Showing 51001 words to 54000 words out of 110620 words
tare da fara cewa " To me ma zai iyan ? Rainin Wayo kawai , Tana faɗin maganan ne taji Muryar sa a bayan ta daf da ita yana cewa " Me kika ce?. Cikin Sauri Aisha Farida ta Juyo tana kallon Sa tare da fara in'ina tana mai cewa " Babu komai ,bance fa komai ba . Matsawa yayi kusa da ita yana kama dan mitsulun bakin ta tare da dan murɗa mata Wanda sai da Ta saki yar ƙara . Dakatawa yayi da hannun sa yana sakin bakin nata kana yace " Cewa kikayi me zana iya ko?. To bari kiga Abin da zana iya ...! Kamin tayi Wani magana ne taga gaba ɗaya ya mata rumfa yana Rufe ta tare da haɗa ta da jikin shi , Da jikin Stairs din ya matseta kam yana jin yanda Zuciyar ya ke Harbawa . Baki da kunya ko? . Ina dashi wallahi.! Waye Ni a wurin ki? . Oga ." Ta basa amsa kai tsaye ,kamin yace " Ƙarya zaki mun?. Kuka ta fashe masa dashi tare da cewa " Ni mai aikin ka ce. Humm sauke Numfashi yayi tare da Cewa" Har yanzu baki san matsayina a wurin ki ba , Ammma......kamin ya ƙare maganan ne ya kai bakin sa yana Ɗaurawa Saman Laɓɓan ta tare da kamawa yana fara tsotsan laɓɓan ta tare da manna mata Wasu irin zafafan kiss Wanda hakan ya kuma daga mata Hankali . Kusan mintuna biyu ya diba a haka , kamin ya zare bakin sa daga nata , hannun sa yasa yana kama ta tare da Rungume ta tsam a jikin sa . Wai tsoron kiss din ma kike ji? Hummm baki san matsayi na ba , amma a gani na Wannan Abin da nayi Miki ya isa ki san matsayi na a wurin ki daga Yanzu .
Kasa masa magana tayi don har a lokacin gumi ne ke sauko mata . Kafe ta da ido yayi kana yace " Maza fita can farkon Falo kisa Israel ya kai ki Inda Mama da Inna Hansai suke . Saurin juyawa tayi har tana karo da kujerar gewayen Falon , Amma bata dakata da tafiyar ta ba , da sauri ta fice daga inda yake . A zuciyar ta kuwa babu abin da take yi sai ja masa Allah ya isan ta .
Motsin Israel taji a kitchen wannan yasata cikin Sauri ta nufi kitchen din tare da Kirar sunan sa " Isreal ." Yess Madam ." Ya furta tare da juyowa yana kallon A'isha yana aje Fraying pan Din hannun sa... Ka ji mun rainin Hankali." A'isha Farida tayi magann tana kama ƙugu cike da fitina . Cigaba tayi da cewa" Ka ga nayi kama maka da Irin shirga² matanan? Ko kuma matan Gida? To Ahir kar ka sake kirana da Madam , just tried to call my name directly A'isha Farida. Amma kar ka ƙara kiran sunana da Madam Bana SO.! To sorry mah. Ya furta maganan cike da ladabi wanda jin ya kuma kirar ta da mah ,yasa A'isha cewa " Isreal Are You not seeing me well?. Baka gani na da kyau ne? Tayaya zaka rinka kirana da sunan iyaye na . Shima bana So . Buɗe baki yayi zai kuma bata haƙuri nan tayi Saurin dakatar dashi tana cewa" Ya isa haka .ina su Mama suke ?. Takowa yayi suna fitowa daga kitchen din a tare yana nuna mata Hanyar da zata bi taje inda Mama Lantana take . Motsin shigowan ne babu ko sallama yasa Aisha Farida da Israel juyawa suna kallon Hanyar shigowa .turus A'isha tayi tana sakin baki Galala tamkar yar fari... Me ya kawo ki nan.? Suka ji Muryar Aaaryaan ya katse wanda basu san yana zaune a bayan su ba . Saurin juyawa A'isha tayi tana kallon sa ,kana ta juya tana kallon Bie-bie dake sauke bakar tabarau din fuskar ta . Cikin Muryar yan duniya ta kalli Isreal tana cewa " Tafi mota na ka fiddo mun da Akwatina na ka kawo mun nan . Ok Mah. Yayi maganan da Sauri yana barin falon. Juyawa Bie-bie tayi tana sakin ma Aaaryaan wani irin murmushi mai tattare da nuna So da kauna . Laifi ne dan mata tazo gidan mijin ta..?
Ta ƙare maganan tare da maida bakar tabarau din idanun ta . Wani irin kallo Aaaryaan yayi mata , Wanda ya fi nata shahara da tacewa .kamin A'isha Taji mai zaice ne tayi Saurin jirgawa tare da barin Wurin tana nufar inda Isreal yace mata su Mama na can . Bin bayan ta Aaaryaan yayi da kallo , a zuciyar shi yana cewa " Wannan Yarinyar wani tsiyan taje kulla maka . Saurin miƙewa yayi tsaye yana ma Bie-bie wani irin kallo na ke shashasha ce . Wuce ta yayi yana nufar falon Mama da Sauri tare da kirar Sunan A'isha duka don ya dakatar da gulman shi da a cewan shi zatayi......!
Mrs.....usm”.
#Mamanteddy
*🕊️FƳAƊE....!🕊️*
***Romantic love Sympathetic and Erotic Story.***
*SHATOU MAMAN TEDDY 🧸*
***26***
*Don Allah kar ki karanta mun Idan baki biyani ba , Littafin nan na kuɗi ne Regular group ₦500... VIP group ₦1000... Special payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932...Idan VTU transfer ne sai ki tura kuɗin ki kai tsaye ta Wannan number 09061467409*
```~Tallah~```
To babban magana ina iyaye mata masu san kasancewa da mazajen su har Abada da'iman? Ina macen da matsaloli na Jinnu ko Sihiri yayi mata katutu ya addabi Zaman Auren ta ke dama Rayuwar ki baki ɗaya ...to Allah nacewa tashi in taimake ka . Mata masu fama da Rashin aure shekaru 30 ko sama da hakan duka a gaban iyayen ki abun tun bai damunki a yanzu dole ya fara damunki...” maza garzaya taskar Empire domin warwarewar duka matsalolin ki ...na duba kuma na gani , Maganin ta babu ɓata sam , da Ayar alƙu'ani take magani ba tsafi kawai Kunsan Magani da Ayar Allah , Allah na saurin amsa kamar yankar Wuƙa . Bhuzuwa Empire Aikin ta ya haɗa ta Hanyar alƙu'ani ,tana ma ƴammata marasa farin jini magani da zallar nono , ƙwai ... mallaka babu irin wanda bata yi , na suratul yaseen, Rahman , Izaja'a , jauharatul kalam da dai sauran su ...masu buƙatar ƙarin bayani ga nombobin su kamar Haka 08139762831 Allah ya taimaka Amin .
*Second Round advert for you mah love*
Ina mata yan ƙwalisa masu son Ado na kece raini dan gane da saka suturu....kun sai dai sutura itace mace , ƙwarai kuwa kaya kike buƙata ? To kin samu . Dangane da Atampha , lace , materials, Shadda Galila & Gezna .Hand bag's, Takalma na yara da manya , Dubai or foreign duka zaku same su a wurin Hajja Fatima a nan birnin Zaria . Ina masu buƙatar mayafai na alfarma da kuma na ƴammata acafai acafai? To duka zaku same su ƙarin daɗi harda Abayas Arabian Gown duka zaku same su a wurin Hajiya Fatima kai abin sai Wanda ya gani , ga tsaruwa ƙyau da rahusa ku dai kawai ku tuntuɓi Wannan number domin ƙarin bayani
**
“Hankalin Aaaryaan idan yayi dubu ya tashi ,nufar falon su Mama yayi kansa na sara masa Wannan yarinyar wai me take nufi? Ta mai dani kaman sa'an Wasan ta? To Meye ma taje tayi ta faɗa ai ko Daddy ma yasan me nake yi and so what don ta faɗa mawa Mama itama ta sani A yau.? Mtswwww Dogon Tsaki yajah yana mai maida Ƙafarsa baya da zummar Ya juya inda Bie-bie take , Wata zuciyar ne tace masa " Ka shiga kayi mata baraza sannan ka fito , at least ai tana tsoron ka , rashin kunya ne da girgiwa yayi mata yawa .
Saurin Amincewa da shawarar Da zuciyar sa ta basa yayi yana nufar Falon Da su Mama suke ita da Inna Hansai A dai dai lokacin ne yaga Mama na zaune idanun ta na tsiyayar da ƙwallah mai tattare da tsananin damuwa ..? Hankalin sa ne ya tashi Wani irin Tsawa ya daka mawa A'isha dake Tsugunne Gaban Mama itama tana kukan , shi duk a tunanin sa Ta faɗa mawa Mama ne zuwan Bie-bie da duniyar cin sa da yake yi da ƴammata da matan Aure duka bai bari ba . Baya tunanin lahira . Keeeee....! Okay You told her?. Kin faɗa mata ko?. Ɗagowa Sukayi mama Lantana da Inna Hansai , haka itama A'isha dake rarraba ido tana kallon sa tare da saurin Girgiza masa kai . Ƙurrr yayi mata yana bin ta tare da watsa mata manyan idanun sa kaman mai son Gano Gaskiya , gyefe daya na zuciyar sa na harba masa da Sauri da Sauri kawai sai yaji baya Son Mama tasan Baɗalar da yake aikatawa .
Masu karanta mun littafi bati Allah ya isa fa kuke karantawa🙄 gwara Don Allah ku bari ki daure ki saya ki wuce wurin let's us back to Our Story .
Mama ne ta buɗe baki xata yi magana amma sai Inna Hansai ta riga ta , A'a Aaaryaan Wani magana kuka yi ne? Ai bata ce komai ba tun Shigowar ta ,ganin Maman nata a wannan halin itama shine fa ta rakube Gyefen ta tana kukan . Hannun sa yasa yana turbitsawa cikin Sumar kansa tare da Sauke Numfashi a hankali ...Muryar Mama ne yaji tana cewa " Me ya faru? Meye baka so ta faɗa mana?. Tsayawa yayi yana ɗan shafa Sajen fuskar sa tare da kame kame , kana ya kalli A'isha Farida da itama idanun ta na akan sa don ta matsu taji mai zaice kuma. Dama Mama nace mata ne gobe zan taho mata da school uniform din ta , zata fara zuwa makaranta a gobe inshallah kuma Nine zan kaita . So i see lyk bata farin ciki ne da hakan . Kai Allah yayi maka Albarka Mama tayi maganan tana sakin Murmushi wanda faffaɗan Hushiryar ta irin nasa sai da ya bayyana . Gimtse fuska A'isha tayi tana kallon sa baki sake tana mamakin dama ya iya karya haka ?.
Takowa yayi yana isowa tsakiyar falon tare da zama a kasan Carpet yana Daura hannun sa akan giwowin Mama . To Mama Idan A'isha ba Wani magana ta faɗa Miki ba , me yakawo Wannan Hawayen na saman Fuskar ki Ummie?. Bana son Ganin Abun da zai Ɓata Miki ko mun ƙanƙantanshi . Wasu Ƙwallah ne suka taho daga Ƙwarmin idanun Mama ,wanda cikin Wani irin murya Na raɗaɗi ta fara cewa " Kayi Aaaryaan ban tsaya tare da kai ba , baka san Daɗin Samun Uwa ta gari ba. Fiddo da ido A'isha tayi a Zuciyar ta tana cewa " Tab Ashe nima banyar aƙas ba , Tsiwar mama na koya , Yanzu Hajiya Kubrah ba Uwa ta gari bace fa take nufi...Hummm Ai mama da kin san Waye shi da abin da yayi mun , Wallahi da kin ƙara Wani kukan akan Wanda kike yi a yanzu . Duka zancen zuci take yi dai dai tana maida Hankalin ta ga Mama ne taji tana cewa " Amma nayi Rayuwar farin ciki na manta da duk Wata damuwa ta ,da bakin ciki rashin Ka da mahaifin ka a tare dani, kasan Wacece ta dauke mun Wannan Damuwar ? A'isha ta , Auta ta .! Itace idan na kalle ta nake jin Zuciyata cikin matsanancin Farin ciki , Samun A'isha A Rayuwa ta alheri ne babba. Ummie...! Yayi maganan tare da kama hannun ta yana sarƙewa da nashi tare da gyada Mata Kai Alamun yana Sauraren duk Abin da take fadi kuma yana jin shi a jinin jikin sa.“ Aaaryan...”
Amsa ta yayi yana furta " Na'am Ummie na”.
Aaaryan ga A'isha ta nan ko bayan Raina , ka kula mun da ita , tun da muke tare ban taɓa bari hawaye na baƙin ciki ya sauka daga idanun ta ba ,ko laifi tayi Ni abun da nake yi goya mata baya , wannan yasa ta taso cikin walwala da jin dadi . Ka kasance kana kulawa da ita tamkar Ni , koma fiye ...” A wannan lokacin ne idanun A'isha Farida suka fara fidda Hawayen tausayin kan ta , Wani irin kallo Tayi mawa Aaaryaan a zuciyar ta tana cewa " Yazo ya rabani da mama na". Kawai sai ta fashe da kuka tana nufar Mama tare da faɗa jikin ta ,tana Rungume ta . Murmushi Aaaryaan yayi yana danne Karayar da zuciyar sa tayi yana cire hannun sa daga Riƙon da yayi mawa Mama tare da Ɗaura hannun sa a kan A'isha yana shafa Gashin kan ta da ya sauko har gadon baya , alamun Rarrashi . Stop crying pls , zan kula dake kaman yanda Mama tace ". Ɗago idanun ta tayi da suka yi duludulu na tsaban kuka kamin tace " Ni kulawa kuma na nawa ,wanda kamin ma ai na gode .! Tana faɗin haka ta komar da kanta tana ƙwantawa a Ƙirjin mama .
Shi kadai yasan mene take nufi , Wannan yasa shi dannewa yana matsawa dab da kunnen ta tare da raɗa mata ƙarikon Rungume ta pls ki koma cikin ta ne da Rayuwa ." . Saurin Ɗagowa tayi tana kallon sa amma sai gani tayi yayi mata kallon sama da ƙasa yana watsarwa . Juyawa tayi tana kallon Mama sai kuma taga ya miƙe tare da cewa " Ummie na bari na koma gida yanzu na taho ma Wannan Small Kid din naki da Uniform din ta”. Dariya mama Tayi don ta gane Tsokanan A'isha yake yi . Ƙwantawa tayi tana Sauke Numfashi a hankali tare da faɗin " Baka san Wacece Ni ba ,but you will know who I'm i verry soon ". Ficewa yayi daga Falon dai dai Israel na shigowa hannun sa ɗauke da tray manya irin bangajin nan asalin babban da Abincicuwa haka yayi ta sintiri yakai ya dawo da kalolin Abinci wani Bowl ya aje wanda yake dauke da Pepe chicken,Lumshe ido A'isha tayi tare da fadin Mama na bari naje ba ba ciki na hakkin sa wallahi yunwa nake ji . A'isha acici....! Inna Hansai tayi maganan tana Dariya .
***
Ɓangaren Naawaaz kuwa tun da yaji Wacece matsayin Mama Lantana a wurin Daddy Farin cikin sa ya ƙasa ɓoyuwa , Wanda ita ko Yusraht takaici ne ya sa ta tun da ta shige Bedroom ɗin Hajiya Kaka bata sake fitowa ba har suka gama tattaunawar su tare da debo jiki suna tahowa gidan Aaaryaan inda Su Mama Lantana suke . A kuma lokacin da suka isa A'isha ta shige Bedroom tana barcin ta don sosai ta mike Ƙafa ta saki jiki abun ta . Hankalin Mama ya tashi Ganin Wanda bata yi tsammani ba . Musamman mahaifiyar Nawaaz wanda ta nuna mata soyayya tun bata da Wayo . Kuka suke yi sosai . Yayin da su Daddy da Hajiya kaka da Sauran yaran nasu samari ke Hamdala ,don Har Anan Aslaam yana Wurin a wannan karon har da Sadeeq don Aslaam fir yaƙi koma gida yace ba zai iya barci ba sai yaga Matar sa don sunan da ya naɗa ma A'isha Farida ke nan a zahiri da kuma birnin zuciyar sa . Bayan faruwar komai ne da ban Haƙuri Daddy da kan sa yaba ma Mama haƙuri tare da roƙon ta a gobe zasu tafi Garin Kaduna don A ƙara sabun ta auren su , sannan kuma anan ne Hajiya kaka take tambayar ta Wacece A'isha a gareta . Shiru Mama tayi idanun ta da fuskar ta na sauyawa wannan shine karo na biyu a rayuwar ta da ta taɓa furta A'isha ba Ɗiyar ta bace. Girgiza Kai Hajiya da Su Daddy suka yi cike da jin Matsananciyar tausayin A'isha Farida , Daddy yayi Alƙawarin Rufe Wannan Sirri na bashi ne mahaifin A'isha ba . Kuma anan yake rokon su duka akan kar su bari A'isha tasan Bashi ne mahaifin ta ba , yayi Alƙawarin kulawa da rainon ta fiye da Mahaifin da yakawo ta Duniya .
Baƙaramin daɗi matanan Daddy yayi masu ba har da Aaaryan wanda yake ta fushe² ganin su Nawaaz a cewan shi wannan wani irin masifan damu ne ?. Aslaam kuwa wani irin narkakkiyar ƙauna da tausayin A'isha ya ƙaraji ya damƙar masa zuciya , Haka ɓangaren Nawaaz ma . Sadeeq dai shiru yayi yana Ganin ikon Allah , a ran shi yana cewa " Meye Na riƙe Yar da ba'a san Asalin ta ba ? Abun da yafi a kaita Gidan marayu ko kuma ta cigaba da Shara da Goge goge ." anan ne aka rufe Wurin da Addu'a, wanda sai a sannan Mama ke cewa " Ina Hajiya Kubrah . ? Dafe kai Daddy yayi tare da cewa" Ayyya kin ga Sam na manta mu taho tare da ita ,Ammma kummmmm......Kamin ya ƙarika ne suka fara Ganin BBC news na Hasko masu Fuskar Hajiya Rahmatu ,wanda cikin sauri Hajiya Kaka da Mommy Lubnah suka hau faɗin 'la'ilah ha'illah . Hajiya Wannan Ai Rahmatu ne . Gani sukayi an rife jikin ta da wani wulaƙantaccen Ƙyalle , fuskar ta kawai ake dauka . Gyefe guda kuma Gawar bokan tsubbu ne warwasss shi ba a sitirtashin ba , yana Kwance baki ƙirin bakin shi kudaje sai bi suke , gaba ɗaya ya sauya ya koma tamkar naman Daji mara kyaun gani . Babu Abin da yan jarida ke Haskowa Fache Marar shi inda aka datse maxantakar sa .!
Nan kuma take BBC news suka fara fadin Waye shi da kuma ita Hajiya Rahmatu wanda suka ce sun ga Gawar sune A tare da juna daga karshe suka bayyana suna son karin bayani daga Ministan Tsaro . Dafe kai Mama Lantana tayi tana taxbihi cike da furta Innalillahi wai'inna ilaihir raji'un. Yanda ake Haska bokan yafi daga masu hankali . Cikin Wani irin yanayi Hjy Lubnah tace " Yaya Abdu don Allah kayi saurin kirar