Showing 75001 words to 78000 words out of 110620 words

Chapter 26 - FYADE COMPLT COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Sep 2024

8159

, So maganan Aure a rayuwa ta indai bake ba , babu wannan . Shi mijin ki da dare Ni kuma da rana . Kin zaɓa Wannan Eaashhan Mama .? Ya kare maganan cikin Wani irin Salo na babu yanda zata yi dashi . Hannun ta tasa tana share Hawayen fuskar ta kana tace " Zamu saka Mama da kowa Naawaaz , Aslaam in tension . Wannan Su ya shafa , Rayuwa ta kece .! Yayi maganan tare da yi ma moton sa key yana hayewa saman ƙwalta . Wani irin ɓacin Rai kawai Taji ya taho mata dangane da shi . Cikin tsayayyar murya ta furta " Ni kuma ba kai ne Rayuwa ta ba , Na tsane ka tun daga lokacin daka ci mun mutunci Yah Aaaryaan baka SO na .! Kuma a yanzu ma na Fahimci inda zancen naka ya nufa , Wato Jiki na kake So kuma kake bi , Idan da babu da ba zaka Kauna ce Ni ba .
Kallon ta yayi amaimakon taga Wani sauyi daga Garesa sai Gani tayi ya sakar mata Wani ƙayataccen murmushi yana daga mata Gira irin na tacewa wato maganan ta banza ,abun da ya tsara babu mai Hanasa .

Dafe kan ta tayi tana buɗe baki tare da Kwarma masa ihu ko a tunanin ta Zai tsaya ,amma sai Gani tayi ya kunna Ac mai dadi da sanyi yana Ratsa Bargo tare da kunna Sanyayyar music na Johnny drill . Mai taken Wait for me ." Haushi ne ya gama cika ta , Cikin Muryar kuka take Fadin na cuci kai na dana kuma Amincewa da kai a karo na biyu Aaryaan. Wai Anya ma kai ne ɓoyayyen masoyi na kuwa?. Ka saka Ni na bar wanda suka shirya rayuwa dani tsaka Ni ga Allah. Bana son ka ..! Juyowa yayi yana mata Wani irin kallo ,wanda yasa ta kame bakin tana cigaba da Matsar ƙwallah . Bana Son Hayaniya kin sa hakan ?. Shiru tayi masa tana cigaba da Sharce Hawayen fuskar ta , tun tana saka Ran ya koma da ita yanzu har ta ga sun fara nisa . Sanyin Ac din moton mai kama dana Snow mai dadi yasa ta fara Lumshe ido a haka bata san lokacin da barci yayi Awon Gaba da ita ba . Kallon ta yayi a haka karfe 12:pm moton shi na shiga Airport din Garin Abuja .

Da ganin sa sun san lambar moton sa don haka cikin Sauri masu tukin jirgin suka nufo inda moton shi yake. A hankali ya zuge window Glass din shi yana kallon su tare da amsa gaisuwar su . Motsa bakin sa yayi cikin rashin Son magana da Miskilanci yace " Private Jet nake buƙata . Ok sir . Abun da suka ce kenan , kamin kaman mintuna Goma sai gasu sun dawo . Komai ya kammala Yallaɓai wata Mace daga cikin su tayi maganan . Fitowa yayi yana ɗaukar brief case din shi , Yana rufe moton ne Ma'aikaciyar Airport din tasa Hannu tana Amsan brief case nasa , yayin da shi kuma ya zagaya maxaunin A'isha dake shan barcin ta sam bata san da Sun iso Airport ba . Fuskar ta ya tsaya yana kallo Ganin Yanda duk suka kumbura Kuncin ta da idanun ta . Hannun sa yasa yana Ɗaukar ta cak tare da Sumbatar Saman Goshin ta kaman ya dauki Teddy yaji wannan yasa shi nufar Step din Jirgin suna shiga . A hankali yake bin fuskar ta da kallo tare da jin zazzafan Kaunar ta da kuma tausayin ta a zuciyar sa . Ina Son ki A'isha ta ..! Ya furta maganan tare da gyara mata belt ɗin ta wanda har a lokacin bata San ma yanayi ba . Kaman Wanda akayi mata Allurar barci . A hankali jirgin nasu ya fara ɗagawa zuwa Ƙasar America hankalin shi kwance zuciyar sa na masa Wani irin sanyi da Dadi . A yanzu sai naga Wa kuma Za'a daura mata ." Ƙurrr yake bin ta da Wani irin kallo mai tattare da dabaibayin sihirtacciyar Ƙauna. Rungume ta yayi da Jikin sa yana Lumshe idanun sa tare da Tunanin ɗazu da yazo Tafiya da ita , Tabbas ya dawo ya tadda ta tana Rubuta a wani takarda wanda tana Ganin sa tayi saurin Ajewa a saman Bed ɗin ta . Murmushi yayi yana shafa Gyefen Kuncin ta tare da cewa " Zamu dawo Wata rana ,zaku ma kiga Mama ba zan Raba ku ba , Amma sai na tabbatar dana Aure ki kamin na yarda mu dawo Nigeria .
**
11:30 na Safiyar Juma'a ne Mama ta shigo Bedroom din A'isha Farida don a tunanin ta barci take yi har iya Wannan Dogon lokacin Bata fito ba. Don haka ta shigo don ta tashe ta daga barcin don Ango da Abokan su su uku suna Falo suna jirar fitowar ta , Sadeeq ne sai Abokanan sa Nawaaz su biyu , da suka kosa suga Amaryar da yake ta yarawa yana faɗin kyawunta . Aslaam kuwa Zazzaɓi ne ya rufe sa matsananci jin da yayi za'a yi ma A'isha Farida aure da Nawaaz . Sosai a daren jiya ya shiga tashin hankali , Wanda tun a daren shima ya yanke shawarar barin Nigeria ko zai samu salama a zuciyar sa . Jirgin karfe 8:am yabi zuwa Kasar Lebanon Don a can yayar Mahaifiyar sa ke Aure ." Wannan yasa a wannan tafiyar sam babu shi a abokan Ango .

A'isha..." Mama ta fara kirar sunan ta a Hankali tana nufar Privacyn ta amma nan taga Wayam Babu ita . Ƙirjin ta ne ya buga da Karfi ,kawai sai taji jikin ta bai bata ba .

Dawowa tayi tana shirin fitowa ne suka yi kiciɓuss da Nawaaz wanda jin shirin Mama ya biyo bayan ta . Nawaaz Ta kira sunan shi ganin sa tsaye da Takarda a gyefen Gadon A'isha . Cikin Wani irin yanayi ya kalli Mama kamin tace ' Ban ga A'isha ba ko tana can sashen Hajiya ne .?


Girgiza ma mama kai yayi tare da Cewa " Mama A'isha ta tafi , Tabi Aaaryaan sun bar kasar nan . Innalillahi wainna ilaihir raji'un Mama tace cikin sauri da Girgiza, Saurin nufar sa tayi tana amshe takardar da ta Gani a hannun sa . A hankali ta fara Karanta maganan A'isha Farida kaman haka " Mama ina Son ki Sosai , Ban SO na tafi na barki ba , Amma sai dai kun kasa fahimtar Soyayyata da Ɓoyayyen masoyi na , Kiyi Haƙuri mama , Ki ba Nawaaz Haƙuri ya Aslaam , Daddy da Hajiya kaka , kunyi mun halarci da bai dace nayi maku hakan ba . Amma kuma ina Son Ɓoyayyen masoyi dole yasa zan bishi . Lahaulaaa walaaaa kuwata Illah billah . Furuncin da Mama tayi kenan tana kallon Nawaaz wanda Jiri ke ɗibar sa , juyawa yayi yana fitowa zuwa Falon da Su Sadeeq suke . Saurin Miƙewa Sadeeq yayi tare da kallon Nawaaz yana cewa " Lafiya ? . Mama ne dake baya ta bashi Amsa da " Aaryaann ya gudu da A'isha....! Maganan Mama ne ya bugi Zuciyar Nawaaz a karo na biyu , Jiri ne ya dibe sa yana yin baya tare da ganin duhuwa Numfashin Sa na Ɗaukewa nan take ......!



#Mamanteddy
Bana jin Dadi ne yau duka na shiyasa kuka jini shiru bana online , Amma ga wannan nan ....'
Mu tare a Night update inshallah

*Littafin Fƴaɗe na kuɗi ne... Regular group ₦500... VIP group ₦1000... special ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932...Don Girman Allah idan baki biyani ba kar ki karanta mun wannan littafi .*

```FƳAAƊE.!```
*(Erotic and Sympathetic Story)*

Ayshatou Mamanteddy

***39-40***
*SUFY'S PRINT GRAPHICS DESIGN*

🏷️ PROVIDING A RANGE OF CONTEMPORARY AND TOP NOTCH CREATIVE DESIGN.....

*📍 OUR SERVICES*
✒️LOGO DESIGN
✒️LOGO PACKAGE
✒️ FLYER DESIGN
✒️ BIRTHDAY FLYER
✒️ INVITATION CARD
✒️ADVERT VEDIO
✒️ DIGITAL INVITATION
✒️ STICKERS DESIGN
✒️AND LOTS OF
📝DM NOW....TO GET A TOP NOTCH ATTRACTIVE AND PROFESSIONAL DESIGN
Whatsapp:07045125150
Thanks you for choosing us nd we appreciate refferals 🥰🤗.
**
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Kalmar da Mama ta furta kenan cike da Tashin Hankali yayin da Sadeeq da Sauran Abokanan sa suka yi saurin taro Nawaaz . Hankali a matuƙar tashe suka tattaye shi Tare da nufar Farfajiyar gidan , Moton Su suka shiga dashi , yayin da Mom Kubrah ke daga Saman benen ta tana Hango Abun dake Faruwa a ƙasa . Cikin Sauri ta juyo cike da zaƙuwa da kuma San Sanin meke Faruwa da Angon da A yau za'a Daura masa Aure da Yar Aikin ta wacce tafi tsana a duk ma'aikatan ta , a yau gashi ta zama yar gida tana neman Aure yaron Gida , a cewan ta kenan , don Wannan Aure na Nawaaz da A'isha yayi bala'in ɓata mata Rai , Amma abun ka ga tana neman Gindin zama a cikin Gidan wannan yasa ta kwantar da kai don tasan a dosane take bata son Abin da zai ballo mata duk Wani Rikici, Sai dai Har a yau akwai yan kunya tsakanin ta da Aaaryaan sam bata iya haɗa ido dashi ,ko da kuwa Gaisuwa ce sai dai ta yi kasa da kan ta. Haka nan shi kuma ya dauke kafar sa a bangaren ta , Don kwana biyu kenan Hajiya kaka ta kira shi tana masa Faɗa akan mene yasa Baya shiga Part ɗin Hajiya Kubrah? . Amma kuma jin hakan sai Hajiya Kubrah tayi saurin katse Hajiya kaka tana cewa " A'a Hajiya yana fa Shigowa , Kin san Kwana biyu baya cika zama bane ba. Jin Wannan zancen na Hajiya Kubrah ya kashe bakin Hajiya Kaka .


Fiddo da idanu Hajiya Kubrah tayi tare da saurin bin Stairs tana sauka . Mama ne dake gyara mayafi tana shirin shiga Mota Taji Hajiya Kubrah na cewa" Hadiza Lafiya kuwa ?. Cike da damuwa da tsananin tashin hankali Mama ta kalle ta tana cewa " Aaryaan ya Gudu da A'isha Farida, Wannan Wani irin Yaro ne a yau da za'a Daura mata Aure da Naawaaz ne zai mana Haka ?.

Kama Kai Hajiya Kubrah tayi cike da makirci irin nata tafara matso Hawaye tare da fadin" Mun shiga uku , Innalillahi wainna...kasa ƙarikawa tayi tana Wani jan Ajiyar zuciya har tana tangadi tare da yin baya Wai a Dole irin ta Girgizan nan sosai . Juyawa tayi tana Saurin bude moton da suka kwantar da Nawaaz Girgiza Nawaaz Take yi tana kuka na makirci da son Kage . Ɗaga wayar ta tayi tana Saurin latsa nombobin Daddy marshal Abdu Kareem , Wanda bugu Biyu yana tare da manyan mutanen sa da jama'ar sa , Ga wasu irin sojoji da suka cika Tun daga Farkon layin har ƙarshen sa . Tana jin ya ɗaga Bata tsaya jin me zai ce ba , Tace " Daddyn Aaryaan a dakata da Daurin Auren nan . Aaaryaan ya Gudu shi da A'isha , bamu san inda suka nufa Ba . Salallami Daddy ya hauyi tare da Sauke Hular kan sa ba tare da ya shirya ba . Nan take gumi ya hau Karyo masa . Shi Nawaaz yana Wani Hali a yanzu ?.

Cike da nuna damuwa Hajiya Kubrah tace " Yana Kwance rai ga Hannun Allah,amma yanzu muna shirin wucewa dashi Asibiti ne .

Hayaniyar Gidan yanda Motoci ke fita da wani irin mahaukacin Gudu Yasa Hajiya kaka da bin son kwakkwafi ta fito tana dan kasa da idanun ta ,wanda Rana yayi mata Yawa . Ganin kuwa Hajiya kaka yasa Cike da kissa Hajiya Kubrah ta nufe ta tana fashewa da kuka tare da Fadin " Hajiya Ta gudu dashi . Saurin Kallon Hajiya Kubrah Mama tayi kamin tayi magana ne Hajiya Kaka ta furta " Wake nan ? Ban gane me kike nufi ? . A'isha da Aaryaan sun Gudu.

Cikin wani irin yanayi irin nasu na tashin hankali na tsufa ta furta "
Ya Ilahi Allah ,garin yaya haka ? Ban gane ba , Tayaya Aisha.... Kwatse Maganan Mama Tayi tana cewa " A'a Bafa A'isha ne ta gudu da Aaaryan ba , Shi Aaryaan shi ya gudu mun da Ƴa ,kuma Wallahi rai sai ya ɓaci .

Kallon Su duka Hajiya Kaka tayi kamin tace " Ƙarfi yasa mata ko kuwa da Kan ta ta Bisa? Suna da Wani alaka ne . Kamin wani ya bata amsa ne ta furta " Akwai babban matsala , Ayi maza a Dakatar da Auren nan , Domun kuwa komai ka iya Faruwa tsakanin Aaaryaaan da A'isha .

Cikin Rashin Fahimta mama tace me kike nufi Hajiya?. A kira mun Alh Abdu Kareem yanzu a Waya ina so nayi magana da shi dole a dakatar da Wannan Auren .

Jin Wannan zancen yasa Hajiya Kubrah sakin Wani irin murmushi a sace ba tare da kowa ya Gani ba kana tayi saurin fara kirar Wayar Daddy , a tunanin ta Auren ne duka za'a fasa . Bugu ɗaya biyu Daddy ya daga Kirar dai dai Hajiya kaka na cewa " Abdul Kareem ina so a yanzu a dakata da Daurin Auren A'isha da Nawaaz , A daura Auren Aaaryan da A'isha Yanzu .!

Dam³ Ƙirjin Mama dana Mom Kubrah ya amsa a lokaci guda . Miƙa masa Wayan tayi tana juyawa tare da jin nadaman maganin data ba Aaaryaaan , Tabbas tasan a yau Allah ne zai ƙwaci A'isha Farida a hannun sa . Allah kuma yasa kada Shaiɗan ya shiga tsakani ,wannan dalilin yasa ta dakatar da Auren Nawaaz da A'isha tasa........!


Mmnteddy

.```FƳAAƊE.!```
*(Erotic and Sympathetic Story)*

Ayshatou Mamanteddy

***41-42***
*SUFY'S PRINT GRAPHICS DESIGN*

🏷️ PROVIDING A RANGE OF CONTEMPORARY AND TOP NOTCH CREATIVE DESIGN.....

*📍 OUR SERVICES*
✒️LOGO DESIGN
✒️LOGO PACKAGE
✒️ FLYER DESIGN
✒️ BIRTHDAY FLYER
✒️ INVITATION CARD
✒️ADVERT VEDIO
✒️ DIGITAL INVITATION
✒️ STICKERS DESIGN
✒️AND LOTS OF
📝DM NOW....TO GET A TOP NOTCH ATTRACTIVE AND PROFESSIONAL DESIGN
Whatsapp:07045125150
Thanks you for choosing us nd we appreciate refferals 🥰🤗.
**

*Littafin Fƴaɗe na kuɗi ne Don Allah Idan baki biya Ni ba kar ki karanta mun ... Regular payment ₦500... VIP group ₦1000... Special ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*

Cikin Wani irin Hasala na ba yanda Rai yaso Ba Hajiya Kubrah ke fadin " Anya Hajiya Wannan maganan taki yayi dai dai Kuwa? . Gaskiya a ƙara Dubawa wannan Al'amari bai yi ba sam , Aaaryan da Nawaaz yan Uwa ne na jini , Yau ne Ranan da Za'a Daura ma Naaawaaz Aure da matar sa , Sai don Kawai Aaaryaan ya Gudu da ita sai ace da Aaaryaan za'a Ɗaura ba dashi ba . A duba Fa Halin da A yanzu Nawaaz ke ciki baya sanin kowa a kansa. To ina ga Kuma ya farfaɗo ya sami wannan mummunan Labari ya kuma ... A'a Hajiya Kubrah Maganan nan taki itama bata Dace ba Gaskiya, Mummunan Labari kaman ya kenan ? Mama Lantana ta katse Hajiya Kubrah tana bin ta da Wani irin kallo na nasan ki kema kin sanni ,babu Wani Alaye da zata nuna mata . Cigaba da cewa Mama tayi " Auren A'isha ba zai taba zama mummunar Labari ba , kuma indai nice mahaifiyar A'isha cikin su babu Wanda zata Aura an fasa Auren duka . Mama ta ƙare maganan cike da Huci don zuciyar ta tafasa yake , Ji take ina ma tana Gaban Aaaryan a yanzu tabbas da Abun da zata yi masa Yawa ne dashi . Jin Maganan Mama Lantana dana Hajiya Kaka yasa Ta masu kallon duka baku isa ba . Bana da lokacin magana daku a matsayin ku na yayan ciki na ,kuma surukai na , na Zartar da Hukunci kuma Dole a dauka . Tana Gama faɗin Haka ta juya tana dan dingisa ƙafarta da yayi mata tsami , kunsan tsufa , Zufa na Karyo mata . Wannan wani irin Shakiyin Yaro ne , Wato dama yana Son Yarinyar nan shine yaki magana ya bar mu ,mu gama zartar da komai sai ya tanfatsa mana babban Aiki . Saurin Ɗaga Ƙafa tayi tana nufar Sashen ta tare da kallon Zabiba Mai kula da Hajiyar .

Zabiba maza Ɗauki waya ki kirawo mun Numbern Alh Abdu Kareemu yanzu . To Hajiya , Zabi tayi maganan tana Nufar Saman Sallayar Hajiya mai kaman Carpet tana ɗaukar yar Wayar Hajiya Wanda bata iya amfani da ita ba ,sai dai ta ba yan Aikin nata suyi mata komai take buƙata . Hajiya Gashi ." Saurin amsan Wayata tayi tare da Karawa a kunnen ta tana cewa " Abdul kareemu kana Saurara na kuwa . Ƙwarai Hajiya ina jin ki ,yayi maganan cike da ladabi kansa a ƙasa tamkar Wanda yake a gaban ta . Hayaniyar Mutane Take ji , wanda a yanzu maganan Guduwa da Aaaryan yayi da Amarya ya fara Wade Wurin don haka har An fara Tsegumi da surutai wanda Dole ayi .

Abdu Ni na haife ku , na haife ka ,na kuma haifar Mahaifiyar Nawaaz , don haka nike kara kirar ka tare da cewa " Ayi maza a daura Auren Aaaryan da A'isha Farida kar a tafka babban Kuskure , kar shaidan ya shiga tsakanin su , kunyar tafi wannan . Hajiya Ki sani mu a kullum bamu da Jah da maganan ki ba sai kin faɗa mana dalili ba. Abun Da yasa kika ji Ban ma kira ki na shaida Miki daurin Auren ba , Saboda yanzu na gama magana da Momyn Nawaaz ,kuma Tayi na'am itama da maganan na Auren A'isha da Aaaryan . Sauke Ajiyar zuciya Hajiya Kaka tayi tana furta Alhamdulillah .

**

Shiru Mommy tayi tana tsayawa a gaban Windown falon ta tare da bin dan Gyefen Harabar Gidan nata da Kallo . Su Hajiya Madina ne ce da Arch. Nasiba da suke aminan Hajiya tun safe suke gidan don dan shirya liyafar su da suka yi niyya , Duk Abin da Ake yi basu sani ba , harkar gaban su suke yi , a dole suga Manyan mata ana farin ciki zasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login