Showing 60001 words to 63000 words out of 110620 words

Chapter 21 - FYADE COMPLT COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Sep 2024

8166

har ƙarshe ana yin shi akan 5k .

Tallah a status for 3 days Ana yin shi akan 2k .

Idan kuma a status ne sau Ɗaya na kwana ɗaya 24hrs ₦500

Idan kuma a saman Page Ne sau Ɗaya ₦500 .

Idan na Sau uku ne a saman Page ₦1k .

Idan kuma aƙasan page Sau Ɗaya ne ana yin shi akan ₦500

Idan kuma ƙasan page ne sau Uku ₦1200

Idan kuma har a kammala book ne a ƙasan page ₦3500

Zaku iya tuntubar nombobina domin ƙarin bayani 08081202932/ 09061466409 .

#Mamanteddy

*🕊️FƳAƊE....!🕊️*

***Romantic love Sympathetic and Erotic Story.***

*AISHATU MAMAN TEDDY 🧸*

Book...3
***29***

*Don Allah kar ki karanta mun Idan baki biyani ba , Littafin nan na kuɗi ne Regular group ₦500... VIP group ₦1000... Special payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932...Idan VTU transfer ne sai ki tura kuɗin ki kai tsaye ta Wannan number 09061467409*

```~Tallah~```
To babban magana ina iyaye mata masu san kasancewa da mazajen su har Abada da'iman? Ina macen da matsaloli na Jinnu ko Sihiri yayi mata katutu ya addabi Zaman Auren ta ke dama Rayuwar ki baki ɗaya ...to Allah nacewa tashi in taimake ka . Mata masu fama da Rashin aure shekaru 30 ko sama da hakan duka a gaban iyayen ki abun tun bai damunki a yanzu dole ya fara damunki...” maza garzaya taskar Empire domin warwarewar duka matsalolin ki ...na duba kuma na gani , Maganin ta babu ɓata sam , da Ayar alƙu'ani take magani ba tsafi kawai Kunsan Magani da Ayar Allah , Allah na saurin amsa kamar yankar Wuƙa . Bhuzuwa Empire Aikin ta ya haɗa ta Hanyar alƙu'ani ,tana ma ƴammata marasa farin jini magani da zallar nono , ƙwai ... mallaka babu irin wanda bata yi , na suratul yaseen, Rahman , Izaja'a , jauharatul kalam da dai sauran su ...masu buƙatar ƙarin bayani ga nombobin su kamar Haka 08139762831 Allah ya taimaka Amin .

*Second advert*
*SUFY'S PRINT GRAPHICS DESIGN*

🏷️ PROVIDING A RANGE OF CONTEMPORARY AND TOP NOTCH CREATIVE DESIGN.....

*📍 OUR SERVICES*
✒️LOGO DESIGN
✒️LOGO PACKAGE
✒️ FLYER DESIGN
✒️ BIRTHDAY FLYER
✒️ INVITATION CARD
✒️ADVERT VEDIO
✒️ DIGITAL INVITATION
✒️ STICKERS DESIGN
✒️AND LOTS OF
📝DM NOW....TO GET A TOP NOTCH ATTRACTIVE AND PROFESSIONAL DESIGN

https://wa.me/message/NM3LPR5VMCG6P1
Thanks you for choosing us nd we appreciate refferals 🥰🤗.

Don Allah kuyi hakuri na jina shiru Kwana biyu abun namu sai a hankali , Amma inshallah yanzu zamu cigaba babu sanya 😄🕊️

Dariya ta basa Sosai ,Amma Abin ka ga ba Gwanin Yin Dariyar ba , Sai ya dake yana kai Hannun sa tare da buɗo Murfin moton yana Fitowa , Gate Ɗin Makarantar ya nufa Inda da isan sa masu Gadin suka Fara Gaishe sa cikin Girmamawa Don babban mutum A ido ana Gane shi , Bare kuma Irin su Aaaryaaan da Rayuwar su Rabi suna Ƙasashen Waje Kabi suna Ƙasar su Wato Gida Nigeria , Dole Al'amarukan su zasu sha Banban da mutanen mu Na gida Nigeria . Wuce Masu Gadin yayi Amsa masu ta hanyar Ɗaga masu Hannu tare da isowa cikin Makarantar Wanda Mamaki ne y Kama shi Hango A'isha Farida A can Gaban Layin Class Ɗin su itace ta hudu . Wata Doguwar Yarinya Mai Dan Jiki tana kama mata kafada Tare da Mata magana Kamar Haƙa " Are You new comer?. Juyawa A'isha Tayi tana Gyada mata kai Tare da Sakar mata Murmushi . Your Name ? . A'isha Farida ta tambaya Ta kai tsaye . Khadija. " Wow nice ni kuma sunana A'isha Farida . Wow Sunan Ƙanwata kenan kike dashi . A'isha Farida To Meye sunan mahaifin ki?. Ɗauke wuta A'isha Farida tayi kana jin Ɗifff daga Gareta . Don bata San Da Wani sunan mahaifi take Amfani ba tun tasowar ta , Abu ɗaya ta sani shine sunan ta A'isha Farida . Motsi A'isha Farida ta fara yi da Baki alamun zata yi magana , Sai Khadija tayi Saurin cewa " Ga Vp nan yi shiru . Wani dogon Mutumi ne Wanda tsayin sa ya ba A'isha Farida Mamaki Daga Kai tayi Sosai tana kallon sa Ganin tun da take bata taɓa Ganin Shantalelen mutum irin Wannan ba . A'isha Abdu Kareem . Juyowa A'isha Farida tayi tana kallon sa tare da Wasiwasi a zuciyar ta . Muryar sa ce ta katse ta yana cewa " Wato Har kin yi ƙawaye ko? . Muje Office na baki Sauran Kayan sport din ki . Murmushi A'isha Farida tayi tana fidda kan ta daga Layin tare da bin bayan Vice Principle . Duk inda ta Wuce bin ta da kallo Ɗaliban da Malaman suke yi , ba wai Yaran Hutu ne irin ta babu ba , Hasali ma akwai wanda suka fita , Amma kyaunta shine Abu Ɗaya dake Dauke masu hankali , ta ko ina ita Kyaƙyƙyawa ce . Bayan shigar su Office ne ta tadda babu Aaaryaan alamun ya dade da tafiya . A hankali take bin sport wear din Da Vp ya bata , Wanda yake kalan blue , Bayan kuma rigar yana Dauke da Tambarin Sunan ta .


A'isha Abdu Kareem . Ƙwalla ne ya ciko Ƙwarmin idanun ta . Are You Happy?. Yayi maganan yana kallon A'isha Farida wacce yaga Jikin ta yayi nauyi duk ta sauya Lokaci daya . Murmushi tayi tana Ɗaukar kayan tare da Karawa a jikin ta tana faɗin " Thank you Sir ."

**

Bayan Fitar Aaaryaaan Asibiti ya nufa kai tsaye don A ƙwana biyu kansa a sama yake , Tun bayan Faruwar Komai tsakanin sa da A'isha Farida har a yau bai Ƙara lafiya ba . Don kwana ki da yaje Asibiti cewa akayi bp din sa ya Hau . Wannan yasa shi Duk Sati yake leƙa likitar shi . Kan sa ya dau Zafi sosai amma kuma idan ya tuna da Rayuwar sa da A'isha sai yaji Sanyi a zuciyar sa .
**
Tun bayan fitar A'isha Mama ke ta Ɗan Ayukan ta ,don ita bata yi sabo da son jiki ba , ta koma ta saka ma Yan Aiki ido tana kallo . Miƙewa tayi suna Aikin tare don mama Na da Zafin Jini . Bayan Fitan Daddy kai tsaye Bedroom din shi ta nufa tana kara gyara bayan Wanda tayi na farko tare da bin Bedroom din da Room freshener . Fitowa tayi wuraren 9:am tana isowa Falo inda Ta tadda Yusra tana baza Mulki tana saman Ɗaya daga cikin Royal din falon Wata karamar Ma'aikaciya nayi mata massage . Ita kuma tana Zaune daga Kasa . Murmushi Mama tayi tana zama gyefen ta tare da kallon Takardan Hannun ta Wanda duka list ne take yi na yanda birthday din ta zai tafi akan Tsari . Wanda a zuciyar ta ta shirya mawa A'isha Farida babban tijara. Ɓoye ɓoyen da suke yi akan ta ,ta dauki Alwashin fasa Komai a wannan Rana . Wanda mutane da dama zasu Hallara .

Murmushi Mama Tayi tana zama a daga Gyefen Yusrah Massage ake yi ne? . Eh mama naji ƙafa na tayi mun tsami ne . Okay ". Mama tayi maganan tana kara gyara zaman ta kana ta kalli mai Aikin tana cewa" Tashi ke jeki yi wani Abin ,Ni Bara nayi mata . Mama da kan ki?. Eh mana to Ai gajiya ce , Ko cikin dare na kan yi ma A'isha na , Don yawon ta kullum sai ina matsa mata kafa , idan tayi barci kaman Mara rai saboda Wahalar da kan ta da take yi . Maganan A'isha Da Mama Tayi nan take Yasa Fuskar Yusra sauyawa . Dan gimtse Fuska tayi tana kauda maganan da cewa " Mama Ga list din yanda nake Son Birthday dina ya kasance . Yanzu the next 2 days zamu tafi Dubai Dake Nasan kwana daya zamuyi ko biyu . Okay to badamuwa Yusrah Sai dai Kash A'isha A yau ta fara zuwa School ,ba zan katse mata karatun ta ba , Sai dai mu bari zuwa Ranan Friday ko sai mu tafi tare ". Mama .! Ta kira sunan ta tare da cabe baki na bangane me kike nufi ba? . Mama ke kadai nake Son tafiya dake , kuma shirye-shiryen da kike magana visa Ticket all that mu Bama amfani dashi ,muna da Permanent Flight na Ya Aaaryaaan wanda zai kai mu Dubai . Don haka ba zamu da kowa ba ,dake kadai nake bukata.


Numfasawa Mama tayi tare da cewa " ban saba Barin A'isha nayi tafiya Ni kaɗai ba . Mama Amma kin san nafi kusa Dake fiye da A'isha Ko?. Saurin kallon Mama tayi tare da cewa " Me kike nufi Yusra? . Yeah Mom . Ai A'isha ba Yar ki bace ba , Amma me yasa kike nuna damuwa da ita fiye da Dan ki Aaaryaaan da kuma Ni kai na?. Lumshe ido Mama tayi cikin Rashin jin dadin maganan nata tace " ba haka bane Yusrah , ina Son ku duka , A'isha Ban taɓa ji dai dai da sakan cewa ba nice na kawo ta duniya ba . Sannan kina Son Ganin ɓacin Rai na ? To ki taka A'isha , Ina SO ki dauke ta tamkar Ƙanwar ki , A'isha bata da wata matsala . Mama pls Enough...!! Yusrah tayi maganan cike da Tsawa na rashin tarbiyya . Okay idan na Zauna lafiya da A'isha Shine kike sona mama ? Amma idan kuma naƙi fa ?.


Sai ku sauya Jaha..." Muryar Aaaryaaan ya katse su wanda basu san ma ya shigo Gidan ba . Don tun da ya dawo direct part ɗin sa na da ya nufa yana shiryawa cikin Shigar sa na track suit Mai masifar kyau da tsada . Fuskar sa cikin farin gilashi mai ɗan fadi wanda ya kusa rabin fuskar shi . Sajen fuskar shi ta kara masa kyau da kwarjini da cikar kamala . Juyowa Duka Duka yi a tare suna kallon shi wanda yake takowa zuwa inda Suke . Mama zan tafi Company na , ki mun addu'a , Wani share ne aka zo zan bada amma zuciya ta bata natsu ba . Sauke ajiyar zuciya mama Tayi tana kallon sa Sak mahaifin sa , Amma miskilincin ta rasa daga inda ya debo . Jarabar da masifar tasan na Hajiya Kaka ne . Shiyasa Hajiyar ke bala'in son shi don tasan Wani halayyar nasa ita ya kwaso . To Aaaryaaan Allah ya kiyaye Hanya , ya kuma dawo da kai lafiya . Ya baka Komai na Halal sharrin dake ciki Allah kar ya baka Amin Mama . A kiyaye taimakon na kasa marasa karfi da kuma bayin Allah talakawa .


Jin kalmar Talakawan da mama tayi yasa Yusrah gimtse fuska tana cabe baki tare da kau da kan ta gyefe . A haka Aaaryaaan ya fita don ta kasa Haɗa Ido da shi bare kuma har ta maida masa da magana duk rashin kunyar ta bata yi masa , don tasan Halin sa ba tun yau ba .akwai shi da zafi ga Saurin hannu . Yasha zane ta tana ƙarama kuma har yanzu bai sha wuri ba tana yi masa ya dauki mataki . Bin bayan sa tayi da kallo har ya fice kana mama ta kalle ta tana cewa " Kayan sunyi kyau yanda kikayi list din su . Amma kin manta da Abu ɗaya .! Mama ta ƙare maganan tana kallon Yusrah wacce ta faɗa Duniyar tunanin Aaaryaaan . Yusrah ...! Mama ta ambato sunan ta tana taba ta ,wanda hakan yasa Yusrah saurin kallon Mama . Mama ne ta ɗan kalle ta tare da cewa " Tunanin me kike yi .? Hummm Mama Abubuwa da yawa Dangane dani da kuma Ya Aaryaann . Kallon Yusrah mama tayi a idanun ta ta fara fahimtar Abubuwa amma sai ta dake tana ƙaryata zuciyar ta cikin Sauri . To mu dawo maganan mu ." Okay Mom".

**

Ƙarfe Uku na yamma A'isha Farida Suka fito Cikin school ɗin , Tuni ta shige cikin Group din su Khadija don yayi dai dai da ita , Sam basa ji , sai dai dukan su yaran masu faɗa aji ne a ƙasan namu . A'isha Yayan ki bai zo daukar ki ba ? . Kin san gida ki shigo moton driver na ya kai ki sai ya wuce dani gida . Kallon ta A'isha Tayi tana Girgiza kai Alamun A'a kamin tace " Ban san Gida ba daga nan Gaskiya . Meye sunan gidan ku ? Zee ta tambaya tana kallon A'isha . Marshal Abdu Kareem . Aaaa Kice Daddyn ki babba ne , Kinga Daddy na Soja ne amma general kin ga baban ki yafi baba na matsayi .

Kamin A'isha tayi magana ne Khadijah tace " Hala ba anan nigeria kika yi karatu ba ,shiyasa baki san hanyar ko mawa Gida ba ,baki dade da Zuwan nan bane ?. Kamin A'isha tayi magana ne ta fara Hango moton Aaaryaaan Wanda ya dauke hankalin daliban Wurin . Kai Khadijah kin ga irin moton da Mommy na tasa a shigo mata dashi ta Ruwa . Kin san milliyan nawa yake kuwa ?. Kamin Khadijah ta ba ma zee Amsa ne A'isha tace " Oya Bye bye Ya Aaryaann yazo.! Muje mu gaishe shi . Da sauri suka nufi side din Aaaryaaan Wanda dawowan sa kenan daga Companyn sa . Ya Aaryaann Ina Wuni." Kallon su yayi yana juyawa Gyefen da A'isha Farida Ke shigowa cikin moton . Dan sakin fuska yayi yana murmushi tare da amsa su . Daga ma A'isha Hannu suka yi Aaaryaaan na jan moton tare da barin Farfajiyar parking lot din .

Shiru A'isha Farida tayi ba tare da ta kalle sa ba , ta juya kan ta . Muryar sa Taji yana cewa " Amsa Nan .' Juyowa tayi cikin Sauri tana kallon karamin cup din dake dauke da Ice cream . Wow thank you Ya Aaryaann . Juyawa yayi yana kallon hanyar gaban sa tare da cigaba da Driving ɗin sa . A hankali ya furta ' Wacece Wannan Matan? Ya akayi tasan Ni Tasan Rayuwa ta , har ta iso Company na? Haaaliii..." Ya furta cikin Wani irin jin daci da zafin Rai .

Cabe baki A'isha tayi a zuciyar ta tana cewa " Ƙwaratan ka ne mana . Shigowar Kira ne ya sa ta saurin kallon wayar sa dake kusa da ita , Sunan Aslaaam ta Gani , Wanda ɗazu tunanin shi ta gama da kuma son Ganin shi . Amma a wannan lokacin har ya katse bai daga ba . A haka har suka kai Gida Aslam na kirar Wayar sa yana kin ɗagawa . Daga karshe ne ya turo masa sakon zan zo Gida yanzu , fatan Baby na Tana cikin koshin lafiya? Ka kular mun da ita sosai . Kallo Daya Aaaryaaan yayi ma sakon yana ɗago da Lulun idanun sa suna haɗawa da A'isha ,wacce tayi saurin ficewa daga moton . Keee .! Taji ya kira ta . Cakkk ta tsaya ba tare da ta Juyo ba . Nan da awa daya malamin Islamiyya zai zo ya koyar dake ki shirya . To . Tayi maganan tana Nufar cikin gidan .

**

Zaune A'isha Farida take a gaban Malamin Islamiyya nan a can Gyefen farfajiyar Gidan . Yayin da Sauran Ma'aikatan kowa ke mamakin Wai A'isha ce ta zama yar gida ,wanda ada baya take cikin su masu Aiko ana wulaƙanta su da cin masu mutunci . Fiqihu yake mata babin tsarki inda Anan ne yake mata fada akan Samarin zamani tare da faɗa mata illolin su . Gaban ta ne ya hau faɗi zuciyar ta na tafasa Innalillahi wainna ilaihir raji'un shine kalmar da ta maimaita jin duk Abin da malamin ke fada babu ɗaya Wanda Aaaryaaan bai yi mata ba . Saurin Miƙewa tayi tana nufar Part ɗin Aaaryaaan inda duk kirar da malamin yake mata bata ji shi ba . Shiga tayi bata same shi a falon ba , wannan yasa ta saurin nufar Resting Room ɗin shi . Kwance ta ganshi ya juya baya yana kallon wani Abu . Ya Aaaryaaan....! Ta kira sunan shi cike da Amsa kuwa .


A Miskilance ya Juyo yana kallon ta tare da miƙewa tsaye . Da sauri ta nufo sa tare da daga Hannun tana fara Wanke fuskar sa da Mari tasss³ har sau uku .wani irin marayar kuka ta fashe masa dashi . Aryaaan ka cuce Ni ka cuci ne me nayi maka? Yanzu Malam ....kawai sai ta ƙara fashewa da kuka tana saka hannun ta tare da dukan shi ta ko ina tana fizgar rigar sa da sai da ta yayyaga masa . Na tsane ka .! Wani irin rintse ido yayi wanda sai a yanzu yaji tashin hankali a furuncin nata . Kuma yau zan bar cikin gidan nan , amma ka sani kamin na bari sai na faɗa mawa Mama duka Abin da ka yi mun . Juyawa tayi yana mai Saurin kai Hannun sa yana riƙe ta . Idanun sa sun kada sunyi Jah . A'isha Taji ya kira ta cikin Sanyin Muryar da bata taɓa jin sa da irin ta ba . Zaki iya tona abin dake tsakani na dake .?

Hannun ta takai tana damkar rigar shi cikin zafi da kuma matsanancin kuka take fadin"
Me zai hana mugu azzalumi , bakin Kwarto .! Amma kuma idan ya kasance nine ɓoyayyen masoyin ki fah.? Wani irin faduwa gaban ta yayi . Zare hannun ta tayi daga rigar sa data cukwikwiye wasu irin hawaye na rige rigen fita mata . Baya tayi tana zubewa a ƙasa Gwiwowin ta na haduwa da tiles din wurin . Idanun sa ta gani ya kada kaman Abun tsoro , a hankali ta furta Karya ne kai ba ɓoyayyen masoyi na bane .tuno da yanda suke hada Hannu yasa ta Miƙewa Da gudu tana tsayawa a gaban sa , Hannun ta ta miƙa masa yanda ta saba , Amma sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login