Showing 48001 words to 51000 words out of 110620 words

Chapter 17 - FYADE COMPLT COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Sep 2024

8164

so Shine Rayuwar A'isha kar wani Abu ya same ta. Inna Hansai ne ta katse su da magana wurin cewa " Ƙwarai Wannan Gaskiya ne , Mu fara kokarin ceto Rayuwar ta da fari ,daga Baya ayi maganan . Hannun sa yakai yana shafa Fuskar ta kamin yace " Mom stress ne yayi mata yawa . Babu inda Zata sha iska sosai . Sai dai mu fita Baranda can yafi iska . Idon sa ne ya sauka akan Mafircin Da Mama Lantana ke firfita dashi . Saurin kai Hannun sa yayi yana Daukar Mafircin tare da fara Mata Firfitan don ta samu iska . Wani irin Dogon Ajiyar zuciya ta ja tare da Ware idanun ta Wal.... Mama Lantana ce ta riƙe Hannun ta tare da kirar sunan ta A hankali . A'isha ...! A hankali ta Ware idanun ta tana kallon Mama Lantana tare da cewa " Mama ...! Naam Aisha kina Gani na?. Gƴaɗa mawa mama Lantana kai tayi Alamun eh kamin ta kuma juyar da idanun ta akan Aaaryaan Wanda take Kwance jikin shi ba ta sani ba . Ido huɗu sukayi Wanda nan take ta Ƙara fiddo da idanun ta Waje . Wani irin Uban Ihu ta saki tana kokarin Miƙewa daga Jikin sa ne taji ya kamata yana kanƙame ta da Ƙirjin sa . Suman kan ta ya shafa tare da furta " ki Natsu.! Ahhh Mamaki ne ya kamata na jin furucin nata . Me yake nufi Wannan ? Juyawa tayi a hankali tana kallon Mama kamin tace " Mama A ina nake ne.? Inna Hansai ce ta amshi magannn tare da cewa " A'isha a gidan Mama fa kike yanzu .


Saurin muskutawa tayi daga jikin sa tana Miƙewa tsaye tare da kama ƙugu . Bin Aaaryaan take da Wani irin kallo kamin tace " Nan Gidan mu ne malam . Duk Abin da ya faru tsakanin mu ka ɗauke shi ya riga da Ya Wuce a yanzu baka da iko a kaina har kana Wani ce mun wai na natsu . Bin ta yayi da Lulun idanun sa kaman mai mata kallon ƙurulla , sai kuma yayi Murmushi yana tashi daga Zaunen tare da kallon Inna Hansai yana cewa " In ba damuwa ina Son magana dake . Tom Dan nan mu je ko?. A tare suka fice daga Ɗakin yayi da A'isha Farida tayi Saurin matsawa kusa da Mama Lantana tana cewa " Mama kin gane shi kuwa?. Murmushi Mama Lantana tayi tana gyaɗa Mata Kai . Mama To A yanzu Meye mafitan mu?. Gidan Baba na zaki koma Ko kuma Gidan Daddyn Aaaryaan?.

**

Ɓangaren Hajiya Kubrah kuwa Ana Wannan Tsaka da Faruwar wannan Al'amarin ne Marshal Abdu Kareem ya iso Gidan , dai dai yana shiga Hajiya Lubnah na kokarin Barin cikin gidan . Tsayawa Yayi yana jin na bakin ta tare da mamakin faruwar Al'amarin . Cikin wani irin murya yake fadin " Aaaryaan yana Wurin a lokacin faruwar Al'amarin kuwa?. Amsa Momy Lubnah ta basa da cewa " Eh yana Wurin . Amma yanzu Kuma Ban san a inda yake ba , hankali na a tashe yake , ban san inda ya nufa ba a halin yanzu . Shiru Daddy yayi na yan mintuna kana taga yayi Murmushi irin tasu ta manya kamin daga bisani yace " Kar ki tada Hankalin ki , a ko ina Aaaryaan yake a halin yanzu baya Wuce dayan biyu. Ko yana neman mahaifiyar sa ko kuma a yanzu haka yana tare da Hadiza . Shiru Mommy Kubrah tayi tana Goge ƙwallahn idanun ta ,kamin tace " To Allah yasa ."

**
Rahmatu kuwa sai da tayi kwana uku a jejin nan sannan boka ya sallame ta , tare da cewa " aiki anyi an gama tun ranan da ta kawo kanta. Jiki babu kwari tamkar an mata duka ta koma Gidan mijin ta , Wanda Tsawon kwana ki uku suke neman ta , har an fara sakawa a tv da wurare. A Farfajiyar gidan ta ne ta fara Ganin Jiri dai dai Kishiyar ta na fitowa wanda ta zama da ita da banza a wurin mijin babu Maraba. Hajiya ...! Ke ce? Yaushe kika dawo..? Daga Jeji nake.? Rahmatu ta bata amsa a buge tamkar mashayiya....Jeji kuma Hajiya?. Eh Daga nan Nake Uwar ki zaki mun ko uban ki?. Shiru Hansa'u tayi tana kama bakin ta don tasan bata da Karfi a cikin gidan , Don a kwanaki da tanemi kwatar yan cin ta , budan bakin mijin nata cewa yayi tabi Rahmatu su zauna lafiya , Amma ta nemi Yin saɓani da ita to zai sallame ta daga Gidan shi , wannan yasa Hansa'u duk Wani cin kashin da Rahmatu zata yi mata take dannewa ta rabu da ita . Ita dai kullum tana kai kukan ta ga mahalicci . Allah ya baki Haƙuri Abin da Hansa'u tace kenan tare da Raɓata tana wucewa , itama Rahmatu na nufar ɗakin ta . Bayan tafiyar Rahmatu ne Hansa'u tayi shiru tana tunanin irin zaman da take da mijin ta , Rabon ta da kwana a dakin mijin ta su hada shimfiɗa tafi shekaru goma . Girgiza Kai tayi tana jajanta ma kanta kamin ta kalli ƙasa . Saurin ƙarikawa Wurin tayi ganin Wasu irin tsutsotsi dake bin Ƙasa Farare . Ikon Allah me ya kawo Wannan Abin kuma nan ?. Sani...! Ta kwaɗa Kirar Sani mai ba flowers Ruwa . Cikin Azama Sani ya ƙariko kana tace " Me yakawo Tsutsa wurin nan .? Saurin kallon inda take nuna masa yayi ganin wasu irin tsutsotsi masu tsawo da bai taba Ganin irin su ba . Ikon Allah Hajiya Ai Wannan Abin mamaki ne kwarai .Wallahi ban sani ba . Ok to a gyara wurin da Sauri Don Allah . An gama Ranki Yadaɗe . Juyawa tayi jikin ta na mata Nauyi don fiye da shekaru a haka take cikin ciwon jiki da na kai ,kullum a mariranci take .
**
Kallon Inna Hansai Aaryaan yayi kamin yace " Inna Don Allah ki faɗa mun Wacece A'isha Farida? Mama ce ta haife ta ko kuwa?. Girgiza Kai Inna Hansai tayi tare da cewa " Aaaryaan tun da ka matsa Zan faɗa maka Gaskiya wanda ko ita A'isha ba tasani ba...A'isha ba Lantana ce ta haife ta ba . Hasali tsintar ta tayi nan take Inna Hansai ta bashi labarin komai na Rayuwar Mama Lantana da kuma A'isha Farida har da labarin ɓoyayyen masoyi wanda ta ƙare da cewa " Ta dauki Soyayya ta daura mawa Aljani , Dalilin da yasa na faɗa maka Wannan Sirrin shine ko bayan Ranmu don Allah ka dauki A'isha Yar uwar ka ,kar ka bari wani Abu ya same ta ,ka kula da ita tamkar yanda mukayi mata a rayuwa ko ma fiye . ” Shiru yayi yana juya maganan nata kan sa na masa zafi . Inna inshallah nayi Miki alkawarin kulawa da A'isha har Ƙarshen Rayuwa ta .”

Nufar Ɗakin Mama Lantana suka yi dai dai A'isha na fitowa daga Dakin ...ke koma ki saka hijab yanzu zamu bar Gidan nan .! Wani irin kallo tayi masa cikin sauri tana kallon Mama Lantana wanda kamin tayi magana Mama Lantana tace ' Babu inda zamu je Aaryaan ,Ni da Gidan mahaifin ka har Abada . Mama ..! Ya isa ta katse shi tana daga masa hannu . Ganin haka yasa A'isha raɓa shi tana ficewa tare da ɗaukar buta tana nufar banɗaki. Tun kan ta isa banɗakin idanun ta suka fara zubda Zafafan Hawaye . Don duk Maganan da Inna Hansai suka yi da Aaryaann taji , A kunnen ta ,don a lokacin ce mawa Mama tayi zata dauki buta a waje daga Hakan ne ta ji maganganun da Inna Hansai ke fada masa . Wanda ko mafarki bata taɓa tunanin ita din tsintacciya bace ba sai a yau . Kuka take sosai tamkar ranta zai fita . Kamin ta fara magana kaman zautacciya tana cewa " ina iyaye na suke? Me nayi masu suka Wulaƙanta mun Rayuwa? Kuma suka so rabani da Rayuwar bayan Wulaƙanta Ni da suka yi har suka so kuma kashe Ni?. Ni yar zina ce ko kuma mene sanadin Faruwar haka? A iya sanina Wanda aka haife su a hanyar da bata Allah ba sune ake Wurgarwa a hanya walau su rayu ko kuma su mutu .

Kusan mintuna Goma sha biyar ta diba a hakan tana tunanin Abubuwa mabanbanta abun kaman Almara take ganin sa . Kamar kuma a mafarki . Bayan ta gama kukan ta ne ta goge Hawayen ta tana dauka ma kanta alkawarin ba zata taɓa faɗa mawa Mama Taji komai ba ko tasan gaskiyar ita ba mahaifiyar ta bace . Wanke fuskar ta tayi tana fitowa tare da Ɗaura Alwala . Bayan ta shiga Dakin ne ta tadda har a lokacin rarrashin Mama Lantana Aaaryaan keyi ,anan kuma Taji yana cewa" Mama Ba a gidan Daddy zan kai ku ba , Gida na na Asokoro ne zan kai ku . Kallon Mama Lantana A'isha Farida tayi tare da cewa " Mama Kiyi Haƙuri mu bishi Don Allah ,Kinga ya dade bai ganki a rayuwa bai ma sanki ba , Ki bashi lokacin nan a wannan karon ki taimaka masa ki zauna tare dashi , ko ba komai zaice ya zauna tare da mahaifiyar sa kaman sauran ƴaƴa .


Inna Hansai ne ta amshe da kwarai kuwa wannan Haka yake , Don Allah Lantana ki duba . Shiru Mama Lantana tayi na yan dakiku kamin daga bisani tace " A'isha Kin amince zaki zauna da Aaaryaan muje Gidan sa mu zauna?. Murmushi A'isha Farida tayi tare da cewa " Eh Mama zan So hakan Sosai . Murmushi duka suka yi kamin Inna Hansai tace " To ai sai a fara kimtsawa tun yanzu . Buɗe baki mama Lantana tayi zata yi magana karar Wayar sa ya katse ta . Daga kirar yayi yana Saurin ficewa daga Dakin Ganin sunan Daddy...don Hajiya Kaka na can Hankali a tashe ta tasa su tana kuka tare da cewa duk inda Hadiza take a nemo mata ita .
**
Ɓangaren Hajiya Kubrah kuwa Ita dai Duk idan ta zauna babu sunan da take ji ana kira mata Sai sunan Hadiza wannan yasata Ɗaga Waya tana kara kirar Ramatu don kwana uku kenan yau bata samun ta . Hamdala tayi jin Wayar nata na ringing wanda bugu biyu ta ɗauka . Ramatu ke wata irin shashasha ce? Wani irin matsala kike so ki saka Ni a ciki , yanzu haka Hadiza tana tare da Aaaryaan tsawon kwana biyu kenan a gidan dake Asokoro. Ahu'uhhhh Taji Muryar Hadiza tana faɗin haka , yayin da Hadiza ke tsalle don jin Wani irin abu na tsungulun takashin ta da Gaban ta yake yi...wanda tsawon kwana biyu ta kasa Ko da Wanka bare ta duba jikin ta . Sai mintsini kawai take ji ta ko ina . Sakin Wayar tayi ƙasa jin Wani irin mintsinan ta da ake yi ta ko ina . Wannan yasa ta Saurin Ƙasa da Zanin Jikin ta. Wani irin uban ihu ta kwarma Ganin tsutsotsi daddabe suna bin Zanin da cinyoyin ta . Tsalle ta hau tana ihu tare da fitowa daga Bedroom ɗin nata tana nufo falon ta cikin ficewar Hayyaci ta nufi Farfajiyar gidan a Tsirara sai tsutsotsi da suka yi mata rumfa suka zama mata zani .
Tirƙashi Allah yasa muyi karshe me kyau....!

#MAMANTEDDY
*🕊️FƳAƊE ....!🕊️*
#Romantic
#Erotic
#Symphatetic
#Story.

WRITTEN BY: MAMANTEDDY

*Littafin fƴaɗe na kuɗi ne Regular group ₦500... Vip group ₦1000 SPC ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*
23
*Vip& Special night update*

**

Innalillahi wainna ilaihir raji'un Kalmar da Sauran ma'aikatan suka hau faɗi kenan ." Hankulan su a tashe wasu na yin baya suna darewa Ganin Yanda Wannan halittu suke yayyame a jikin Hajiya Ramatu . Mata biyu ne masu dauriyar Hali suka nufi inda Rahmatu take cikin Sauri suna fadin Hajiya Lafiya.? Daya daga cikin su kuwa cikin sauri ta fice Kallabin ta tana Ɗaurawa a Ƙugu zuwa cinyoyin Hajiya Ramatu wanda ko karamin yaro ya ganta yasan mahaukaciya ce tuburan . Hayaniya ne yasa Hansa'u lekowa ta windown t tana fadin Lafiya meke Faruwa ne?. Hajiya don Allah ki fito babu lafiya .

Cewan Wata daga Ma'aikatan ganin yanda Hajiya Rahmatu ke zabura tana faɗin Gidan Hajiya Kubrah zan tafi , zan Faɗa mata yanda mukayi da bokan ne don iyayen ku ku sake Ni , rirrike suka ƙara yi suna cewa " Hajiya Don Allah ki fito babu lafiya . Suna tsaka da Faɗin haka ne Hansa'u ta fito cikin sauri dan Ƙwali a hannu . Hajiya lafiya ? . Wani irin muguwar kallo Ramatu tayi mata tana mai cewa " Ke kuma a wane zaki tare Ni kina tambaya ta lafiya? .ko zaman ki nake yi da sai na faɗa Miki inda zan tafi? To ko shi mijin nawa bai ishe Ni ba a tafin hannu na yake bare ke da kike karkashin sa ...' duka maganan tana yin shi irin na mahaukata sababbin Kamu daga Ni kasan ƙwaƙwalwa babu lafiya . Kasa magana Hansa'u tayi sai tsayawa da tayi tana kallon ma'aikatan tare da goge Hawayen dake kwaranya mata .

Suna tsaka da Hakan ne moton Alh. Samad ya shigo cikin gidan wurin ne yayi tajun² ganin Isowar mai gidan , Wanda Ganin Haka yasa Alh Samad saurin fitowa daga moton yana Nufo inda suke a tsaitsaye . Lafiya meke Faruwa ne anan Wurin?. Yayi maganan cike da murya irin tasu na manya , da kuma iya taku irin na police . Don shi Babban Ɗan Sanda ne ,Kuma shanyayye ,don Hajiya Ramatu ta shanye tasss da sihiri baƙaramin Wahalar ta Hansa'u tasha ba . Kamin kowa ya basa Amsa ne Muryar Ramatu ya katse shi tana sheƙewa da Dariyar irin na mahaukata, To ke Hansa'u Ga Sa'a na Nan bake ba...ei..ei ta ƙare maganan tana Kame kame wanda da gani kasan babu lafiya .

Cigaba tayi da cewa " Kin gani ko? Har sakin ki ya taɓa yi kuma nice na san sirrin , kina so ki sani? Wurin boka na kai sunan ku wani irin tsalle tayi tana kokarin sauke dankwalin jikin ta da Suka rufa mata jikin ,wanda Ganin haka yasa Hansa'u fashewa da kuka tana rike Hajiya Ramatu tare da riƙe ta tana faɗin Allah ya isa tsakanin mu da Wanda ya zalunce ki Hajiya Rahmatu . Ya isa...! Cika ta Hansa'u..! Alh Samad yayi maganan tare da Dakatar da ita . Allah ya isa dai tsakani na da ita, kin cuce Ni Rahmatu kuma kije Ni na sauwake Miki na sake ki ki koma Wurin bokan da kuke tare .


Wani irin Dariya Ramatu ta sheƙe dashi kana tace " Ai kwana uku da shi nayi a jeji muna tare..... Innalillahi wainna ilaihir raji'un Alh Samad yayi maganan yana cire hular kan sa . Kallon Hajiya Rahmatu yayi tare da Cewa " Muje ki kaini wurin Bokan. Yayi maganan yana daga Wayar tare da daga Wayar sa yana kirar Jami'ai don a yau ya lashi takobin kama bokon ko da kuwa shaiɗan ne sai yayi masa lalas sai ya ga bayan sa , zai nuna nasa a duniya ya zama izina ga masu biye mawa Bokaye ,zai nuna masu bokan ba kowa bane Fache makaryata masu fakewa suna zina da mata ....!


GN
Mmmnteddy
*🕊️FƳAƊE ....!🕊️*
#Romantic
#Erotic
#Symphatetic
#Story.

WRITTEN BY: MAMANTEDDY
*#MRS UTHM*
*Littafin fƴaɗe na kuɗi ne Regular group ₦500... Vip group ₦1000 SPC ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*
25
**
“Yanda yaga Ya fasa Ihun yasa shi dakatawa daga Tunkarar nata da yake yi , Jah yayi ya tsaya yana kallon ta ƙasa-ƙasa kana daga bisani ya sakin mata Wani irin murmushi wanda yafi kama mata dana mugun ta . Juyawa yayi kan sa tsaye yana nufar Dressing mirror tare da fara kimtsa kansa wannan yasa A'isha Farida saurin juyawa tana kallon Ƙofar fita tare da juya masa Baya . Bata ko son Ido biyu da shi Don tsoro ne ya kamata , A zuciyar ta tana tambayar kanta mene ya kawo ta anan Ɗin ? Sai ku wani zuciyar ya bata amsa da : Koma Meye ai maganin ki , ke kika kawo kanki , maganin ki kenan ... A hankali ne ta furta " Wayyo Mama na kizo ki taimake Ni .! Dariya ce ta kusa Ƙwace masa Amma kuma sai ya danne yana mai cigaba da kimtsa kan sa . Har ya kammala bata sani ba ,ita dai Taji hannun sa ne yana juyo da ita tare da Fuskar ta shi . Kallo Ɗaya tayi masa tayi ƙasa da kanta tana shaƙar Daddadan Turaren sa , Sanye yake cikin shigar da bata taɓa Ganin sa dashi ba, Wanda yayi mata masifar kyau , Shiga ce jikin sa irin na cikakken Ɗan Hausa Fulani. Wata irin bowel yard ce ya sanya mai launin Milk da Hula ƙube a kan sa , Idanun ta a ƙasa suke amma babu abun da take Hangowa Fache Ƙyawun sa da take Gani . A zuciyar ta ne ta furta " Ƙyaun Ɗan maciji mugu .' Muryar sa Taji yana cewa " Oya fice mun Daga Bedroom , ko bana nan kika kara kuskuren shigowa ko Hummm yayi mata kwafa tare da cewa ' Ba sai na bata lokaci na Wurin faɗa Miki mai zai biyo baya ba . Ke Nasan kin sani ai .

Saurin nufar Hanyar ficewa tayi wanda a wannan lokacin tana nufar ƙofar taga ya bude da kanshi ,cikin sauri ta fice tana ganin ta fita ne ta Jah ta tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login