for me right?. Kallon Gyefe Naawaaz yayi cike da Girgiza Kai yana jin tausayin kan su , No bata Jirar ka , bata SO na And You too . Cike da haɗe Gira Aslaam yace " ban gane ba .! Kai ma bata Son ka Nima haka , Aaaryaan ......Nan take ya fara bashi labarin komai wanda Jin hakan yasa Aaslaam miƙewa tare da Fadin " Wannan Wani irin rainin Wayo ne , Aaaryaan zai nuna mana Bariki ne ? Who is he?. Waye shi ne ? Abun da yake takama dashi ina dashi , kuma daga yau zuwa Gobe zan Wuce America ina zai shiga a can inda ban sani ba. Sauke Numfashi Nawaaz yayi tare da cewa " A'a Aslaam A'isha tana Son Aaryaann , a bakin Mama Nake jin Shine ɓoyayyen masoyin ta Wanda ya kula da ita tun tana yarinya , Sannan kuma itace Yarinyar da yake mana maganan ta wanda yace bata Gani da dare . Ɗauke Wuta Aslaam yayi idanun sa na ciko da Ƙwallah , me kake nufi Nawaaz na rabu da A'isha na barta? Bari na Har Abada ?. Yesss Ka haƙura A'isha ba taka ba ce ba kuma nawa bace , ta Aaaryaan ce . Muyi hakuri mu Rungumi ƙaddara Aaryaan da A'isha ya dace , Shi ya amshi mutum cin ta yayi mata FƳAAƊE dole zaman lafiya zai dore a tsakanin su inshallah . Akasin mu kasan Dole wata rana muka tuna sai mun ji zafi ko bamu nuna mata ba . Kaga Idan ko Har Aaryaan Na Son A'isha hakan yayi dai dai . Amma kayi Tunani .

Sauke Ajiyar zuciya Aaslaam yayi wasu irin zafafan Ƙwallah na zubo ma Kuncin sa . Ohhh Allah shine furucin da Nawaaz yayi jin Alamun kuka daga Aaslaam . Mu maza ne Fa ba mata ba Aaslaam , alƙawari ɗaya zaka yi shine cigaba da kulawa da A'isha Farida tamkar ƙanwar ka har Abada . Kasa magana Aaslaam yayi sai cije laɓɓan sa na ƙasa yayi da ƙarfi yana damtsewa da Haƙorin sa . Ina matuƙar Son A'isha Amma nayi secrifice na bar ma Aaaryaan , Amma bafa zan daina Kaunar a zuciya ta ba har Abada . Na kuma taya shi murna da Allah ya mallaka masa ita .

Alhamdulillah Naawaaz ya furta cike da farin ciki tare da cewa " Abotan mu mai ɗaurewa ce har Abada yanzu yaushe zamu je America mu taho dasu duka su dawo Nigeria, Mama hankalin ta yaki kwanciya . " Shiru Aaslaam yayi yana tunanin yaushe ne ya kamata su tafi din ....?.

**
A daren ranan da A'isha da Aaaryaan an yi artabo duk yanda yaso yaga yayi wani Abu da ita taƙi masa . Daga Karshe sume masa tayi Gauuu wanda sosai Hankalin sa ya tashi . Tun daga Nan Kwanan su uku kenan yau , tsakanin shi da ita Hugging kissing ba yan nan baya kara yi mata yunkurin wani Abu tun da ya lura Ta nuna masa
51-52


Bai kuma ƙara yunƙurin yi mata Wani Abu ba tun da ya lura Ta nuna masa bata SO kuma ba ya son duk Wani Abu da zai samar masu Ɓaraka a tsakanin su . Kaman Kullum yau a gajiye take Domin Basu jima da Dawowa daga Shopping Mall ɗin da ya kaita tayi sayayya ba ,a yanzu idanun ta sun fara Buɗewa daga Zaman America akasin da baya da take tunanin ƙasar tarzoma ne ,amma zuwan ta sai ta gano sam ba haka bane . Kwance A'isha take a jikin sa tana kai popcorn daya bayan daya zuwa dan mitsulun bakin ta . Lumshe ido take don jin dadin Popcorn din take yi daɗin shi har tsakar kan ta . Shi kuwa Aaaryaan idanun sa na akan system din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login