Showing 69001 words to 72000 words out of 110620 words
gimtse fuska . A zuciyar shi yana cewa " Duka shine ya jawo wannan husumar , da wannan matsalar . Hannu malamin yake bashi amma kallon sa baiyi ba sai ce masa da yayi " A'isha bata da lafiya yanzu haka . Don haka kaje kar ka dawo sai na neme ka ." Jikin malam a sanyaye ya ce " To kamin Aaaryaan ya juya bai bukatar jin ma na bakin shi.
**
Bayan ya dawo Gidan ne Hajiya Kubrah ta aiko masa da Basket na Abinci na ma jinyata tare da sanar masa ayi ma A'isha ya jiki . Sosai yaji dadin hakan , don duk mai Son A'isha son sa yake yi. Wannan yasa shi nufar moton sa daga shi sai jallabiya ya nufo Asibitin hankalin sa kwance don shi yasan A'isha tana lafiya likita ya tabbatar masa da hakan . A reception ya tadda mama tana kallon sa tare da cewa " Aaryaan Yauwa kaga gwamma da kazo ,ina so zanje nayi Alwala na yi sallah ne .ka tsaya akan A'isha , Doctor Yace kar Wanda ya shiga Dakin ta samu barci . Murmushi yayi tare da cewa " To Mama ga Abinci ma Momy tace a kawo maku .
Kallon sa Mama Lantana tayi cike da rashin Fahimtar wacce Mommy kana tace " Wace kenan ciki ?. Momy na mana .! Ƙirjin Mama ne ya buga amma sai ta dake tare da cewa " Ta dawo kenan . Eh mama . Okay sannun ta da dawowa ai kila zuwa gobe ma mun koma kaga sai itama na Gaishe ta da jiki . Kallon Mama yayi irin na okay kamin ya juya yana nufar hawa na uku inda A'isha Farida ke kwance a private room ɗin ta ita kadai .
**
Da gudu Yusra ta sauko daga benen tana kwala kirar Momy Lubnah tare da fadin " Mommy...! Cikin sauri Mom Lubnah ta furta " Yusrah wannan kirar kuma fa meke faruwa ne? . Mommy kiyi farin ciki , Mom Kubrah ta dawo yanzu haka Gidan Daddy zan tafi .
Kallon sama da ƙasa Mom Lubnah tayi mata kana tace " A'a Ba zaki tafi ba a yanzu . Sai dai zuwa Gobe , Ɗazu fa naji kince kuna da test da misalin 5pm yanzu kuma ai lokacin yayi . Mom ai ko a can Gidan ta zan iya yi . Ban san Wannan ba . Mommy tayi maganan tare da haɗe fuska ,ganin Hakan yasa Yusra juyawa a hankali tana wucewa duk da ranta bai so hakan ba .
**
Shigar Aaaryaan Dakin da Take Kwance yasa shi tsayawa yana manna bayan sa da kofar da ya rufe . Ajiyar zuciya ya sauke yana bin gadon da take kwance da kallo zuwa kyakkyawar fuskar ta wanda sunan tana barci ne amma Kuma ka ɗauka murmushi take saboda smiling face din nan nata . Murmushi yayi yana takawa tare da ake Basket din yana sunkuyawa Gwiwowin sa kasa . Hannun sa yakai yana shafa fuskar ta zuwa zagayayyen dan mitsulin bakin ta , Kiyi Haƙuri A'isha , Ni ne na janyo duka Wannan , But I'm so sorry . Hummm Iska ya furzar tare da cigaba da zagaye bakin ta da dan Yatsar sa . Wanda sam bai san lokacin da ya sunkuya yana kissing din laɓɓan nata masu sheƙi ba . Kusan mintuna Uku Ya ɗauka a haka kamin A hankali ta fara buɗe idanun ta tana sauke su a saman Sumar kan sa . Buɗe baki tayi da Sauri tana shirin saka masa ihu duk da babu kwari a tare da ita nan taji ya Zura Harshen sa . Yana ɗago da Lulun idanun sa , Tare da mata kallon kukan zaki yi?. Gumm tayi tana kallon sa hawaye na fara saukowa daga Ƙwarmin idanun ta . Jah baya yayi tare da zare bakin sa daga nata , dai dai mama Lantana na murdo Handle Door ɗin tana shigowa . ALLAH Alhmdlh . Sannu A'isha na kin tashi . Kallon Mama Lantana A'isha Farida tayi wacce take tahowa zuwa inda Gadon nata take . Kuka ta fashe ma mama Lantana dashi tana faɗin " Mama...! Saurin zama mama Lantana tayi a gyefen ta tare da kamota tana Rungume ta , Hannun ta tasa tana shafa bayan ta alamun Rarrashi . A'isha bani da abun faɗa Miki a yanzu ,kin san komai sai dai nace mu Rungumi ƙaddara . Ni har abada mama ce a wurin ki ,kece kaɗai ɗiyata . Domin kuwa wannan Na dade da barin ma Momy Kubrah . Mama ta ƙare maganan tana nuna Aaaryaan da Hannu .
Kallon sa A'isha tayi kamin tace " Mama Amma ai ba zaki daina So na ba ko?. Kuma ma ina Iyayena suke ,me nayi masu suka.....ya isa , Mama Lantana tayi maganan tare da rufe bakin A'isha da Hannun ta . kar ki ƙara faɗin Haƙa A'isha , kuma ina so ki manta da komai ko na sanin ke din Wacece ? Nice dai Mahaifiyar ki kuma ba zan chanja ba .
Mama Kina da labarin Auren A'isha kuwa nan da Wata guda ? Ina jifa Hajiya kaka ? Shin baki faɗa mata abun da na faɗa Miki ba Mama ? . Bazan ... Aaryaan ka manta da cewa " Akwai Aure tsakanin ka da A'isha , Dauke ta tamkar kanwa ta jini . Naawaaz shine zai Auri A'isha inshallah , Aslam kuwa dan uwan kunne amini , zai fahimci komai Ni da kai na zan masa magana kuma na basa Haƙuri . Yanda bugun Zuciyar A'isha ke har bawa da sauri ² ta dauka ranta ne zai bar gangar jikin ta . Cikin sauri ba tare da sani ba ta furta " Mama Ɓoyayyen masoyi na fa ? Ni shi nake so ... Lumshe ido Mama Lantana tayi tana budewa tare da furta " Ki manta dashi A'isha ,na dade ina faɗa Miki ba mutum bane Aljani ne , idan ba haka ba , ya akayi bakya ganin sa sai cikin dare . Kiyi Haƙuri ki manta da Ɓoyayyen masoyi ,kisa Naawaaz a zuciyar ki . Kallon Aaaryaan tayi suna haɗa ido ,kawai sai ta fashe da kuka . Tana furta " Tom mama na amince . Shiru Mama tayi tana dafa ta kana tace " Naawaaz miji ne kuma Nasan zai kula dake sosai fiye da kowa . Mikewa Aaaryaan yayi yayin da A'isha Farida tabi bayan sa da kallo , Hawayen idanun ta na Dada tsananta , ina Ruwar mu ta baya zata dawo a yanzu , maganan take a zuciyar ta ,kamin tace " Shi ne yace yayi mun Alƙawari ba zai barni ba har Abada , Amma kuma a yanzu mama ya sadaukar kenan? Mama dai bata fahimci zancen nata ba ,don wannan iya shi da ita ne zasu gane me suke fadi , hannun sa yasa yana murɗa Handle Door tare da barin Dakin Zuciyar sa tamkar..........
Tom pah yau ake yin ta , Shin Auren zai faru nan da Wata guda kenan ko kuwa dai mu cigaba da cewa " Allah yaba mai rabo Sa'a . Team Nawaaz Wannan page naku ne💃🏻😄
Sai mun hadu a Night update .
Wannan pagen bonus ne ,zaku iya yawata dashi duk inda kuka so.💃🏻
*Littafin Fƴaɗe na kuɗi ne ga masu buƙatar biyan tasu ga tsarin yanda yake... Regular group₦500 vip group₦1000... SPC₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 ,idan VTU transfer ne zaki tura ta Wannan number 09061466409 .*
Taku ce 💯📚 MAMANTEDDY
```FƳAAƊE.!```
*(Erotic and Sympathetic Story)*
Ayshatou Mamanteddy
***33/34***
*SUFY'S PRINT GRAPHICS DESIGN*
🏷️ PROVIDING A RANGE OF CONTEMPORARY AND TOP NOTCH CREATIVE DESIGN.....
*📍 OUR SERVICES*
✒️LOGO DESIGN
✒️LOGO PACKAGE
✒️ FLYER DESIGN
✒️ BIRTHDAY FLYER
✒️ INVITATION CARD
✒️ADVERT VEDIO
✒️ DIGITAL INVITATION
✒️ STICKERS DESIGN
✒️AND LOTS OF
📝DM NOW....TO GET A TOP NOTCH ATTRACTIVE AND PROFESSIONAL DESIGN
Whatsapp:07045125150
Thanks you for choosing us nd we appreciate refferals 🥰🤗.
**
Tamkar zata tsarwatse ya fito sarari saboda tsaban Tashin hankali , Mama ta amince kenan da Auren A'isha da Nawaaz,amma me yasa tayi hakan?Ba su duba bane , A'isha Dana kadai ta dace , zan kula da ita fiye da Naawaaz . Duka maganan Zuci yake yi kamin zuciyar sa ta cigaba da cewa " Baka nuna kana Son ta bane , Miskilancin ka shike kokarin raba ka da Farin cikin ka na Har Abada . Asibitin baki Daya ya bari don kuwa a wannan Rana yaji sam baya buƙatar Tafiya Gida , don ko zama yayi to tunanin ta Zai rinka yi . Lumshe Lulun idanun sa yayi kamin ya buɗe su yana hade Girar sama da ƙasa , tamkar Wanda zai ba wani Umar Ni . Wrist watch din hannun sa ya kalle yana Ganin Ƙarfe biyar da Mintoci . 6:pm ma'aikatan sa suke barin Aiki . Wannan yasa shi ɗaga Wayar sa yana latsa nombobin Sectary ɗin shi Miss liliey .
Zaune take tana taɓe taɓe a computern dake saman table din ta , Fuskar ta cikin Shadow Space mai launin transferent irin Jah amma ba mai Turi ba . Jikin ta cikin English wears ne Mai kyau kaman jikin kura , yarfi yarfi sai light make up dake fuskar ta . Kallon wata karamar Ma'aikaciya tayi tana ya tsina baki tare da kallon takardun gaban ta da ta kawo mata tana cewa " Wannan duka shine today's Profit? . Yes ma'am . Okay Jeki zan kira ki idan da wani Abu . Ok thank you Miss liliey . Sauke Numfashi tayi tana hada hannun ta biyu tare da daurawa a saman Table Din tana Tallabo Kuncin ta . Mtswww Dan tsaki tayi tare da cewa " I'm tired of this ....na gaji Kullum ina yi don dalili Ɗaya amma har yau na kasa archving abun da nake so dan gane da Sir Aaaryaaan . Huhhhuuuhhh Dole cikin biyu zan yi daya . Ko kissa na ya fuzge sa , ko kuma Na faɗa masa da Baki na . Saboda ....Kirar wayar ta da taji ana yi ne ya katse mata Tunanin mafitar nata . Wanda Ganin Numbern Sir Aaryaann yasa Ya saurin cire Shadow Space din fuskar ta , a kuma dai dai Nan manager na shigowa . Miss liliey kin amsa takardar Profit na yau na Wannan.... Cikin daga murya da masifa ta kalli managern tana cewa " I beg Mr Man baka ganin Daya kira zanyi ne? Ka bari mana idan na gama then we will discuss later . Sakin Baki managern yayi tare da cewa " Amma kin san Wannan shine lasisin zaman ki ma'aikaciyar wannan Companyn ko? .
Ka iya bakin ka A yanzu yallaɓai ne da kansa yake kira na Malam... Sir Aaaryaaan..? Yayi maganan cike da mamaki don yasan waye Aaaryaan baya kula Sabgar liliey sam , shi baya kaunar mace mai rawar kai to liliey kuma fa sai Dai Haƙuri . Jin da Oga Sir suke magana yasa Manager yin shiru yana kallon yanda liliey jiki ke rawa kaman yana a gaban ta .. Ok sir , I will wait for you."
Datse kirar tayi tana kallon Manager tare da ficci tana cewa " Sir Aaryaann yana hanyar zuwan sa yanzu , sannan yace " Yana da magana damu duka , PA sani Sectary sai kuma kai Manager zamu tsaya. Ok abun da Manager yace kenan tare da juyawa Yana barin mata office din . Wani irin irin farin ciki miss liliey keji har bargon jikin ta . Ohhh Allah komai da lokacin sa , Wai yau nice Sir Aaryaann ya kira , har da fada ....wani dan ihu tasa ki tana faɗin saura kirisssssss ."
**
Ɓangaren A'isha a Washe gari da Safe aka sallame su inda Duk yanda taso taga Aaaryan bata gansa ba , Driver ne ya taho ya dauke su , da mama da Kuma Mom Lubnah don itama tun safe ta taho duba jikin A'isha , sai dai muce Alhamdulillah don jiki ya warware .
Koda suka iso Gida kai tsaye part Din Mama Lantana suka nufa , tare da Shigewa zuwa ƙayataccen falon ta . Mama ne ta dafa Saman Goshin A'isha tana cewa " Bakyajin komai ko ?. Lumshe ido A'isha tayi tana budewa tare da cewa " Mama barci kawai nake Son yi . Assalamu alaikum." suka ji wani Sanyayyar murya an yi sallama ,wanda a tare suka juya suna kallon Inda Mom Aslaam ke shigo Fuskar ta Dauke da murmushi . A'a Hajiya kune Da Hantsi .? Mom Lubna tayi maganan don sun san juna ƙawaye ne Sanadin yaran nasu. Murmushi Mom Aslaam tayi tana takowa ,inda A'isha Farida ta tsaya tana sakin baki tare da tunanin Wannan matan Bahaushi ya ce kuwa ? Yanayin ta da yanayin surar ta bai kama dana yan Nigeria ba . Kuma wacece ita ? Tambayar da take ga mawa kan ta kenan a zuciya ita kadai .kana mama Lantana tace Sannu Hajiya Da zuwa ga Wuri . Yauwa Sannu Ya Ɗiyar tawa da jiki . ? Mom Aslaam tayi maganan tare da jan jiki tana zama a daya daga Cikin kujeran falon . Cigaba da Kallon ta A'isha tayi tana lissafin dukiyar da yayi kuka a jikin ta . Ko murmushi tayi hasken Gold din wuyar ta da hannayen ta su suke haskakawa . Ko ba'a faɗa maka ba ,boko ne da kuma Gayu a hade . Sai dai shigar Hausa Fulani ne jikin ta ,wato wani satin lace mai launin Milk da red a hadee Babu Tarkacen da yawa . Wanda tsadan ta ta haura Miliyan guda . Banda gwalgwalan data jera . Mayafin jikin ta ta cire tana ajewa a Gyefe tare da kallon A'isha tana faɗin " Taho Ɗiyata...!
Kallon Mama da Mom Lubna A'isha tayi kamin taji Muryar Mom Lubnah tana cewa " Momyn Aslaam ce , jeki ku gaisa ,tazo duba ki ne. Murmushi Mom Aslaam tayi tana cewa" Kuma suruwar ta , duk da idan ta Auri Aslam aje surukutan zamu yi a Gyefe ki dauke Ni mahaifiyaaaa. Wani irin bugawa Ƙirjin A'isha Farida yayi Ƙwallah na ciko idanun ta . Su Mama ta kalla wanda suma kaman yanzu ne sukaji al'amarin sabo tabbas da matsala abun da ko wannen su ke fadi a zuciyar sa kenan .
Shiru A'isha Farida tayi a ranta tana faɗin " Tabbas inda dacewa ne za'a bi Aslam ne ya cancanta , bai taba nuna mun ki ba , duk da ya taso a baiyi zaman Nigeria ba , bare kuma yasan yanda zai zauna da mutum iri na , Amma a haka soyayyar zuciyar sa bai karaya ba akai na . Shine mutum na farko da ya fara nuna mun sakin jiki da goyon baya akan duk abun da nake yi . Lumshe ido A'isha tayi tana tuno da Haduwar su ta farko a Trading Company na Naawaaz da yanda kwace ta ta hanyar bata jakar maggi . Wannan kyauta ce yayi mun wanda tun da nake babu wanda ya taba mun ,tsakani na da kowa hantara ne ,masu so na ƙalilan ne saboda hali na da rashin ji . Shiru tayi tana mai tunano Nawaaz da kuma haduwar su a mall , ni ba matan Shahararre bane , Mr Xxx , Wanda ya dauki iskancin ruwan sa Abincin sa.
Come on my baby girl 🥰 , Muryar Mom Aslaam ya katse ta ,inda a hankali ta taka tana nufar inda take . Hannu Mom Aslaam tasa tana kama A'isha tare da Rungume ta tana furta " Nice to meet you my daughter ya jikin naki, Ya warware ko?. Zama A'isha tayi a hankali a gyefen ta tare da murmushi tana faɗin " Alhamdulillah Mommy . Good Mashaallh " . Juyawa Mama Tayi tana cewa " Bari a kawo maki Lemu da Ruwa Hajiya . Kamin su cigaba da fira da Momy Lubnah suna dan taɓawa sama sama tare da Dan darawa . Murmushi Mom Aslaam tayi tana cewa " Kin tuna Shakiyin Yaron nan Aaaryaan shekarun baya yazo yana cewa " Yayi mata .!
Jin wannan furuncin nata yasa A'isha Saurin kallon ta , Dariya Mom Lubnah tayi tana cewa " Kwarai fa har da fadin Wai ita Makauniya ce yake tunani bata Gani , shi fa da Gaske at that time Kaunar yarinyar yake ,ko shakiyanci ne irin nasa oho ,yanzu dai ai baya maganan wani shekara ma......" Dariya suka keche dashi a tare suna haɗa hannu Mom Aslaam na cewa...........!
```FƳAAƊE.!```
*(Erotic and Sympathetic Story)*
Ayshatou Mamanteddy
***35-36***
*SUFY'S PRINT GRAPHICS DESIGN*
🏷️ PROVIDING A RANGE OF CONTEMPORARY AND TOP NOTCH CREATIVE DESIGN.....
*📍 OUR SERVICES*
✒️LOGO DESIGN
✒️LOGO PACKAGE
✒️ FLYER DESIGN
✒️ BIRTHDAY FLYER
✒️ INVITATION CARD
✒️ADVERT VEDIO
✒️ DIGITAL INVITATION
✒️ STICKERS DESIGN
✒️AND LOTS OF
📝DM NOW....TO GET A TOP NOTCH ATTRACTIVE AND PROFESSIONAL DESIGN
Whatsapp:07045125150
Thanks you for choosing us nd we appreciate refferals 🥰🤗.
**
A hankali A'isha Farida ta janye Jikin ta daga wurin tana Miƙewa ba tare da tace masu komai ba ta nufi Dakin ta , Hankalin ta a tashe . Zuciyar ta na buga mata da ƙarfi da ƙarfi . Shigar ta Bedroom din yasa ta saurin rufe kofar tana saka key , A hankali tamkar mara jini a jika ta nufi Ƙayataccen Gadon ta tana Faɗawa tare da fashewa da Wani irin kuka mai tattare da rauni da tsuma zuciya . Kuka take tana cira tamkar wacce take ban kwana da duniya . Wanda ta dauki tsawon lokaci tana yin shi ,kamin daga Bisani wani nannauyar barci yayi Gaba da ita mara dadi .
Ɓangaren su Mama kuwa Ganin A'isha ta mike yasa Mama Lantana buɗe baki zata yi mata magana , Amma sai Mom Aslaam ta dakatar da ita ,tare da cewa " barta ta Huta , kin san jikin majinya ta . Indai don Nice to Yanzu muka fara Haɗuwa da A'isha , Nan gaba kadan ma Sirika zata zama gare Ni ai . Murmushi su Mama suka yi kana mama ta zauna suna cigaba da taba hirar tasu ta manya . "