Showing 42001 words to 45000 words out of 110620 words
Jimmalo tayi tana ficewa kitchen din tare da girgiza Kai . Dawo Ki faɗa abun dake Ranki yar Rainin Wayo kawai .
Haushi ne ya kama Jimmalo ganin Yanda A'isha ke damunta da cika baki da Tsiwa kuma tasan Irin su a iya cika bakin suka tsaya tana ganin Abin ta shin hankali da wanda yafi ƙarfin ganin ta sai ta riga kowa Guduwa . Waigowa Jimmalo tayi tana kallon A'isha kana tace " Ke kar fah ki nemi Raina mun Wayo kina jina ? Wallahi ba don Na samu labarin Nawaaz na Son ki ba da sai nayi ƙasaƙasa dake . Tsayawa A'isha tayi tana juya maganan Jimmalo " badon Nawaaz na Son ki ba da sai nayi ƙasaƙasa dake.” Nawaaz kuma ? Abun da tace kenan tana ɗago idanun ta wanda nan taga Tuni Jimmalo ta bace da ganin ta . Hummmm ....Wani irin numfashi ta sauke kamin ta juya tana rage Ƙarfin Gas din zuwa can ƙasa tana Gyara Rigar Aikin ta tare da fitowa tana nufar part ɗin Hajiya Kubrah . Tun a falon take ganin Sauyi daga Ma'aikatan don kowa bin ta yake da kallon da ta kasa fahimta . Mtswww Tsaki taja masu tana nufar rest Room inda take jin magannn Su Hajiya Lubnah wacce bata taɓa Sanin ta ba.
Mom me zaku yi da Wannan wayar bulalan haka ?. Aslaam ne yayi maganan yana kallon su Mum Kubrah wacce take ta hamdala da zuwan su , don burin ta bai wuce ta tijara A'isha Farida a gaban kowa ba . Juyawa tayi tana kallon Jimmalo tare da cewa " Oya yanzu a tara mun duka ma'aikatan Gidan nan mata da maza. Cikin Sauri Jimmalo ta miƙe tana cewa “ Tom An gama yanzu Ranki Yadaɗe . Aaaryaan kuwa dake gyefe su kallon Bulalan baiyi ba bare har ya tambayi na menene . Suna cikin Haka ne A'isha Farida ta shigo Resting Room ɗin nata . Cikin zummar ta don ita bata san mene ake shirya mata ba kai tsaye ta nufi Wurin tana zubewa a gaban su . Ɗago ido tayi tana kallon Hajiya Kubrah tare da cewa “ Barka da warhaka Hajiya ” . Ban za Hajiya Kubrah tayi mata sai cabe baki da tayi tana cewa “ Sauke idon ki ƙasa.” Da'alama baki da kunya da Tarbiyya kina kallo na ido cikin ido ke ga shahararriya ko ” .
Sunkuyar da kan ta Ƙasa A'isha Farida tayi yayin da Aslaam yake kallon Mum yana shirin magana ,shi kuwa Aaaryaan har a lokacin idon sa baya akan su yanda kasan baiji da ganin komai . Kiyi Haƙuri Don Allah. Banza Tayi ma A'isha tana kauda kan ta , Nan A'isha ta juya tana kallon Momy Lubnah wacce tun shigowar A'isha Farida idon ta ke akan ta har a wannan lokacin . Ganin kallon da take mata yasa A'isha jin tsammm duk ta damu a sanyaye tace "Hajiya Barka da Zuwa . Kamin ta ji na bakin Hajiya Lubna ce Mom Kubrah tace " Tashi mu je biyo baya na . A hankali ta miƙe tana bin bayan Hajiya Kubrah wanda Nan Itama Mom Lubnah ta biyo bayan su . Benene na biyu ta ga sun hau na cikin Gidan . Inda taga Sun nufa can bangaren da idan mutum ya tsaya zai hango komai na farfajiyar Gidan . Hannun ta Hajiya Kubrah ta danka tare da nufa da ita Wurin zaf³ Don a tunanin A'isha Kila fadawa da ita Wurin zata yi . A dai dai kariyar da ya tare suka tsaya ....nan taga Mutane sun fi Mutum Ɗari mata da maza . Wani irin Mari Hajiya Kubrah ta wanke Fuskar A'isha da shi tana cewa kalli can.! Kalli mutanen nan duka nace .”
Dafe Kuncin ta A'isha tayi idanun ta na fara fidda zafafan Ƙwallah masu ɗumi da Raɗaɗi . Hajiya me nayi ?. Uban ki kika yi mun." Alama Hajiya Lubnah tayi da Hannu tana miƙa ma wata Yar Aikin su Hannu ita kuma tana bata Mick tare da fara magana cikin izza da giyar kuɗi ta fara cewa " Kunga Wannan Yarinyar da kuke Gani Abun da zamiyi mata a yanzu ya zama makowacce Yar Aiki izina , Ki tsaya a matsayin ki na yar Aiki kaman yanda muka aje ki kar ki kuskura Kice kin kyatare iyakar ki . Numfasawa Momyn Nawaaz tayi tana cigaba da cewa " Wannan Yarinya da kuke Gani Ta shiga ta fita Wurin son Ganin ta tarwatsa mana kan Yaran mu . Nawaaz da Aslaam , ke har Wa ne da zaki da Yaran mu su so ki wai har suyi yunkurin son Auren ki , har da Faɗa duka a kanki . Don haka wannan bulalace da zamu zane ta iya fanshe Haushin da ta bamu zamu zane ta a gaban kowa ne don wanda yake hari da kokarin yin irin Abun da tayi ya zama masa izina ....Bani Bulalan cewan Hajiya Kubrah tana faɗin Nine zan fara zane ta nayi mata Hukuncin da ya dace ”.
**
Gyara Ɗaurin Zanin ta take na atampha mai dai dai kudin dan talaka . Daura kallabin ta tayi tana saka Mayafin ta Cofee brown Wanda ya shiga da Atamphan nata ... Mama Lantana kenan kun san da da Akwai son Kwalliya Sam bata son kazanta . A'a Hajiya Lantana Kin ganki kuwa? Kodai Wani bazawarin aka yi mana kamu ?. Inna Hansai tayi maganan tana Murmushi ganin yanda Mama tayi kiba tayi kyau sosai . Wai kin ganki kuwa Wallahi kullum Dada kiba kike yi abun ki , Anya zaki shiga adaidaita kuwa.? . Gyara Mayafin Mama Lantana tayi tare da cewa " To dama a kullum Damuwa ta Shine Aisha Ta , Naga ta girma ta mallaki Hankalin ta yanzu kuma Alhamdulillah yarinya na ta zama budurwa kin ga mai yayi saura , sauran ƙarike ne. Ehm Gaskiya fa , Allah Alhamdulillah . Yanzu kuma ina kika nufa ne da Hantsin nan ? Ko zaki leka Resturent ɗin ki ne .? . A'a Mama Lantana tayi maganan tana Girgiza kai ,kamin ta cigaba da cewa " Yau na tashi ne ina Ƙwaɗayin son Ganin nayi ido biyu da ɗiyata ,don haka daga nan sai Gidan Aikatau ɗin A'isha Farida ta . A'a To bari mu tafi tare mana ,Nima na matsu naga Farida Kusan kwana nawa ?” . A tare suka fito daga Gidan Mama Lantana tana saka mawa Kofa Ƙwaɗo tare da gangarowa wajen layi .
**
Ɓangaren Su Aaryan kuwa suna zaune ne suka ga Nawaaz ya shigo wurin sam baya ko kallon Gaban sa . Kai lafiyan kuwa? Aaryaan yayi masa maganan yana bin sa da Kallo . A'isha...! Ya furta sunan tare da nufar Stairs da Sauri yana wuce su . Ganin hakan yasa Aslaam da Aaryan Saurin bin bayan sa , Don sai a yanzu suka fahimci Tabbas Su Hajiya Lubnah Da Akwai Abin da suke shirin yi ne wanda su basu kawo ba . Shi kuwa Nawaaz shigowar sa Gidan ne Ganin yanda Ma'aikatan suka taru a wuri ɗaya ko wa idon sa na akan bene hawa na farko yasa shi shima kallon Wurin ,anan ne Yaga Abin da su Mommy ke shirin Aikata ma A'isha Farida . Wannan yasa shi isowa cikin hanzari .
Ɗaga Bulalan Hajiya Kubrah tayi tana shirin saukewa a jikin Farida Wanda cikin Sauri Aaaryaan da basu san da zuwan su ba ya riƙe Bulalan ta bayan ta . Mommy meye wannan meye Haka? Me kuke kokarin yi ne . Yah Aaaryaan Abun da Mommy ke kokarin yi shine dai dai ...! Suka ji Muryar Yusraht daga Bayan su tana tsaye tare da harɗe Hannayen ta biyu , Idanun ta cikin Black shadow . Nawaaz ne cikin ɓacin Rai yace " You're Stupid , Baki da Tunani.! Hannun ta tasa tana sauke bakar gilashin fuskar ta kana ta tako zuwa inda suke ,kaman mai shirin magana kawai su dai sun ga ta rarumi A'isha ne ta shaƙe ta tana duka . Kuka A'isha Farida tasaka mai ban tausayi wanda cikin zafin Rai Aslaam ya ƙwace A'isha daga Hannun Yusraht , Shi kuwa tsananin Haushi sam Nawaaz bai San lokacin da ya koɗa ma fuskar ta wani irin Mari ba , Wanda lokaci guda shatin yatsunsa suka bayyana a Kuncinta .
Wurin ne da mai'akatan yayi tajin² na tsoro da mamakin Wannan Al'amari ,ita ko Yaya Maryamu farin ciki tayi Ganin yanda Nawaaz ya wanke fuskar Yusrah da Mari . Innalillahi wainna ilaihir raji'un shine kalmar da Hajiya Lubna tayi . Nawaaz yau kaine ka Mari Ƙanwar ka yar uwar ka ta jini akan bare , Wacce baka san Asalin ta ba , talaka kaskantacciya yar Aikin ku ?. And SO What mom? . Ina Son A'isha kuma na shirya na Rabu da kowa don na zauna da ita ,ita kadai a rayuwa ta .
Tafa Hannu Hajiya Kubrah ta hauyi na salallami kana tace “ Wannan Abin da suke yi yaran nan akan wannan karfan ba haka kurum bane , i have Already told you that, Yanzu kin gani da idanun ki ko? Sihiri ne . Bayan Aslaam A'isha Tayi tana cigaba da Kukan ta cikin tsananin tashin hankali,tun da take bata taɓa Ganin musiba irin na yau ba a rayuwar ta . Ba kuma ta taba yarda Naawaaz Son ta yake ba , ta dauki hakan a matsayin suna so ne suyi lalata da ita kaman yanda Aaaryaan yayi mata cin mutunci .
Juyawa Hajiya Kubrah tayi a fusace tana cewa " Kaima Aslaam naji naka Labarin cewa kana Son A'isha Farida wanda duka baku isa ba ,ko don kin isan shine zaku tsaya har ku mun katanga na kasa dukan A'isha ?. To bani Wuri kamin yanzu Ranka ya ɓaci.? Kallon ta Aslaam ya tsaya yi yana ƙoƙarin bata hakuri ta fizgo A'isha dake bayan shi tana Wurgar da ita gyefe . A cikin ku naga Wanda zai hanani dukan A'isha Farida.! Juyawa tayi tana kallon Aaaryan tare da cewa " Bani Bulalan Hannun ka? . Kasa miƙa mata Bulalan yayi ya tsaya yana kallon ta ....oh ko kaima Son ta kake yi?. Shiru yayi yana kallon Hajiya Kubrah , kamin ta kuma cewa cike da Tsawa " Idan son ta kai ma kake yi to ka riƙe Bulalan ku gani ba zan bige ta ba A wurin nan. Kallon A'isha Farida yayi suna yin ido Hudu gaba ɗaya ta gama ficewa a hayyacin ta , hular kan ta sun wurgar mata , Ga kan ta babu kitso gaba ɗaya gashin ta ya gama rufe mata fuska . Girgiza masa kai tayi tana narke masa Alamun kar ya bata Bulalan ,Amma kawai sai yaji Mom ta fixge Bulalan A hannun sa tana dagawa tare da shirin Sauke Bulalan a jikin A'isha .
Kubrah Don Allah idan ke kin cika cikakkiyar mara mutunci ki bigi A'isha Farida bance ki dakata ba don Uwar ki da Ubanki .! Wani irin Yamm Wurin yayi jin wata murya ta daban . Gaba daya hankula ya dawo kan Mama Lantana da Inna Hansai wanda shigowar su kenan suka ga Wannan Abun dake faruwa . A'isha ne tayi saurin furta " Maaama cikin tsananin kuka tana nufar wurin tare da shirin fadawa don ta isa inda take . A'isha Dakata .! Muryar Mama ya kuma katse ta , Wanda Hajiya Lubna mutuwar tsaye tayi.... Ita ko Kubrah Wasu irin ƙwallah ne na tashin hankali ya ciko Ƙwarmin idanun ta . Idan kin haifu ki taba mun Ɗiyata , na rantse ba zaki zaune Bulalan ba sai na shigar Miki biyu masu kyau , idan ke daya kike yi mata kenan . Cikin tashin Hankali Hajiya Kubrah ta kalli sojojin dake a kasar tana cewa " ku daura kun bindiga a kan ta ku har be mun ita yanzu nan ....! Wani irin ihu A'isha Farida ta saki tare da nufar Varrier ɗin tana Faɗawa b tare da tayi tunanin a ina zata sauka ba ......Momyn Nawaaz ne tayi saurin cewa " Inalillalahi wai'inna ilaihir raji'un......"
#MAMANTEDDY
*🕊️FƳAƊE...!🕊️*
#Romantic
#Sympathetic
#Erotic
#Story.
20
Littafin fƴaɗe na kuɗi ne ban yarda Wanda bai biya ba ya karanta Don Allah...Masu buƙatar book din Regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932.
**
Aslaaam ne da Su Aaryaan cikin gigita suka yo inda A'isha Farida ta Faɗa Wanda a tare suka ja wani irin ajiyar zuciya mai ƙarfi don Ganin Allah ya kiyaye Tahowan nan nata da tayi a kasan wasu Sojoji ne Wanda cikin ikon Allah daya daga cikin su yayi nasarar tare ta yana kama ta tare da cafeta . Ganin Har A lokacin Sojan bai Sauke A'isha Farida daga Jikin sa bane yasa Aaryaan cikin Ɗaga Murya yace " Dallah malami dan Sauke ta , ka riƙe ta goya ta zaka yi ne ko kuwa haɗa ta da jikin ka zaka yi ku koma Ɗaya?. Jin haka yasa Sojan sauke A'isha yana kallon ta tare da cewa " Pls be careful of your self okay?. Sam A'isha Bata tsaya bi ta kansa ba inda Mama Lantana take tsaye har a kuma Wannan lokacin sojojin bindigogin su na kan ta . Rungume Mama Lantana tayi tare da fashewa da kuka . Muryar Hajiya Lubnah ne ya katse su tana cewa " kuyi maza ku sauke Wannan bindigan daga Kan Hajiya Hadiza . Tayi maganan cike da bada Umarni hankalin ta a tashe don har duniya ta nade ba zata taba mantawa da macen da ta zama sanadin Farin cikin Yayan nata ba . Kun san Mama Lantana da sanin yanda ake tijara talaka mai fadin Rai bata yarda da Raini ko wulaƙanci ba . Cikin Zafi Mama Lantana tace " A'a Lubnah Kar wanda ya sauke bindigar sa daga kai na , So nake su maida bindigogin su yanzu . Maza Ku ɗaura tayi magana n cikin daka Tsawa tare da kallon murtika² Sojojin da fuskar su babu imani A shirye suke suyi kisa .
Cigaba da magana Mama Lantana tayi tana cewa " Ba umarni ne Hajiyar ta baku ba ? Ko kuwa bata isa daku bane?.
A'a Aaaa ....! Kar wanda ya maida Bindigar nan akan ta . Cewan Hajiya Lubnah tana faɗin Don Allah Hajiya Hadiza ki saurare Ni ki kuma fahimce Ni ... Kamin Mama tace Wani Abu ne Hajiya Kubrah cike da Ruɗewa gaba ɗaya duhu² take Gani. Cikin Wani irin murya Na rawa tace " Me ya kawo ki Hadiza? Me kuma kika zo yi anan?.
Wani irin kallo Mama Lantana tayi mata kana ta juya tana kallon A'isha da har a lokacin tana Rungume da ita tana zubar Hawaye . Ɗiyata ce tayi sanadiyar shigowa na cikin gidan nan . Kuma shigowar ta ita kan ta akasi ne , don badon Ita ba ,kuma da Nasan Cewar nan Gidan Alh .Abdu ne Da babu abun da A'isha zata zo tayi a cikin gidan nan ,Kinga kuwa komai zuwan Akasi ne . Kin yi mun kuma kiyi ma Yata? Ai kuwa Kinga Hakan ba zai yiwu ba.? Da kin kuskura kin bige A'isha Farida Wallahi tallahi ba zan jira hukuma Ni da kaina sai nayi Miki duka a cikin gidan nan .
Cikin Wani irin Ɗaurewar Kai Yusraht tace " Ke Malama Wacece ke? mommy See how she's talk to you Amma kun kasa kasa² da ita tana talaka . Tasssss... Hajiya Lubnah ta Wanke Fuskar Yusraht wanda cikin gigicewa ta ɗago tana fashewa da kuka tare da cewa " Wacece ita ? Akan talaka kika mare Ni? Daga Hannu tayi zata Kuma Wanke fuskar ta da Mari Aslaam yayi saurin riƙe Mom Lubnah pls Easy pls . Kiyi Haƙuri Yusraht yarinya har yanzu bata iya magana ba . Karya ne wannan .! She's almost 25th ace bata san ya ake magana da babba?. Nawaaz ne ya kalli Mom Lubnah tare da cewa " Mom i didn't Understand Everything? Mommy wacece Mahaifiyar A'isha a tare damu . ? Ita din Wacece naga alamun kin nuna sanayya a ganin ta na farko da kikayi .
Kallon Nawaaz tayi tana cewa " Yusra ban taɓa nuna maki fushi na ba ,amma yau kin gani to komai zan yi Miki akan Hajiya Hadiza....shin kun san Wacece itama kuwa ? To matar Alh.Abdu Kareem ce . What...? Yusra tayi maganan tana dafe Ƙirjin ta tare da kallon Mommy . To yanzu sun rabu ne? Ta furta maganan cike da mamaki Wanda Jin Haka yasa Hajiya Kubrah saurin juyawa da sauri tana shirin barin Wurin . Bayan ta Aaaryaan ya biyo wanda sam bata lura dashi ba. Hajiya Lubnah ce ta cigaba da cewa ' Bai taba sakin ta ba ,kuma har kwanan Gobe da Igiyoyin Auren sa Akan ta . Mutuniyar kirki yar gidan mutunci...Mom Lubnah ta ƙare maganan tare da kallon inda take hango Mama Lantana , wayammmm ta Gani basa Wurin Alamun sun dade Da Tafiya suna Ficewa daga Gidan .
Hasbunallah . Naawaaz ka taimake mu duk inda Hadiza take ka nemo ta a yanzu .itace farin cikin Alh Abdu Kareem wanda tsawon shekaru talatin yake yake yi amma da ciwo a zuciyar shi . Kamin ta ƙare magana ne tuni Nawaaz da Aslaam suuka juya tare da barin wurin suna nufar Farfajiyar Gidan da Sauri har da Gudu.
**
Ɓangaren Hajiya Kubrah kuwa tana sauka daga Stairs jikin ta Ko ina Rawa yake yi . Kirar Wayar Ƙanwar nata tayi Wato Hajiya Rahmatu . Kira ɗaya biyu ta daga Wayar ....Rahma ina cikin tashin hankali, Wai ba bokan nan yace kurciya akayi mata ba? Kuma ko shekara biyar ba'a yi ba kika ce mun yace Ya mutu shiyasa Asirin da mukayi mata na tashi duniya tana karuwanci ya ƙarye ya koma Kan Ɗan ta Aaaryaan yanzu .....Cikin Sauri Rahmatu ta katse ta cike da rashin Fahimtar maganan wace take yi . Hajiya Kubrah wai maganan Wacece kike yi ?. Wacce banda Wannan yar bokayen Hadiza Hadiza nace mahaifiyar Aaaryaan..... Cakkk maganan nata