Showing 81001 words to 84000 words out of 110620 words

Chapter 28 - FYADE COMPLT COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Sep 2024

8170

sauke Numfashi kamin ya kai Hannun sa yana shafa Fuskar ta tare da cewa " I love You much m Bieby , Ki shirya yau Rana ce ta Musamman pls make me Happy ,kar kisa na ji na tsani Wannan Ranan a rayuwar mu , Saboda Wannan shine farkon jin dadin Rayuwar tamu ,mun bar kowa don mu rayu tare , kar kisani zubar da Hawaye a wannan Ranan. Gani tayi ya juya yana cewa " Ina zuwa yanzu . Shiru tayi jikin ta na Sanyi tausayin shi ne taji ya kama ta. Bin bayan sa tayi da kallo Ganin ya nufi Wani Corridor . A hankali ta fara tana matsawa tare da zama a daya daga Kujerun falon . Hannu biyu tasa tana rafka ta gumi . Sauke Numfashi tayi tana Lumshe idanun ta tare da fara tunanin Aaryaan farkon Shigowar shi cikin Rayuwar ta .

**
Cikin dare ne Mama bata nan , hakan yasa A'isha fitowa da fitilar Touch light din hannun ta . Hijabin Wuyar ta take gyarawa kana daga bisani ta sako silipers tana nufar Dandalin sayar da Gyada na yaran layin nasu . Kun san lalurar ta sam bata Gani da kyau wannan yasa ta a daren yanke Shawarar Salamtu mai gyada ta zaɓa mata na Ashirin kokko ɗaya . Nigerian People komai sai anyi cuwa² nan take Salamtu ta rairaye Gyaɗa sannan kuma ta bata Ruwa² duk Tarkace ne . A'isha bata ce komai ba tasa Hannu ta amshi gyada ta koma gyefe ta cinye tassss sannan taba Salamtu Gwangwani . A'isha Farida kudin gyaran kawo mana . Wani irin Dariya A'isha Farida tayi na Rainin Hankali kana tace " Salamatu kenan . Banda bakin iskanci Nine zaki ba Ruwa ruwan Gyaɗa kina tsammani na baki kudi . Kin bani Tarkace wanda ina zuwa Gidan ku Mama Zubar da irin su take yi shine Ni kika bani .? A Nigeria fa muke , in this money 💰 scarcity , Kema kin fito nema and You are expected ni na baki kudi . To naci gyada bulus babu kobo ko Naira da zan baki .

Kama ƙugu Salamatu tayi tare da cewa " Kutumelesi." Ai wallahi Uban ki yayi kaɗan . Yau zan maganin Rashin kunyar ki , Dama mai Hali baya Fasawa kin manta duk ƙarfin ki yanzu bakya gani ne da kyau . ? Juyawa Salamatu tayi tana cewa " Ku kashe mun Hasken Wurin naci Uban Yarinyar nan .! Jin haka yasa A'isha Jin tsoro don tasan a yanzu fa Sai dai Salamatu ta jibga ta . Saurin kara Hasken Fitilar tayi da Hannun ta ,tana Jah baya tare da Rugawa da Gudu Salamatu na bin ta . Sam bata san ta shiga Kan Titi ba sai dai karar Horn taji a gigice tare da jan burki .
Cike da tashin hankali ganin har a lokacin tana tsakiyar titin bata sauka ba yasa Aaaryaan Saurin fitowa daga moton nasa yana nufo inda take . Hannun ta ya kama cikin Tsawa yake kallon ta , Ke baki da hankali ne ? A wannan daren zaki tsaya a titi? Idan wani Abin Hawan ya buge ki ya kashe banza , wuce ki tafi Gida.! Ya kare maganan yana saukar da ita akan Gyefen Hanya . Saurin yin bayan sa tayi tana cewa " Yaya na Don Allah kar ka barni, Salamatu ne zata Bige Ni.? Juyawa yayi yana kallon Gyefen sa , don yaga Wanda suka taho taren tun fitowar sa ta gudu , wannan yasa shi Cewa wacce Kuma wannan ?. Gata nan tana bina .! Tayi maganan tana ƙara shigewa bayan sa abun ka ga yarinta har da Riƙo masa Riga tana cukwikwiye shi . Huuuuhhh Iskan bakin sa ya furzar tare da juyowa yana kallon ta , Rage tsawon sa yayi sosai don tayi masa kasa da yawa . Ai ta tafi tun ɗazu baki gan ta bane .? Gyada masa kai tayi tana Cewa" Ai bana Gani da dare, Itama shiyasa ta samu daman zuwa tace zata Bige Ni inda da Rana ne wane ita...ai ko gidan su duka ne basu ishe Ni ba ." Ta ƙare maganan yana kallon kuri irin nata , zuciyar sa ne yaji ya tsinke masa ,kalmar ta na farko ya dawo masa ,Ni bana Gani , murmushi yayi yana cewa " Meye Sunan ki ? . A'isha." Ta basa Amsa kai tsaye tana Washe masa baki kunsan ta da fara'a . Kai kuma fa?. Murmushi yayi yana ɗan cizar laɓɓan sa a hankali kaman mai tunanin wani Abu kamin yace " Ɓoyayyen masoyi."
Oho wato kai Masoyi na ne kenan?. Dariya yayi mata don shi kan sa bai san dalilin da yasa yace mata sunan sa ɓoyayyen masoyi ba ,kawai ya tsinta harshen sa ne da fadin hakan . Eh A'isha .
Buɗe baki tayi tana dariya kana tace " To shikenan Bari yanzu na koma Gida mama kar ta dawo bata ganni ba. A'a bari na kai ki Gida zaki iya mun kwatance?.

Gyada masa kai tayi nan ya sunkuya yana cewa " Hau baya na goya ki muje ." Thnkyou tayi maganan cike da wauta da Haukar yarinta bata san mutum ba kawai ta dare bayan sa . Girgiza Kai yayi suna tafiya tana masa surkulle har suka isa Kofar gidan su . Anan ya sauke ta yana cewa " To shikenan amma ki daina tsokanar faɗa . To ɓoyayyen masoyi na, gaskiya bayan ka da daɗi Sosai ,zaka zo Gobe ka kara goya Ni a bayan ka haka?. Shiru yayi don ba a garin yake ba , kasuwancin sa ya kawo sa ,sannan kuma a goben ranan zai koma Abuja . Baka ce komai ba , ko ba zaka goya Ni ba?. Murmushi yayi yana cewa " Zan Goya ki mana ai Ni din duka na kine. Da gaske ? Tayi maganan tana fiddo da idanun ta wanda bata Ganin sa . Kayi Alƙawari? Ta kuma tambayar sa wanda kai tsaye yace " Eh A'isha Gobe zan dawo .yeee Bara na faɗa ma mama idan ta dawo . A'a kar ki faɗa mata , Ni ai ɓoyayyen masoyi ne ,nayi Miki alkawarin zuwa duk lokacin da kika neme Ni . Dan Murmushi tayi tana cewa " Na gode . Ki tafi Gida yanzu ,maza Shiga , kiyi barci mai Dadi .

Juyawa tayi zata Shiga Cikin gidan sai kuma ta Juyo da Sauri tana kai Hannun ta tare da Son taba fuskar shi . Fahimtar hakan da yayi ne yasa shi yin ƙasa tana shafa Fuskar shi da Hannu biyu , kai Ɓoyayyen masoyi kai Kyaƙyƙyawa ne kaman Mama na . Murmushi yayi yana jin ta tana cewa" Gobe da Rana zaka zo ko Daddare , ko ma dai wani lokaci nena taba Fuskar ka ne yanda idan kazo zan san kai ne. Dan Dariya yayi kana ya riko Hannun ta yana cewa " Kinga yanda zamu rinƙa bambancewa duk idan Nazo da Daddare zan rinka zuwa. Ji tayi yana motsa mata yan yatsun ta na tsakiyar , kana yace Wannan yatsar naki a kullum zan fara riƙewa kamin na riƙe duka hannayen ki .

Ina son ka ɓoyayyen masoyi sai da Safe . Murmushi yayi yana cewa ". Love You too. Tun daga Wannan rana shakuwa da soyayya tamkar yaya da kanwa ya shiga tsakanin su . A kwana a tashi har ta Fahimci ba dan Garin bane ,don yakan ce mata zai koma Gida sai ya kwana biyu ya dawo . Kaunar A'isha yake yi sosai don a familyn su babu Wanda bai san labarin ta ba , don makantan da take dashi yafi tausaya mata akai har ya rinjayi zuciyar sa . Sosai ya bada gudunmawa ganin ilimin ta ya inganta ta samu ilimin daidai gwargwado . Haka kuma duk yanda Mama take son Ganin sa Abun ya fasskara mata , yana jin motsin ta zai Gudu ,daga nan ne mama tayi masa suna da Aljani ba mutum ba a cewan ta . Sosai yake taimaka ma A'isha don har kudin makaranta da sauran abubuwa shi yake mata , don ya bincike akan labarin rayuwar ta a layin nasu , yanda ma aka ce mata ita din shegiya ce bata da Uba a karuwanci ne Mama Lantana ta same ta .."

Motsin shigowan Aaaryaan yasa A'isha Farida sauke Ajiyar zuciya mai nauyi tare da dawowa daga Duniyar tunanin ta da Aaaryaan wanda ada take masa Lakabi da ɓoyayyen masoyi don bata san sunan sa ba sam sai a yanzu . Tahowa yayi inda take ganin da yasa ta saurin miƙewa Hawayen idanun ta take sharewa don tuna labarin ta ya taba mata zuciya . Babyn Aaaryaan me yasa ki kuka .? Yayi maganan cike da Nuna caring da loving . Kallon sa tayi kawai sai ta nufe sa da Sauri tana shigewa jikin sa tare da Rungume shi tana kankanesa tare da cigaba da rera masa Sabon kuka wanda yake narkar masa Da zuciya . Hannun sa yasa yana shafa Kan ta a hankali tare da Rungume ta da dayan Hannun sa. Ya Aaryaann Na tuba kayi Haƙuri...!

Ɗago da Ita yayi daga Jikin sa yana daga mata Girar sa sama tare hura mata Kisss uhhhhmmm💋 . Kallon sa tayi yayin da ya kuma motsa laɓɓan sa yana furta " I love You ,Bai kuma jira jin me zata ce ba ya kama ta yana nufar Wani Falo da ita wanda bata san ina ne ba , fahimtar abun da ya faru da ita ne yayi shine ta tuna wani bangare ne na rayuwar su . Wannan yasa shi kawai yi mata Hakan don bayason Ganin Ya a haka . Hannun ta tasa ta goge Hawayen Fuskar ta , a haka suka shiga Wani Wani irin ƙayataccen Bedroom Wani sanyi na ratsa bargon ta mai dadi . Kallon sa tayi tana son Magana Amma sai taga yana mata Murmushi tare da cewa " Ko kefa share Hawayen ki ,ba zan kara bari kiyi kuka ba indai muna tare . Gyada masa kai tayi , tana kallon sa taji ya kuma cewa " It is Okay for you? . Ya yi maganan yana shiga Daga cikin Bedroom din . Yayi maki ko? Nan ne Bedroom ɗin mu Ni dake .! Murmushin da take yi ne ta daina . A hankali tace " Da kai kuma?.

Eh mana ai Ni mijin ki ne ?. Yayi Maganan tare da takowa zuwa inda take . Kasa masa magana tayi , wannan ya bashi damar dan risinawa yana rage tsawon sa tare da sa hannun sa yana ɗago fuskar ta . A'isha Ina Son ki tun ba yau ba , kece wacce na fara yi ma Soyayyar har karshen rayuwa. Plsssss ki kirani kai tsaye da sunan mijin ki , bakya SO?. Yayi maganan yana kallon cikin idanun ta da suka ciko da ruwa . Girgiza masa kai tayi alamun Aaa , Hawayen na zubo ma Kuncin ta . Kasa yayi da Muryar sa yana cewa " Ki bani dama ,zan koya Miki yanda zaki So ni don Allah kar ki hanani...." In fara?. Yayi maganan yana kallon idanun ta da Fuskar ta . Gyada masa kai tayi alamu ta amince, kawai sai taji ya jawo ta yana Wani irin haɗa ta da Ƙirjin sa , abun da bata taɓa ji yayi mata Irin shi ba , Laɓɓan ta ya kama yana hadewa da nasa tare da fara ligwigwitar su ta sama da ƙasa , yana mata Wani iri. Haukan kissing , Wanda jikin ta ne ya fara zuuuuuzuuuzuuuu mannata yayi da jikin sa kaman zai tsaga ta ya shigar su zama daya . Hawayen idanun ta ne suka fara ambaliya wanda bata san dalin zuwan su ba a wannan lokacin . Kusan mintuna Goma suka deba a haka , ganin hakan yasa ta saurin kwace jikin ta jin yanda yake sauke Hannun sa yana Kasa da braziyan ta tare da fara shafa Jikin ta zuwa nonon ta wanda nan take ta kwace kan ta cikin sauri tana Jah baya .

Hannun ta tasa tana Saurin gyara rigar ta tana cigaba da rera gajiyayyar Kukan ta . Kallon ta yayi yana dafe kan sa , Idanun sa na ciko da Wasu irin ƙwallah , Gani tayi ya zube Gwiwowin sa kasa saman tiles din wurin . A'isha A'isha ba zan iya Kwana ban yi sex ba , Ina bukatar ki...Ban saba Wannan Rayuwar ba shigowan ki rayuwa na kawai zaman gidan mu ki sauya Ni , nafi kwana ki ban yi sex da ko wa ba , please ki yarda dani Daga wannan ba zan ƙara Miki ba sai munyi Aure ... Maganan sa ce ta dauke jin yanda marar sa ta riƙe sai da Ya dauke wuta na Mintoci kana ya cigaba da cewa " Kece mamata my future wife , ki tausaya mun daga Yau shikenan , gobe aure za'a yi mana anan ,sai mu fara Sabon Rayuwa . Na gaji da Tatsuniyar gizo da kokin ka ya Aaryaann , Wallhi ba yar iska bace Ni , Ni ba zan yarda ba.... Ta ƙare Maganan tana rushewa da Kuka , Wanda yasa shi Cikin wani irin murya tamkar mai shirin shiɗewa yace " pls A'isha ban san kukan ki ,zan jure koda zan mutu amma gobe zaki bar Ni ? Gobe zan sa daura mana Aure , daga lokacin mun zama mata da miji ." Cikin share Hawaye tace " Eh . A hankali ya mike yana ciza laɓɓan sa kana yace " Bara naje Falo , ki shiga Privacy ki watsa Ruwa ga kayan ki can inda suke , Sai ki fito kici Abinci . " Kasa masa magana tayi Har ya.............!


A kwanan ku shirya sabon littafi na wanda na dade ina sarrafa alƙalami na tare da tsaftace shi a kwakwalwata nake kuma bata darare na wurin son ganin na nishaɗantar daku a wannan tafiyar tamu ta gaba , bafa yanzu Ba😜 , sai mun kammala Wannan cikin natsuwa idan mun kai har sallah to shikenan idan kuma mun kammala kamin sallah to inshallah zamu fara yin shi . Labarin da ya dade a zuciya ta kuma nake sarrafa Alkamina akan sa tsawon shekaru yake a memory na sai a yanzu na idan tun daga Farko har karshe , nasan kun matsu da son jin Mene sunan shi , ku biyo NI a sabon littafi na mai taken SHAHARARREE
(MR XXXX).
Labarin danbarwa nishaɗantar fadakarwa tare da sanyaku cikin zunzirutun nishaɗi , sai dai wannan karon babu ƴammata a cikin tafiyan🤪 matan Aure kaɗai wannan littafin naku ne😄. Mr xxxxx. (Shahararre). Wanda suke ready You can starded payment right now , idan kuma zaki bari sai an fara ne ,to Nima nafi son hakan😄🥰 ku nuna mun Soyayyar ku kaman yanda kuka saba , Don nasan matan Oga akwai ku da rufun baiti🤣

Ina godiya da Addoin ku akan rashin lafiyar da nayi na gode sosai ,sannan kuma jiki yanzu Alhamdulillah ,sai dai muce Mashaallh Allah ya ba wanda basu da lafiya lfy' ya karo masu Afuwa Amin . Ngs kwarai .
#Mmnteddy."

```FƳAAƊE.!```
*(Erotic and Sympathetic Story)*

Ayshatou Mamanteddy
***45-46***
*SUFY'S PRINT GRAPHICS DESIGN*

🏷️ PROVIDING A RANGE OF CONTEMPORARY AND TOP NOTCH CREATIVE DESIGN.....

*📍 OUR SERVICES*
✒️LOGO DESIGN
✒️LOGO PACKAGE
✒️ FLYER DESIGN
✒️ BIRTHDAY FLYER
✒️ INVITATION CARD
✒️ADVERT VEDIO
✒️ DIGITAL INVITATION
✒️ STICKERS DESIGN
✒️AND LOTS OF
📝DM NOW....TO GET A TOP NOTCH ATTRACTIVE AND PROFESSIONAL DESIGN
Whatsapp:07045125150
Thanks you for choosing us nd we appreciate refferals 🥰🤗.
**
Har ya fice daga Bedroom din. A hankali take bin Wurin da kallo kamin ta dafe kan ta da taji yana juya mata da dakin baki Ɗaya . Jan ƙafafun ta tayi a hankali tana zama a ƙayataccen Bed Din har kuma a lokacin idanun ta basu daina zubar da Hawaye ba da ta rasa na Meye . Zuciyar ta ne ya fara ce mata ' Wai dama A'isha Farida zaki taba Saka ƙafarki anan Ƙasar America? Yau dalili ya sanya ., Humm Ya'yan masu kudi suna Hutawa Allah ya basu na duniyar Allah ka basu na lahirar ya bamu tare . Ƙirjin ta ne ya buga Dammm tuno da Ita bata san ma ina dangin ta suke ba . Hawayen idanun ta ne suka ci-gaba da Sauka mata . Kuka take sosai kusan na mintuna Biyar kamin ta motsa bakin ta cike da Wauta tana faɗin " Zan mawa Ya Aaryaann magana ya kai Ni Saudiyya na roƙi Allah ya haɗa Ni da iyaye na ,na gansu kamin na mutu , Goge Hawayen fuskar ta tayi tana miƙewa tare da nufar Privacy .

Ɓangaren Aaaryaan kuwa Magani yasha Yana jin Ba laifi Sha'awar dake taso masa tana lafafawa . Bathroom ya nufa Yana Watsa Ruwa wanda ya dade cikin ruwan Ɗumin yana Jin kan sa Wani iri tamkar bashi ne ba , Gani yake kaman Wani Aaaryaan din Aka sauya bashi ba , mutumin da idan yaso mace ko ta halin kaka sai ya biya bukatar sa ,sam bai san Wani abu wai shi juriya ba indai yana bukace baya ji baya gani , shi da kamin ma ya buƙata an buƙace shi a yau shine ya durƙusa Gwiwowin sa ƙasa amma bai samu biyar buƙatar sa ba . Lumshe manyan idanun sa yayi yana kai Hannun sa tare da shafa Sajen fuskar shi da ya kwanta . Ƙarar Door Bell ne da yaji yasa shi miƙewa yana fitowa Izuwa Bedroom ɗin nashi . Tsayawa yayi yana saka short nicker da Singlate fari yana tahowa Falon . Kiciɓuss Suka yi Da A'isha Farida Wanda itama Karar Door Bell din yaje har inda take wannan yasa ta fitowa itama cikin Sauri .

Tsayawa tayi tana slow tare da bin sa da kallo , Wanda shima kallon ta yake Ganin yanda suka sha'afa a kallon juna yasa ta Saurin juyawa tana Kokarin farin wurin ne taji caraf ya riƙo Hannun ta . Ba tare da Ya juyo ba ta tsaya , kallon ta yake yi kamin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login